Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fara hawa kan step itama tana tsoran kar taje momy ta had'a da ita.

Ruma tana hawa sama bata tsaya ko ina ba sai bedroom d'in su tana zuwa taga basa ciki, futowa tai ta wuce bedroom d'in momy. Ruma tana nufar bedroom d'in momy taji abdul yana kiran sunan momy cikin tashin hankali. Da sauri ruma ta shiga tana shiga taga rukee kwance jini yana butowa ta hancinta sai nunfarfashi take. 6angare guda kuwa momy ce sume a wajan.

Dora hannu ruma tai ta fasa uban iwu tare da qarasawa wajan rukee tana girgiza ta, aunty rukee! Aunty Rukee ki tashi momy tai ce tai miki dukan nan shikenan momy zaki kashe min 'yar uwa da duka. Mashkhur kuwa da yake qasa iwun da yaji ne yasa shi miqewa ya haye sama da sauri.

Yana zuwa bai tsaya ko ina ba sai d'akin momy yana shiga shima yaga rukee kwance a qasa tana nunfarfashi sai kiran sunan ALLAH take da annabi, tana kalmar shahada. Gefe guda momy ce kwance kamar matacciya. Cikin tashin hankali mashkhur yace abdul lafiya?. Shima abdul cikin tashin hankali yace, da na shigo dai naga rukee tana ta tari, momy ta riqeta tana kuka ban sai mai ya same taba.

Daga qarshe kuma da momy taga jikin rukee yayi tsanani shine ta sume. Haba abdul ai yanzu 6ata lokaci muke kawai ka taso mu kai su asibiti. Ruma jeki ki kira ammi mashkhur ya fad'a yana kallan ruma. Ba musu ruma ta miqe cikin tashin hankali ta nufi part d'in ammi. Zahra, ilham, faruq, haidar ameer, suna zaune a kan draining suna shan fura da nono. Hjy kaka da ammi suma suna gefe akan kujera suna shan tasu.

Ruma ce ta shigo a guje tana kuka, cikin mamaki ammi tace ruma lafiya kika shigo ko sallama babu. Cikin kuka tace ammi yaya mashkhur ne yace na kiraki momy da ruma basu da lafiya mutuwa zasuyi, abinda ruma ta iya fad'a kena ta juya a guje tabar d'akin. Cikin tashin hankali ammk ta miqe tabi bayan ruma.

Itama hajiya kaka miqewa tai tafi bayan ammi, su haidar da su ilham kuwa suma nan da nan suka fara 'yar rige-rige miqewa daga draining suka bi bayan su ammi hankali tashe. To su ammi suna qarasawa part d'in momy hankali tashe suka shige basu tsaya ko ina ba sai sama, suna hawa sama suka wuce bedroom bedroom d'in ammi.

Su ammi da hajiya kaka harma da sauran yaran gidan hankalin su ya tashi sosai da sosai. Cikin tashin hankali ammi tace mashkhur da abdul mai kuke jira ku tashi a kai su asibiti mana. Abdul cewa yayi aa ammi sai dai a kai rukee amma momy suma tai, tashin hankali abinda ya samu rukee ne yasa ta suma. Ammi kallan faruq tai tare da cewa faruq d'auko ruwa a zuba mata.

Ko kuma abdul ku d'auki rukee ku kai ta asibiti tana cikin matsanan cin hali fa. Ba 6ata time abdul ya d'auki rukee tana mashashara, suka fuce shida mashkhur a hanzarce. Su mashkur suna fita faruq ya dawo hannu riqe da bottle d'in ruwa jiki na rawa ya miqawa ammi. Da sauri ammi ta kar6a bottle d'in ruwan ta bud'e sanan ta fara shararawa momy a jiki da fuska.

Wata iwar qara momy ta saki tare da cewa! Na shiga uku wayyo rukee ta na kashe 'yar ta da hannuna. Cikin tashin hankali hajiya kaka tace halima mai kikayiwa jiki ta haka?. Hankali kowa ya tashi sabida jin furicin da momy take. Momy kuwa nan da nan ta dawo cikin hayyacin ta da taji hajiya kaka tana mata tambayar nan.

Itama ammi sake watsawa momy tambaya tai da cewa! Halima mai kikayiwa rukkayya?. Baki na rawa momy tace maganin 6era na zuba a kifi shine ta shigo taci batasan na zuba magani a ciki ba, ni kuma ina kicin a lokacin,, momy ta qarasa magar tana fashewa da kuka. Nan da nan hankalin kowa ya sake tashi masu kuka nayi masu salati nayi.

Muryar momy tafi ta kowa qara a wajan nan sabida tsabar tashin hankali ita kad'ai tasan a wana hali take. Ammi cikin tashin hankali ta d'auki wayar momy ta fara draining d'in number dady domin sanar da shi halin da ake ciki. Kowa hankalinsa a tashe yake musaman ma momy abin ba'a cewa komai wani irin ihu take zuciyar ta kamar zata fashe haka take ji.

To fah haka kowa yayi carko-carko a bedroom d'in momy har dady ya dawo gida. Lokacin da dady ya dawo yayi ta kiran su mashkhur, da abdul a waya amma basa d'auka ba da yake wayar a gida suka barta. Anaso abi su mashkhur asibiti dan ganin halin da suke ciki amma ba'a san wana asibiti suka tafi ba. Ana haka aka fara kiran sallah magriba, dady miqewa yayi tare da su haidar suka wuce masallaci.

Suma su ammi ala dole suka koma part d'in su domin yin sallah cike da tashin hankali. Dama momy ba dalili take qin yin sallah ina ga dalili ma ya samu. To fah su dady suna futowa daga masallaci motar su mashkhur ta shigo cikin gidan a guje da yake get d'in gidan a bud'e yake. Dady da su haidar da sauri suka qasa wajan motar su mashkhur d'in dan jin mai ke faruwa.

Mashkhur yana shigowa gidan koh parking bai tsaya yi ba ya kashe motar ya futo. Yana futowa dady ya qaraso shi da su faru, dady kallan mashkhur yayi tare da cewa! Mai sunan baba ya jikin rukkayya?.

Ido jajir mashkhur yace innalillahi'wa'inna'ilaihirraji'un. Dady Allah yayiwa rukee cikawa kullu nafsin za'ikatul maut. Mashkhur yana gama fad'in haka ya bud'e bayan motar tare da d'auko rukee ya sa6ata a kafad'a ya cige da ita cikin gidan.

Dady kuwa jinjina kai yayi cikin matsanancin tashin hankali yace ALLAH ya jiqanki rukkayya dama kowa tasa yake jira. Haidar da faruq kuwa kafin kace mai tuni sun fashe da kuka mai sauti sai kace ba maza ba. Abdul kuwa jiki a sanyaye ya futo daga motar tare da kallan su haidar yana cewa! Ku sai kace ba maza ba addu'a za kuyi mata ba kuka ba ku tawo mu shiga ciki.

Haka abdul da su haidar suka bi baya dady jiki a sanyaye amma har lokacin su haidar basu dena kurma iwu ba. Mashkhur kuwa yana qarasawa cikin gidan ya wuce babban falon gidan na kowa da kowa ya kwantar da rukee a qasan carpet. Haidar da faruq kuwa basu tsaya ko ina ba sai part d'in ammi suna shiga su ammi suka tawo a guje saka makwan jin sautin kukan nasu.

Cikin tashin hankali ammi tace faruq lafiya kuke kuka? . Cikin shasheqa haidar yace ammi rukee ta mutu. Nan da nan waje ya d'imame da salati,. Ita kuwa ruma wata uwar qara ta saki tare da fad'uwa qasa sumammiya. Amma ina ba wanda ya kula da ruma ta sume dan kowa ya kama gaban sa dan zuwa ya ganewa idan sa gaskiyar zance.

Faruq kuwa yana qoqarin fita ya hangi ruma baje a sume. Jiki na rawa ya nufi firinji ya d'auko ruwa mai sanyi ya zuba mata. Ruma tana tashi ta sake kwarara uban iwu tare da cewa! Ya faruq ina 'yar uwata take qarya kuke bata mutu ba koh. D'ago ta faruq yayi tare da ruqo hanun yana cewa zo muje. 6angaran dady kuwa bai tsaya ko ina ba sai part d'in momy, yana zuwa ya shiga d'akin ta.

Kwance ya ganta tana ta rusa uban iwu. Cikin murya mai ciki da damuwa yace halima. Da sauri momy ta tashi tare da cewa su mashkhur d'in sun dawo ya jikin rukee?,. Girgiza kai dady yayi tare da cewa, halima nasan ke ba mai tawakkali amma dan ALLAH kiyi haquri abinda nake so nace miki kullu nafsin za'i katul maut. Cikin tashin hankali momy ta miqe tsaye tare da cewa! Dadyn abdul mai kake nufi?.

Jinjina kai dady yayi tare da cewa ALLAH ne ya bamu rukkayya kuma yafi santa akan mu dan haka ALLAH ya d'auke abar sa. Wani uban iwu momy ta sake tare da danna wani uban ashar tana cewa qarya ne wlh rukee tana nan bata mutu ba ni nasan mafarki nake. Jinjina kai dady yayi tare da cewa! To dama ai ke baki da tawakkali in kin gama kukan kije ki ganewa idanun ki gawar ta tana babban falo.

Dady daga haka ya kama hanya domin fita daga part d'in momy. Momy wani uban iwu ta saki tare da cewa! Abubakar karka sake cewa 'ya ta gawa wlh bata mutu ba, daga haka momy ta kwasa a guje domin zuwa ta ganewa idanuwan ta. Dady kuwa jinjina kai yayi tare da cewa! ALLAH ya kyauta ALLAH ya jiqanki rukkayya yasa kin huta.

Sanan yafi bayan momy zuciya cike da jimamin rashin d'iyar sa rukee. Hhmmm tsayawa gayawa masu karatun lattafin ADALILINTA, tashin hankali da iyalan gidan alhaji abubakar suka shiga wlh sai mu shafe page d'aya har mu tafi double page ban gama gayawa masu karatu lattafin ADALILINTA ba. Dan sun shiga tashin kololuwar tashin ankali sosai musamman da sukayi tozali da gawar ruma.

A gidan nan wadda basuyi kuka ba su biyu ne daga dady sai mashkhur kukan zuci kawai sukeyi wadda akace yafi na fili ciwo. Shima abdul ba wani kuka yayi ba kawai dai hawaye sun zubo mai ne. Momy kuwa sau uku tana suma tana farfad'owa sabida bama iya tashin hankali ta mutuwar rukee ba harda fargabar mai zai samu abdul.

Kaf gidan nan ba wadda ya rintsa sai ameer kowa kwana yayi akan gawar rukee, masu yi mata salati nayi masu karanta mata qur'ani sunayi dan so suke zuwa gobe kafin a kai ta makwancin ta su sauke mata qur'ani, dan tun dare ammi da hajiya kaka sukayiwa rukee wankan gawa suka suturtata a cikin farin likkafani.

Tofa washe gari bayan kowa yayi sallah asubayi haka suka dawo suka cigaba da yiwa rukee karatun qur'ani dan har a tsakanin su, sun kusan sauke mata qur'ani. Dady yaso a kai rukee da wuri amma ina hakan bai samu ba, dan har sai da haka fara qoqarin shiga masallacin jumma'a. A lokacin ma har an gama karance mata qur'ani tass.

To haka aka fita da gawar rukee cikin makara nan ma zukaga hauka wajan momy su zahra kuwa kuka da birgima kamar suma zasu mutu ruma kuwa sai da ta sake sumewa. To bayan an gama sallah jumma'a aka sallaci gawar rukee, kai ba laifi rukee ta samu mutane sosai da yake babban masallaci ne gashi ta samu ranar jumma'a, duk da dai ba acikin ranar ta mutu ba, amma da alama ta samu rahma ba gashi dama in ka mutu ranar jumma' a ko aka kai ka ba tambayar kabari.

Bayan an gama yi mata sallah aka rankaya domin kai ta makwancinta na gaskiya.
6angaran su ammi kuwa sun duqufa suna bawa momy haquri sabida momy kusan haukacewa tai, sai wani uban iwu take kurmawa. Kafin kace kwabo tini gida ya cika fam da yan uwa da abokan arziki. Duk 'yan uwan momy sun zo harda mahaifiyar ta amma badda saratu wadda itama tana can hankali a tashe dan har yanzu bata san masababin mutuwar rukee ba da yake momy bata cikin hayyacin da zata yi mata bayani ko waya basuyi ba.

Dan abakin mahaifiyar su saratu tace rasuwar, saratu tana son zuwa amma tana tsoran dady dan tun sanda ya koreta daga gidan har yau bata sake dawowa ba. Abdul kuwa suna dawowa daga kai rukee maqabar ta ko zaman makoki bai tsaya ba ya wuce d'aki ya kwanta saka makwan kansa da yake sarawa ga jikin sa duk ya mace............

Hmmmm shiyasa akace in zaka gina ramin mugunta gina shi dai-dai da kai dan watarana kana iya fad'awa. Yanzu dai muguntar da momy ta shirya ta fad'a kan ta. Waii to ALLAH ya jiqanki rukkayya.

Karfa masu karatu su manta boka yacewa momy kwana goma da mutuwar zahra mashkhur zai bita. To ga asirin zahra ya fad'a kan rukee, gana mashkhur ya fad'a kan abdul. Karku manta abdul yasha zo6an asirin momy mai makwan mashkhur yasha. Hmmm kuna ganin abdul zai cigaba da rayuwa nan da kwana goma kuwa? 😭😭😭 wayoo abdul d'ina mai kyakyawan hali da farar zuciya. 😭😭😭😭

Yau iya abinda zan iya kawo muku kenan sabida nima naji mutuwar Rukee😭😭😭😒😒😒😒😒😒...............

Mu had'u a next page gobe.

ADALILINTAπŸ’œβ€πŸ’œ

BY AMINA BAYEROπŸ’œβ€πŸ’œ

typing..........

*page 102*

Abdul kuwa suna dawowa daga kai rukee maqabar ta ko zaman makoki bai tsaya ba ya wuce d'aki ya kwanta saka makwan kansa da yake sarawa ga jikin sa duk ya mace............

To fa mutan gidan sunyi kuka har sun gaji da kukan sun dan gana. Abinci ma dai kam ba kowa ne yake iya ci ba a cinki gidan sai 'yan zaman makoki, lokaci guda mutan gidan sunyi zuru-zuru musamman momy wadda ta zabge ta rame sosai da sosai. Kana ganinta zaka she da tana cikin damuwa Lokaci guda duk tabi tayi sanyi.

6angaran abdul kuwa daurewa kawai yake yana qarfin hali, dan cutar cin shi take a hankula, duk yabi ya rame, amma kowa sai yake tunanin jimamin mutuwar rukee ce dan haka ba wanda ya damu sosai. To kwanci tashi ba wahala har anyi sadakar ukun rukee, kuma ranar da aka cika sadakar uku kowa ya watse ya koma gida, mahaifiyar momy ce kawai bata tafi fa.

Nights............

Mashkhur yana kwance a bedroom d'in shi akan bed yaji wayar shi tana ringing. Hannu mashkhur yasa ya janyo wayar tare da zubawa mai kiran ido. Sunan dady mashkhur ya gani a hanzarce mashkhur ya d'aga wayar ya kafa a kunne. Tare da cewa! Hallo dady, ina jiran ka kazo ka same ni a 6angare na. Tom dady ga ninan zuwa, daga haka mashkhur ya kashe wayar sanan ya miqe ya zura takalmansa ya fuce daga bedroom d'in shi.

Mashkhur yana fita shima abdul yana bud'e room d'in shi yana futowa. Da kyar abdul yake iya tafiya sabida yana jin jiki ba laifi. Kallansa mashkhur yayi tare da cewa, abdul haka jikin naka ya koma. Murmushi qarfin hali abdul yayi tare da cewa, hmm yaya mashkhur kenan mai ka gani?. Cikin mamaki mashkhur yace kaga yadda kabi ka rame kuwa lokaci guda haba abdul addu'a rukkayya take buqata ka dena sawa kan ka damuwa.

Wani dogwan nunfashi abdul yaja tare da cewa wlh yaya mashkhur ba mutuwar rukee ce take damuna ba nima kai na nama rasa mai yake damuwa kawai cuta nake a tsai tsaye inajin ciwo sosai. Cikin tausaywa mashkhur yace sannu ko nazo mu tafi asiniti ne?. Girgiza kai abdul yayi tare da cewa, ka brri zuwa gobe in ban warware ba sai mu tafi.

Jinjina kai mashkhur yayi sanan yace yanzu ina zaka haka ka futo ka koma ka kwanta ka huta. Girgiza kai abdul yayi tare da cewa, ina son shiga ciki sabida ina son ganin zahra da ammi. Jinjina kai mashkhur yayi cikin tausaywa yace to zawo mu fita nima wajan dady zani. Daga haka mashkhur da abdul suka fita suna hira, duk da kuwa abdul qarfin hali yake maganar ma da kyar yake bare tafiya kamar zai fad'i haka yake ji.

Suna zuwa qofar part d'in ammi abdul ya shige shi kuma mashkhur ya wuce part d'in dady. Mashkhur yana shiga part d'in dady tun kafin ya hau sama ya tarar da dady zaune a falo yana kan kujera yana karanta AL QUR'ANI baki d'auke da sallama mashkhur ya qarasa ya zauna a kujera yana jiran dady ya kai aya.

Dady yana kai aya ya ajiye qur'ani tare da kallan mashkhur. Cikin ladabi mashkhur ya sake gai da dady, bayan dady ya amsa ya fara korawa mashkhur baya ni kamar haka!?. Mai sunan baba zuwa gobe in ALLAH ya kai mu zaka tafi abuja domin kai ta kaddun ka, sabida samun gurbin aiki. Jinjina kai mashkhur yayi tare da cewa, amma dady sai nake ganin ko za'a bari sai anyi sadakar bakwan rukkayya, kaga yau akayi sadakar uku gashi kamar naga abdul bashi da lafiya yana jin jiki sosai.

Girgiza kai dady yayi tare da cewa, tun kafin rukkayya ta rasu nake son tafiyar ka, amma ALLAH bai yiba, yanzu na gama magana da su gobe in ka isa lafiya zaka kai musu takaddun bai fi kai kwana biyar ba ka dawo, kuma wanda ya mutu ya riga da ya mutu, rukkayya addu'a kawai take buqata a gare ku, kuma zuwa gobe ni da kai na zan raka abdul asibiti suk da nasan damuwa ce kawai ta rashin rukkayya ce take damun sa.

An sai ma ticket zuwa gobe da safe jirgin ku zai d'aga. Jinjina kai mashkhur yayi tare da cewa tom shikenan dady ALLAH ya kaimu goben. Daga haka dady da mashkhur sukayi sallama mashkhur ya koma bedroom d'in shi zuciya cike da jimamin rukee da kuma rashin lafiyar d'an uwan sa abdul......

ABDUL............

A hankula ya qarasa babban falon ammi, zahra ya gani zaune da ilham da hajiya kaka sunyi shiru. Da kyar abdul ya iya qarasawa wajan zahra ya zauna tare da cewa zahra ta ya haquri. Murya a dashe zahra tace da gudiya tare da d'agowa ta zubawa yaya abdul ido. Kafin zahra ta kai da magana hajiya kaka tace abdul kaga yadda kayi zuru-zuru lokaci guda ka rame ka dena sa damuwa a ranka haka duk mai rai ai mamaci ne muma tamu muke jira.

Jinjina kai abdul yayi tare da cewa gaskiya ne hajiya kaka in sha ALLAH zan kiyaye. Zahra kuwa cewa tai sannu yaya abdul, Murmushi abdul ya qaqalo tare da cewa yauwa zahra ta. Ilham cewa tai dan ALLAH yaya abdul ka dena sa damuwa a ranka haka wlh duk kabi ka rame. Murmushi abdul yayi tare da cewa, ke ilham nifa ba abinda yake damuwa ina da zahra a duniya mai zai dame ni abdul ya qarasa maganar yana kashewa zahra ido d'aya kamar ba wanda yake jin jiki ba.

Murmushi zahra tai tare da cewa ai kuwa dai yaya abdul nima in ina da kai ba abinda zai dame ni. Jinjina kai hajiya kaka tai tare da cewa kai wanan qauna dai taki kullum bata tsofa gaskiya dai mai sunana in kika haifi d'a namiji ki samai sunan abdul. Murmushi zahra tai tare da cewa kai hajiya kaka sai dai in kika haihu a samai ai kece akan hanya.

Duk da kowa yana cikin jimami amma sai da suka dara har abdul d'in. Da kyar abdul ya miqe tare da cewa ina ammi take tana sama kuwa?. Zahra cewa tai ehh tana sama ko dai yaya abdul nazo na riqe ka karka fad'i nai asara wlh. Murmushi abdul yayi tare da cewa, kiyi zaman ki baby na zan iya hawa karma ki wahalar da kan ki.

Tom shikenan yaya abdul d'in na kabi a hankula zahra ta qarasa maganar tana gyara zama. Abdul kuwa tafiya ya farayi tare da cewa tom shikenan zanyi yadda kike so. Daga haka ya kama hanya steps ya fara hawa da kyar, abdul yana d'aurewa ne kawai amma da kyar yake iya d'aga qafar sa ga step d'in da tsayi ba laifi.

Ko da abdul ya gama hawa step d'in sai da ya huta sosai sanan ya kama hanyar bedroom d'in ammi. Abdul yana zuwa ko tsayawa knocking d'in qofar ba yi ba ya murd'a handel d'in da kyar sanan ya sa kai ya shiga baki d'auke da sallama. Ammi da take kan gado tana jan carbi, fuska a sake ta amsawa badul sallamar.

Amma tana ganin yadda ya koma gabanta ya fad'i rass sabida raban ta da ganin abdul d'in tun ranar da aka kai rukee makwancin ta na gaskiya. Cikin damuwa ammi tace abdul mai yake damun ka haka, da kyar abdul ya iya qarasowa kusa da ammi ya zauna Cikin murya mai ciki da larura yace hmm ammi bana d'an jin dad'i ne ya qarasa maganar yana d'an kwanciya a kafad'ar ammin.

Cikin damuwa ammi ta ruqo abdul jikin ta tare da cewa, abdul ka dena sa damuwa a ranka addu'a ya kamata kai wa rukee ita kad'ai take buqata ka dena damun kanka haka kaga lokaci guda yadda ka zabge ka rame ka da na sanka da tawakkali kuma?. Ammi ta qarasa maganar tana shafa bayan abdul. Ajiyar zuciya abdul yayi tare da cewa ammi wlh ni ka d'ai nasan mai nake ji a cikin jiki na amma ba damuwar mutuwar rukee ce take damuna ba.

Cikin tashin hankali ammi tace abdul kamar ya baka san mai yake damun ka ba ko dai a kai ka asibiti ne. Girgiza kai abdul yayi tare da cewa ammi ki bari zuwa gobe in ban samu sauqi ba sai a tafi asibitin koh?. Jinjina kai ammi tai tare da cewa amma dai kaci abinji? Girgiza kai abdul yayi tare da cewa yau kwana na uku kenan bana iya cin abinci sai da ruwa ko tea.

Da sauri ammi ta janye shi daga jikin ta tare da cewa bari naje na kawo ma abinci, haba abdul kwana uku baka ci abinci ba ba dole ka rame ba. Daga haka ammi ta fuce daga bedroom d'in. Ammi ta d'auki 30 minutes kafin ta dawo bedroom d'in hannu riqe da tire. A cikin tire d'in cup d'in tea ne sai plate d'in indomie da soyayyan kwai.

Baki d'auke da sallama ammi ta shigo bedroom d'in, tana shigowa ta ajiye tire d'in a table, sanan ta tai makawa abdul ya miqe zaune. Bayan ya zauna ta fara bashi tea da indomie a baki. Duk da abdul baya sha'awar cin abinci amma haka ya daure ya ringaci. Kad'an abdul ya iya cin abinci, ammi tayi-tayi yacinye amma ya kasa ci, haka dai dole ammi ta haquri ta fitar da tire d'in ta dawo.

Lokacin data dawo sai taga kamar jikin abdul ya sake rikicewa. Ammi taso dai akai abdul asibiti cikin daran nan amma dady yace a bari sai zuwa da safe. Haka ammi ta zauna tai ta karantawa abdul addu'a'i har dai baccin wahala ya kwashe shi. Ita haka ammi ta kwanta a kusa da abdul d'in zuciya cike da tausaya mai har bacci yayi awan gaba dashi.

Washe gari.

Misalin qarfe takwas ahmad ya zo d'aukar mashkhur domin kai shi airport, haka mashkhur ya tafi zuciya ba dad'i, ga yadda hankalinsa ya tashi dan ganin jiki abdul ya sake rikicewa. Mashkhur yana tafiya aka tafi kai abdul asibiti. Gidan duk sai yabi yayi jigum ba dad'i, momy hankali ya sake tashe tana jira su dady su dawo ko likitoci zasu samu su shawo kan cutar abdul.

Misalin qarfe goma aka

Please Login or Register in order to submit comment