Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

raban daya sha wani nau'in kayan maye? Harma ya mata, haka nan yaji yana mugun sha'awar shan su, dan haka miqewa yayi ya bud'e dirowar ya kwaso kwayoyin, da magagunan mura. Yau dai mashkhur ka d'an ya sha bai yi overdose ba, yana gama sha yabi lafiyar gado ya kwanta.

Washe gari........

Ahmad da safe yazo yayi ta buga qofar mashkhur amma ina yaji shiru, ahmad duk da bai gani ba" amma yasan shaye-shayen banzan nan mashkhur yayi dan haka ba 6ata lokaci yayi wucewar shi asibiti.
6angarn mashkhur kuwa bashi ya tashi daga bacci ba sai misalin qarfe goma na safe.

Jiki ba kwari mashkhur ya miqe ya shige toilet yayi wanka, sanan ya futo ugu d'aure da towel, yana fitowa bai nufi ko ina ba sai kan merro, yana zuwa ya zauna akan kujerar merro, tare da zubawa face d'in shi ido ta mudubi. Nan da nan mashkhur ya fara tambayar kan shi wai sabida mai ya kasa dena shaye-shayan nan?, a da in da akwai abinda mashkhur ya tsana game da mutum shaye-shaye ne amma sai gashi yanzu ya tsinci kansa a wanan halin.

Hmm ya zama dole na hana kai na shanye-shayen nan, dan ina gab da lalata rayuwa tavwlh ko zan mutu sai na dena shaye-shayen nan mashkhur ya fad'i hakan a zuciyar shi. Haka dai ya miqe jiki ba kwari ya fara sa kayansa, bayan ya gama sa kanyan, falo ya nufa ya had'a t ya fara sha, yana sha yana tunanin yanda rayuwar shi zata kasan ce. Mashkhur tunani ya fariyi akan rayuwar shi zata koma dai-dai, yana rabuwa da zahra zai fara rayuwa mai 'yanci da dad'i.

Ina miqa dubun godiya ga masoyana masu bibiyar littafin ADALILINTA, ina yi muku fatan alkhairi a duk inda kuke,, kuma in sha ALLAH ina sa ran a ciki wanan watan October d'in zan kammala rubuta littafin nan qarshan watan October ko kafin ma ya qare..............

Mu had'e a next page.

ADALILINTA💜❤💜

BY BAYERO💜❤💜

Typing...........

*page 84*


Miqewa mashkhur yayi ya koma bedroom ya dauko wayar sa tare da kunna ta, ai kuwa mashkhur yana kunawa sai ga kiran dady ya shigo kamar dady jira yake ya kunna wayar. A aljiwu ya mashkhur ya zura wayar sanan ya d'auki key d'in gidan ya fuce abinsa. Yana fita ya nufi motar sa ya tayar ya fuce daga gidan a guje. Har ya d'au hanyar titi yaji wayarsa tana qara ringing, duk da mashkhur bai duba ba yasan dady ne yake kiran sa,.

Cigaba da tafiya yayi ba tare da ya d'auki wayar ba, badan komai Mashkhur yaqi d'aukar wayar ba sai dan yasan dady haka zai ce ya bawa zahra wayar,, kuma mashkhur yana tsoran zahra ta gayawa dady abinda yake faruwa. Cigaba da tafiya mashkhur yayi yana tinanin ya zai shawo kan matsalar nan?. Yana cikin tunanin nan sai yaji wayar tasa ta sake ringing a karo na uku kenan.

Jiki ba kwari mashkhur ya ciro wayar ya d'aga tare da sata a hand's free ya ajiye ta a geba,, sanan ya d'an rage gudun motar. Sallama'aikum dady ina kwana, da kyar dady ya iya amsawa da cewa! Lpy qalau, wai mashkhur sabida mai kake rabamin hankali nane?,, wata siririyar ajiyar zuciya mashkhur ya saki tare da cewa! Dady raba hankali kuma?.

Cikin fad'a-fad'a dady yace kwarai kuwa tun yaushe nace ka had'a ni da mamana a waya kaqi yaushe raban da muyi waya da ita, duk duk kabi ka d'agawa kowa a gidan nan hankali?. D'an shafa gefan kansa mashkhur yayi da hanun hagu tare da cewa tom dady yanzu ina hanya na kusan komawa gida amma ina kowa gidan in sha ALLAH zan had'a ka da ita kuyi magana.

Tom shikenan ALLAH ya kai ka lpy in ma baka bugomin ba, zaka tsince ni a rasha wlh, naga waca wai nai kake toyawa. Dan zaro ido mashkhur yayi tare da cewa! Haba dady yanzu sai kazo rasha akan wanan qaramin abun muma ai mun kusan dawowa. Dady kuwa cewa yayi yo to ai ba sai nazo ba na ganewa idanuwa na abinda yake faruwa, ai wanan sai ka samu a cikin zargi.

Kuma maganar dawowa kullum haka kake cewa kun kusan dawowa, wai ni mai ya hanakh dawowa ne bayan ka gama jarabawa. Am dady kasan ban kar6o result d'ina ba shi yasa,. Tom ALLAH yasa muga alkhairi a cikin result d'in, murya a sanyaye mashkhur yace amin, daga haka dady ya kashe wayar mashkhur kuma ya cigaba da tafiya zuciya cike da jimamin taya zai had'a zahra da dady, suyi waya?.

To da wanan tunanin mashkhur ya isa asibiti, yana isa ya wuce d'akin da aka kwantar da zahra yana zuwa yaga ahmad tsaye a bakin qofa hannu riqe da waya. Da sauri mashkhur ya qaraso tare da cewa! Ahmad lfy na ganka anan ka tsaya a baki qofa?, hmm wlh mashkhur da akwai matsala, yanzu kai nake qoqarin kirama sai gaka,, da sauri mashkhur ya zaro ida, tare da dafe qirji yana cewa! Matsala kuma ahmda, matsalar me?.

Gyara tsayuwa ahmad yayi tare da cewa! Tun da nazo asibitin nan zahra take ta faman kuka akan sai na had'a ta da dady, sunyi magana a waya, ba irin rarrashi da ban baki da banyi mata ba amma sam taqi yadda. Ajiyar zuciya mashkhur ya sauke tare da cewa! Hmm nima yanzu dady yayi min waya akan sai na had'a su sunyi magana da ita.

Jinjina kai ahmad yayi tare da cewa! To yanzu ya kake ganin za'a yi?. Jim mashkhur yayi can kuma yace kawai kaje ka rarrasheta kace mata zaka had'a ta da dady amma karta gaya mai abinda ya faru, nasan tana ganin mutuncin ka zata yadda da hakan. Shiru ahmad yayi can kuma yace! To mashkhur bari na gwada ALLAH yasa ta yadda dani dan yanzu naga kamar laifin ka ya fara shafata a wajan zahra.

Daga haka ahmad ya shiga bedroom d'in, yana shiga a zaune ya samu zahra fuskar nan tata fa kunbura tayi ja alamun taci kuka harta qoshi. A hankula ahmad ya zauna a gefan kujera da take kusa da gadan ta tare da cewa! Tom shikenan zan biga mai amma dan ALLAH zan roqeki alfarma d'aya qanwata kiyimin. Da kyar zahra ta iya d'aga kai tare da cewa inaji.

Yauwa qanwata dan ALLAH in kukayi waya da dady kar ki gaya mai abinda ya faru kinga zaki d'aga mai hankali sosai, dan ALLAH kiyi haquri kawai kice wayarki ce ta samu matsala shi yasa. Jim zahra tayi kafin tace tom shikenan yaya ahmad amma gaskiya ko ba yau ba sai na gaya mai, gyad'a kai ahmad yayi tare da cewa! Ehh ki gaya mai amma ki bari sai kin samu sauqi kun koma nigeria.

Murya a sanyaye zahra tace tom shikenan, sosai zahra ta sake birge ahmad a zuciyar shi yace lalai zahra tana da kyan hali ga haquri ga sauqin kai. Daga haka ya miqe yace tom bari naje ina zuwa,, ahmad yana fita ya hangi mashkhur ya tafi duniyar tunani,. Qarasawa ahmad yayi tare da dafa mashkhur yana cewa! Mashkhur!!.

Firgigit mashkhur ya dawo daga tunanin daya tafi, tare da kallan ahmad yana cewa! Ahmad ya kukayi da ita ta amince?. Murmushi ahmad yayi tare da cewa! Ai kasan zahra bada ga nan ba tana da sauqin kai da haquri, harta amince. Shima mashkhur d'in murmushi ya saki tare da cewa! Alhamdulilah, ahmad kuwa cewa! Yayi dakata, ai bawai cewa tai bazata fad'a gaba d'aya ba, tace ko ba yau ba sai ta fad'awa dady.

Nikuma nace kawai ta bari sai kun koma nigeria sai ta gaya mai, in kuma kafin nan ka rarrasheta ta haqura shikenan. Fuska a sake mashkhur yace karka damu in sha ALLAH ma bazata fad'a ba ai bata da surutu, kamar ilham. Ahmad kuwa yana ji mashkhur ya ambaci sunan ilham yaji wani farin ciki ya sake lulu6e shi,, amma sai ya d'an maze dan kar mashkhur d'in ya gane, yace yanzu ka shiga ka bigawa dady sai ka had'a su.

Daga haka mashkhur ya wuce bedroom d'in" shi kuma ahmad ya zauna akan sit d'in wajan ya fara qoqarin bugawa gimbiyar sa ilham. 6angaran mashkhur kuwa yana shiga bedroom d'in ya qarasa kan gadon zahra tare da zama a gefan ta, da sauri zahra ta had'e rai tare da juyar da fuskar ta gefe. Sau d'aya mashkhur ya kalle ta sanna ya kawar da kai tare da cewa! Ya jikin naki?.

Sai da zahra ta d'au 'yan sakanni kafin tace da sauqi, shima kamar an mata dole ta iya fad'in hakan. Mashkhur kuwa bai damu da hakan ba sabida bai ma yi zatan zata amsa ba, sabida shi in da sabo ya saba da shariyar da take nuna mai. Waya mashkhur ya zaro tare da cewa! In dady ya tambaye ki ina wayarki kice mai, ta fad'a bayan drowar kicin.

Sanan kuma in ya tambaye ki mai yake damunki kice mai zazza6i da ciwan kai kike. Shiru zahra tai ba tare da ta amsa ba, sai da mashkhur ya sake cewa! Kinji koh? Sanan ta iya d'aga kai alamun eee. Jiki a sanyaye mashkhur ya fara qoqarin kiran dady, dan yadda yaga alamun zahra,, beyi tinanin zata iya rufamai asiri kamar yanda yake tunani.

Yana buga wayar ya sata a hand's free bigu uku wayar tai dady ya d'auka, mashkhur ne ya fara magana da cewa! Hello dady na qaraso gidan gatanan zan had'a ka da ita. Zahra kuwa d'agowa tai tare da watsawa mashkhur wani kallo banza wanda shi kansa bai san mene fassarar shiba, nan ma jikin mashkhur sai ya sake sanyi sosai sabida yasan asirinsa ya gama tunuwa.

Dady kuwa cewa yayi to bata wayar,, mashkhur yasan zahra bata iya kar6ar wayar ba sabida 'yan yatsunta dan haka d'an qara matsawa gab da ita yayi ya kara mata wayar a kusa da kunan ta. Zahra kuwa lumshe idanunwanta tai sabida qamshin turaran mashkhur da take mutuwar su ne ya bigi hancin ta" da kyar ta iya bud'e baki tace dady ina kwana.

Wata ajiyar zuciya dady ya saki wanda daga zahra har mashkhur d'in ba wanda bai gita ba tare da cewa lpy qalau mamana, kwana biyu naji ki shiru hankalina ya tashi sosai na biga wayar ki amma naji tana ringing ba ayi piking ba. kallan mashkhur zahra tai, sukayi 4 eyes d'an girgiza mata kai yayi alamun karta fad'a, wata siririyar harara zahra ta watsa mai tare da cewa! Am dady dama wayar ce ta fad'a bayan drowar kicin shi yasa.

Mashkhur kuwa mamaki yake wai zahra shi take yiwa wanan hararsr hmm lallai abin ya girmama, mashkhur ya fad'i hakan a zuciyar sa. Dady kuma cewa yayi, eh haka yayan naki ya gaya min, amma nace ya dakko miki haryanzu bai d'akko miki ba, zansa ya siyar miki sabuwa, murya a da she zahra tace tom dady na gode ina ammi. Tana nan lpy ga tanan ma bari na baki ku gaisa.

Muryar ammi ceta karad'e kunnan zahra da mashkhur!!! Hello zahra cewar ammi! murya a shaqe zahra tace ammi ina kwana? Lpy qalau zahra ykk? Jim zahra tai na wasu daqiqu kafin tace lpy lau ammi. Ammi kuwa cewa tai zahra ga muryar ki nan naji ta canza da kyarma fa kike magana mai yake damunki lpy kuwa,, d'agowa zahra tai ta sake kallon mashkhur a karo na biyu, da sauri mashkhur ya qara girgiza mata kai tare da sa d'an yatsan sa a kan bakinsa alamun karta fad'a.

Lumshe ido zahra tai sanan ta bud'e kafin tayi ma magana ammi ta sake cewa naji kinyi shiru zahra anya lpy kuwa. Aaa ammi lpy qalau kawai dai ina fama da zazza6i da ciwan kai ne shi yasa. Daga mashkhur har zahra sai da suka ciyo sautin fara'ar ammi, bayan ammi ta gama fara'ar cewa tai uhmm zahra ko dai ko dai.

Cikin rashin fahimta maganar ammin zahra tace ammi ko dai ko dai me, dariya ammi tai tare da cewa na canko mana ko dai baby za!!!!!!!! Kafin ammi ta qarasa magar mashkhur yasa dogwan d'an yatsan sa ya katse wayar. Dan ko ba'a gaya mai ba yasan mai ammi take son fad'a shiyasa ma yayi saurin qatse wayar. Zahra kuwa da sauri ta kalli mashkhur tare da cewa! Sabida mai ka kashe wayar bafa mu gama wayar ba,.

Mashkhur kuwa zubawa zahra ido yayi ba tare da yace mata uffan ba" mashkhur sai a yau ya sake jinjina haquri da kawai cin zahra, da yaga bafa fad'awa su dady ba. zahra kuwa cikin haushi ta juya kanta gefe zuciya cike da tsanar mashkhur ko ta ina. Sam zahra bata gane mai ammi zata fad'a ba shi yasa sam bataji dad'i qatse wayar da Mashkhur yayi ba, duk a tunaninta ta d'auka ammi magana mai mahimmanci zatai, ko kuma ta gaya mata maganin da zata sha..............

Tofah kwanci tashi ba wahala a wajan uban giji yau kemanin kwanan zahra goma a asibiti kenan jiki ba laifi yayi kyau sosai, dan yanzu tana iya motsa yan yatsun natama targad'an da tai duk ya warke, sauka gocewar qashin da tai. Qafarta ma tayi kyau sosai amma dai har yanzu bata iya taka ta. Kanta ma ya kusan warkewa.

Zahra kuwa tun sanda ta cika sati d'aya a asibitin tace itafa ta gaji da zaman asibiti, gaskiya a sallame ta, haka dai likitoci da ahmad sukai ta lalla6ata, kullum zahra sai tayi kuka da magiya akan a sallame ta. Sabida ita zahra a rayuwar ta sam ba abinda tafi tsana, in ka cire mashkhur irin zaman asibiti, sam bata san zaman asibiti.

Dan ko lokacin da mashkhur ya ta6a dukannta kwana uku tayi, da daddare ta takurawa ammi akan sai sun dawo gida, haka dai ranar aka sallamosu a bisa dole har doctor habib ya dawo da su gida.
Tofah abu ya girmama yau, dan zahra taqi ci taqi sha,, kuma taqi yarda tasha magungunan ta tun safe sai kuka take kan sai na sallameta ta gaji da zaman hospital.


Haka ahmad da likitoci sukai ta rarrashin zahra, akan tayi haquri nan da kwana biyar za'a sallameta amma ina zahra sam taqi yadda. 6angarn mashkhur kuwa yana gida yana sharara bacci sabida shi har ga ALLAH ya gaji da koke koken zahra, akan sai an mayar da ita gida, shi yasa ma yau yace bazai je asibitin ba hutawa zai yi tinda yaga jikin zahra yayi kyau, kuma tunda aka kawo ta bai ta6a fashin zuwa ba sai yau.

To fah abu kamar wasa ya zama gaske zahra wuni tai yau bataci abinci ba bata sha magani ba, dan ko ruwa taqi sha wai ita sai an mayar da ita gida ta gaji da zaman asibitin nan, ba irin rarrashin da likitoci ba suyiwa zahra ba, amma ina taqi yadda, ahmad tun yana rarrashin ta har ya gaji ya zuba mata ido, kuma gashi sai bugawa mashkhur yake wayar a kashe.

To suma likitocin sun gaza da rarrashin zahra dan haka suka yanke shawarar zasu sallameta in yaso sai ta koma gida ta cigaba da jinya. Ahmad ma ya amince da hakan sabida yasan zahra mai haquri ce, amma tunda yau ta kai qarshe tofah ba abinda zai sa ta sakko, shiyasa ma ya amince da hakan.

To an rubutawa zahra takaddar sallama, sana an bata magungunan da zata ringa sha, safe da rana harma da dare. A motar asibiti aka mayar da zahra har gida, lokacin da aka kai ta gidan,, a gado aka d'aukko ta kamar wata gawa aka kai ta sama. Ai kuwa anci sa'a qofar falon a bud'e take, dan haka likitoci suka shinfid'e ta akan doguwar sofa falan.

Daga haka likitoci sukayi sallama da zahra sukai tafiyar su abinsu. Falo ya rage daga ahmad sai zahra, ahmad kuwa miqewa yayi ya nufi hanyar bedroom d'in mashkhur dan yasan yana ciki gidan tinda gaya motarsa a parking space d'in gidan sanda suka shigo. Ahmad yana qarasawa qofar bedroom d'in mashkhur ya murd'a Handel d'in qofar ya shige. Yana shiga ya hangi mashkhur akan bed yana ta sharar bacci.

Daga shi sai 3 kwata ko riga babu a jikinsa, gefe guda kuma kwalabar totalin ne da robar lemo. Jinjina kai ahmad yayi tare da cewa ALLAH ya shirye ka mashkhur, daga haka ya qarasa kan gado, tare da zama akan bed d'in. Hannu yasa ya fara d'an dukan mashkhur yana cewa! Mashkhur!!! Mashkhur!!! Mashkhur!!!. Da kyar mashkhur ya iya bud'e lunsasun idanuwansa tare da zubawa ahmad.

Cikin sanyayiyar murya mashkhur yacew ahmad sannu da zuwa harka dawo?. Gyara zama mashkhur yayi tare da cewa! Mun dawo dai koh?, cikin mamaki mashkhur yace kun dawo kuma kai da wa?. Ba wani 6ata lokaci ahmad ya bashi amsa da cewa! nida matar ka zahra mana,, cikin mamaki mashkhur yace zahra kuma? Ya qarasa maganar yana miqewa zaune.

Gyad'a kai ahmad yayi tare da cewa, gwara, cikin mamaki mashkhur yace mai kuma ya dawo da zahra gidan nan, ita da bata da lafiya ko tafiya bata iyayi?. To mashkhur ya kake so muyi, sanin kanka ne kullum sai zahra tayi kuka, akan sai an sallamota ta dawo gida, to yau kukan da tai yafi na kullum dan wuni tai tana kuka taqi cin komai taqi sha, kai har magani ma taqi kar6a ta sha wai ita sai an dawo da ita gida, shi yasa aka sallamo mu.

Cikin mamaki maskhur yace yanzu kana nufin tana cikin gidan nan kenan? Ahmad kuwa cewa yayi kwarai tana ma falo a kwance. Cikin mamaki mashkhur ya sake cewa! To yanzu wazai cigaba da yi mata jinya. Ko shayi babu ahmad yace kai ne mana, cikin mamaki mashkhur yace ni kuma ahamd tayaya?. Fuska a d'aure ahmad yace oho kai ka sani, daga haka ahmad ya miqe ya fuce daga d'akin, yana zuwa falo yayiwa zahra sallama ya fuce daga saman benan ya koma part d'in sa.

*hmmm shin kuna ganin mashkhur zai yiwa zahra jinya kuwa?.

* to taya kuke ganin jinyar zahra da mashkhur zata kasance?.

*kai ai koni amina bayero zanso naji ya wanan chakwakiyar zata kasance ku biyoni a next page dan jin yazata kaya, karku bari a baku labari.................

ADALILINTA💜❤💜

BY BAYERO💜❤💜

Typing...........

*page 85*

Fuska a d'aure ahmad yace oho kai ka sani, daga haka ahmad ya miqe ya fuce daga d'akin, yana zuwa falo yayiwa zahra sallama ya fuce daga saman benan ya koma part d'in sa.

6angaran mashkhur kuwa, ahmad yana fita daga bedroom d'in yaji wayar shi da take gefansa tana ruri. Da sauri mashkhur ya kalli wayar dan ganin waye?.

Bakowa ne yake kiran mashkhur ba face dady,, ajiyar zuciya mai cike da damuwa mashkhur ya sauke tare da kai hannu ya d'auki wayar. Ba 6ata lokaci ya d'aga wayar ya karata a kunne tare da cewa! Hello dady, ta d'aya bangaran dady cewa yayi! Salamma'alaikum,. Gyara zama mashkhur yayi tare da amsa sallamar yana cewa! Dady ina wuni.

Lpy qalau da fatan kuma kuna lpy? Gyara zama mashkhur yayi tare da cewa! Duk muna lpy dady kuma da fatan kuna lpy?. Amsawa dady yayi da cewa! Eh muna lpy muma, ina mamana, murya a sanyaye mashkhur yace tana nan lpy qalau, ko na had'a kune? Dady cewa yayi eh ai dule ma ka had'a ni da ita tinda nace ka siyar mata waya kaqi.

Ajiyar zuciya mashkhur ya sauke tare da cewa! Yau in sha ALLAH zan d'auko mata wayar,,. Dady kuwa cewa yayi karma ka d'auko, nifa na gaji da wanan zaman naku, wlh nan da 2 week's in baku dawo nigeria ba ni zanzo da kai na kuma on expected zanyi ma. Hankalin mashkhur ya tashi sosai da yaji hakan,, amma sai ya dake yace! In sha ALLAH ma kafin lokacin zamu dawo jira nake kawai na kar6i result d'i na.

Dady kuwa cewa yayi tom ALLAH ya kaimu, ina maman nawa, okay bari naje na kai mata wayar, mashkhur ya qarasa fad'in hakan yana miqewa tsaye. Mashkhur yana miqewa direct falo ya nufa,, har ya kusan fita ya tina ba riga a cikinsa dan haka katse wayar,, yayi sanan ya koma drowar ya dakko t shirt yasa sanan ya d'auki wayar, ya fuce.

Yana fita fallon ya hangi zahra shinfid'e akan sofa, tana kwance cikin rigar asibiti blue, rigar da kad'an ta d'ara guiwa. Mashkhur yana qarasawa ya fara watsawa zahra wani kallon up and down, 6agar zahra kuwa itama batai sanya ba wajan mayar mai da irin kallon da yayi mata. Mashkhur yana qoqarin yin magana wayar shi ta fara ringing.

Yana dubawa yaga sunan dady kamar yadda yayi tinani, hannu yasa ya d'aga wayar tare da sata a hand's free, yana cewa hello dady ga tanan, mashkhur yana qarasa fad'ar hakan ya qarasa sofa da zahra take kwance, sanan ya ajiye mata wayar a gefe fuskar ta, tare da watasa mata wata lafiyayie harara.

Mashkhur bai jira martanin da zahra zata mayar mai ba ya kama hanyar fita daga part d'in. Mashkhur yana fita bai tsaya ko ina ba, sai a qofar part d'in ahmad,. Ba 6ata lokaci ya fara knocking d'in qofar,, bai fi 3 mints yana buga qofar ba sai ga ahmad yazo ya bud'e qofar. Cikin mamaki ahmad yace wata sabuwa kace taka ta kawo ka kenan shigo to, ahmad ya qarasa maganar yana matsawa mashkhur hanya.

Au kenan kana nufin bana zuwa sai tawa ta kawo ni kenan mashkhur ya qarasa maganar yana shigewa ciki. Rufe qofar ahmad yayi tare da cewa! Ehh mana kai yaushe rabanka da ka shigo part d'in nan. Ajiyar zuciya mashkhur yayi tare da zama akan sofa yana cewa! Yanzu dai ahmad ba wanan ba dan ALLAH zauna muyi magana.

Fuska ba walwala ahmad ya zauna a kusa da mashkhur yana cewa! Inaji mai ya kawo ka? D'an yamutsa fuska mashkhur yayi tare

Please Login or Register in order to submit comment