Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tai kai ruma ai wanan ya wuce kuma. Haka dai zahra da ilham sukai ta rarrashin ruma har sai da ta saki jiki da su amma tace sam bazata bisu kaduna ba tana tare da ammi.

Washe gari.

Zahra da ilham sun gama had'e kayan su tsaf domin fatiya kaduna. Maman zahra baki har kunne zahra zata bita kaduna, 6angaran qanan zahra kuwa abun ba'a cewa komai tun jiya suke ALLAH-ALLAH yau tayi domin su zahra su zo. Bayan su zahra sun gama karyawa ahmad yazo ya d'auke su suka kama hanyar kaduna. Sauran mutan gidan kuwa yaya abdul da su faruq harma da su ammi zuciya fal da jimami, mijin zahra wato mashkhur kuwa bai san abinda ake ba yana d'aki yana sharar bacci.

Hmmmm wace irin tarba 'yan uwan zahra zasuyiwa zahra da ilham kuwa?.

Mu had'e a next page.




BY AMINA BAYERO 💜❤💜

Typing.........

*page 110*

Bayan su zahra sun gama karyawa ahmad yazo ya d'auke su suka kama hanyar kaduna. Sauran mutan gidan kuwa yaya abdul da su faruq harma da su ammi zuciya fal da jimami, mijin zahra wato mashkhur kuwa bai san abinda ake ba yana d'aki yana sharar bacci..............

Masha ALLAH su zahra an iso garin kaduna lafiya qalau. Ahmad hon biyu yayi a katafaran baban gidan mai gadi ya wangale get, masha ALLAH gida ya qiru yadda ya kamata. Bayan sun shiga ahmad yayi parking, maman zahra ce ta fara futowa daga nan sai ilham sai kuma zahra. Zahra sai wani d'ari-d'ari take kamar ba gidan su ba ko ilham ta fita sakin jiki.

Murmushi maman zahra tai tare da cewa mu shiga daga ciki koh? Zahra kallan ilham tai kamar dai bata gamsu ba, ilham ruqo hanun ta tai tare da cewa haba zahra ya kike abu kamar wata ba gida jiya kizo mu shiga mana nan ma ai gida ne koh?. Ahmad da ya fito daga mota cewa yayi hmmm ke dai bari kawai gidan ku ne nan ma zahra ilham ce ma ya kamata tayi hakan ba ke ba, tinda ita gidan surikan tana, ahmad ya qarasa maganar yana sakarwa ilham murmushi mai kashe zuciyar masoya.

Itama ilham murmushi tai tare da sakar mai tana cewa zahra towo mu shiga. Daga haka suka rankaya suka kama hanyar shiga kowa da abinda yake saqawa a ransa. Suna shiga babban falon gidan suka hangi gaba d'aya yaran gidan sun zauna da dukkan alamu su suke jira. Suna hango su zahra suka tawo a guje sukayi mata oyoyo.
Nana ce ta fara qarasowa ta rungume zahra cikin jin dad'i tace oyoyo aunty ta.

Murmushi zahra tai itama ta rungume nana zuciya cike da farin ciki. Bayan nana ta saki zahra ta koma ta rungume ilham, haka dai yaran gidan suka bi suka qanqame zahra suna mata oyoyo, bare ma khaulat da twins. Maman zahra ce tace haba ku sake ta mana haka ita fa ba irin ku bace batasan hayani ya. Mai ma kwan su saki zahra suka sake ruqunqume ta.

Nana ce tace kai dallah ku cika ta haka ko so kuke tace baza ta zauna a gidan nan ba. Da sauri suka cika ta suna cewa aaa muna so ta zauna. Murmushi maman zahra ta saki tare da cewa aikuwa dai karku jawo tace sai ta koma can yanzu ma da kyar ta yarda muka tawo tare, da badan ilham zata rakota ba ai baza yadda ta biyu ba.

Nana ce ta jawo hanun ta tare da cewa hmm mama ki rabu da ita zata saba a hankula ne tawo mu zauna aunty. Tabb ai qanwata bata da sabo ba irin ku bace ta fita da ban a cikin ku, ahmad ya qarasa maganar yana zama akan kujera. Haba yaya ahmad mai kake nufi kenan kana nufin harni bazata saba dani ba?.

Girgiza kai ahmad yayi tare da cewa aa ni ban ce ba nana amma ki jarraba ki gani. Murmushi nana tai tare da cewa hmmm zaka gani ne nan da 3 days na shawo kan ta,. Jinjina kai ahmad yayi tare da cewa ayi mu gani dai, shikenan yaya ahmad zaka gani ka dawo nan da 3 days ka gani ai zaka zo koh?. Haba nana mai zai hana nazo nan ni da zuciya ta tana nan gidan ma, ya qarasa maganar ya kallan ilham tare da shafa zuciyar ka.

Ahmad sannu ka manta dani a wajan koh? Mama ta qarasa maganar tana jefo mai fulo. Cafe fulan ahmad yayi tare da cewa aaa mama gaskiya na fad'a fa,. Murmushi mama tai tare da cewa to ahmad sannu ai ko kazo bazan ringa bari kana ganin ta ba yada kazo haka zaka kwashi qafa ka koma gida ta qarasa maganar tana jifan sa da hararar wasa.

Kai mama mene na d'aga hankalin haka, ba dai nasan ko ina a gidan nan ba, sanda zanzo na shiga mu gama hirar mu na tafi ai baki sani ba. Kai Ahmad anya kuwa kai ne ba canza akayi min ba, a gabana kake cewa hablka ko, murmushi ahmad yayi tare da cewa nima fa bayin kai na bane, sace min zuciya tai mama amma tinda gata nan sai ki kwato zuciyar d'an ki.

Ahmad ya qarasa maganar yana jifan ilham da kallo mai ciki da soyyaya. Hmmmmm to kaga har kasa taji kunya koh, to kuma ga qanan ka suna kallan ka,. Murmushi ahmad yayi tare da cewa hmmm wai ke nana haka aka koya miki tarban baqin koh, bazaki kawo musu abinci ba a haka za'ayi miki auran?. Kai yaya ahmad aure fa kace tabb ai bani ce akan layi ba.

Da in nace za ayi miki aure ba cewa kike nine babba ba sai nayi zaki to yanzu dai gashi ni zanyi aure daga ni sai ke ai. Murmushi nana tai tare da cewa aa yanzu daga kai sai aunty zahra tukunna sai ni ko aunty. Wani shu'umar murmushi ahmad ya saki mai cike da abubuwa da dama amma a fili sai yace yarinya kenan in ana sallah ba'a magana, ita zahra tin yaushe akayi bikin ta.

Wata uwar Dariya nana ta saki tare da cewa hmmm naqi wayon yaya abdul, kasan yarda naci burin bikin aunty zahra kuwa taya ma za'ayi bikin ta yanzi ni ban yarda ba nasan wasa kake min bari naje na kawo muku abinci nana ta qarasa maganar tana miqewa. Murmushi ahmad yayi tare da cewa dai-dai kenan tinda baki yarda ba zaki ga wasa kuwa.

Zahra kuwa d'an ta6e baki tai a zuciyar ta tace tabb aure akayimin ko muna aure ai wanan ba aure bane. A fili kuwa batace komai ba in ma banda sunkuyar da kai da tayi. Miqewa ahmad yayi tare da cewa mama bari dai na je na huta kafin na futo mu koma. to bazaka ci abinci ba ne? Girgiza kai ahmad yayi tare da cewa banajin yunwa sai anjima zanci. Daga haka ahmad ya wuce hanyar d'akin sa.

Maman zahra cewa tai to ku taso mu shiga ciki kuyi wanka tukunna sai kuci abinci. Ba musu su zahra suka miqe suka bi maman. Bayan sun hau sama sun d'anyi tafiya, sai gasu a qofar wani bedroom. Murd'a handel d'in d'akin maman zahra tai tare da cewa to ku shiga ciki da toilet a ciki sai ku wanka, zan sa a kawo muku trolley d'in kayan ku.

Ilham cewa tai tom shikenan maman, zahra zo mu shiga daga haka suka shige ciki ita kuma maman ta qara gaba. Masha ALLAH bedroom d'in ya tsaru sosai da sosai yaci ado komai pink color ne a ciki ga iyayan teddy's akan bed d'in suma pink color ne. Kai zahra d'akin nan yayi kyau sosai ya tsaru cewar ilham ta6e baki zahra tai tare da cewa hmmm ba laifi nifa wlh sam bana son zaman gidan nan wani d'ari-d'ari nake.

Haba zahra sai kace wanda za'a sace mu gidan kune fa wai sabida mai kike hakane?. Zahra tana qoqarin magana taji an murd'a handel qofar an shigo. Nana ce ta shigo fuska a sake tana cewa naje can na kawo muku abinci sai khaulat suka cemin kuna sama, amma ai da kun jira ni mun tawo tare nima fa qanwar ku ce ku saki jikin ku dani. Murmushi ilham tai tare da cewa ah sosai ma nana ai kin zama qawata yanzu.

Murmushi jin dad'i nana tai tare da cewa yauwa aunty ilham ku zauna bari na baku labari ta qaraso kan bed ta fara tattare teddy's d'in nata daga kan bed. Zama zahra da ilham suka a kan sofa suna qarewa nana kallo. Black beauty ce ta ajin farko, tinda ga shigar jikin ta zaka son ita mai son gayu ce. Ko mai na jikin ta too mach ne wato pick kana ganin shigar nana da bedroom d'in ta zaka sheda ita ma'abociyar son pink color ce.

Tana da d'an jiki amma ba sosai ba dan har ta d'an fi su zahra da ilham qiba, amma da kad'an ta fisu. batun diri kuwa ba'a cewa komai, dan komai yaji a jikin nana. Idanuwan ta mai dai-dai ta ne farare tass hancin ta ma haka. Ga bakin ta shaf d'in shi mai v ya fita sosai sabida ko magana take bakin tama abin kallo ne sabida yadda take motsa baki kai kace style take. Ga kumatun nan nata ma dai dai ta ga dimple.

Haqoran nan nata farare tass, baqa ce nana amma ba can sosai ba madede ciya ce a taqai ce dai za'a ce mata chocolate color. ga fatar ta sai wani kyalli take wow masha ALLAH, kana gani zaka son wuto ya kwanta a jikin nana. Kai duk in da ake neman chocolate beauty nana ta kai harma ta wuce. Sakin baki zahra da ilham su kai suna binta da ido dan har ga ALLAH tayi masifar birge su musamman ma ilham da take matuqar son jinsun baqaqe.

Sabida ita ilham a rayuwar ta fari ma baya birge ta ko dai dan ita farar fata ce oho, ilham tana matuqar son baqin fata musamman ma irin nana da ita baqin ta mai kya ne har shining take. Bayan nana ta gama kwashe teddy's d'in kan bed d'in dawowa tai tsakiyar su zahra da ilham ta shige da kyar. Tana ni shi tace to na dai shigo da izinin ku ku matsamin nima na shiga tsakanin ku.

Sake matsa mata zahra da ilham sukayi sanan ta samu ta zauna. Murmushi tai tare da cewa wai aunty zahra sabida mai bakya son magana ne? Nifa wlh banajin dad'in in kina irin wanan abun. Murmushi zahra tai tare da cewa aaa nana ba haka bane. Hmmmm hakane mana aunty zahra sam banajin dad'in abinda kike yi wlh. Ilham cewa tai ki kwantar da hankalin ki nana zaku saba.

Murmushi nana tai tare da cewa ALLAH yasa aunty ilham amaryar yaya ahmad ko, murmushi ilham tai tare da cewa sosai ma fad'i kan ki tsaye. Dariya nana tai tare da cewa kai ALLAH ya kai mu lokacin bakin ku mu raqashe ke kinga yadda nake tsara-tsaran bikin nan kai ai duk friends d'ina sun san da bikin yaya ahmad, kai aunty ilham kin san kuwa mene na manta ban gaya miki ba.

Cikin son jin gulma ilham tace aaa qanwata mazaki gayamin menene?. Wai wata qawata ce fa take son yaya ahmad lokacin da taji labarin ya kusan aure har kuka tai kai gaskiya tana son shi naso fa ya aure ta ALLAH ne bai yi ba. D'an had'e rai ilham tai tare da cewa matar mutum kabarin sa ALLAH ne yayi nice matar sa ba ita ba kuma ni zai aura. Kai aunty ilham mai yayi zafi nima nafi son ya aure ki ai kin ma fita kyau ita baqace fa.

Nan da nan ilham ta saki fuska tare da sakin murmushi tana cewa ALLAH ko my nana. Dariya nana tai tare da cewa wama zai had'a da ita amma gaskiya aunty ilham kina da kishi sosai kinga yadda kika had'e rai dan nace naso ya aure ta. Murmushi ilham tai tare da cewa hmmm ke dai bari. Kuma fa wlh kun dace ke da yaya ahmad zan so naga yaran da zaku haifa kyawawa.

Murmushi ilham tai cikin farin ciki tace in sha ALLAH zaki gani nan bada jimawa ba, mu haifi yara baqaqe ko kyawawa. Ta6e baki nana tai tare da cewa baqaqe kuma ke kinfi son baqi irin mu kenan gyad'a kai ilham tai tare da cewa eee wlh nafi son baqaqe nana. Nana cewa tai ah farare sun fi fah, girgiza kai ilham tai tare da cewa nifa fari baya birge ni sosai kamar baqi.

Nana cewa tai tabb ai fari duniya ne amma dai sai kuyi to colors wasu farare irin ki wasu baqaqe irin yaya ahmad ko?. Cikin zumud'i ilham tace kwarai nana kin kawo shawara haka za'ayi wlh. Wata uwar shewa ilham da nana suka saki tare da tafawa abin su. Zahra kuwa jin jina kai tai a zuciyar tace tabb tinda nana da ilham suka had'u sai ta ALLAH kuma.

Haka dai ilham da nana su kai ta hira abin su gwanin ban sha'awa sun saba kamar wasu qawaye. Bayan sun gama hirara zahra da ilham sukayi wanka suka canza kaya sanan nana ta zubo musu abinci suna ci suna hira.

Bayan sallah hud'u nana da zahra suna zaune suna hira kad'an-kad'an ita kuma ilham tana can grading ita da yaya ahmad suna shan hira abin su. Nana miqawa zahra plate d'in cincin tai tare da cewa aunty dan ALLAH kici tin d'azu fa nake bin ki kici kin qi. Girgiza kai zahra tai tare da cewa aa nana na qoshi sai an jima. A dai-dai lokacin maman zahra ta shigo bedroom d'in.

Ta samu nana tana takurawa zahra akan sai taci cincin d'in. Kai nana ki rabu da ita mana tinda bataso bata da lafiya fa ba komai take son ci ba. D'an zaro ido nana tai tare da cewa mai yake damun aunty ta kuma mama?. Zahra itama zubawa maman ido tai dan taji mai zata ce dan isa a iya sanin ta lafiyar ta qalau.

Murmushi mama tai tare da cewa ke dai rabu da ita kawai karki takura mata. Miqewa nana tai tare da cewa bari naje na kira aunty ilham tinda baki gayamin ba ai ita zata gayamin. Nana tana fita zahra tace mama naji kince rashin lafiya wacce irin larura kike nufi?. Murmushi maman zahra tai tare da cewa hmmmm tambaya ta kike ko kamar baki sani ba.

Jim zahra tai tana tinani ita dai a iya tunanin ta tasan ba abinda yake damun ta. Can taji maman tata tace au har kin manta da jika na kike. Cikin mamaki zahra tace mama wana jika kuma, na cikin cikin ki mana. Kai mama wlh da gaske naki bani da jiki fa, murmushi maman zahra tai tare da cewa hmmmmm mu dai bar magana taso muje na kai ki wajan baban ki yace yana son ganin ki.

6angaran ahmad kuwa bayan sun gama shan hirar su da ilham sunyi bankwana ba 6ata lokaci ya kama hanyar tafiya kano. Zahra da ilham kuwa kai abin ba'a cewa komai yau sun sha tarba da tarairaya ko kwakwaran motsi ba'a barin su suyi. Abban zahra ma yayi farin cikin da zuwan ta kai kafin dai wani lokacin dangi da 'yan uwa da aboka nan arziki sunji labarin ganin zahra, duk da dai ba kowa ne yasan tana raye ba sai a lokacin.

Washe gari.

Yau mutan ne suka ringa zuwa ta ko ina dangi mama da abba domin ganin zahra. Kowa yazo sai ya sheda kamar da zahra take da maman ta wanda basu yarda bama suna zuwa in sukaga yarda maman ta suke kama da zahra sai sun yarda. Musamman ma kakar zahra ta wajan uwa tana qaunar ta sosai kai zahra taga dangi.

zahra tana jin dad'i yarda qanan ta suke nuna mata qauna ga respect d'in ta da suke yi, kafin wani d'an lokaci zahra tai mugun sabo da 'yan uwan ta yanzu ba laifi tana sakin jiki suyi hira da qanan nata harda da mama da abba, amma dai zahra hankalin ta duk yayi wajan yaya abdul, duk da ta fara jin dad'i zaman kaduna, amma kullum tinanin yaya abdul take har mafarkin sa take.

KANO.

bayan mashkhur ya tashi daga bacci ya shirya, wajan hajiya kaka ya fara shiga ya gai da ita sanan ya wuce wajan ammi. Yana shiga ya babban falon ya tarar da ruma da ameer suna zaune ruma tana cewa haba ameer d'i na kaci abin ci ko kad'an ne kaji kayi haquri ka dena kuka. Ameer kuwa sai kuka yake yana cewa ni bazan ci ba sai an kai ni wajan aunty zahra.

Bayan mashkhur yayi sallama ruma ta amsa mai kuma ta gai da shi zama yayi akan kujera tare da cewa ameer waya ta6amin kai ne haka kake kuka da safiyar nan. Tasowa ameer yayi tare da cewa wananan matar ce, cikin mamaki mashkhur ya ruqo ameer tare da wace wace matar kuwa ameer?. Shiru ameer yayi yana tinanin wace mata zai ce.

Kai ameer mata kuma maman zahra ce fa ruma ta fad'a hakan. Cikin mamaki mashkhur yace kai ameer mai tai ma haka mama sunan ta fa ba mata ba. Share majina ameer yayi tare da cewa ta tafara min da zahra ta,. Cikin mamaki mashkhur yace ta tafi da ita ina kuwa?. Gidan ta mana wai kaduna, cikin mamaki mashkhur yace kaduna kuma ameer yaushe ko jiya fa sai da na ga zahra banda qarya fa.

Aa yaya mashkhur ba qarya yake ba da gaske ne yau da safe suka tafi harma da ilham. Mamaki ne ya sake daskarar da mashkhur cikin zuciyar shi yace to ni kenan maye matsayina kuma da izinin wa ta tafi?. Kai wanan abu yayi yawa wai ni mai aka mayar dani mutum da matar sa amma bashi da iko da ita sabida rashin tsari?. Mashkhur yana kai nan ya hango ammi ta riqe abdul suna saukowa daga kan step a hankali.

Jiki a sanyaye mashkhur ya miqe ya nufi su abdul zuciya fam a cike kamar ta fashe sabida baqin ciki. Yana qarasawa ya ruqo abdul tare da cewa abdul sunnu congratulations masha ALLAH, tinda gashi yanzu har ka fara takawa koh?. Murmushi abdul yayi zuciya cike da kewar zahra yace hmm wlh kuwa jiki masha ALLAH yaya mashkhur ina samun sauqi sosai.

Daga haka mashkhur ya qarasa da abdul kan kujera suka zauna. Cikin muryar majinyata abdul yace haba ameer ka dena kukan nan haka ka bari zamuje mu d'auko ta ni da kai, kayi haquri ma taje rasha ta dawo, bare nan da kaduna ka dena kukan nan haka mana. Cikin kuka ameer yace to yaushe zamuje gidan matar.

Dariya ammi tai tare da cewa kai ameer wai sai ka ringa cewa mata, maman tace fa, kuma gidan su ta tafi. Wani kallo ameer ya watsawa ammi tare da cewa, wlh ba gidan su bane nan ne gidan su. Zama ammin tai akujera tare da cewa to shikenan jeka kaci abinci ka. Noqe kafad'a ameer yayi tare da cewa aa sai kin gayamin yaushe zahra taza dawo.

Ammi gyara zama tai tare da d'an satar kallan mashkhur tana cewa ba rana bare wata dawowar ta ba yanzu ba ameer. Mashkhur ji yayi kamar an nitsa mai mashi a zuciyar shi sabida tsabar damuwa, shida ko kwana biyu yayi bai ga zahra ba sai yaji kamar zai mutu bare wata tabbb. Kafin kace kwabo gumi ya tsinke mai nan da nan jikin sa yayi sanyi.

Ammi kuwa wani siririn murmushi ta saki dama da biyu ta fad'i maganar tana so taga yadda mood d'in mashkhur zai kasan ce. Kuma tabbas ta son yanzu mashkhur ya fara son zahra amma taurin kai irin nasa ya hana ya fad'a. A zuciyar ta tace hmmm zakai bayani ne da kyau ba kai mai taurin kai ba, in sha ALLAH daga wanan karon ka gama taurin kai ai so ba wasa ba. Amma a fili miqewa tai tare da cewa abdul sannu bari na zubo ma abinci kaci...............

Godiya mai tarin yawa ga wanda suke min addu'ar samun sauqi da kuma ya jiki ngd sosai ALLAH yabar qauna ana tare in sha ALLAH na samu sauqi, yanzu zan cigaba da yi muku posting kullum.

Mu had'e a next page.

BY AMINA BAYERO 💜❤💜

Typing..........

*page 111*

zuciyar ta tace hmmm zakai bayani ne da kyau ba kai mai taurin kai ba, in sha ALLAH daga wanan karon ka gama taurin kai ai so ba wasa ba. Amma a fili miqewa tai tare da cewa abdul sannu bari na zubo ma abinci kaci...............

Mashkhur kuwa rai ba dad'i ya miqe ya bar d'akin zuciya cike fall da kewar zahra. Bai tsaya ko inaba sai bedroom d'in shi yana zuwa ya kwanta ya fara tinanin menene mafita?. Wani irin so da shauqi zahra ne suka kama mashkhur ko ta ina yana rufe ido ita yake gani. Mashkhur yana cikin wanan halin yaji wayar shi tana ringing, jiki ba kwari ya miqa hannu tare da d'aukar wayar yana duba sunan mai kira.

A hanzarce mashkhur ya d'aga sabida ganin sunan dady, bayan mashkhur sun gama gaisawa da dady, dady yace mai yazo yana son ganin sa. Mashkhur yana kashe wayar zuciya ba dad'i ya miqe ya fuce daga bedroom d'in. Mashkhur yana fita bai tsaya ko ina ba sai part d'in dady. Yana shiga ya wuce d'akin dadyn bayan dady ya bashi izini baki d'auke da sallama.

Fuska sake dady ya amsawa mashkhur sallamar, bayan mashkhur ya shigo har qasa ya tsuguna ya gai da dady bayan sun gama gaisawa ya tashi ya zauna. Gyaran murya dady yayi tare da cewa, nasan kana ta jiran wanan ranar ko? Cikin mamaki mashkhur yace dady wace rana?. Yau mana kasan lokacin da na d'ibar ma na sakin mamana ya wuce kuma baka sake ta ba sabida mutuwar rukkayya,.

Amma yanzu tinda komai ya wuce na baka dama zaka iya sakin mamana yanzu nan,. Mashkhur wani kallo ya d'ago yakewa dady kallan bai gamsu da maganar dady ba,. Dady kuwa kora jawabi ya cigaba da yi sanan bayan ka sake ta ya kamata ka nemi mata kai aure. Haba dady da kan ka kuma kake maganar saki? Mashkhur ya fad'i hakan hankali a tashe. Cikin mamki dady yace ee mana ai abinda kake so kenan kuma ya kamata na cikama alqawarin da na d'aukar ma.

Haba dady karka manta ALLAH ne yace ayi saki amma shi ma kansa bayaso ayi,. Ah mai sunan baba ban gane wanan maganar taka ba nifa ba tursasaka nai akan ka saki mamana ba kai kace zaka sake ta kuma kunce bakwason junan ku ba

Please Login or Register in order to submit comment