Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta rufe idan ta ruf zuciya cike da mamakin abinda zahra tai mata.

Zahra kuwa jiki a sanyaye ta fara sa kayan da ta d'ebo a kwabar, itama dai kan ta bada son ran ta tai wa ilham hakan ba amma ba yarda ta iya in batai wa ilham hakan ba zatai ta takura mata akan sai taji mai ya faru, kuma zahra tasan ta gayawa ilham mai ya faru tsakanin ta da mashkhur wata fahimtar zatai wa lamarin da ba kuma ga tsokanar da zata ringa yi mata akai-akai.

Zahra da ta gama sa kaya har zata je ta rarrashi ilham kawai sai ta kashe globs d'in d'akin ta fuce abin ta zuciya cike da jimami. Hakan kuwa ba qaramin sake qonawa ilham zuciya yayi ba. Zahra sai da ta gama leqawa sosai taga ba alamun mashkhur a wajan sanan ta qarasa fita daga d'akin. Tana fita ta wuce d'akin da aka sauke mamanta. Zahra tana zuwa ta murd'a handle d'in ta shige ko sallama batai ba dan tasan maman tata tayi bacci ma yanzu.

Amma ga mamakin zahra tana gama rufe qofar taji muryar maman tata da take kwance akan bed tace sai yanzu kika dawo ni da nayi tinanin bazaki dawo ba dan har na cire rai. Am dama uhh, haka zahra tai ta inda-inda tana son yin qarya amma ta kasa, dama ba sabawa tai dayin qaryar ba shi yasa in tazo yi take d'an kakarewa.

Murmushi maman tata tai tare da cewa basai kinyi min qarya ba kawai zo ki kwanta. Zahra ta d'an yi mamaki yadda maman tata ta gane ta cikin sauqi amma sai ta qarasa kan bed d'in tana cewa aa ba qarya zan miki ba kawai dai haka zance miki wanka naje nai kuma daga haka na taya ilham hira shi yasa na dad'e.

Murmushi maman tata tai sanan tace bakomai tin da dai kin dawo kwanta mana. Zahra ba musu ta kwanta zuciya cike fall da tunanin abinda ta aika tawa ilham. Zahra tana cikin wanan tinanin taji maman ta ta janyo ta jikin ta tana cewa wai dan ALLAH sabida mai zahra bakya farin ciki da gani na ne ni na kasa ganewa ko wani laifi nai miki?. Da sauri zahra ta girgiza kai cikin mamaki tace cewa haba mama sabida mai kika ce haka mai kika gani?.

Hmmm ba dole nace haka ba sai wani d'ari-d'ari kikeyi dani, lokacin ma da akace nice maman ki nazo zan rungume ki kika qi bari na ta6a ki sam banji dad'in hakan ba sai nake ganin kamar bakya farin ciki da gani na. Da sauri zahra ta girgiza tana cewa wlh ba haka bane, a da ina tunanin bazan ta6a sa iyaya na a ido na ba har na koma ga ALLAH shi yasa dana ganki naji tsoro nasha wata aljannar ce.

Murmushi maman zahra tai sanan tace hmmm lallai kam yanzu bama kya addu'a ALLAH ya bayyana miki iyayan ki duk kin manta damu yanzu misali in daga kan ki ban qara haiwuwa ba in na mutum bamu had'u ba shikenan bazaki ringa yimin addu'a ba. Aaa mama ba haka bane kusan kullum in nai sallah ina addu'a ALLAH ya jikan ku in kun mutu in kuma kuna raye Allah ya qara muka lafiya.

Cikin mamaki maman zahra tace au kenan da gaske bakya addu'a ALLAH ya bayyana miki mu?. Gyad'a kai zahra tai sanan tace hakane mama sabida sam ban ta6a tinanin ko da wasa ba, zan sake had'uwa da ku ba shi yasama bana addu'ar. Murmushi maman zahra tai tare da cewa haba zahra ki dena stinkewa da lamarin uban giji in aka ce miki ALLAH shikenan komai ya qare kin ji zahra ta.

Murmushi zahra tai tare da cewa hakane mama ALLAH ya bani kunya abinda nake tinanin bazai faru ba gashi yanzu ya faru. Sosai ma zahra kullum ina addu'a ALLAH ya sa kina hannu na gari gashi addu'a ta ta kar6u tabbas duk da ban sani ba amma nasan iya soyayar da gidan na nan suke nuna miki ko mu da muka haife ki iya abinda zamuyi miki kenan.

Cikin farin ciki zahra tace hakane mama ina son dady sosai ina son ammi ina son ilham ina son yaya abdul ina son hajiya kaka. Tabbas bazan ta6a fatan na rasa d'aya daga cikin su ba sabida sun bani gudum mawa sosai a rayuwata, dady ya d'auke ni fiye da 'yayan ya so ni fiye da duk wanda ya haifa a cikin gidan nan, yana nunawa kaf 'yan gidan nan banbanci akai na sanan yana fifitani fiye da kowa.

Itama ammi tana qaunata kamar yarda take son 'yayan ta sam bata ta6a banban tani da 'yayan ta ba. Itama ilham tana so na kamar ciki d'aya muka futo ta d'auke ni kamar usainar ta ko hasana ta mayar da damuwa ta kamar tata sam bata so taga ina cikin damuwa. Hajiya kaka itama ta qauna ce ni sosai, ta mayar da ni jika mafi soyuwa a cikin jikokin ta komai ta samu nawa ne a duniyar nan.

Yaya abdul kuwa ya mayar dani farin cikin rayuwar sa tun ina qarama yake so na tunda nake a duniya ban ta6a yi mai lefi ba ko nayi mai lefi sai dai yayi murmushi ya shimin albarka.

Yaya abdul yana so na fiye da kan sa yana qauna ta fiye da kowa a duniya yana sona fiye da rayuwar sa ko da wasa bi ta6a yimin abinda banji dad'in sa ba b ta6a dukana ba, ko zagi ko, hantara bare kyara duk wanda ya quntatamin ko da wasa sai ya gane kuskuran sa, yaya abdul shine rayuwata mama, yaya abdul shine farin ciki na yaya abdul shine komai nawa a rayuwa ta in na rasa shi mama zan iya rasa rayuwa ta zahra ta qarasa maganar tana zubar da hawaye.

Da sauri maman zahra ta sake janyo zahra jikin ta tana rarrashin ta har sai da tai shiru. Bayan zahra tai shiru maman zahra tace lokaci guda naji qaunar abdul ta rufe min zuciya tabbas kuwa ya riqe min amanar dana bashi, lallai kuwa dama ALLAH yace yana fitar da rayayye daga jikin matacce, tinda gashi ya fitar d abdul mai kyan hali daga cikin uwar sa Halima mai mumunan hali.

Haka dai maman zahra tai ta rarashin zahra bayan zahra tai shiru tace naji kin yabi ammi, dady, abdul, ilham hajiya, to sauran fa. Murmushi zahra ta saki tare da cewa hmm suma duk suna qaunata ya haidar da ya faruq suna sona basu ta6a goran tamin ba ko banbanci, sun d'auke ni kamar 'yar uwar su ilham. Tun kafain su san ni ba jinin su bace har suka sani. shima ameer yana sona fiye da yayyan sa. Itama ruma tana sona itama daga qarshe aunty rukee kafim ta rasu ta fara so na.


Murmushi maman zahra tai tare da jinjina kai tana cewa masha ALLAH naji kin ambaci kowa shi mijin naki ina kika sa shi. Wani siririn murmushi zahra ta saki a zuciyar ta tace hmmm lallai wanan ai shine sarki azzalumai da macuta amma a fili cewa tai mama nifa na gaji bancci nake ji. Dariya maman zahra tai tare da cewa hmm fad'i gaskiya dai kunya ta kike ji ko, shiru zahra tai ta rungumo maman tata tana cewa kema ina qaunar ki mama na, muyi bacci sai da safe good night.........

ADALILINTA 💜❤💜

BY AMINA BAYERO 💜❤💜

Typing......

Double page.

Washe gari.

Bayan zahra da maman ta sunyi sallah asubayi kwanciya sukayi suka ringa hira har gari ya qarasa wayewa. Misalin qarfe 7 maman zahra ta koma bacci ita kuma zahra sauka tayi daga kan bed d'in ta fuce daga bedroom d'in. Tana fita bata tsaya ko ina ba sai d'akin su, tana turawa ko shiga ba tai ba ta hangi ilham tana bacci, rufo qofar zahra tai ta qara gaba sabida bata so ta shiga ta tashi ilham daga bacci.

Zahra bata tsaya ko ina ba sai qofar d'akin ammi tsayawa tai tana zahra tana so ta shiga ta duba jikin yaya abdul kuma ta gai da ammi amma tana jin kunya ammi sabida halin da ta ganta ita da mashkhur jiya. Zahra sai da ta dad'e a bakin qofa sanan ta murd'a handel d'in d'akin ta shiga baki d'auke da sallama. A zaune taga ammi a gefan gado tana addu'a tana tofawa yaya abdul.

Fuska a sake ammi ta amsawa zahra sallamar. Wata irin kunya ce ta sake rufe zahra amma zahra sai ta dake ta rufo qofar ta qarasa wajan ammi sai wani sunkuyar da kai take tare da tsugunawa qasa tana gai da ita. Murmushi ammi tai tare da cewa oh zahra yau kece harda tsugunawa qasa ki gai da ni ni yaushe raban ke da ilham ku min irin gaisuwar nan sai dai fa ku fad'o jiki na kamar wasu yara.

Sake sunnar da kai qasa zahra tai tama rasa mai zata ce. Ammi ce tace to lafiya qalau tashi ki zaune, ammi ta sakarwa zahra fuska kamar kullum yadda kasan bataga abinda suke ai katawa da mashkhur jiya da daddare ba, sam ammi taqi ta nunawa zahra komai. Zahra miqewa tai ta zauna a kusa da ammi ta sake sunyar da kai tana wasa da hanunta tana cewa ya jiki yaya abdul.

Ah jiki abdul alhamdulilah da sauqi sosai kullum fa baya iya bacci da dadare amma kinga yau tinda ya kwanta bai tashi ba har yanzu sai bacci yake, da sauri zahra ta d'aga ido ta kalli yaya abdul a zuciyar ta tana tinanin ko dai mutuwa yayi ammi basa gane ba. Zahra da ta d'ago taga yaya abdul yana sauke nunfashi a cikin nutsuwa ajiyar zuciya tai tare da cewa alhamdulilah.

Zahra suna had'a ido da ammi ta sake sunyar da kai qasa. Murmushi ammi tai tare da cewa kai zahra yau fa na kasa gane miki wlh ko dai dan kinga maman ki tazo shine ni kika mayar da ni suruka sai wani sunkuyar da kai kike. Da sauri zahra tace ammi hmm wlh ni, kai zahra wlh mai in zaki fito kiya magana kiyi magana ki dena wanan inda in dai sai kace mara gaskiya.

Qara gyara zama zahra tai cikin jin kunya tace wlh ammi abinda ya faru jiya ba laifi na bane, nima bada son rai na hakan ya faru ba. Cikin mamaki ammi tace mefa zahra mai ya faru wana laifi kikayi, ai ni in fad'an ku da ilham ne nasan ma kun shirya yau ta saba toshe miki bakin in zaki magana. Cikin kunya zahra tace ammi nasan fa kin gane wlh da gaske nake bana son rai na hakan ya faru ba ba laifi na bane kawai qarfa-qarfa yayi min.

Miqewa ammi tai tare da cewa ni kinga kicin zan shiga na d'ora breakfast sai na dawo. Da sauri zahra tabi bayan ammi tana tai mata rantsuwa. Ammi kuwa sai cewa zahra take ita bata gane akan mai zahra take magana ba. Haka dai ammi da zahra suka qarasa kicin ana ta abu d'aya daga qarshe dole zahra ta haqura tai shiru da bakin ta ta fara taya ammi had'a breakfast suna yi suna hira.

Bayan ammi da zahra sun gama had'a breakfast d'in sun jera shi a draining zahra ta wucewa sama domin yin wanka. Zahra tana shiga bedroom d'in ta ruqo qofar, a dai-dai lokacin ilham ta futo daga wanka. Fuska sake zahra tace ilham harkin tashi daga baccin kenan ai d'azu nazo naga kina bacci shine na fuce na wuce wajan ammi.

Nan da nan ilham ta had'e fuska tam fuskar nan tata ta koma ba annuri. Zahra ta d'an sha jinin jikin ta amma sai ta sake tace to ilham da sanyi safiyar nan ya da haka ko dai fad'a kukayi da yaya ahmad. Nan ma ilham shiru ba amsa, zahra sake cewa tai haba ilham ina miki magana kina ta wani shashamin qamshi bazaki gayamin mai ke damun ki ba.

Cikin murya mai nuna tsantsar 6acin rai ilham tace aaa taya kuwa zan gaya miki a binda yake damuna tinda ni ba uwar ki bace. Jiki a sanyaye zahra ta qarasa bakin kwabar tace haba ilham wai ke baki san wasa ba wasafa nake miki jiyan nan haba saki ran ki mana. Ilham da take sa kaya wani dogwan tsaki taja tare da cewa kyaji da shi.

Haba ilham dan ALLAH kiyi haquri amma ke in kikayimin laifi kina bani haquri nake haqura amma ke in nai miki laifi kiqi haqura sai kin gama wahalar dani haba ilham meye haka?. Shiru ilham tai bata cewa zahra komai ba, zahra kuwa jiki a sanyaye ta wuce toilet tana nadamar abinda tai wa ilham. Ilham kuwa bayan ta gama shiryawa qasa ta sauka abinta.

Zahra tana fitowa daga wanka ta shirya tsaf sanan ta fuce daga d'akin ta sauka qasa. Zahra tana gama sauka ta qarasa draining tare da zama a kusa da kujerar da ilham ta zauna. Tare da cewa wai har yanzu ilham fushi kike yi dani dan ALLAH kiyi haquri mana, shiru ilham tai batace komai ba zahra ta dad'e tana yiwa ilham magiya akan tayi haquri daga qarshe dai zahra sai kifa kai tai akan draining ta fara kuka.

Ilham tana qoqarin yiwa zahra magana taji muryar mashkhur yana cewa ilham. Da sauri ilham ta juya baya tana mamaki har yaushe mashkhur yazo bata sani ba. Fuskar mashkhur a murtike yace ilham yaushe raban da ayi miki mugun duka a cikin gidan nan?. Cikin mamaki ilham tace duka kuma yaya mashkhur?, rai a 6ace yace zaki amsa min tambaya ta ko sai kinji saukar mari a fuskar ki.

Da sauri ilham tace ah wlh yaya mashkhur na manta gaskiya an dad'e ni bada ban kan nai qarya ba sai nace ba'a ta6a yimin mugun duka ba. Zahra kuwa da taji lamarin mamaki ya bata dan haka sa sauri ta d'ago fuskar ta cike fam da hawaye. Mashkhur kuwa cigaba da magana yayi da cewa okay ba'a ta6a ba ko to daga yau ba kuka ba ko 6acin rai kika sake sata sai na miki abinda baki ta6a tinanin ba mashkhur ya qarasa maganar yana jifan zahra da wani qasai taccan murmushi.

Zahra kuwa wani mugun kallo ta watasa mai tare da kawar da fuska gefe, ilham kuwa mamaki ne ya kashe ta a zaune. Mashkhur sake had'e rai yayi ya dawo da kallan sa kan ilham yana cewa na lura da duk take-take kin kin bi duk kin takura mata, wlh ko kallan banza kika sake yi mata zaki gane baki da wayo. Cikin mamaki ilham tace tom yaya mashkhur na dena in sha ALLAH.

Ni kuwa amina bayero nace tom mashkhur mai yake nufi?.

Daga haka mashkhur ya juya ya haye sama, cikin mamaki ilham tace kai zahra ban gane ba wai mai yake faruwa ne fitar dani daga ciki duwo. Wata siririyar harara zahra ta saki tare da cewa ban sani ba. Ilham cewa tai ke ba fa batin wasa nake mike ba mai ya ke faruwa ne tsakanin ki da shi bakiji abinda ya cemin ba akan ki.

Zahra ta6e baki tai tare da cewa oho shi yasani. Jinjina kai ilham tai tare da cewa hmmm lallai inaga abinda nake buri yana gab da faruwa. Cikin mamaki zahra tace me kenan murmushi ilham tai tare da cewa zaki gani mana, ni dai nasan kina 6oyemin wani abu amma dai bazan damu ba nasan ban cancanta naji ko mene ba sabida da na cancanta ni zaki fara gayawa.

Ajiyar zuciya zahra ta sauke tare da cewa sabida mai kikace haka?, girgiza kai ilham tai tare da cewa ai gaskiya na fad'a na fahimci dai yanzu kina 6oyemin wani abu in na takura miki da tambaya kuma kiji haushi na. Murmushi zahra tai tare da cewa hmm duk dai nasan so kike kiji mai ya faru jiya koh? Gyad'a kai ilham tai alamun ee murmushi zahra tai tare da cewa wlh abun ne jiya ya d'aure min kai shi yasa kikaga jiya na canza miki.

Wlh ilham jiya in gaya miki naji kunyar da ban ta6a ji ba a wajan ammi. Murmushi ilham tai tare da cewa haba mai ya faru haka ta waje na. Dariya zahra tai tare da cewa kai ilham da san jin gulma zo muje d'aki na gaya miki mai ya faru karta kashe ki. Dariya ilham tai tare da cewa hmmm ai kuwa dai dan tsaf zata iya kashe ni, daga haka ilham da zahra suka wuce sama riqe da hanun juna.

Misalin qarfe 3 na rana dady da ammi suka matsawa zahra akan sai ta bi maman ta sun koma kaduna. Zahra kuwa tace aaa sabida sam bata so tatafi tabar yaya abdul, yaya abdul kuwa masha ALLAH jiki sa yayi sauki dan yanzu yana iya gane kowa da komai, amma dai wuni yayi yana kuka sabida baqin cikin abinda momy ta aikata. Daga qarshe dai yaya abdul sai da yasa baki akan zahra ta amince ta bi maman ta kaduna.

Zahra taji dad'i sosai sabida yau tinda yaya abdul ya tashi bai yi magana ba sai lokacin. Zahra kuwa cikin farin ciki tace ta amince tinda yaya abdul yasa baki amma da sharad'i biyu. Da su dady suka tambaye ta sharad'in menene sai zahra tace musu na farko bazata tafi yau ba sai gobe nabi kuma bazata tafi ita kad'ai ba dole sai ilham ta raka ta. Da su ammi sunce ilham bazata je ba amma daga qarshe sai suka amince sabida maman zahra tace dan ALLAH a barta su tafi tare da ilham d'in.

6angaran mashkhur kuwa bai san wai nar da ake toyawa ba sabida yau gaba d'aya baya gadin tun da safe ya fuce bare yaji labarin tafiyar zahra. Zahra kuwa yau wuni tai a waja yaya abdul sai hira suke abinsu. Abun gwanin ban sha'awa, yana nuna mata stantsar farin cikin sa na ganin iyayan ta.

Dady kuwa yana futa bai tsaya ko ina ba sai part d'in momy, yana shiga yaga ruma zauna a falo ta rafka uban tagumi. Kallan ta yayi tare da cewa ruma lafiya kika zauna kikayi jigum bare kije wajan mamana da ilham ki zauna sai ki zauna ke kad'ai, kin san dai yanzu rukkayya ta rasu fa, bazaki ji dad'in zama ke ka d'ai ba.

Rai ba dad'i ruma tace dady bakaji abinda momy ta aikata musu ba taya zan shiga cikin su ai tsorona ma zasuji. Murmushi dadg yayi tare da cewa aa ba abinda zasuyi miki ba wani tsoro ke da kin kusan barin gidan ma. Cikin mamaki ruma tace ina kuma zan koma dady?. Aure zan miki mana ko bakya so, aure kuma dady wa zaka auramin kasan dai ni bani da wani saurayi.

Doctor habib zan aura miki yace a mai da baikwan su da yayar ki rukkayya kan ki kuma na mayar ko bakya son shi ne. Jiki a sanyaye ruma tace tom shikenan dady ALLAH ya tabbatar da alkhair, ameen ruma ALLAH yayi miki albarka kije ki kwaso kayan ki ki koma 6angaran maryam da zama kinji. Ba musu ruma ta miqe tare da cewa tom shikenan dady.

Dady kuwa direct ya wuce sama d'akin momy zaune dady yaga momy akan dadduma da dogwan carbi duk tabi ta rame ta koma abin tausayi. Saratu kuwa tana gefen gado a zauna ta zabga uwan tagumi. Baki d'auke da sallama dady ya shiga da sauri momy ta juyo ciki tsoro ta amsa sallamar baki na rawa suka fara gai da dady ita da saratu.

Fuska ba walwala dady ko amsa gaisuwar momy da saratu bai ba ya zaro farar takaddar aljiwun sa ya miqawa momy. Momy cikin mamaki tace dadyn abdul menene a cikin takaddar fuska a d'aure dady yace ki bud'e ki gani. Daga haka yayi fucewar shi, hannu na rawa momy ta bud'e takaddar ta fara karantawa. Da sauri tayar da kaddar tare da cewa saratu nima dadyn abdul ya sake ni saki biyu kinga in aka had'a a waccan saki uku kenan na shiga uku ni Halima........

Bayan magariba

Tsaki zahra taja tare da cewa ke ilham matsalar ki kenan wlh, ke dama ana gaya miki abu sai kin fassara, tun dazu dana gaya miki maganar nan kin bi kin ishe ni da jita jita. Murmushi ilham tai tare da cewa wlh zahra da gaske nake miki in yaya mashkhur baya son ki bazai wani tsaya yayi romance dake ba, yadda ma yake da kyakyamin nan har zai kai bakin sa naki har yama sha yawun ki.

Cikin mamaki zahra tace ke ilham banda sharri ni nace miki ya sha yawuna kai ilham na shiga uku. Dariya ilham tai tare da cewa kai yaro-yaro ne, in ma banda abinki kin ta6a jin inda akayi hote kisses hoto kisses d'in ma na shan baki kice wai ba'a sha yuwa ba hmmmmm. Ke ilham waye yace miki zazzafan kisses mukayi ne aa?. Minti nawa kuka d'auka a can?.

Nifa ba wani dad'ewa nai ba kina dai fita daga d'akin ammi nima ko 5 minutes banyi ba na futo daga nan fa na had'u da shi, to muna rabu da shi na shigo d'akin nan. Tinani ilham ta farayi tare da cewa inazuwa bari kiga. Daga haka ilham ta janyo wayar ta sanan ta shiga WhatsApp ta fara dubo chat d'in su ita da yaya ahmad.

Kallan zahra tai tare da cewa a cikin 50 a cire biyar saura kenan? Zahra bata wani tsaya dogwan tinani ba tace remin 45. Wani shu'umar murmushi ilham ta saki tare da cewa to minutes arba'in da biyar kuka d'auka kuna romance. Kai ilham taya kika gane hakan?. To lokacin da na shigo muka fara chat d'in nan da yaya ahmad kuma da lokacin na lissafa.

Ajiyar zuciya zahra ta saki tare da cewa hmmm ALLAH dai ya kyauta amma dai jiya naji kunya wlh. Kai zahra gaskiya kun bani cittah fa kai ALLAH dai ya kai mu lokacin tariya yadda naga alama ke da shi kuna da wanan jarabar ai yi d'aya zakuyi, zaki samu ciki ki haifa mana kyakyawan baby. Zahra tana qoqarin yin magana taji an turo qofar an shigo.

Da sauri suka d'aga kai dan ganin mai shigowa, ruma ce riqe da trolley a hanun ta. Murmushi zahra ta saki tare da cewa hajiya ruma 2 days, jiki ba kwari ruma ta shigo tare da cewa sanun ku dady ne yace wai na dawo nan da zama zan d'an fi jin dad'i. Ilham ce tace ai kuwa dai kin san gobe zamu tafi kaduna gidan su zahra kuwa?.

Ilham ta fad'i hakan cikin farin ciki, zahra cewa tai ee kinga kema sai mu tafi tare. Cikin tsoro ruma tace wa ni aa ku dai kuje Allah ya kaiku lafiya ya dawo da ku lafiya. Cikin mamaki ilham tace sabida mai bazaki bimu ba. Zama ruma tai a kusa da su tare da cewa yadda momy da sunty saratu suka zanbad'a muku cutar nan wane ni naje gidan. Zahra cewa

Please Login or Register in order to submit comment