Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dai mashkhur ya tuno fansar da zai d’auka akan zahra sai ya saki wani shi’umin murmushi, a haka har bacci ya kwashe shi. Ni kuwa amina bayero nace wanna wace kalar d’auka fansa mashkhur zai yiwa zahra haka? Ohoo.🤷🏻‍♀️

Washegari........

Yau mashkhur sai zagaya gidan yake duk in da yasa zai had’u da zahra sai yaje. Amma abin mamaki ya kasa samu yaga zahra, ita ka dai a ke6e. da yamma mashkhur yana saman bene daga part d’in su ya hango zahar sin dawo daga makaranta islamiya kuma tare da su haidar suka shigo, shiyasa ma baiyi yunqurin yi mata magana ba. Zahra kuwa sam batasan abinda zai had’a ta da mashkhur, tun sanda yayi mata dukan nan bata bari ko hanya su had’a. Toh wanin ranar dai haka mashkhur yay ta zagayansa amma bai had’u da zahra ba.

Washegari.......

Yau mah haka mashkhur ya d’inga zagaya gidan duk dan ya samu ganin zahra amma ina hakan ya faskara.
Da Misalin qarfi biyar na yamma, mashkhur ya shirya domin zuwa guarden d’in gida koh zai samu zahar da yake yau alhamis ba makarantar islamiyya. Mashkhur yasan in basu da islamiyya zahra tana yawan zuwa guarden d’in tayi karatu.

A hankula ya fara tafiya kamar wani mara gaskiya yana zagaya guarden d’in ko zai had’u da zahra,ai kuwa karaf suka had’a ido da dady yana zaune yana karatun jarida. Kalan juna suka shigayi can kuma dady ya mayar da kallansa kan jaridar ya cigaba da karatun sa. Shiru mashkhur yayi domin yasan har yanzu dady fushi yake da shi akan abinda yayiwa zahra ko maganar kirki basayi, koh ya gai dashi baya amsawa. Har mashkhur ya juya zai fita daga guarden d’in kawai sai yaji bai kyauta ba in yayi hakan dan haka jiki ba kwari ya qarasa wajan dady.

Dai dai sai tun qabar dady mashkhur ya tsuguna., sai da mashkhur yafi minti biyar yana tsugune ba wanda ya yiwa wani magana a cikin su. Can kuma mashkhur ya fara magana murya a sanyaye!! Dady dan ALLAH kayi haquri, bazan iya jure ganin kana fushi dani ba. Shiru dady yayi mai bai bashi amsa ba, mashkhur kuwa sake qaryar da murya yayi tare da cewa dan ALLAH dady kayi haquri, ka dai na fushi dani wlh bana so naga iyaye na suna fushi dani kaga ALLAH mah sai yayi fushi dani.

Dagowa dady yayi tare da kallan mashkhur d’in duk yabi ya marairai ce kamar wanda yayi nadama da gaskyan gaske. Dafa shi dady yayi tare da cewa yanzu kana nufin kayi nadamar abinda kayiwa mamana kenan?, shiru mashkhur yayi sabida har ga ALLAH bai yi nadamar abinda yayiwa zahra ba, ammah ba yanda ya iya dole ya d’agawa dady kai alamun ehh yayi nadama. Murmushi jin dad’i dady yayi tare da cewa yauwa mai sunan baba haka nake so in kayi laifi ka ringa nadama, dan bana son taurin kan nan naka.

Murmushi ne yaso ya su6ucewa mashkhur domin yasan ba har zuciyar sa yake fad’in hakan ba kawai iya taku ne, irin nasa. Muryar dady yaji ta daki kunnan sa!! Yauwa mai sunan baba taso ka zauna a nan, dady ya fad’a yana nuni da 6angaran dama na kujerar da yake kai, wato yana nufin mashkhur ya zauna a kusa da shi. Ai kuwa ba musu mashkhur ya miqe tare da ya zauna a kusa da dadyn.

Dafa shi dady yayi tare da cewa yanzu mai kake buqata,kasan dai gobe qarfe takawa n (8:00am) na safe jirgin ku zai tashi. Cizar le6e mashkhur yayi tare da cewa dady ba abinda nake buqata kud’in ma daka bani har yanzu basu qare ba. Jinjina kai dady yayi tare da cewa it’s okay, na bayar ai maka a.t.m d’in rasha kana zuwa sai ka fara amfani da shi na zuba maka kud’i a ciki, gyad’a kai mashkhur yayi tare da cewa nagode dady.

Kallansa dady ya sake yi tare da cewa amma sai naga kamar da akwai abinda yake damun ka koh?. Girgiza kai mashkhur yayi tare da kwanciya a kafad’ar dady yana cewa nifa dady ba abinda yake damuna kawai dai kewar kuce take damuna gani nake kamar bazan iya rayuwa ba kuba. Girgiza kai dady yayi cikin tausayawa tare da shafa sumar kansa yana cewa, no karka ce haka in sha ALLAH komai zai wuce kamar yau ne fa zakaje ka dawo, kuma duk shekara d’aya da rabi zaka ringa dawowa hutu kaji?.

Daga kai mashkhur yayi tare da cewa hakane dady, kwanciya mashkhur ya sake yi ajikin dady, duk jikinsa yayi sanyi. Haka dady yay ta rarashin mashkhur har sai da yasaki jikinta sukai ta hira, mashkhur yaso ya koma cikin gida koh zai had’u da zahra, amma sam dady yaqi barinsa ya tafi. Sai magariba sanna suka tashi shida dady sukayi alwala, sanna suka wuce massalacin gidan, da yake lokacin da dady ya gina gidan har massallaci acikin gidan.............

Misalin qarfe tara na dare, zahra da ilham suna d’aki a zaune suna hira, shi kuma ameer yana tsakiyar su akan bed yana bacci. Ilham ce tace zahra da zaman banzan nan da muke ya kamata fah mu tashi muyi hadda tunda bama jin baccin, kuma kinga har shafi biyu zamu bayan zuwa asabar. Da sauri zahra ta miqe daga kwanciyar da tayi, tare da cewa ai kuwa dai ilham gwara da kika tina min ni wallahi ma na sha’a fa. A tare suka shiga toilet suka d’auro al wala sanan suka futo, suna futow zama skayi sanna suka fara karatun Qur’an.

Sai da sukayi wajan awa d’aya suna haddace shafi d’aya, yanzu sun gama harda shafi d’aya saura d’aya. Ilham ce tace gaskiya zahra na gaji kawai kizo mu kwanta zuwa gobe sai mu qarasa haddar, kinga yanzu fa har sha d’aya tayi ta qarasa maganar tana sauke idon ta akan agogan bango bedroom d’in. Girgiza kai zahra tayi tare da cewa ni dai gaski bana jin bacci sai na qarsa shafin nan sanna zan kwanta. Miqewa ilham tayi tana hamma tare da cewa gaskiya ni dai kwanciya zanyi bacci nake ji zuwa gobe ko bayan nayi sallar asuba na qarasa, daga haka ilham ta ajiye Qur’an d’inta a qaramar drowar, sanna ta kwanta tayi addu’a bacci.

Zahra kuwa cigaba da karatun ta tayi cikin kwanciyar hankali.
Sai wajan qarfe sha d’aya (11:00 pm) zahra ta idar da haddar da takeyi, rufe qur’ani tayi, sanna taje ta ajiye shi, har zata kwanta taji tana jin yunwa, sabida yau bataci abincin dare ba sakamakwan ammi tuwan alkama tayi kuma zahra sam bata cin towan alkama, in dai ammi tayi sai dai ta dafa mata wani abinci ko kuma ita zahra ta dafa indomin, kuma gashi yau zahra bata samu ta dafa indomin ba, zahra ji tayi bazata iya jurewa ba, dan haka ba 6ata lokaci ta nufi cikin domin samarwa kanta abinci da zata ci........

Mashkhur...........

Misalin qarfe goma da rabi na dare (10:30 pm) mashkhur yana kwance yana juyi akan bed d’in sa duk yabi ya damu, yama rasa mai yake mai dad’i sabida bai had’u da zahra ba ya d’au fansar abinda tayi mai, kuma gashi zuwa gobe da safe zai bar gidan. Haka dai mashkhur yayi ta juye-juye akan gado, yana tinanin menene mafuta?. Can kuma yaji cikinsa yana murd’awa sakamakwan yunwar da yake ji. Sai yanzu mashkhur ya tina da wani abinci mah sabida rabansa da abinci tun breakfast d’in safe, kuma shima ba wani abincin kirki yaci ba.

Duba agogon wayarsa da take kusa da shi mashkhur yayi domin ganin qarfe nawa?. Yanzu misalin qarfe sha d’aya da minti biyar (11:05 pm) jiki ba kwari mashkhur ya miqe domin samawa kansa abincin da zai ci, dan yunwa karda ta illa tashi. Qarasawa bakin fridge yayi tare da bud’ewa domin samun abinda zai ci. Abin takaici duk lemuka da youghurt d’in fridge harma da kayan marmari, duk sunyi qanqara, wani siririn tsaki ya ja tare da kama hanya ya fuce daga bedroom d’in.

Yana fita daga bedroom d’in sa fucewa yayi daga part d’in nasu gaba d’aya, ya wuce part d’in ammi domin yaje ya zubo abinci. Ai kuwa mashkhur yaci sa’a lokacin da ya je qofar part d’in ammi a bud’e ya same qofar dan haka ba 6ata lokaci ya kutsa kai yana shiga bai tsaya ko inaba sai qofar KICIN. A dai dai lokacin zahra ta gama had’a cornflakes da madara ta ruqo qaramin tangaran d’in data had’a cornflakes d’in ta kamo hanyar futa. Karaf idan ta ya sauka akan mashkhur da yake qoqarin shigowa kicin d’in, ga bantane ya fad’i rass.

Mashkhur kuwa yana d’agowa sukayi 4 eyes da zahra, shima ji yayi gaban sa ya fad’i rass harda rufe idon sa ya bud’e koh gizau take mai amma ina itace dai. Zahra kuwa tini gumi ya tsinke mata jikinta sai wani rawa yake sabida tsabar tsoro tama kasa motsawa bare ma tayi tinanin fita daga kicin d’in. Sunfi wajan mimti biyar suna kallan kallo, kowa da abinda yake saqawa a zuciyarsa. Mashkhur ne ya katse shirun da cewa!! sannu fa, ya fad’a fuska ba annuri.

Gaban zahra ne ya sake fad’uwa, in banda INNALILLAHI ba abinda take furtawa azuciyarta. A hankula mashkhur ya fara nufo in da zahra take tsaye. Ganin mashkhur yana qoqarin nufo ta hakan ne yasa zahra ta ringa ja da baya da baya, sabida tsabar tsoro har sai da zahra ta saki tangaran d’in cornflakes d’in hanunta ya fad’i qasa ji kake tass. tangaran d’in ya fashe a qasa, mashkhur kuwa tsallake tangaran d’in yayi tare da cigaba da binta................
Tofah nikuwa amina bayero nace mai mashkhur zaiwa zahra haka?🙆🏾‍♀️ Ohoo 🤷🏻‍♀️

Ina taya d’aukakin ‘yan Nigeria murnar samun saban shigaban qasa, da kuma governors ALLAH ya taya ruqo kuma yasa muga canji, bakamar tsohuwar gamnatin baba buhari ba. Allahuma Ameen.....

Ina yiwa mutanan kano state wato ‘yan kwankwasiya congratulations 🎉🎊🎈 abba gida-gida ya zama governor. Tom ALLAH ya taya ruqo kuma yasa kayi mana adalci Allahumma Ameen.🙏🏼

ADALILINTA 💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

My WhtsApp Number 08142246343.

Free book

Now book on 2023.
[11/06, 22:24] Maman Xuhra: “ADALILIN”

ADALILINTA 💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜


Typing.............

*page 46*


Tangaran d’in ya fashe a qasa, mashkhur kuwa tasallake tangaran d’in yayi tare da cigaba da binta.......

Yana binta tana sake ja da baya, ai zahra bata an kareba kawai taji ta biqe da bangon kicin d’in alamun tazo qarshan kicin d’in, bazata iya cigaba da ja da baya bah. Ganin mashkhur ya na nufota ya kusan qarasowa in da take hakan ne yasa ta rintse idonta sosai, tana sauke nunfashi da qyar, gumi kuwa duk yabi ya jiqa mata jiki. Mashkhur kuwa bai tsaya ba sai da yazo gabb da ita.

Hankalin zahra ya sake tashi saka makwan yanda taji saukar nunfashi mashkhur akan face d’inta. Mashkhur kuwa sosai abin ya bashi mamaki sabida tsabar tsoro irin na zahra tun kafin ma satan mai ke tafe da shi, ta tsorata. sosai mashkhur yake kallan fuskar zahra yana jin tsana zahra tana qaruwa a zuciyar ta, gabb da fuskarta ya kara tasa fuskar ta yanda suna iya jiyo sautin nunfashi junan su. Bakin sa ya bud’e tare da hura mata iska a fuskar ta.

Da sauri zahra ta ware idon ta cikin tsoro da mamaki, ai kuwa karaf suka 4 eyes. Da mamakin zahra wani shi’umin murmushi taga mashkhur ya sakar mata. Abin ba qaramin mamaki ya bawa zahra ba tinda take da mashkhur a duniya bai ta6a yimata murmushi ba sai yau. Iskar da ya sake hura mata a fuskar tane ya dawo da ita daga tinanin data tafi. Da sauri ta kalle shi baki na rawa tace da! da! Dan ALLAH ya! ya! ya!, dasauri ya d’ora hanunsa akan le6an sa yana cewa shiiiiiiiiiiii, a alaim tayi shiru.

Kwallace ta taru a idan zahra jikinta sai rawa yake gashi ya takure ta yana gaf da ita ba halin guduwa. Sake sakin wani shi’umin murmushi mashkhur yayi saka makwan ganin zahra duk tabi ta razana. Magana ya farayi kamar rad’a bakomaii yake cewa ba face, haba mene na kuka kuma? Tingafin ma kisan meke tafe dani?. Cikin muryar kuka zahra tace dan ALLAH yaya mashkhur kayi haquri karka sake duka na wlh bada sani na fasama laptop ba.

D’an zaro ido mashkhur yayi alamun mamaki tare da cewa au ai ni nama manta da zancan laptop d’in da kika fasamin. Shiru zahra tayi tana tantamar abinda mashkhur ya fad’a mata. Iska ya sake hura mata a fuska sabida ta dawo daga tinanin da ta tafi. Da Sauri zahra ta dawo daga tinanin da ta tafi, kin masan meke tafe dani kuwa? Giriza kai Zahra tayi alamun aa. Murmushi mashkhur ya saki tare da cewa it’s okay, ki kwantar da hankalinki ni ba dukan ki zanyi ba sabida ba shine a gabana ba.

Da sauri zahra ta sauke ajiyar zuciya tare da cewa da gaske ba dukana zakai ba?. ehh mana ya qarasa maganar yana kashe mata ido d’aya. Shiru zahra tayi sabida har yanzu tsoransa take ji. Matsawa baya mashkhur yayi sabida ya gaji da facing d’in zahra da yake sabida tsabar tsanar ta da take nunkuwa a zuciyar sa. Itama zahra ajiyar zuciya ta saki tare da sauke nunfashi sabida dama can bataji dady abinda yake mata, duk sai taji wani iri, kawai dai dan yayan tane kuma tanajin tsoran sa, amma da wani ne bazata bari yayi mata hakan ba.

Gyaran murya mashkhur yayi tare da cewa kawai inaso ne na sanar dake abu mai MAHIMMANCI da ya kamata ki sani. Yana gama maganar ya qarasa fridge ya bud’e tare da dakko juice, bayan ya d’akko juice d’in wajan ajiye cup ya nufa ya d’akko cup d’in tare da tsiyaya juice a cup sanna ya d’auka ya fara sha. Zahra kuwa mamaki ne ya kamata wata maganamai mahimmanci mashkhur zai gaya mata hakane? Wannan wace magana ce mai mahimmanci da bawanda zai gaya mata sai mashkhur.

D’agowa tai ta kalle shi shima ita yake kallo hannun sa rige da cup d’in juice. Murya a sanyaye zahra tace yaya mashkhur wannan wace magana ce haka?. Kawar da kansa yayi daga kallanta tare da cewa ki kwantar da hankalinki zama kisan ko mene. Shiru zahra tayi tana sairaran mai zai ce. Maganar sace ta daki kunnan ta, cewa yayi! Nasan zaki mamaki taya akai na tsane ki koh? Bana qaunarki kullum a cikin hantararki nake da kyararki, na ware ki ke kad’ai a cikin gidan nan na nuna mika karan tsana koh.

Da sauri zahra tace ehh hakane yaya mashkhur ina mamakin hakan, tabbas nasan da akwai abinda yasa ka tsaneni, dan nasan ba ta yanda yaya zai tsani qanwarsa uwa d’aya uba d’aya batare da wani laifin ba. Murmushin qeta mashkhur yayi tare da cewa harda sauri haka ai dama kin bari kin gama jin mai zan gaya miki kafin ki yanke hukun ci. Shiru zahra tayi sabida sam takasa ganewa mashkhur.

Ajiye juice d’in yayi tare da qarasowa in da take tsaye suna facing d’in juna. Qwara kuwa gaskiya kika fad’a ba ta yanda za’ai d’an uwa ya tsani ‘yar uwar sa, ba tare da wani kwakwaran dalilin ba, musamman ma ni da nake son qanne na, kuma nake ganin duk abinda sukayi min bazan ta6a iya rabuwa da suba. Shiruwa zahra tayi tana sauraran abinda mashkhur yake cewa. Cigaba da magana yayi kamar haka!.

Kin san dae halina sam bana son mutane su ringa zuwa gidan nan, kuma ko baqi akayi a gidan nan bana iya sakewa, sabida ni sam banasan hayaniya da kuma na ringa tammali da wanda ba ‘yan uwana ba?. D’aga kai zahra tayi alamun eh kuma tana mamakin mai ya kawo wannan maganar. Mashkhur kuwa cigaba da magana yayi da cewa!! to kinga wanda nasan ASALINSU ma bana son tarayya dasu bare mah WANDA basan daga ina suka FUTOBA.

Da sauri zahra tace to yaya mashkhur mai ya kawo zan can nan kuma?. Jinjina kai mashkhur yayi tare da cewa ai gwara na fara yimiki bayani ta yanda zaki fi fahimtar zancan. Cigaba da magana yayi da cewa bakomaii ne ysa kikaga ina nuna miki qiyayyan nan ba face ke ba JININA bace!. Da sauri zahra ta zaro idan ta tana cewa yaya mashkhur ban fahimci me kake nufi ba?. Jinjina kai yayi tare da cewa ina nufi ke ba ‘yar GIDAN NAN bace, bugu da qari ma ba ammi da dady bane suka HAIFEKI.

zahra kuwa ji tayi nunfashin ta ya tsaya cak sabida tsabar furgici da razani. Murmushin jin dad’i mashkhur yayi tare da cewa yanzu kinji dalilin da yasa na tsane ki ko?. Yana gama fad’ar haka ya kama hanyar fita. Da sauri zahra ta dakatar da shi da cewa haba yaya mashkhur yanzu dan ka tsaneni shine zakace ni ba ‘yar gidanna bace kuma ba ammi da dady bane iyayae na? To idan basu suka haife niba su waye iyaye na.

Da sauri mashkhur ya juyo yana kallanta tare da cewa da ki yadda da kuma karki yanda keki yiwa kanyi ni dai nasan na tameki na gaya miki gaski, dan karma ki qara sakin jikin ki kiga dady yana nuna miki kula ki zata kece ‘ya mafi soyuwa a gare shi. Kuma zance suwaye suka haife ki, bansani ba, ko da yake ma ai ko su ammi da dadyn ma basu sani ba, kamar dai naji momy tana cewa wai a TITI mamanki tabawa hajiya kaka sadakar ki ya qarsa maganar yana ta6e baki.

Murya na rawa zahra tace wlh yaya mashkhur bazan ta6a yadda da maganar nan ba, ko ka manta nida ilham aka haifemu ‘yan biyu ko kuma kana nufin nida ilham d’in duk ba’a gidan nan muke ba. Wata shi’umar dariya mai sauti mashkhur yayi tare da cewa to kada ALLAH yasa ki yadda mana. Inma banda rashin hankali irin naki taya zakice wai ke da ilham ‘yan biyu ne, to bari kiji ilham ‘yar gidan nan ce ammi da dady ne suka haife ta, ko bakiga muna yanayi da ita bane?.

Shiru zahra tayi dan yanzu tama rasa mai zata cewa mashkhur, kokwanto take mashkhur da gaske yake ko kuwa?. Muryar sa ce ta bigi kunnan ta yana cewa, amma bari na tai maka miki ta yanda za’ai ki fahimci abinda nake nufi koma ki gasgaza zance dana ce miki. Kije mudubi kitsaya ki kalli kanki sai ki tantace dawa kike kama a gidan nan kina kama dani ko kuwa kina kama dasu Abdul, kuwa kina kama da ammi ko dady, hardai kikaje kikaga kina kama da d’aya daga cikin ‘yan gidan nan to ki yarda ke ‘yar gidan nan ce kuma qarya nake miki, in kuma kikaga bakya kama dasu to ki yarda da magana ta tacewa ke ba d’aya daga cikin a halin gidan nan bace.

mashkhur yana gama fad’in hakan ya fuce yana sakin mirmushin saman nasara shi yama manta da wani abincin da yazo nema, ya wuce part d’in su. Yana fita kuwa zahra ta silale qasa tai zaman da6aro, nunfashi yana qoqarin d’auke mata, tanaso ta qaryata maganar da mashkhur ya gaya mata amma ina zuciyarta ta kasa bata dama. Zahra ta shiga matsanincin tashin hankalin da tinda tazo duniya bata ta6a shiga ba. Zahra tafi awa d’aya tana zaune anan ta kasa ko kwakwaran motsi. Sai wajan qarfe sha biyu na dare (12:00am) sanna ta rarrafa da kyar ta wuce d’akin su.

Tana shiga d’akin su ta zauna akan bed tana mai da nunfashi kamar wanda tayi ‘yar tsere da zaki. Da qyar zahra ta miqe sabida sarawar da kanta yake mata mudubi ta nufa dan ta tabbatar da maganar da mashkhur ya gaya mata. Tana isa bakin mu dufin ta fara duba fuskarta, amma ina bata tantance dawa take kamaba saka makwan ba wani hasken arziki, da yake glob din light blue ne bashi da wani gaske. Tayi tinanin ta mayar da hasken d’akin white, amma tana tsoran kar ilham ta tashi, dan tasan tana kunna gasken bedroom d’in ilham zata tashi.

kuma bataso ta san abinda ya faru tsakaninta da mashkhur har sai ta tabbatar da maganar mashkhur gaskiya ne. Jiki ba kwari zahra ta juya ta koma kan bed ta kwanta zuciya ciki da baqin ciki. Fulo ta jawo ta rungume shi tana ta sauke ajiyar zuciya sabida sam tama kasa kuka. Addu’o’i zahra ta shiga yi tana qar yata abinda mashkhur ya gaya mata a zuciyar ta, hakan da tayi yasa zuciyar ta d’an yi sanyi. Haka zahra tai ta addu’a har sai wajan qarfe biyu da rabi na dare (02:30 am) ta samu tayi bacci shima ba wani bacci mai d’adi tayi ba kawai bacci takai ci ne..................

6angaran mashkhur kuwa yana shiga bedroom d’in sa ya saki wata siririyar qarar farin ciki da samun nasara tare da daka wani uban tsalle ya fad’a kan gado. Mashkhur wani uban farin ciki ne ya mamaye shi, yanzu ji yake duk duniyar nan tayi mai dad’i ba abinda yake damunsa, zuciyarsa fasss yake jinta. Juyi kawai mashkhur yake akan bed d’in ga sanyi a.c da yake dukan sa kawai yaji duniyar tayi mai dad’i, dan yanzu ma kwata-kwata baya storan tafiya rasha, harma ALLAH-ALLAH yake gobe tayi jirgin su ya d’aga rasha, yaje can ya fara SABUWAR RAYUWA, daga haka bacci mai dad’i ya kwashe mashkhur.............

Washegari gari.........

Tun da asuba mutan gidan suka tashi suna shirya-shiryan tafiyar mashkhur. Zahra kuwa da kyar ta tashi ta iya sallah tana idar da sallar ta sake narkewa akan gado zuciya cike da damuwa. Yau duk yaran gidan bazasu makaranta ba sabida zasu raka yayan su mashkhur airport. Mashkhur ma zuciya cike da farin ciki ya tashi, bayan yayi sallar asuba yaciga da shirn tafiya. Misalin qarfe bakwai na safe (07:00 pm) kowa ya gama shiryawa domin tafiya airport.

Ammi tayiwa mashkhur nasiha sosai da sosai hajiya kaka mah haka, dady ma sosai ya yiwa mashkhur nasiha akan sabuwar rayuwar da zai fara. Ba bata lokaci masu rakiya suka fara shiga motoci domin yin rakiya. Dady, momy,abdul, ilham, rukee, ruma, sune wanda zasu raka mashkhur domin zuwa airport. Ammi da hajiya kaka kuwa suna gida, zahra da ammer kuma suna kwance a gado, zahra tana cikin baqin ciki da damuwa ameer kuwa yana ta sharar baccin sa.

Haka motacin suka fita a jeri suka kama hanyar airport, 6angaran mashkhur kuwa zuciyar sa fass ba abinda yake damun sa har ALLAH-ALLAH yake su qarasa airport d’in.
Lokacin da suka qarasa airport d’in jirgin yana gaf da tashi, dan haka su dady basu 6ata lokaci wajan sallama da mashkhur ba, abdul kuwa har hawaye sai da yayi suka rungume junan su. da qyar suka saki junan su shima mashkhur bai ji dad’i rabuwarsa da d’an uwansa abdul ba.

Mashkhur bai dad’e da shiga jirgin ba, ya tashi. Haka su dady suka kama hanyar gida jikin su duk yayi sanyi.

Zahra......
6angaran zahra kuwa su ilham suna fita ta miqe da kyar jiki ba kwari. Mudubi ta nufa tare da zama a kujerar mudubin. Sosai ta tsurawa kanta ido dan ta tantace abinda mashkhur ya gaya mata. Gabanta ne ya fad’i rass lokacin da ta gama kallan kansa a mudubi, tinda take 6ata ta6a tinanin bata kama da kowa a gidan nan ba, ko dai dan sabida ita farar fatace kamar ‘yan gidan shiyasa bata fahimta ba?. Sai a Lokacin wasu zafafan hawaye suka shararo mata, magan ganin mashkhur ne suka shiga fad’o mata d’aya bayan d’aya.

Wani kukane mai qarfi ya kwace mata, hankalin zahra ya tashi nesa ba kusa ba. Nikuwa amina bayero banga lefinki ba zahra ko ni akace min ba ‘yar gidan mu bace ai hankali na sai ya tashi.😢🙆🏾‍♀️
Kuka take sosai wanda hakan har sai da ya tashi ammer daga bacci. Shima kukan ya farayi yana cewa!! Aunty zahra kizo ki sauke ni daga kan gadon na gaji. Amma ina zahra bama

Please Login or Register in order to submit comment