Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tai tare da cewa! Ai lokacin na gaishe ka baka amsaba shiya na harare ka, oh shiyasa kika yimin hararan nan taki ta gefan ido koh?  Gyakai Ilham,  tai tare da saki siririyar dariya.

Shima Ahmad dariya ya saki tare da cewa!  Gaskiya hararar nan tana burgeni yaushe zaki koyamin nima.  Hararar shi ilham tai ta gefan ido da yake hakan ya zame mata jiki tare da cewa!  Hmm lalai ma ai zaka iya in kasa kanka ba sai an koyama ba,  a wannan lokacin da ilham ta harari Ahmad,  hakan ba qaramin birge shi yayi ba,  sosai yaji ya qara QAUNAR ta.  Tom shikenan tinda bazaki koya min ba,  ajiyar zuciya ilham tai tare da cewa,  nima ba koya min akayiba ni na koyawa kai na,  kai ma sai ka daure ka koya ta qarasa maganar tanq d'an kawar da fuska gefe.

Jinjina kai Ahmad yayi tare da cewa! Tom shikenan a hakan ma na gode da mukayi hira naji dad'i sosai ya qarasa magar yana shigowa get d'in gida.  Ajiyar zuciyar ilham tai tare da cewa,  nima ngd.  Parking d'in motar Ahmad yayi tare da cewa!  Da fatan gobe ma zaki biyota mu kai ta makaranta daga nan musha hira koh?  Yamutsa fuska ilham tai tare da cewa!  Gaskiya ba lalai ba sai na duba na gani,  haba ilham dan ALLAH  ki biyota mana ya fad'a cikin sanyayiyar murya.  Har zuciyar ilham taji dad'in tayin da Ahmad yayi mata.

Tom shikenan tinda ka takura in na tashi da wuri sai na rakata,  murmushi Ahmad yayi tare da cewa! Yauwa ginbiya mata in sha ALLAH  ma zaki tashi,  murmushi ilham tai tare da cewa!  Kai dai ka fiya dad'in baki bud'e min qofa na fita,  shima murmushi Ahmad yayi tare da cewa!  Ai gaskiya na fad'a ya qarasa maganar yana bud'e key d'in qofofin motar,  yana cewa!  Ki bari na zagaya na bud'e miki qofar mana nifa banaso ki ringa wahalar da kanki,  murmushi ilham tai tare da cewa! Aa zan bud'e da kai na by ta qarasa maganar tana bud'e qofar.

By too sai nazo anjima cin girkin ki yanzu nima school zan wuce dariya ilham tai tare da cewa!  Bakaji yaya abdul yana cewa!  Ban iya girki ba ai ni ban iya girki ba,  ta qarasa maganar cikin zaulaya,  Ahmad kuwa cewa!  Yayi kin iya mana ai ni ko bai yi dad'i ba zanci bare ma zaiyi dad'in nasan sharrin yaya abdul ne kawar,  murmushi ilham tai tare da cewa!  Hmm ka dai wuce makarantar ka karka makara bye tana gama fad'ir haka ta fuce daga motar,  bye too cewar Ahmad fuska d'auke da murmushi. Da sauri ilham ta wuce fuska d'auke da fara'a da farin ciki,  Ahmad kuwa ba 6ata lokaci ya fice daga gidan,  ya wuce school.

Cikin farin ciki da annashuwa ilham take hawa step d'in benan,  tana zuwa ta bud'e qofar ta shige,  tana shiga fallon ta yarda mayafin a gefe ta zauna akan kujera,  farin cike ne fal zuciyar ta nan da nan ilham ta fara tunanu hirarta da yaya Ahmad wani abin tai murmushi wani abin tasa hannayanta biyu  ta rufe fuskar ta.  Ilham  ta nitsa duniyar tinani sosai,  dan har sai da mashkhur ya futo ya shiga kicin ya zuba aminci yaci bata dawo daga tinanin taba.  Sam mashkhur bai kula da ilham tunani take ba,  dan hankalinsa baya kanta,  sai da ya zo fita daga fallon sanan ya lura da tunanin da ilham ta tafi.

A hankula mashkhur ya tako ya qaraso wajan da ilham take,  cikin kausa shiyar murya yace Ilham!  Ilham amma ina ilham tayi nisa a cikin tunani,  hannu yasa ya shafa kumatunta yana cewa!  Ke ilham.  Firgigit ilham ta dawo daga tunanin data tafi,  mashkhur ta gani tsaye da littafi a hanunsa da dukkan alamu school zai je.  Zuba mata ido yayi tare da cewa!  Ilham mai kike tunani haka wanan wana kalar mugun tunanin kike kina qara da ke kina wanan tunanin mai yake damunki gayamin naji.  Da sauri ilham ta Girgiza kai tare da cewa! Yaya mashkhur ba abinda yake damuna mai ka gani.

Wani kallo mashkhur ya watsa mata tare fa cewa! Kin d'auki wajan 30 minutes kina tunani kice mai na gani karki rai namin hankali bazaki gaya min mai yake damun kiba?.  Hajiyar zuciya ilham ta sauke tare da cewa!  Wlh yaya mashkhur ba komai kawai ina tunanin ammi da Hajiya kaka  ne shi yasa,  jinjina kai mashkhur yayi a zuciyar shi yana nazarin Ilham tana mace tana haka,  watarana ma da za a yi mata aure,  a fili kuma cewa yayi!  Okay saura kwana hudu zuwa uku ku koma ki dena wanan tunanin bakyau,  ki dena barin damuwa a ranki kina qarama.

Murmushi ilham tai tare da cewa!  In sha ALLAH yaya mashkhur na dena,  murya qasa-qasa yace ALLAH yasa daga haka ya kama hanyar fita,  Ilham kuwa cewa!  Tai a dawo lpya,  amsawa mashkhur yayi da ameen my ilham.  Daga haka mashkhur ya fucewar shi.  kicin ilham ta shige ta kwaso abincin breakfast d'in ta jera musu a draining sanan ta wuce bedroom tai kwanciyar ta,  ba jimawa bacci mai dad'i yayi awan gaba da ita ba abinda takeyi a cikin bacci sai kyawawan makarkai  ita da yaya Ahmad sunyi aure sun haifi yara kyawawa,  nikuwa AMINA BAYERO nace lalai Ilham so yayi miki faka-faka..........

Lokacin da zahra ta dawo tasha labari mai dad'i a wajan ilham dan itama sai da tayi farin ciki,  ranar dai Ilham wuni tayi cikin farin ciki.  Kuma a ranar dady ya suyowa zahra da Ilham  I phone masu tsada,  I phone 11 ya suyo musu zahra fara ita kuma ilham baqa kai ranar ilham da zahra sunyi farin ciki bacci ma da kyar sukayi mussaman ilham da farin ciki ya had'e mata biyu. 

Washe gari........
ci abinci yau ilham kuwa a gaban dady d
Misalin qarfe bakwai sauri su ilham sun gama girki kuma sun shirya, harma suna yaya abdul harma da yaya mashkhur tace zata raka zahra,  kuma ba wanda ya hanata dama shi mashkhur bai cika shiga abinda ba ruwan shiba.  Lokacin da su zahra suka qarasa wajan motar a ciki suka tarar da yaya Ahmad ya kifa kansa akan sitiyarin mota ya tafi duniyar  tunanin,  daga ganima ya dad'e da futowa yana jiransu dama yau sun kusan makara.  Hannu zahra tasa ta fara kwankwasa glass d'in motar fir gigit Ahmad ya dawo daga tunanin  ilham daya tafi,  yana dagowa yaga zahra tsaye tana kwankwasa glass ita kuma ilham tana daga gefan ta.




Fuska a sake Ahmad ya zuge glass d'in tare da cewa!  Sanunku da fitowa!  Yauwa yaya Ahmad ina kwana da fatan ka tashi lpy?  Cewar zahra,  cikin sakin fuska Ahmad yace lpy qalau kuma da fatan kun tashi lpy?  Ya qarasa maganar yana sauke idonsa akan ilham wanda take kallon gefe sai wani basarwa take.  Cikin qasai tacciyar murya yace Ilham ina kwana?  Da sauri ilham ta jiyo tare da cewa!  Ina kwana?  Murmushi Ahmad yayi tare da cewa!  Lpy qalau ilham da fatan kin tashi lpy,?,  gyad'a kai tayi tare da cewa!  Lpy qalau amma sam taqi tayi fara'a.

Haka zahra da ilham suka bud,e baya suka shige Ahmad yaja mota a guje suka fuce.  Zahra kuwa mamaki take wannan wana irin jan aji ilham take,  shima Ahmad yana mamakin yadda ilham take da wuyar sha'a ni,  kamar ba itace jiya suka sha hira ba.  Da wanan tunanin ahmad har ya qasa makarantar su zahra,  zahra kuwa bakinta ta kai dai-dai kunnan ilham cikin rad'a tace sai kin je a garan jan aji,  aji ya tsinke,  ta qarasa maganar tana sakin murmushi mugunta daga haka ta fuce daga motar tana cewa!  Yaya Ahmad sai anjima.

Okay bye qanwata ayi karatu da kyau qanwata?,  in sha ALLAH yaya Ahmad,  daga haka ta rufe qofar motar tai wucewarta cikin makaran.  Ahmad kuwa juyowa yayi ya kalli ilham tare da cewa!  Wai Ilham yau mai yake damunki naga kina had'e rai sai kace ba kece bakece mu sha hiraba?  ya qarasa maganar yana zuba mata kyawawan idanuwan shi,  hankalin ilham ya d'an tashi lokacin da zahra tace mata a garin jan aji sai aji ya tsinke dan haka ba shiri ilham ta saki fuska tare da cewa!  Ba komai wlh,  shima murmushi yayi tare da cewa! Ko dai tsoran qanwata kikeji harta zane ki?.

Dariya ilham tai tare da cewa! Lalai ma ni kuma sai na tsaya ta dake ni,  jinjina kai Ahmad yayi tare da cewa!  Ba dole ba ai gaba take da ke tinda matar yayan kice.  Girgiza kai tai tare da cewa!  Aa nifa ba a haka na d'auke ta ba a matsayin 'yar uwata ko nace ma hassana ta na d'auke ta ilham ta qarasa maganar tana sakin murmushi mai ciki da qaunar zahra.  Jinjina kai Ahmad yayi tare da cewa! To ALLAH ya sake had'a kanku hassana da husaina,  dawo gaba dan muji dad'in hirar koh?  Ba musu ilham ta miqe,  ta futo daga baya sanan ta dawo gaba abinta......... 

Mu had'e a next page.


ADALILINTA💜❤💜  

BY AMINA BAYERO💜❤💜

                                    Typing............

                                    *page 72*

Jinjina kai Ahmad yayi tare da cewa! To ALLAH ya sake had'a kanku hassana da husaina,  dawo gaba dan muji dad'in hirar koh?  Ba musu ilham ta miqe,  ta futo daga baya sanan ta dawo gaba abinta.........  

Daga haka Ahmad yaja mota suka fara tafiya. Can kuma yace yau baza muyi hirar bane?,  hmm in kana so ai sai ayi Ilham ta fad'i hakan tana gyara mayafin jikinta,  da sauri Ahmad yace kai sosai ma ai ni inasan hira musamman ma ta irinku kyawawa murmushi ilham tai tare da cewa!  Aa dai ai kune kyawawan.  Zaro ido ahmad yayi   tare da cewa!  Ah gaskiya ki dena zagina ni har wani kyakyawa ne?  Murmushi ilham tai tare da cewa!  Kwarai ma kuwa, hmmn tom shikenan godiya nake duk da nasan kawai kin fad'a ne.

Dan had'e rai ilham tai tare da cewa!  Ok baka yadda da magana ta ba kenan?   Da sauri  Ahmad yace no na yadda mana ALLAH ya wuci zuciyar gimbiyar mata,  ba kunya ilham tace amen,  murmushi Ahmad yayi da yaji ilham tace amen a zuciyar sa yace lalai ma ilham  wanan ko kimin 'yar karar nan kice banyi laifi ba,  kai shiya nake qara sanki a fili kuma cewa!  Yayi tom da fatan dai zuciyar taki ta wuce,  gyad'a kai ilham tai tare da cewa!  Ehh ta wuce mana.  Yauwa haka akeso,  daga haka sukayi shiru na wasu lokutan kafin yace!  Yauwa da fatan dai baki manta da taimakwan da nace zakiyimin ba ko.

Juyawa ilham tai ta kalli ahmad tare da cewa!  Ehh to na manta da zancan amma yanzu daka tinamin na tuno,  jinjina kai Ahmad yayi tare da cewa! Yauwa ilham dan ALLAH  a cire maganar wasa kinji inaso muyi magana mai mahinmanci,  gaban ilham ne ya d'an fad'i amma dakewa tai tace mai tom shikenan inajinka.  Shiru Ahmad yayi na wasu lokutan kafin yace!  Kinsan mene?  Girgiza kai ilham tai tare da cewa!  Sai ka fad'a,  Ahmad kuwa raqe gudun motar yayi,  sanan ya mayar da hankalinsa kan tukun kafin yace!  Da akwai wata yarinya da nake mutuwar so yadda bakya tsammani.

Ilham jin maganar tai babbara kwai ita da take shirin taji yace yana son ta amma yace wata yarinya?.  Ahmad kuwa ci gaba da magana yayi da cewa!  Sosai nake qaunar Ta kuma na dad'e inason ta,  amma sam ita bama tasan ina son taba,  ina tunanin ma bani ne a gabanta ba,  tom shine nake neman shawara amma a matsayin ki na qawata 'yar uwata kuma qanwata KI bani shawara.  Shiru ilham tai tana nazarin zancan ada hankalita ya tashi sosai da taji yace wata yarinya,  amma sai tai tunanin wataqila itace fa,  murmushi jin dad'i ilham ta saki sanan tace tom kasan mai zakayi?.

Da sauri  ahmad ya kalle ta tare da cewa!  Aa ilham mai zanyi,  haba yaya ahmad sai kace ba namiji ba?  Ni wlh ma ka bani kunya,  cikin mamaki ahmad yace kunya kuma ilham kunyar me?  To ba dole nace ka bani kunya ba sai kace ba namiji ba kawai kaje ka gaya mata.  Lumshe ido ahmad yayi ya bud'e sanan yace bawai bazan iya gaya mata bane kawai ina tsoran taqi amincewa ne sabida in bata amince ba wlh bansan yadda zanyi da rayuwa ta ba,  yarinyar ta kamani sosai yadda bakya tsammani,  gani nake anya zata sone,  sabida yarinyar kyakyawace mai aji ina tinanin da kyar in zata soni.

Ajiyar zuciyar ilham ta sauke tare da cewa!  Haba yaya ahmad wace mace ce zataqi sunka akan me zataqi sanka,  kanada kyau kana da ilimi bugu da qari ga mutunci da karrama mutane kana da sakin fuska,  duk wani abu da 'ya mace take buqata ka tara shi d'ari bisa d'ari,  ni ina da tabbacin yarinyar nan bazata qikaba.  Da sauri  ahmad ya kalli ilham tare da cewa!  Har da ke?  Jim ilham tai zuciyar ta taf ciki da farin ciki,  ta dafe qirjin ta irin kamar ta tsoranta nan tace ni kuma?  Ggyd'a kai ahmad yayi tare da cewa! Kwarai,  jim ilham tai na wasu lokutan tare da cewa!  Ai nasan bani bacema.

Cikin mamaki ahmad yace sabida mai kikace haka?  Shiru ilham tai na wasu lokutan kafin tace sabida nasan bani bace ba shiyasa nace hakan,  a dai-dai lokacin ahmad ya shigo get d'in gidan,  daga haka bai sake cewa! Komai ba har sai da ya parking d'in motar sanan ya juyo ya kalli ilham wanda take qoqarin fita,  cikin murya mai ciki da rauni ahmad yace ilham ya zaki tafi ba mu gama maganar mu ba,  juyowa ilham tai tare da cewa! Oh yaya ahmad ya haquri nayi tinanin mun gama ne shi yasa,  ta qarasa magana tana gyara zamanta,  tare da kafeshi shi da idanuwan ta.

Cikin voice mara qara Ahmad yace!  Ilham kinsan wace yarinya ce?  Gaban ilham ne ya fad'i rass amma sai ta d'an dake tace aa yaya Ahmad tayaya zansan wace yarinya ce,  nida baka gayamin ba kuma ban ta6a ganin taba.  Jim ahmad yayi na wajan minti 2 kafin yace Ilham ke CE yarinyar da NAKESO,  duk da Ilham tasan Mai ahmad zai ce mata amma lokacin daya fad'a sai da gabanta ya fad'i yayi mugun fad'uwa rass rass rass,  har sau uku gabanta ya fad'i.  Cikin rawar murya Ilham tace ni kuma yaya ahmad?  Da sauri  ahmad ya d'aga kai tare da cewa! Kwarai ilham ke nake nufi.

Sosai dad'i ya sake lulu6e zuciyar ilham,  amma a fili cewa tai aa yaya ahmad ni nasan wasa kakemin ba ni bace yarinyar da kake so. Kamar ahmad zai yi kuka yace haba Ilham akan me zanyi miki wasa  da irin wanan kalma mai daraja da tasiri,  wlh wlh wlh rantsuwa musulmai ilham kece wanda nake so,  na dad'e ina qaunarki a zuciyata tun sanda na fara ganinki a duniya naji ina son ki kuma daga lokacin kullum dake nake kwana dake nake tashi a zuciyata,  watarana ma in sanki ya motsa ko bacci bana iyayi,  dan ALLAH Ilham ki ceci ruhina ahmad ya qarasa maganar kamar zai sa kuka.

Shiru ilham tai na wasu lokutan kafin yace to shikenan sai na duba na gani,  ajiyar zuciya ahmad ya sauke sanan yace ni dai ilham ban takura miki akan dole sai kin soni ba,  amma dan ALLAH karki qini Ilham,  shiru ilham tai ba amsa,  can kuma tace bari na shiga ciki.  Tom shikenan ilham amma zuwa yaushe zaki gama shawarar?  Jim ilham kafin tace nima bansan zuwa yaushe ba amma zuwa gata zamu koma gida Nigeria,  cikin tashin hankali ahmad yace Nigeria kuma ilham ?  Gyad'a kai tayi alamun ehh,  cikin karyayiyar murya ahmad yace pls ilham zuwa gobe dan ALLAH ki yanke shawarar,  bud'e murfin mota ilham tai tare da cewa! Tom ALLAH ya kai mu gobe tana gama fad'in hakan ta fuce daga Motar.

Wani uban tagumin ahmad ya rafka yana tinanin yaya zata kaya tsakanin shi da ilham gobe? Jikinsa duk yabi yayi sanyi tabbas Ahmad ya shiga tashin hankali yadda masu karatun littafin ADALILINTA basuyi stammani,   Ahmad bai ta6a tinanin haka so yake da zafi ba sai akan ilham ashe adacan ahmad da 'yan matansa ba soyayya suke ba kawai abota da hira yake?  Abinda ahmad yake tinani kenan,  cikin rashin kwarin jiki ya futo daga motar  ya wuce part d'in shi zuciya ba dad'i,  amma ta wani fannin in ya tina ya sanar da ilham abinda yake zuciyarsa sai yaji  dad'i,  ba kamar da can da batasan abindda yake yake damunsa ba.....

6angar ilham kuwa ji tai jikinta duk yayi sanyi tana shiga gida batabi takan kowa ba ta wuce bedroom d'in zahra ta kwanta.  Wani irin mugun son Ahmad da tausayinsa ne ya kamata,  a lokacin da yake mata magana akan yadda yake son ta ji tai kamar itama ta gaya mai yadda take qaunar shi,  kawai dakewa tai ada tayi tinanin baza jawa ahmad lokaci harma sai ta koma nigeria  zata sanar da shi tinda tana da waya,  amma a halin da ta ganshi yau duk sai ya karya mata tsatsauran qudirinta akan shi,  wani siririn hawaye ne ya ziraro mata mai ciki da qauna da tausayin  ahmad,  haka dai ilham tai-tai juyi akan gado har bacci ya kwashe ta....





Lokacin da zahra ta dawo daga school sai da ilham ta bata labarin abinda ya faru tsakaninta da yaya ahmad,  zahra kuwa tanaji ta fara roqan ilham akan dan ALLAH ta amincewa yaya ahmad zuwa gobe,  cikin murya mai ban tausayi zahra tace!  Wlh ilham yaya ahmad ya dad'e yana sanki ki amince mai karki sa shi wani hali wlh har yaba tausayi,  itama ilham cikin muryar ban tausayi tace!  Ai zahra ko baki fad'a ba zuwa gobe zan sanar da shi ina qaunar shi kuma na amince,  sabida nima bakiji yadda zuciyata take min quna akan son yaya ahmad ba wlh zahra ina qaunar yadda bakya tinani  dama haka so yake?.

Ta6e baki zahra tai tare da cewa!  Ni da bansan so ba ilham taya zakimin wanan tabbayar,  jinjina kai ilham tai tare da cewa!  Hakane zahra amma in sha ALLAH zaki samu MASOYI mai sanki fiye da yadda yaya ahmad yake son ki,  murmushin yaqe  zahra tai tare da cewa!   Anya ilham zan samu wanda yake sona a duniya kamar yadda yaya ahmad yake qaunar ki?.  Nikuwa AMINA BAYERO nace tabb ai zahra ki dena cewa anya zaki samu mai sani,  kina ma dashi kin manta da yaya abdul da yake mutuwar sanki,  ko da yake ai bakisan yaya abdul yana miki son aure da muddin rai ba.

Ilham kuwa cewa zahra tai!  Haba zahra ba'a yanke tsammani,  kikasan ko nan gaba yaya mashkhur zai soke fiye da yadda yaya ahmad yake sona?.  Wani siririn tsaki zahra ta saki tare da cewa pls ilham mubar zancan nan kawai, ta qarasa maganar tana qoqarin tashi da sauri ilham ta ruqo ta tare da cewa!  Dan Allah dawo ki zauna, na dena yi miki zancan yaya mashkhur d'in tinda bakyaso,  zama zahra tai tare da cewa! Dama ya fiyemin alkhairi ai.  Cikin nazari ilham tace yanzu zahra taya zan iya cewa yaya ahmad na amince da soyayya shi kuma ina son shi.

Zubawa ilham ido zahra tai tare da cewa! Kamar ya ta yadda ya gaya miki yana qaunar ta haka kema zaki cemai kin amince kina son shi,  rausayar da kai ilham tai tare da cewa! Wlh zahra bazan iya kallon idon shi na gaya mai ina qaunar shi ba kuma na amine da soyayyar shi.  Tom ilham kema kanki bazaki iya gaya mai kina qaunar shiba bare ni mai tsoro,  kawai ki d'auko biro da takadda ki rubuta mai sai ki bashi zuwa gobe koh?   Murmushi ilham ta saki tare da cewa hakane zahra,  ba shiri ilham ta miqe ta nufi jakar zahra ta bud'e jakar ta dakko pepa da biro ta fara rubutawa,  zahra kuwa murmushi tai tare da cewa! Kai ilham sarkin zumud'i ke da zaki bari sai gobe kafin mufita sai ki rubuta?.  Dariya ilham tai tare da cewa! Ke rabu da ni ba'a bore da sanyi jiki...........

Washe gari........... 

Kamar kullum da sassafe su ilham,  suka gama girki sanan sukaci,  zahra tana futowa daga wanka,  ilham ta shiga nan da nan zahra ta fara shiryawa,  tana gama shiryawa ta fara qoqarin d'aure gashinta da ribbon amma sam ta kasa,  sabida gashin nata ya qara tsayi da yawa saka makwan ta tsefe kitson da ilham tai mata,  direct falo zahra ta nufa hannu riqe da ribbon da hijab d'in ta,  tana fita taga ba kowa a  fallon sai yaya abdul, direct wajansa yaya abdul ta nufa,  tana zuwa ta zauna a kusa da shi tare da cewa!  Yaya abdul good morning,  murmushi abdul yayi tare da cewa! Good morning too my babe how are you?  Murmushi zahra tai tare da cewa! I'm fine yaya abdul and you?  I'm very  fine my babe,  miqa mai ribbon d'in tai tare da cewa! Gashi yaya abdul ka d'aure min gashina na kasa.

Kar6ar ribbon d'in yayi tare da cewa! Okay my babe,  daga haka zahra ta kifa kanta akan cinyar yaya abdul d'in shikuma abdul ya fara tattare mata gashin nata da yake duk ya rufe mata fuska.  A dai-dai Lokacin mashkhur ya futo daga bedroom d'in shi ai kuwa kararaf idon shi ya sauka akan abdul da zahra,  zahra ta kwantar da kanta a cinyar abdul d'in shi kuma sai faman tattare mata gashin yake,  haka nan mashkhur yaji gabansa ya yanke ya fad'i rass,  sam basu san mashkhur ya shigo falon ba sabida a hankula yake takawa kamar mai sand'a.

A sannu a hankula mashkhur ya qarasa kan draining ya zauna,  ya fara had'a t,  sai a lokacin ma abdul ya lura da futowar mashkhur d'in.  Tinanin mashkhur ya tafiyi akan abinda idon sa ya gane mai,  har cikin zuciya shi yasan abinda zahra da abdul suke sam basu kyauta ba,  zahra tana da aure amma har yanzu bata yanke alaqarta da  abdul ba,  sai ma abinda ya qaru?.  A cikin zuciyar shi kuma sai yaja tsaki tare da cewa!  To mene na damun kai na ma bayan saura 'yan watanni na sake ta nida ba ma qaunar ta nake ba,  mashkhur yana kai nan yaji abdul yace kai baby na wlh gashinki ya cika yawa ga santsi nayi missing d'in yi miki tsifa wlh.

Cikin shagwara zahra take cewa!  Kai yaya abdul nifa yanzu na girma bazaka qara yimin tsifa ba sabida na iya ta qarasa maganar tare da d'ago kanta daga cinyar yaya abdul d'in,  murmushi abdul yayi tare da jan hijab d'in hannun zahra da qarfi yana cewa!  Ke bama tsifa ba har hijab yau ni zansa miki.  Mashkhur kuwa sakin baki yayi sakatata yana kallon ikwan ALLAH,  tunda yake bai ta6a jin haushin abdul ba sai yau,  kuma bai ta6a ganin  abdul bai kyauta ba sai yau.  Da sauri  mashkhur ya kawar da kansa daga kallonsu ya mayar kan cup d'in t d'in shi.

Karaf mashkhur yaji muryar zahra tana cewa!  To yi sauri ka sakamin karna  makara,  shima mashkhur d'in d'an juyowa yayi dan idon sa ya gane mai gaskiya zancan ai kuwa yana juyowa yaga abdul yana sawa zahra hijab d'in.  Da sauri  mashkhur ya kawar da kai a zuciyar shi yace Lalai dama yarinya nan 'yar iska ce haka? Ko a mafarki mashkhur a yadda yake tinanin zahra bai ta6a tinanin zata aikata wani abu makamancin hakaba amma sai gashi ya gani da idon shi ba labari,  nan da nan mashkhur yaji ya qara tsanar zahra fiye da dah ji yayi sam bazai iya shan shayin ba,  miqewa yayi ya koma bedroom.

Yana shigewa Ilham,  ta futo annu riqe da jakar zahra tana cewa!  Zahra taso mu tafi, da sauri zahra ta miqe tare da cewa!  Yaya abdul by sai na dawo murmushi abdul yayi tare da cewa! By take care my babe,  murmushi itama zahra tai tare da cewa! Take care too,  ilham kuma cewa tai yaya abdul sai na dawo,  okay uwar kishi kema so kike a

Please Login or Register in order to submit comment