Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amince bazan gaya musu ba. To ina qoqarin tashi daga wajan sai ga ammi da dady son sauko daga kan bene. Sanan sukace na tsaya zamuyi magana. Wai kin san da dady ya tambaye shi ya amince ya cigaba da zama dani a matsayin mata mai yace?. Girgiza kai ilham tai tare da cewa mai yace.

Wai haka yace bai amince ya cigaba da zama dani a matsayin mata ba. Cikin mamaki ilham tace haka yace? Gyad'a kai zahra tai tare da cewa! Kwarai nima da aka tambaye ni nace ban amince ba. Daga haka dady yace naje na kwanta to ban dai san yaya suka qarqare ba. Tom bayan wasu lukuta shine ammi tazo kirana, ehh dama ina so naji mai ammi tace miki jiya wai ilham ta fad'a tana gyara d'aurin towel d'in da yake qirjin ta.

Nan da nan zahra ta bawa ilham yadda sukai da ammi tinda dafa tambaya har zuwa checking d'in ta da kai. Jinjina kai ilham tai tare da cewa oh ni dai zahra wanan lamarin ya ishe ni wlh, yanzu dai kuna nufin auran nan naki ke da yaya mashkhur sai an raba wlh kullum fatana ku fahimci junan ku amma lamarin yaci tira.

Ta6e baki zahra tai tare da cewa tinda bama son junan mu mai ya rage ai kuwa dole araba auran nan, zahra ta qasa maganar tana miqewa. Jiki a sanyaye ilham tace to ALLAH ya fimu sanin komai, ALLAH ya sai sai ta lamarin dan darajar annabi wlh suma ammi da dady basa son a raba auran nan fa.

Hmm ni bari na shiga wanka in na fito wanka muje muyi breakfast yunwa nake ji dan zancan nan bashi da wani amfani, zahra ta qarasa maganar tana qoqarin cire kayan ta. Itama ilham miqewa tai ta nufi kwaba ta fara d'ebo kayan da zata sa bayan ta d'ebo ta fara sawa ita kuma zahra tana cire kayan ta ta d'auki towel ta d'aura sanan ta shige toilet.

Zahra tana fitowa daga toilet ta shirya sanan suka fuce ita da ilham domin yin breakfast. Suna qarasawa wajan draining suka tarar da haidar da faruq suna kan draining suna breakfast. Jinjina kai ilham tai tare da cewa watanni saban gani da safe, yau kune kuka riga kowa zuwa wajan breakfast mai ya faru ne?.

Haidar kallan faruq yayi sukai murmushi tare da cewa! Uwar gulma ba abinda ya faru kawai ALLAH ya shirye mu ko ba haka ba faruq, gyad'a kai faruq yayi tare da cewa! Sosai ma kawai ALLAH ne ya kintsa mu. Ilham cewa! Tai kai wanan zancan da sake ku da sai wajan qarfe goma kuke tashi in baku da school anya kuwa.

Ilham tana rufe bakai taji muryar abdul yana cewa! Hmmm ke dai bari ilham wlh ba tsoran ALLAH ne yasa suka fito da wuri ba kema dai kin san yaran nan basa ji. Dariya ilham tai tare da cewa haba ni nasan da haka yaya abdul mai ya faru ne ko sunyi gamo ne. Murmushi abdul yai tare da cewa! Wlh gamo sukayi da yaya mashkhur yau da ruwa aka tashe su sallah asuba.

Dariya ilham tai tare da cewa! wai wa yaga su yaya faruq ansha ruwa a fuska. Harara zuka zuba mata haidar yace to uwar munafurci tinda kinji abinda ya futo damu ai hankalin ki sai ya kwanta. Faruq cafe zancan yayi da kai dai bari haidar ai shi yasa zahra take birge ni ba ruwanta da shiga abinda ba ruwan ta.

Murmushi zahra tai tare da hmmm gaskiya ya haidar da ya faruq ALLAH ya shirye ku yanzu har sai an tashe ku sallah asuba zaku tashi. Haidar cewa yayi kai zahra ana yaban ki sallah zaki kasa alwala kuma? Hmm kai dar bari tana tare da ilham ba dole ba ai kasan 'yar qa'ida ce, cewar faruq. Daga haka abdul ya katse zancan da cewa good morning my babe da fatan kin tashi lpy yau dai ALLAH yayi tare zamuyi breakfast.

Murmushi zahra tai tare da cewa morning too yaya abdul how was your night?. Murmushi abdul yayi tare da cewa! Very fine, ya qasa magar yana qarasowa kusa da zahra tare da ja mata kujerar draining. Zama zahra tai tana cewa nagode nake yaya abdul, shima abdul daga haka ya ja kujera ya zauna a kusa da zahra abinsa.

Itama ilham kujera taja tare da cewa shikenan kuma yanzu kulawar da nake samu a wajan yaya abdul na rasata tinda zahra kika dawo wato ni baza'a jamin kujerar ba. Hhh dama can ke ta roba ce zahra ce ta qarfe, faruq ya fad'a yana yiwa ilham gwalo. Sosai ma ai shishigin tane kawai yasa ta shiga gurbin zahra ta zauna a wajan yaya abdul haidar ya fad'a yana zubawa zahra harara.

Huro hanci ilham tai tare da cewa wlh wuce nan dama can ina da fawa a wajan yaya abdul. Ah ba wani mai guri tazo mai tabar ma sai ta nad'e ko ba haka ba haidar faruq ya fad'a yana kallan haidar. Haidar cewa yayi sosai ma hakane, daga haka haidar da faruq suka had'a baki wajan sakin dariyar mugunta. Haka haidar da faruq sukai ta tsokanar ilham, itama tana ramawa gefe guda kuma yaya badul da zahra suna breakfast d'in su hankalin kwance tare da hirar su mai dad'i..................

AMMI.............

bayan ta gama yin wanka tayiwa ameer shima, kincin ta wuce ta zubawa dady a binci bayan ta gama zuba mai breakfast d'in shi a tire ta jera sanan ta wuce part d'in dady. Bayan ta kai mai abinci zama ammi tai suna cin abincin tana sheda mai bafa abinda ya shiga tsakanin zahra da mashkhur. Dady lamarin bai mai dad'i ba sosai, kallan ammi yayi tare da cewa, yanzu shikenan raba auran mamana da mashkhur ya tabbata.

Ammi tana qoqarin magana taji an murd'a handel d'in bedroom d'in da qarfi an banko qofar. Daga ammi har dady mayar da hankalin su sukayi kan qofar suna jiran ganin mai shigowa. Momy ce ta shigo, fuska a had'e sai da ta shigo tsakiyar d'akin sanan tayi sallama. Dady kuwa sabida baqin ciki ko sallamar bai samu damar amsawa ba afili sai a zuciya ya amsa ya mayar da kansa ya cigaba da cin abinci.

Fuska a sake ammi ta amsa sallamar tare da cewa barkan ki da shigowa ina kwana halima?. Fuska ba yabo babu fallasa momy tace lpy, ammi mayar da kai tai cikin plate d'in abinci suka cigaba da cin abincin su ita da dady kowa da abinda yake saqawa a zuciyar sa. ALLAH sarki kice abincin ma tare kuke cin wai ko har yanzu bazaku girma bane.

Shiru dady yayi nan ma baice komai ba, hmmm ko da yake tinda har kwanan haramin kuke dan kunci abinci a plate d'aya ma zan damu ne. Nan ma shiru ba wanda ya tankawa momy, hmmm magana nake so nayi da miji na in ba damuwa zaki iya bamu waje?. Murmushi ammi tai tare da cewa ba komai ai sai na baki waje tinda kina so.

Zata miqe kenan dady yace maryam zauna duk abinda zata fad'a sai dai ta fad'a anan inaji ba inda zaki. Ta6e baki momy tai tare da cewa hmm lalai 'yan gwal kenan gaskiya dadyn abdul ka mallaku ba laifi. Ehh na godewa ALLAH da kika gane hakan na mallaku mana, dady ya bawa momy amsa fuska ba walwala.

Zama momy tai a gefan gado tare da cewa! Eee naga alama ai kasha barbad'e da rubutun malam koh?. Shiru dady yayi mata ba amsa, ita dai ammi sai taji bataji dad'in abinda momy tace ba amma sai ta sunkuyar da kai ta cigaba da cin abincin ta. Dama cewa nai inason tafiya kaduna nace bari nazo na gayama. Jim dady yayi na wasu lokutan tan can kuma yace to bazaki je ba.

Kamar ya bazani ba ni mai zanyi ma a gidan in na zauna naga sai nai sati ko qafata baka gani ba a d'akin nan ba sabida ni ba mayyar miji bace kuma ba damu da nacewa miji ba, da nayi tafiyar da banyi ba mai zai qarama mai zai ragema. To hakan har wani abun alfahari ne a wajanki dan kinqi zuwa wajan na ai mala'iku ne zaki kwana suna tsine miki duk ranar kwanan ki dady ya fad'a yana watsa mata harara.

Ta6e baki momy tai tare da cewa! Au ashe kasan hakan ai nasha asirin da tai ma ya manta da kai wanan hadisin. Shiru dady yayi bai cewa momy komai ba, momy kuwa cewa tai qanin mahaifina ne ya rasu kuma shi ya riqeni tun ina yarinya sai daga baya na dawo gidan mu harka ganni ka aure ni dan haka ubana ya mutu ko waca mallaka tai ma ba ruwana sai ka barni naje.

Dady kallan momy yayi tare da cewa to bari na tambaye ta koza ta bani uwar ni kinsan dai shi aikin mallaka haka yake kar kuma naje na barki ki tafi nai mata laifin. Sakin baki momy tai tana mamaki jin abinda dady yace, dady kuwa kallan ammi yayi tare da cewa! Ya kike gani na barta taje ko kuwa ya kikace?. Duk dady yayi hakan ne sabida ya turawa momy haushi. Gyara zama ammi tai tare da cewa ka barta mana tinda mahaifin ta ne ya rasu.

Kallan momy dady yayi tare da cewa to kinci darajar masu daraja, kije na barki amma ki bari sai ranar talata sabida ranar litinin doctor habib zai kawo kud'in auran rukkayya. Wani dogwan tsaki momy taja tare da cewa, lalai mijin tace ba shakka yanzu in badda an mallake ka har sai ka tambayi matar ka zaka barni zuwa gidan mu koh?.

Kuma dawa kayi shawara har zaka bayar min da 'yata?. Dady cewa yayi kinga halima dallah karki samin ciwan kai ki kama gaban ki ko kuwa ranki ya 6ace. Miqewa momy tai tare da cewa! Dama mai zan zauna nayi a nan tinda an riga da han shanye ma zuciya aiki banza kawai ta qarasa maganar tana kama hanyar fita.

Tana fita dady ya ajiye spoon d'in hanunsa a cikin plate ya kalli ammi tare da cewa kai jarabar matar nan ta ishe ni nayi dana sanan auro ta wlh. Itama ammi ajiye spoon d'in hanunta tai tare da cewa! Ka dai na fad'in hakan ba gashi yanzu ka samu arzikin 'ya'ya har uku da ita ba, kayi haquri ka cigaba da yi mata addu'a ko ALLAH yasa zata gane.

Hmmmm maryam kenan si in dai halima ce koh to bazata ta6a shiryuwa ba tin ina yi mata addu'a har na gaji, wlh badaban hajiya ba da tini na saki matar nan bata ganin mutunci na gashi bata jin magana ta yadda kika son ba matata ba ta dad'e da yanke wata hakaqa da ni. Sosai ammi ta ringa bawa dady haquri akan momy har ya wuce suka cigaba da cin abin su, da kuma hira................

3 days ago.

Yau ta kasance ranar talata kuma yau ce ranar da za'a kawo kud'in ilham da rukee?. Ammi da zahra harma da ilham tun da safe suke ta aikin da girki kala-kala na tarar baqin. 6angaran momy kuwa ba abinda ta tsinana sam bama tasan harda kud'in ilham za'a kawo ba. Tana can tana shirya-shiryan tafiya kaduna gobe.

Tom misalin qarfe 12 na safe aka kar6i kud'in sa ranar rukee. Ita kuma ilham sai qarfe 4 na rana aka qar6i kid'in sa ranar ta, kuma gaba d'ayan su an sa musu rana nan da wata uku kacal. Hmmm zo kaga farin cikin wajan ilham da su ammi da zahra kai gaba d'aya gidan kowa yana taya ilham da rukee farin ciki. Sun had'e waje guda suna tsara shirya-shiryan biki.

Su 4 suke ta hirar yadda biki zai kasance daga zahra sai ilham rukee da kuma ruma, da yake yanzu ruke suna shiri sosai musamman ma da zahra sun fahimci junan su sosai da sosai. 6angaran momy kuwa da taji harda kud'in ilham aka kawo hankalin ta in yayi dubu ya tashi don ko abinci bata iya ciba, sabida tsabar baqin ciki dan ita duk abinya 'ya'yan ammi zasu cigaba to fah bata son shi.

Washe gari................

Momy da sassafe ta fara shirin tafiya kaduna, da taso ta tafi da su rukee amma dady ya hana ta yace sai dai ta haqura da zuwa. A ala dole momy ta haqura da tafiya da su ta barsu a gida. 6angaran su ruma kuwa farin ciki ba'a magana dan suma suna so a barsu a cikin gida ko dan su shiga cikin 'yan uwan su. Tofa motar momy ta d'aga zuwa kaduna zuciyar momy cike da magayan qudiri kala-kala.

Hmmm wana asiri momy zata yi a wajan Boka?..........

Kuna ganin zata samu nasara ko kuwa?.......

Mu had'u a next page gobe.




ADALILINTA💜❤💜

BY AMINA BAYERO 💜❤💜

Typing.............

*page 100*

6angaran su ruma kuwa farin ciki ba'a magana dan suma suna so a barsu a cikin gida ko dan su shiga cikin 'yan uwan su. Tofa motar momy ta d'aga zuwa kaduna zuciyar momy cike da magayan qudiri kala-kala.

Hmmm da tini yau zan gama littafin nan amma ALLAH baiyi ba wlh a page d'ari nai niyar tsayawa. 😂

To momy ta sauka garin kaduna lafiya qalau, tana sauka gidan su ta fara zuwa. Bayan ta huta taci abinci misalin qarfe uku ta shirya ta tafi gidan saratu. Ko da taje bata wani tsaya yiwa mai gadi bayani ba sabida mai gadi ya haddace fuskar ta. Tana shiga gidan taga 'ya 'yan kishiyar saratu baje a babban tsakar gidan suna wasa.

Momy ko amsa gaisuwar da suke mata batayi ba, sabida ita yanzu burinta ta shiga ta samu saratu kawai, su wuce wajan boka ayita ta qare kawai. Momy tana shiga part d'in saratu, ta ganta ta fito tana qoqarin fita daga gidan. Suna ganin janan su sukayi wata irin shegiyar shewa sanan suka rungume junan su. Momy ce tace ina zuwa haka bayan na ce miki ina tafe zanzo?.

Wlh yaya halima na gaji da jiran ki ne shiyasa nace kawai bari na biyo ki gidan mu nayi tinanin kin fasa zuwa sai gobe. Girgiza kai momy tai tare da cewa! Hmmm saratu kenan ai bazan iya bari sai gobe ba kinga yadda na matso muga boka nan kuwa?. Jan hannun momy saratu tai tare da cewa! Zo mu shiga ciki dai na bigawa boka waya kin san yanzu ganin sa yayi wuya sabida mutane yadda suka tururuwar zuwa wajan sa.

Ajiyar zuciya momy tai tare da cewa! To muje dai ALLAH yasa yana free bashi da aiki. Suna shiga suka zazzauna akan kujera sanan momy ta zaro waya ta fara bigawa boka. Bayan ya d'aga ko gaisuwar arziki basuyi ba dama ba'a batin sallama saratu ta fara kora mai jawabin zasuzo yanzu. Bayan ta gama korawa boka jawabi boka cewa yayi su bari sai gobe da wuri suzo yau yana da aiki sosai ko sun zo ma bazai saurare su ba.

Bayan saratu sunyi gama magana da boka kashe wayar tai tare da kallan momy tana cewa kinji abinda yace ko da yake wayar a hands free take. Cikin damuwa momy tace naji saratu. Jinjina kai saratu tai sanan tace yanzu ya kenan ko zaki kwana anan ne gobe sai mu tafi da safe?. Da sauri momy tace kai rufamin asiri kar dadyn abdul ya cinye nama na d'anye kuma gashi mijinki yana nan ya ga na kwana a gidan nan kinsa yana ganin mutunci na sosai fa.

Ke yaya halima mai dadyn abdul ya isa yayi miki ai yanzu kinci dubu sai ceto sai dai ya zuba miki ido, kuma mijina ai baya nan ya tafi umara shi da babbar 'yar sa. Wani tsaki momy taja tare da cewa! Kina nan kika bari ya tafi da 'yar kishi koh? Ke kuma ko oho ai ke ya kamata ya tafi da ke, inaga bai fi sau biyu ya kai ki umarar ba koh?.

Saratu cewa tai hmmm ke dai bari yaya halima ai ina gab da maganin komai ni asibiti ma zanje ai min dashan 'yan uku biyu maza d'aya kuma mace dan na gaji da rashin haihuwar nan yanzu mai gidan nan yana fad'uwa ya mutu kishiyata ce fa zata cinye gadan da wanan mitsiya tan 'yayan nata. Momy kuwa cewa tai ai kuwa dai ai miki ma dashan 'yan hudu ma biyu mata biyu maza in cikin ya isa haihuwa sai a miki cs a ciro miki baby's d'in ki kema ki zuba mulkin ki a cikin gidan nan yadda kike so wlh.

Murmushi saratu tai tare da cewa! Wlh kuwa yaya halima kin bani shawara cikin wanan month d'in zanje ai min dashe in mai gidan ya dawo, ni bazan ma gaya mai dashe za'ayi min ba. To dama taya zaki gaya mai ai sai dai yaga kin zubo 'yaya kawai, masu gadar dukiya. Wata uwar dariya saratu da momy suka saki tare da tafawa.

To haka dai saratu ta ziga momy, momy taqi komawa gida, ta kwana a gidan saratu sabida gobe su tafi waja boka da wuri. To ranar dai saratu da momy kwana sukayi suna shirya-shiryan asirin da za suyiwa ammi da iyalan ta basu suka kwanta ba sai ukun dare, dan tinda suka kwanta ko sallah asuba basuyi ba, dama can sallah ba damun su tai ba.

Misalin qarfe 8 na safe suka momy da saratu suka tashi daga bacci. bayan sun tashi saratu ciga kicin ta had'a musu breakfast, sanna suka karya bayan sun karya sukayi wanka, bayan sunyi wanka suka shirya misalin qarfe 9 na safe saratu ta jasu a motar ta sai wajan boka.


Tofah momy da saratu sun iso wajan boka lafiya, kuma sunci sa'a ba mutane a wajan boka sune suka fara zuwa. Suna qasarowa suka shiga wajan boka suka zaune momy tana qoqarin yin magana boka ya tuntsure da wata shed'aniyar dariya bayan ya tsagai ta yace dakata-dakata halima duk abinda kike tafe da shi na sani tun kafin kizo.

Sanan boka ya d'auki qasa a fefe da wata kwarya da wani baqin ruwa ya had'a a waje d'aya sanan ya barbard'a wani koran magani!! ba akan d'akin kishiyar ki bane kikazo? Boka ya watsawa momy tambayar Ehh harda shi. Dariya boka ya saki sanan yace da matar shi zahra koh? Nan ma momy gyad'a kai tace k'warai boka.

Sai mahaifiyar mijin ki da wata mace 'yar kishiyar ki?. Hakane boka, jinina kai boka yayi tare da cewa leqo kwaryar nan ki gani. Momy da saratu da sauri suka leqa dan ganin meye a ciki. Mashkhur suka gani kwance yana bacci hankali kwance akan bed. Momy da sauri tace shine boka maza ka turamai bala'i ka haukata min shi yanzu.

Da sauri boka ya sake sakin wata dariya tare da cewa! Bazan iya aikata mai wani mugun abu ba a halin yanzu. Cikin mamaki momy tace akan mai?. Gyara zama boka yayi tare da cewa! Sabida yau yayi azkhar kuma kin san mutum in dai ya karanta tofa ba wani aljani da zamu iya aikawa ya cuce shi. Cikin tashin hankali momy tace to yanzu boka ya za'ayi.

Girgiza kai boka yayi tare da cewa! Karki damu qara shafa kwaryar yayi sai ga ilham ta futo 6aro-6aro ita da rukee suna ta dariya da dukkan alamu ma hira sukeyi. Da sauri momy tace boka waccan mai jan kayan 'ya ta ce karka ta6a ta mai blue d'in kayan ce 'yar kishiyar tawa. Dariya boka yayi tare da cewa! Muguwa 'yar uwar mu kenan ai nasan 'yar kice, kuma 'yar kishiyar ki nake son nuna miki ba ita ba.

Ajiyar zuciya momy tai tare da cewa saura zahra da hajiya uwar mijin. Barbad'a magani boka ya sakeyi a cikin kwarya tare da zuba idanuwa a cikin kwaryar. Boka ya d'au tsawan mintina yana dubawa amma zahra bata futo ba. Can kuma yace wanan yarinyar tana tare da surikar ki da wanan yarinyar, kuma surukar nan taki tafi qarfin mu tana da dafa'i sosai a jikin ta dan haka hotan ta bazai iya futowa anan ba, cikin mamaki momy tace zahra ba.

Dariya boka ya sakeyi tare da cewa! Nace miki suna tare da surukar ki amma karki damu zanyi maganin ta, maza ki gayamin abinda kike so ayi mata. Gyara zama momy tai tare da cewa! Shi dai namijin mashkhur ina so a haukata min shi yabi duniya, yamabar garin nan ita kuma zahra inaso a kashe min ita, sai ilham 'yar kishiya ta ina so a rabata da mijin da zai aure ta, asa mata baqin jini ba namijin da zai iya son ta ta qare rayuwar ta ba aure.

Sanan mijinta da akai mata bai ko da shi a mayar da bai kwan kan 'ya ta ruma. Da sauri saratu tace haba yaya halima haukata mashkhur ba wani haukata mashkhur ai wanan mao sauqi ne asirin fa zai iya karyewa kamar yadda asirin da muka yimai a bayan na shaye-shaye ya karye, kawai shima a kashe mana shi. Wata uwar dariya boka yasa tare da cewa! Qanwarki ta fiki wayo tabbas asirin zai iya karyewa kamar yadda na shaye- shaye da rashin san karatu ya karye.

Cikin mamaki momy tace yauwa boka dama ina so ka dubamin kamar asirin mallaka da shaye-shyen da nayiwa mashkhur ya karye koh? Wai boka me yasa asirin da mukayi mai ya karye. Jinjina kai boka yayi tare da cewa! Na farko dai asirin shaye-shye ya karye, na mallaka kuwa yana nan bai karye ba sabida yaran yana da taurin kai ne shi yasa kike ganin kamar na mallakar ma ya karye amma har yanzu zuciyar mashkhur tana tattare da jin maganar ki kin mallake shi sosai

Sanan boka ya d'ora da! Abinda yasa asirin nan ya karyr matar shi ce ta ringa tofa mai addu'o'in karya sihiri a ruwa da shayi har sau uku hakan ne yasa asirin ya karye, duk ya amayar da asirin shaye-shaye da kika bashi yaci. Jinjin kai momy tai tare da cewa! Ai sai ita shegiyar 'yar, 'yar tsuntuwa kawai boka mutuwar farar d'aya nake so kayiwa zahra. Dariya boka yayi tare da cewa an gama aiki in dai da kud'i.

Murmushi saratu tai tare da cewa boka da kud'i mana nima ina da damuwa. Dariya boka yayi tare da cewa! Naga duk abinda yake damunki, amma ki bari sai na gama da yayar ki tinda ke a garin nan kike ba damuwa ko da yaushe zaki iya zuwa. Murmushi saratu tai tare da cewa! Nima nafiso a gama da yayar tawa, dan na matso a kwar da matsalar gidan yaya halima.

Dariya boka yayi

Please Login or Register in order to submit comment