Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kama ma a qabari d'aya za'a binne mu ko kuma kabari na yana kusa da naka. Murmushi mashkhur yayi tare da cewa hmmm amma kike cewa in zaki haiwu zaki iya mutuwa. Hmmm kawai na fad'a ne amma in sha ALLAH zan haiwu lafiya qalau na haifa ma baby mai kama da kai.

Murmushi mashkhur yayi tare da cewa hmmm ki dena cika baki karfa kizo ki haifamin mai kama dake. Uhmm to baka son mai kama dani ne?. Aa ai nama fison mai kama dake in ringa kallonta inajin dad'i. Haka mashkhur da zahra sukai ta hirar su gwanin ban sha'awa har bacci yayi awan gaba da zahra.

Mashkhur kuwa zahra tana bacci ya tashi yayi wanka sanan ya shirya ya fice daga gidan. Zahra ba ita ta tashi daga bacci ba sai wajan sallah magriba tana tashi ta shiga toilet tai wanka, sanan ta futo tai sallah. Bayan ta idar da sallah tinanin mai zataci ta farayi dan tasan yanzu duk abinda taci ba zama zai yi a cikin ta ba.

Haka dai ta sauka qasa ta d'ebo fresh milk a class cup sanan ta dawo sama tana ta tinanin ina mashkhur ya tafi haka. Bayan zahra ta dawo zama tai a gefan bed sanan ta d'auko wayar ta. Hmmm zahra tinani ta fara wa zata fara gayawa tana da ciki?. Contact number zahra ta shiga ta dailing d'in number ilham.

Bugu uku ilham ta d'auka, tana d'auka murya a sanyaye tace hmm sai yanzu ki kai niyar kira na kenan tun yaushe nake kiran ki ke ko d'an jajan first night d'in nan ma bazaki bugo ki min ba ko. Murmushi dole zahra tai sanan tace hmmm ke dai ilham bari kawai nima na shiga cikin tawa matsalar taya zaki jini.

Cikin mamaki ilham tace matsala kuma zahra matsalar mai fa?. Hmmm ke dai ilham bari kin san tinda aka gama d'aurin aure aka kai ku nake ta faman bacci sam bana moruwa cutar bacci ta kamani, daga qarshe kuma duk abinda naci na amayar da shi, wai da mukaje asibiti ashe ciki ne dani.

Cikin matsanancin mamaki ilham tace ke zahra ban san wasa fa ciki kuma?. Wlh ilham da gaske nake ciki har na tsawan wata uku inaga ma a first night na tsinci abuna. Wani iwun farin ciki ilham ta saki wanda sai da zahra tai saurin janye wayar daga kunan ta. Kai ilham meye haka kuma? Ke kuwa zahra ba dole nai farin ciki ba ciki kika cemin fa.

Haka dai zahra da ilham sukai ta tattaunawa har mashkhur sai da ya dawo sanan zahra ta samu tai sallama da ilham. Haka mashkhur yayi ta lalla6a zahra har ta samu ta d'anci abinci. Bayan gama ci mashkhur ya bata gift d'in da ya siyo mata. Jikin na rawa zahra ta fara bud'e ledar hannu na rawa dan taga gift d'in mai ta samu.

Hmmm zahra tana gama bud'e ledar kafin ta bud'e kwalin ta saki iwun farin ciki tare da hugg d'in mashkhur saka makwan ganin kwalin wayar I phone 15 pro max wanda ba a dad'e da lunching d'in taba. Haba teadyna kiyi a hankula kar kimin 6ari mana duk dan sabida tsabar farin ciki babyn da zaki haifa min ne fa yasa na siyo miki wanan, sauran gift d'in ma ki bari sai kin haiwuma.

Hmmm lallai zahra tayi goshi ga I phone 15 pro max ga ciki awnnnnnnn.

Mashkhur da zahra sun d'an d'agawa junan su qafa wajan yawan sex sabida kar suyi 6arin baby. A sati bai fi suyi sau biyi ba har ciki zahra yayi kwari ta fara zuwa awo. Haka zahra da mashkhur su kai ta kula da cikin sosai yarda ya kamata, kuma suna qara shan soyayyah su abun gwanin sha'awa kullum qara shaquwa suke.

6angaran su ammi da mama harda da sauran mutan gidan da suka san zahra tana da ciki zo kaga farin ciki, da yake dai bata gayawa kowa ba har sai da ya fara futowa suka gani. Sai shirya-shirya suke kamar ba qaramin ciki ba, yarda kasan ciki ya stufa zahra ta kusan haiwuwa.

6angaran nana da abdul kuwa soyayyah suke mai kyau da stafta ba laifi yanzu abdul yana qaunar nana sosai,. Dan har manya sun shiga zancan ansa musu rana aure.
6angaran ilham ma tana zaune ita da mijin ta ahmad lafiya qalau suna shan soyayyah su yarda ya kamata abin dai sai wanda ya gani. Itama 6angaran ruma suna zauna da mijin ta lafiya......

Momy and saratu.......

Tofa momy da saratu sunyi ladama sosai da sosai, sun zama abin tausayi, duk kud'ad'an da suke da shi ya qare sabida hidima da kan su, kai har sai da ta kai ta kawo abinda zasuci yana neman yafi qarfin su. Hakan ne yasa sukai sauri suka futo da mazace duk da basu da wani arziki kamar tsofafi mazajan su na da.

Hmmm ashe dai anan wahalar take, momy dai wata uku tai a gidan mijin ta ya fara jibgar ta, laifi kad'an tai duka ne da zagi zai biyo baya, kullum mijin ta a cikin dukan ta yake. Saratu kuwa ta gamu da kishiyoyi shu'umai wanda suka fita makirci da yake a gida d'aya aka had'e su. Su ba boka bare malam makircin baki kawai suke had'a mata a wajan miji.

Lokaci guda itama mijin ta ya tsanata, ga uban girkin da take ci in girkin ta ya zagayo. Duk da bata da 'yaya sai ta dafawa 'yayan kishiyoyi da kishiyoyin girkin in ranar girkin tane. Ga yaran da uban yawa kamar kiyashi. Lokaci guda itama saratu ta rame ta fige ta lalace, kai abun tausayi dai da saratu da momy sam ba mai bawa wani haquri sabida duk a cikin matsala suke........................

Hmmm Allah yasa mu dace shi yasa ba kyau zalin ci.

Mu had'e a next page.


[23/04, 7:39 am] Oum Farhan❤️🩷: ADALILINTA 💜❤💜

BY AMINA BAYERO 💜❤💜

TYPING...........

*Page 137*

Lokaci guda itama saratu ta rame ta fige ta lalace, kai abun tausayi dai da saratu da momy sam ba mai bawa wani haquri sabida duk a cikin matsala suke...................

After 6 month.

Gaskiya ni daga nan ka wuce dani gida dama kace bazaka barni na tafi gida ba sai edd na ya cika to tinda yau ya cika kawai ka kai ni gida, zahra ce take fad'in hakan wanda take zaune agaban mota da qatan cikin ta, shi kuma mashkhur yana daga gefe yana driving.

Haba mom on born ki bari mana muje gida ki shirya sosai sai na kai ki yaufa edd naki ya cika daga asibiti sai gida kuma. Ee naji daga asibitin sai gida, tun yaushe su ammi suke cewa ka dawo dani gida amma in banda naci irin naka kaqi wai sai edd na ya cika, to tinda yanzu ya cika ai sai ka kai ni gida na haiwu. nifa bazan sake kwana a gidan ka ba yau a gida zan kwana.

Haba teadyna coll down mana, in sha ALLAH yau zan kai ki gida amma ai sai ki bari muje muyi sallama ko, mashkhur ya qarasa maganar yana satar kallon zahra. Wace kalar sallama ce bamuyi ba ni zahra pls yaya mashkhur ka kai ni gida haka ko so kake muna cikin sallama na haiwu ne?. Haba my wife kema kinsan zanyi missing d'in ki na qarshe ne fa daga shi zan mayar da ke gida wlh.

Ajiyar zuciya zahra tai sanan tace hmm ka d'aukar min alqawari ko?. Murmushi mashkhur yayi tare da shafa hanun zahra yace uhmm na d'aukar miki alqawari mom on born ALLAH ya sauke ki lafiya teadyna. Murmushi zahra tai tare da cewa thank you dadyn on born, wani shu'umun murmushi mashkhur yayi sanan yace hmm na qagu ajiyar nan tawa ta futo fili fa ni..........

Mashkhur yana qarasawa gida yayi horn, ba jimawa mai gadi ya bud'e get, yana bud'e mashkhur ya shiga yayi parking d'in motar sanan ya futo. Bayan ya futo ya nufi 6angaran zahra ya bud'e mata qofa sanan ya miqa mata hannu domin ya temaka mata ta miqe. Zahra riqe lallausan hanun mashkhur tai sanan ta fara qoqarin miqewa tana dan nunfasawa, dan cikin yayi mata nauyi sosai.

Abinka da cikin fari, ba'a saba ba. Bayan mashkhur ya taimakawa zahra ta futo, rufe murfin motar yayi sanan ya riqe hanun ta suka fara tafiya a hankula. Bayan sun shiga ciki sunzo dai-dai matatakala tsayawa zahra tai tare da cewa hmm nifa na gaji ka bari na wuta sai muhau saman. Kallan ta mashkhur yayi cikin tausayawa yace aa ki bari kawai na d'auke ki.

Girgiza kai zahra tai sanan tace! Aa ni nafiso na taka da kai na, sabida na qara motsa jikina. Tom shikenan my teady ki daure mu qarasa hawa d'in kinga sai ki wuta sosai koh?. Gyad'a kai zahra tai tare da d'an matsa hanun mashkhur da ya ruqe ta tace ok ba damuwa muje. Haka zahra da mashkhur suka cigaba da tafiya a hankula har suka gama hawa.

Basu tsaya ko ina ba sai bedroom, suna shiga zahra tace kai yah ALLAH ta qarasa maganar tana dafa goshi. Bakomai yasa zahra hakan ba face ganin uban kayan baby's d'in da ya cika bed d'in, kai kusan duk inda ka ratsa a gidan nan sai kaga kayan baby, bama iya gidan zahra ta har gidan ammi da mama sun fara tanadin kayan baby.

Itama ilham ta fara tanadin kayan baby's da yake itama tana nan da cikin ta na wata shida kuma ga babyn zahra da mashkhur ma haka suke ta siyo kayan baby. Itama ruma tana can tana fama da cikin ta na 6 month's kamar dai ilham.
Amma dai zahra da mashkhur sunfi kowa haukan siyan kayan baby's.

Oh sannu bari na kwashe miki kayan baby sai ki wuta ko. Haka mashkhur ya nufi kan bed ya hau kwashe kayan babyn nasu. Bayan ya gama kwashewa hanun zahra yaja sanan ya kai ta kan bed d'in ta zauna. Bayan ta zauna ficewa yayi bayan few minutes ya dawo hannu riqe da plate d'in ganye da kayan marmari kamar yarda ta saba ci kullum sabida babyn ta.

A hankula mashkhur ya qaraso ya ajiye plate d'in a gefe sanan ya fara bawa zahra abaki, a hankula zahra ta fara cin abinci haka mashkhur ya bawa zahra har sai da ta gama cinyewa tasss da yake yanzu tana dan cin abu sosai da cikin ta ya stufa. Bayan zahra ta gama ci mashkhur fitar da plate d'in yayi sanan ya dawo bedroom d'in.

Teadyna sannu fa taso muje nai miki wanka kinga dai daga hospital muka dawo. Da kyar zahra ta iya miqewa tare da cewa tom shikenan muje, haka suka shige toilet abinsu. Dama dai tinda cikin zahra ya shiga wata 8 mashkhur yake mata wanka sabida bata iyawa. Suna shiga mashkhur ya cire mata kaya yana cire mata mai ma kwan yayi mata wanka kamar yarda ya fad'a, kawai sai ya fara latse mata breast d'in ta.

Wanda suka sake futowa masha ALLAH, haba hero wai baka gajiya da latse su ne, dan ALLAH ka rabu dani haka. Hmm pls teady ki bari na sake shafe twins d'in na kafin magajiya ya qaraso. Hmmm ai shikenan zahra ta qarasa maganar tana yamutsa fuska. Haka mashkhur ya gama latse zahra sanan yayi mata wanka, shima yayi suka futo d'aure da towel.

Duk da kuwa zahra towel d'in ma yayi mata kad'an sabida cikin jikin ta. Suna futowa mashkhur ya kwantar da zahra akan bed sanan shima ya kwanta. Nan da nan suka fara kisses d'in su cikin kwanciyar hankali. Bayan sun gama romances, sex suka farayi cike da qaunar junan su...............

Zahra ranta fari qal da taka sun shiga mota ita da mashkhur ya kama hanyar gida. Hmmm ji wani yarda kike ta farin ciki sai kace wanda kake ALLAH-ALLAH mu rabu koh? Ke ku irin kukan rabuwa da masoyin nan bakyayi kenan?. Hmmm ba haka bane hero ai ba guduwa zanyi ba zan dawo kuma dai gidan ammi ai ba bakwan ka bane duk sanda ka buqaci ganina ai sai kazo.

Hmmm ni gaskiya ban gamsu ba, ce miki akai irin ganin nan nake nufi ne hmmm teadyna bazaki gane yarda nake cikin jimaman rashin ki da zanyi ba kece rayuwa ta kece farin cikina kece nutsuwata kece komai nawa zahra, naso ki fiye da komai a rayuwa ta hmmm duk yarda zan miki bayanin yarda nake son ki bazaki gane ba zahra ta.

Hmmm doguwar ajiyar zuciya zahra ta saki cikin tausayawa mijin ta tace nima ina qaunar ka yaya mashkhur fiye da yarda kake tinani kasan, nima bada son rai na zan barka ba amma ai ina haiwuwa zan dawo wajan ka kaji,. Murmushi mashkhur ya saki tare da cewa aa kice dai zaku dawo waje na keda babyn mu. Murmushi zahra ta saki tare da cewa oh ni nama manta da babyn ai.

Haka zahra da mashkhur su kai ta hirar soyayyah su har suka qaraso gida. Ko da suka qaraso gida sai da sukai wajan rabin awa a mota basu futo ba sunan nan suka kiss da hugg d'in juna, da abubuwan dai da suka saba har sai da magriba ta fara kawo kai sanan suka fuce daga ciki. Haka mashkhur ya riqe hanun zahra suka cigaba da tafiya abin gwanin ban sha'awa.

Suna qarasawa daf da zasu shiga 6angaran ammi zahra tace uhmmm saki ni haka nan zan iya tafiya. Kallon ta mashkhur yayi tare da cewa aa naqi d'in kunyar mai zakiji ni ba mijin ki bane wai. Kallon mashkhur zahra tai tare da cewa da ammi fa a ciki. Uhmm ai nasan tana ciki, kuma tasan muna abinda yafi hakan ma.

Banza zahra taiwa mashkhur bata sake cewa komai ba haka suka rankaya suka shiga babban falon ammi baki d'auke da sallama. Suna shiga zahra ta janye hanun ta da qarfe tare da gallawa mashkhur harar su ta ma'aurata. Hjy kaka da ammi ne zaune a akan kujera suna jin sallamar su zahra da mashkhur sukq mai da kallon su wajan qofa.

Da sauri hjy kaka ta taso cikin farin ciki ta nefo zahra tare da cewa oyoyo mai sunana, ta qarasa maganar tana rugume zahra. A hankula zahra itama ta rungume hjy kaka tare da cewa oyoyo hjy kaka ta. Hjy kaka ki mata a hankula fa kinga dai halin da take ciki, mashkhur ya fad'i hakan a hankula yarda dai ammi bazataji ba.

Sakin zahra hjy kaka tai tare da cewa to sannu mara kunya, kabi ka riqe mana 'ya ka hanamu ita, to bari kaji yau zato kenan ko kana so ko baka so sai ta haiwu tai kwana arba'in cif-cif zata dawo gidan ka. Kai hjy kaka yanzu meye na d'aga muryar kuma ko so kike ammi taji mashkhur ya fad'i hakan a hankula, hmmm ai kana jin kunya gyatumar taka amma ni bakajin kunya ta ko da kake cewa nai mata a hankula ta naqi.

Hjy kaka ta qarasa maganar tana jan hanun zahra tana cewa tawo mu tafi ki zauna ki wuta yau kin dawo gida kenan. Hmm ai dama hjy kaka na dawo gida sai na haiwu kuma zan koma zahra ta fad'a tana sakin murmushi. Yauwa yanzu naji magana aa kullum shi yana maqale dake bazai barki ki sarara ba. Wani kallo zahra ta watsawa hjy kaka tare da cewa kai hjy kaka meye haka kuma.

Ee sai na fad'a d'in ai ga uwar nan taku tanaji tinda bajin magana kuke ba, baku san kara ba daga ke har shi. Hanun ta zahra ta kwace daga rukwan da hjy kaka tai mata, sanan ta qarasa wajan ammi cike da kunya ra d'anyi qoqarin tsugunawa domin gai da ammi. Da sauri ammi ta miqe tare da riqe zahra tana cewa aa tashi dai kam na yafe tsugunawar nan ai kinyi nauyi sosai kawai ki zauna, sai mu gaisa a zauna.

Zauna a hankula ammi ta qarasa maganar tana zauna da zahra akan kujera, bayan zahra ta zauna itama ammi zama tai a gefan ta. Mashkhur qarasowa yayi bayan ya tsuguna har qasa ya gai da ammi, sanan ya tashi shima ya zauna a hakan kujerar zuciyar shi cike fall da so da kewar zahra.

Miqewa mashkhur yayi ya fuce sakamakwan jin kiran sallah magriba da akeyi. Yana fita ammi ta kalli zahra tare da cewa sannu fa wai har yanzu lokacin haiwuwar taki baiyi bane?. Aa ammi yau edd nawa ya cika shi yasama na dawo gida zahra ta qarasa maganar tana cire hijab d'in ta. Oh masha ALLAH, kicigaba da yawai ta addu'a de, muma muna nan muna tayi allah ya sauke ki lafiya.

Ameen maryam Allah yasa tai haiwuwar sauqi komai yazo mata cikin sauqi hjy kaka ta fad'a cikin tausayawa zahra. Zahra jiki a sanyaye har suna had'a baki ita da ammi wajan cewa ameen. Miqewa hjy kaka tai tare da cewa bari naje nai sallah daga nan zan tawo miki da tofin haiwuwar dama na dad'e da kar6o miki da baki zo ba har gidan zan sa akawoni na baki.

Bayan hjy kaka ta fita zahra miqewa tai tare da cewa nima bari baje nai sallah. Uhmmm nima saman zan hau bari muhau tare. A hankula zahra da ammi suka jera suna tafiya,. Wai ammi ina ameer ne? Zahra ta tambaya tana gyara d'ankwalin kanta, Sun fita da abdul tun dazo har yanzu basu dawo ba..........

Mu had'e a next page.

[23/04, 7:39 am] Oum Farhan❤️🩷: ADALILINTA 💜❤💜

BY AMINA BAYERO 💜❤💜

  Typing................

*page 138*

A hankula zahra da ammi suka jera suna tafiya,. Wai ammi ina ameer ne?  Zahra ta tambaya tana gyara d'ankwalin kanta, sun fita da abdul har yanzu basu dawo ba.

To daran ranar nan dai zahra da kyar ta iya bacci sai wani juyi take kamar mai naqudar, tun ammi tana tinanin naquda take har ta dai na tinanin hakan ta tafi bacci,.
Shima 6angaran mashkhur bai iya baccin ba juyi yayi tayi yana tinanin matar sa zahra, sai yaji kamar in ya murgina zai ganta a gefan sa kamar yarda ya saba kullum ya rungume abarsa.

Misalin qarfe d'ayan dare mashkhur ya d'auko wayarsa ya turawa zahra gajeran message d'in karta kwana. Firgigit zahra da take kwance tana tunanin mijin nata ta miqe zaune, sai da ta d'an duba fuska ammi sosai taga ta tafi bacci da gaske, sanan ta motsa a hankula ta zura hannu kan qaramar durowar gefan gadon ta zaro wayar ta a hankula.

Kamar yarda tai tinani sakwan mashkhur ne, tana ganin hakan ta saki ajiyar zuciya mai nauyi sanan ta fara kamaran ta message d'in da ya turo mata kamar haka! Hmm wife nifa na kasa bacci tun dazu tunanin ki nake?. Murmushi zahra ta saki bayan ta gama karanta message d'in, sanan tai mai reply da me too sahibina nima na kasa bacci kawai tunanin ka nake.

Bayan zahra ta tura mai message d'in kwanciya tai sanan ta shige cikin blanket d'in gaba d'ayanta ta rage hasken wayar sosai yarda dai ammi bazata gane ba. To haka zahra da mashkhur sukai ta shan soyayyar su suna shedawa junan su yarda sukai mussing d'in junan su, kai in taqai ce muku zance basu suka kwanta ba sai da sukai sallah asubayi sanan bacci yayi awan gaba da kowanana su.

Zuciyoyin su cike da kewa da son ganin juna.
To haka zahra tai ta sharar bacci, misalin qarfe goma safiya ammi ta had'a mata breakfast ta kawo mata har sama, sanan ta tashe ta. A bisa dole zahra ta tashi, dan da ammi zata bi za6in zahra sai ta gama baccin ta zatai breakfast, to amma tasan ammi bazata kyaleta ba dole ta haqura ta tashi taci.

Zahra tana gama breakfast d'in ko wanka batai ba ta koma baccin ta abinta,. To haka zahra tai ta sharar bacci ba ita ta tashi ba sai qarfe 12:00am ta farka shima dai zuwan ilham ne yasa ta farkawa. Cikin farin ciki zahra tace ilham sannu da zuwa kece haka kamar an watso ki. Murmushi ilham tai tare da cewa ee shine kika dawo gida ko ki sanar dani kwana biyu ma ko kirana bakyayi a waya.

Kai ilham yaushe ne bamuyi wayar ba jiya ne kawai fa sai yau, yau d'in ma kinga ta qare bamuyi wayar bane, kuma ai na riga dana gaya miki na dawo gida tun jiya kawai dan baki hau online d'in bane. Ee jiya ban hau online ba, yaufa da zanzo na ganki sai nace bari na fara zuwa na gai dasu ammi sai na tawo shine ina zuwa akace min kin dawo shine kawai nace ahmad yayi tafiyarsa zuwa da yamma ya dawo ya d'auke ni.

Murmushi zahra tai sanan tace to yau sunan ahmad d'in ake kira gazau haka ko d'an karar masoyan nan ma babu?. Murmushi ilham tai sanan tace aa wai na fad'a ne kawa amma kinsan hmm har gobe ina son kayana kamar yarda yake sona, nifa kullum san shi qaruwa yake a zuciyata kamar yarda son yaya mashkhur kema yake qaruwa a zuciyar ki.

Murmushi zahra tai sanan tace kai ilham ina karma ki ganganci had'a kan ki da soyayya ta da yaya mashkhur sabida ko qafarmu baku kamo ba,  nifa yanzu na riga da na gane in ba yaya mashkhur a rayuwata, to bazan ta6a samu nutsuwa ba, ni bazan ma iya rayuwar ba gaba d'aya, zahra ta qarasa maganar tana gyara zaman ta da kyar. Wata shu'umar dariya ilham ta saki sanan tace tabbb!

Yau de abu kamar a mafarki wai zahra ce take cewa in ba yaya mashkhur bazata iya rayuwa ba, mai makwan da da kike cewa kinfi kowa tsanar sa, kuma in baya raye sai kinfi jin dad'in rayuwar ki, wai ni kam zahra mai yaya mashkhur yake miki haka ne duk kika gigice akan son sa lokaci guda kika manta da d'in bin zunubun daya aikata miki a rayuwa kika tsane shi a da?.

Lashe lips d'in ta zahra tai tare da cewa!  Hmmm ilham kenan bazaki ta6a ganewa ba duk bayanin da zan miki kawai mafita guda ki amince yaya mashkhur rayuwata ne. Jinjina kai ilham tai tare da cewa na amince mana, amma wai in tambaye ki mana dama haka irin su yaya mashkhur suke sace zuciyar mace lokaci guda, hmm da na d'auka ko yatsa kika sawa yaya mashkhur a baki haka zaki zare abinki ba tare daya gatsa ba.

Zubawa ilham ido zahra tai sanan tace kamarya?  Ban gane mai kike nufi ba. Ina nufin da nayi tunanin yaya mashkhur bai iya soyaya ba ko hmmmmmm bazai iya ba ashe lamarin ba haka yake ba. Murmushi zahra ta saki sanan ta shafa qatan cikin ta tace oho dai ga sheda nan ma ya barmuku, har ajiya yayi dan ku tabbatar ya iya harka fa.

Wata uwar dariya ilham da zahra suka saki a tare sanan suka tafa abun su. Ammi ce ta shigo baki d'auke da sallama sanan tace hmmm ilham da zahra ai ku in kuka had'u waje guda bakwa moruwa in banda tashin shewa ba abinda akeji, ammi ta qarasa maganar tana miqowa zahra ruwan tofi a cup, gashi ki daure ki shanye. Kar6a zahra tai tare da cewa to ammi,. Ammi tana fita ilham tace ke zahra wai dama haka yaya mashkhur ya mayar dake mara kunya.

Yanzu maganar nan kike fad'a ko kunya bakyaji ai da dane bazaki iya cewa haka ba, in ana zancen nan ma kallon 'yan iska kikewa mutane. Murmushi zahra tai tare da cewa hmm bazaki gane ba ilham, nifa zaman takura nake yanzu a gidan nan, sabida mun riga da mun sabawa kanmu da kanmu, kai jiya fa da kyar ni nai bacci harna tsargu na haiwu na koma gidan mijina ni.

Lallai zahra ke yanzu har kin manta da tsoran haiwuwar kawai a matsa kike. To ilham ya zanyi ko naji tsoran haiwuwa ko banji ba dole na haiwu  in

Please Login or Register in order to submit comment