Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abdul yay ta rarrashi zahra har sai da tayi shiru. Ilham ce ta shigo bedroom d’in tare da cewa yaya abdul wai kaje inji ammi, da sauri abdul ya miqe tare da cewa babyn abdul sai da safe, duk da zahra bata cikin mood mai dad’i sai da ta murmusa. Abdul yana fita ilham itama ta juya zata fuce, murya a dashe zahra tace ilham ina zaki Kuma?.

Juyowa ilham tayi tare da cewa ai zahra bana so na takura miki ne shiya. Tasowa zahra tayi tare da cewa taya ‘yar uwa ta zata takura min, ido ciki da kwalla ilham tace zahra kwana biyu duk kinbi kin canzamin kin zamar min abar tsoro, rungumota zahra tayi tare da cewa haba ilham ki dena cewa haka kema kinsa ba a cikin hayyacina nayi miki hakan ba kawai damuwace tasa hakan. Haka dai zahra da ilham sukai ta rarrashi junan su abin gwanin ban sha’awa. Suna cikin hakan ameer ya shigo d’akin.

Da sauri zahra ta saki ilham tare da bud’e wa ameer hanuwanta alamun hug. Da sauri ameer ya noqe kafad’a tare da cewa nifa Aunty zahra na dai na kulaki shine jiya kika rufe d’aki kika qi kwana dani, kuma kika sani kuka. Da sauri zahra ta qaraso gaban ameer tare da tsuguwa a gabansa tana cewa tom shikenan ameer d’in na dai na bazan qaraba zo muje muci kayan dad’i da dady ya siyo mana, daga haka suka wuce kan bed zahra ta fara bawa ameer cakes d’in abaki bayan ta gama bashi, suka fara wasan akan gado kamar yanda suka saba, daga haka dai bacci ya kwashe ameer,suma zahra ita da ilham kwanciya sukayi..........

To tundaga wannan lokacin dady ya qara son zahra kullum nuna mata kulawa yake bama iya dadyn ba duk mutan gidan farantawa zahra suka sam basa bari ta zubar da hawaye, momy ce da rukee kawai suke nunawa zahra tsana shima dai sai a bayan idon dady.
Tom itama zahra ta fara sakin jiki amma ba sosai ba sabida yanzu kwata-kwata zahra ta canza ta qara zama shiru-shiru sometimes ma in aka zauna ana hira a gidan sam bata sa baki.

Watarana ma in zahra ta tuna ita ba ‘yar gidan bace haka zata zauna a d’aki tai jigum ita kad’ai, haka dai su dady zasu ta jan zahra a ciki suna yimata hira da kuma wasa da dariya. Tom yanzu zahra ta fara sakin jikinta a gidan amma har yanzu bata magana sosai dama can da ita bada gwanar magana bace shiru-shiru ce ga kuma haquri, haka dai rayuwa tai ta juyawa yanzu zahra zaman gidan yana mata dad’i sabida ba mashkhur kuma tana karatun ta hankalinta kwance...........

To masu karatun littafin ADALILINTA wai bakuyi tinanin ina oga mashkhur ba kuwa?. Tom ku biyoni domin kuji oga mashkhur a wana hali yake kuma da ya qarasa rasha mai yake aikatawa acan yana karatu ko kuwa?..............

Ku biyoni a next page.

Ina mai baku haquri sakamakwan kwana biyu bana yi muku typing..... wlh banajin dad’i ne shiyasa, ina yi muku fatan alkhairi ALLAH yabar qauna...

Now book on 2023.
[11/06, 22:24] Maman Xuhra: “ADALILINTA”

ADALILINTA💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

Typing.............

*page 48*
Haka dai rayuwa tai ta juyawa yanzu zahra zaman gidan yayi mata dad’i sabida ba mashkhur kuma tana karatun ta hankalin kwance.

Mashkhur.........

Tofa su mashkhur sun sauka garin rasha lfy qalau, lokacin da suka sauka ko minti goma ba suyi da sauka ba, sai ga wani drive kallo d’aya zakayiwa drive kasan cikakyan d’an rasha ne shine zai kai shi gidan da zai zauna. Su biyu drive motar ta d’auka shida da wani, bai fi sa’an mashkhur d’in ba. kana ganin mutumin zaka she da d’an Nigeria ne duk da kuwa mutumin bai yi hausba amma mashkhur yana kallansa yasan shima d’an Nigeria. Har suka qaraso in da zasu ba wanda yayiwa wani magana tsakanin mashkhur da abokin tafiyar sa.

A bakin wani katafaran gida drive su mashkhur yayi parking. Yana yin parking ya futo ya bud’e wa su mashkhur qofa domin su samu su futo, bayan sun futo da kansa yasa key ya bud’e gidan. Yasalam tsayawa ma na yiwa masu karatun littafin ADALILINTA tsaruwar gidan wlh 6ata bakine, sabida gidan nan ya cika gida abinda da gidan turawa☹️. Kallan su drive yayi cikin harshan turanci yace musu su shigo gidan, ba musu mashkhur da abokin tafiyar sa suka kutsa kai domin shiga gidan.

Key biyo driven ya zaro, mashkhur ya fara miqawa tare da yi mai bayani cikin harshan turanci, cewa yayi kai sama zaka hau anan zaka ringa zama, yana gama gayawa mashkhur haka ya zura hannu a aljuhu ya ciro A T M ya bawa mashkhur, hannu mashkur yasa ya kar6i a t m d’in sanna yayi wucewar sa dan yama manta da kayan sa a bayan mota. Drive juyawa yayi ya miqawa abokin tafiyar mashkhur mukullunsa da a t m d’in sa sanna shima yayi mai bayanin a qasa zai zauna.

Shi dai abokin tafiyar mashkhur d’in sai da ya tsaya ya kwashi kayansa sanan ya shige part d’in sa.
Mashkhur kuwa yana hawa sama yasa key ya bud’e qofar ya shige ciki , a hanzarce ya shige domin mashkhur ya gaji sosai. Hmmm nikuwa amina nayero sai da idona yaja ruwa sabida tsabar d’aular da na gani a cikin gidan nan iyama falo ina ga an shiga ciki, mashkhur yana qoqarin cire rigar sanyin sa yaji an fara knock d’in qofar, wani siririn tsaki ya saki tare da nufar qofar ya bud’e.
Drive nan ya gani ya kwasomai ja kunkunam sa da kuma a kwati nan sa .

Mashkhur kuwa juyawa yayi ya koma, wato yana nufin sai dai drive ya shigo mai da kayan. Haka dai drive ya kasowa mashkhur kayansa ya kawo mai d’aki. Yana fita mashkhur ya kulle qofar da key sannan ya fara zagaya gidan. Bedroom uku ne a gidan kuma ko wanne da gado a ciki, ga kuma toilet, sai baban falo sai kuma kicin guda d’aya. Duk bedroom d’im gidam harma da kicin akwai qofar fita, ventilation shima dai ban ventilation d’in a sama yake kana shiga ventilation zakaga duk tsakar gidan gidan.

Falo kuma wani dogwan glass ne kamar get haka ake zuge shi, shima kana shiga cikin glass d’in ventilation ne, wajan glass d’in duk flowers abin gwanin ban sha’awa. Tsayawa gaya muku kayan alatun gidan nan har sai in gama page d’in nan ban gama gaya muku ba.
To mashkhur wanka yayi sanan yayi oder abinci, da yake da akwaii wani qaramin littafin a kan dinining, a cikin littafin da akwai abinci kala-kala da kuma Number da zaka biga kayi order...............

To yau kimanin kwana uku kenan da zuwan mashkhur rasha, kuma ba inda yake zuwa komai in ya buqata oder yake. Yanzu dai saura 4 days ya fara zuwa makarantar.
Yana zaune akan sofa a falo yana danna laptop d’in sa yaji, ana knocks d’in qofar. Abin ya bawa mashkhur mamaki sosai sabida shi sam yasan bai yi oder kumai ba barema yace, zuwa akai a kawo mai abinda yayi oder. Bugu da qari ma mashkhur ba wanda ya sani a garin bare yazo gurin sa cikin mamaki mashkhur ya tashi ya nufi hanyar qofar.

Yana bud’e qofar, kallo d’aya ya yiwa wanda yake tsaye a bakin qofar ya gane shi, ba kowa bane face abokin tafiyar nan tashi. miqawa mashkhur hannu mutumim yayi tare da furta assalama alikum, shima mashkhur d’in miqa hannun sa yayi tare da cewa wa’alaikasslam. Fuska a sake mutumin yace can I come in, wato yana nufin zan iya shigowa ciki?. Shiru mashkhur yayi na wasu daqiqu kafin yace yes you can. Mashkhur yana gama fad’in hakan yayi shigewarsa ciki shima bakwan bin bayan mashkhur d’in yayi.

Kallansa mashkhur yayi tare da cewa you can sit, wato mashkhur yan nufin zaka iya zama, ya qarasa maganar tare da nuna masa kujera. Zama yayi tare da cewa thak You. Shima mashkhur d’in zama yayi sanan ya cigaba da danna laptop d’in sa. Sunfi wajan 20 minit a haka ba wanda yace komai. Can mutumin yace wanan wana irin mutum ne haka? Cikin harshan hausa ya fad’i hakan amma sam bai san abinda ya fad’a ya futoba, kuma bai mayi tinanin mashkhur bahaushe bane, kawai dai yasan d’an Nigeria ne.

Mashkhur kuwa yaji abinda yace sarai, amma sam bai nuna mai haka ba, dan koh kallansa bai yi ba.
Excuse me my friend, cewar baqon mashkhur d’in. D’agowa mashkhur yayi tare da furta lafiya? Shima mashkhur d’in sam bai san sanda ya cewa mutumin nan lafiya ba sabida bai so ya nuna mai yana jin hausa ba. Cikin mamaki mutumin ya kalli mashkhur tare da cewa wow dama kana jin hausa?, shiru mashkhur yayi can kuma yace kawai inaji. Jinjina kai mutumin yayi tare da cewa nima cikakyan bahaushe ne.

Ta6e baki mashkhur yiya tare da cewa yayi kyau. Shiru d’akin yayi na wasu mintina kafin mutumin yace dama abinda ya kawo ni shine, naga muna zaune a gida d’aya ne kuma ba musan juna ba shine nace ya kamata, nazo musan juna tinda kai kaqi zuwa. Jinjina kai mashkhur yayi tare da cewa ka kyauta fa. Mutumin kuwa cigaba da magana yayi tare da cewa ni dai sunana AHMAD daga Nigeria nake, kuma ina zaune a garin kano fatan kasan karin.

A tai qai ce mashkhur yace ehh nasan shi. Jiniina kai ahmad yayi tare da cewa to kai a wane state kake a Nigeria d’in?. Cikin qosawa da magana mashkhur yace kano. Murmushi ahamd ya saki tare da cewa wow ashe state d’in mu d’aya ma? D’aga kai mashkhur yayi alamun ehh. Ahmad ya lura da mashkhur sam ba mai san magana bane ko kuma baya son mutane sosai shiyasa ya taqai ta zancan da cewa okay bari na barka haka karna cika ka da surutu.

Shiru mashkhur yayi ba tare da ya bawa ahmad amsa ba. Har ahmad ya zai tafi ya juyo tare da cewa kash sorry fa na manta ban tambayi sunanka ba, pls ya sunan ka ne?. Mashkhur kuwa mayar da kallonsa yayi kan laptop d’insa tare da cewa Muhammad mashkhur. Jinjina kai ahmad yayi tare da cewa wow nice name. A taqai ce mashkhur yace thank you. Ahmad kuwa qarawa yayi da cewa, amma in ba damuwa zan iya kiranka da mashkhur koh. A ta qai ce mashkhur yace Yes you can try.

Ahmad kuwa murmushi yayi tare da cewa ngd by, bai jira amsar mashkhur ba ya fuce. Yana fita mashkhur yaja wani siririn tsaki, sabida sam shi bayasan surutu ko hayaniya shi yasama bayasan ya shiga cikin baqiin fuska in dai ba da daliliba..........

Tom yau shine ranar farko da mashkhur ya fara zuwa makaranta. Masha ALLAH mashkhur yaci interview, dan haka streat aka wuce da shi aji. Shima ahmad ya ci tasa interview amma shi ba’ ajinsu d’aya ba sabida mashkhur d’an science ne shi kuma ahmad d’an art ne, dan haka ko wanne 6angaran su daban, sai dai in zasuyi subject d’aya ne sai a had’e su.

Kai mashkhur fa yayi farinjini sosai a makarantar rasha, mata da maza suna son abuta dashi, sabida sun san cikakyan kyakywan Nigeria ne. Musamman matan
makarantar, mashkhur dai yaga ‘yan matan rasha farare tass kuma kyawawa, amma sam ba wanda ta birge shi a cikinsu sabida har yau ko kallo basu ishe shiba. Suma matan sunyi naci akan mashkhur ya kulasa amma ina mashkhur yaqi dan haka a ala dule suka rabu da shi, dan ko abotama yaqi yanda su had’a.

Yauzu mashkhur satin su uku da fara zuwa makaranta shida ahmad. Yanzu ahmad kusan kullum sai yazo wajan mashkhur hira, tun mashkhur baya sakar mai fuska har ya dawo yana sakar mai fuska, haka dai zasu zauna suta hira abinsu, duk da dai ba wata hirar arziki suke ba, da yake mashkhur ba mai sun magana bane sosai.
Tofah mashkhur yamai da hankali sosai yana karatu amma sai dai abu d’aya ne yake damunsa. Ba komai bane yake damun mashkhur ba face nacin wata budurwa a makarantarsu wai ita ZEE. Duk yan matan makarantar sun rabu da mashkhur sabida sunga irin shamisu qanshin da yake amma ina banda zee, dan ita bata gajiya da yiwa mashkhur magana, kuma gashi ko tai mai magana ma ba amsawa yake ba. Zee dai ruwa biyu ce, tana kama da ‘yan Nigeria kuma tana kama da ‘yan rasha, amma dai gaskiya tafi kama da ‘yan rashan.......

Tom yanzu mashkhur ya saba da zaman rasha sosai kuma sun shaqu da abokinsa ahmad sosai, sabida kusan kulluma in dai basa makaranta suna tare. Yanzu mashkhur ya san wajaja da dama a qasar rasha. Dan wataran haka suke futa waja shaqatawa ko shopping shida ahmad, abunsu dai gwanin ban sha’awa.

Mashkhur ya lura da har yanzu ba wanda ya bugo mai waya daga gida, kenan abinda yake zargi ya tabbata wato su dady sun san mai ya gayawa zahra. Shima mashkhur d’in yana so ya biga gida amma sam ya kasa sabida yasan yayiwa dady da ammi harma da hajiya kaka laifi dan haka mah bai yi gigin buga musu waya ba kawai ya share. Amma dai watarana suna waya da abdul shi kuma abdul bai ta6a gayawa mashkhur, sun ji abida yacewa zahra ba shima mashkhur d’in bai tambaye shi hakan ba.

Tom mashkhur fa ya mayar da hankali sosai yana karatu, hakan ba qaramin burge malama makarantar yake ba, harma da d’aliban. dan wasu har baqin ciki suke mai mussaman ma ‘yan Nigeria da yake akwai ‘yan Nigeria acan ba laifi. Yanzu mashkhur yayi wajan wata shida a makaranatar amma abin mamaki shine har yanzu zee taqi ta rabu da mashkhur. Mashkhur kuwa har yau bai ta6a bud’e baki yayiwa zee magana ba. Haka dai take ta tusa kanta a wajan mashkhur kamar mayya dan har ‘yan makarantar mah har dariya suke mata sabida yanda mashkhur yake shareta baya mata magana.........

One yers a go. (Bayan shekara d’aya).

Kwanci tashi ba wuya a wajan ALLAH yau mashkhur shekararsa d’aya a qasar rasha. Kaii duk wanda ya d’ora idon sa akan mashkhur sai ya qara sabida ya sake kyau sosai hutu ya kwanta a jikinsa, wow ai koni amina bayero sai da na kyasa🤗. Yanzu an bawa su mashkhur hutun 3 week wato(sati uku), amma dai hutun bana komawa gida bane sai nan da wata biyar mashkhur zai koma gida yayi hutu, kafin nan yayi shekara d’aya da rabi kenan.

mashkhur ne zaune shida ahmad suna biga ludo game a waya. Mashkhur kuwa sai fama dariya yake, ba komai ne yasa mashkhur yake dariya ba face, ganin ya kusan cinye ahma, wato ya kusan d’aukar king 👑, shikuma ahmad ko d’a d’aya bai shigar gida ba, sabida yanda mashkhur yake takamai ‘yayan sa a ludo d’in. Wani siririn ihu mashkhur ya saki tare da sa Dariyar mugunta yana furta i am the 👑 Murmushin yaqe Ahmad yayi tare da cewa ba komai is playing, wato yana nufi bakomai wasa ne.

Girgiza kai mashkhur yayi tare da cewa ai ko wasan ne dai na fika, hakan yana nufin na fika iya ludo kenan?. Hararar wasa abdul ya watsa mai tare da cewa kai kama isa?. Dariya mashkhur ya sake saki tare da cewa ai ‘yar goge raini mu kai, dan haka da ga yau ni ba sa’ an ka bane a ludo, ka gane ko?. Mashkhur yana rufe bakinsa kafin ahmad ya kai da bashi amsa sukaji, qararawar knocks. Cikin mamaki mashkhur yace to waye haka?

Ohoo ai kai za’a tambaya nasani ko oder kayi? Cewar ahmad. Da sauri mashkhur ya girgiza kai tare da cewa ahh ni fah, ba wata oder da nayi sabida yau ni da kai na nayi girki. Murmushi ahmad ya saki tare da cewa haba mashkhur kaje ka bud’e qofar mana kasan ko wannan mayyar budurwar takace zee tazo, ya qarashe maganar yana sakin murmushi tsokana. Harara mashkhur ya tsawa abdul tare da cewa haba dai mai zanyi da wanna kwarmashashiyar yarinyar nan? ita da ko gidan nan ma bata sani ba?.

Oho nasani mah ko kun je kun jone da ita in dare yayi ku shan soyayyar ku, nikuma ka barni a cikin kokwanto. Had’e rai mashkhur yayi tare da jan dogwan tsaki, ya nufi qofar sabida knocks d’in yayi yawa. Rai a 6ace mashkhur ya bud’e qofar, ba komai ne ya 6ata mashkhur rai ba face sharrin da ahmad, yayi mai yanzu akan zee.
Mashkhur yana tafiya bud’e qofar Ahamd kuwa ya saki dariyar mugunta sabida yasan ko ba komai, ya rama baqin cikin da mashkhur ya sa shi, akan ludo............

ADALILINTA💜❤️💜

BY AMIMA BAYERO💜❤️💜

Free book.

Da sauri ahmad ya miqe daga zaune saka makwan wani ihu da yaji mashkhur ya saki.
Bakomaii ne yasa mashkhur sakin ihun ba face abinda ya gani a bakin qofar.
Bakomai mashkhur ya gani a qofar ba face DADY da ABDUL, tsalle mashkhur ya daka tare da rungume abdul yana cewa oyoyo, my real brother. Sosai suka qan qame junan su, ku wannan su zuciyarsa ciki da farin ciki.

Ahmad kuwa tsayawa yayi ta baga yana ganin ikwan ALLAH shi duk a tinanin sama wani mugun abun ne ya samu mashkhur ya tsala uban ihun nan. Cikin farin ciki mashkhur ya saki abdul tare da rungume dady, yana cewa oyoyo my dady na. Shima dady murmushi ya saki tare da rungume mashkhur d’in yana cewa mai sunan baba kenan ka kyauta fa. Ko dady bai gayawa mashkhur sabida mai yace mai ya kyauta ba, yasan ba zai wuce akan abinda ya gayawa zahra bane, dan hakama bai nemi qarin bayani ba.

Cikin farin ciki mashkhur ya saki dady tare da cewa dady ku shigo mana. Ba musu su dady suka shigo shi kuma mashkhur ya rufo qofar. Har qasa ahmad ya tsuguna ya gai da dady tare da yi mai sannu da zuwa, cikin farin ciki da sakin fuska dady ya amsawa ahmad. Murmushi mashkhur yayi tare da kallan su dady yana cewa dady ga abokina sunan shi ahmad a gidan nan yake amma shi a qasa yake kuma makarantar mu d’aya, amma shi d’an art ne.

Murmushi dady yayi tare da cewa masha ALLAH amma fa yana da hankali sosai, kuma nayi mamaki sosai yanda kuka saba da juna, kai da bakasan mutane mah. Kallan ahmad mashkhur yayi tare da cewa hmm dady ai abokin nawa ne yana da naci, ya qarasa maganar yana sakin siririyar dariya. Shima ahmad d’in dariya ya saki tare da cewa wlh kam dady, ai sai da nayi da gaski sanan naci sa’a mashkhur ya fara kulani. Dukkan nunsu dariya sukayi, abdul kuwa cewa yayi hmm ai kawai yaya mashkhur yaga kafishi hankali ne, shiyasa ya ke kulaka dan sam yaya mashkhur bayajin naci.

Had’e fuska mashkhur yayi tare da cewa abdul gaskiya ka rai na ni, amma zanyi maganin ka. Kai yaya mashkhur wasa nake ma fa, mai yayi zafi haka, mai da kallansa yayi kan ahmad tare da cewa yauwa abokin yaya mashkhur wasa nake ma, kawai dai kayi dace ne shiyasa yaya mashkhur yake kulaka, abdul ya qarasa maganar yana sakarwa ahmad murmushi. Jinjina kai ahmad yayi tare da cewa gaskiya dai kam amma mashkhur wanan qanin naka yafika sauqin kai nesa ba kusa ba.

Kwari kuwa ahmad ai abdul yana da sauqin kai ba kamar yayan saba, cewar dady. Tom shikenan dady yanzu mai kake so kaci nai ma oder?, cewar mashkhur, girgiza kai dady yayi tare da cewa aa ni yanzu bana buqatar komai sai dai zuwa anjima. Mai da kallansa kan abdul mashkhur yayi tare da cewa my abdul kai me kakeso ai ma oder?. Girgiza kai abdul yayi tare da cewa ni dai yanzu so nake ka bani masauki nai wanka sanan kwanta bacci kafin na tashi kuma ka girkamin abinci da hanunka, bana oder ba, ya qarasa maganar cikin zaulaya.

Murmushi mashkhur yayi tare da cewa tom shikenan zan yima abinda kace in ma da wasa kake in ma da gaske kake, duk zanyi ma. Cikin jin dad’i abdul yace kai yaya mashkhur gaskiya shi yasa nake son ka wlh nayi missing d’in ka sosai. Harararsa mashkhur yayi tare da cewa to in da gaske kake kana kewata ka dawo qasar nan mana muyi karatu tare?. Da sauri dady ya cafe zancan da cewa ehh yaza ai ku tafi dukkan ku ni kuma ku barni ni ka d’ai?.

To dady baga su faruq da haidar ba, cewar mashkhur, girgiza kai dady yayi tare da cewa haba mai sunan baba ai su faruq, yara ne ku kuma kunga ai kun tasa. Tom shikenan dady ai nima kamar yau ne zan dawo kuma gashi ina tare da abokina ahmad ai shikenan. Haka dai suka zauna sukai ta hira, daga qarshe dady da abdul suka shiga ciki sukayi wanka sanan suka kwanta bacci domin su huta. Mashkhur kuwa kicin ya shiga ya fara dafa musu abinci, kamar yanda abdul ya biqata, shima ahmad bin mashkhur yayi domin taya shi............

Tom mashkhur yaji dad’i zuwan su dady sosai da sosai. Shima dady yaji dad’i yanda ya samu mashkhur d’in, dan har makarantar su mashkhur dady yaje, domi yaji mai mashkhur yake aikatawa. Ai dady da yaji labarin mashkhur yana qoqari ba qaramin dad’i yaji ba, kuma yayi farin cikin hakan sosai. Yau su dady sunyi kwana goma ya rage saura kwana hud’u su dady su koma dama sati biyu zasuyi, kenan lokacin da su mashkhur zasu koma hutun makaranta.

Yau dady har mota ya siyawa mashkhur sabida su rage zirga-zirga a motar haya. Mashkhur yayi farin ciki sosai, bama shi ka d’ai ba har abokinsa ahmad shima yayi farin ciki.
Tom kafin dady ya tafi sai da ya ke6e shida ahmad ba tare da sanin mashkhur ba. Dady ya tambayi ahmad akan mashkhur yana aikata abinda bai dace ba?. Ahmad ya shedawa dady cewa mashkhur baya aikata abinda ba dai-dai ba. Dady yaji dad’i hakan, kuma har Number sa ya bawa ahmad, yace mai duk sanda mashkhur ya fara aikata wani abun da yaga bai dace ba ya bugomai ya sanar mai, ahmad cikin ladabi ya cewa dady in sha Allah.........

To yau fa ta kasance su dady zasu koma gida, mashkhur kuwa duk jikinsa yayi sanyi, kamar yayi kuka,amma ba yanda ya iya a ala dole ya haqura.
Bayan su dady sun tafi, washegari mashkhur da ahmad suka koma makaranta a cikin sabuwar motar da dady ya siya musu. Yauma kamar ko da yaushe zee tana ganin mashkhur ta fara nane mai, mashkhur kuwa ko kallanta bai ba ya shige aji.........

4 monthly a go (Bayan wata hud’u)......

Yanzu fa su mashkhur sun dage da karatu sosai da sosai, sabida saura wata d’aya su fara jarabawa,bayan sun gama jarabawa kuma su tafi gida hutu.
Mashkhur kuwa ya dage da karatu baji ba gani, harma yafi ahmad karatu da yake shi mashkhur d’an science ne, shi kuma ahmad d’an art....
Toh Yanzu fa ya rage saura sati d’aya su mashkhur su fara Exams (jarabawa). Dan haka mashkhur ya dage da karatu dan yanzu ko hira basa samu suyi shida ahma........

Tofa yau su mashkhur zasu fara jarabawa, dan haka mashkhur bai yi bacci ba, bayan ya gama karatu, sallar dare ya tashi yayi, yana roqan ALLAH ya bashi sa’a.
Tom yau mashkhur da murna ya futo daga d’akin jarabawa sabida duk question d’in ba wanda ya bashi wahala. Lokacin da ya futo daga jarabawar ya samu ahmad cikin mota yana jiran shi dan haka ba 6ata lokaci ya shige suka tafi......

To kwanci tashi ba wuya a wajan ALLAH, dan yanzu su mashkhur sun qare Exams d’in su tass, result suke jira kawai sai su koma gida hutu. Mashkhur kuwa ya dage sai addu’a yake duk da yasan yana da qoqari, amma hankalinsa bai kwanta ba sabida yana so

Please Login or Register in order to submit comment