Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

magiya tana bashi haquri.

Wanka mashkhur ya shiga bayan ya futo ya shirya cikin qananun kaya yayi kyau sosai abinka da kyakyawa. Key d'in motarsa ya d'auka sabida sam ya gaji da zaman gidan musamman ma in ya tina zahra tana ciki. Lokacin da mashkhur ya sauka qasa zai fita zahra tana ganin shi, da yake tana koridon ventilation d'in bedroom d'in ta tana shan iska, tana kallan sa ta sama harya shiga mota a zuciya zahra tace kalle shi kamar mutumin kirki ALLAH Ya shiryeka.

Fucewa daga bedroom d'in zahra tayi ta nufi kicin ta d'ora jalof d'in shinkafa, tana d'orawa ta futo ta fara gyara gidan. Sai da zahra ta gyara ko ina na gidan tass d'akin mashkhur ne kawai bata gyarawa ba. Bayan ta gama gyara gidan d'aki ta koma ta sakeyin wani wanka, bayan ta gama Ta d'akko doguwar rigarta ta atanfa ta saka tare da mayafi. Sanan taje ta zuba abincI taci, bayan ta gama cin abincin tv fallo zahra ta kunna domin kallo.

MBC 2️⃣ ta kamo, ai kuwa cikin sa'a zahra ta tarar ana film din focous. Zahra tana matuqar qaunar film d'in focous lokacin da tana Nigeria sun ta6a kallansa ita da ilham harma dasu faruq, suna cikin kallon lokan makaranta islamiyya yayi, zahra da ilham suka tafi makaranta. Bayan sun dawo haidar ya bawa su zahra labarin yada aka qare film d'in amma zahra tana matuqar so taga qarshan film d'in da idon ta. Da sauri zahra ta miqe ta d'auki cup akan draining table ta bud'e firij ta d'auko juice ta zuba a cup d'in sana ta dawo ta zauna ta fara kallon.

Zahra fa ta tafi duniyar kallom film ko kwakwaran motsi batasanyi sabida tanajin dad'in film d'in sasai ta duqufa, sai kallo take. A dai-dai lokacin mashkhur ya dawo gidan, parking d'in motar yayi bayan yayi parking ya fud'e bayan motar ya kwaso ledojin kayan Da ya siyo, sanan ya tawo, yana qarasawa bakin benan ya fara hawa step d'in benan, har ya qarasa sanan ya bud'e qofar fallon ya shiga.

6anran zahra kuwa bama tasan mashkhur ya shigo ba d'an ita tama manta da rayuwar wani mashkhur, sam bata jikin hankalinta ta d'ora qafa d'aya kan d'aya hanunta riqe da cup d'in da mashkhur yake shan t.......... .

Tofa ya kuke ganin zahra da mashkhur zasu qarke?. Kuna ganin mashkhur zai kyale zahra ko kuwa?. Amma fa karku manta mashkhur ya yiwa zahra kashedi na qarshe. Kuma yace ba wuto tazo yiba sai gashi ya kamata dumu-dumu tana wutawa.

Ku biyoni a next page dan jin ya zata qarke tsakanin zahra and oga mashkhur.


ADALILINT πŸ’œβ€πŸ’œ

BY AMINA BAYERO πŸ’œβ€πŸ’œ

My number 09162226240.

Typing............

*page 54*

6anran zahra kuwa bama tasan mashkhur ya shigo ba dan ita tama manta da rayuwar wani mashkhur, sam bata cikin hankalinta ta d'ora qafa d'aya kan d'aya hanunta riqe da cup d'in mashkhur da yake shan t................


A gajiye mashkhur ya qarasa shigowa falon, karaf idonsa ya sauka akan zahra ta d'ora qafa d'aya kan d'aya da cup d'in shan t d'insa a hanunta tana kallo tv sai murmushi take sheqawa alamun film d'in yanayi mata dad'i, dan mashkhur ya lura Sam zahra batasan ya dawo ba. Tsayawa yayi yana kallan ikwan ALLAH, shida yace mata ba hutu tazoyi gidan ba amma har wani kallan tv take tanajin dad'in, cikin zuciyarsa yace lalai yarinyar nan ta samu sake, amma zanyi maganin ki yanzu ya qarasa maganar yana ajiye ledojin kayan da ya siyo dasu a gefe.

Qarar ledojin da mashkhur ya ajiyene ya dawo da zahra daga duniyar kallan data tafi, da sauri ta jiyo ta kalli inda taji qarar ledar, karaf idon ta ya sauka akan mashkhur wanda yake qoqarin ajiye ledojin a wajan. Ya salam abinda zahra ta furta kenan a zuciyarta, nan da nan gumi ya fara keto mata duk sanyi A. C fallon, ita tama manta da wani mashkhur ta tafi duniyar kallo tabbas tasan yau jikinta sai ya gaya mata.

Sam ta kasa wani kwakwaran motsi gashi taga mashkhur yana tunkaro ta. A zuciye mashkhur ya kai hannu zai tsinkawa zahra mari, da sauri zahra ta rintse ido tare da sakin cup d'in hannuta qasa tassss, ya fashe a wajan. mashkhur kuwa harya kai hannu kusa da fuskar zahra sai kuma ya dakata koh me ya tina oho. A zuciye mashkhur yace lalal yarinyar nan, ni zaki nunawa taurin kai koh? Wai ke mai kunnan qashi koh? Wlh yau duk fitsarar da take kanki sai na sauke mike ita zaki gane baki da wayo.

Kallanta yayi fuska a had'e yace jeki kusa da window d'in can ki tsaya, ba musu zahra ta nufi wajan tagar jiki na rawar tsoro. Bayanta mashkhur yabi, suna qarasawa, mashkhur ya sake tamke fuska sosai yace ciromin mayafin jikin ki, ya qarsa maganar yana kawar da kansa kefe, nan da nan zahra ta fara zaro ido, a zuciyar ta sai mai-mai ta ciremin mayafin jikin ki kuma? To mai zaiyi da mayafin nawa, wata uwar tsawa mashkhur ya daka mata da cewa!! Ba magana nake miki ba ko sai jikinki ya gaya miki zaki ciro ne? Ya qarasa magana yana watsa mata harar mai cike da tsana.

Nan da nan zahra ta qara kid'imewa da yake tana tsoran tsawa sosai musamman ma ta dodonta mashkhur dan haka ba 6ata lokaci ta fara qoqarin cire mayaginta daga kan ta. Tana gama cire wa ta miqamai hanunta na rawa, a zuciye mashkhur ya fizge mayafin. Gashi kanta ko d'an kwali babu, dama parking tayi da yake tana da gashi sosai. Da mamakin zahra gani tayi mashkhur ya fara yayyaga mayafin gida-gida, shiru zahra tayi tana ganin ikwan ALLAH.

Sai da ya yayyaga mayafin gidan shida ta tsaye, zahra bata ankare ba sai ji tayi mashkhur ya danqo hannayanta duka biyun da qarfin gaske. Har zahra zata fara ihu, mashkhur yace wlh kika yimin ihu sai na zubar miki da haqora, ba yanda zahra ta iya haka ta haqura tai shiru. Jan hannayan nata yayi duka biyun ya d'ora akan window, Zuge glass d'in window d'in yayi nan da nan sanyi ya fara hurowa da yake garin da sanyi sosai yayyafin qaqarama ake, hannun zahra d'aya mashkhur ya d'ora akan qarfan windo, sanna ya fara nad'eshi da mayafin zahra da ya yaga.

Mashkhur bai saki hanun zahra ba sai da ya kulle shi katamau a jikin qarfan tagar yanda ko kwakwaran motsi bazata iya da hanun ba sanan ya saki. D'aya hanun ma haka yay mai shima, duka biyun sai da ya kulle su a jikin qarfan taga, kuka zahra ta farayi tare da cewa dan Allah yaya mashkhur kayi haquri ka kwance ni wlh bazan qaraba, sanyi nake ji, ta qarsa maganar murya tana rawa. Kee rufemin baki koda wasa kika qara ambatar sunana sai na sumar dake kuma Allah yasa naji kin isheni da kuka, sai na faffasa miki baki, ya qara maganar rai a jagule yana jan wani dogwan tsaki, tare da barin wajan.

Nan da nan hawaye masu zafi suka fara gangarowa a idanuwan zahra, ta rasa wannan wace tsana mashkhur yake mata? Shi da yake tausayin 'yan uwansa wanda bayaso ko quda ya ta6asu yana matuqar qaunar su ilham, amma sai gashi ita yana mata haka, gaskiya ko bata shiga zuciyar mashkhur ba tasan tsanar da yayi mata ba qarama 6ace.

Mashkhur kuwa yana barin wajan bedroom d'in sa ya wuce rai a dagule. Gaskiya dady baku kyautamin ba Wlh bana qaunar ta bazan ta6a santaba kuma na tsane amma sai da kuka aurami ita gaskiya bakumin adalci ba, a fili mashkhur yake fad'in hakan. Yana cikin wanan hali aka fara kiran sallar magriba. Mashkhur ba 6ata lokaci ya shiga toilet ya d'auro alwala, sannan ya futo ya gabatar da salla.

Bayan ya idan da sallar kwanciya yayi akan bed rai a jagule sam zuciyarsa ta kasa mai sanyi. Haka yay ta tinani yana juyi akan gado har lokacin sallar isha'i yayi. bayan ya idar da sallar isha'i kwanciya yayi bacci mai nauyi yayi awan gaba da shi.
Zahra fa tun tana jure tsayiwa da iskar da takeji harta gaza, wani irin mugun sanyi ne yake damunta gashi window d'in a bud'e ba damar ta rufe hanunta a d'aure. Nan da nan mura mai zafi ta kama zahra da yake ita ba ma'abociyar san sayyi bace.

Abu kamar wasa har qarfe tara da rabi zahra tana cikin wanan halin, duk tabi ta fita daga hayyacinta nunfashima da kyar take ga zazzabi daya rufeta, ga qafafuwanta sun kunbura, duk jikinta yayi jajir abinka da farar fata.
Misalin qarfe goma na dare mashkhur ya farka daga nanauyan bacci da ya tafi, miqewa yayi ya shiga toilet ya wanke fuska sanan ya kama hanyar zuwa falo. Yana qarasawa falan idonsa ya sauka akan window da ya d'aure zahra, duk ta fita cikin hayyacinta.

Nunfashima da kyar take sai ajiyat zuciya take saukewa ga wata rawar sanyi da take. A hankula ya fara takawa domin qarasawa wajan, zuba mata ido yayi yana kallan yanda ta fita daga hayyacin ta, ya dad'e yana kallanta can kuma yaja wani siriri tsaki tare da juyawa wajan draining table. Yana qarasawa ba 6ata lokaci Ya d'auki wata qaramar wuqa cikin jeri cokulan table d'in sanan ya juyo, ya cigaba da tafiya kamar bayasan taka qasa.

Sai da ya d'auki tsawan munti biyu yana tafiyar nan a hankula kafin ya qarasa wajan tagar da ya d'aure zahra. Tsayawa yayi yana tinanin ta ina zai fara kwance ta dan yasan yana kwanceta jikinsa zata fad'a kuwa, shikuma gashi bazai ta6a riqe zahra ba wai dan karta fad'i. Hannu yasa ya zuge tagar dama yana sane ya bar tagar a bud'e sabida sanyo ya shigo ya takurawa zahra. Bayan ya rufe window d'in, juyowa yayi ya fara yanke d'auri da yayiwa zahra a windo d'in, a lokacin zahra ta d'an fara farfad'owa da yake sanyi ya daina shigowa.

Yana gama yankewa zahra ta saki jiki ta fad'i qasa tammm, mashkhur yana ganin sanda zata fad'i amma sam yaqi tareta. Zahra taso tayi ihu amma bazata iyaba jikinta duk yayi sanyi, sabida awarta biyar (10 hours) a d'aure kuma a tsaye . Sabida fad'uwar da tayi har sai da goshinta ya d'an fashe, abin dai abin tausayi. Mashkhur kuwa ji yayi ya d'an fara tausaya mata kad'an, sabida halin da ta shiga. Amma da ya tina zahra cefa wacce yafi tsana aduniya kuma yasan in dai ka farajin tausayi mutum so zai iya shiga nan da nan yaji ya daina tausayai mata, sa ma haushin ta da ya qara turniqe shi.

Cikin tsawa yace tashi ki share wajan da kika fasa cup d'in can in kuma ba hakaba jikinki ya gaya miki yanzu-yanzu nan. Duk da azabar da zahra takeji a jikinta hakan bai anata jin abinda mashkhur yake cewa ba, jiki na rawa zahra ta fara qoqarin miqewa daga kwanciyar da tayi domin ai watar da abinda mashkhur ya sata. Kai ni kuwa amina bayero nace mashkhur anya kana da imani a cikin zuciyar ka kuwa? In banda jiri ba abinda zahra take ga wani mahaukacin cikwan kai da mura da suke damunta, kwata-kwata ma dai bata cikin hayyacinta dan da qyar take iya bud'e ido komai dishi-dishi take ganinsa.

Haka ta miqe tana taga-taga kamar zata fad'i sai. dafe bango take, mashkhur kuwa cewa yayi wlh na futo baki gyara wajan ba sai kin gane baki da wayo, Ya qarasa fad'i tare da jan wani dogwan tsaki ya juyawa, ya wuce d'akinsa. Dakyar zahra ta iya qarasawa wajan da cup d'in ya fashe ALLAH ya taimaketa gida uku cup d'in ya fashe, dan haka hannu na rawa ta kwshe su domin kaiwa dozbin. Amma ina ta qasa miqewa, haka dai ta ringa jan qafafuwanta tana rararfe har ta qarasa wajan kwando dozbin d'in ta zubar.

Sai da ta tsaya a bakin sharar ta huta sosai sanan ta fara rarrafawa domin shiga bedroom d'inta. Dakyar ta iya qarasawa da rarrafe bedroom d'in ta, sanan ta shige. A bakin qofar bedroom d'in ta zauna wani mugun ciwan kai ne yake damunta ga zazza6i daya rufeta, ga mura ka kuma goshinta ya fashe, ga qafafuwa duk sun kunbura. Tafi rabin hours a haka sam ta kasa komai, can dai ta daure ta rufe qofar tana so ta sawa qofar key amma bazata iya tashi ba, haka dai zahra ta rarrafa har zuwa wajan bed d'inta, sai da tayi namijin qoqari kafin ta iya hawa kan gadon nan.

Da kyar ta iya sa bargo ta rufe jikinta, jikinta sai rawa yake sabi da tsabar sanyi da takeji. Kai ranar dai duk san sallar zahra bata iyaba ba, dama batayi sallar magriba da isha'i ba, da yake tun qarfe shida na yamma ya d'aure ta sai goman dare ya kwance ta, ita zahra ma ta manta da wasu salolin da ake binta, kai ai koni amina bayero sai da na zubarwa da zahra hawaye dan zahra ta bani tausayi sosai😒. A Haka dai baccin azaba ya kwashe zahra.
6anran mashkhur kuwa ranar bacci yayi harda munshari dan ko ba komai yasan yau ya quntatawa zahra.

Washegari.............

Ringing d'in wayarsa ne ya tashe shi daga bacci, har wayar ta katse mashkhur bai samu damar d'auka ba. Nan da nan wani ringing d'in ya sake shigowa, hannu ya miqa kan qaramar drowar kusa da bed d'in ya zaro wayar domin ganin wake kiran wayar. Sunan ahmad ya gani ya futo 6aro-6aro akan wayar, ajiyar zuciya ya sauke tare da d'aukar wayar ya kara a kunan sa. Okay kawai mashkhur yace sanan ya katse wayar, sai da ya shiga toilet yayi brush ya wanke face d'in sa sanan ya futo, yana futowa ya zira jallabiya, sanan ya fuce daga bedroom d'in gaba d'aya.

Yana futa falo ya nufi hanyar bud'e qofar gidan, yana fud'ewa yaga Ahmad a tsaye ya riqe ugu da alama ya dad'e da tsayuwa a wajan. Rai a had'e Ahmad yace gaskiya mashkhur ka cika iyayi, tun yaushe na cema, ina tsaye? na kira wayar takama da kyaur ka d'aga, nacema kazo ka bud'e amma sai da ka shanyani?. Haba Ahmad yanzu meye Na mitar tinda dai na bud'e ma, kawai ka shigo!! Da sauri Ahmad yace aa ai ni dama ba wajan ka nazo ba.

To idan ba wajena kazoba wajan wa kazo? Cewar mashkhur, wajan qanwata zahra nazo mana ko ka manta yau zan kaita school ne?. Mashkhur kuwa bai san santa murmushi mugunta ya kwace masa ba, sabida tinawa da yayi da abinda ya yiwa zahra jiya tambas yasan bazata iya moruwaba yau dan taji jiki. Mamaki ne ya kama Ahmad shi dai yasan mashkhur ko maganar zahra bayaso, amma shine yanxu yana jin ance zahra yake wani murmushi. Ahmad kawar da maganar yayi da cewa, yanzu dai kaje kace ta shirya ta futo in kai ta, makaranta kasan yau muma zamu koma school kuma muna da lectures.

mashkhur yama manta da wata makaranta da zasu koma, sai yanzu da ahmad ya tina mai. Shiru Ahmad yayi yana jiran amsar mashkhur, can mashkhur ya kalli ahmad fuska d'auke da murmushi yace kai yaufa bazata iya zuwa makarantar nan ba because she is not feeling fine ya qarasa maganar yana sakin Murmushi mugunta. Shima ahmad murmushi yayi tare da cewa mashkhur ko dai ko dai? Mashkhur ciki rashin gane inda magar ahmad ta daso yace ko dai me?.

Hmm mashkhur kenan ko dai ka angwance ne yau ban sani ba? Ahmad ya qarasa maganar fuska a sake. Nan da nan annurin fuskar mashkhur Ya 6ace 6at, wani dogwan tsaki mashkhur ya saki tare da cewa, look Ahmad bana san wanan iskanci, aikin banza aka gayama ni irin kane, to sam ni wannan bai dame ni ba, kai barima kaji, ko zanyi abinda kake tinani bazan ta6ayi da itaba barema bayi zanba, yana gama fad'ar hakan ya wuce yabar ahamd a tsaye.

Jinjina kai Ahmad yayi tana mamakin hali irin na mashkhur abin dai yana bashi mamaki sosai, Allah dai ya shirye ka Ahmad ya furta cikin zuciyar sa. Shiga ciki ahmad yayi ya fara jiran zahra ko ALLAH zai sa ta futo, sai da ahmad ya kai har qarfe tara na safe yana jiran zahra bata futo ba, yana shirin fita mashkhur ya futo da shirin zuwa makaranta ba 6ata lokaci suka wuce tare. Ahamd yanaso ya tambayi mashkhur mai yake damun zahra amma yasan ko ya tambaya mashkhur ba bashi amsa zaiyi ba, haka nan da ya ha qura suka tafi zuciyar ahma cike da tinanin zahra a wana hali take?.

ZAHRA.......

6anran zahra kuwa tinda ta kwanta ba ita ta tashi ba sai qarfe sha biyu na rana ta tashi. Da wani matsanancin ciwan kai da mura ta tashi ga zazza6i, jikinta duk yayi stami, hankalinta ya tashi sosai da ta tina batayi sallar magriba da isha'in jiya ba, ga kuma ta asuba d'in yau. Jiki ba kwari ta miqe, tare da sa hannu ta riqe kanta da yake mata barazanar rabewa. Toilet ta shiga, ta had'a ta gasa kanta da qafarta da ta kunbura suntum, da sauran jikinta da yake mata tsami.

Daga haka tai wanka ta da brush sanan ta d'ara alwala, ta futo jiki d'aure da towel. Sanan ta zura dogwan higab tayi sallar asubayi, sauran salolin da ake binta batayi ba, ta bari sai lokacin su na yau yazo sai ta had'a tayi. Bayan ta gama addu'o'i ta da lazumi miqewa tai ta cire hijab d'in sanan ta nufi mudubi. akan kujerar mudubi ta zauna, kalla fuskarta tayi, idanuwanta sun kunbura sosai goshinta ma haka. Hannu tasa ta fara mulmula goshin nata, duk da tanajin azaba haka ta daure. Ba yan ta gama mulmulawa ruwan zafi ta d'akko ta qara gasa goshin nata duk da kuwa tanajin azaba kawai daurewa take, ba laifi goshin nata ya sace sosai, kunburin ma saura kad'an.

Daga haka mai ta fara shafa sanan ta zura bayan taidar da gama ta nufi drowar kayan ta. Doguwar rigar mara nauyi ta saka.

Sai da da zahra ta gama leqawa falon ta tambatar mashkhur baya falon sana ta futo. A hankula ta nufi kicin, tanaso d'ora abinci amma tana tsoran ta fara mashkhur ya zo ya tarar da ita. Zahra bata shirya shan sabuwar muguntar mashkhur ba dan haka bedroom d'in ta ta koma, cikinta cike da yunwa. Ventilation d'in bedroom d'in ta ta shiga domin shan iska kamar yadda ta saba, kamar ance ta kalli qasa!! gani tai ba motar mashkhur hakan ne ya nuna mata cewa mashkhur fa ya fita,, cikin farin ciki, ta koma kicin ta dafa indomei da kwai, sanan ta d'ora t, bayan ta gama a kicin d'in ta zauna ta ci abinci sabida uwar yunwa da takeji.

Tana gamawa ta fita falo tare da bud'e firij, maganin mashkhur na mura da na shaye-shaye ta gani da yawa a ciki, Da sauri ta d'akko maganin mura tasha murfi d'aya, sanan ta d'auki ruwa ta koma bedroom d'in ta. Tana komawa ta bud'e qaramar drowar, ta samu maganin ciwan kai tasha, daga haka tayi sallar azahar ta kwanta bacci mai nauyi yayi awan gaba da ita. ALLAH SARKI ZAHRA BAIWAR ALLAH.............

Abinda yasa kuga kwana biyu bana yi muku posting shine!! Inayi posting bakwamin LIKE πŸ’— , shiyasa kukaga banayi muku posting, in bakwa buqata ku fita daga group d'in mana amma sai ku bud'e ku karanta bakuyi min like ba. Wlh in dai bakwa like zan daina posting gaba d'aya na rufe group d'in, in kuma wasu daga cikinku sunayi zan cire wanda naga basiyi, nabar masuyi, daga yau duk wacca naga ta bud'e kuma ta karanta batayimin like ba sai na cire ta daga group tinda littafin free ne bana kud'i ba, dama na kud'i ne sai kuce biya kuke shiyasa bakwa like d'in..........

Amma in kunji ba dad'i kuyu haquri, gani nai Gwara na gaya muku gaskiyar karna cutar da kai na, ina yimuku fatan alkhairi kuma da fatam zaku gyara na barku lpy sai ku biyoni a next page........


ADALILINTAπŸ’œβ€πŸ’œ

BY AMINA BAYERO πŸ’œβ€πŸ’œ

My number 09162226240

Typing............

*page 55*

Tana komawa ta bud'e qaramar drowar, ta samu maganin ciwan kai tasha, daga haka tayi sallar azahar ta kwanta bacci mai nauyi yayi awan gaba da ita...............

Tunda zahra ta kwanta bata motsaba, sai wajan qarfe hud'u saura da akayi kiran sallar la'asar. Jikinta duk a mace ta tashi ga zazza6i da cuwan kai daya sake kamata, haka dai ta daure ta miqe ta shige toilet. Wanka tayi da ruwan sanyi sabida tsabar zafin da jikinta yake mata, tana gama wanka wata mura mai zafi ta qara rufe ta. Haka dai ta lala6a, ta d'aura alwala ta futo, tana fitowa jikinta ya fara rawa wani mugun sanyi taji ya rufeta.

Dakyar zahra ta iya sa kayanta ta gabatar da sallar la'asar, sallar ma a zaune tayi, sabida har yanzu qafafuwanta zafi suke mata. Bayan zahra ta gama lazumi miqewa tai zata koma kan gado dan kwanciya kawai taji ana knocking d'in qofar ta. Shiru zahra tayi tana tinanin waye yake kwankwasa mata qofa? Tasan dai mashkhur bazai ta6a kwankwasa qofar taba, haka dai ta wuce jiki ba kwari domin ta bud'e karma tace mashkhur ne yake bugawa ta jawowa kanta wasa masifar.

Zahra tana isa ba 6ata lokaci ta bud'e qofar, mamakine ya bayyana akan idon zahra sakamakwan wanda ta gani a bakin qofar, Ba kowa bace face zee wato qawar mashkhur. Yamutsa fuska zee tayi cikin yaran English tacewa zahra, dama pepper soup nake so ki dafamin yanzu, ki hanzarta ki dafamin banason ki6atamin lokaci. Daga haka zee tai wucewar ta tabar zahra a tsaye, cike da mamaki. Shiru zahra tayi tana tunanin taya zata dafawa zee pepper soup alhalin tana cikin wanan halin na rashin lafiya, ya sallam, abinda zahra ta furta a cikin zuciyar ta kenan.

Juyawa zahra tayi ta koma cikin bedroom d'in ta, tinanin ta farayi, bataso taje ta dafawa zee pepper soup, sabida batajin dad'i, amma tasan in bata yiwa zee abinda takeso ba sai jikinta ya gaya mata a wajan mashkhur. Tina hakan da zahra tai ne yasata sauri tashi ta nufi drowar.

Please Login or Register in order to submit comment