Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ido. Aaa kawai ka tafi zan dawo nima, dan ALLAH zahra yaushe zaki dawo nifa na gaji da jiran ki in kika bari na sake dawowa gidan nan wajan ki komai ma zai iya faruwa. Cikin mamaki zahra tace dame-dame ne zai faru yaya mashkhur ni ban gane ba.

Hmmm hakki na zanzo kar6a na gaji da jira yau kusan shekara biyu kenan fa. Zahra basarwa tai kamar bata son da zancan ba tace wana haqqi kuma yaya mashkhur ni ban gane mai kake nufi ba. Oh baki gane ba zaki gane zahra in kika zo zan nuna miki komai daki-daki tinda baki son haqqin auratayya ba. Oh dama sabida haka kake so na dawo wlh ni ba inda zan dawo.

Haba zahra ki dena cewa haka dan ALLAH kiyi haquri ki dawo kinji matata. D'an ya mutsa fuska zahra tai sanan tace to zan dawo amma in ka amince zakayi min alqawarin ba wani haqqin aure a tsakanin mu. Mashkhur bai san sandda ya zubawa zahra wani kallon rainin hankali ba, a zuciyar shi yace tab tinda nake a rayuwa ta anya an ta6a raina min hankali irin na yarinyar nan kuwa?................

Batin gaskiya ni amina bayero zahra banji dad'in amincewa mashkhur da kimayi ba. 😑

Naso gashin mashkhur yafi haka a gashin da na tanadar mai gashi d'aya akayi kawai na yanke ne sabida na kammala littafin naga kamar naja labarin ne. Amma dai komin banza ya tsuguna wa zahra. πŸ˜‚πŸ˜‚

Kuna ganin mashkhur zai amince da abinda zahra ta fad'a kuwa?. πŸ€”πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

Mu had'e a next page.

Inaga zuwa anjima da daddare zan sake muku wani posting d'in wanan na jiya ne.

[23/04, 8:29 pm] Oum Farhan❀️🩷: ADALILINTA πŸ’œβ€πŸ’œ

BY AMINA BAYERO πŸ’œβ€πŸ’œ

Double page...........

Mashkhur bai san sandda ya zubawa zahra wani kallon rainin hankali ba, a zuciyar shi yace tab tinda nake a rayuwa ta anya an ta6a raina min hankali irin na yarinyar nan kuwa?................

Ya qarasa maganar a zuci yana cizan le6an sa, Cikin mamaki zahra tace yaya mashkhur wanan kallon fa kamar zaka kai min duka. D'an zaro ido mashkhur yayi tare da cewa haba matata taya zan dake ki ko gani nai ana shirin dukan ki zan tare miki iya qarfi na ai. Hmmm lallai kam zahra ta fad'i maganar cikin rashin gamsuwa.

Haba zahra yanzu fa na canza ba mashkhur d'in da kika sani bane da wanan wani daban sabo ba wancan ba. Uhmm amma dai kuna kama koh!? Murmushi mashkhur yayi tare da cewa bari na tashi na tafi dai tinda bazaki bini ba. Daga haka mashkhur ya miqe, itama zahra miqewa tai tare da cewa to ka gai da su ammi da hajiya kaka. Bazaki raka niba? Mashkhur ya fad'a yana kafe zahra da ido.

Eee bana son fita ne amma zan raka ka iya bakin qofa, tom shikenan ginbiya ta duk yadda kikace haka za'a yi. Ah ni ban kai nan ba, zahra ta fad'a tana d'an sakin murmushi, kin wuce har nan a zuciya ta nifa yanzu na zama mijin tace ko ince kan tace ma. Hmmm da ba'a san asalin barbela ba sai ace daga madina ta fito zahra ta fad'i hakan a zuciyar ta amma a fili cewa tai gaskiya ne.

Suna qarasowa bakin qofar mashkhur ya sake cewa dan ALLAH zahra ki dawo da wuri kinji?. Tom shikenan yaya mashkhur zan dawo, aaa ni gaskiya ki dai na cemin yaya gwara ki cemin mashkhur kai tsaye ma, da kice min yaya ya kama ki canza min suna mai dad'i a matsayina na mijin ki kuma masoyin ki. Murmushi zahra zai tare da sunkuyar da kai qasa tana d'an toshe baki.

Hakan kuwa da tai ba qaramin kyau ya qara mata ba, nan da nan mashkhur ya sake daskarewa cikin dad'ar voice yace pls my wife ki canza min. Aaa gaskiya ni bazan iya ba cewar zahra, tabb ai kuwa in baki canza ba yau a gidan nan zan kwana rungume da ke. Auzubillahi zahra ta fad'i hakan tana d'an girgiza kai.

Rai ba dad'i mashkhur ya d'an janyo zahra tare da cewa haba zahra meye haka sai kace na gaya miki abinda bai dace ba?. Shiru zahra tai ba amsa, to ni gaskiya in baki canza min suna ba yau ina nan tare da ke, kin san irin leat night d'in da mukayi a russian shi za!!!! Da sauri zahra ta sa hanunta ta d'an toshi mai baki tare da cewa haba wai kai sabida mai ka kasa mantawa da wanan daran ne?.

Murmushi mashkhur yayi tare da sake janyo zahra jikin sa suna feces cikin siririyar murya mai cike da shauqi yace ai bazan ta6a mantawa ba sabida ranar hmmmm kai dole ta shiga tarihin rayuwa ta, shi yasa nake ce miki kizo mu koma gidan mu mu tare, nasan kinji dad'i night d'in ranar to in muka tare zaki ringa jin dad'i fiye dana ranar ma ya qarasa maganar yana kashewa zahra ido.

Kai yaya mashkhur dad'i na da kai yanzu ka canza sai kai ta magagganun da basu dace ba, ni ka dena tinamin wanan daran nama manta mai ya faru ba wani dad'i fa. D'an zaro kyawawa idanuwan sa mashkhur yayi sanan yace da gaske kike, gyad'a kai zahra tai alamun ee. Tom shikenan bari na fara tina miki, da sauri zahra tace aaa bana so dan ALLAH ka bari bana buqata.

Ajiyar zuciya mashkhur ya sauke sanan yace to ki gayamin ko so kike yau mu kwana tare ne?. Girgiza kai zahra tai cikin siririyar murya tace aaa, haba farin ciki na bakya so ki kwana da mijin ki ki samu lada?. Cikin zuciyar zahra cewa tai tab a haka zan dawo gidan naka kana nuna mai tarka a fili? Mashkhur kuwa yaji abinda zahra tace sabida maganar ta futo fili tana cikin nazarin nan taji mashkhur yace sosai ma a haka zaki zauna ma harki haifa min 'yan 4.

Dan zaro ido zahra tai cikin mamaki tace mai kuma kaji nace, komai ma naji ya qarasa maganar yana jan kyakyawa kuma tun ta. Tom saki ni zan gaya ma ka tafi ni, oh kora ta ma kike, girgiza kai zahra tai sanan tace aaa, tom shikenan gaya min naji mashkhur ya qarasa maganar yana d'an rage tsayi tare da sai ta kunan sa dai-dai bakin zahra.

Lumshe ido zahra tai sanan ta ruqo wuyan mashkhur da d'an 'ya tsunta cikin siririyar murya tace my husband, ta qarasa maganar tana d'an cizan mashkhur agefan lallausan kunnan sa a hankula. Lumshe ido mashkhur yayi tare da d'an cizan le6an ido lumshe ya d'ago tare da cewa good my wife amma sai na rama. Kai mai zaka rama kuma?: zahra ta qarasa maganar tana zuba mai ido.

Had'e goshin su yayi waje guda a hankula yace cizo, amma ni a lips d'in ki ko a hmmm kin dai san inda zance ki za6a a ina zan rama?. Dan harar zahra ta watasa mai sanan tace a lips d'in dai sai ya fi. Murmushi mashkhur ya saki sanan ya kai bakin sa sai tin na zahra ya fara tsotsa a hankula. Lumshe ido zahra ta a zuciyar ta ta ayyana wanan karan bazata ta6a biyewa mashkhur ba.

Yana cikin shan bakin nata ya d'an ciji lips d'in zahra na qasa a hankula. Zahra kuwa hakan ba qaramin dad'i yayi mata ba amma da sauri ta janye bakin ta, tare da cewa ka rabu dani haka ya isa. Ido cike fall da sha'awar ta mashkhur yace my wife ya qarasa maganar yana kai hannu kan cikakun breast d'in ta. Da sauri zahra ta turo hanun sa sanan ta kama hanya toilet da sauri.

Tana qarasawa ta shige tare da cewa ka gai da mutan gidan kafin mashkhur ya kai da qarasowa tini zahra ta banko qofa ta sa key. Wata nanauyar a jiyar zuciya mashkhur ya sauke jiki a sanyaye ya juya ya fuce daga bedroom d'in zuciya cike da begyen zahra. Ko da zahra taji fitar mashkhur bata fito ba sabida tasan halin sa zai iya tsayawa a bakin qofa in ta fito ya dawo.

Bayan minti biyar da fitar mashkhur zahra taji qarar shigowa. Ana shigowa taji muryar ilham tana kwallara mata kira zahra! Zahra! Wata nanauyar a jiyar zuciya zahra ta sauke sanan ta bud'e key d'in ta fito daga toilet d'in. Tana fitowa ta cewa ilham ya tafi koh? Eee ya tafi mana amma dai hala ba wulaqanci da kika saba yi mai kika yi mai ba ko.

Zahra had'e rai tai tare da cewa shi nayi mai mana, kai zahra amma gaskiya bana jin dad'i abinda kikeyiwa yaya mashkhur sabida mai kike so ki hana ruwa gudu ne dan ALLAH ki amince da yaya mashkhur haka ya sha wahala ilham ta qarasa maganar idon ta tab cike da kwalla. To 'yar dad'i wa zahra ta qarasa maganar dariya tana tsinke mata.

Ilham kuwa cikin murya kuka tace au haka zakice zahra? Shiru zahra tai ba amsa, rai ba dad'i ilham ta fara qoqarin miqewa. Da sauri zahra ta janyo ta tare da cewa ke dallah baki son wasa ba im joking fa. Kallon zahra ilham tai sanan tace haba kina nufi ki amince?. Murmushi zahra tai tare da gyad'a kai, wani tsallan farin ciki ilham tai tare da rungume zahra tana cewa ina son ki 'yar uwa ta.

Murmushi zahra tai tare da cewa nima ina qaunar ilham, da sauri ilham ta saki zahra tare da cewa zahra naji jikin ki yana qamshin turaran yaya mashkhur ilham ta fad'a tana dan zaro ido cikin mamaki. Harara zahra ta gallawa ilham tare da cewa to meye damuwar mijina ne fa naga kina yimin kallon zargi, zahra ta qarasa maganar tana zaro idanuwa.

Ah zahra mai da wuqar kice yau an sake shan romance d'in da kyau ai mijin ki bazan hana ba. Murmushi zahra tai tare da cewa ya san ranki ke kin isa ma ki hana ni ta qarasa maganar tana miqewa domin shiga toilet. Maza a tafi ai wanka wama yasan iya mai kuka ai kata ai wanan lamarin sai da wanka tsarki zahra, murmushi zahra tai saki da cewa kamar kuwa kin san shi zance nai, dad'in ta dai ko mai muka aika ta da aure a tsakanin mu ba iskanci bane.

Sakin bakin ilham tai tana mamkin yaushe zahra tai qarfi a soyayar bata sani ba ko kunya dawo da magana bataji. Ilham tana cikin wanan tinanin nana ta shigo fuska ba walwala, rai ba dad'i nana ta qaraso kusa da zahra ta zauna tare da cewa aunty ilham ya ake ciki ta amince kuwa?. Murmushi ilham tai tare da cewa kwantar da hankalin ki nana ai yaya abdul ya zama naki halak malak, wata siririyar qara nana ta saki tare da rungume ilham tana cewa alhamdulilah.

KANO.

Night.

Mashkhur yaje gida lafiya qalau sumul kafin ya qarasa gida ya warware tass kamar ba mara lafiya ba, ranar dai ya saki jiki sosai ya koma kamar da, dan har abincin dare yaci shida 'yan uwan sa. Su ammi kuwa sunyi mamaki hakan sosai amma sai suka danne duk da suna so su san mai yasa mashkhur farin ciki haka shida ya fad'a cutar so.

Sai daga qarshe ammi ta samu lbr a wajan maman zahra akan mashkhur yazo har gida wajan zahra, kuma zahra ta amince. Ammi taso zahra bata amince da wuri haka ba amam ya zatai bazata iya shiga tsakanin miji da mata ba kuma daga ita har dadyn sun yi farin ciki da hakan. Kuma har sun fara tinanin tarewa zahra da mashkhur nan kusa. 6angaran mashkhur da zahra kuwa daran ranar sun sha soyayyah ta waya abin ba'a cewa komai har mashkhur ya fara sa zahra taji ta tsani zaman ko ina sai gidan sa.

ABDUL.

6angaran abdul kuwa yana nan zuciya cike fall da baqin cikin rabuwa da zahra qarfin hali kawai yake. Yauma kamar kullum da da daddare yana kwance ya rufe ido kamar mai bacci amma a zahirin gaskiya tinanin zahra kawai yake. Abdul yana cikin wanan halin yaji wayar shi ta fara ringing,.

Har ta gama ringing d'in abdul bai d'aga ba sabida tsabar baqain ciki rabuwa da zahra. Haka wayar tai ta ringing abdul bai d'aga ba a ringing na had'u ne ya miqe, sanan ya zubawa wayar ido. Wani dogwan tsaki abdul yaja saka makwan ganin wanan mayyar number ce take kira, a fusace ya d'auka ya kara a kunan sa cikin fad'a-fad'a yace kee dan ALLAH in bazaki iya yimin cikakyan bayani akan kiba kuma bazaki iya gaya min mai kike buqata ba karki sake kira na.

Cikin tattausar murya nana tace am sorry yaya abdul cool down pls, abdul ji yayi muryar kamar ta zahra, amma sai ya d'au hakan a matsayin gizau ne kawai, rai ba dad'i abdul ya danne zuciyar shi sabida shi baya son yawan fad'a. Cikin raunaniyar murya abdul yace ina jinki mai ke tafe da ke kuma taya kika san sunana?.

Ajiyar zuciya nana ta sauke tare da cewa ka dena wanan tunanin yaya abdul dole nasan sunan abindda nake so. Cikin mamaki abdul yace abinda kike so kuma ban gane ba. Eee yaya abdul wlh tinda na dora ido na akan ka naji ina son ka kuma ina qaunar ka zuciya ta ta nuna min kai mutum ne mai kirki da nagar ta shi yasa lokaci guda na kamu da son ka. Ina son ka tsakani da ALLAH yaya abdul.

Ni mace ce mai rauni tinda har na bud'e baki nace ina son ka ka tausaya min yaya abdul wlh ban ta6a sanin so ba sai aka aka ka. Kuma a matsayi na na mace mai kunya da rauni na cire wanan na fito na gaya ina qaunar. Cikin mamaki abdul yace wai wacece haka dan ALLAH?. Nana hafsat ce, jim yaya abdul yayi yana tianin a ina ya ta6a jin sunan. Im sorry nana hafsat ban gane ki ba fa, cikin dad'ar murya nana tace! nana fa qanwar ZAHRA.

Hmmmm kuna ganin abdul zai amince da soyayar nana ko kuwa dai?.

Mu had'e gobe a next page.

Ina muku fatan alkhair.


[23/04, 8:29 pm] Oum Farhan❀️🩷: ADALILINTA πŸ’œβ€πŸ’œ

BY AMINA BAYERO πŸ’œβ€πŸ’œ

*page 121*

Typing..........

Im sorry nana hafsat ban gane ki ba fa, cikin daddad'ar murya nana tace! nana fa qanwar ZAHRA.

Wata nanauyar ajiyar zuciya abdul ya sauke sanan yace nana mai kumatu hmm baki da dama wlh, dama ke kike ta turo message d'in nan hmmm kin iya wasa fa kwana biyu bakya zuwa yaushe zaki zo musha hira ne. Nana cikin mamaki ta kalli ilham da take zaune a kusa da ita, amma sai ta d'an sake dakewa tace aaa yaya abdul wai a wasa kake d'auka I'm very serious fa.

Wani qasaitaccan murmushi abdul ya saki tare da cewa ke dai kin cika wayo nana, wai yaushe zaki zo ne?. Hmmm yaya abdul kenan ai ko da yaushe kace nazo sai nazo ni da nake nema a wajan ka. Tom shikenan kizo yanzu ma ni kinji wai ke da kike nema a waje na nifa ba yaro bane ni zakiyiwa wayo koh?. Rai ba dad'i nana tace oh haka ma zakace tom shikenan ai, daga haka ta katse wayar.

Abdul kuwa dariya yayi sosai kamar bashi ya gama baqin ciki ba har ga ALLAH shi ya d'auka nana da wasa take, dan yasan ta cika surutu da wasa. Abdul sake kiran nana yayi amma sai yaji wayar a kashe, abin ya d'an bashi mamaki kad'an harma ya fara tinanin ko da gaske nana take can kuma wata zuciyar tace mai ba haka ba. Haka dai abdul ya kwanta zuciya cike da kokwan ton lamarin nana.

6angaran nana kuwa tana kashe wayar ta kalli ilham tare da cewa yanzu ilham duk kalaman da nai mai a wasa yake d'auka nana ta fad'i hakan kamar zatai kuka. Kar ki kuka nana da gaske yake miki fa wlh ya d'auka da wasa kike mai amma ni zan gaya mai da gaske kike. Girgiza kai nana tai tare da cewa ni dai aunty ilham inaga kawai zan haqura ne ta qarasa maganar tana zubar da hawaye.

Miqewa ilham tai tare da cewa ina zuwa bari na d'auko waya ta daga haka ta wuce bedroom. Ilham tana shiga ta dauki wayar ta tana ganin zahra ta nanad'e a bed tana shan soyayya ita da sahibin ta mashkhur sai kace ba yau suka shirya ba. Girgiza kai ilham tai sanan ta fuce daga d'akin tun kafin ta qarasa wajan nana ta dannawa yaya abdul kira.

Bayan ya d'auka sun gama gaisawa ilham cewa tai yaya abdul mai yasa kayiwa nana hakan nasan dai ba halin ka bane yaya na. Oh ilham ni sa'an wasan ki ne ko kema harda ke za'amin irin wanan wasan?. Haba yaya abdul kasan ina son ka bazan ma haka ba wlh da gaske nake duk abinda nana ta gayama hakane, amma da ta gayama sai ka d'auka a matsayin wasa, kuma al halin ba haka bane yanzu ma kuka takeyi.

Oh wayyo ni ai nayi tinanin kawai tana joke ne shi yasa ban d'au zancan serious ba. Aaa yaya abdul da gaske nana take fa tom shikenan jeki ki kai mata wayar, murmushi ilham tai tare da cewa tom shikenan. Daga haka ilham ta qarasa wajan nana da ta had'a kai sai shar6ar kuka take abin gwanin ban tausayi.

Dafata ilham tai tare da cewa nana, ido cike da hawaye nana ta d'ago. Murmushi ilham tai tare da miqawa nana wayar tana cewa gashi yaya abdul ne. Cikin murya kuka nana tace to ni aunty ilham mai zan ce mai nasan duk abinda zan gaya mai bazai yadda ba kawai a matsayin joking zai d'auka. Girgiza kai ilham tai tare da cewa ke dai ki kar6a, zai yadda mana.

Jiki a sanyaye nana ta kar6i wayar, ilham kuwa cewa tai to nana na shiga daga ciki in kin gama ki same ni a d'aki, daga haka ilham ta wuce tabar wajan. Cikin daddad'ar murya abdul yace hello, nana mai makwan ta amsa kukan ta tacigaba dayi zuciya cike fall da son yaya abdul d'in. Haba Nana ta mai kumatu kiyi haquri ki dena kukan nan haka kinji.

Cikin kuka nana tace dole nai kuka yaya abdul na nuna maka ina son ka amma ka watsamin qasa a ido koh kana d'auka wasa nake ma, ta qarasa maganar tana sakin wani saban kukan. Cikin daddad'ar murya abdul yace I'm sorry nana, kimin afuwa ALLAH na d'auka wasa kike min kin san bazan miki haka da ganga ba bazan so kyakyawar fuskar nan taki da wanan kyakyawan kumatun naki su jiqe da ruwan hawaye ba duk ta dalilina.

Kiyi haquri kinji nana dan ALLAH ki dena kukan nan, bai dace kyakyawa irin ki ta ringa zubar da hawaye akan qaramin abu ba. Oh gani kake son da nake maka qarami ne koh? Nana ta qarasa maganar tana sakin wanu saban kukan, kai wanan ma tafi zahra rigima abdul ya fad'a a zuciyar shi yana sakin murmushi, amma a fili cewa yayi oh nifa ba haka nake nufi ba nana ya haquri ki dena kuka.

Bana so ki ringa kukan nan fa, haka dai abdul yayi ta rarrashin nana cikin daddad'an kala mai masu sanyaya zuciya har ta dena kukan. Bayan tayi shiru ajiyar zuciya abdul yayi tare da cewa yauwa nana ko kefa. Cikin dashashiyar murya nana tace to shikenan yanzu zaka so ni kuwa, duk da nasan dai ban kai nan ba. Lumshe ido abdul yayi ya bud'e tare da cewa ko dai ban kai ki so ni ba.

Ai nana duk inda ake buqatar mace mai nutsuwa da tarbiya ga ilima da iya zama da mutum kin kai har kin wuce duk wani Quality's d'in da ake buqata aso mace kina da shi nana, inma ba yarinta irin taki ba ai ni kin san bamu dace ba kinma fi qarfi na nesa ba kusa ba. Wani saban kukan nana ta saki tare da cewa kawai dai kace baka so na basai ka biyo min ta nan ba.

Taya zakace nafi qarfin ka kana kyakyawa da kai fari tass ga mutunci ni kuma fa baqace, ya zakace nafi qarfin ka kawai yaya abdul kar ka wahalar dani in baka sona ka gayamin, na haqura na qare rayuwa ta ba aure cikin baqin ciki. No nana ki dena cewa haka pls kiyi shiru ki saurare ni. Nana wlh da gaske nake miki kina da kyau. Kuma farar fata ai batafi baqa kyau ba impact ma ni baqar fata tafi birge ni sabida tafi farar fata kyau kawai mutane ne basu gane hakan ba.

Aaa yaya abdul ni yanzu duk ba wanan ba ka amince da soyayyah ta nima zaka so ni ko kuwa?. Ajiyar zuciya abdul yayi, sanan yayi jim na wani lokacin kafin yace tom shikenan nana na amince da soyayar ki kuma ina godiya da tarin farin ciki da soyayar ki a gare ni. Wani siririn iwun dad'i nana ta saki tare da cewa kaii da really yaya abdul.

Ee mana da gaske nake miki nana, wayyo yaya abdul naji dad'i hakan, wlh dama nasan bazaka qi amincewa da soyayyah ta ba sabi da kana da mutunci kana da kirki ga sanin ya kamata. Haka dai nana tai ta surutai abdul yana jin ta yana sakin murmushi dan shi har ga ALLAH ma nishad'i nana take bashi.

Amma abdul kawai yace ya amince ne bawai dan yana son nana ba aa kawai dai sabida yasan in yaqi nana yayi mata tsantsar wulaqanci, tinda ita a matsayin ta na mace tace tana son sa, tabbas yasan son gaskiya ne tunda har ta cire kunya. Kuma ba laifi nana tana birge abdul sosai, musman fatar ta da kumatun nan nata kai komai nata ma yana burge abdul.

Nana da abdul sun sha hira sosai dan har sai da airtime d'in ilham ya qare, yaya abdul ya sake bugowa. Can dai yaya abdul yace nana ki je ki bacci haka dare yayi, murmushi nana tai tare da cewa kai yaya abdul yaufa bazan iya bacci ba, cikin mamaki abdul yace sabida mai?, hmmm sabida wanda nake so ya amince da soyayyah ta mana.

Murmushi abdul yayi tare da cewa hmm nima dai bazan iya yin bacci ba sabida kyakyawa kamar nana tace tana so na. Dariya nana tai tare da cewa banda zaulaya fa yaya abdul, hmmm nana baki da dama, nana mai kuka. Murmushi tai tare da cewa to ai kai ka sani kukan, to ai na baki haquri kiyi haquri kinji.

Murmushi nana tai tare da cewa na haqura ai, okay yanzu dai kije ki bacci sai da safe. Okay by good night and sweet dreams take care. Take care too my nana ki kula da kumatun nan naki sosai, murmushi nana tai tare da cewa tom shikenan zan kula dasu by. Daga haka nana ta miqe tare da kashe wayar zuciyar ta fasss, dan tasan

Please Login or Register in order to submit comment