Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yaqi goge mai a kwakwalwa sa dawo mai yake tiryan-tiryan.

Nan da nan mashkhur yaji feeling d'in zahra ya kama shi ko ta ina ji yake inama ya ya rufe ido ya bud'e ya jita a kusa da shi ko dan su sake aikata abinda ya faru daran su a Russian ko ya samu ya samu nutsuwa da kwanciyar hankali. Mashkhur yana jikin tunanin nan yaji wayar shi ta fara ringing, da kyar mashkhur ya iya janyo wayar sanan ya zuba mata kyawawan idanuwan sa.

Sunan ahmad ya gani a kan screen d'in wayar, a kasalance mashkhur ya sa dogwan d'an yatasn sa ya d'aga wayar sanan yayi shiru abinsa. Ahmad kuwa gyaran murya yayi tare da cewa hmm surikina kuma abokina kace yau miskilancin ne ya mutsa, ba magana. A jiyar zuciya mashkhur yayi tare da cewa, ahmad yau kwata-kwata banajin dad'in garin ne.

Hmmmmm mashkhur dama ina zakaji dad'i abdul bashi da lafiya. Cikin mamaki mashkhur yace what abdul kuma dama har yanzu bai samu sauqi ba. Shima ahmad cikin mamaki yace kai au wai kai a tunanin ka ya samu sauqi kenan?. Mashkhur cewa yayi hmm wlh ahmad rabo na da shi tun sanda nai tafiya, kuma na buga mai wayar tashi a kashe.

Lalai mashkhur ai yanzu jikin abdul yayi worst sosai dan ko magana ba iya yi, jiya da na kai qanena gaisuwa sai da na tausayawa badul duk ya bi ya rame bama ya iyacgane kowa, yana tari jini yana fitowa ta bakin sa. Cikin tashin hankali mashkhur yace innalillahi'wa'inna'ilaihirraji'un, ahmad ai ni duk ban san wanan ba da tini na dawo ba wanda ya gaya min.
Amma ba'a kai shi asibiti bane? Mashkhur ya tambayi ahmad cikin rud'ani.

hmmm kai dai bari mashkhur wai an kai shi amma likitoci basu gano mai yake damunsa ba, ko sunyi gwaji basa ganin ko wace cuta, dan yanzu ma dady yace min wai nan da 3 days za'a futar da shi waje. Cikin 6acin rai mashkhur yace nan da qarfe uku zuwa hud'u zan dawo kano yanzu zan sai ticket kazo ka d'auke ni ganinan dawowa. Daga haka mashkhur ya qimtse wayar rai ba dad'i.

Mashkhur hankalinsa ya tashi sosai ga baqin cikin ba'a gaya mai jikin abdul yayi worst ba. Mashkhur ba 6ata lokaci ya fara had'a kayansa dama yau ji yake n bai ga zahra ba wani abun zai iyasa samun sa. Bayan mashkhur ya gama had'a kayan sa online ya hau ya sai ticket yaci sa'a nan da qarfe 3 jirgi zai tashi daga abuja zuwa kano.
Dan haka ba 6ata lokaci ya sai ticket, sanan ya shirya tsaf ya bar hotel d'in domin zuwa airport.........

KANO.

Gaba d'aya mutan gidan suna zaune a babban falon ammi, sabida kowa yana jiran zuwan saratu momy ta addabawa kowa akan sai ya zauna, harma da dady tace shima ya zauna sabida har da mijinta zata zo. Abdul dai yana tsakiya abinsa, sai bacci yake yana sauke nun fashi da kyar zahra kuwa ta rafka tagumi a gefan sa ta zuba mai ido ko qaftawa batayo sosai, wai sabida karta qifta yaya abdul ya mutu.

Ana cikin hakan akaji sallamar mashkhur, ya shigo riqe da trolley a hannu. Shi kuma ahmad yana can a cikin mota yana waya da maman shi akan zatazo yau, in tazo zataje gidan su ilham taga surukar ta sanan tai mata gaisuwar mutuwa. Mashkhur yana shigo bai kula kowa ba ya ajiye trolley, a gefe sanan ya nufi inda abdul yake.

Yana zuwa ya zauna shima a d'ayan gefan abdul kamar yadda zahra ta zauna ya fara shafa kan abdul cike da tausayawa da kulawa da qauna. Sosai mashkhur ya tsorata da ganin halin da abdul yake ciki. Dady da ammi kuwa zuba mai ido sukayi basuce mai komai ba dan ganin yadda ya shigo ya share su kuma gashi ya wani had'e rai alamun yayi fushi, suma qanan nasa da suka ga mood d'in da yake basuyi mai magana ba sabida sun san bayasan magana in yana cikin 6acin rai.

A hankula mashkhur ya saci kallan zahra sau d'aya sanna ya d'auke idan sa. Nan da nan yaji zuciyar shi ta d'an yi mai sanyi. Cikin raunaniyar murya yace dady ammi momy hjy kaka ina wunin ku da fatan na same ku lafiya. Haka kowa ya amsawa mashkhur, sai a lokacin su ilham suka samu damar gaisar da yaya mashkhur yana wani amsawa da kyar.

Ita kuwa zahra ko kallo mashkhur bai ishe ta ba barema ta gai da shi. Momy ce ta ce mashkhur dawowa ba sanarwa?, da kyar mashkhur yace ba dole na dawo ba ashe haka jikin abdul yayi tsanani sosai ba a gayamin ba, yanzu in da qarar kwana sai da a kirani naga gawarsa kenan. Mashkhur yana kai nan ko gama rufe bakin sa bai yi ba abdul ya sarqafe da wani mugun tari.

Nan da nan falo ya sake kid'i mewa kafin kace kwabo an kewayar abdul. Wani irin tari yake mai ban tausayi ga jini yana futowa ta hancin sa da baki. Nan da nan waje ya karad'e da salati, zahra kuwa tuni ta fashe da gigitanccan kuka tare da qanqame yaya abdul ta hana kowa ya ta6a shi sabida tsabar qarfin hali da tashin hankali.

Uhmmm zo kaga tashin hankali a wajan mashkhur da yake shine bai saba ganin abdul a makamancin halin nan ba. Kai abdul dai abun tausayi tun yana iya tarin harma ya kasa da kyar yake, dan kowa yana ganin sa zai sheda abdul yana kan gangara. Zahra kuwa kifa kanta tai akan cikin yaya abdul tana ta raf sa uban iwu hajiya kaka kuwa sallaya da hijab ta d'auka ta kalli gabas daga gefe ta fara sallah.

Ammi kuwa tuni ta koma gefe ta fara kuka harda hawaye ko ta ina, abin tausayi sabida harga ALLAH tanajin abdul a zuciyar ta kamar ita ta haife shi ji take kamar ta cire mai cutar ta mayar jikin ta. Momy ma Hankali ya sake tashi ji take kamar ta bugawa saratu taji suna ina ne?. Ai kuwa momy tana gama tunanin nan ta tsinkayi sallamar saratu a qofar falon.................

Hmmmm kuna ganin abdul zai rayu kuwa?.

Momy zata tona asirin ko kuwa?.

Ku biyoni a next page dan jin amsar tambayar nan karku bari a baku labarin next page.

AMNAH: ADALILINTA💜❤💜

BY AMINA BAYERO💜❤💜

Typing..............

Page 104*

Momy ma Hankali ya sake tashi ji take kamar ta bugawa saratu taji suna ina ne?. Ai kuwa momy tana gama tunanin nan ta tsinkayi sallamar saratu a qofar falon.................

Gaba d'aya kowa d'aga kai yayi dan ganin mai shigowa, banda zahra da abdul, sabida ita zahra ma kanta yana kife a akan cikin abdul. Momy ce ta mike fuska sake tace sanin ki da zuwa ina AISHA take?. Itama saratu fuska sake tace wlh tana waje ta had'u da dan ta ahmad ne shi yasa suka tsaya suna magana. Shi kuma mijin nawa yana daga waje yana jira ai mai iso.

Murmushi momy tai sannan tace lah ai dama ya shigo ba komai, kije ki cemai ya shigo ai ga dadyn abdul d'in ma tin dazu yake jiran zuwan sa. Saratu waya ta d'auka sanan ta bigawa mijin ta tace su shigo. Duk wajan ba wanda ya gane wana ahmad ake nufi sabida bama susan ahmad yana gidan ba mashkhur ne kawai ya tafi dogwan nazari.

Saratu bayan sun gaisa da dady da ammi wajan abdul ta wuce cikin tausayawa tace wai yaya halima ashe haka jikin abdul d'in yayi tsanani, wlh nasha cutar bata ka haka ba. Momy cewa tai hmm ke dai bari kawai ai jikin abdul abun ba'a cewa komai dan ni har na fara cire rai da shi. Momy tana fad'in haka zahra ta sake sakin wani gigitaccan kuka mai cin rai,.

Kafin ma saratu ta kai da magana sukaji sallama. Nan da nan kowa ya sake d'aga ido domin ganin mai sallam. Kishiyar saratu ce aisha sanyi da niqab a fuskar ta sai ahmad da yake gefan ta sai wani manne mata yake ya riqe hanunta sosai. Daga haka sai mijin saratu ya biyu bayan su. Kowa mamaki ya kama shi sosai da sosai musamman mashkhur da ilham suna tunanin mai ya had'a ahmad da kishiyar saratu?.

Suna qarasa shigowa ahmad ya saki hanun matar fuska sake ya tsugauna ya gai da su momy da ammi, harma da dady sanan ya koma kusa da mashkhur ya zauna. Itama kishiyar saratun tana shigowa suka fara gaisawa da su ammi bayan sun gama gaisawa ta samu waje ta zauna. Shima dady fuskar shi sake ya tasu ya tari mijin saratu bayan sun gama gai sawa suka samu waje suka zauna akan kujera d'aya.

Nan da nan suma yaran gidan suka fara gaisar da baqi. Ammi ce tace zahra bazaki tashi ki gai da baqin ba kin zauna kina ta kuka. Zahra da take kifa akan cikin abdul ko motsi batai ba barema asa ran zata miqe. Muryar mijin saratu ce ta karad'e wajan da cewa, ashe haka lamari ya faru Allah yayiwa rukkayya rasuwa tom ALLAH ya jiqan ta Allah ya yimata rahra yasa ta wuta.

Nan da nan waje ya qarad'e da ameen. bayan mijin saratu ya gama yiwa rukkayya addu'a. Sanan ya dawo kan abdul tare da jajan ta musu, bayan ya gana yiwa abdul addu'a da jajanta wa su dady da momy sai ya d'ora da cewa! Hmm ashe abun 'yar gida za'a yi maj, d'a na ahmad nan ya kawo kud'in aure lokacin ina umara shi yasa ban samu damar zuwa ba.

Nan da nan mamaki ya sake kama mutanan wajan gaba d'aya jin mijin saratu ya kira ahmad da d'an sa. Mijin saratu kuwa cigaba da magana yayi da cewa! Maman shi tana ta complain akan sai tazo wajan surukar ta, yauma tana ta cewa in munzo nan zata biya taga surukarta tai musu gaisuwa ashe ashe nan ne gidan su surukar tamu.

Kishi saratu kuwa da ta qurawa abdul ido tana kallo kamar mayya cewa tai aikuwa dai wai ina surukar tawa take ma, ta qarasa maganar tana kallan ahmad fuska sake. Murmushi ahmad yayi yana qoqarin magana yaji dady yace ALLAH sarki ashe ahmad ma d'an gida ne kai ai gaskiya ahmad mutumin kirki ne, ai abokin yayan ilham d'in ne, cikin ikwan ALLAH suna ta amince sun shaqu ashe da sanarya abun.

Nan da nan mamaki ya sake kashe mutanan wajan, suna ta mamki taya hakan ta kasance su basu ta6a sani ba. Muryar hajiya kaka ce da ta idar da sallah ta kare falon, nan da nan kowa ya mayar da kallan sa wajan ta. Haba mai sunana ki rabu da abdul haka nan shima kansa nasan har cikin zuciyar shi baya jin dad'i kukan nan da kike da yana da lafiya bazai bari ki zubar da hawayan nan ba.

Yanzu mai ne!!!! Ai hajiya kaka tana kai nan, akaga kishiyar saratu ta taso a guje ta nufo hajiya kaka cikin tashin hankali take cewa kece wlh ina AMANA TA take ina amana ta take kar ki cemin bake ce ba, ta qarasa maganar tana ruqo hajiya kaka da qarjin gaske. Nan da nan waje ya sake rud'ewa da mamiki. Ahmad kuwa da sauri ya taso ya nufo maman tasa yan cewa!

Mama mene haka? Ki sake ta mana baki san ta ba haba mama dan ALLAH ki rabu da hajiya kaka. Maman ahmad kuwa cewa tai wlh itace ahmad itace kace ta bani amana ta wlh kece ina amana ta take. Daga haka maman abdul ta yanke jiki ta fad'i qasa sumamiya. Nan da nan waje ya sake ruked'ewa da salati, cikin mamaki mutanan wajan suke tambayar hajiya kaka mai ya had'a ta da maman ahmad.

Zahra kuwa hayaniyar da ake ne ta dawo da ita cikin hayyacin ta ita ta d'auka ma yaya abdul ne ya mutu tana d'agowa taga yana nunfashi ta saki ajiyar zuciya sanan ta juya tana kallan dandazon mutan gida harma da wasu baqi, ga wata mata sun kewaye ta a tsakiya tana sanye da hijab da niqab, tanayi rashe rashe a qasa alamun suma tai. Mashkhur yana gefan zahra a zaune mamki ya sake rufe shi.

Da sauri ammi ta d'auko ruwa mai sanyi ta watsawa maman ahmad, nan da nan matar ta farfad'o tana farfad'owa tace ALLAH yasa ba mafarki nake ba. Tana bud'e ido ta ta miqe da sauri ta sake riqo hajiya kaka tana cewa amana ta amana ta amana ta ina amana ta dan ALLAH ki gayamin gaskiya ina kika kai min amana ta?. Cikin zafin nama mijin sarstu ya riqo maman ahmad yana cewa ke aisha wai baki da hankali ne ki saki baiwar ALLAH nan ta wuta ina kika san ta ne?.

Hajiya kaka kuwa cewa tai hankali ta rass yake ki kwantar da hankalin ki amanar ki tana nan. Nan da nan waje ya sake ruked'ewa da salati. Cikin mamaki dady yace hajiya mai ya had'a ki da itane ita da ko fuskar ta baki gani ba zaki ce wai amanar ta tana nan wace amana ta baki mu kun samu a cikin duwo fa. Hajiya kaka kuwa cewa tai ni nasan mace d'aya ce ta bani amana a duniya.

Ko banga fuskar ta ba zan sheda ta, cikin mamaki ammi tace hajiya amanar mai ta baki?. Hajiya kuwa Kallan matar tai sanan tace amanar 'YAR TA ta bani. Cikin mamaki dady yace 'yar kuma hajiya, kwarai kuwa ciremin niqab d'in fuskar ki dan na tabbata ke ce ko kuwa hajiya kaka ta fad'a tana zubawa matar ido. Matar da sauri ta towa wajan hajiya kaka ta cire niqab d'in cikin kuka tace wlh nice hajiya.

Nan da nan mutan wajen suka zubawa matar ido, kafin su gama tantace kamar ta hajiya kaka tace tabbas kece abubakar wanan itace haifiyar ZAHRA. nan da nan waje yayi tsit kowa ya zubawa matar ido. Ai kuwa yadda kasan mayar tayi kaki ta ajiye zahra kai komai iri d'aya na zahra, ba abinda ya banbanta matar nan da zahra. Cikin kuka matar tace alhamdulilah in 'yar ta take?.

Hajiya kaka nuna mata inda abdul yake a kwance tai wadda zahra tana zaune tana ta zazzaro idanuwa dan ita yanzu kallan zautaciya takewa kanta gani take kwakwalwar tace ta samu tasala shiyasa take ganin wanan abubuwan. Matar a guje ta nufo zahra cikin farin ciki da kuka mai cin rai. Zahra kuwa tashi tai ta kwasa a guje ta koma wajan ammi ta qanqame ta tana cewa wayyo ammi shikenan na haukace wata aljana nake gani mai kama dani dan ALLAH karki bari ta ta6a ni.

Tabbb ai kaf wajan nan ba wanda yake iya cewa komai sabida tsantsar mamaki kowa ya daskare a zaune dan bama iya zahra ce take ganin kwakwalwarta ta samu matsala ba har da wasu daga cikin falon wasu kuwa gani suke mafarki kawai suke. Matar kuwa cikin kuka ta fiyo zahra tana cewa wlh nice mahaifiyar ki ni na haife ki da kai na.

Tana qarasa magar ta rungume zahra wadda take qanqame da ammi. Mijin saratu kuwa cewa yayi alhamdulilah ALLAH na godema ka bayyana min 'ya ta wadda na dad'e da cire rai da ita. Dady kuwa cewa yayi masha ALLAH abun al hajabi baya qarewa a duniya yanzu dai mu samu waje mu zauna sai ai komai a zaune. Maman zahra kuwa sai riqo zahra take tanayi mata magiya kan tazo wajan ta itace maman ta.

Baban zahra kuwa cewa yayi haba aisha ki rabu da ita mana haka? Yanzu ta tsora ta sosai ki bari ta dawo hayyacin ta tinda ALLAH ya bayyana mana ita ai an gama mai wahalar. Mahaifiyar zahra kuwa durqushewa tai qasa ta saki wani saban kukan ahmad kuwa ruqo ta yayi yana ta rarrashin ta haka ta dena kuka.

6angaran momy da saratu kuwa hankalin su in yayi dubu ya tashi musamman saratu ga wani mamaki da ya sake rufe su kota ina. Kamar yadda dady ya fad'a haka kowa ya zauna zuciya cike da zullumi da mamaki. Ammi kuwa cewa tai haba zahra mene haka kuma ki tafi wajan mamaki mana ki dena gudan ta. Zahra kuwa sai kuka take tana cewa wlh ba mamanta bace aljana ce.

Ahmad da kyar ya rarrashi maman zahra ta dena kuka sanan suka dawo tsakiyar falo suka zauna. Itama ammi zama tai zahra duk tafi ta riqe ta kamar zata koma ciki. Haka kowa ya zauna jiki a sali6e ba kwari kowa da abinda yake saqawa a ransa. Dady yana qoqarin yin magana abdul ya qara sakin wani mugun tari wanda yafi na kullum.

A guje zahra ta saki ammi kamar wata mahaukaciya ta qarasa wajan yaya abdul ta riqe shi gama. Kai abdul dai abin tausayi ko iyayan zahra sai da suka tausaya mai, momy cikin kuka tace dan ALLAH ku bani hankali ku nan ina da magana, ammi cikin kuka tace haba halima baki ga halin da abdul yake ciki ba ki bari jikin sa ya lafa sai ki fad'i abinda kike so ki fad'a.

Momy cikin kausashiyar murya tace abinda zan fad'a ya shafi samun lafiyar abdul ki bari na fad'a abinda yake rai na ko wanan wahalar da abdul yake ciki ta ragu. Kowa yana jin haka ya zubawa momy ido musamman mutan gida. Dady kuwa cewa yayi halima mai kike jira kuwa in dai kinsa abinda zai sa abdul ya samu lafiya ki fad'a mana ko menene, ni zan samo da kai na.

Momy sahare kukan ta tai sanan ta kalli saratu tace saratu sai dai kiyi haquri ranar wanka ba'a 6oyan cibi bazan ta6a bari abdul ya rasa ran sa kan asirin mu ya rufu ba. Nan da nan sartu ta fara zaro ido tana qifcewa momy ido, mamaki kuwa ya sake kama mutan wajan akan wanda suke ciki.

Momy kuwa gyara zama tai sanan ta fara bayani kamar haka!. Da farko dai dadyn abdul ina son sanar da kai aure na da kai ba yin kan ka bane ni ce nan ni da mahifiyata mukayima asiri kaji duk duniya ba wandda kake so sama dani har ka aure ni ka kawo ni cikin gidan ka. Nan da nan mamaki ya kama mutanan wajan, musamman ma dady.

Momy kuwa cigaba da magana tai kamar haka! Bayan na aure ka na cigaba da yima 'yan tsibbace-tsibbace na. Haka muka cigada zama har ALLAH ya azurta tani da haihuwar abdul. Bayan na haifi abdul an d'an kwana biyu shine ka gida da muka taso ka had'a ni da kishiya ta maryam harma da mahaifiyar ka hajiya. Tinda nasa qafa gidan muka fara rayuwa mashkhur ko kallo na baya son yi bare yayi min magana

Duk da yaro ne bazai gaza shekara uku ba amma na lura yana da tauri kai, dan sam baya so na. Ni kuma hakan ba qaramin 6ata min rai yake ba. Amma abun mamaki shine duk da mashkhur baya so na amma yana son d'ana abdul dan yawanci ina kai abdul wajan hajiya raino, amm in naje d'aukar abdul sai naga mashkhur yana son shi sosai har kuka yake wataran akan sai ya d'auke shi.

To daga haka dai na fara qoqarin ci gaba da karatu, amma dadyn abdul ya nunamin baya so. A lokacin na tayar mai da hankali sosai da sosai akan sai naje karatu, daga qarshe dai ya zuba min ido ya barni. A lokacin abdul yana qarami sosai dan ko cikayyan wata biyar bai ba amma tin daga haka na ajiye shi a wajan hajiya na fara zuwa makaranta karatu sai da a ringa ba shi madara............

ADALILINTA💜❤💜

BY AMINA BAYERO💜❤💜

Double page...............

Kullum wajan hajiya nake kai shi amma in na dawo sai na gan shi a wajan kishiya ta maryam. Tun hakan yana damuna har ya dena damuwa, dan sai nake ganin ma kamar ma raino take min, kuma na lura ita da d'an ta mashkhur suna san shi baza ta cutar min da shiba shi yasa hankalina ya kwanta kullum da kai na nake kawo shi wajan ta, sai dare nake qar6ar shi.

Kai wataran ma bana zuwa na kar6e shi acan yake kwana in yayi bacci. Ni kuma duk a lokacin bana damuwa sabida a ganina 'yar rai no na mayar da ita ina can ina karatu na ita kuma tana gida tana min rainon d'a. kai har ta kai ta kawo wataran sai nai sati ban sa abdul a idona ba. To bayan shekara 2 na gama karatuna lokacin abdul yayi wayo kuma ya bud'e idon sa da maryam.

A lokacin ni kuma na zo d'aukan abdul sabida nagama karatu amma qiri-qiri abdul yaqi sam yaqi yadda dani kuka yake sosai in nace zan d'auke shi kai ko d'aukar shi ma baya bari ni. A lokacin dadyn sa yace kawai na barshi anan tinda sun saba da maryam d'in in ya qara wayo zai dawo da kansa, lokacin naji ba dad'i sosai. Gani nake ita d'an ta mashkhur ko kallo na bayayi bare yayimin magana, amma ni gashi d'ana ya maqale mata.

Naji haushin hakan sosai ina ganin ita ta had'a 'ya'ya biyu gashi ni bani da ko d'aya ni da d'ana amma yana gudu na. Hakan ne yasa nayi waya da mahaifiyar ta da saratu na sanar musu, kuma basuyi qasa a guiwa ba suka ce zasuje wajan boka ya bani magani in nai wa abdul zai rabu da maryam gaba d'aya ya dawo waje na ko kallanta bazai sake yi ba. Daga haka momy tai shiru ta share hawaye da bakin zanin ta.

Falon yayi stit kowa yana sauraran momy, kai har abdul da baya cikin hayyacin sa yana iya jiyo abin da momy take cewa da yake wajan yayi stit.Tom momy kuwa cigaba da magana tai da cewa a lokacin na tambayi dadyn andul ya barni naje kaduna sabida yaqi. Ni dama burina in ya barni naje gida domin kar6o maganin da saratu da haifiya ta suka kar6o min wajan boka.

Hakan ne yasa mahaifiya ta da saratu suka je wajan boka suka qar6o min maganin farraqa maryam da abdul. Bayan sun qar6omin washe gari saratu tazo kawo min, tana cikin yimin bayanin yadda zanyi amfani maganin dadyn abdul ya shigo ashe yaji komai. Har saratu tana cewa anya maginin zai yi aiki ni kuma nace akayiwa ubansa ya ci bare wani abdul.

Muna cikin dariya dadyn abdul ya shigo rai 6ace yace saratu tabar mai gidan karta qara zuwa ni kuma ya mareni sanan ya sake ni saki d'aya. Daga haka na koma gida da zama najima sosai dadyn abdul bai zo biko, ina gab da gama takaba mahaifina ya zo ya samu hajiya yiyi ta bata haquri

Please Login or Register in order to submit comment