Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka yanke duk wata alaqa da take tsakanunku da ita, tinda yanzu kana da mata, duk abinda kake buqata daga wajan zee, zaka kasame shi a wajan matar ka. Da sauri mashkhur ya bud'e idanuwan sa tare da cewa, haba Ahmad kai ma kenan kana zargin ina wata ma'a mala wanda bata dace ba da zee? Ya qarasa maganar yana kafe Ahmad da idanuwansa.

Ehh mana mashkhur ina zargin da akwai wani abu da yake shiga tsakanin ka da zee wanda bai dace ba tunda gashi ka kasa rabuwa da ita. Cize le6e mashkhur yayi tare da girgiza kai yana cewa! To gaskiya Ahmad kana jahiltar kanka, dan tunda nake ban ta6a zina da zee ba, kai ko jikintama ban ta6a ta6awa ba bare ma wani abu mai qarfi ya shiga tsakanina da ita, kai bari kaji ni sam bata ta6a birgini ba barema naji ina sha'awar kasancewa da ita, dan haka Ahmad ka dena tinanin hakan.

Sosai mamaki ya bayyana akan fuskar Ahmad! Yanzu mashkhur kana nufu ba abinda ya ta6a shiga tsakanin ku da zee? D'aga kai mashkhur yayi tare da cewa! Kasan dai bazan yima qaryaba koh?, qwarai mashkhur nasan bazaka yimin qaryaba amma abin ya bani mamaki sosai. D'an zaro ido mashkhur yayi tare da cewa! To mai ya baka mamaki kuma?. Mashkhur ai dole nayi mamki, dan ni duk azatona kuna aikata abinda bai dace ba, amma mashkhur tinda kasan ba abinda ya ta6a shiga tsakanin mai zai hana ka rabu da ita.

Ajiyar zuciya mashkhur ya sauke tare da cewa! Hakane zan rabu da zee amma ba yanzu ba. Haba mashkhur kamarya ba yanzuba in baka rabu da ita yanzu ba sai yaushe kenan?. No Ahmad ka dai na tayar da hankalinka mana da gaske nake zan rabu da zee, nama fika san na rabu da ita. Da sauri Ahmad ya girgiza kai tare da cewa! Wlh mashkhur baka fini son ka rabu da yarinyar nan ba, dan daka fini so da tini ka rabu da ita. Murmushi yaqe mashkhur yayi tare da cewa Ahmad kenan, duk duniya ba wanda nafi tsana kamar wacca yarinyar da su dady suka auramin ita, kuma dady yace sai na rabu da zee na dai na shaye-shayen kuma sanan na futo da ruselt mai kyau a school, zai yarda na saketa.

Tom Ahmad in banyi hakan ba taya kake tunanin zan rabu da yarinyar can. Jinjina kai Ahmad yayi sam bai ji dad'in maganar mashkhur da yace ya tsani zahra fiye da komai ba, kuma har yana zancan zai saketa. Murya a sanyaye ahmad yace gaskiya kuwa mashkhur zakai ganganci arayuwarka idan ka rabu da ZAHRA. Ai nan da nan mashkhur ya had'e rai tare da cewa pls Ahmad it's okay mubar maganar nan haka, Ahmad kuwa cigaba da cewa yayi! No mashkhur a matsayin na abokin ka amininka kuma d'an uwanka dole na gayama gaskiya.

Zahra macace mai haquri ga ilmi ga tarbiya ga hankali da sanin ya kamata, kai duk wani abu da mace ta cancanta a sota a addinin muslinci zahra tana da su to mai zai sa ka rabu da ita kuma!!! Da sauri mashkhur ya katse Ahmad da cewa look Ahmad bakasan komai daya sahafi rayuwata da yarinyar nan ba, dan haka dan Allah ka rabu dani good night, daga haka mashkhur bai jira amsar Ahmad ba yayi wucewar shi bedroom d'in shi. Ahmad kuwa girgiza kai yayi tare da furta mashkhur kenan, ALLAH ya shiryeka yasa ka gane gaskiya, daga haka shima ya kama hanya yayi fucewarsa daga fallon ya wuce part d'in shi.

Mashkhur yana shiga bedroom d'in sa, ya kwanta akan bed zuciyar sa, na masa wani tiriri baqin ciki. Babban baqin ciki, mashkhur shine! Yana so ya saki zahra bayan sun koma gida amma gashi har yau ya kasa cika ko d'aya daga cikin sharad'an da dady ya yanka mai shi yanaso ko yayane ya fara rage shaye-shayen da yake amma sam ya kasa. Sam mashkhur ya rasa mai yake damunsa haka, gashi har yau mashkhur bai fara mayar da hankali a school ba, dan wataran ko yaje makaranta baya shiga ajin su, sam sai yaji baya buqatar shiga aji, wataran kuma yana iya daurewa ya shiga, amma ko ya shiga ajin hankalin sa baya kan karatun sai ya ringa wasu tinane-tinane na daban.
Ranar dai mashkhur ko baccin arziki bai iyaba sai da asuba ya kwanta.....

Washegari.............

Bayan zahra tayi sallar asuba ba ita ta tashi daga bacci ba sai qarfe bakwai na safe, zahra tana farkawa ta kalli agogwan bangwan bedroom d'in, da sauri zahra ta miqe ta shige toilet. Tana shiga ba 6ata lokaci tai wanka sannan ta futu d'aure da toilet, dreck bakin mudubi zahra ta nufa ta tsaya tana kallan kanta. Le6an nata ya sace gaba d'aya ba kunburi, amma yayi jajawaur kamar ta shafa jan baki. Sosai zahra take qarewa kanta kallo a mudubin ba laifi ta d'an wad'a ba kamar da datake cikin kwanciyar hankali ba, kana ganin zahra in dai ka santa farin sani a da, zakasan tana cikin damuwa.

Gefan fuskarta zahra ta shafa zuciya shike da kewar ammi, sam zahra bata ta6a tinanin nan kusa zata rabu da su ammi da sauran 'yan uwanta ba, ashe da datake rayuwa a cikin su ma rahma ne?. Lumshe ido zahra tai ta saki wani siriri murmushi saka makwan tinawa da tai da kakarta wato ajiya kaka, zahra tayi kewar hjy kaka sosai. Shafa kanta yayi wanda yake baje da gashi har kafad'a sam zahra ta gaji da zama a haka da gashin ta a tsefe, dan datana gida da tini ammi tayi mata kitso , dama zahra bata zuwa gidan kitso sai dai ammi tayi mata.

Ajiyar zuciya zahra tai ta juya ta nufi drowar Kayanta, tana bud'ewa a hanzarce ta kwaso uniform d'in ta sanan ta ajiye akan bed, sai da zahra ta shafa mai sanan ta fara shiryawa, bayan ta gama shiryawa tsaf dreck falo ta nufa, tana zuwa ta ajiye Jakarta akan kujera sanan ta wuce kicin. Tana shiga ba 6ata lokaci ta fara had'a confilask da madara, sabida yau ta makara shiyasa ma bata tsaya wani girki ba. Zahra tanaci tana tinani wai itace yau kullum ita take dafawa kanta abinci? Ita da ada sai dai ta futo taci watarana ma ko plate d'in bata d'aukewa sai dai a d'auko mata, amma sai gashi yanzu sai dai ta dafa, inma bata dafa ba bazata ciba.

Haka zahra ta tafi duniyar tinanini koh confilask d'in kirki bataci ba, sai juyashi take da cokali harma wanda ta zuba a cikin madarar ya fara narkewa tana can duniyar tinanin. Knowing d'in qofar da akeyi ne ya dawo da zahra daga tinanin data tafi, da sauri ta matsar da ma dai-dai cin tangarin d'in data had'a confilask d'in a ciki sanan ta fuce daga kicin d'in a hanzar ce. Tana fita fallon ta d'auki jakar ta dan ko ba'a fad'a mata ba tasan Ahmad ne yazo kai ta makaranta. Zahra tana murd'a qofar, tana ta bud'e alamun ma ba'a sa mata key ba a haka ta kwana.

Qarasa bud'ewa zahra tai, Ahmad ta gani tsaye a bakin qofar, murya a sanyaye zahra tace yaya ahmad ina kwana, ta qarasa fad'a tare da d'an durqusawa qasa. Lafiya qalau qanwata da fatan kin tashi lafiya? Gyada ka zahra tai tare da cewa lafiya qalau na tashi, okay zomu tafi school, dan kin kusan makara, ba musu zahra ta futo tare da janyo qofar. daga haka zahra da ahmad suka wuce mota, bayan sun shiga motar a hanzarce Ahmad ya tayar suka wuce school.

MASHKHUR...........

Tinda mashkhur ya kwanta bashi ya tashi ba sai qarfe shad'aya, na safe. Yana farkawa ya kalli agogwan bangwan bedroom d'in. Wani siriri tsaki baqin ciki mashkhur ya saki, saka makwan ganin ya makara sosai kenan yau bazai samu damar zuwa school ba?. Jiki ba kwari mashkhur ya miqe ya shiga toilet yayi wanka, tare da brush. Yana futowa ya zira kayan sa sanan ya biga waya yayi oder abinci da zai ci. Ba'a fi 30 mints ba oder mashkhur ta qaraso, zama yayi ya fara cin abincin zuciya cike da damuwa.

Mashkhur yana cikin cin abincin nan yaji wayar shi ta fara ringing, zubawa yawar idanu mashkhur yayi dan ganin waye? Sunan ZEE ne ya bayyana 6aro-6aro da manya baqi akan screen d'in wayar, kawar Da kansa yayi daga kan wayar ya cigaba da cin abincin sa, har wayar ta kaste mashkhur bai d'aga ba. Tana kastewa wani kiran ya sake shigowa, Stil zee ce take kiran, sai da kiran ya kusan tsinkewa sanan mashkhur ya d'aga, Yana d'agawa shiru yayi bai yi magana ba.

Can kuma 6angar zee tace!! Hello honey yau naga baka shigo school ba lafiya?. Shiru mashkhur yayi bai bawa zee amsa ba, hello honey kana jina? Murya a dace mashkhur yace ina lafiya, okay honey nima gaskiya bazan iya zama a makaranta ba, kai bakazo ba ganinan zuwa! Daga haka Zee ta kashe wayar, wani siriri tsaki mashkhur yaja tare da kawar da abinci da yake gabansa, sam baya son zuwan zee a halin yanzu sabida baya cikin mood mai dad'i. Rai ba dad'i mashkhur ya tashi ya shige bedroom d'in shi.

Ai kuwa ba'a fi 30 mints ba zee tai parking d'in motar ta a cikin gidan, tana parking ta futo a hanzarce sanan ta kama hanyar hawa step. Doguwar rigar ce a jikin blue wanda ta tsaya a iga guiwar ta, rigar mai siririn hannu ce. Sai takalminta shima blue, sai kuma wani glass mai tsada data sa, gashin nan nata yasha gyara sai gyalli yake ta d'aure shi a tsakiyar kai d'am. Sai wayarta i phone 13 wanda tasha park shima blue, Ba laifi tayi kyau sosai da yake kyakyawace ba laifi, tana qarasa hawa benan, ta fara knocking d'in qofar! Tafi 10 mintis tana kwankwasa qofar amma mashkhur bai zo ya bud'e mata ba.

Can kuma zee taji wayarta ta fara ringing da sauri ta kalli wayar dan ganin waye? Sunan my honey ne ya bayyana akan screen d'in wayar, a hazarce ta d'auka tare da cewa hello honey? Daga d'aya 6angara kuma ji tai mashkhur yana cewa qofar a bud'e take ki shigo, daga haka ya katse wayar. Zee kuwa a zuciyar ta sai taji ba dad'i kenan duk bugun da take mashkhur yana ji?, sam zee ta rasa gane mashkhur wana kalar mutumi ne haka ? Halaryarsa wani kala ga wani jan aji da yake mata, tana mace amma namiji yana ja mata aji haka, wani dogwan tsaki zee taja tare da bud'e qofar ta shige.

Tana shiga bata samu mashkhur a fallo ba dan haka direct ta nufi bedroom d'in shi, kwance ta ganshi akan bed yana kallo a laptop d'in shi. Sosai zee ta zubawa mashkhur ido tana kallansa, wani irin kyau taga yayi mata sai taji kamar taje ta rungume shi ta bayan sa, in yaso su cigaba da kallon tare, wata irin sha'awar shi ce lokaci guda ta rufeta. Wayarta ta ajiye akan table sanan ta cire takalminta ta hau kan bed d'in, har lokacin mashkhur bai d'aga ido ya kalli zee ba kamar ma bai san da zuwan taba.

Da zee taga shariyar tayi yawa a hankula ta fara matsawa kusa da mashkhur, takai gab da shikenan tana qoqarin ta6a guskar sa, mashkhur ya bige hanunta tare da watsa mata wani irin banza kallon. Nan da idon zee yaja ruwa kamar zatai kuwa tace wai honey sabida mai kake min haka ne? Ni yau bazan ta6a iya jurewa ba wlh, ta qarasa maganar tare da fashewa da kuka. Shiru mashkhur yayi bai ce komai ba, zee kuwa cigaba da cewa, tai wai honey sabida mai duk abinda nake bana birge kana ne?.

Honey nifa yau bazan iya jurewa ba pls ka bani dama ko sau d'aya ne wlh ji nake kamar zan mutu bakaji yarda nakejin fleeing d'in kaba a jikina, da sauri mashkhur ya d'ago tare da cewa wai zee me kike nufi ne, mai kike buqata ne?. Cikin muryar kuka zee tace SEX nakeso muyi yau-yau d'in nan, da sauri mashkhur ya zaro idanunshi tare da cewa SEX kuma Zee?, ehh mana honey, da sauri mashkhur ya girgiza kan shi tare da cewa! No zee bazan ta6a iya hakan ba, a gigice zahra ta d'ago tare da cewa sabida mai honey.

Zee addinina bai yarda da hakan ba, sam ba kyau haramun ne ka kusanci wata in dai matar kaba, idanuwa cike da hawa zee tace honey na sani mana amma ai babana ya cemin in kukayiwa ALLAH laifi zaku iya roqanshi ya yafe muku, to mai zai hana bayan munyi ka roqe shi ya yafema?. Girgiza kai mashkhur yayi tare da cewa ai ba haka abin yake ba zee, abinda dadyn ki yake nufi shine!! In mukayiwa ALLAH lefi a rashin sani ko kuma bayan munyi laifin sai mukayi nadama kuma mukasawa zuciyarmu bazamu qaraba har a bada, tom in muka qori ALLAH gafara zai iya yafe mana, shine abinda dadyn ki ya gaya miki baki gane ba.

Amma yanzu in nayi ai ina sane kenan nayi zina , kuma hukuncin zina a wajan ALLAH yana da tsauri sosai, kuma ALLAH bayasan mu aikata zina sabida babban lefi ne, kai zee nifa kwata-kwata bana sha'awar hakan ma, dan duk abin zai sa na sa6awa uban gijina ina qoqarin kuje mai. Zee tana gama jin bayanin mashkhur ta fashe da matsanan cin kuka tare da kifa kanta akan guiwar ta, mashkhur kuwa zuba mata ido yayi, yana kallan ikwan ALLAH. Can kuma yace haba zee ki dena kukan nan kinga dai ke maca ce, kuma aure zakiya, yanzu in mukazo mukayi sex dake in kikayi aure mai zaki cewa mijinki in ya gane ke ba budurwa bace kin ta6a ma'a mala da wani namijin na daban ba shi ba?.

Da sauri zee ta d'ago tare da cewa! No honey karka damu da wanan, nifa a halin yanzu ba budurwa bace, zaro ido mashkhur yayi dacewa what? Gyad'a kai zee tayi alamun ehh, mashkhur bai masan sanda yace tayaya?, zan gayama amma sai ka yarda inna gayama zaka amince da ni, shiru mashkhur yayi yana nazari da tinani, yana cikin tinanin nan yaji zee tace, dama ni tunda ina bin maza da dama, mamana tace bazatai min aure da wuri ba sai na gama karatu hakanne yasa na zama karauwa, bama iya maza kad'ai nake biba harda LESBIAN inayi...........

Koyi haquri jiya banyi muku posting ba, ban gama typing d'in da wuri ba shiyasa.


ADALILINTA 💜❤💜

BY AMINA BAYERO 💜❤💜

                               Typing................

    *page 63*

Mamaki ya kama mashkhur sosai,  sabida tinda yake bai ta6a tinanin zee karuwa bace kuma  'yar lesbian. Nan da nan kyakyamim zee ya cika mashkhur,  Sam mashkhur bazai ta6a iya saduwa da zee ba,  sabida shi mutumne mai kyakyami,  bazai ta6a iya kusantar macan da taje tayi ma'a mala da maza daban-daban ba kuma ga mata,  kai bama zee ba ko mace data ta6a saduwa da wani namijin ne sau d'aya sam mashkhur bazai iya ma'a mala da itaba,  shi mashkhur ma in zai sadu da wato,  to yafi san wanda bata taba ma'a mala da wani namijin ba kuma matarsa wanda yake tsananin so,  tom shine mashkhur yake ganin zai iya aikata hakan da ita.

Tinani mashkhur ya tafiyi taya zai sha'wo kan zee ta haqura da abinda takeso ta ai kata da shi? Wani siririn tsaki yaja, nan da nan yaji haushin zee ya cika shi, dama tinda ba amincewa yayi da qudirinta ba kawai dai yace mata taje zai yi shawara ne, dan ta rabu da shi ya huta, jiki a sanyaye mashkhur ya ja bargo ya lulu6e jikin sa, zuciya cike da kyamar zee...

ZAHRA.
Yauma Ahmad yazo da wuri d'aukar zahra daga school, zahra tana futowa daga school Ahmad ya d'auke ta suka kama hanyar gida. Suna cikin tafiya Yaya Ahmad ya kalli zahra yace qanwata, in ba damuwa inaso na tambaye ki?, tom shikenan yaya Ahmad inajin ka?, shiru ahamd yayi bai ce komai ba, zahra dataga shirun yayi yawa cewa tai! Yaya Ahmad inajinka fa, oh sorry qanwata dama inaso na tambaye ki ya sunan wanan qanwar jinki mashkhur?.

Nan da nan zahra ta had'e rai tare da cewa haba yaya Ahmad, ya zakace qanwar mijina, nima ai 'yar uwata ce, Au ya haquri qanwata! Dama abinda yasa nace qanwarsa! Kinga ai gidan su d'aya da shi kuma sai kin fi ganewa. Kwa6e fuska zahra tai tare da cewa hmm tom gaskiya ba haka zancan yake ba kuma nima ai 'yar gidan ce, tunfa ina jaririyata nake gidan to kaga nima ai 'yar uwata ce Ko so kake ka cireni daga cikin 'yan uwana? . Ohh sorry qanwata wlh bansani ba, murmushi Ahmad ya saki tare da cewa shikenan kinga fad'uwa tazo dai-dai da zama.

Kallansa zahra tai tare da ce yaya Ahmad ban gane abinda kake nufi ba, haba qanwata sai kace ba bahaushiya ba?, murmushi zahra tai tare da cewa eh ina yawan jin kalmar amma bansan mai take nufi ba shiyasa. Tom bari in miki gwari-gwari ina nufi komai zai zomin cikin sauqi, jinjina kai zahra tai tare da cewa tom wacce daga ciki kake nufi, husaina tawa ko ruma ko kuma aunty rukee?, Dan zaro ido Ahmad yayi tare da cewa ohh shema da yawan su, ni dai guda d'aya na sani ita nake nufi ikhram ko ilham take da suna? Ahmad Ya qarasa maganar cikin kokwanto.

Wata siririyar dariya zahra tai tare da cewa kace husaina ta kake nufi, ilham sunan ta. Husainar ki kuma taya akai ta zama husaina taki?, hmm yaya Ahmad kenan bakasan ya muke da ilham bane kawai dan tabbas nasan da ina Nigeria bana boka bana malam muna tare da ita ai ko bacci ma baya rabamu komai tare mukeyi da ita. Murmushi Ahmad yayi tare da cewa alhmdllah!! Wlh zahra najin dad'in hakan kinga komai zai zomin cikin sauqi, qanwata kin san mene? Girgiza kai zahra tai tare da aa yaya Ahmad sai ka fada'a ina jinka.

Kin tina ranarnan da nace miki wata rana zan gaya miki abinda yake damuna kinta ko qanwata ?. Da sauri zahra ta tace qarai yaya Ahmad na tina, yauwa qanwata, wlh ba komai ne yake damuna ba face SON ILHAM. Zaro ido zahra tai tare da dafa qirjinta tace ilham kuma yaya Ahmad? Kwarai qanwata wlh kullum da ita nake kwana nake tashi tun sanda na d'ora idona a kanta naji ina sonta, wlh kullum a cikin tinaninta nake ko baccin kirki bana iya yi, koma da nayi tinanin na samu mashkhur da zancan amma dai kinsan halin mashkhur da shariya ba lallai ne ya d'auki maganar serious ba.

Shiru zahra tai dan ita tama rasa mai zata ce, shi kuma Ahmad cigaba da cewa yayi! Ina fatan dai bata da wani saurayi koh? Wani siririn murmushi zahra ta saki tare da cewa aa gaskiya a iya sanina bata kula samari sabida ko zance dady baya barinta fita ma. Ajiyar zuciya Ahmad ya saki tare da cewa amma a ganinki zata so ni kuwa? Jim zahra tai na wasu daqiqu chan kuma tace gaskiya yaya Ahmad ban sani ba ko zata soka ko akasin haka tinda kaka yanzu bama tare da ita. Jinjina kai Ahmad yayi tare da cewa hakane qanwata, amma dai da fatan zaki tayani nema ko ya qarasa maganar ciki da zaulaya.

Gyad'a kai zahra tai tare da cewa mai zai hana yaya Ahmad in dai na had'u da ita zan taya ka. Tom qanwata kimin addu'a ALLAH yasa dady ya bani ita, tom shikenan yaya Ameen. Suna kawo qarshan nan Ahmad yana kusa hancin motar sa cikin gida, yana gama parking zahra ta bud'e murfin muta ta fuce, shima Ahmad d'in zare key d'in motar yayi tare da fucewa daga motar, zahra ta wuce hanyar bene, shi kuma Ahmad ya kama hanyar part d'in shi.

Zahra tana gama hawa kan step d'in benan, ta qarasa bakin qofar a han zarce, har zahra zata fara kwankwasawa sai tai tinanin qilama qofar a bud'e take, a hankula zahra tasa hannu ta murda Handel d'in qofar, ai kuwa cikin sa'a taga qofar ta bud'e, a hankula zahra ta qarasa tura qofar sanan ta shige ciki. Tana ba 6ata lokaci ta juya domin rufe qofar, muryar mashkhur taji yana cewa! Ki sawa qofar key, da sauri zahra ta juya bayan ta, a zaune akan sofa ta ganshi yana ta danna laptop d'in shi, kamar ma bashi yayi magar ba.

Juyawa zahra tai ta sawa qofar key, sanan ta juyo ta kama hanyar bedroom d'in ta, a zuciyarta tana cewa kai dai wlh ka fiya san laptop, akan laptop ma sai da ka kusan kasheni. Zahra tana gifta mashkhur taji yace! In kikaji ana bugu karki sake ki bud'e qofar?, sunkuyar da kai zahra tai tare da cewa in sha ALLAH zan kiyaye, muryar mashkhur zahra taji yana cewa karma ki kiyaye jikinki ne zai gaya miki, zahra bata sake cewa komai ba ta juya ta cigaba da tafiya, tana isa bedroom d'inta, ta shige.

Zahra tana shiga ta fara qoqarin cire uniform d'in ta tana gama cirewa ta saka wasu kayan nata, bayan ta gama sa kayan, toilet ta shiga ta d'auro alwala sanan ta futo tana futowa, ta shinfid'a dadduma ta fara gabatar da sallah, bayan zahra ta idar da sallah ta gama lazimin, cire hijab d'inta tayi sanan ta d'auko mayafi ta yafa. Yunwa zahra takeji sosai hakan ne yasa ta kama hanyar fita fallo, a hankula zahra take takawa har ta qarasa fallon.

Har lokacin mashkhur yana zaune akan sofa, amma sai dai yanzu ba laptop d'in yake dannawa ba ga dukkan alamu karatu yake ko dai wani abu makamancin hakan da yake littafine a hanunsa, kuma hankalinsa ya karkata akan littafin. Kamar mai sand'a haka zahra ta shige kicin d'in, ba 6ata lokaci ta fara dafa indomei, bayan ta gama ko kwai bata tsaya soyawa ba ta juyeta a plate sanan ta d'auki ruwa, ta fuce daga fallon, zahra tana futowa ruwan jarkar hanunta ya fad'i, da sauri ta tsuguna ta d'auka tana d'agowa ta kalli mashkhur.

Wata uwar harara taga yana watsa mata wanda sai da

Please Login or Register in order to submit comment