Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta tai duk da ba'a wanke take ba amma dai zahra gani take bazata iya zama haka ba, tinda ba ita kad'ai bace a d'akin. Bayan ta gama sa bre d'in audigar ta 6are ba manna a pants d'in sanan ta fara qoqarin sawa nanma zahra da kyar ta iya sawa tasha wuya sabida qafarta tayi mata tsami.

Sai da zahra ta gama sa pants d'in sanan ta fara neman rigar ta amma ina bata ganta ba, towel ta d'aura a qirjinta tana tinanin ko mashkhur ya fita da rigar ne ita dai kamar taga ya shigo da rigar amma bata ganta ba. Zahra tana cikin tinanin nan ta hango rigar ta akan sin, wani siririn tsaki taja a zuciyar ta tace kai to in badda abin yaya mashkhur taya zan iya d'aukar rigar nasa.

Zahra ta dad'e sosai tana nazarin nan can kuma ta yanke shawarar gwara ta dadafa ta d'auko rigar tasa ajikinta dan bazata ta6a yadda har sai mashkhur ya shigo ya d'auko mata ba, dan gaskiya ganin abin take ba tsari gaba d'aya kuma kunya zataji, dan tinda aka d'aura musu aure da ya mashkhur bata ta6a kallansa a matsayin miji ba kamar yadda shima bai ta6a kallanta a matsayin mata ba.

A hankula zahra ta fara rarafawa har ta qasa bakin sin d'in, sosai zahra ta zira hannu ta saman sen d'in dan ta ciro rigar ta amma ta qasa. Qara d'aure towel d'in zahra tai sosai a qirjin ta sanan ta kama sen d'in tana qoqarin miqewa. Zahra tana miqewa ta zaro rigarta ai kuwa batayi aune ba sai ji tai ta su6ale qasa suuuuu, ta fadi harta bige qeyar ta.

Ai zahra batasan sanda ta saki wata gigitacciyar qara ba.
6angaran mashkhur kuwa yana tifa daga toilet d'in ya rufo sanan ya nufi kan bed, da kyar mashkhur ya iya nad'e farin bed sheets d'in da zahra ta 6ata da jini. Yana cirewa ya fuce daga d'akin bayan ya fita yana zuwa falo ya fuce yana sauka daga kan benan ya cillar da bed sheet d'in a shara dan mashkhur gani yake bazai iya wanke bed sheet d'in ba.

Bayan ya jefar komawa yayi ya goge ledar katifar da ruwan sabulu yana gogewa katifar ta fushe da yake A. C a kunna take, bayan katifar ta bushe wani saban bed sheet d'in ya d'akko ya shinfi d'a sanan ya fara fesawa room d'in air freshener, mashkhur yana cikin fesa air freshener yaji zahra ta saki wata gigitacciyar qara a toilet, da sauri mashkhur ya yar da air parishioners hanunsa sanan ya nufi toilet a guje..........



Kai wanan jinyar zahra da mashkhur d'in tana bani cittah 😂

Kuma nasan zata baku ko?.

Kai mashkhur fa ya fara shiga taskwan wahalar jinyar zahra.

Wanan page d'in na ranar Friday ne, sai yau nasamu damar yi, sabida hallom da tamaryamu, sabi da su nai a bisa dole.😂

Sai ku gode musu.

To mu had'e a next page Monday...

Happy weekend.


ADALILINTA 💜❤💜

AMINA BAYERO 💜❤💜

Typing..........

*page 91*

mashkhur yana cikin fesa air freshener yaji zahra ta saki wata gigitacciyar qara a toilet, da sauri mashkhur ya yar da air parishioners hanunsa sanan ya nufi toilet a guje..........

A guje mashkhur ya qarasa bakin qofar toilet d'in, yana qarasawa ya murd'a Handel d'in qofar ya shige a gigice da yake har lokacin zahra bata dai na kurma uban iwu ba. Mashkhur yana shiga ya daskare tsaye a bakin qofar toilet d'in, sabida halin da ya isake zahra. Towel ne d'aure a qirjinta, Kwance take akan hanunta da ya lankwashe, ga santala-santalan cinyoyinta tubarakallah masha Allah sun bayyana a waje sakwan towel d'in yaye sosai sabida fad'uwar da tai.

Kanta kife yake a tayal d'in toilet d'in bakin ta da hancin ta sun d'an bashi dan har jini ya fito,. Sosai mashkhur ya zubawa, zahra ido ya kasa ko kwakwaran motsi yama rasa taya zai fara taimakwan ta, sabida ya d'an rud'e bai ta6a ganin mace a wanan yanayin ba sai zahra. Wani uban iwu zahra ta sake gwalawa tare da ambatar sunan shi da qarfi tace, wayyo yaya mashkhur kazo ka tai make ni hanuna ze 6alle.

Mashkhur yana jin hakan ya sake rud'ewa ya nufi zahra da sassafa yana qarasawa inda take ya tsuguna jikinsa sai rawa yake,. Jiki na rawa mashkhur ya kai hannu zai d'ago zahra, amma sam ya rasa taya zai fara ta6a jikinta, sai ya kai hannu zai ta6a ta sai kuma ya janye. Wata qara zahra ta sake kwalawa tare da cewa! Wayyo dady ammi hajiya zan mutu.

Mashkhur yana jin haka bai sai sanda ya kai hanunsa kan damtsan hanun zahra ba ya d'ago ta da sauri jikin sa na rawa.
Mashkhur yana d'ago zahra yaga bakinta ya fashe ga jini yana d'an zubowa ta hanci, nan da nan hankalin mashkhur ya sake tashi jiki na rawa ya kai hanunsa kan hanci zahra ya fara goge mata jinin.

Da sauri zahra ta d'an doke hanun mashkhur tare da ja da baya ta d'auki rigarta da take qasa ta fara rufe jikinta tana ja da baya. Jiki na rawa mashkhur ya d'an sake matsawa kusa da zahra da ta raku6e a bayan sin tana ta kuka. Sannu ki dena kuka mana kinji pls kiyi shiru haka.

Wata uwar harara zahra ta watsawa mashkhur cikin muryar kuka zahra tace baza'ayi shiru d'in ba, tun lokacin da nake neman tai mako bakazo ka tai make niba sai da hanuna ya kusan karyewa sanan kazo zakace na dena kuka, to bazan dai na ba d'in kuma yau-yau sai na gayawa dady yazo ya d'auke ni mu koma gida na gaji da zama da kai in ba haka ba kashe ni zakayi, zahra ta qarasa maganar tana sakin wani saban kukan.

Ga takai cin mashkhur ya ganta a wanan halin ga zafin ciwo da take ji.
Shiru mashkhur yayi dan shi yama rasa abin cewa! Amma sai dai haka mashkhur ya d'aure ya sake matsawa kusa da zahra tare da cewa! Wai ke ya kike so nayi da rayuwata ne?, kullum ina qoqarin faranta miki amma bakya gani duk kinbi kin addabi rayuwata haba, dallah rufe min baki banza raguwa kawai ya raqasa maganar yana zubawa zahra ido.

Zahra kuwa sake qanqame jikinta tai tare da cewa! Bazanyi shiru d'in ba kukama yanzu na fara ta qarasa maganar tare da sakin wani uban iwu.
Da sauri mashkhur ya sa hannu ya rufewa zahra baki tare da cewa! Haba wanan wana kalar rashin mutuncin ne. Da qarfi zahra ta fara qoqarin cire hanun mashkhur daga bakin ta,.

Mashkhur kuwa yana ganin haka ya sakar mata bakin tare da cewa! Wlh kika sake kika qara yimin qarar nan yanzu sai na miki mugun duka a toilet d'in nan shashasha kawai. Zahra kuwa taso ta sake sakin wani iwu, amma dai tana tsoran kar ya dake ta kuma gashi ko kaya babu a jikinta kunya zata ji.

Sake nanad'e jikinta zahra tai a fefan sin sanan ta kifa kanta a guiwowin ta, ta saki wani saban kuka mai cin rai da dashashiyar muryar ta. Mashkhur kuwa yana ganin hakan yaji jikinsa duk ya sake mutuwa, ga tausayin zahra ya rufe shi sosai, shima mashkhur d'in qifa kansa yayi a guiwar qafafuwan sa kamar mai kuka, dan shi sam baya san damuwa ko hayaniya da takura a rayuwar sa.

Zahra tana zaune a qudindine a bakin sin ta kifa kai tana kuka, shi kuma mashkhur yana tugune ya kifa kai ciki da damuwa.
kwakwalwar mashkhur ta cazu sosai, dan yama rasa mafita. Can da mashkhur yaji kukan zahra yayi yawa, d'agowa yayi sanan ya sa hannu ya d'ago kan zahra tare da cewa kiyi haquri kinji?.

Karo na farko kenan da mashkhur ya ta6a bawa zahra wani haquri a rayuwar ta ko itama lokacin da zahra taji yace tayi haquri sai da mamaki ya daskarar da ita a zaune dan bama tasan sanda ta dena kukan ba.
Hannu mashkhur yasa zai janyo zahra, da sauri zahra ta d'in turo hanun mashkhur d'in tare da cewa ni kawai ka rabu dani gwarama na mutu a haka na huta.

Sannu ki bari na mayar da ke bedroom mana ya qarasa maganar kamar ya saki iwu sabida tsabar damuwa. Shiru zahra tai ba amsa, mashkhur yana so ya d'auki zahra amma yama rasa taya zai fara ta6a jikin nata. Gani yake bazai iya ba wani iri yake ji in ya kai hannu jikin zahra,. Bara na fita kisa rigar sai na dawo na mayar da ke bedroom mashkhur yana qarasa fad'in hakan ya miqe tare da fuce.

Zahra kuwa yana fita taja tsakin baqin ciki, a zuciyar ta kuwa tana mamaki wai yau ita mashkhur yake bawa haquri, duk da dai zahra ta san ba har cikin zuciyar shi yake bata haqurin ba, kawai sabida baya san takurawa da kuka ne shi yasa so yake tayi shiru. Da qyar zahra ta iya kwakwaran motsi sabida hanunta da ta fad'i akan sa,. A hankula zahra ta fara qoqarin sa rigar, amma batayi garajan cire towel d'in ba a kai ta fara qoqarin sa rigar.

Hannu d'aya zahra ta iya sawa, amma sam ta kasa sawa a d'ayan da ta kwanta a kan sa da yake yayi tsami sosai. Zahra tafi 20 minutes tana qoqarin sa d'ayan hanun rigar amma ta kasa. Haka dai ta cigaba da qoqarin zirawa tana cikin wanan halin mashkhur ya sake dawowa toilet d'in,. Jiki ba qari ya qaraso tare da cewa! Bari na tai maka miki, shiru dai zahra tai bata ce komai ba,, sabida wani haushi da nauyi mashkhur da take ji. Sai da mashkhur ya d'au minti uku kafin ya iya kai hanunsa jikin zahra.

Shima dai da kyar ya iya fara sa mata d'ayan hanun jiki na rawa har wani gumi-gumi yake duk da kuwa da akwai towel a jikin zahra, ba wai tsirara take ba. Kafin mashkhur ya qarasa sawa zahra rigar nan sai da gumi ya jiqa jikinsa sabida shi bai saba ganin mace a hakan ba. Zahra kuwa tun abin yana bata kunya har ya kusa bata dariya sabida yadda taga jikin mashkhur yana rawa da kyar yake iya ta6a jikin ta kamar wanda yake ta6a wuta yana sawa yana hutawa.

Mashkhur yana qarasa sawa zahra rigar ya d'auke ta kamar yadda ya saba, yana d'agata towel d'in ya fad'o mashkhur bai bi ta kan towel d'in ba yayi fucewar shi jiki na rawa hannu d'auke da zahra. Mashkhur yana fita daga toilet d'in ya wuce da zahra kan bed yana zuwa ya zaunar da ita a hankula kamar wani kwai.

Zahra kuwa mashkhur yana ajiye ta, ta saki wani saban kuka, bawai dan zafin ciwan da take jiba aa kawai dan ta takurawa rayuwar mashkhur d'in.
Mashkhur kuwa kan table ya qarasa tare da d'aukko tissue yana d'auko kwalin tissue d'in ya dawo kan be kusa da zahra ya zauna, sanan ya zaro tissue d'in gud'a d'aya, tare da kai hannu sa hanci zahra jiki na rawa ya fara goge mata bakin da hancin ta da suka fashe.

Zahra kuwa sautin kuka ta qara harma shasheqa, mashkhur kuwa shiru yayi dan bai sab yadda zai rarashi zahra ta daina wanan kukan nata ba da yake uzzirawa rayuwar sa. Mashkhur yana gama gogewa zahra hanci ya fita kicin ya dafa mata ruwan tea sannan ya d'ebo bread a plate ya dawo d'akin. Har time d'in zahra bata dai na kuka ba dan har fuskar ta tayi jajarin kamar ka ta6a jini ya fito,.

Jiki ba kwari mashkhur ya ajiye cup da plate d'in a kan qaramar wardrobe d'in gefan kwabar. Sanan ya hau kan bed, ya zauna suna face's d'in juna shida zahra. A hankula mashkhur ya ruqo hannayan zahra duka biyu, riqe su mashkhur yayi sosai yana tinanin ta ina zai fara. Ajiyar zuciya mashkhur ya sauke tare da cewa! Ki dena kukan nan ya isa haka kinji, zahra kuwa maimakwan tai shiru kamar yadda mashkhur ya buqata wani uban kukan ta sake saki.

Shiru mashkhur yayi tare da zubawa, zahra ido yana kallan ikwan ALLAH, kuka take sosai harda majina. Mashkhur bai sai sanda wani siririn mashkhur ya kwace mai ba saka makwan yadda yaga zahra tana kukan da kyar alamun itama kanta ta gaji da kuka. Girgiza kai mashkhur yayi tare da cewa! Hmm ALLAH ya kyauta kema kanki da kyar kike kukan kin gaji bare ma ni mai ji.

Zahra kuwa tana jin haka ta qara sautin kukanta kamar wadda akace za'a zare mata rai. Cikin mamaki mashkhur yace! To yanzu kuma mai akayi miki haba pls ki dena kukan nan ki bari na huta kema ki hutawa rayuwar ki. Zahra kuwa harara ta watso mai tare da cewa! Bazan dai na ba, ajiyar zuciya mashkhur ya sauke tare da cewa!

Wlh in kina so mu koma nigeria da wuri ki dena kukan nan in dai kika de na kukan nan qarshan week d'in nan zamu koma kina samun sauqi. Da sauri zahra ta kali mashkhur tare da cewa! Da gaske, d'an harara mashkhur ya watasa mata tare da cewa! I'm Really,, nanauyar ajiyar zuciya zahra ta sauke nan ta fara share hawayan ta.

Shima mashkhur d'in siririyar ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa! Alhamdulilahi a cikin zuciyar sa. Haka dai mashkhur ya cigaba da rarashin zahra taci abinci sanan ta sha maganinta ta koma wani saban baccin.

To ranar dai haka mashkhur ya wuni cikin damuwa da takurawar zahra, dan abu kad'an in yayi mata bai mata ba, ya shiga uku zama zatai tai ta rusa uban kuka, har sai da takai ta kawo mashkhur ya dai na hantarar ta da yi mata barazana kawai rarrashin ta yake.

Bugu da qari ga jigilar kai zahra toilet da flushed d'in audiga kai ranar mashkhur yaga ta kansa.
Haka dai ya lalla6a zahra tai bacci sau da zahra tai bacci ya samu sukuni, ranar dai da batsanan cin ciwan kai mashkhur ya kwanta sabida yadda zahra ta ringa caza mai kai.

Nigeria................

Zaune ammi take akan bed d'in ta hannun ta riqe da wayar ilham tana ganin picture d'in candy d'in su zahra, wadda zahra ta turowa ilham. Ita kuma ilham tana daga gefe tana yankewa ammi faracan qafa, sunayi suna hira sama-sama. Suna cikin haka wayar ilham da take hanun ammi tai qara alamun shigowar saqo, karaf a idon ammi.

Ammi zubawa message d'in kyawawan idanuwan ta tai, da mamakin ammi sai taga anyi save d'in number da my husband to be..... Daga haka bata qarasa karantawa ba message d'in ya yanke, mamaki ne sosai ya kama ammi, amma sai batacewa ilham komai ba da batati niyar karanta message d'in ba amma ganin sunan da ilham tai save da shi hakan ne yasa ta shiga message din.

Ilham kuwa tana jin qarar message d'in hakan ya tabbatar mata da ahmad ne ya turo shi, nan da nan jikin ta ya fara rawa-rawa alamun rashin gaskiya. Tana tinanin ammi zata bud'e message d'in ko kuwa, duk da ilham tasan ammi bata da bin kwakwafi, amma tasan tabbas in ammi taga save d'in sunan ahmad kashin ta ya bushe.

Kafin kace kwabo gumi ya tsinkewa ilham a zuciyar ta tana ta addu'o'i wadda ita kanta batasan wana kalar addu'o'i take ba. Ammi kuwa tana shiga wajan message d'in sunan ta qarasa karantawa my husband to be in sha ALLAH. Sosai mamaki ya kama ammi dan bata ta6a tinanin ilham tana da wani saurayi ba, bama hakan ne yafi bata mamaki ba yadda tai save d'in sunan ne ya bata mamaki.

Hankali a d'an tashe ammi ta fara karanta message d'in kamar haka! Amincin ALLAH ya tabbata a gareki gimbiya ta da fatan dai kina lpy, ALLAH yasa hakan. In sha ALLAH yau zanzo wajan dady kiyi addu'a sosai akan ALLAH yasa ya amince, dan ni na matsu wlh na ganki sabida tinaninki kinsa ko bacci bana iya yi, by take care.

Ammi tana gama karantawa ta d'ago ta kalli ilham wanda tini gumi ya gama jiqa mata fuska, kana ganinta kaga cikakiyar mara gaskiya. Ammi kuwa d'auke kanta tai daga kan ilham ta mayar da shi kan message d'in tana karantawa one by one. Ammi ta d'au 30 minutes tana karanta message d'in da ahmad da ilham suke yi, har lokacim bata kai qarshan message d'in ba da yake messages d'in suna da yawa sosai.

Abinda ya d'an kwantarwa da ammi hankali game da lamarin taga dai duk messages d'in, basa gayawa juninsu abinda bai dace ba kawai dai hira su sukeyi ta soyayya mai ban sha'awa, ga kuma yadda taga ahmad yana yawan tinatar da ilham akan abinda ya dace! Da wanda bai dace ba, duk da ammi batasan wane yake messages d'in ba amma gaskiya tasan yana da tarbiya sosai.

Amma ammi tasha mamaki yadda ilham take shan soyayya, dan ammi bata ta6a tinanin ilham tasan mene soyayya ba barema tayi sai gashi yau ta kamata dumu-dumu. Cikin wani yanayim da ilham bata gama sanin namenene ba ammi ta d'ago ta kalle ta tare da cewa! Hmmmm my husband to be in sha ALLAH koh, jinjina kai ammi tai tare da cewa! To waye wanan haka ilham?...............

Hmm shin ya ilham da ammi zasu qarke kuwa?.......

Kuna ganin in ahmad yazo wajan dady, dady zai amince da soyayar su da ilham har ya bashi auran ta ko kuwa......

Ya 6angaran mashkhur da zahra kuwa?.........

Ku biyo ni gobe a next page dan jin ya zata kaya.


ADALILINTA 💜❤💜

AMINA BAYERO 💜❤💜

Typing..........


*page 92*

Cikin wani yanayim da ilham bata gama sanin namenene ba ammi ta d'ago ta kalle ta tare da cewa! Hmmmm my husband to be in sha ALLAH koh, jinjina kai ammi tai tare da cewa! To waye wanan haka ilham?...............

Nan da nan ilham ta fara zazzaro ido duk tabi ta rud'e alamun rashin gaskiya duk ya tattara a gare ta. Gyara zama ammi tai tare da cewa! Magana fa nake miki ilham kika yimin shiru, ba ki na rawa ilham tace ammi hmm uhmm ni! Ni! Ni! Nima ban sam shi ba. Kallan rainin hankali ammi ta watsawa ilham tare da cewa! Kamar ya baki san shiba.

Ammi da gaske nake ban san shi ba ilham ta qara fad'in hakan cikin kama-kame da rashin gaskiya. To bakin san shiba kikayi save d'in number kenan?, Hmmm ilham kenan ni zaki yiwa qarya koh? Karfa ki manta ko zakiyiwa kowa qarya a duniya to banda ni a ciki sabida nasan halinki tsaf koya kikayimin qarya sai na gane komin qanqatar qaryar kuwa.

Wani yawun tashin hankali ilham ta had'iye tare da sunkuyar da kai qasa dan tama rasa wace amsa zata bawa ammi dan tasan ammi ta riga da ta kamata damo-damo ba ta da wata sauran mafita. Ilham yaushe kikayi saurayi har kika fara soyayya da shi ban sani ba?, ammi ta watsawa ilham tambayar fuska d'auke da mamaki.

Jiki na rawa ilham tace aa nifa ammi ba soyayya muke da shiba, shine kawai yake so na ammi nifa kwata-kwata bana san shi. Murmushin takai cin qaryar da ilham take zubawa ammi tai tare da cewa! Hmm gaskiya ne ilham, nasan ai bazaki ta6a aika ta hakan ba ba tare da nasani ba, shikenan tashi kije kinga bama sai an sha wahala ba, tinda yace yau zai zo ya zuwa dadyn ki, in dady ki ya sanar da ni sai nace aaa tinda kinga ai bakya san shi ko?.

Da sauri ilham ta d'ago ido sabida yadda taji ammi tana kora jawabi. Ilham bata san sanda tace! ammi yanzu in yazo sai ace mai nace aa bana som shi koh?, fuska a sake ammi tace ee mana ilham ai bakya san shi kuma kinga baza a baki wanda bakya so ba ko?. Ammi dai duk tayi hakan ne sabida tanaso taji gaskiyar zancan abkin ilham dan tasan tabbas ilham qarya take mata suna soyayya da shi.

Nan da nan matsa nan cin tashin hankali ya bayyana a fuskar ilham sam sai taji inama inama batayiwa ammi qaryar nan ba, dama kawai gaskiya ta fad'a ko mai zai faru ya faru. Ammi kuwa cewa tai kin gama yanke min farcan kuwa?, jiki a sanyaye ilham ta girgiza kai tare da kama qafar ammin ta cigaba da yanke mata.

Sam ilham ta dai na gane komai kawai dai ta riqe farcan ammin ne amma ba yanke shi take ba, ammi kuwa zubawa ilham ido tai tana sake fahimtar abinda yake damun ta, ilham tafi 5 minutes hannu riqe da d'an yatsan ammi, sam tama manta yankan farce take dan tama tafi duniyar tunani, ammi kuwa tana daga kefe ta zubawa ilham ido tana kallan ikwan ALLAH.

Qafar ta ammi ta janye duk dan ilham ta dawo cikin hayyacin ta amma ina ilham bama tasan ammi ta janye qafar tata ba. Miqewa ammi tai tare da komawa kusa da ilham ta zauna a hankula. Bayan ta zauna ruqo hanun ilham tai a hankula, a firgice ilham ta dawo hayyacin ta tare da d'agowa dan ganin waye ya riqe mata hannu haka.

Ammi ta gani a kusa da ita riqe da hanunta, ilham tayi mamaki sosai ta yadda ammi ta taso kuma harqta dawo kusa da ita ta zauna bata sani ba ita da take yanke mata farce. Ajiyar zuciya ilham ta sauke tare da cewa! Ammi har na gama yanke miki farcan ne?, zubawa ilham ido ammi tai tare da cewa! Ilham ai ke zan tambaya tinda ke kike yanke min farcan taya zan sani ni.

Shiru ilham tai dan tama rasa mai zata ce dan ita har ga ALLAH tama manta ta gama yankewa ammi farcan ko kuwa. Girgiza kai ammi tai tare da cewa! Ilham kenan kina bani mamaki sosai ni a tinani na, duk duniyar nan in kika d'auke zahra ba wanda ya cancan ta ki gayawa damuwar ki sama da ni, karfa ki manta ni mahaifiyar kice meye ribar ki in kin 6oyemin damuwar ki.

Kuma in baki gayamin damuwar ki ba wazaki gayawa kin dai san yanzu zahra bata nan koh?, ko mene karkiji tsoro ki gayamin zan fahimce ki menene tsakanin ku da shi kuma waye shi a ina kuka had'u da shi?. Gayara zama ilham tai tare da cewa! Ammi kiyi haquri nasan dai nayi miki laifi sosai, na farko na 6oye miki gakiya sanan nazo na sake yi miki qarya yanzu, duk da kuwa kin hani mu qarya akan gaskiya.

Hakane yanzu dai inajin ki ki gayamin gaskiyar abinda yake faruwa, ammi ta

Please Login or Register in order to submit comment