Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

to ba wani wanka da zakiyi a haka zaki dafamin abinci. Tom zahra kawai tace, sanan ta koma ta d'auki mayafinta ta rufe jikinta, haka zee ta tusata a gaba har qofar kicin, sanan tace ta dafa mata coffee da cake.

Zahra ba musu ta shiga ta fara dafawa zee abinda tace, kwa6a cake d'in ta farayi, bayan ta kwa6a ta dora coffee, tana zauke coffee d'in ta zuba kwa6in cake d'in a oven sai da ta saita hutar oven d'in sanan ta rufe. Har zahra taza futo taji muryar mashkhur, yana cewa sorry my zee abu mai mahimmanci nake a Ciki shiyasa kikaga na dad'e. Cikin shagwa6a zee tace ai honey sai da nace zan tayaka kace aa, wai sabida mai bakaso mu ringa kasancewa tare ne?. Shiru mashkhur yayi bai bata amsa ba.

Can kuma zee ta sake cewa honey ya kamata fa ka bani tariyinka? Gigiza kai mashkhur yayi tare da cewa no zee ki barshi kawai ba yanzu ba. Okay honey tinda bazaka gayamin kai waye ba yau ni zan gayama koni wace, mashkhur kuwa shiru yayi nan ma bai ce mata komai ba, zahra kuwa tanajin haka ta sake la6ewa a bakin cikin d'in domin jin mai zee zatace, duk da kuwa bata gane wani turanciin zee d'in inta fad'a.

Gyara zama zee tai cikin yaran English ta fara bawa mashkhur tarihinta kamar haka! Mahaifiyata haifarfiyar rasha ce, mahaifin mamana kuwa babban mutum ne yana da kud'i sosai, duk yaransa mazane, maza uku mahaifiyata ce kawai mace, kuma itace 'yar autar cikinsu. Mahaifina kuwa haifafan d'an NIGERIA ne kuma musulmin, mashkhur kuwa yana jin haka ya d'ago da sauri tare da firta Nigeria kuma musulmi? Gyad'a kai zee tai alamun eee. Ba iya mashkhur ba har zahra da take la6e a kicin sai da mamaki ya kamata.

Zee kuwa cigaba da magana tai kamar haka!! Mahaifina yace min iyayansu su biyu suka haifa shida qanwarsa zainab. Kuma iyayan su talakawa ne sosai basu da komai da kyar suke iya cin abinci a rana, kuma duk 'yan uwan mahaifin babana suna da kud'in sosai, kawai taimaka mai ne bazasuyi ba. a haka dai har mahaifinsa ya rasu, bayan ya rasu zuciyar mahaifiyarsu ta biga itama ta mutu. A lokacin mahaifina da qanwarsa sunga tashin hankali sosai, akan nan dai suka cigaba da cikin qonci da talauci, gashi duk 'yan uwansu basa tai maka musu. Bayan shekara uku da mutuwar iyayan mahaifina qanwarsa zainab ta fara cuta, ciwan hantane yake damunta haka mahaifina yay ta jinyar ta cikin talauci har ciwan hanta ya kasheta.

Hankali mahifina ya tashi sosai dan a lokacin ma yayi qoqari komawa Christian da yake a tsakiyar yarabawa suke, kuma duk kafirai ne, musulman kad'an ne suma su mahaifin nawa yarabawa ne, suna zaune a state d'in shiru zee tai tana qoqarin tuno sunan state d'in da mahaifiyata yake, can kuma tace Lagos. Bayan qanwar mahaifina zainab tayi wata uku da rasuwa mahaifina ya samu ofer d'in tafiya rasha karatu. To a lokacin dayazo karatu suka had'u da mahifiya a school, mahaifiyata taso mahaifina sosai, duk da kuwa musulmi ne.

A sannu a hankali suka fara soyayya da mahaifina, soyayyar su tayi qarfi sosai, hakan ne yasa mamana ta samu mahaifiyata da magar aure su. Mahaifin mamana ya amince mahaifiyar mamana kuwa bata amince ba. Amma mahaifin mamana yayi watsu da maganar mahaifiyar mamana da yake 'yan uwanta maza sun goya mata baya akan haka. Lokacin da mamana tazowa da mahaifina maganar bai yi gaddama ba ya amince da hakan, daga haka kuwa aka d'aurawa musu aure. Lokacin qanqani mahifina ya zama mai kud'i gaske da tai makwan dukiyar mamana.

Bayan iyayena sunyi aure da shekara biyar mamana ta haifeni, A lokacin babana ya roqi mamana alfarma akan ta amince na zama musulma a sa mun sunan qanwarsa zainab da yake babana yana qaunar qanwar tasa zainab. Mahaifiyata kuwa cewa tai aa sai na girma zan za6i wana addi ni nake so, amma ta amince a samun zainab d'in, haka kuwa kayi aka samun suna zaiba sukuwa dangin mahaifiyata suke kirana da zee. Daga haka zee tai shiru alamun labari ya qare, mashkhur kuwa duk sai yaji jikinsa yayi sanyi, dajin labarin zee musamman ma yarda yaji mahaifina ya tsinci kasanta a halin rayuwa, kuma ba wanda ya iya tai maka mai.

Tunatarwa........

Gaskiya mutane ya kamata mu ringa tausayawa talakawa da marayu, ko dai wani na qasa damu, yanzu a zamanin nan tai mako yayi qaranci, sam masu kud'i basa san tai makawa na qasa da su komai dukiyar su. Ta kusani cewa abinda ka bayar shine rabanka, kuma rashin tausayawa na qasa da kai yana jawo musifu a qasa. Karku manta manzan Allah S A W, shine shugaban duniya yafi kowa muqami da sarauta da daja, Allah wanda ya halice kowa yafi san shi fiye da ko wana bawa, amma manzan Allah da yafi kowa arziki, baya kwana da ko kwallin dabino, sabida kulluma akaci abinci a gidansa sadakar ragowar ake komun yawansa, bai yarda ya kwana da wani ba a gidan saba wasu kuma a waje suna jin yunwa, baya tanadin na gabe, duk arzikinsa na mutane ne.

To ku duba kugani, d'an gatan Allah ma yake temako bare kai wani bawa, qarshema duk abinda ka tara tafiya zakai ka barshi a duniya bazaka tafi da komai ba sai da aikin na alkhairi . In kana taimakawa na qasa da kai kaga da kyau in kuma bakayi hmmmmmmmm Allah dai ya kyauta kawai dan sai kayi nadamar hakan a lokacin da nadamar bazata amfana ma komai ba. Dan Allah 'yan uwana in munsa muna da shi komun qanqantar sa, mu ringa tai mako na qasa da mu ko almajiri ne............

Continue...

Kallan zee mashkhur yayi wanda ko a fuska labarin nata bai bata wani tausayi ba, ce mata yayi yanzu ke wana addini kika za6a? Wanne kikeyi? Murmushi zee tai tare da cewa Christian wato arniya. Dorawa tai da lokacin dana girma haka nan naji nafi sha'awa addinin mamana shiyasa na shiga, mahaifina yayi-yayi dani akan na zauna a akan na koma musulinci naqi, da babana yaga naqi shiga musulinci yace na canza sunana zuwa na arna sabida sunan zainab, sunane mai kyau. Ba musu ni da mahifiyata muka canza sunana zuwa blessing amma har yanzu dangina basu dai na cemin zee ba kuma nima da shi nake using a school ai nasan kasan wannan ko?.

Gyad'a kai mashkhur yayi alamun ehh, kallanta mashkhur yayi tare da cewa!! Zee ya kamata ki shiga musulinci sabida shine gaskiya, murmushi zee tai tare da cewa nasani honey kawai dai bana ra'ayin shigane sabida da akwai sharad'in da bazan iya cika shiba, zan gayama amma ba yau ba. Zee tana gama fad'in hakan ta kwalawa zahra kira kamar haka!! House girl wai har yazu baki gama yimin girkin ba, zahra kuwa da sauri ta bar wajan data la6e, itama ta manta da wani girkin data d'orawa zee ta shagala da jin labarin.

Tana qarasawa ta kashe oving d'in bayan ta kashe ta bud'e nan da nan qamshin ya cika cikin d'in cake d'in yayi ja sosai, kana ganinshi zai baka sha'awa. Zahra tana saukewa ta ta juyewa zee a plate, dama cake d'in gudu hud'u tayi mata, ma dai-dai ta, daga haka ta d'auki coffee d'in ta jera a matsakai ci plate tare da cake d'in ta nufi hanyar falon. Tana isa fallon da hararar mashkhur ta fara karo, zahra kuwa kawar da kanta tayi, ta qarasa gaban zee d'in ta ajiye plate d'in, har zata wuce zee tace haka aka koya miki cake d'in ina ice d'in? Shiru zahra tai ita tayi tinani zee bata buqata ice shiyasama bata sa mata ba.


Maza tashi kije ki d'auko ice ki shafa min, zee ta fad'a cikin tsiwa, ba musu zahra ta miqe ta koma kicin. Tana shiga ta bud'e frig ta d'auko robobin ice d'in, kala biyu zahra ta d'ebo red and white ta d'ako sanan ta d'auko wuqar shafa butter, daga haka ta koma fallon domin shafawa zee ice. Zahra tana isa ta fara ai watar da shafawa zee ice, zee d'in kuwa zai wani bin zahra da kallo take kamar wata mayyah. Zahra ta tsargu sosai da yarda zee take kalonta amma ba yarda ta iya haka ta haqura ta cigaba da shafawa cake d'in ice. Duk da mashkhur bashi da kula amma ya lura da irin kallon da zee takewa zahra.

Bayan zahra ta gama shafawa zee ice, har zahra zata tafi zee tace ta d'akko mata ruwa da cup, haka zahra ta wuce ba musu ta d'akko mata tana dire mata ta kama hanyar bedroom d'in ta, zee kuwa sakin baki tai tana qarewa bayan zahra kallo. Mashkhur kuwa mamaki ne ya kamashi irin kallan da zee takewa zahra, amma bai kawo komai a ransa ba yayi tinanin kawai dai dan zahra ba 'yar rasha bace kuma zee bata saba da ganinta ba shiya take mata wanan kallan.

Zahra kuwa tana shiga bedroom toilet ta nufa ta d'oro alwala ta futo, ta fara gabatar da sallar la'asar. Bayan ta idar rokwan Allah tayi akan ya kareta daga sharrin zee dan ita yanzu kallon da zee take mata harya fara bata tsoro. Bayan ta gama toilet ta koma tayi wanka, bayan tayi wanka ta futo ta shirya, daga haka ta kullo bedroom d'in ta sabida storan shigowar zee ta cutar da ita, bayan haka kwanciya tai tana ta tunanin ilham, tayi missing d'in ilham sosai musamman in ta tina komai tare sukeyi, har bacci daga haka dai bacci mai nauyi yayi awan gaba da ita...............


ADALILINTA💜❤💜

BY AMINA BAYERO 💜❤💜

My number 09162226240

Typing............

*page 60*

Bayan ta gama toilet ta koma tayi wanka, bayan tayi wanka ta futo ta shirya, daga haka ta kullo bedroom d'in ta sabida storan shigowar zee ta cutar da ita, bayan haka kwanciya tai tana ta tunanin ilham, tayi missing d'in ilham sosai musamman in ta tina komai tare sukeyi, har bacci daga haka dai bacci mai nauyi yayi awan gaba da ita...............

Lokacin da zahra ta tashi daga bacci, zee tafi gidan su,, haka zahra ta sha zamanta a d'aki har dare yayi. dare yanayi taci ragowar abincinta ta kwanta, duk da kuwa bata jin baccin haka ta kwanta lamp kamar mage. Gaban zahra ne ya fad'i sakamakwan tunawa da tayi da iyayanta da suka haifeta, haka nan taji tana jin ciwan rashin su a tare da ita duk da kuwa tasan bata rasa komai a rayuwa ba, dan ammi da dady sun cike mata gurbin iyaya kuma tabbas tasan ko iyayanta iya qaunar da zasu nuna mata kenan. bazasu nuna mata fiye da gatan da su ammi suke nuna mata ba. 6agara kaka kuwa zahra tana ganin tafi kowa sa'ar kaka a duniya.

Amma dai duk da haka zahra tana buqatar ganin iyayanta na haihuwa, tinda koba komai su suka haifeta, kuma tanaso taji dalilin da yasa mahaifiyarta wanda tasha wahalar haihuwarta ta bayar da amanar ta akan titi ga wanda batasan suwaye mah ba, yanzu da a hanun mugayan muatane ta danqata shikenan, zahra batasan sanda wasu zafafan hawaye masu zafi suka gangaro mata ba, tunda zahra tasan ba su ammi ne suka haifeta bata ta6ajin zafin rashi sanan iyayanta ba irin yau, bawai dan muguntar da yaya mashkhur, yake mata ba aa kawai haka nan takeso taga iyayanta.

Dan tasan ko tana gaban iyayanta Allah zai iya had'ata da miji irin yaya mashkhur kuma ya ringa azaftar da ita, dan wahalar da yaya mashkhur yake bata da rashin iyayanta ta d'auke su a matsayin qaddarar ta kawai. Hakanan zahra taji qaunar iyayanta suna shigar mata rai a hankula musamman ma mahifiyarta, dan zahra duk da batasan wace maman taba, tambas tasan ba a san ranta ta bayar da amanar taba. Can kuma wata zuciyar tacewa zahra ke kina da tambacin mamaki ce mah ta bayar da ke?.

Shiru zahra tai tana nazarin abinda zuciyar tace mata, can kuma sai ta tuna da magar hajiya kaka da tace lokacin da mahaifiyarta ta bawa hajiya kaka ita kafun ta gufu, da hawayen baqin cikir rabuwar uwa da 'ya a idonta. Sanan kuma mamnta taba da da takardar address d'im gidansu yaya mashkhur ya yar an qona a rashin sani. Kuma yaya abdul da hajiya kaka sun ce mata suna kama da mamanta sosai. Nan da nan zahra zuciyar tayi mata sanyi sosai dan tasan ko ba komai har yanzu mahaifiyarta tana mata addu'a duk da kuwa zahra bata ta6a sa ran zata qara had'uwa da iyayan taba, a duniya.
Zahra dai tana cikin saqa da warwara bacci mai nauyi yayi awan gaba da shi.

Washe gari...........

Tunda sassafe zahra ta shiga kicin ta soya dankali da kwai sanan ta dora ruwan T. Tana gama had'awa ta futo da kayan abinci ta wuce d'akinta, tana shiga bedroom d'in ta ta saki ajiyar zuciya, sabida basu had'u da yaya mashkhur. Daga haka toilet ta shiga tai wanka sanan ta futo ta fara qoqarin shiryawa, yau ba kayan da tasa jiya tasa ba sabida jiya bata ciresu da wuriba tayiwa zee girgi dasu, kuma taci abincin dasu, dama uniform d'in nata wajan kala biyar dady ya siya mata.

Yau doguwar riga ta d'akko itama dai irin uniform d'in jiya ce sak sai dai ita in ka d'ora 'yar cikin sai kasa doguwar rigar a sama ba sai kasa skit ba. Itama doguwar rigar kamar tsayin skit haka take da kad'an ta wuce guiwa, amma zahra tanasa doguwar safa yarda baza'aga qafar taba. Bayan ta gama shiryawa tayi parking d'in kan nata, bayam ta gama parking d'in kanta, zama tai ta fara cin abincin ta. Tana gama cin abincin ta zura takalminta sau ciki da mini hijab d'in ta, sanan ta sunkuci jakarta, dan tama manta da abinda class meant d'in ta suka bata dan bata samu damar cire suba sai lokacin ta tuna da su.

Amma zahra gudun kar yaya mashkhur ya futo fallo hakan ne yasa bata samu damar cire chocolates d'in da suka bata ba, haka ta rataya jakar ta kama hanyar fita daga bedroom d'in. Wow yauma fa zahra tayi kyau fiye da jiya ban gama tabbatarwa da zahra kayakyawa bace ta ajin farko sai yau, nikuwa amina bayero nace hmmm nan gaba mashkhur ya saki zahra wlh yayi babbar asara. Zahra tana fita daga bedroom d'in ta bataga mashkhur a fallo ba dan haka sand'a ta farayi kamar wata munafika.

Tana ciki san d'ar nan naji alamun futowar mashkhur, ai zahra bata san sanda ta kwasa a juge tai hanyar fita daga fallon ba, ai kuwa tana zuwa ciki rashin sani ta bige goshinta ji kake qum. Duk da bigewar da zahra tai hakan bai hanata ficewa daga fallon ba da sauri, tana fita bata tsaya hutawa ba ta sauka daga kan step d'in benan, gudu-gudu, sauri-sauri. Tana gama sauka daga ken step d'in benan, ta riqe goshinta saka makwan wani rad'ad'i da yake mata.

Tundaga nesa Ahmad ya hango zahra a qarshan step d'in benan, a tsaye tana riqe da gashinta, Ahmad ganin hakan ne yasa shi qara saurin tafiyar tasa, yana qarasawa yacewa qanwata lafiya na ganki riqe da goshi? D'agowa zahra tai tare da kawar da fuskarta gefe kamar zatai kuka tace bigewa nai a goshina. Ayyya sannu a dai dai ina kika bige ne? D'agowa zahra tai tare da nuna masa gefan goshin ta, Ahmad kallan gefan goshin nata yayi tare da cewa ayyah kuma gashi wajan harya fara kunbura ko na milmila mike ne?.

Zahra bata kawo komai a zuciyar taba sabida ta d'auki yaya ahmad kamar yaya abdul, dan a matsayin d'an uwanta ta d'auke shi dan haka d'aga mai kai tayi alamun ehh. Matsowa yayi tare da riqe kanta ta baya nan da nan zahra ta yamutsa fuska alamun tsoro dama kunsan zahra da mugun tsoro. Dariya Ahmad yayi tare da cewa gaskiya qanwata kin cika tsoro wlh, da sauri zahra ta ware idanta tass tare da sakin Murmushi jin kunya. Gaban Ahmad ne yayi mugun fad'uwa lokacin da suka had'a ido da zahra, sakamakwan mugun kamar da yaga zahra tayi mai da MAMANSA.

Yasalam Ahmad ya furta, sam ya kasa janye idonsa daga kallan zahra, zahra kuwa da sauri ta sunkiyar da idon ta tare da cewa yaya ahmad lafiya? Firgigit Ahmad ya dawo hayyacinsa, cikin sarqewar murya tace wlh kina kama da MAMANA sosai, itama zahra gabanta ne ya fad'i sosai tare da furta maman ka kuma?. Nan da nan Ahmad ya dawo cikin hayyacin sa tare da fara magana cikin rawar murya am!! Ina! Ina! Wai! Ina nufin da kikayi murmushi sai kikayi kamada mamana, amma ai bama kwa kama kwata-kwata, kawai dai su6utar baki nai.

Shiru zahra tai dan sam sai taji bata yarda da amsar da yaya ahmad ya gaya mata ba, amma duk da hakan bata nuna mai ba kawai dai wani murmushi tai mai cike da kokwanto. Ahmad kuwa kawar da zacan yayi da cewa! Bari na lailaya miki goshin kinga harya fara kunbura, daga haka bai sake cewa komai ba ya fara lai layawa zahra ita kuma sai fama saki ashhh. Suna cikin wanan halin mashkhur ya sauko daga kan benan yaji karo da su. Hakanan mashkhur yaji gabansa ya fad'i rass sam sai yaji bai ji dad'in yarda yaga Ahmad da zahra ba kawai binsu yayi da wani kallo wanda su kansu basu san fassarar shiba, sanan yayi wucewar sa wajan parking space domin d'aukar motar sa.


Can kuma mashkhur a zuciyar sa ya ja tsaki tare da cewa ko da yake mai ne na damuwa ba, ai dai ba santa nake ba kuma very soon zan sake ta, kuma ai nasan tabbas Ahmad bazai ta6a ai kata abinda bai dace ba, duk yarda kai wani abun ne ya faru. Mashkhur yana kawowa zuciyar hakan Sai yaji zuciyarsa ta yimai fasss! Haka yaja motar sa a guje yabar gidan.

Zahra kuwa tasha jinin jikinta da kallon da mashkhur yayi mata, shima kansa Ahmad d'in Bai ji dad'in yanayin da mashkhur ya same shi shida matar sa zahra ba, duk sai yaji ba dad'i sai yanzu yaga rashin dacewar hakan da yayiwa zahra, duk da kuwa shi bada wata manufa yayi mata hakan ba. Ahmad kuwa girgiza kai yayi tare da cewa qanwata zo mu tafi makaranta karmu makara, daga haka suka wuce motar, bayan sun shiga motar fucewa sukayi daga gidan.

Sam zuciyar zahra, ta kasa mantawa da magar da ahmad ya gaya mata akan cewa suna kama da mamansa, can kuma wata dabara ta fad'owa zahra. Gyara zama tai tare da cewa! Yaya ahmad wai a wani state kake da zama, hararar wasa Ahmad ya gallawa zahra tare da cewa au wai ke bakisan a wana state nake ba? Ehh mana wlh yaya ahmad ban saniba, jinjina kai Ahmad yayi tare da cewa to bari kiji kusan kullum in muna Nigeria ina yawan zuwa gidan ku wajan abokina mashkhur, amma ban ta6a ganin kiba! Shima wataran yana yawan zuwa gidan mu.

Kallansa zahra tai tare da cewa kenan garin mu d'aya kai ma a kano kake?, da sauri ahmad ya d'aga kai tare da cewa kwarai kuwa aini d'an kano ne gaba da baya haifanfan kano ne. Jinjina kai zahra tai, dan yanzu ta tabbatar Ahmad da gaske yake basa kama da mamansa, sabida zahra ita tasan iyayanta a kaduna suke shi kuma yacee mata cikakyan d'an kano ne, dan haka nan da nan zahra ta cire shakkun da yake zuciyar ta, kuma ta yarda da maganar Ahmad d'ari bisa d'ari. Daga haka har Ahmad ya kawo zahra school ba wanda ya sake cewa komai.

Suna isa Ahmad yayi parking tare da kallan zahra yana cewa! Ai yau dai tinda an kai ki ajinku ba sai na rakaki ba koh? Da sauri zahra ta d'aga kai alamun ehh, nan ma Ahmad zubawa zahra ido yayi sam ya kasa d'aukewa, sabida ganin abun yake kamar al mara. Zahra kuwa bata lura da hakan ba hankalinta duk ya karkata wajan bud'e murfin motar domin fita, tana shirin fita taji yaya ahmad yace mata a dawo lafiya qanwata ayi karatu da kyau, amen yaya ahmad in sha ALLAH. Daga haka zahra tai ficewar ta tabar yaya ahmad yana binta da kallan qurillah.

Sai da zahra ta 6acewa Ahmad sanan ya dai na kallanta, wayarsa ya dakko yayi daily d'in number, number anyi save d'in ta da MAMANA. Ba 6ata lokaci Ahmad ya dannawa number kira, ta fara ringin, har sai da wayar ta kusan katsewa sanan akai parking. Wayar a hands free ya sata, sallama Ahmad ya farayi, daga can matar ta amsa mai cikin muryar bacci tace my soon, ka katsemin bacci na da wanan daran zaka kira ni. Murmushi Ahmad yayi tare da cewa am sorry mamana kinsa yanzu safiya ce a rasha shiya.

Okay my soon ba matsala nayi kewarka sosai fa? Murmushi Ahmad yayi tare da cewa nima ai nayi kewaki, mamana kin san mene kuwa? Da sauri matar da amsa da aa! Wlh naga wata mai KAMA DA KE sak. Duk da ahmad baya gaban maman tasa sai da yaji yanayin yarda ta zabira, cewa tai kai Ahmad a ina kuma? Amsa mata Ahmad yayi tare da cewa anan rasha mana yanzu muka rabu ma! Ajiyar zuciya matar ta saki, dan ita a tunanin ta duk yarinyar 'yar garin rasha ce shiyasa ma ta kawar da magar da cewa! Tom yakake my soon?.

Lafiya qalau mamana amma sai naji da nayi miki zancan yarinyar kamar gabanki ya fad'i koh? Da sauri maman tasa tace no kawai dai abin ne ya bani mamaki wai mai kama dani, shiyasa kaga hakan, jinjina kai Ahmad yayi harga ALLAH ya yarda da maganar maman nashi, dan haka bai kawo komai a ransa ba, to mamana bari na barki kiyi bacci a gai da su HAMIDA! okay zasuji in sha ALLAH.

Please Login or Register in order to submit comment