Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gida. Hakan ba qaramin mamaki ya bawa ammi ba,

Ita kuwa hajiya kaka haushi taji amma ta danne bata nunawa kowa ba. Tom haka rayuwa tai, ta juyawa kullum halima acikin yiwa dady asiri take kuma baya wani kamashi sosai kamar yadda da yayi mae. Saka makwan su hajiya kaka da shi kansa dadyn suna yin addu’ar da mlm Ibrahim ya basu sosai.

Yanzu dady yana kwattata adalci sosai, kuma son momy ya ragu a zuciyar ba kamar daba.ko da yake haka aikin asiri yake. Yanzu dady hankalin sa ya koma kan ammi baiwar ALLAH kulluma santa qaruwa yake a zuciyar dady. Mashkhur kuma sae girma yake yana qara kyau kae ka gansa sae ka rantse ba d’an Nigeria bane.

Sabida tsabar kyansa da hutu. Sabida tsabar hutun da yake samu in ka ganshi baza kace mae d’an shekara d’aya ba. Tom haka rayuwa tai, ta juyawa abubuwa masu dad’i da sab’anin haka suna faruwa. Kullum dady ALLAH qara bud’a mae yake, dan yanzu ya zama mae kud’i sosai. Dan harya fara gina qatan gida da zae had’e su ammi da momy.

Yanzu shekar d’aya kenan auran dady da momy kuma har yanzu bata haihu ba kuma bata samu ciki ba. Itama b’an garan ammi bata sake haihuwa ba. Bayan wata uku ALLAH ya bawa momy ciki lokacin mashkhur yana da shekara biyu abinsa ya qara kyau da girma ga wayo kuma.

Amma sae dai hasken fatar sa ya ragu amma duk da haka inka ganshi fari zaka kira shi. Lokacin da dady ya samu labari cikin momy yayi farin ciki amma ba kamar lokacin cikin mashkhur ba. Kuma ya nuna mata kulawa amma ba kamar yadda yayiwa ammi ba.

Haka momy tai, ta rainon cikin ta cikin kulawa da qoshin lafiya har ALLAH yasa cikinta ya cika watan haihuwa. Saratu qanwar momy tazo tayata zama har ALLAH ya sauke ta lafiya. Dady ya tanadarwa baby kayan jaririn duk wani tana din suna yayi kai harma ragunan suna ya tana da.

Ranar wata litinin da safe momy ta fara na quda, haka dady da saratu qan war momy suka tafi hasibiti. Bayan an kae momy asibiti wajan qarfe sha biyu na rana ta haihuwa. Ta haifi san kacecan d’anta kyakyawa fari tass mae kama da dady sak.

Dady yayi farin ciki sosai, itama kanta momy tayi farin ciki. Wajan qarfe hud’u na yamma aka sallamo su momy daga asibiti.
Washe gari ammi da hajiya kaka suka shirya domin suje yin barka. Da sukaje sunga wula qanci sabida koh kallan su momy batayi ba.

Sae da sukayi rabin awa kafin a ma basu jaririn. Hajiya kaka kuwa data d’auki jaririn sae taji tana qaunarsa sabida kamar da yayi da dady, dan haka addu’a ta hau yi mae ALLAH yasa karya kwaso halin uwar sa.

Ai kuwa da momy taga hajiya kaka tana yi mae addu’a, tana tofe shi da sauri tazo ta amshin d’anta wai nono zata bashi. Daga hajiya kaka har ammi basuji dad’i hakan ba. Ba shiru suka tattara suka tafi gida.

Ranar suna yaro yaci sunansa ABDUL MAJID, an sha suna anyi budiri duk da ba wani ‘yan uwan arziqi bane da momy. Itama ammi taje gidan suna amma hajiya kaka tace bazata ba. Duk wandda ya kalli mashkhur a gidan sunan abdul majid sae ya tanka sabida tsabar kyan sa. Harda masu cewa ALLAH yasa abdul majid yayi kama da shi.

Mashkhur ruwa biyu ne yana kama da ammi yana kama da dady. Amma yafi kama da ammi, ammi kyakyawace ta farko. Kawai dae mashkhur hasken fatar dady ya kwaso, sai yanayin jiki sai wasu abubuwan da baza’a rasa ba amma fuskar sa ta ammi ce. Yanzu mashkhur shekarar shi uku. ya bawa abdul majid shekara uku kenan.

Bayan momy tayi arba’in dady ya kammala gina gidan sa. Suka fara shirye-shryen komawa. Ranar juma’a ammi da hajiya kaka suka tare, ita kuma momy sae ranar asabar ta tare. Part d’in ammi da ban part d’in hjy kaka da ban sai part d’in momy itama da ban. Gida ne na al farma.

Duk wandda ya kalli gidan nan sae ya qara, haka sazila duk wandda ya shiga sae ya tofa al barkacin bakinsa sabida gidan nan yayi kyau sosai, kuma an kashe mae dukiya.
A lokacin mashkhur aka sashi a makaran ta, sabida yana da wayo ga saurin hadda ce magana,

A ta qaice dae yana da basira da saurin d’aukar karatu. Momy tun data ga dady irin son da yakewa mashkhur takejin haushi. Taga duk gidan yadda suke son mashkhur musamman dady da hajiya kaka, hakan ba qaramin b’ata mata rai yayi ba. Rigima ta tayarwa dady wae an fi son d’an ammi ba’a son d’an ta.

Dady kuwa cikin fad’a yacewa momy dole yaso mashkhur tindda shine d’an sa na fari, kuma ae abdul majid jaririne bae girma ba. Sanna ya qara da cewa ya lura bata so hajiya kaka da ammi so d’aukar mata abdul majid Kuma bata zuwa ta gai da haiya kaka duk safiya kamar yadda ammi take, kuma bata shiga b’an garan ammi.

A tai qai ce dae ita dady ya d’orawa laifi. Ita dae ammi abidda yasa bata son zuwa wajan momy sabida wula qanci momy. Momy kuwa data ga kulluma dady ita yakewa fad’a kuma ita yake d’orwa lafi, gashi koh umma tayi asirin ta aiki saratu ta kawo mata ba kama dady yake ba, dole sa sakko ta rage rashin mutunci da girman kae.

Sae ta fara zuwa part d’in ammi suna gaisawa watarama har zama take wae hira tazo. Ita dae ammi bata saki jikinta da momy ba. Kuma kullum momy sae taje ta gaida hajiya kaka wata rana ma har abdul majid take kae wa hajiya kaka ya zauna a wajan ta har yayi bacci.Itama kakan bata yadda da itaba amma dae tana qauran abdul majid sosai,

yaran ya shiga ranta. 6an garan mashkhur kuwa yana zuwa boko wuni yake sabida harda islamiyya. Kuma kwata-kwata baya yadda da momy bare yaje wajan ta amma yana qaunar abdul majid in dae momy ta kae abdul majid wajan kaka haka mashkhur zai tayi mae wasa yana cewa abashi ya d’au ke shi..............

Yauwa zan tafi hutun Typing Bazan yi posting ranar asabar da lahadi ba (week end) zan ringa tafiya wutun mako. Abidda yasa waccan week end d’in nayi posting sabida ranar jumma’a na fara posting din littafin ADALILINTA.
Ayi hutun mako lafiya.🙏🏼

Typing.........

ADALILINTA 💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

*ina godiya ga masoyana masu bibiyar littafin nan mai suna ADALILINTA. Ina yi muku fatan alkhairi, kuma da fatan zaku cigaba da bibiya harna sauke littafin ADALILINTA.

*Dan ALLAH in kun karanta ku d’inga comment......pls. Sabida hakan shi zai bani qarfin guwar cigaba da rubutawa.💜❤️💜

*ga masu buqatar littafin ADALILINTA da nayi posting su d’inga karantawa, sai suyimin magana ta wannan Number 08142246343 WhtsApp kawai badda kira. Free book ne bana kud’i ba kuma now book.

New book on 2023
[11/06, 22:24] Maman Xuhra: “ADALILINTA”

ADALILINTA 💜❤️💜

BY AMINA BAYERO 💜❤️💜

Typing.........

* Page 20*
Haka mashkhur zai tayi mae wasaa yana cewa abashi ya d’au ke shi.........

Mashkhur yana qaunar abdul majid sosai amma sam baya son momy. Shima abdul majid d’in duk da bashi da wayo amma in yaga mashkhur sae yay ta murna yana washe baki.
Tom haka rayuwa tai, ta juyawa amma yanzu momy ta sakko sosai.

Dan yanzu tana zuwa wajan ammi kusan kullum, kuma kullum sae taje ta gai da Kakà. Itama ammi ta d’an saki jiki da momy har hira suke wataran, ammma momy tana damuwa da rashin ko in kula da mashkhur yake mata d’an ko kallo bata ishe shiba.

Tom yanzu dae abdul majid ya fara girma sosai kuma ya sake kyau ga haske kamar bala rabe fari ne tass kamar jini ya futo. Amma fa duk kyan abdl bae kae mashkhur ba, kawai dai abidda zai nunawa mashkhur shine haskyan fata, shima mashkhur ba wae bashi da hasken bane kawae dae bae kai abdul ba.

Yanzu abdul majid watan sa biyar da haihuwa, a lokacin da abdul maji yayi wata biyar a lokacin momy ta cewa dady, zata koma makaranta domin cigaba da karatu. Dady kuwa yace ba zata jeba kuma ba wani karatu da zata cigaba da zuwa, bugu da qari ga abdul majid watan shi biyar ko shekara bae yi zata fara zuwa makaranta.

Ai alokacin ba qaramin rikici aka sha a gidan nan ba, dady yace bazata koma makaranta ba koh ammi bata cigaba da karatu ba sae ita. Ita kuma momy tace Wallahi sae ta koma makaranta kuma ita ina ruwanta da ammi itama in taga dama ta koma ta cigba da karatin.

Haka akai ta rikici dady kuma yace sae dae ta zab’a ko makaranta ko aure.? Momy kuwa cewa tae Wallahi duk biyan tana so, tana son karatu kuma tanasan auran ta. Fad’a fa yaqi ci yaqi cinyewa tsakanin momy da dady dan yanzu har ta kai su hjy kaka da ammi sun san meke faruwa.

Hakan ne yasa hajiya shiga fad’an. Tacewa dady tundda ya hana momy taqi kawai ya barta taje. Dady yaso yayiwa hajiya kaka musu ita kuma hajiya kaka tace umarni ta bashi sabida bata son tashin hankali, in dae momy zata kare mutuncin ta a matsayin matar aure taje tayi karatun.

Dady yacewa hjy kaka to ya batin rainon abdul?. Hajiya kaka tace ita a bar mata shi zata raine shi.
Ai da momy ta samu labarin nan ba qaramin farin ciki tayiba, dan ranar ko bacci bata samu tayi ba sabida farin ciki.
Duk da dady baya so haka ya biyawa momy kud’in rijista da kud’in sa.

Kuma ta fara shirye-shryan “zuwa.
Lokacin da momy zata fara zuwa school d’aukar abdul tayi taje ta direwa ammi wae ta kawo mata raino, Duk dan ta qonawa ammi zuciya tae hakan.
Ammi kuwa baiwar ALLAH cikin fara’a da faran ciki ta karb’i rainon abdul d’in tace mata a dawo lafiya.

Dama shi abdul majid haquri ne da shi sosai. Koh kuka baya yi sabida tsabar haqurinsa kuma sam bashi da qiwa. Dan haka wunin ranar abdul da ammi suka shaqu, kamar maman sa.
Bayan momy ta dawo tazo ka karb’i abdul a lokacn ma har yayi bacci.

Washe gari wajan hajiya kaka ta kai shi raino. Tana ajiye shi a wajan hjy kaka ta wuce. Tana fita ammi tana shigowa hanunuta riqe da mashkhur domin su gai da hjy kaka kafin akai mashkhur makaranta. Da sallama ta shiga.
Amsa mata hjy kaka taye tare da cewa mae ya samu mijin nawa naga yana b’ata rai.

Tab’e baki ammi tayi tare da cewa kinsan mashkhur da taurin kae wae yau bazai je da abinciba dan nida dadyn sa munce sai yaje da abinci shene yake ta shan qamshi, wae harda cewa koh yaje da shi ba’ci zai ba haka zae dawo da shi.
Kallan sa hjy kaka tae tare da cewa haba baby na kayi haquri ka tafi da shi kaji.

Qara had’e rai yayi kamar wani babban mutum tare da cewa ni fa ba yanwa nake jiba dan ALLAH kakata kice su rabu dani ni bazani da shiba. Kafin hajiya kaka tayi magana ammi ta cafe zancan tare da cewa Wallahi hajiya taurin kan mashkhur ya fara isata yaro be kai ya kawo ba ya ringa tauri kae sai abidda yakae so zai yi,

Wallahi in bae shiga hankalinsa ba dukan sa zan fara yi. Haba maryam kiyi mae a hankali mana zae dae na nan gaba, ai duka baya shirya yaro. Sanan ta mae da hankalin ta kan mashkhur tace kayi haquri ka tafi da shi kaji. Shiru mashkhur yayi kamar ba da shi ake ba.

Ammi kuwa riqo hannun sa tayi tare da cewa ba magana ake ma ba bazakayi magana ba?.
Ai mashkhur ko kallan ammi bae yi ba bare ma tasa ran zai mata magana. Bugunsa ammi tayi da ge fan hannunta tare da cewa wae ba magana ake ma ba. Abin mamaki har yanzu mashkhur bai yi magana ba bare tasa ran zai bata amsa.

Da sauri hajiya kaka ta taso tare da cewa haba maryam rabu da shi dan ALLAH, yaro ne ai wata rana zai dena. Da kyau mashkhur ya d’auki abincin nan sae da hajiya kaka tai-tai mae magiya kafin ya d’auka ya wuce wajan drive.

Itama ammi juyawa tae dan ta koma part d’in ta. Abin mamaki kawae sukaji abdul majid ya kwad’a ihu. Da sauri ammi ta juyo tare da cewa hajiya lafiya yake kuka?. Wallahi nima bansan mae ya sa shi kuka ba. Shiru yayi yana ta kallan ammi, murmushi ammi tayi tare da cewa bari naje na gama aiki nazo na d’auke shi.

Har ta juya zata fita taji ya qara sakin wani kuka. Juyowa ammi ta sake yi abin mamaki kafin tayi magana kawai taga yama miqo mata hannu alamin ta d’auke shi.
Daga ammi har hajiya kaka murmushi abin ya basu, hajiya kaka tace zo ki tafi da shi sofa yake ki d’au ke shi.

Ammi tana d’aukar abdul ya fara dariya yana jin dad’i. Itama taji dad’in hakan sosai dan haka wuce wa tae da shin b’an garan ta.
Ammi tana zaune a falan ta tana bawa abdul madara taji sallama a qofar falon ta. Hijab d’in ta ta zura ta d’auki abdul ta wuce domin taga wake mata sallama.

Tana leqawa qofar falonta taga drive mashkhur riqe da bilas d’in abincin mashkhur. Qarasowa yayi tare da cewa hajiya ina kwana an tashi lafi?. Lafiya qalau har ka dawo daga kae mashkhur makarantar ne?. Ehhh hajiya na dawo sae dae nayi-nayi mashkhur ya tafi da filas d’in nan amma Wallahi hajiya yaqi.

A jiyar zuciya ammi tae tare da cewa bakomai dama tindda bae yi niyaba bazai tafid da shi ba, kawai kawo filas d’in. Bayan ammi ta karb’i filas d’in ta wuce ciki. Zama tai ta cigaba da bawa abdul madara, a zuciyar ta tana ta mamaki taurin kae da kafiya irin ta d’an nata mashkhur.

Tom yanzu momy satin ta d’aya da fara zuwa jami’a. Kuma kullum ammi take kai kawowa abdul koh ta kaiwa hajiya kaka sae ammi taje ta karb’e shi sabida ammi tana qaunar abdul sosai.
Shima mashkhur kullum sae yaje makaran ta kuma tun safe in ya tafi baya dawowa sae qarfe hudu.

Yanzu abidda ammi take ta fama da shi, shine tauri kai da kafiya irin ta mashkhur. Wani irin mugun taurin kae ne yake damunsa in dae yace ayi mai abu dole sae anyi mae, in kuma aka qiyi mae sae yayi kwana uku bai yi magana ba kamar wani kurma. Kuma yaqi cin abinci.

Hakan ba qaramin tayarwa da ammi hankali yake ba tun yana d’an shekara uku da wata biyar yake haka ina da ya girma. Mashkhur dady ne kawai yake iya tan kwara shi,, shima ba da duka ba da fad’a ba ta lallami kawai yake binsa.

A makaranta kuwa mashkhur yana mae da hankali sosai duk abindda aka biya mae yana ganewa. Yana da saurin gane karatu, shiyasa yake da farin jini sosai. yawanci duk malaman su suna son shi sosai, dama gashi da farin jini uwa uba ga kyau..............

Typing......


ADALILINTA 💜❤️💜

BY AMINA BAYERO.💜❤️💜

*free book*💜❤️💜

*ina godiya ga masoyana masu bibiyar littafin wanna littafin mai suna ADALILINTA. Ina yi muku fatan alkhairi kuma da fatan zaku cigaba da bibiya ta harna sauke littafin ADALILINTA.............💜❤️💜

*Dan ALLAH in kun karan ta ku d’inga comment.......pls sabida hakan shi zai bani qarfin guiwar cigaba da rubutawa.......💜❤️💜


ADALILITA 💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

Typing.......

*Page 21*
Yawanci duk malaman su suna son shi sosai, dama gashi da farin jini uwa uba ga kyau........

Yanzu ammi da abdul sun shaqu sosai, kamar ita ta haife shi. Itama momy taji dad’i hakan dan ita a tinaninta ammi raino kawai take mata shiyasa ma in zata fita take kaiwa ammi yanzu ta dena kai wa kaka shi. Kuma koh ta dawo daga makaranta bata d’aukar abdul a wajan ammi,

Bacci ne kawai yake had’a momy da abul, nonan ma ta dena bashi sae da daddare in ta karb’o shi daga wajan ammi, wataran kuma in yayi bacci sae da safe. 6an garan mashkhur shima yana qaunar abdul sosai, duk abidda dady ya suyo mae sai yace shi abdul zai bawa,

Haka ammi zatai ta fama da mashkhur akan abdul bazai iya ciba amma mashkhur yace Wallahi shi dae sai an bawa babyn sa. A ala dole ammi zata bashi kad’an dan mashkhur ya rabu da ita ta huta. 6an garan dady kuwa yana jin dad’in yadda ammi take son abdul majid.

Shi yasa kullum qara son ammi yake sabida yasan bata da mugun hali kamar momy. A yanzu dady haquri kawai yake da momy amma sam ta ishe shi, sabida bata bashi kulawa sam tafi kula da karantin ta. Ta mayar da shi banza koh kallo bai ishe ta bare ta sauke mae haqoqin sa na aure.

Hakan ba qaramin qonawa dady rai yake yiba yana dana sanin auran momy a rayuwar sa. Dan shi dady kawai yana d’agawa momy qafa ne sabida abdul da yake tsakaninsu in ba dan haka ba da tin ya sake ta. Yanzu dady ya fita daga safgar momy ya rabu da ita, ya mayar da hankalin sa wajan ammi.

Ammi tana bawa dady kulawa sosai, suna shan soyayar su kamar ita kad’ai ce a wajan dady. Shima dady yana bawa ammi kulawa sosai kullum son ta qaruwa yake a zuciyar ta.
Mashkhur kuwa yana ta hazaqa a makaranta dan jarabawar farko ta d’aya yazo.

Ai kuwa yasha kyauta sosai a makaran tarsu. Shima 6an garan dady da ammi kai harda ma hjy kaka sun yi mae kyauta sosai, kuma sunyi farin ciki da hakan. Itama momy ta kawowa mashkhur kyautar sa amma qiri-qiri ya qi karb’a, momy taji haushi hakan da mashkhur yayi mata ta rasa mae tayi mae ya tsane ta haka.

Ammi ce ta bawa momy haquri tare da karb’ar kyautar tana sananr da ita halan mashkhur. Momy kuwa a zuciyar ta sae da ta d’au al washin sae ta tankwara mashkhur ko ta yaya ne, sae ya gane kuskuran sa. Koh da ammi ta bawa mashkhur kyau tar momy qiri-qiri yaqi karb’a wae baya son abin momy.

Tom haka rayuwa tai, ta juyawa yanzu momy watan ta bakwai da fara zuwa makaranta. A lokacin abdul shekarar sa guda (1 years) a duniya a lokacin ya qara kyau da wayo, kuma sun shaqu da ammi sosai dan yanzu sai yayi kwana uku a wajan ammi, bai je wajan momy ba.

Wataran momy ma in tazo d’aukar shi kuka yake sakaw wai bazai jeba haka zata haqura ta koma part d’inta. Hakan kwata-kwata baya bawa momy haushi sabida yanzu ita karatun ta tasa a gaba taji dad’i hakan ma. Dan yanzu ma koh ta kan abdul bata bi tama tattara kayan sa gaba d’aya ta kaiwa ammi.

Ita gani take kamar raino take kai wa ammi. Shima dady yaji dad’i zaman abdul a wajan ammi sabida yasan halin momy yanzu sae ta bawa abdul tarbiya mara kyau, amma yasan ammi bazata tab’a bawa abdul tarbiya mara kyau ba.

Bayan shekaru biyu. (Too year a go)

Momy ta gama karatinta tsaf kuma ta karb’i takaddun karatinta. Mashkhur kuwa alokacin shekarar shi biyar (5 years) ya sake kyau da wayo amma fa har yanzu yana nan da taurin kansa, kuma har yau baya kula momy koh gaisheta baya yi. Abdul majid kuma shekararsa biyu ya sake kyau da wayo.

Abdul ba wandda ya saba da shi kamar ammi dan shi gani yake kamar ammi ce ta haife shi. Alokacin mashkhur yana prmy 1 a makaranta yana gane wa sosai kuma har yanzu shi yake zuwa ta d’aya a ajinsu.
Yanzu momy kad’ai ci ya isheta gashi kwata-kwata abdul yaqi yadda ta d’auke.

Ko momy taje ta d’aukko abdul sae ya koma wajan ammi. Hakan ba qaramin tayar wa da momy hankali yayi ba. Momy ba irin dabarar da batayi bah akan abdul ya dawo gunta amma ya fafire akan bazai dawoba.

Momy da tarasa yadda za tae wajan dady taje tace mae ya d’aukko mata abdul majid, ya dawo mata da shi. Dady kuwa haquri ya bata tare da cewa kinga abdul da ammi sun saba ki bari a hankula zai dawo wajanki, amma yanzu baza’a iya raba shi da ammi ba sun shaqu.

Hakan ba qaramin b’atawa ammi rai yayi ba, har tana cewa dady Wallahi ita bazata yadda ba ammi ta kwace mata d’anta tilo. Kuma itama ai ammi tana da d’an hasalima mashkhur ba sona yake ba koh kullo ban ishe shi. Dady cewa yayi haba halima ai mashkhur yaro ne watarana zai dae na halinsa.

Kuma itama ammi haka take ta fama da shi akan ya ringa yi miki magana amma yaqi.
Afusace momy ta tashi tare da cewa kawai ni ammi ta cuceni nida d’ana yaqi yadda dani, yanzu ammi duk yaran nan sun zama nata Eee yee? Ni kenana na tashi a babu haba yazai ai ayimin haka.

A fusace shima dady ya miqe tare da cewa kinga halima kin isheni Wallahi uban waye yace kije makarantar ki bar abdul a wajan maryam d’in ?. Ai sai da nayi-nayi da ke kan bazaki ba ki haqura da makarantar amma kikaqi koh? Kuma naga maryam (ammi) tai makwanki tayi sabida ta rungumin abdul hannu biyu kamar ita, ta haife shi koh?

Yanzu da abindda zaki saka mata kenan ai godiya ya kamata kiyi mata ba rashin mutunci ba?. Dan haka Wallahi ki shiga hankalin ki, kuma karki qara tirsa sa abdul akan sae ya dawo wajanki, in lokaci yayi ya girma kuma yayi wayo in dae ya gane kice mahifiyar sa zai dawo wajan ki. Kuma Wallahi kika qara tayar min da fad’a a gidan nan sae na sab’a miki kinjini ko?.

Yana gama fad’ar haka yabar part d’inta a zuciye. Wani bak’in cikine ya turniqe zuciyar momy, da tsana da haushin ammi. Tama rasa abidda za tai sai safa da marya take ita kad’ai a d’aki. Can kuma ta d’auki wayar ta, ta bugawa umman ta. Tana d’agawa koh sallam batayi ba ta fara gayawa umman ta abidda yake faruwa.

Bayan ta kammala gayawa mahifiyarta abidda ya faru umman, tata tace, ki kwantar da hankalinki komai yazo qarshe yanzu zan tafi wajan boka zai mana maganin komai. Tom umma amma ya za’ai nazo karb’ar maganin da zanyi amfani da shin in bokan ya bani? Kin sai dae ba zai barni nazo kaduna ba yayi fishi da ni sosai.

Ahh ki kwantar da hankalinki zuwa gobe in na karb’o sakwan bokan zan ai koh saratu ta kawo miki. Yauwa umma shi yasa nake sonki Wallahi zuwa goben in saratun tazo sai na bata sak’o ta kawo miki koh?. Yawa halimeme na ko kefa nagode, ai ba komai umma ni dae kawai naga sakwan bokan.

Karki damu nice fa zuwa gobe zakiga saratu da saqo, yanzu ma zan shirya na tafi wajan bokan. Daga haka sukayi sallama momy ta kashe wayar. Sae a lokacin momy ta samu nutsuwa, kicin ta wuce domin taci abinci, bayan taci ta qoshi ta shige d’aki tayi kwanciyar ta.

Washe gari da misalin qarfe biyu saratu ta sauka a gidan su mashkhur. Bata tsaya ko inaba ta wuce b’an garan yayar ta halima. Tare da kwad’a sallama. Momy da suri ta futo baki washe kamar gonar audiga tare da cewa a saratu har kin qaraso? Ehh Wallahi yaya halima tundda safe na tawo fa,

motar muce ma ta lallace shiyasa ma ban qaraso da wuri

Please Login or Register in order to submit comment