Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tae ta barni da jaririyar, hajiya kaka ta qarasa maganar kamar ta zubar da hawaye. Tabb gaskiya hajiya matar nan ta kwa6a miki aiki, cewar driven. Kallan sa hajiya kaka tae tare da cewa dan ALLAH bawan ALLAH koh zaka tae makamin mun ne mubi indda matar tabi koh ALLAH zae sa mu same ta?.

Jinjina kae driven yayi tare da cewa hajiya bari na gaya miki gaskiya, koh munbi matar nan Wallahi bazamu ganta ba, sabida nasan tama dad’e da guduawa dan ba tsayawa zatai’ba. Dama da yawa irin matan nan in sunyi cikin shege sun haife in dare yayi sae suzo , su wurgar da yaran. Ina gama itama matar zuwa tai, ta yar da yarinyar ta had’u da ke a wajan ta baki ita.

Hajiya Barima nagaya miki wani abu , ni fa drive ne kuma na saba bi ta wanna hanyar, kinga in muka shiga cikin jejin nan Wallahi wahala zamu sha. Kuma bayan jejin nan wani babban asibiti ne sae kuma gidan marayu. Dan haka hajiya bari na baki shawa kawae ki tafi da yarinyar nan gida, kinga zuwa gobe koh wajan ‘yan sadda ne sae ki kai ta.

In yaso daga can su kae ta gidan marayu, in kuma baki yadda da hakan ba to hajiya kiyar da ‘yar nan a wajan nan ki kama hanyar ki kitafi... shuru hajiya kaka tae tana sauraran driven nan. Yana gama fad’ar hakan kafin hajiya kaka tayi magana abdul yace, aaa hajiya kaka karki yar da babyn nan ina sonta, kuma maman ta tace inkula da ita.

Shiru hajiya kaka tayi tana tinanin mafita, ita dae tasan koh abdul bae ce karta yar da yarinyar ba, ba zata tab’a yar da itaba. Kuma haka nan taji tana tausayin yarinyar, muryar driven nan ce ta dawo da ita daga duniyar tinanin da ta tafi. Hajiya in kin gama tinanin sae ki biyo ni mu koma muga koh motar zata tashi, in kuma bata tashiba sae na raka ku, ku samu wata, dan dare ya farayi.

Dan tun d’azu dana tafi ban samu mae gyaran motar ba. Jiki a sanyaye hajiya kaka ta ruqo hannun abdul, suka bi bayan driven nan. Suna zuwa driven ya shiga matar ya fara qoqarin tayar da ita. Abin mamaki kawai sukaga motar ta tashi. Da sauri driven ya d’ago ya kalli hajiya kaka tare da cewa hajiya kinga ikwan ALLAH motar ta kama, kwai ku shigo mu tafi.

Qara rungume jaririyar a qirjin ta hajiya kaka tayi tare da bud’e murfin motar, bayan ta bud’e murfin ta ruqo hanun abdul, suka shiga ciki motar. Ba 6ata lokaci drive ya kama hanya suka fara tafiya. Gaskiya hajiya yarinyar nan tana da bai’wa a tattare da ita, ceawar drive. Kallan sa hajiya kaka tayi tare da cewa!!! Waace yarinyar kenan?.

Bata amsa driven yayi da cewa jaririyar da take annunki mana. Me kagani kace haka malam?. Hmm hajiya inaga fa mutuwar motar nan tawa kawae tsari ne, na uban giji, kuma ni na gamsu da hakan kwai ALLAH ne yayi zaki had’u da yarinyar nan. Nunfasawa hajiya kaka tayi tare da cewa ba mamaki, zata iya yuyuwa hakan ne.

Nide hajiya zan baki shawara bakisan baiwar da take tattara da yarinyar nan ba, dan haka in dae zaki iya riqe yarinyar nan kawai ki riqe ta. Jinjina kae hajiya kaka tayi tare da cewa ni dae ina ji ajikina ba shegiya bace yarin yar nan, sabida na gamsu da bayanin da mahaifiyar tayi min, dan haka insha ALLAH sae nayi qoqari na nemawa yarinyar nan mahaifan ta.

Jinjina kae driven yayi tare da cewa toh hajiya ALLAH ya baki ikwan hakan, kuma ALLAH ya raya ta, yasa ta zama abin al fahari. Ameen malam, daga haka suaka cigaba da tafiya, daga driven har hajiya kaka ba wadda ya sake cewa komai. Basu suka shigo garin kano ba sae wajan qarfe shad’aya da rabi (11:30pm) na dare. Koh da suka shigo garin kano har qofar gida driven ya kawo su.

Lokacin ma abdul har yayi bacci. Tashin abdul hajiya tayi suka fita daga motar, ko da hajiya kaka ta tanbaya nawa zata bawa driven haka yace ta barshi kawai. Ita kuma hajiya kaka tace aaa sae ta bashi ae ya qona man motar sa, tindda daga kaduna har kano ya kawo su, kuma gashi har qofar gida ya kawo su. Haba hajiya kawai ki barshi nima ae d’an garin kano ne koh ban kawo ku baa ae dole nazo kanon ko?.

Haka dae driven sukai ta jayayya da hajiya kaka, daga qarshe dae driven bai kar6i kud’in hajiya kaka ba, amma hajiya kaka ta roqeshi zuwa gobe ya dawo, ba musu drive ya amince. Yana tafiya hajiya kaka ta riqe hanun abdul suka qarasa qofar get d’in gidan. Bugu get d’in hajiya kaka ta farayi, tana cikin bugun qofar taga motar dady ta haske su da fitila tana horn.

Dady yana ganin su hajiya kaka da sauri ya bud’e murfin motar tasa ya futo. Qarasuwa inda suke yayi tare da cewa hajiya ta lafiya na ganku a cikin darann nan kun dawo? Yanzu fa wajan qarfe sha biyun dare (12:00am) kuma nida mukayi da ke sai ranar asabar zan!!!!! Ai dady bae kai da qarasa maganar da zai yi ba ya lura da jaririyar da take hanun hajiya kaka.

Cikin mamaki yace hajiya wanna wace jaririya ce haka?. Abdul ne yace dady maman tace ta bamu ita kuma!!!! kafin ya qarasa maganar hajiya kaka ta katse shi ta hanyar cewa mu shiga ciki zan yima baya ni. Jinjina kae dady yayi tare da cewa yanzu muma muka dawo daga asibiti maryam (ammi) ce ta haihu, ta samu MACE, yanzu ma haka suna cikin mota ita da halima (momy).

Masha ALLAH kace wannan karan maryam ALLAH ya azirta, ta da mace, jinjina kae dady yayi tare da cewa ehh Wallahi rukayya ta samu ‘yar uwa. Nunfashi hajiya kaka ta sauke tare da cewa yanzu sae ka bud’e mu shiga tin d’azu nake bugu amma mae gadi bae bud’e ba, ehh hajiya inaga fa bacci yake. Daga haka dady ya ciro key ya bud’e gidan.

Yana bud’ewa hajiaya kaka ta kama hanun Abdul suka shiga ciki. Shikuma dady get d’in ya zuge sanan ya koma motar ya shugu da ita. Yana shigowa da motar ya bud’ewa su ammi murfin motar. Ammi ce ta fara futowa tana tafiya a hankula sae momy biya da ita hanun momy riqe da babyn ammi.

abdul da yake tsaye shida hajiya kaka a gefe da gudu ya fizge hanunsa daga hanun hajiya kaka ya nufi ammi a guje. Ita kuma hajiya kaka ta shige ciki. Abdul yana qarsawa wajan ammi ya fad’a jikin ta da gudu. Murmushi ammi tae tare da cewa oyoyo my big son ya hanya? Da fatan dae kun dawo lafiya?. Dariya abdul yayi tare da cewa lafiya qalau ammina kinsan mene?

Girgiza kae ammi tayi tare da cewa aa my son sae ka fad’a. Murmushi abdul yayi tare da cewa wata maman baby ce ta bamu baby nida hajiya kaka. Dariya ammi tae tare da cewa kae my son wacece maman babyn nan? Kudai ‘yar tsana hajiya ta siya ma a hanya, ko kuma dan kaga baby a hanun momy?. Aaa ammi nifa ba ‘yar tsana aka suya min ba kinga ma takaddar da maman baby ta bani,

Ya fad’a tare da miqa mata takaddar da matar ta ba bashi, karb’a ammi tai tana murmushi, jin muryar momy tae tana cewa au wae ke maganar wasa kike d’aukan tane? Koh d’azu da dadyn mashkhur ya tsaya bad’e get bakiga jaririya a hanun hajiya ba?. Da sauri ammi ta juyo ta kalli momy tare da cewa Wallahi ban kulaba kinsan ae harna fara bacci a lokacin.

Ta6e baki momy tae tare da cewa ae muna shigowa hajiya ta wuce ciki da jaririyar a hanunta, sae mu shiga ciki ki ganewa idon ki, kuma muji ‘yar ta uban waye, koh a gidan mutuwar ta samu ta!!! Maganar dady ce ta katse, wadda ya dawo daga rufe get d’in gidan saka makwan mae gadin gidan ya tafi bacci.

Ko zo mushiga da ga ciki koh? Ba musu suka kama hanyar shiga cikin gidan.
Suna shiga gidan suka tarar da hajiya kaka afalan ammi tare da mashkhur riqe da babyn da hajiya kaka tazo da ita, tv a kunne da alama mashkhur bai yi bacci ba ya tsaya kallan dare. Da sauri mashkhur ya taso hannu riqe da babyn nan tare da cewa saninku da zuwa,

Momy naga kuma wata babyn a hanunki ko twins muka samu ne? Ya fad’a yana washe baki. Da sauri momy ta girgiza kae tare da cewa aa ba twins bane ammi dae ‘ya d’aya ta haifa kuma ga tanan a hanuna, ita kuma wanan ta hanun taka ban san daga indda kakar ka ta samo taba. Da sauri mashkhur ya juya ya kalli hajiya kaka tare da cewa wae da gaske hajiya kaka ba ammi ce ta haifi wanna kyakyawar babyn ba?

Kuma a ina kika samu jaririya haka?. Muryar dady ce ta katse shi da cewa keee mae sunan abba ka shiga hankalin ka har ka kae girman da zata titsiye hajiya kana tanbayar ta? Zan sab’a ma ka sake yiwa hajiya kalar tanbayar nan. Sunkuyar da kai mashkhur yayi tare da cewa insha ALLAH dady bazan qara ba. Alokacin mashkhur bae fi shekara goma ba (10 years) shi kuma Abdul bae fi shekara takwas ba (7 years).............

Ina godiya ga masu yimin ya jiki, kuma ina yi muku fatan alkhairi. Kuma duk wadda yake min comment..... kuma yaga ban sadaukar da page gare shiba, yayi haquri nan gaba zan sad’aukar mae da shi..

*Fatan alkhairi ga duk mae bibiyar littafin ADALILINTA, kuma da fatan zaku cigaba da bibiyata harna sauke shi.

*ga masu buqatar karanta littafin ADALILINTA, da nayi posting sae suyimin magana ta wannan number 08142246343 WhtsApp kawai bandda kira, free book ne bana kud’a ba kuma new book.

Now book on 2023
[11/06, 22:24] Maman Xuhra: “ADALILINTA”
ADALILINTA💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

Typing..........

*Page 28*
Alokacin mashkhur bae fi shekara goma ba (10 years) shi kuma abdul bae fi shekara bakwai ba (7 years)

Mashkhur komawa yayi kusa da hajiya kaka ya zauna hannu riqe da jaririyar da hajiya kaka tazo da ita. Itama ammi da dady zama sukayi akan kujera, shima abdul kusa da ammi ya zauna. Momy kuwa qarasawa tai indda hajiya kaka take zaune ita da mashkhur, tare da miqawa hajiya kaka baby tana cewa!!!

Hajiya ga jikarki nan fa an samu mace, karb’ar ta hajiya kaka tae tare da cewa masha ALLAH, ALLAH ya raya mana ita. Ta6e baki momy tae tare da cewa Ameen, tana gama fad’in haka tace mashkhur ina rukee take d’aukko min ita, ba musu mashkhur ya ajiyewa babyn da take hanun sa kusa da hajiya kaka ya kama hanya shiga d’aki.

Bae fi minti biyar(5 minti) ba ya futo hanunsa ruqe da rukee, yana qarasowa ya miqawa momy ita. Momy tana kar6ar rukee ta kama hanya domin tafiya part d’in ta. Tana qoqarin fita taji muryar dady ta katseta da cewa halima ina zaki? Juyowa tai tare da cewa 6an gare na zan tafi na kwanta dan nagaji bacci nake ji.

Kallanta dady yayi tare da cewa to ki dawo ki zauna hajiya za tae magana da mu, game da jaririyar da tazo da ita. Ba musu momy ta dawo ta zauna, bayan ta zauna ya kalli hajiya kaka tare da cewa hajiya muna sauraran ki?. Jinjina kae hajiya kaka tae tare da miqewa tsaye. ajiye jaririyar ammi da take hanunta tai kusa da jaririyar da tazo da ita.

Bayan ta kammala kwantar da ita ta dowo ta zauna. Tana zama ta fara bud’e taro da addu’a bayan ta kammala addu’a ta fara magana kamar haka!! Dama munyi da baban abdul zaizo ya d’auke mu ranar asabar, amma sae gashi mun kasa zama a gidan mutuwar, sabida mutane sunyi yawa, wajan kwanciya ma da qyar muka samu.

Kuma gashi Abdul sae kuka yake min ya gaji wae mu dawo gida. Dan haka na yanke shawarar mu dawo gida, haka muka kama hanya da yamma liqis muka tawo. daga haka hajiya kaka ta kwashe labarin abidda ya faru ta fad’awa su dady, tun daga futar drive sallah har yadda akai motar ta samu matsala, da kuma fitar da sukayi samun wata motar har suka had’u da wannan matar

Da bayanin da tae musu da takaddar da ta bawa abdul, da kuma yadda akai matar ta gudu, haka dae hajiya kaka tae ta bawa su dady labari har yadda sukayi da driven da kuma yadda aki driven ya kawo su har qofar gida. Jikin kowa yayi sanyi a wajan nan badda momy da taji haushin yarinyar ma ya kamata, kae har mashkhur da baya son mutane sae da yaji ya tausayawa yarinyar.

Maganar dady ce ta dawo da su daga tinanin da suka tafi. Cewa yayi yanzu hajiya ina takaddar take?. Kalan Abdul hajiya tae tare da cewa abdul ina takaddar da matar nan ta baka?, da sauri abdul ya kalli ammi tare da cewa ammina ina takaddar da na baki? Da sauri ammi ta d’aukko takaddar a gefan ta dama anan ta ajiye, sanan ta miqawa dady da yake zaune a kusa da ita.

A hanzar ce dady ya kar6a takaddar daga hannun ammi tare da bud’ewa dan yaga mae ke rubuce a takaddar, yana bud’ewa ya zubawa rubutun ido tare da fara karantwa a fili dan kowa yaji. Rubutun da akayi bae wuce layi biyar ba. Abidda aka rubuta aciki shine.

DAN ALLAH GA YARINYA TA NAN AMNA A KULAMIN ITA NA WASU LOKUTAN. TANA CIKIN HATSARI SHIYA NA YI NESA DA ITA SABIDA INA SON TAYI RAYUWA MAE TSAYI DAN ALLAH A KULAMIN DA ITA. BAYAN SHEKARA 2 ZUWA UKU DAN ALLAH A TINT6ENI TA WANAN NUMBER.

Bayan Number da matar ta rubuta a cikin takaddar harda addressed d’in gidan da za’a kae yarinyar bayan wasu shekarun. Amma kwata-kwata ba sunan ta ko na mahifin yarinyar. kuma daga qarshe ta rubuta dan ALLAH kar’a dawo da ita yanzu sabida rayuwar ta tana cikin hatasari in dae, zata zauna da ni da mahaifin.

Abin ya d’aurewa kowa a wajan kae in ka cire momy, da sam ita bata gamsu da bayanin ba ma🙅‍♀️. Dady jinjina kae yayi tare da cewa yanzu hajiya mene shawararki game da yarinyar nan?. Shuru hajiya kaka tae tare da cewa inaga gaskiya kawai mu nemi iyayan ta tindda ga address d’in gidan kawai mu mayar musu da ‘yar su.

hakan zai fi , sabida gaskiya ina tausayawa yarinyar nan kwara mu mayar da ita wajan iyayyan ta, shine gatan da zamu iya yi mata. Shuru dady yayi yana sauraran abidda hajiya take cewa. Bayan hajiya ta gama maganar dady ya d’ora da cewa hakane hajiya amma sae nake ganin mae zai hana mu tae maki rayuwar yarinyar nan in zamu iya?.

Shuru hajiya kaka tayi kafin tace nima ada nayi tinanin hakan, amma daga baya naga gwara mu mayar da yarinyar nan gaban iyayan ta, sabida yarinyar nan qaramace kuma yau aka haifeta tafi buqatar kulawar mahifiyar ta fiye da kowa, kuma kaga sae muji wana hatsari yar nan take fuskan ta da har iyayan ta bazasu iya zama da ita haka ba.

Jijina kae dady yayi tare da cewa tom shikenan hajiya insha ALLAH za’a mayar da ita gidan iyayan ta kamar yadda kike so, zuwa gobe sae muje mu mayar da ita koh?. Kafin hajiya kaka ta bashi amsa ammi ta cafe zancan da cewa!!! amma hajiya sae nake ganin kamar wannan ba mafita bace, sabida duk abidda zai sa uwa ta d’auki d’an da ta haifa kuma da cikin halak ta bada shi AMANA ga wadda bata saniba to fa abinnan ba qaramin bane,

Kawai hajiya ni a ganina mu tausayawa jaririyar nan mu tae maki rayuwar ta mu riqe ta zuwa na wasu lokutan koh, nan da shekara d’aya ne. Kafin nan yarinyar nan ta fara wayo kuma nasan wannan lokacin komai ya lafa kuma zata iya tsallake atsarin da take ciki a yanzu, nasan kuma mahaifiyar ta zata kar6e ta da hanu biyu, kuma tayi farin ciki da zuwan ta.

Daga hajiya kaka har dady sun gamsu da maganar ammi, dady ya fud’e baki zai yi magana kenan momy ta riga shi magana da cewa!! Haba maryam wannan wace kalar banzar shawara ce haka? Akan mae zamu riqe tsinttanciyar yarin yarnan da bamu son asalinta ba? Tom Wallahi in kina tinanin yarinyar nan zata zauna a gidan nan ki de na, dan Wallahi bazamu zauna da itaba.

Tana rufe bakin ta taji dady yace kee dalla rufe mana baki, ashe halima baki da tinanin bare tausayi, tom Wallahi baki iska ki hana yarin yar nan zama’a gidan nan ba, ke barima kije inddai kikaga yarinyar nan bata zauna a gidan nan ba to sae dae hajiya ce tace bazata zauna ba. Yana qarasa maganar ya kalli hajiya kaka alamin so yake yaji ta bakinsa.

Sae da hajiya kaka tabi kowa acikinsu da ido bandda mashkhur da abdul, sanna tace!!! Kwai Abubakar ka barta agidannan na wasu lokuta kamar yadda marya(ammi) ta bamu shawara. Haba jajiya yanzu dan ALLAH sae mu zauna da yarinyar da bamu san asalinta ba? Cewar momy

D’ aure fuska hajiya kaka tayi tare da cewa halima ki shiga hankalinki kafin na 6ata miki raii, haba qaramar yarinya ma sae kin nuna mata rashin imani?, Wallahi karna sake jin kin tofa magana mara kyau game da yarinyar nan kina jina?. A daqile momy ta bud’e baki tace naji, tana gama fad’ar hakan ta tashi ta wuce part d’in ta.

Bayan ta fita dady ya kalli hajiya kaka yace hajiya sae kuna haquri da wasu halaye na halima, dan ALLAH kiyi haquri hajiya, nunfasawa hajiya kaka tayi tare da cewa bakomai Abubakar. Sannan ta d’ora da cewa!! Yauwa maryam (ammi) yanzu sae ki had’a da ‘yar da kika haifa sae ki d’inga rainon su kina shayar da su kafin muga abidda ALLAH zae yi koh?.

Jinjina kae ammi tai tare da cewa ehh hakane amma fa har yanzu ruwan nono na bae zoba sae dae na fara basu mada, kafin yazo. Tom shikenan ki fara basu madarar kafin ruwan nonon yazo cewar hajiya kaka, daga dady har ammi sun yadda da shawarar nan. Dady kuwa cewa yayi kae mashkhur ka d’auki abdul kuje ku kwanta, dare yayi gobe zakuje makaran ta fa.

Tom dady yana fad’ar haka ya taso ya fara qoqarin riqe hannun abdul. Shi kuwa abdul kuka ya saka wae shi bazai tafiba sae an bashi babyn sa sun tafi da ita, shi tare da ita zai kwana. Dukan su dariya sukayi har shi kanshi mashkhur duk da kuwa bae so hakan ba. Ammi kuwa cewa tae ka bari zuwa gobe sae kazo ka d’auke ta kaji abdul d’ina.

Wani saban kukan ya saki tare da cewa shifa wallahi sae an bashi babyn sa ya tafi da ita. Cikin nishad’i dady yace abdul zo ka fad’a min taya akai wannan ta zama babyn ka? Cikin zaulaya dady yayi maganar, dena kukan abdul yayi tare da cewa ai maman babyn ce tace na kula mata da babayn kuma tace qan watace koh hajiya kaka?.

Dariya suka qarayi hajiya kaka tace hakane abdul toh zo ka nunamin wace babyn taka a cikin su? Da gudu abdul ya qarasa kusa da hajiya kaka ya fara leqan fuskar jariren, da suke kusa da ita a kwance. Yana gama leqa fuskokin jarire ya nuna wandda suka zo da ita da ya tsa yace ga babyn nawa nan. Dariya suka sake yi sanan hajiya kaka tace aa ba ita bace d’ayar ce, cikin zaulaya ta fad’i hakan..............

Wanan shafin na sadaukar da shi ga maman xuhura sabida tana yimin comment..... ina miki fatan alkhairi .......

ADALILINTA💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

Typing........

*page 29*
Dariya suka sake yi sanan hajiya kaka tace aa ba ita bace d’ayar ce, cikin zaulaya ta fad’i hakan........


Bibbiga qafafuwa ya farayi yana cewaw Wallahi ni dae wannan ce baby na wannan kuma baby ammi ce. To taya akayi ka gane babyn taka?, cewar ammi, murmushin su na yara abdul yayi tare da cewa ae ita baby na da farin towel aka rufeta, ita kuma babyn ammi da zani aka rife ta, dariya suka sake yi suna qara jijina wayo irin na abdul.

Hajiya kaka ce ta katsewa su da cewa tom shikenan mun yadda babyn kace amma kaje ka kwanta in aka gama yi mata wanka aka bata madara zan kawo maka ita. Dariya abdul yayi tare da cewa tom shikenan hajiya kaka bari nima naje yaya mashkhur yayi min wanka koh? Mumurshi hajiya kaka tayi tare da cewa tom shikenan jeka sae na kawo ma babyn taka.

Daga haka hajiya tacewa mashkhur, ka tafi da shi kayi mae wanka ka bashi abinci. Tom shikenan hajiya kaka sae da safan ku ALLAH ya tashe mu lafiya, dukan su suka had’a baki wajan cewa Ameen, daga haka mashkhur yaja hanun abdul suka shiga ciki. Bayan su shiga ciki mashkhur yayi wa abdul wanka sanan ya shiga kitchen ya zubo mae abinci.

Bayan abdul yaci abinci suka hau kan bed suka kwanta. Haka abdul yay ta isar mashkhur da mita akan ba’a kawo me babyn sa ba, shikuma mashkhur yana bashi haquri!! Kayi haquri abdul ka kwanta hajiya kaka zata kawo ma babyn ka daga haka bacci ya kwashe abdul, shi dae mashkhur haka yay ta tinanin kala-kala game da babyn abdul yana runtse idanuwansa yake ganin ta, acikin farin towel d’in nan

Hakan nan yaji yana tausayin ta, kuma yana son jin wana kalar hatsare take ciki in dae aka mayar da ita wajan iyayan ta nan kusa, daga haka bacci barawo ya kwashe shi.
6an garan su hajiya kaka kuwa bayan tafiyar su abdul, ban d’aki ta shiga ta taro ruwan zafi a bokiti, sabida tayiwa babyn abdul wanka.

Bayan ta gama yi mata wanka aka canza mata wasu kayan. Kallan ammi hajiya kaka tae da take zaune a kusa da dady ta ce mata, maryam kinsa mene? Aaa hajiya mae ya faru? Kinsan kuwa tindda muka tawo da yarinyar nan batayi kuka ba sae da yanzu da zan mata wankan nan. Jinjina kae dady da ammi suka, sanan ammi tace gaskiya daga gani hajiya yarinyar nan zatai haquri sosai.

Nima abidda nake tinani kenan, cewar hajiya kaka. Shikuwa dady tausayin yarinyar ne ya kama shi har cikin zuciyar sa yaji yana son yarinyar. Miqewa dady yayi ya karb’i yarinyar daga hanun hajiya kaka ya dawo ya zauna daga indda ya tashi tare da cewa ammi, maryam zo kiga kyakyawar yarinya masha ALLAH.

Laqa fuskar ta ammi tayi ta zubawa yarinyar ido. Fara ce tas dan har wani ja ma take, ga bakin ta jajawur, hancinta madae-dae cine, idanuwanta tama haka ga saje tindda ga kan ta har qoshin ta, ta zubawa dady ido sae kallan sa take. Wani so da qaunar yarinyar ne ya kama ammi sae taji kamar ita ta haife ta, ga tausayin ta da take ji.

Maganar hajiya kaka ce ta qatse su daga kallan babyn da suke. Cewa tai Ni dae zan tafi part d’ina , sae kiyi qoqarin bata madara dan nasan yinwa take ji. Tom shikenan hajiya kaka ALLAH ya tashe mu lafiya cewar ammi, shi kuwa dady miqawa ammi jaririyar yayi tare da miqewa dan ya raka hajiya kaka part d’in ta.

Bayan ya dawo daga raka hajiya kaka part d’in ta da kansa ya d’akko madara da fida dan su bawa jariran madara. Da tai makwan ammi suka gama had’a madarar. Babyn abdul suka fara bawa madarar bayan ta sha ta qoshi, itama babyn ammi aka bata tasha. Bayan sun gama basu madarar ammi ta d’auki babyn

Please Login or Register in order to submit comment