Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta6a ganinta ba. Wae ina abdul yake ne?. Kwab’e fuska momy tayi tare da cewa inafa abdul zai biyoni yana tare da ‘yar sadakar yarinyar nan da kuma uwar goyansa ina zai biyo ni.

Tabb gaskiya yaya halima kinyi sake yanzu shikenan matar nan ta qwace abdu?. Ke dae bari saratu wallahi yanzu abdul sae yayi sati bae zo wajena ba, shiyasa ae nake hana rukee zuwa part d’in ammi, kar inje itama a kwace min ita. Ai kuwa dae yaya halima kinyi dae dae, ke dai bari ae yanzu komai zai zo qarshe tindda boka ya kusan kashe mana shegiya.

Kinga bama abdul d’in ba har sauran ‘yayan ke zaki cigaba da ruqe su. Dariyar mugunta momy tae tare da cewa ai kuwa zasu ci uban su, ita kuma ‘yar banzar yarinyar nan yadda ita zanyi. Haka dae momy da saratu suka cigaba da tattauna mugun quddurin su, daga qarshe momy tayiwa saratu sallam, ta wuce kano.

Sae da magariba su momy suka isa kano. Bayan momy ta isa gida part d’inta ta wuce, tana shiga tayi wanka taci abinci, ta kwanta zatai bacci kenan ta fara naquda. Tana cikin wanna halin dady ya shigo b’an garanta, ba bata lokaci ya d’auke ta ita da hajiya kaka suka tafi asibiti, ita kuma ammi ta zauna a gida sabida su zahra da ilham.

Suna isa asibiti aka shigar da ita d’akin haihuwa, ba 6ata lokaci ta haifi zan kad’ed’iyar ‘yar ta mace. Itama dae still da su abdul take kama. Kuma a daran aka sallamo su. Bayan an sallamo su, ammi ta shigo tayi mata barka, haka yaran gidan sukae ta shiga d’aukar baby. Yanzu momy ta fara tinanin taya zata bawa ammi maganin boka, tindda yanzu tasan ammi zata ringa shigowa b’an garanta sabida ta haihu.

Can wata dabara ta fad’o mata, murmushi tayi tare da tashi ta shige d’aki. Jakar ta data dawo da ita daga kaduna ta bud’e. Maganin boka nan ta ciro, tare da alkakin da ta tawo da shi. Dama tana da wata ajiyayyiyar zuma a d’akin ta. D’akko ta tayi tare da bude robar zumar sanna ta barbad’a maganin bokan, tasa yatsanta ta juya.

Bayan ta juya ta zuba zumar alkakin, bayan ta gama zubawa ta kulle shi a leda. Falo ta wuce domin d’akko jaririyar ta su kwanta. Har lokacin dady bae shigo part d’in ta ba dare yayi sosai kuma gashi yau a part d’in yake. Azuciyarta ta ayyana yana tare da ammi, bataji dad’in haka ba. Qarasawa tai bakin qofar part d’in domin ta rufe.

Tana qoqarin rufewa ta hango dady da ammi suna tafe suna dariya da alamin hira sukeyi. Wani haushine ya sake rufe ta can kuma ta saki murmushi mugunta, tare juyawa da zauri ta shiga ciki, tana shiga cikin d’akinta ta d’auko wanan alkakin da ta kulle a leda . Tana dauka tai sauri ta fice ta koma falo..........

ADALILINTA💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

Typing.........


*page 32*
Tana shiga cikin d’akin ta d’auko wanan alkakin data kulle a leda. Tana dauka tai sauri ta fice ta koma falo.............

A zaune ta tarar da ammi, shikuma dady yana qoqarin shiga ya kirawo ta. Washe baki tayi tare da cewa ah maryam kece kika futo da daddaran nan koh mijin naki kika rako ne, murmushi ammi tayi tare da cewa aaa kawai dae mun tawo tare ne shi zuwa yayi ya kwanta ni kuma farfesun nama na dafa miki, sabida kice koh kyaji kwarin jikinki, tindda kinga baki dad’e da haihuwa ba.

Cikin fara’a da sakin fuska momy ta ce nagod sosai, qarasowa tayi tare da karb’ar filas d’in, tana karb’a ta migawa ammi ledar alkakin tare da cewa bismilla ga al kaki nan daga kaduna naza da shi, nima yanzu na d’aukko shi inaci. Girgiza kae ammi tayi tare da cewa Alhamdulilahi, bazan iyaci ba sabida bana son cin zaqi in zan kwanta.

Had’e rai momy tai tare da cewa gaskiya banji dad’i ba, ai sae nayi tinaninma bakya son cin abunane, gaskiya koh yayane kici. Murmushi ammi tayi tare da cewa haba halima mae yayi zafi haka bari dae naci koh kad’an ne ta fad’a tare da karb’ar laidar hannun momyn. Itama momy mumrmushi tai tare da cewa yauwa koke fa. Bud’e ledar ammi tayi, guda d’aya ta d’auka.

Miqewa tai tare da cewa tom bari na koma 6an garena, kar su ilham su tashi daga bacci su fara kuka, da sauri momy ta kalli ammi tare da cewa to ai banga kin ciba?. Dariya ammi tayi tare da cewa bari dae naci alkakin nan hankalinki ya kwanta, tana fad’in haka takai alkakin bakin ta tafara ci, sae dai kashhh ammi ta manta batayi bismillah ba, duk abindda ammi zataci tana bismilla amma bandda wanan karon,

Ko da yake in ALLAH yayi qaddara zata same ka, ba yadda ka iya. Daga haka ammi tayiwa momy da dady sallama ta wuce part d’in ta. Tana komawa part d’inta ta samu ilham tana ta kuka, tare da yaqushin zahra. Dama haka ilham take in dae aka kwantar da su waje d’aya da zahra tana tashi daga bacci zata fara yaqushin zahra har sae ta tasheta daga bacci.

Madara ta had’a ta basu bayan ta basu ta sake kwantar da su, tana kwantar da su suka fara bacci. Miqewa tai ta wuce d’akin su mashkhur.
A nitse ta murd’a handle d’in qofar ta shiga, a zaune ta tarar da mashkhur yana ta karatun QUR’ANI. Kallan tuhuma ta fara yi mae, wato alamin yayi mata wani lefin ko ya qijin magana.

Murmushi yayi tare da sunkuyar da kae, itama murmushin taye tare da wuce gadn su faraq da haidar. Bancin su suke cikin kwanciyar hankali, dama yanzu faruq da haidar a gado d’aya suke kwana, chan gaba kuma gadan mashkhur da abdul. Tana qarasawa ta hau kan gadan a hankali sabida karta tashe su.

Addu’a ta fara yi musu, bayan ta gama ta tofe su da addu’a, sanna ta sake lillib’e da bargo. Miqewa tai ta wuce gadan su abdul, har yanzu mashkhur bae ajiye qur’ani ba karatu yake ta yi. Tana qarasawa ta zauna kusa da abdul ta fara yimai addu’a shima, bayan ta gama ta tofe shi da addu’ar. Daga haka ta miqe ta koma kusa da mashkhur ta zauna.

Zuba mae ido tayi tana sauraran karan qira’arsa abin sha’awa ya firge ta sosai, sai da yakai qarshan aya sanan yayi hamdala tare da ajiaye Qur’anin. Yana ajiyewa tin kafin ammi tayi maga yayi sauri ya riqe hanunta tare da cewa dan ALLAH ammina kiyi haquri. Ajiyar zuciya ammi ta saki tare da cewa toh mashkhur in ban haqura ba ya zan yi?

Ni ba hanaka karatu nayi ba amma bana so ka ringa kae dare kamar haka bakayi bacci ba, kaga daga safe dae har zuwa yamma kana makaranta in kuma ka dawo kayi karatu, shine zaka raba dare kana karatu, ka ringa samun hutu mana. Wallahi momy so nake na qarasa haddace surar nan kinga saura sura uku fa mu fara shirye-shryan sauka, amma kiyi haquri zan dai na insha ALLAH.

Tom shikenan mashkhur ALLAH ya tai maka kuma ya nuna mana lokacin saukar. Ammen ammina, murmushi ammi tayi tare da cewa wae mashkhur kana so na kuwa? Da sauri ya kalle ta tare da cewa haba ammina, ai duk duniya ba wandda nake so kamar ki. Murmushi ammi tayi dama kawai tsokanar shi take, sabida tasan mashkhur yana qaunar ta sosai.

Amma ammi sabida mae kika yimin wanan tanbayar?. Ba dole na ringa kokwanto ba, baka nuna min kulawa a matsayina na mahaifiyar ka, koh baka ga yadda abdul yake yimin ba?. Kwab’e fuska yayi tare da cewa haba ammina wallahi inason ki sosai. Dariya ammi tae tare da jan kumatun sa, kai da wasa nake ma.

Dariya yayi tare da bud’e mata hannu alamun su hugging d’in juna, matsowa tayi suka rungume juna. Lumshe ido mashkhur yayi sabida yaji dad’i hakan, itama hajiyar zuciya ta sauke sabida harga ALLAH ammi tana son mashkhur, kawai wasu daga cikin halayan sa ne bata so. Sae tin kunnan sa takai bakainta ta fara yimae addu’a.

Lumshe ido kawai mashkhur yake sabida har cikin zuciyar ta yake jin addu’a ga wani irin son ammi da yake qaruwa a zuciyar sa. Sun jima a haka daga qarshe ammi ta sake shi, kallan sa tayi tare da cewa ka qara yin addu’a kafin ka kwanta, tom shikenan ammi zanyi, kiss ta yi mae a kumatu tare da yi mae sallam ta fuce.

Tana fita mashkhur yayi addu’a tare da kwanciya ya rufe jikin sa da bargo. Tinani ya farayi, akan abidda yakewa ammi. Sam bae san sabida mae yake jin maganar momy fiye da ammi ba. In ammi ta gaya mae magana ba sosai yake jiba, amma indai momy ta gaya mae magan yana ji, Sam ya rasa sabida mae yake jin maganar momy, haka dae mashkhur yayi ta tinani kala-kala har bacci yayi awan gaba da shi.

Bayan ammi ta shiga d’aki ta, gado ta hau ta kwanta, addu’a ta farayi, bayan ta gama ta tofe zahra da ilham, sanan itama ta shafa a jikin ta. Tana gama ta rufa da bargo domin yin bacci. ji tayi jikinta ya fara mutuwa, can kasala ta fara d’aukar ta, daga qarshe ma ji tayi jikin ta ya mutu gaba d’aya, tana so ta tashi ta d’aukko magani ta sha, amma ta kasa.

Abu kamar wasa har ukun dare ammi ta kasa motsa gaggar jikinta. Hmm da alama fa maganin bokan su momy ya fara aiki.🤔 bacci ma ya gagari ammi, kai koh magana ma ta kasa, ya salam. Abu kamar wasa har asuba momy ta kasa motsi. Yadda ammi dae taga rana aka taga dare.

Yau mashkhur koh sallar asuba bae iya tashiba sabida karatun daran da yayi, dama dady ne yake tashin sa ko ammi. Yana farkawa ya kalli a gogo, qarfe takwas harda rabi na safe, abin ya bawa mashkhur mamaki sabida ya san kullum sae ammi ta tashe su, in lokacin makaran ta yayi koh sallar asaba, sae gashi yau koh sallahr asuba bata tashe suba, gashi sun makara a makaranta.

A hanzarce ya tashi ya shiga toilet domin yin alwala, bayan ya futo ya shinfid’a dadduma ya fara sallah. Yana idar wa ya tashi abdul domin shima yayi sallah, bayan ya tashe shi ya wuce dakin ammi. Yana zuwa ya fara kwankwasa d’akin, amma shiru, in badda kukan ilham ba abidda yake ji, ya dad’e yana buga qofar amma shiru, har ya juya zai koma sae ya tina yau fa dady ba’a part d’in su ya kwana ba yana part d’in momy.

Dama abidda ya hana shi shiga kenan, karya je dady yana d’akin ammi, dama in dae dady suna tare a d’aki d’aya da ammi basa shiga. A hanzar ce mashkhur ya tura qofar d’akin ya shiga. Yana shiga ya hango ammi a kwance, ilham kuwa sae kuka take tana ta yaqushin zahra. Da sauri ya qarasa kan bed d’in tare da am batar sunan ammi. Ammi kuwa tana jin mashkhur ba halin magana.

Idanuwan ta a bud’e suke, amma ta kasa motsi. Agigice mashkhur ya fara bibbiga kafad’ar ta yana kiran sunan ta, ammi!! ammi!! ammi kina jina kuwa, koh dae baki da lafiya ne? A firgice ya kai hanunsa kan hancin ammi, nunfashi yana futowa ammi ta kasa magana bare motsi, ammina dan ALLAH kiyi magana, ki tashi ammi.

Amma ina ammi shuru, kuka ya farayi yana jijjiga ta tare da cewa ammi kina jina? Ammi dan ALLAH ki tashi kiyi magana. A dai-dai lokacin dady ya shigo cikin d’aki. Da sauri ya qaraso tare da cewa kai mashkhur mene haka? Sabida mae kake ta jijjiga maman ka kana kuka. Da sauri mashkhur yace dady ammi ta dae na magana kuma ta dae na mosti.

Agigice dady yace what!!!!!! Da sauri ya qaraso kan gadan tare da d’ora hannun sa akan hancin ta, ajiyar zuciya dady yayi sabida yaji nunfashin ta, yana nan. Jijijga ta dady ya hau yi tare da cewa maryam mae yake damun ki, ki tashi ko baki da lafiya ne?. Shiru ammi batayi magana ba, a gigice dady yace mae sunan babana jeka ka kira hajiya tazo mu tafi asibiti.

Da sauri mashkhur ya fuce domin sanar da hajiya kaka, koh da hajiya kaka ta samu labari ammi bata da lafiya ta kasa magana da motsi hankalin ta ba qaramin tashi yayi, a gigice ta wauce part d’in ammi. Tana zuwa ita da dady suka d’auki ammi suka wuce asibiti. Suna fita mashkhur da abdul suka zauna su kai ta kuka. Mashkhur ya dad’e bai yi kuka ba, duk abindda zai sashi kuka ba qarami bane.

Kuka mashkhur ya ringa yi sosai musamman ma in ya tina magagganin da sukayi da ammi a daran jiya da, kuma yadda suka rungume juna ammi tana yi mae addu’a, sae yaji kamar mutuwa ammi tayi. 6an garan abdul kuwa kuka harda birgima, ihu yake sosai, suma su haidar da sukaga yayyan su suna kuka gashi sun tashi basuga ammi ba suma kuka suka fara.

*Ga masu buqatar karanta littafi ADALILINTA da nayi posting sai suyimin magana ta wannan number 08142246343 WhtsApp kawai bandda kira. free book ne bana kud’i ba, kuma new book.

Now book on 2023.
[11/06, 22:24] Maman Xuhra: “ADALILINTA”
ADALILINTA💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

Typing........

*page 35*
Bayan mashkhur ya gama kowayawa abdul hadda kuma ya tabbatar abdul d’in ya iya shima karatun Qur’ani ya fara...............

Haka ya zauna yayi ta hadda Qur’ani, Sai da dady ya dawo da daddare sanna mashkhur ya kwanta yayi bacci. Bayan dady ya dawo yaci abinci wanka yayiwa su zahra sanan ya kwantar dasu dama tun a asibiti hajiya kaka ta basu madara, shima kwanciya yayi amma ina kamar jiya bacci ya gagara haka dae yayi ta juyi, da yagaji da kwanciyar tashi yayi, ya d’auro alwala sanan ya fara sallar lafula, yana yiwa ammi addu’a.

Har hakayi sallar asuba dady bae kwanta ba yana sallah yana yiwa matarsa ammi addu’a. Ana fara kiran sallah ya je ya tashi mashkhur da abdul dan suyi alwala. Bayan sun dawo daga masallaci dady da kansa ya shiga kicin ya fara dafa abincin su mashkhur da wandda zai kai asibiti, shikuma mashkhur ya fara yiwa qannan sa wanka, bayan ya gama yi musu ya fara shirya su cikin uniform d’in makaranta wandda aka basu jiya.

Bayan ya gama shima ya fara shiryawa shi da abdul. Dady kuwa bayan ya gama girkin zubawa su mashkhur wandda zasuci yayi, sanan ya zuba musu wandda zasu tafi da shi makaranta, daga haka yaje ya fara yiwa su zahra wanka bayan ya gama yi musu wanka yasa musu kaya sanan ya basu madara, daga haka shima ya fara shiryawa.

Bayan ya gama shiryawa, ya d’auki su zahra da su mashkhur suka futa. Bayan sun fita daga gida ya ajiye su mashkhur a makaranta sanan ya wuce da su zhara asibiti. Yauma kamar kullum likitoci basu gano mae yake damun ammi ba haka su dady suka wuni a asibiti, da daddare ya d’auko su zahra suka dawo gida.

Tom yau kwana biyar kenan da kwantar da ammi a asibiti kuma har yanzu ba’a gano mai yake damunta ba. Kullum su mashkhur suna zuwa makaranta, kuma har yau dady ne yake yi musu girkin makaranta da yamma kuma mashkhur yayi musu in suka dawo. Momy kuwa sai shirye-shiryan suna take da yake ranar da ammi ta cika kwana biyar a asibit ita kuma ranar ‘yarta ta cika kwana shida a duniya.

Dady kuwa ya lura da shirn sunan da momy take, dan haka zuwa yayi ya samu momy ya ja mata kunne akan kartayi suna, da tace mae sabida mae sai dady yace mata sabida matar sa ammi bata da lafiya, taso tayi mae musu amma kwata-kwata ta kasa sabida yanzu taga haushinta yake ji koh shiga harkarta ma bayi yake ba, a al dole ta haqura amma har ga ALLAH momy bataji dad’i ba.

Washe gari dady kafin ya tafi asibita ya siyo rago ya yankawa ‘yar momy kuma yasa mata suna RUMAISA’U. Ranar su mashkhur basuje makaranta ba sabida sun makara, dan haka ranar dady bae je asibiti dasu zahra ba agida ya barsu, mashkhur ya kula da ilham shikuma Abdul ya kula da zahra. koh da dady yaje asibiti haka hajiya kaka tace ita ta gaji da zaman asibiti kwara su tafi gida su cigaba da jinya tindda ba’a gano mae yake damun ammin ba.

Dady bai so hakan ba amma bayadda ya iya haka yaje wajan doctor ya gaya mae cewa indda hali a sallame su, tindda har yanzu ba’a gano mae yake damunta ba. Likita yayi na’am da maganar dady dan haka arana aka sallami su ammi suka koma gida. Da su ammi suka dawo gida su mashkhur sunyi murna da dawowar su sosai.

Amma da sukaga ammi bata samu lafiya ba, basuji dad’i ba , jigum jigum sukayi. Bayan su hajiya kaka da ammi sun dawo gida hajiya kakace ta cigaba da kula dasu mashkhur da kuma zahra da ilham, ita take musu girki, kuma ita take shirya su haidar in zasu makaranta, sanna kuma ita take kula da ammi. Hajiya kaka ita takewa ammi wanka da tsarki, daga rana zuwa dare.

Shi kuma dady kullum shi yakewa ammi wanka da safe, in kuma yana part d’in ta da daddarae shi yake kula da ita sam dady baya gajiya da yiwa ammi hidima. 6an garan mashkhur kuwa sunyi saurakr Qur’ani mae girma, dady da hajiya kaka harma da mashkhur d’in sunyi farin ciki da hakan sosai.

Babban baqin cikin mashkhur shine ammi bata da lafiya yayi saukar qur’ani, sabida yasan ammi tana son ranar saukarsa amm kash sae gashi bata da lafiya tana kwance. Sunyi sauka lafiya kuma sun gama lafiya sae dai mashkhur beyi taran sauka a gida ba, sabida ammi bata da lafiya. Bayan mashkhur yayi saukar qur’ani dady ya cire shi daga makarantar su ta wuni ya sashi a wata babar makarantar computer science .

Ranar asabar da lahadi kuma yana zuwa wata makarantar islamiya, ana yimusu hadisi da littafan addini sanan kuma sunayin bitar Qur’ani. Mashkhur yana mae da hankalinsa sosai akan karatun sa, sabida yana son burinsa ya ciki, dama mashkhur yana da kwakwalwa shiyasa baya shan wata wahala sosai a makarantar su ta computer science. 6an garan su abdul da haidar ma sun cigaba da zuwa karanartar suma suna karatu sosai.

6an garan momy kuwa ba abindda ya dame ta sha’aninta kawai take, tindda ammi ta kwanta cuta sau uku tazo ta dubata, shima dady ne yayi mata dole shiyasa tazo ta dubata, gashi yanzu ammi tayi wajan wata uku a kwance. 6an garn su zahar kuwa sun sake girma sunyi wayo sosai ga kyau musamman ma zahra, suna samun kulawa sosai awajan hajiya kaka.

Yanzu momy ta samu dama sosai dan haka ta qara jan mashkhur a jikinta, kuma kullum in suka zauna bata da aiki sai hurewa mashkhur kunne akan ya dae na kula zahra, yanzu mashkhur ya qara tsanar zahra sosai, koh kallan ta bayayi, kuma koh zata kwana tana kuka bazi d’auke ta ba, haka zai tsallake zahra ya d’auki ilham.

6an garan abdul kuwa kullum qara son zahra yake in yaje makarnta har alawoyi yake siyo mata. Alokacin su zahra basufi wata takwas da haihuwa ba, amma duk da hakan sae abdul ya bawa zahra da ilham alawar nan kuma ba laifi suna sha, musamman ma zahra sabida zahra tanada son zaqi. 6an garan ammi kuwa tana nan a yadda take jiki ba sauqi, har yau komai yi mata akeyi..........

Dan Allah kuyi haquri da wanna yau kunga ban yi muku typing sosai ba koh one page typing d’in bai kai ba , wallahi yau sae da daddare na fara typing......

Daga yau na gama yin typing sai kuma bayan azumi... ina yiwa ‘yan uwana musulmai barka da watan ramadan, kuma da fatan zamuyi ibada lafiya.... insha ALLAH bayan azumi zan cigaba da rubuta littafin ADALILINTA........💜❤️💜

HAPPY RAMADAN KAREEM...

*ina godiya ga masoyana masu bibiyar littafin ADALILINTA, ga masu buqatar cigaba da karanta littafin ADALILINTA bayan azumi sai suyimin magan ta wannan number 08142246343 WhtsApp kawai bandda kira, free book ne kuma new book.

New book on 2023.
[11/06, 22:24] Maman Xuhra: “ADALILINTA”
ADALILINTA💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

Typing..........

*page 33*
Suma su haidar da sukaga yayyan su suna kuka gashi sun tashi basuga ammi ba, suma kuka suka fara..............

Bayan su dady sun qarasa asibiti, aka kwantar da ammi a gadan asibiti. Likitoci sosai sun taro akan ammi domin gano mae yake damun ta. Yanzu likitoci wajan awar su uku akan ammi amma basu gano mae yake damunta ba, tashin hankali tun likitocin suna sa ran zasu gano mae yake damun ammi harma sun fitar da rai.

Koh da likita yayiwa dady bayani halin da ammi take ciki ankalinsa ba qaramin tashi yayi ba. da dady ya gayawa hjy kaka kuwa kuka ta ringayi shi kuma yana rarrashin ta, shima dady kawai daurewa yake sabida hajiya kaka, amma in badan haka ba shima zai iya kukan. Haka dae suka wuni a asibiti kuma har lokacin ba’a gano mae yake damin ammi ba, kawai dae anyi mata allurar bacci.

6an garan su mashkhur kuwa sae da sukayi wajan awa biyu suna kuka, daga qarshe dae mashkhur share hawa yansa yayi ya fara rarrashin qannan sa. Bayan ya gama rarrashin su kowa yayi shiru ya shiga kicin domin dafa musu abinci, indomi ya dafa musu da kwai, bayan ya gama ya zuba musu, shi daebae ciba sabida bazai iya ciba, shima abdul da kyar ya yarda yaci.

A gaba yasa qannan nasa ya rafka uban tagumi yana tinanin mahifiyar shi, ana cikin haka kuwa ilhma da zahra suka fara kuka. Da sauri abdul ya miqe ya shiga d’akin ammi, shima mashkhur d’in a ala dole ya bishi sabida yasan abdul bazai iya rarrashin ilham ba sabida bata da haqur irin na zahra. Yana shiga yaga abdul yana ta jijjiga zahra alamin tayi shiru.

Mashkhur kuwa yana shiga d’akin ya nufi indda ammi take ajiyewa su ilham madara, d’aukowa yayi sannan ya zauna akan sofa, bayan ya zauna ya fara had’a musu madara. Fida biyu ya had’a miqawa abdul d’aya yayi tare da cewa abdul bawa babyn ka wannan ni zan bawa ilham, da sauri abdul ya karb’a ya fara bawa zahra. Shima mashkhur d’in zama yayi gefan gadon sanna ya d’auki ilham ya fara bata.

Har mashkhur ya gama bawa ilham madara abdul koh rabi bae bawa zahra ba. Harda mashkhur zai fita kawai sae yaji tausayin zahra, jiki a sanyaye ya koma ya karb’i fidar zahra tare da cewa abdul bari na bata tindda na gama bawa ilham koh? Da sauri abdul ya miqawa mashkhur fidar tare da cewa bari naje nayi fitsari, mashkhur bai so d’aukar zahra ba amma, a ala dole ya d’auke ta ya fara baza madarar.

Zahra kuwa zubawa mashkhur ido tayi tana ta kallan sa, kamar taga wata sabuwar halinttar. Shi kuwa mashkhur dayaga hakan kawar da kae yayi tare da jan wani dogwan tsaki. A haka dae ya cigaba da bata madarar tana kallansa yana galla mata harara kamar wata babba. Nikuwa nace abin babba ne🤔. Bayan mashkhur ya gama bawa zahra madarar kwantar da ita yayi akan gadon ya d’auki ilham ya fuce.

Yana fita shima abdul ya shigo ya d’auki zahra. Toh haka dae su mashkhur suka wuni a 6an garan ammi su kad’ai, sae dai mashkhur yayi musu girki suci, dama ga faruq da haidar da cin tsiya, shi kuwa mashkhur daya gaji

Please Login or Register in order to submit comment