Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da zata ce ki dawo gaskiya dai duk yadda a kai gwaggo bata nan nasan da bazata barki ki kwana ba.

Gyara zama maman zahra tai sanan tace ke nifa ba a gidan gwaggo zan kwana ba, a gidan su suruka ta zan kwana. Murmushi nana tai tare cewa yauwa mama ina ta zuci-zuci na tambaye ki wai ya kikaga matar da yaya ahmad zai aura kyakyawa ce kuwa, murmushi maman zahra tai tare da kallon ilham tana cewa sosai ma kyakyawace ta ajin farko gata nan ma tana jin ki ai.

Dariya nana tai sanan tace kai gaskiya mama bana son wanan abu sai ki tayimin wasa taya zakije gidan surukan ki ki kwana kuma. Murmushi maman zahra tai tare da cewa wlh nana I'm very serious nake gaya miki kin san mene kuwa labari mai dad'i. Ciki zumud'i nana tace aa mama meya faru ne dama daga jin muryar ki kina cikin farin ciki yau wai mai ya faru ne.

Murmushi maman zahra tai tare da cewa ina wanan yayar taku da nake baki labari ta, oh mama nasan dai haka zakice kinyi mafarkin ta ai kullum haka kike cewa wlh ki fitar da rai da ganin ta dan nasan bazaki ganta ba kuwa, yarinya ki rabu da ita tun tana jariri amma yanzu wajan shekara 18 to 19 zaki ringa sa rai da ita haba nifa lamarin nan ya ishe ni, kawai dai kin riga da kinyi asara 'yar ki sai dai kiyi haquri kawai.

Cikin farin ciki maman zahra tace kullum haka kike cewa baza ta dawo ba fa nana, kwarai mama wlh bazata dawo ba kawai ki cire rai da ita kinji. Tom shikenan nana yanzu in nace miki na ganta zaki yarda kuwa?. Wata uwar dariya nana ta saki sanan tace lallai mama abin naki ya sake gaba kice yau har kamarta kika gani a mafarki in kika cemin a mafarki zan yarda mana mama.

Tsaki maman zahra ta saki sanan tace ke bana son maganar wasa da gaske nake. Cikin rashin yadda da magar maman tata nana tace, to inaji a ina kika ganta, a gidan su suruka ta matar da yayan ki ahmad zai aura mana. Kai mama wlh naga kamar kin fara zaucewa hala kinje kinga wata kyakyawar yarinya ne a gidan kikace ita ce 'yar taku tayama zaki gane ta ita da kika ce tun tana jariri kika bada amanar ta haba mama ki ringa duba lamarin nan mana?.

Au wai nana baki yarda ba kenan bafa ita na gane ba wanan matar dana bawa ita na gane kuma baki ga yadd muke kama da ita ba, kai in baki yarda ba ki tambayi abban ki mana ko yaya ahmad. Cikin mamaki nana tace wai mama da gaske kike nifa har yanzu gani nake wasa kike min, tsaki maman zahra taja sanan tace ki bari zan turo miki hoton ta ta WhatsApp ki gan ta finely.

Daga haka maman zahra ta kashe wayar gaba d'aya tare da kallan zahra tana cewa kin jini da ita ko wlh ta cika surutu, gani take duk wasa nake mata ta mayar dani kakar ta maman zahra ta qarasa maganar tana shiga camera wayar tata. Tana shiga ta sai ta fuskar zahra tai mata hoto har kala biyu sanan ta shiga WhatsApp domin tura wa nana.

Zahra da ilham kuwa sai kallan juna suke suna ta gulma ta ido da yake sun k'ware wajan maganar ido. Maman zahra kuwa tana turawa nana hoton zahra ta shiga gallery tare da cewa, bari na nuna miki qanwar taki duk da dai ba wani kama kuke ba ai kin fita kyau, maman zahra ta qarasa maganar tana murmusawa.

Maman zahra tana cikin gallery taga kiran nana ya shigo, wata siririyar dariya ta saki tare da cewa kun gani ko sai yanzu ta yarda amma sai na gama ja mata aji tukunna zan d'auka maman zahra ta qarasa maganar tana ajiye wayar gefe. Ilham kuwa sakin baki tai tana kallan maman zahra sabida lokacin da maman zahra tai maganar gani tai kamar zahra ce take maganar.

Ilham ko a hanya taga maman zahra dole ta sheda ita ta haifi zahra ko ba'a gaya mata ba sabida kamar tayi yawa sosai. Kallan su maman zahra tai tare da cewa kun barni ina ta magana ni kad'ai bazaku tayani ba ko. Murmushi zahra tai tare da sunyar da kai qasa ita kuma ilham cewa tai hmm haba mama zamu taya ki mana.

Murmushi maman zahra tai tare da cewa yauwa suruka ta ai naga da dukkan alamu kinfi zahra wayo. Murmushi ilham tai tare da cewa sosai ma wazai had'a ai zahra bata da wani wayo. D'agowa zahra tai tare da cewa kai ilham, harar zahra ilham tai tare da cewa ba gaskiya na fad'a ba. Dariya maman zahra tai tare da cewa hmm lallai suruka ta daga ganin ki mai wayo ce ke.

Murmushi ilham tai sanan tace mama ki d'auki wayar mana kinga dai tun dazu nana sai kiran ki take, Murmushi maman zahra tai sanan tace okay bari na d'auka tinda kinsa baki. Zahra kuwa kunan ilham ta sai ta bakin ta sanan tace kai ilham banda zaqewa fa, kinga yadda kika zaqe ko ni da take mamata banyi hakan ba sai ke har kin wani riqe sunan nan koj?.

Ilham tana qoqarin bawa zahra amsa, sukaji nana ta saki wani uban iwu tana shewa eeeeee mama ashe da gaske kike wayo shikenan na zama me yaya wayyoo dad'i dan ALLAH mama tana ina ki had'a ni da ita nifa kar kusa yanzu ki gani a kano nazo wayyo dad'i.

Zahra kuwa ji tai wani sirrin murmushi ya su6uce mata yadda taji qanwar nana tana zumud'in ganin ta. Maman zahra kuwa cewa tai kai nana baki da hankali a daran nan zaki drive har daga kaduna har zuwa kano karma ki soma ranki zai 6ace sosai a wajan abban ki. Nana kuwa cewa tai wlh mama bakiji yarda nake zumud'i ba dan ALLAH gobe ki dawo tare da ita.

Ajiyar zuciya maman zahra ta sauke sanan tace hmm nana kin ganta nace tazo mu tafi taqi zuwa sabida yayan ta bashi da lafiya shi yasa ma na zauna na jira ta. Nana cewa tai kai mama baki gaya mata kece kika haife ta ba ai nan ba gidan su bane gaskiya ki d'auko mana ita ki dawo da ita gida.

Maman zahra kuwa cewa tai kai nana gidan su ne mana ai tafi sabawa da can kamar ke fa ace ki koma wani gidan da baki san suba ki bari a hankula zan lala6ata har ta amince. Nana kuwa cewa tai aaa wlh mama gaskiya mude a dawo mana da 'yar uwar mu, murmushi maman zahra tai sanan tace tana jin ki har kin bata dariya ma. Cikin farin ciki nana tace yauwa bani ita na gaya mata da baki na.

Cikin farin ciki maman zahra ta miqawa zahra wayar tana cewa gashi ku gaisa bari na shiga toilet nai alwala in kun gama ki bata aunty tata ilham su gaisa. Zahra kar6ar wayar tai tare da cewa tom, zahra tana qar6a ta kara a kunan ta duk da kuwa wayar a hans free take. Murya a sanyaye zahra tace hello. Cikin farin ciki nana tace wow kamar yadda kike da kyau haka voice d'in ki take da dad'in sauraro 'yar uwa ta.

Murmushi zahra tai tare da cewa nagode, yauwa aunty ya sunan ki ne? Cikin dad'ar murya zahra tace sunana fatima zahra. Wayyo ashe sunan naki ma da dad'i ni kuma sunana nana hafsat, kema sunan ki ai yana da dad'i. Dariya nana tai sanan tace kai da gaske kike ko dai kawai kin fad'a ne?. Murmushi zahra tai sanan tace da gaske nake mana.

Kai naji dad'i fah dan ALLAH ki dawo gida ki biyo mama ku dawo tare kizo kiga qanan ki wlh ina son ki aunty zahra ta dan ALLAH ki dawo kin ji. Kafin zahra ta kai g bawa nana amsa taji nana tana cewa kai fawas maza zo ka gaisa da yayar mu, zahra tana jin murya yaran yana cewa wace yaya kuma, nana ce tace kai itama 'yar gidan nan ce ta girme ni wanan fa wadda mama take cewa tana mafarkin ta to itace fa.

Zahra jin muryar yaran tai yana cewa kai amma mama tace mana ta rasu tun tana jariri, nana cewa rai uhmm to haka kawai take gaya muku amma tana raye zo ku gaisa zan nuna ma hoton ta. Daga haka nana tace yauwa aunty zahra ga qanin mu nan wanda yake bina zaku gaisa da shi. Murmushi zahra tai sanan tace tom ba damuwa.

Daga haka yaran yace hello aunty ina wuni, sanan yace aunty nana ya sunan ta?. Kallan zahra ilham tai suka saki wanu siririn murmushi sanan ilham tace lafiya qalau fawas, zahra kuwa sakin baki tai tana kallon ilham har suka gama gaisawa da fawas. Daga qarshe nana ta gaisa da ilham cikin farin ciki, bayan sun gama gaisawa tace yauwa bari dai na nunawa fawas hoton ki nasan dai har yanzu bai gama yarda ba amma in yaga hoton ki zai yarda.

Nana tana kashe wayar zahra ta ajiye wayar zuciya fass cike da farin ciki. Maman zahra tana futowa daga toilet ilham ta nufi kwaba domin d'auko mata dadduma. Fuska cike da farin ciki maman zahra tace uhmm au wai ajiye wayar ki kai nana ce fa ai tai ta kira kenan har gari ya waye dan in abinta ya tashi ma yanzu sai ta tarkati gaba d'aya qanan ta sun gaishe dake.

Murmushi ilham tai tare da fara shinfid'a daddumar tana cewa, kai gaskiya dai ga dukkan alamu nana tafi zahra surutu da saurin sabo. Inafa wazai had'a ai nana tana da saurin sabo sosai gaskiya amma ita zahra naga bata da sabo gashi har yanzu taqi sakin jiki dani. Maman zahra tana rufe baki ta wayar ta ta fara ringing, kingani ko ai na gaya miki itace ni dai sallah zanyi d'aga kiji nasan bani ta bugowa ba.

Murmushi zahra tai sanan tace tom daga haka ta d'aga wayar maman zahra kuwa ta tayar da sallah ilham dawowa kusa da zahra tai ta zauna. Zahra tana d'agawa nana tace yauwa aunty zahra ga qanan mu nan suna son ganin ki ga fawas ga kaulat ga twins arif da irfan, yanzu ki hau online zamuyi video calll kinji aunty dan ALLAH karki ce aaa yanzu duk suna nan suna jira ki hau WhatsApp zan kiraki video call ..................

Oh wa yaga zahra da qanne tab!?. 🤔😂


Mu had'e a next page mondy wanan page d'in jumma'a ne.

ADALILINTA💜❤💜

BY AMINA BAYERO💜❤💜

Typing...........

*108*

yanzu ki hau online zamuyi video call kinji aunty dan ALLAH karki ce aaa yanzu duk suna nan suna jira ki yanzu zan kiraki video call ..................

Kallan zahra ilham tai tana tinanin mai zata cewa qanwar ta nana, murmushi ilham tai ta d'agawa zahra kai almun eee. Cikin saririyar murya zahra tace tom shikenan ba damuwa, nana tana jin haka cikin zumud'i ta katse wayar. Wayar tana katsewa zahra tace wa ilham yanzu ya za'ayi kawai sai mu shigar mata WhatsApp bata sani ba.

Tsaki ilham tai tare da fizge wayar hanun zahra tana cewa to menene ba maman ki bace kuma ai ita ta baki wayar ta qarasa maganar tana qoqarin kunna data wayar. Duk maganar da suke a hankula suke yarda maman zahra bazataji ba. Ilham tana kunna data ta fara qoqarin shiga WhatsApp. Tana shiga ai kuwa sai ga kiran nana ya shigo.

Da sauri ilham ta miqawa zahra wayar tare da cewa d'auki d'auki ta bugo. Girgiza kai zahra tai tare da cewa aaa ni fa bana so, tsaki ilham ta sake ja a karo na biyi tare da cewa ke dallah ki d'auki wlh na matsu na gansu sai kiran ya tsinke, zahra noqe kafad'a tai alamun aaa. Ilham kuwa da sauri ta d'aga video call d'in ganin yana qoqarin tsinkewa.

Tana d'agawa ta miqawa zahra tare da cewa kar6i, zahra kuwa shiru tai bata bawa ilham amsa ba, wani qaramin staki ilham ta sake ja a karo na uku tare da cewa wlh zahra kina da matasala ta qarasa maganar tana qoqarin sai tawa zahra fuskar ta a video call d'in. Ilham tana sai tawa zahra fuska video call d'in yayi connecting. Zahra bata kai da magana ba taga wasu kyawawan yara guda uku suna iwu tare da cewa aunty.

Ilham kuwa zuba musu ido tai tana qare musu kallo. Ko ba'a gayawa su zahra ba sun san wacece nana a cikin su, duk ta girme su black beauty ce sosai, gashi tana da d'an jiki dan harma tafi zahra qifa kana ganin ta ko ba'a gaya ma ba zaka sheda babba yarinya ce 'yar gayu kuma 'yar wuto. Sai qanin ta mai bin ta shima suna kama da nana sosai, amma sai dai shi fari ne sa6anin nana da take baqa.

Daga ita sai wata qanwar su wadda bazata gaza shekara 8 ba itama kyakyawace tana kama da zahra sak itama farace amma ba sosai ba dan bata kai yayan nata haske ba. Daga ita sai wasu kyawawan yara farare tass maza wanda baza su gaza shekara 2 zuwa uku ba. Amma su ruwa biyu ne suna kama da baban su sanan suna kama da maman su.

Wani siririn murmushi zahra ta saki tare da cewa sanun ku, suma murmushi suka saki suna cewa yauwa daga haka suka fara gai da zahra, zahra tana amsawa da kyar dan ita sam ba'a saba gai da ita ba shi yasa take jin abin babbara kwai. Maman zahra da take gefe wanda ta idar da salla murmushi tai tana qarewa zahra kallo tare da saurarar mai suke tattaunawa.

Nana da sauran yaran suna tayiwa zahra magana amma bata iya basu amsa daga ee sai aaa sai kuma murmushi da sunkuyar da kai. Nana ce tace haba aunty kin qi ki saki jikin ki damu mufa qannan kine ko bakya farin ciki da ganin mine?. Dan zaro ido zahra tai tare da girgiza kai tana cewa aaa wlh ba haka bane ina farin ciki sosai da ganin ku.

Itama nana murmushi tai tare da cewa dama wasa nake miki naga dai bakyason magana ne shi yasa nace miki haka ina aunty tamu? d'ayar yarinyar ce mai kama da zahra ta kalle nana tare da cewa aunty nana su biyu ne dama?. Girgiza kai nana tai tare da cewa matar da yaya ahmad zai aura fa nake nufi. Murmushi d'ayan namijin mai bin nana yayi tare da cewa ee ai kuwa muna so mu ganta tana ina?.

Murmushi itama zahra tai sanan tace gata nan a kusa dani bari in baku ku gaisa ta qarasa maganar tana miqawa ilham wayar. Ilham qar6a wayar tai tare da sai ta wayar a fuskar ta fuska a sake tace sanun ku fa, murmushi nana tai tare da cewa yauwa aunty ina wuni, ilham kuwa ba kunya bare sunkuyar da kai ta amsa gaisuwar nana. Suma sauran yaran nan da nan suka fara gau da ilham.

Tsaf ilham ta ke amsa gaisuwar da suke mata fuska a sake. Bayan sun gama gaisawa ilham ta Kali mai kama da zahra tare da cewa ya sunan ki, cikin iyayi yarinyar ta lankwasa murya tare da cewa sunana khaulat. Murmushi ilham tai tare da cewa kai suna mai dad'i kai ya sunan ka ilham ta tambayi namijin mai bin nana cikin sakin fuska yace ni sunana fawas, murmushi ilham tai tare da cewa masha Allah saura twins ku ya sunan ku.

D'aya daka cikin su ne yace ni sunana arif, arif yana rufe baki d'ayan ya ce nikuma sunanan irfan, ai sunana ya fad'i dad'i koh aunty irfan ya fad'a yana kallan ilham. Dariya ilham tai tare da cewa hmmm duk sunan ku yana da dad'i sosai. Nana ce tace kai nifa baki tambaye ni sunana ba ta qarasa maganar tana yatsina fuska kamar wata yarinya.

Murmushi ilham ta sake yi tare da cewa ai nasan sunan ki nana ko kema sunan ki yana da dad'i sosai. Murmushi nana tai tare da cewa nagode sosai kefa aunty ya sunan ki, gyara zama ilham tai tare da cewa ni sunana ilham, murmushi nana tai sanan tace oh ba wanan ba na gaskiyar. Oh na gaskiya sunana sakina.

Kai wlh sunan nan yana birge ni ina da wata qawa itama sunan ta sakina kuma fa kusan halin ku iya d'aya tana da saurin sabo. Murmushi ilham tai tare da cewa ah wai ina da saurin sabo a hakan?. Kai sosai ma ai kinfi aunty zahra sabo ita naga kamar ma bata son yi mana magana. Girgiza kai ilham tai tare da cewa hmm haka take ba iya ku kad'ai ba, ita bata da surutu sosai.

Nana cikin mamaki tace to kema bata miki magana sosai?, dariya ilham tai tare da cewa ah banda ni ai ni usainar tace tana yimin magana mana sosai har isa ta take da surutu . Murmushi nana tai tare da cewa wow da gaske gaskiya in ta dawo nan sai munsa ta ta ringa surutu kinga duk nan ba shiru-shiru fa.

Murmushi ilham tai tare da cewa kai anya zamu barta ta dawo gidan ku kuwa gaskiya da kyar. Khaulat cewa tai kaii ba yayar mu bace, shi kuma fawas cewa yayi aa muma muna son aunty mu sai ta dawo. Murmushi ilham tai cikin zaulaya tace to muma muna son ta bazamu baku ita ba sai dai kuzo har nan ku ganta.

Nana kuwa cikin mamaki tace tab gaskiya bamu yarda ba sai ta dawo nan ai nan ne gidan su. Murmushi ilham tai tare da cewa ai nan d'in ma gidan sune, khaulat yamutsa fuska tai tare da cewa naga ai cewa akayi maman muce ta haife ta ba maman ku ba. Da sauri nana ta ce ke khaulat mene haka, ilham kuwa cewa tai nasani ai amma ita ma nan tana da wata maman a gidan mu kuma maman bazata barta tazo ba.

To haka dai ilham da qanan zahra su kai ta mahawara tun suna musu har suka dawo yiwa ilham magiya akan zahra ta dawo kaduna gidan su. Ilham daga qarshe dai ce musu tai to shikenan zata dawo in sha ALLAH. Haka ilham ta zauna su kai ta hira da qanan zahra lokaci guda suka saba da ilham, zahra kuwa har lokacin taqi sakin ciki da su, sam ta kasa sabawa da su kamar yadda ilham ta saba da su.

Qanan zahra har cewa suke wai in za'a tawo a zo da ilham itama. Haka dai su kai ta hirar su har sai da suka d'au awa d'aya suna hira shima bada san ran su sukayi sallama ba. Bayan sunyi sallah ma ilham da zahra suka miqe da niyar tafiya, maman zahra kallan su tai tare da cewa au baza ku zauna ku kwanta anan ba?. Murmushi ilham tai tare da cewa dama ai zahra anan zata kwana tare da ke ni kuma wajan hjy kaka zani na taya ta kwana.

Ilham tana sane ta fad'i hakan ba wani wajan hjy kaka da zata kwana kawai sabida tayi wayar dare kamar yadda suka saba da ahmad ne tasan in ta kwana anan ba hali, zataji kunyar maman ahamd d'in, amma ba daban haka ba zata iya kwana abinta. Zahra kuwa d'ago wa tai tana kallan ilham alamun bataji dad'i abinda tai mata ba, ilham kuwa kawar da kai gefe tai tare da cewa to zahra sai da safe kije ki zubawa mama abinci, daga haka ilham ta juya ta kama hayar fita tana cewa to mama sai da safe.

Murmushi maman zahra tai tare da cewa ALLAH ya tashe mu lafiya zahra zo mana kika tsaya a tsaye. Zahra kuwa jiki a sanyaye ta qarasa wajan maman tata ta zauna a mesa da ita. Naga alama dai sam baki da saurin sabo kamar ilham sai wani d'ari-d'ari kike dani kamar zan sace ki. Murmushin dole zahra tai tare da sunkuyar da kai gefe. Matso ki zuba mana abinci muci koh?.

Girgiza kai zahra tai ciki siririyar murya tace aa ni na qoshi. Maman zahra kuwa cewa tai aa ko dai bakya so naci abinci gidan surukan nawa ne murmushi zahra tai tare da girgiza kai, zahra dai ta d'auka maman tata tana nufin gidan su surukar ta ilham, amma a binda maman zahra take nufi shine gidan su mijin 'yar ta. Matsowa zahra tai tare da fara zubawa maman ta abinci jiki a sanyaye.

Maman zahra kuwa sake zubawa zahra ido tai tana ganin tsantsar kamar da suke. Dama maman zahra tun sanda ta haifi zahra take ganin kamar zatai haquri, sabida ranar da zata bayar da ita wuni tai batai kuka ba. Zahra tana gama zuba maman tata abinci ta ajiye a gaban ta tare da d'agowa tana cewa gashi nan. Zahra gani tai maman tata tana ta kallon ta, da sauri ta sunkuyar da kanta qasa kamar ba mace ce take kallan ta ba macan ma maman ta.

Murmushi maman zahra tai tare da cewa ai tare zamuci ni bazanci ni ka d'ai ba sai dai in bakya so maman ki taci abincin gidan su mijin 'yar ta koh?. Zaro ido zahra tai tare da d'agowa ta kallin maman tata tana dafe qirji. Hakan da zahra tai sai ya bawa maman ta dariya amma sai tace kwarai mana. Girgiza kai zahra sai cikin siririyar murya tace ni kam bani da wani miji.

Murmushi maman zahra tai tare da cewa hmmm mu dai ci abinci kawai, zahra a bisa dole ta d'auki spoon ta fara cin abincin a hankula,. Itama maman zahra spoon ta d'auka ta fara cin abinci zuciya cike fall da farin ciki, maman zahra ta lura da yadda zahra take cin abinci a hankula, maman zahra cewa tai ko dai bakya son cin abinci ne kin san fa mace mai ciki ba komai take iya ca ba.

Da sauri zahra ta ajiye spoon d'in sabida kwarewar da tai bakomai ne yasa zahra kwarewa ba face maganar maman ta. Da sauri maman zahra ta tsiyayi ruwa a glass cup ta miqawa zahra tare da sai ta mata cup d'in a baki. Da sauri zahra ta d'ora hanunta akan na maman ta ta fara shan ruwan bayan ta gama sha ta saki hanun maman tata.

Maman zahra sauke cup d'in tai tare da kallan zahra tana ce mata sannu. Cikin da shashiyar murya zahra tace yauwa, maman zahra da ta lura zahra bata son maganar cikin sai ta canza magana da cewa! Dama kin dad'e da sanin yayan ki ahmad amma ahmad yayi waw ta sosai ta yadda akayi ya kasa gane kamar mu duk zuwan shi gidan nan.

Zahra kuwa cikin sanyayiwar murya tace hmm na san shi mana sosai wataran har hira muke da shi tare muka zauna a russian kullum shi yake kai ni school.

Please Login or Register in order to submit comment