Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baki ahmad yayi ya zubawa mashkhur ido dan shi mamaki ma ya danqarar da shi a zaune ko motsi ya kasa.

Mashkhur kuwa cigaba da magana yayi da cewa! Wlh ahmad zee ta cuceni sai da naci burin muna komawa Nigeria na saki zahra nayi haqurin zama da ita na shakara harda watanni, sai da na kusan sakin ta, saurafa qiris nai mata saki UKU zee tai min haka, inalilahi shikenan zahra zata mutu da aure na. Ahmad kuwa shiru yayi dan shi yanzu lamarin mashkhur ya dena bashi mamaki tsoro yake bashi.

Mashkhur ne ya sake cewa! Ahmad kai min shiru pls ka daure ka bani shawarar abinyi yanzu?. Rai a 6ace ahmad yace! Da yake ni mahaukaci ne irinka ba? Wai kai mashkhur ina kakai iliminka na addini kai harma dana bokwan ina ka kai su? In banda hauka da rashin tausayi irin naka yarinya tana cikin wanan halin rai a hanun Allah, bare kai mata addu'a amma zancan saki kake ko?.

To wlh mashkhur bari kaji zahra ta mutu harda alhakinka, wajan salwantar mata da ranta, kuma ba abinda zai sa naqi gayawa dady. Mashkhur wanan wace irin tsana kakewa zahra haka? Mashkhur mai zahra tayi maka a rayuwa haka? Mashkhur zahra wa ta kashema a rayuwa kake nuna mata mumunar tsana da qiyayya haka? Pls mashkhur ka gayamin zahra wana mummuna zunibi ta aikata maka kake mata wanan qin haka?.

Shiru mashkhur yayi ba amsa, har ga ALLAH yaji magagganun ahmad har cikin zuciyar shi sai yanzu yaga abinda yayi kamar bai dace ba, amma dai duk da hakan mashkhur bai dai na jimamin zahra zata mutu da auran sa ba. Ahmad ci gaba da magana yayi kamar haka? Wlh mashkhur ban ta6a tinanin rashin imanin ka ya kai haka ba.

Shin kana tunanin ALLAH zai kyaleka, ka azabtar da zahra mashkhur kuma wlh in!! Da sauri mashkhur ya katse ahmad da cewa! Kaga ahmad ya isa haka ka barni naji da abinda yake damuna. Rai a 6ace ahmad yace naqi d'in mashkhur bazan barka da abinda yake damunka ba d'in, kai har wani abu ne yake damun ka wai?.

Yanzu mashkhur in wani yayiwa qanwarka ilham haka zakaji dad'i?, rai a 6ace mashkhur yace? Look ahmad bana san maganar banza yanzu har fatama kake a wulaqanta min qanwa koh?. Da sauri ahmad ya girgiza kai tare da cewa! No mashkhur bazan ta6a yiwa ilham wanan fatan ba, kai ko gani nai wani zai mata sai na bi mata haqin ta kai bama ilham ba har sauran qannan ka bazan so ayi musu abinda kayiwa zahra ba.

Amma abinda nake so na nuna maka shine! yanda bazaka so ayiwa qannan kaba haka itama 'yan uwan zahra da iyayan ta baza su so ayi mata haka ba, yanzu mashkhur mene ribarka a nan. Fuska ba walwala mashkhur yace! Ni nayi mata hakan ne? Ko ni nasa zee d'in tai mata? Ko kuma a gabana aka yi mata akan ne, dan ALLAH ahmad mu mai da hankalin mu akan abinda yake gaban mu mubar wanan zancan.

Shiru ahmad yayi zuciya cike da takaici ya kawar da kai yana jinjinawa taurin kai da mugun hali irin na mashkhur, ahmad gane yake kamar har yanzu mashkhur bai sadudaba, da badan kyakyawar alaqar da take tsakanin zahra da ahmad ba, da kuma soyayyar da take tsakanin ilham da ahmad ba, da tuni ahmad yabar asubintin nan ya tafi gida.

Kuma bayan ya tafi gida, washegari yabi jirgin safe yabar garin, yabar mashkhur ya san yanda zai yi da jarabar da ya janyo, amma ahmad yasan in yayi akan bai yi adal ciba, sam bai kyautawa zahra ba kuma bai san yadda rayuwar zahra zata kasance a wajan mashkhur ba...............

*hmmmmm kuna ganin zahra zata rayu kuwa?.

*bakwa tinanin zee tayiwa zahra lahani?.

*mai ya samu zahra da ta fad'o daga wanan dogwan benan mai shegen tsayi?.

Ku biyu ni a next page dan ji yazata kaya.

Ina yi muku barka da jumma'a, kuma da fatan za kuyi hutun mako lpy.


ADALILINTA💜❤💜

BY BAYERO💜❤💜

Typing...........

*page 79*

Kuma bayan ya tafi gida, washegari yabi jirgin safe yabar garin, yanar mashkhur ya san yanda zai yi da jarabar da ya janyo, amma ahmad yasan in yayi akan bai yi adal ciba, sam bai kyautawa zahra ba kuma bai san yadda rayuwar zahra zata kasance a wajan mashkhur ba...............

Jigum sukayi ba mai cewa d'an uwansa qala kowa da abinda yake tunawa. Suna cikin wannan yanayin, likita ya qaraso, har ahmad da mashkhur suna 'Yar rige-rige miqewa, suna gama miqewa suka nufi doctor d'in dan jin mai ke tafe da shi. Doctor ya mara lafiya? Ahmad ne ya tambaya cikin harshan turanci.

Gyara tsayuwa doctor yayi kafin yace yanzu tana emergency room an sa mata oxygen, sam ma bata cikin hayyacin ta,. Nan da nan hankali ahmad da mashkhur ya sake tashi musamman ma ahmad, doctor kuwa ci gaba da magana yayi da! Bayan haka qashin qafarta ya goce, dan yama kusan karyewa, sanan d'an yatsanta d'aya na dama ya karye,. Na hagu kuma d'aya yayi targad'e d'aya shima ya goce.

Nan da nan hankali mashkhur yayi mugun tashi ganin wanan ruwan bala'in da ake lissafowa kuma wai duk akan mutum d'aya wato zahra. Doctor kuwa ci gaba da magana yayi da! Sanan goshinta ya fashe sosai za muyi mata dinki,. Mashkhur kuwa sam ya gaji da jin wanan matsalolin dan haka inda ya tashi ya koma ya zauna zuciyar shi na bugun 10-10.

Lokaci guda yaji tausaniyin zahra ya kama shi ta ko ina, duk da kuwa bai ma ganta ba, dan yasan a halin yanzu ran ta yana hanun ALLAH. A taqai ce dai sai da aka caji mashkhur wajan 1 million, sanan akan fara yiwa zahra d'auri da dinki. Haka mashkhur da ahamd sukai ta jira har goman dare ba'a futo da zahra ba.

Hmm zo kaga tashin hankali, wajan mashkhur da ahmad, mussaman ma mashkhur da ko kwakwaran motsi baya iyayi sabida tashin hankali. Daga qarshe dai likitoci suka shedawa su mashkhur sai zuwa gobe za'a futo da zahra daga emergency room, kuma baza su samu damar ganin ta yau ba sai zuwa gobe.

Jiki a sanyaye ahmad yace! Mashkhur tashi mu tafi gida, jim mashkhur yayi kafin yace! No ka tafi kawai, ni zan zauna anan. Shima girgiza kai ahmad yayi tare da cewa! Ka zauna kayi me anan, bayan ko ka zauna ba ganinta zakayi ba to mene amfanin zaman naka? kawai ka taso mu tafi malam zuwa gobe ma dawo, ahmad ya qarasa maganar yana jan hanun mashkhur da yake zaune bashi da alamun miqewa.

Haka dai mashkhur ya miqe zuciya cike da zullumi kala-kala,. Suna fita suka shiga motar kamar yanda zuka zo, ahmad ne ke tuqawa, shi kuma mashkhur yana mazunin gaba. Har tafiyar su ta fara nisa amma, ba wanda yacewa d'an uwansa qala. Can kuma ahmad yace! Mashkhur! Shiru mashkhur yayi kamar bazai amsa ba sanan yace, na'am.

Qara mai da hankali ahmad yayi kan tuqinsa sanan yace, mashkhur ni abokin ka ne, amma wlh bazan dena gayama gaskiya ba dule na gayama gaskiya ko zaka rabu dani, yamutsa fuska mashkhur yayi tare da cewa! To mai kuma ya kawo zancan rabuwa anan, murmushi ahmad yayi tare da cewa! Hmm sabida nasan zaka iya aikata hakan shi yasa na fad'a.

Shiru mashkhur yayi bai bawa ahmad amasa ba, ahmad kuwa ci gaba da magana yayi da cewa! Yanzu abinda ya faru da zahra kana ganin ba laifinka a ciki ko?, gyad'a kai mashkhur yayi alamun ehh. Jinjina kai ahamd yayi tare da cewa! Gaskiya kuwa ka jahilci kanka mashkhur. Fuska ba walwala mashkhur yace look ahamd bana san irin wanan banzar maganar dan ALLAH live me.

Jinjina kai ahmad yayi tare da cewa! In sha Allah bazan dena gayama gaskiya ba a matsayina na abokin ka, sai dai duk abinda zakace kace. Lumshe ido mashkhur yayi ya bud'e tare da cewa! Wai duk ba akan zahra bane kake gayamin abinda ran ka yake so ba?. Kwarai mashkhur akan ta ne ahmad ya qarasa maganar yana d'an kallan mashkhur.

Jinjina kai mashkhur yayi tare da cewa that is good, kasan mene? Girgiza kai ahamd yayi tare da cewa! Sai ka fad'a. Gyara zama mashkhur yayi ya d'an kwantar da kai akan kujerar motar sanan yace, ga shawara mai kyau, mai zai hana in na sake ta kawai ka aure ta, kaga kai sai kayi mata adalcin ko, tinda ni bana yi mata adalci zalintar ta bake. Ahamd har cikin zuciyar shi yaji maganar da mashkhur ya gaya mai.

Rai ba dad'i yace mashkhur mai kuma ya kawo wanan maganar kasan mai kake fad'a kuwa? Kwari kuwa ahmad na sani, ai gani nayi hakan zai fi. Jinjina kai ahmad yayi tare da cewa! To bazan iya ba. Shafa sumar kansa mashkhur yayi tare da lumshe idanuwan sa, sanan yace! Ayyah to kagani fa, kai kasan bazaka iyaba amma ni kake so kayimin dole!?

Karfa ka manta hadisin manzan ALLAH da yake cewa! Imanin d'ayan ku bazai cika ba har sai ya sowa d'an uwansa abinda ya sowa kansa.
To taya ni kuma zaka so min abinda baka so? Kasan ai bakayi min adalci ba koh?.
Jinjina kai ahamd yayi a zuciyar sa yana mamaki wanan hali irin na mashkhur har da janyo hadisi.

Lalai mashkhur ashe ka san hadisin nan, ai nasha ai baka iya wanan ba tinda ka iya riqe wanan bazaka manta ragowar ba koh? To sabida mai baka amfani dasu? Ahmad ya watsawa mashkhur tambayar. Shiru mashkhur yayi bai bashi amsa ba, dan wayar sama ya zaro ya fara dannawa,. Ahmad kuwa cigaba da magana yayi da cewa! Dama abinda yasa nace bazan aure taba, bawai dan bana qaunar ta bane.

Kuma ba wai dan bata da abinda za'a so ta bane, aaa sai dai ina ganin ana barin halak dan kunya ne ba dad'i a matsayinka na aminina koma nace d'an uwana ka saki mata na aura kuma bugu da qari ni, ina da wanda nake son na aura,. Muryar mashkhur ahmad yaji yana cewa! Okay in dai dan nine ka dai na jin kunya, na amince ma in na saketa ka aure Dari bisa dari.

Sanan zancan kana da wanda zaka aura ai kai namiji ne koh? Allah yace ka auri mata d'ai-d'ai-d'ai har guda hudu, to kaga ba laifi in tazo a ta biyu. Har cikin zuciyar shi ahamd baya jin dad'in maganar da mashkhur yake watsa mai amma a fili dakewa yayi yace, tom shikenan mashkhur, ni kuwa in sha ALLAH zanyi yadda kake so, zan baka mamaki sosai.

In ka saki zahra kuma har dai bata da wanda take so, sanan iyayanta suka bani ita nayi ma ALQAWARIN zan AURETA, in sha ALLAH, sabida zahra ta cika mace ta ko ina ba namijin da zai qita wlh. Mashkhur jin magar ahmad yayi kamar almara dan har maganar mai mai ta kanta take a kunnan mashkhur. Ahmad kuwa cigaba da magana yayi da cewa! Nasan wadda zan aura tana da kishi sosai amma bazata hana na aure ta ba.

Jim mashkhur yayi kamar ba shi ya cewa ahamd ya auri zahra ba, haka nan yaji wani abu yana mai yawo a qoqon zuciyar shi amma sam ya rasa menene?. Ahmad ne ya dawo da mashkhur daga gajeran tinanin daya tafi. Da cewa shikenan hankalinka ya kwanta koh? Da kyar mashkhur ya iya d'aga kai tare da cewa eh.

Daga haka ba wanda ya sake cewa komai har suka qarasa gida suna qarasawa, mashkhur ya fuce daga motar, zuciya cike da zullumi, shima ahmad d'in fucewa yayi. Ba 6ata Lokaci kowa ya Kama hanyar part d'in shi, mashkhur yayi sama shi kuma ahmad ya wuce qasa. Rai ba dad'i mashkhur yasa key ya bud'e qofar ya shige abinsa.

Yana shiga bai tsaya ko inaba sai a bedroom d'in shi, yana shiga bedroom d'in nasa ya ajiye wayar shi da key d'in gidan a qaramin table sanan ya fara rage kayan jikinsa, ya koma daga shi sai jageran wando, sanan ya d'auki towel ya wuce toilet direct. Mashkhur yana shiga toilet ya ware shower a tsakiyar kansa, duk da kuwa sanyi da ake tsalalawa a garin.

Amma sam mashkhur bayaji ji yake zuciyar shi tana mai mugun zafi, mashkhur yafi 20 minti a haka sai daga baya yaji sanyi ya fara ratsa ko wacca gaba ta jikinsa sanan ya kashe shower. bayan ya gama wanka brush yayi sanan ya futo ugu d'aure da towel. Yana fitowa ya sake jin wani mugun zafi ko ta ina a jikinsa, sanyi ake a garin sosai, amma mashkhur zafi yake ji sakamakon yanda zuciyar shi take mai mugun quna.

Robot d'in A.C mashkhur ya dauko sanan ya qureta har qarshe, daga haka ya wuce wardrobe ya d'auko kayan bacci ya zira. Mashkhur yana gama sa kayan baccin sa yaji, cikinsa ya murd'a alamun yunwa, sai a time d'in mashkhur ya tina rabansa da abinci tun safe. Wani siririn tsaki mashkhur yaja sanan ya fuce daga bedroom d'in.

Yana fita bai tsaya ko ina ba sai kicin, ba 6ata Lokaci ya fara had'a coffee, sabida a wanan halin da yake ciki coffee d'in kawai yake tinanin zai iya sha. Bai fi 10 minti ba ya gama had'a coffee d'in nashi, yana gama had'awa ya d'auko cup ya juye, sanan ya d'auki cokali ya fuce daga kicin d'in. Yana fita ya koma bedroom d'in shi, jiki a sanyaye mashkhur ya ajiye cup d'in coffee d'in a table sanan ya zauna akan bed yana faces d'in coffee d'in.


Hannu biyu mashkhur yasa ya rafka uban tagumi, abu biyu ne zuwa uku suke damun mashkhur. Na farko halin da zahra take ciki, na biyu kuma fargabar zee batayiwa zahra wani lahalin da zai kasa warkewa ba, har dady yace bazai sake taba, na uku kuma maganar da ahamd ya gaya mai na cewa zai auri zahra. Sam mashkhur ya rasa sabida mai ya damu da abinda ahmad yace, mashkhur yana san ya cire zancan a zuciyar shi amma ya kasa.

Mashkhur ya d'au tsawan 30 minti yana tinanin nan, ringing d'in wayar shi ne ya dawo da shi daga dogwan tinanin daya tafi. Ajiyar zuciya mashkhur ya sauke, sanan ya bud'e lumsashin idanuwansa ya zuba akan wayar tasa da take ta faman ringing. Rass-rasss-rasss, gaban mashkhur ne ya fad'i har sau uku saka makwan sunan dady dayaga ya bayyana akan screen d'in wayar.

Nan da nan mashkhur yaji zufa ta fara keto mai duk da kuwa A. C da take d'akin, jim mashkhur yayi ya zubawa wayar kyawawan manyan idanuwan sa, sam ko kwakwaran motsi mashkhur ya kasa barema asa ran zai d'auki wayar. Haka dai wayar mashkhur ta qaraci ringing d'in ta har sau uku ta gama mashkhur bai d'auki wayar ba.

Da kyar mashkhur ya miqa hannu ya d'auki cup d'in coffee d'in ya kai bakin sa, mashkhur yana sha yaji duk coffee d'in ma ba dad'i, haka dai mashkhur ya d'aure ya cigaba da sha sabida yunwa. Da kayar mashkhur ya iya shan rabin coffee d'in, yana shan rabi ya ajiye sauran akan table, sam mashkhur ji yayi duniyar bata yi mai dad'i gaba d'aya.

A cikin zuciyar shi kuwa sai cewa yake! ALLAH ya isa tsakanina da ke zee kin cuce ni over. A fili mashkhur yaja wani tsaki tare da miqewa tsaye yana tinanin mafita. Sam mashkhur ya kasa samun mafita dan haka yanke shawara yayi gwara yasha kayan maye kawai qila zai iya samun mafita zuwa gobe. Har mashkhur ya kama hanyar fita, kawai yaji zuciyar shi bata amince da hakan ba.

Can qasan zuciyar shi yaji tana cewa! No mashkhur sam hakan bai dace ba yanzu wanan bashi nevmafita ba, bai kamata kayi hakan ba, yaushe raban da kasha kayan mayan? ka nemi wata shawarar kawai. Da hannu bibiyu, mashkhur ya dafe kansa yana tinanin mene mafita,. Ya salaam!! Abinda mashkhur kenan ya iya firtawa,, da kyar mashkhur ya iya taka qafa ya koma bakin bedroom, yana zuwa yasa hannu ya canza globe d'in d'aki daga fari zuwa light blue.

Daga haka ya haye kan gado ya kwanta lamo. Haka zuciyar mashkhur tai ta quna, sam ya rasa farin ciki a daran yau, ba kamar dazu ba da yake farin ciki ya gama exam zai koma Nigeria, ko dan yayiwa zahra saki uku. Mashkhur dai yana cikin wanan tinanin bacci yayi awan gaba da shi.
A firgice mashkhur ya farka saka makwan wasu mugayan mafarkai da yake game da zahra wai ta mutu.................

Mu had'e a next page.......


ADALILINTA💜❤💜

BY BAYERO💜❤💜

Typing...........

*page 80*

Mashkhur dai yana cikin wanan tinanin bacci yayi awan gaba da shi.
A firgice mashkhur ya farka saka makwan wasu migayan mafarkai da yake game da zahra wai ta mutu.................

Nan da nan mashkhur zufa ta 6alle mai ko ta Ina, da sauqi ya dafe qirjin sa tare da firta alhamdulilah, saka makwan ganin mafarki yake ba gaske ba. Jiki na rawa mashkhur ya miqe ya kama hanyar fita daga bedroom d'in, yana fita daga bedroom d'in bai tsaya ko ina ba sai a firij, yana zuwa firij hannu na rawa, ya bud'e ya dauko bottle d'in ruwan sanyi.

A take a gurun yayi bismillah ya kafa bottle d'in ruwan a baki, ba jimawa mashkhur ya shanye ruwan tass, sanan ya yarda bottle d'in ruwan a qasa ya sake d'auko wata bottle d'in ruwan ya kafa a baki. Itama bai sauke ta ba sai da ya sha rabi sanan ya sauke ta. Nan da nan mashkhur ya fara mai da nun fashi kamar wanda yayi 'yar tsere da zaki.

Da qarfi ya rufe murfin firij d'in kamar wanda yayi mai lai fi, sanan ya koma bedroom hannu riqe da bottle d'in ruwan da ya rage. Mashkhur yana shiga ya zauna akan bed tare da ajiye ruwan akan table, tinanin ya farayi anya bazai koma asibitin da aka kwantar da zahra ba kuwa!?. sabida sam ya kasa samun nutsuwa gaba d'aya.

ALLAH ka tashi kafid'un zahra, abinda mashkhur ya furta kenan zuciya cike da damuwa,. Daran ranar dai sam mashkhur ya kasa rintswa yana rintswa sai ya hango zahra kwance cikin jini rai a hanun ALLAH. Dan haka miqewa yayi ya shiga toile ya d'auro alwala, sanan ya futo ya zira jallabiya, bayan ya saka jallabiyar dadduma ya shinfi d'a ya fara gabatar da sallah.

Haka mashkhur yayi ta sallar dare ko waca sujjada in yayi sai ya roqi ALLAH akan ALLAH ya bawa zahra lpy. Haka dai mashkhur yayi ta sallah sai wajan qarfe ukun dare ya samu ya rintsa. Shima ba wani baccin arziki yayi ba, kawai dai ya kishin gid'a ne, dan ana kiran sallar asubayi, ya sake d'aura wata alwalar sanan ya wuce masallaci.

Bayan ya dawo kicin ya shiga ya fara dafa indomieen, bayan ya gama indomieen d'in, t ya d'ora, t d'in yana gama tafasa ya juye a cuo sanan ya fuce da breakfast d'in. Yana zuwa ya zube akan draining ya zauna ya zubawa abincin ido, yana so yaci amma sam hankalinsa baya kan abinci duk hankalinsa ya karkata kan zahra, mashkhur tinani yake yanzu zahra tana wana halin? Ta farfad'o ko kuwa.

Da kyar mashkhur ya d'aure ya fara shan t d'in yana shanye t d'in yaji gaba d'aya indomieen ta fitar mai daga rai, ji yayi ba zai iya ci ba. Dan haka ture ta yayi gefe ya miqe ya koma bedroom d'in shi. Yana shiga ya wuce toilet yayi wanka sanan ya futo ya fara qoqarin shiryawa,. A hanzarce mashkhur ya shirya, bayan ya gama shiryawa waya ya d'auko ya fara kiran ahmad, amma sam wayar a kashe take.

Wani siririn tsaki mashkhur yaja sanan ya miqe tare da zura wayar shi a aljiwun sa. Bayan ya gama zira wayar a aljiwo qaramar drowar gefan bed d'in shi ya bud'e ya d'auki key d'in motar shi sanan ya fuce daga bedroom d'in. Mashkhur yana fita daga bedroom d'in ya kama hanyar fita daga part d'in. Bayan ya fita a hanzarce ya rufo qofar da key sanan ya fara sauka daga step d'in benan da sauri.

Mashkhur yana qarasa saukowa daga step d'in benan yaci karo da ahmad yana qoqarin hawa benan, fuska ba walwala mashkhur ya miqawa ahmad hannu alamun masabaha, fuska a sake shima ahmad ya miqawa mashkhur hanun nasa suka gaisa, kamar yanda addinin muslinci ya tanadar. Bayan sun gama gaisawa ahmad yace, naga ka fito da wuri haka ai ni nasha ka manta da fitar ma.

D'auke kai mashkhur yayi tare da cewa! A kan mai zan manta, tun dazu na kira wayarka a kashe nayi tinanin baka tashi daga bacci ba shi yasa na futo zan tafi ai. Girgiza kai ahmad yayi tare da cewa! Hmm ai daran jiya ban iya bacci ba mashkhur kwana nai ina tinanin zahra. Shiru mashkhur yayi yana nazarin maganar ahmad dan bai ma san sanda yace wa ahamd d'in ba, kwana kai kana tinanin ta ko kwana ka kana tinanin halin da take ciki?.

Mashkhur ya qarasa maganar yana kafe ahmad da manya idanuwansa, cikin mamaki ahmad ya kalli mashkhur tare da cewa! Mashkhur mai kuma kake nufi da hakan?,. Ta6e baki mashkhur yayi tare da cewa! Duk yanda ka d'auka haka nake nufi tawo mu tafi ya qarasa maganar tare da yin gaba yabar ahmad tsaye baki a sake.

Haka ahmad shima yabi bayan mashkhur d'in yana mamakin da nazari akan maganar mashkhur dan sam yama rasa inda ya dosa. Mashkhur yana qara sawa wajan motar ya bud'e motar tasa ya shiga mazaunin driver ya zauna, sanan ya tayar da motar. Shima ahmad yana qarasowa ya zauna a

Please Login or Register in order to submit comment