Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

murmushi zahra tai ba tare da tace komai ba, miqewa mashkhur yayi ya ruqo hanun zahra tare da cewa tawo muje toilet muyi wanka da brush.

Bayan mashkhur da zahra sun futo daga wanka, ko kaya basu saba yaja hanun zahra zuwa wani bedroom d'in sabida karsu tashi abdul daga bacci. Ba 6ata lokaci suka fara bawa junan su haqqi cikin kulawa da soyayyah, sukayi sex d'in su mai dad'i, bayan sun gama suka koma bacci.
Sai wajan qarfe 11 zahra da mashkhur suka tashi daga bacci sanan sukai wanka.

Bayan sun sa kaya kicin suka shiga su kai girki a tare sanan sukazo suka ci a tare. Bayan sun gama ci sama suka koma sukayiwa abdul wanka tare sanan zahra ta shayar da shi cikin kulawa da temakwar mashkhur. To ranar zahra da mashkhur wuni su kai suna shan soyayyah kamar saban aure, sam abdul baya takura musu da yake shi mai haquri ne kamar zahra ko kuka baya yi in ba yunwa yake ji ba.

Ana kiran sallah azahar mashkhur ya fita domin sallah itama zahra tayi tata a gida bayan ta idar ta zauna zaman jiran mashkhur, tana tinnin har qarfe 04:30pm bai dawo daha masallacin ba. Zahra tana cikin wanan tinanin taji wayarta ta fara ringing, ilham ce take kira. Murmushi zahra tai sanan ta d'aga baki d'auke da sallama.

Bayan sun gama gaisawa ilham cewa tai hmm lallai zahra an koma gida miji shine kika ya dani ko waya babu, to nace in bari na kira ki. Dariya zahra tai sanan tace hmm ke dai bari ilham kimin uzuri kullum ina maqale da mijina muna shan soyayyah ina zaki ganni. Dariya ilham tai sanan tace hmmm lallai kice ahi yasa bana ganin ki ko a online.

Inafa zaki ganni ilham muna tare da mijina muna cin saban amarci yanzuma fita yayi masallaci da bazaki same ni bama a wayar ko kin kirani bazan ji ba. Kai zahra ai shiga uku dama ance irin ku shiru-shiru ke da yaya mashkhur in kuka tashi soyayah kunfi masu maga, wlh fad'i ki qara. Haka zahra da Ilham suka d'an sha hira sanan su kai sallama.

Suna sallama zahra ta kira nana, bayan nana ta d'aga sun gaisa, zahra tai ta tsokanar ta irin ta amare. Nana kuwa sai complain take kawowa zahra, zahra tana bata haquri tana cewa a haka zata saba. Bayan zahra sunyi sallama da nana ba jimawa mashkhur yazo, tasowa zahra tai tare da cewa sannu ka da dawowa husband.

Yauwa dear but I want to supers you, murmushi zahra tai sanan tace ok, are you ready my wife, gyad'a kai zahra tai tare da cewa! Yes my husband im ready. Murmushi mashkhur yayi sanan yace ok lest go. Daga haka mashkhur ya kama hanun zahra suka sauka qasa. Bayan sun sauka zahra gani tai sun kama hanyar fita daga falo zuwa farfajiyar gidan.

Amma zahra bata ce komai ba suka ci gaba da tafiya. Bayan sun fita tun daga qofar fita daga babban falon mashkhur ya rufewa zahra fuska da hanun sa a hankula suka cigaba da tafiya. Sun d'aya tafiya kad'an sanan suka tsaya mashkhur ya bud'ewa zahra ido a hankula. Zahra sakin baki tai gani wata rantsatsiyar lafiyayyiyar baqar mota zubin marcedes a gabanta.

Motar sai shining take sabuwa ce qall sabida har da ledoji. Murmushi zahra tai sanan tace hmm congratulations yaya mashkhur motar tayi kyau sosai wlh kace sabuwar mota kayi kai gaskiya na tayaka farin ciki. Congratulations for you my wife cause this car is you on. Zahra wani iwun farin ciki tasa tare da cewa you really.

Yes teddy im really mashkhur ya qarasa maganar yana miqawa zahra saban mukullun motar. Hannu na rawa zahra ta qar6i key d'in motar sanan ta rungume mashkhur sosai tama rasa mai zata ce, shima mashkhur rungume zahra yayi da hannu biyu. Ai zahra kawai sai ji tai kukan farin ciki ya kwace mata.

Bibbiga bayan zahra mashkhur yayi alamun rarrashi, haka yay ta rarrashin zahra har ta samu ta dena kuka. Yaya mashkhur nama rasa da bakin da zan maka godiya zahra ta qarasa maganar tana sakin mashkhur daga hugging. No my teddy bana buqatar godiyar ki, ya kamata na had'a miki da ni zan had'a miki da godiya bayan gift d'in mota.

Na baki gift d'in motar ne sabida kin haifa bin abdul gift d'in born na baki kuma ina mai gode miki zahra ta duk abinda kike so a duniyar nan ki gayamin zan miki shi in dai zai saki farin ciki. Kuma duk abinda na mallaka naki ne bai cancanta kina kuka ba hakan qaramin gift d'in nan ba, na dad'e dayi miki orders motar nan tun kafin ki haifi abdul.

Sabida nayi miki born gift da ita amma kinga bata qaraso ba sai yanzu. Zahra ina sonki ina qaunar ki ina begen ki kuma bazan ta6a manta halaccin da ki kai min a rayuwa ba, lokacin da bana son ki kuma nake cikin wani halin da ba ko wace mace ce zata aure ni ba amma kika yiwa su dady biyayyah, kika aure ni kaka jure duk abinda nai maki wanda bai dace.

Kuma duk da hakan baki dena yimin addu'a ba, kin shiga matasala sosai ta dalilina zahra a rayuwar ki. Ni kuma ADALILINKI rayuwa ta canza I love you zahra bazan ta6a rabuwa dake ba duk abinda zakiyi min a rayuwa komai mununsa zan iya zama dake a duk halin da kika shiga. Mashkhur yana qarasa fad'i hakan zahra ta fad'a jikin sa a karo na biyu cikin kuka tace nima yaya mashkhur ina qaunar ba bazan ta6a rubuwa da kai ba har a bada.

Mu had'e a next page wanda shi nake sa ran ya zama last in sha ALLAH.


ADALILINTA 💜❤💜

BY AMINA BAYERO💜❤💜

*Page 150*

Typing........

Mashkhur yana qarasa fad'i hakan zahra ta fad'a jikin sa a karo na biyu cikin kuka tace nima yaya mashkhur ina qaunar ba bazan ta6a rubuwa da kai ba har a bada.

Qara rungume zahra mashkhur shima yayi cikin kalamai masu tausasa zuciya yake rarrashin ta, daga qarshe dai yaja hanun ta suka shiga ciki haka mashkhur yayi ta rarrashin zahra harta dena kuka. Ranar zahra ko bacci bata iya ba sabida tsabar farin ciki duk juyawar da tai sai ta hango motarta haka ita kad'ai tai ta sakin murmushi kamar ta6a6iya.

Washe gari zahra tayiwa 'yan uwan ta shela ilham yaya abdul nana haidar faruq ammi mama kai duk wani makusan ci zahra ba wanda bata fad'awa ba har videos tai musu ta nuna musu rantsatsiyar motar ta sabida tsabar farin ciki. Tom haka mashkhur da zahra suka cigaba da shan soyayyah su, kamar yarda mashkhur ya fad'a sai da yayi one week bai tifa ko ina ba kullum yana tare da matar sa.

Bayan one week d'in daya d'auka ya koma wajan aiki zuciya cike da qaunar matarsa da babyn sa.
Tom yau zahra tayi kwana goma sha biyu da komawa gidan mashkhur,. Misalin qarfe 3 na rana mashkhur da zahra suna kwance akan bed sun qanqame juna suna bacci kamar yarda suka saba bayan sex.

Mashkhur yana bud'e ido ya fara sosa qafar zahra da farcan qafarsa ta cikin blanket, kamar yarda sukewa junansu in zasu tashi daga bacci. A hankula zahra ta bud'e ido, tana bud'e idon ta taga mashkhur ya lumshe ido kamar dai ba shi yake mata hakan ba. Wuyansa zahra ta shafa tare da had'e fuskar su waje guda tana sauke dogwan nunfashi.

Mashkhur yana bud'e ido suka sakarwa junan su murmushi lokaci guda. Sun jima a hakan kafin zahra tace tashi mi wanka, haka suka wuce toilet hannu riqe da juna domin wanka. Sun d'an jima kad'an kafin su fito d'aura da towel hanun su riqe dana juna. Bayan sun sa kaya marasa nauyi mashkhur zama yayi a gefan bed zahra kuma ta qarasa kan qaramar drowar domin cire wayarta daga caji.

Tana qarasawa taga kamar wayar mashkhur ana kira kuma adede time d'in kiran ya tsinke. Zahra kallo screen d'in wayar tai taga ammi 2 miss call dady 2 miss call. Zahra d'auko wayoyin tai daga tata har ta mashkhur d'in tare da cewa hmmm dady 2 miss call ammi 3 yaya mashkhur wana lefi kai haka. Murmushi mashkhur yayi tare da cewa ni ai na girma da lefi se de ke.

Zahra miqa mai wayar tai sanan ta kunna tata. Kiran ammi 2 na yaya abdul 2, kai Allah yasa lafiya nima kaga ammi da yaya abdul sun kirani har sau biyu, zahra ta qarasa maganar tana zama kusa da yaya mashkhur. Jim mashkhur yayi can yace to ALLAH yasa lafiya bari na kira naji, zahra jim tai gabanta yana fad'uwa.

Mashkhur yana bigawa ammi bigu uku ta d'auka. Bayan mashkhur sun gama sallama da gaisawa da ammi, jim yayi dan sauraran ta. Zahra ji tai mashkhur yace masha ALLAH yaushe? Bayan yayi jim yace me aka samu? Okya wana hospital d'i? Tom shikenan zan gaya mata. Bayan mashkhur ya katse wayar kallon zahra yayi da tuni ta fara fad'ad'a fuskarta da murmushi.

Tsira mata ido mashkhur yayi yace daga waya sai murmushi baki san mai aka cemin ba. Hmmm ai nasan haiwuwa akai to wacece ta haiwu ilham ko ruma?. Murmushi mashkhur yayi tare da cewa sai dai ki canka da kan ki, jim zahra tai sanan tace ruma koh? Dan zahra tasan basu wani jima da waya da ilham ba kuma ruma ce take cewa tun safe bata jin dad'i

Girgiza kai mashkhur yayi sanan yace aa ilham ce, wani iwu farin ciki zahra tai tare da cewa alhamdulilah fatan tana lafiya koh? Gyad'a kai mashkhur yayi alamun ee. To mai ta haifa kai ko ni, murmushi mashkhur yayi tare da nuna kan sa da d'an yatsa,. Ah masha Allah namiji ta haifa kenan to yaya mashkhur maza mu shirya muje.

Hararar zahra mashkhur yayi tare da cewa ba nace miki bazaki sake fita ba sai kinyi shekara. Zaro ido zahra tai sanan tace kai wlh aa ilham ce fa, ee naji zan je na wakilce ki. Turo baki zahra tai sanan tace bana san wakilcin ka da kai na zani in ba haka ba yau kwana zanyi ina kuka. Tinda baki da imani ba ki wahalarmin da kan ki koh?, ee ai gwara wai sabida me ma zakace bazani ba.

Ee sabida ke yanzu in kinje waje kwana kike bakya dawowa ki manta da mijinki. Ah haba a hospital d'in zan kwana, aa ai sai kice zaki tafi gida. Wlh yaya mashkhur bazan je ba ni ko minutes biyar ka kai ni zanyi wlh. Tom naji tashi ki shirya muje kima kwana in na kai ki bazan hanaki ba, ai zakice zaki suna koh?. Tab yanzu sai na tsaya ka hanani zuwa suna zahra ta fad'a a ciki-ciki.

Me kikace mashkhur ya fad’a yana zuba mata albarkacin idanuwan sa. Miqewa zahra tai tare da cewa aa ni ba abinda nace. Ba 6ata lokaci zahra ta shirya tsaf, sanan ta canzawa abdul kaya. Shima mashkhur banyan ya shirya ba 6ata lokaci suka kama hanyar hospital suna tafe suna hira, yana sake koyawa zahra driven dama tun kafin zahra ta haifi abdul mashkhur yake koya mata driving.

Kuma a halin yanzu zahra ta iya tana jira abdul ya cika 3 months ne sanan sai ta fara driving. Amma zahra tana d'an tuqa ta mashkhur wata in sun fita tare amma ba wani tafiya mai tsayi ba. Tom haka zahra da mashkhur suka qarasa hospital zuciyar zahra cike da zumud'i. Kashe motar mashkhur yayi sanan ya juyo ya kalli zahra, na gaya miki de na sake mai-mai ta miki ba kwana zanzo na d'auke ki qarfe shida.

Girgiza kai zahra tai tare da cewa gaskiya ka bari sai 8 kaji, wani kallo mashkhur ya watsa mata tare da cewa au tin daga nan zaki fara, in kikayi wasa zan mayar dake inda na d'auko ko yanzu. Tom shikenan ALLAH ya baka haquri naji duk sanda kake so kazo ka d'auke ni. Hannu mashkhur yasa ya d'auki abdul dake cinyar zahra sannan yace muje.

Haka zahra da mashkhur suka jera zuwa ciki. Kana ganin su dole sai sun birge ka sabida sunyi mugun dacewa. A nitse suke tafiya kuma a tare suke d'aga qafa su sauke kamar wani had'in baki. Bayan su shiga sun tarar da mutan gidan da dama a hospital d'in, a lokacin ma ilham tana bacci, dan haka bayan mashkhur ya d'auki baby yayi mai addu'a sallama yayiwa zahra ya tafi.

Masha Allah babyn ilham shima kyakyawa ne dan suna d'an kama ma da abdul d'in zahra. Shima fari ne tass masha Allah, kama yake da uwar shi ilham zam. Tom bayan ilham ta tashi daga bacci sun sha hira sosai da zahra kamar dai ba itace ta haiwuwa dan ilham tafi zahra d'auriya da jarumta.

Kamar yarda zahra tacewa mashkhur sai wajan qarfe 8 dan har sai da tai sallah isha'i ma sanan mashkhur yazo d'aukar ta. Haka zahra ta rabu da ilham kamar kar a rabu da alqawarin zuwa gobe zata dawo. Haka mashkhur suka koma gida shi da zahra da baby abdul, suna tafe suna hira har suka qarasa. Bayan sun qarasa zahra tai wa abdul wanka, sanan itama da mashkhur su kai wanka,. bayan sunci abinci suka kwanta.

Bayan sun kwanta aka sakeyi musu waya, domin sanar da su itama ruma ta haiwu a daran ta haifi d'iya mace. Zahra ta sake jin farin ciki sosai, cikin wanda take ciki, tana godewa ALLAH da ya azurta su da d'iya mace, itama zahra taso ilham ta haifa musu mace amma Allah ya bata namiji sai gashi ruma ta haifa musu d'iya mace da soke so.

Tom ranar zahra haka ta kwana cikin farin tana ta ALLAH-ALLAH gobe tayi mashkhur ya kai ta da safe tun kafin ma ya tafi office. Mashkhur da kyar ya iya tashi sallah asuba sabida mutuwar jiki da ciwan kai sama-sama yana dawowa ya koma bacci. Ko da zahra ta tashe shi da safe haka yace shi ba zai iya fita office ba yau ba shi da lafiya amma in rana tai sanyi zai kai zahra taga babyn ruma.

Tom har wajan azahar mashkhur bai dena ciwan nan ba, zahra ta damu sosai itace kawo wanan kawo wanan, amma mashkhur ya kasa cin koma. Sai wajan qarfe 3 sanan ya yarda ya sha tea da cake shima sai da zahra ta fara yi mai kuka tukunna yaci kad'an ya sha magani, haka zahra ta maqale shi suka kwanta tare.

Wajan bayan magriba mashkhur ba lefe yaji gwarin jikin sa dan har sun samu sunci abinci tare da zahra. Da yake itama kasa cin abinci tai sabida rashin jin dad'i mashkhur. Bayan sunci sun d'an yi hira sama-sama duk da kuwa mashkhur baya son magana sabida kawai yaga hankalin zahra ya d'an kanta.
Ranar dai zahra da mashkhur basu je ganin babyn ruma ba kamar yarda suka so.

Washe gari.

Mashkhur ya samu sauqi sosai, dan bayan sunyi salla asuba ma, duk yabi ya takurawa zahra. Dole zahra ta biye mai yayi abinda yake so sanan wani saban bacci ya d'auke su. Wajan qarfe 7 suka farka, bayan sun farka a hanzarce suka shiga su kai wanka. Sanan zahra tayiwa abdul wanka shima ta shirya shi ta ba shi nono ya sha. Bayan ya sha breakfast su kai ita da mashkhur a hanzarce.

Ba wani abinci kirki bane dan zahra ta tsaya d'ora abinci zata 6atawa mashkhur time. Da cake da tea su kai breakfast d'in, shima suna sha mashkhur yana ta tsokanar zahra cikin sigar soyayyah murmushi zahra kawai take a zuciyar ta tana hmmm ka samu sauqi dole ka takuramin ai amma ni bazan biye maka ba mu koma gidan d'azu.

dan tasan ba qaramin akin mashkhur bane tana biye mai zasu sake wani sex d'in kuma suzo su kasa fita, tinda yanzu zahra taga alama mashkhur baya gajiya da hakan. Bayan sun gama breakfast d'in zahra sama ta koma ta d'auko abdul da hand bag d'in ta bayan ta d'auko ba 6ata time suka fita. Suna tafe mashkhur yana sake yankawa zahra horning akan karta sake tace zata kwana.

Da yake tun daran jiya aka sallamo ruma da ilham d'in daga hospital suna gida. Bayan mashkhur ya sauke zahra a gida ko ciki bai shiga ba ya tafi sabida sauri yake.
Hannu riqe da abdul zahra ta kwad'a sallama babban falon ammi. Hjy kaka da ammi ta gani zaune sun hira, bayan sun amsa fuska sake hjy kaka tace ah wa nake gani kamar 'yar gaban goshi da safiyar nan.

Murmushi zahra tai tare da cewa au kama ma kike gani hjy kaka to nice, zahra ta qarasa maganar tana qarasawa. Lallai to sannu ki da zuwa shi ina yake ko yana daga waje ne?. Aa ya tafi office sauri yake sai anjima in ya dawo. Allah sarki Allah ya dawo da shi lpy bani jikan suruka ta na d'auka. Murmushi zahra tai sanan ta miqawa hjy kaka tana sauke nunfashi kamar wanda ta d'auko tilin kaya.

Ammi ina kwana zahra ta qarasa maganar tana zama a gefan ta. Itama ammi fuska a sake tace lafiya qalau zahra sannu da qoqari kalar wanan nishi haka kamar kin d'auko kayan wanki. Dariya zahra tai tare da cewa ai kin san tafiyar ce da d'an tsayi kuma abdul yanzu yayi nauyi. Kai zahra da lalaci dande abdul ina yayi wani nauyi da zai gajiyar da ke haka.

Hmmm ammi kenan bazaki gane ba kinga hannunna ma duk ya qage. To ai da kin sani koya shi ki kai. Ni ai ban iya goyo shi ni kad'ai ba ammi. Hmmm gaskiya zahra ya kamata ki iya har yayi 2 month baki iya goyo ba yanzu in bakya goya shi taya zai saba. Ah ina goya shi mana in yaya mashkhur yana nan sai ya d'ora min shi a bayan.

Hmmn wanan ga6intar taki zahra Allah ya yaye miki ita kina girma mai makwan wayo sai rashin wayo. Kai ammi kullum sai ki tacewa bani da wayo yanzu in abdul ya girma a gabansa zaki ringa cemin bani da wayo zahra ta qarasa maganar cikin shagwa6a tana kwanciya a jikin ammi. Dariya ammi tai sanan tace sosai ma tinda inna yi miki fad'a bakya gyarawa.

Kinga in nai miki a gaban sa kyaji kunya ki gyara, ah kafin nan ma nayi hankali. Hmmm to ALLAH yasa zahra Allah yayi muku albarka ya kawo zuri'a d'ayyi ba yasa ki haifa mana 'yan biyu. Zaro ido zahra tai sanan tace tabbb wlh ammi bazan iya ba daga abdul bazan sake haiwuwa ba bana so. Ah kamarya bakya so ah gaskiya ta gaban goshi kar ki soma cewa haka.

Cewar hjy kaka, ammi cafe zance tai da hmmm ai gani takr kamar bazata iyaba hajiya, nima lokacin da na haifo mashkhur sai da nayi irin tinanin ta bazan sake haiwuwa ba. Amma daga qarshe da ban sake haiwuwa da wuri ba bakiga yarda na damu ba, yawanci mata haka suka wanan tinanin bayan sunyi haiwuwar fari wlh.

Hmmm shikenan ammi ki kwantar da hankalin ki zan miki takwara tukunna ai biyu sunyi koh. Hmmm zahra kenan tom ALLAH uban giji ya nuna mana lokacin ya qara muku zaman lafiya da farin ciki me d'orewa. Cikin jin kunya zahra tace ameen ammi mu sanan ta miqe tare da cewa bari naje wajan su ilham...............

ADALILINTA 💜❤💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

DOUBLE PAGE....

Tom jeki ki duba ko sun tashi ba lallai ne ma sun farka daga bacci ba. Tom ammi bari naje na duba, zahra ta qarasa maganar tana kama hanyar hawa sama.
Zahra tana zuwa murd'a handel d'in room d'in qofar tai ta shiga, kamar yarda ammi ta fad'a suna kwance suna bacci ko wacce da babyn ta a 6angaran ta.

Zahra qarasawa tai ta leqa fuska babyn ruma. Masha allah zahra ta furta cikin zuciyar ta, ba laifi babyn itama tana da kyanta dede gwargwado. Idon ta biyu ba bacci take ba a hankula zahra tasa hannu ta d'auke ta sanan ta zauna akan bed. Hmmmm sai yanzu kika zo uwar soyayyah sannu to. Murmushi zahra tai tare da cewa har kin tashi kenan.

Eh na tashi shine jiya kince zaki zo nai ta baza idanuwa shiru kake ji ko babyn ruma ya kamata kizo ki ganta. Wlh nayi niyar zuwa yaya mashkhur ne baya jin dad'i shi yasa. Oh Allah sarki ina bacci amma jikina ya bani kinzo ilham ta qarasa maganar tana tashi zaune. Hmmm ilham uwar qarya, to naji karki yarda amna wlh da gaske nake.

Hmmm tom na yarda maman baby mai za'a sawa babyn namu cewar zahra. Hmmm nima dai ban san mai za'a sa mai ba sai abinda baban sa yace. Zahra kinga da yaron nan ya fara sacewa kamar shi ta fara futowa sai naga kamar suna kama da abdul qarami fa. Eh nima na gani wlh tun sanda aka haife shi na lura da hakan cewar zahra, uhmm to ya za'ai jini ba wasa ba.

Daga haka babyn ilham ya fara kuka wanda kukan sa sai daya tashi ruma daga bacci. Ruma tana ganin zahra ta miqe daga kwance fuska cike da murmushi suka fara gaisawa, zahra tana mata barka. Zahra tayi mamaki ganin yarda ilham take bawa d'an ta nono kamar ba sabuwar haiwuwa ba hankalin ta kwance ko kunya.

Zuba mata ido zahra tai sai yanzu take yarda da ake cewa ilham ta fita wayo sosai ita kuma doluwa ce. Zahra kalar wanan kallon kamar baki san ni ba. Hmmm ai gani nan kamar bake ba inye su ilham an zama uwa koh?. Hmmm zahra kenan tinda ke kika zama uwa ai kowa zai zama. Harar ta zahra tai tare da cewa to me kika mayar dani.

Uhmm sa'a ta mana na mayar dake, hmmm ke kin san dai ko da minti d'aya mutum ya girme ka ya girme ka bare ma da kwana d'aya ma, ke ko ban giirme ki da kwana d'aya ma ba, ai ilham dole ki bani respect tinda yayan ki nake aure zahra ta qarasa maganar tana mata kallon up and down. Hmmm sannu yaya zahra sai uban son girma amma ba wayo.

Hmm kyaji da shi de mara kunya zahra ta fad'a fuska a had'e. Haka de ilham da zahra su kai ta fad'a kamar dai yarda suke wataran in ta motso su.
To zahra taji dad'in wunin da tai sosai a gidan ammi sun sha hira da ilham da ruma.
Misalin qarfe 5 na yamma zahra da ilham suna zaune a qasa suna cin abinci.

Ita kuma ruma tana daga kan gado tana bawa 'yar ta nono da yake ita ba yunwa take ji ba tun abinci rana ya ishe ta. Abdul yana kan cinyar zahra a kwance yana ta sharar bacci abinsa da yake bata wani jima da ba shi nono ba. Tun daga qofar room su zahra suka ji murya ammi tana cewa haba kizo mu shiga ciki mana sai ki ringa wani abu kamar wata baquwa.

Suna gama jin haka sukaji an murd'a handel d'in qofar an shiga ammi ce ta fara shigowa sanan baquwar ta biyu bayan ta. Gaban zahra fad'uwa yayi rass saka makwan ganin baquwar. Duk da kamaninta sun canza tayi muni zahra ba zata ta6a manta taba. Da sauri zahra da ilham suka kalli juna cikin mamaki. Ba kowa bace face momy wato halima, maman yaya abdul da ruma.

Allah sarki ruma da sauri ta sauke babynta ta gyara rigarta sanan ta taso da sauri ta nufa mahaifiyarta ta ta fad'a jikin ta, tare da fashewa da wani kukan mai ban tausayi. Allah sarki ruma raban da taga mahaifiyar ta tun lokacin da asirin ta ya tuno dady yayi mata saki uku. Gashi yanzu har tayi aure ta haiwu, dan ita ruma tama cire ran zata sa momyn ta a ido.

Itama momy fashewa tai da kukan tausayi tare da cewa Allah nagode ma da ka sake nuna min 'yar ta da na dad'e ina son ganin

Please Login or Register in order to submit comment