Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tare da cewa na farko dai abinda za'a yi shine!. Zan had'a zahra da abinda tafi so a rayuwar ta, wato gyad'a zahra tana son gyad'a musamman mai gishiri kuma ta dad'e bata ci taba, aciki zan mata asirin taci. Shi kuma mashkhur zan had'a mai nashi da abu mai sha sanyi, a cikin zan had'a mai asirin. Ita kuma 'yar kishiyar ki ilham, gashinta silli d'aya za'a ciro miki.

In an ciro miki gashin nata sai ki had'a da garin maganin da zan baki ki qona to daga nan zata rabu da mijin da ka yi mata baiko zai ji ya tsane ta itama zata ji ta tsane shi mahaifin ta da kansa zai mai da baikwan kan 'yarki rumasa'u. Murmushi saratu tai tare da cewa! Aikin ka yana kyau boka. Itama momy cikin jimami tace to boka ni dai kasan ba magana nakewa zahra ba taya zan bata gyad'a taci?.

Boka kuwa cewa yayi, hhhhhhh karki damu naga yanzu wata shaguwa mai kyau ta shiga tsakanin ta da babbar 'yar ki mace ita zaki bawa ta bata. Girgiza kai momy tai tare da cewa boka ai yanzu rukee bata jin magana ta sam ta halinta ya kuma irin na qanwarta ruma tafi son 'yan uwanta dani. Girgiza kai boka yayi tare da cewa! Zan baki wani maganu ki barbad'awa wa 'yayanki a nama to zaki mallake su duk abinda kikace suyi shi zasuyi bazasu qara yi miki musu ba.

Murmushi momy tai tare da cewa yauwa boka aikin ka yana kyau nawa kake buqata. Mutsuka ido boka yayi ya bud'e tare da cewa! Za'a samo hantar sauro za'a samo hanjin quda da farcan kiyashi, sanan zamu yanka bijiman shanu biyi mu bawa aljanu jini su sha dan suji dad'in yi mana aiki. Cikin mamki saratu tace boka ina zamu iya samo wanan sai dai mu baka kud'i kawai a suyo.

Dariya boka yayi tare da cewa ku bawa d'an guduwa, zai kawo duk abinda ake buqata, ku ajiye mai kud'in anan. Momy bud'e jakar ta tayi ta curo damin kid'i dubu d'ari biyar tare da kallan saratu tace saratu bani da cash iya wanan ne koh kin futo da cash ne. Bud'e jakar ta saratu tai ta zaro dubu d'ari biyu tare da cewa! Kinga nima da abinda na fito dubu d'ari biyu ce kawai.


Kallan boka momy tai tare da cewa! Boka nawa kake buqata. Dariya buka yayi tare da cewa, bani nake buqata ku kuke buqata sabida tai maka muku zanyi, ku tattara kud'in gaba d'aya ku ajiyewa d'an guduwu a gefe zai siyo muku, in zaku dawo gobe ki dawo da adadin yawan kud'in da zaku ajiye sabida gobe zan had'a muku maganin gobe ki dawo ki kar6a.

Momy kar6ar kud'in hanun saratu tai tare da cewa! An gama boka. Dariya boka yayi tare da cewa! Wanan yarinyar zahra ce zata fara mutuwa daga nan sai mijinta yabi bayanta bayan kwana goma da mutuwar ta. Murmushi momy tai tare da cewa! Godiya dubu boka ALLAH ya biya ma. Wata uwar tsawa boka ya bugawa momy tare da cewa' ba'a kira musu sunan ALLAH anan wajan.

Nan da nan momy da saratu suka bawa boka haquri sanan suka tarkata jakunkunan su da takalman su suka fuce. Suna shiga cokin mota, momy ta kalli saratu tare da cewa gaskiya saratu wanan aikin yayi tsada sosai,. Haba yaya halima ba dole yayi tsada ba wanan karon rai za'a kashe fa?. Jinjina kai momy tai tare da cewa! Hakane amma yanzu saratu sai na sake kwana a garin nan?.

Haba yaya halima mai nene ai ba komai, wlh in dai da biyan buqata ba shikenan ba. Murmushi momy tai tare da cewa hakane burina ya kusan cika sai na sa maryam ta zubar da hawaye da idanun ta sai na sa mata ciwan zuciya. Daga qarshe kuma na rabata da d'ana adul ya dai na yi mata biyayya kai har sai na sa badul ya d'aga hannu ya zuba mata uban Mari.

Dariya saratu ta saki tare da cewa anya yaya halima abdul zai iya marinta itace fa uwar goyan sa ita ya bud'e ido ya gani ba ke ba nasan ma yafi santa kuma yafi ganin mutuncin ta a kan ki. Sosai ma ai yaran nan baya ganina da gashi kullum sai yaje ya gai da ita, ni kuwa sai yayi wata bai shigo waje na ba, amma zata gane bata da wayo mai yafi zafi na kashe mata d'an ta sanan na rabata da abdul ai sai goma ta had'ewa maryam da ashirin..................

ADALILINTA💜❤💜

BY AMINA BAYERO💜❤💜

Double page.........

Washe gari............

Haka momy da saratu suka qara kwasar qafa suka tafi wajan boka,. Suka qarbi magungunan su, sanan yayi musu bayani yadda momy zatai amfani da ko wanne. Daga haka suka cika mai kud'i sa sanan suka tafi. Gidan saratu su momy su koma suka bud'e babin wata hirar. Bayan sun gama suka wuce gidan au momy tai wa iyayan ta sallama sanan, sanna saratu ta kai ta tasha a mota suka rabu saratu tana yiwa momy fatan nasara...........

KANO..............

to fah 6angaran su zahra kuwa sun samu fahimta juna sosai da rukee, rukee lokaci guda ta koma mutuniyar kirki sallah ku wuce ta batayi tayi nadama sosai ta koma ga ALLAH. ga wata irin amintaka da shaquwa da ta shiga tsakanin su da zahra, yanzu zahra da ilham sunyi sanyi zahra ta mayar da rukee kamar ilham, a kusa da juna suke kwana wataran ma kusan kwana suke suna hira.

Yau alhamis, ta kasance saura kwana d'aya a raba auran zahra da mashkhur. Ilham da ruma suna sama suna ta hira. Ita kuma rukee tana can sit room d'in baqi ita da dactor habib suna shan zance. Zahra kuma tana can wajan ammi tana yarfa mata kitso mai kyau. Ammi tana gama yiwa zahra kitso zahra ta miqe tare da kwasar ribbons d'in ta tana cewa ammi bari naje qasa.

Ammi cewa tai bazaki tsaya nai miki parking d'in ba, noqe kafad'a zahra tai tare da cewa gaskiya yaya abdul ne zai yimin parking ya fiki iyawa. Murmushi ammi tai tare da cewa oh har yanzu dai ba wadda ya iya yi miki parking sai yaya abdul tin kina yarinya haka kike cewa gashi har kin girma baki dai na ba.

Da sauri zahra ta fita daga bedroom d'in ammi, tin daga saman bene zahra take kwallawa yaya abdul kira. Doguwar rigar yadin rariyace a jikin zahra ba laifi ta d'an kwanta a jikin ta, ga gashin nan nata ya fazo har baya, da yake kalaba ammi taiwa zahra duk ta watse ta ko ina zahra tana qoqarin sauka daga bene kallabar suka sake warqa stewa dan har sun rufe mata ido.

A dai dai lokacin mashkhur shima ya fara hawa kan step d'in, mashkhur kuwa cigaba da hawa kan step d'in yayi tare da zubawa zahra idanuwa. Wadda take sauka da sauri tana qoqarin bud'e qashin da ya rufe mata fuska, ga jikinta sai girgiza yake. Musamman ma breast d'in ta da suka cika tam a qirjin ta. har time d'in kwallawa yaya abdul kira zahra take. Mashkhur yana zuwa tsakiyar benan ya dai na tafiya ya zubawa zahra ido ciki da shauqi.

Zahra tana qoqarin bud'e gashin ta tazo tsakiyar step kenan taji sunyi wani mugun karo da mutum. Zahra ta fad'a qirshin mashkhur, da sauri tasa hannu ta rungume shi sanan tace yaya abdul d'in na. Mashkhur ji yayi kamar an watsa mai garwa shi a zuciyar shi da yaji zahra ta ammabci sunan abdul.

Zahra kuwa sake kwantar da jikin ta tai a qirjin sa sanan ta lumshe idon ta. Mashkhur yana jin tudin breast d'in zahra ya sauka akan qirjin sa sai yaji wata nutsuwa kuma zuciyar shi tai mai sanyi kad'an. Zahra kuwa tana gama kwantar da jikin ta a qirjin mashkhur ta ji qamshi turaran mashkhur ya daki hancin ta.

Da sauri zahra ta saki mashkhur tare da ja da baya. Mashkhur ta gani tsaye fuskar shi wani iri ita ba damuwa take nunawa ba kuma ita ba faran ciki take nunawaba. Mashkhur kuwa wani mugun kallo ya fara bin zahra da shi a zuciyar shi yana aiyyan da abdul ne kenan haka za tai mai?. Zahra kuwa cikin tsoro tace kayi haquri nayi tinanin yaya abdul ne.

Mashkhur kuwa wani irin tsaki yaji zuciyar shi yace wato da abdul ne da tini yaga wanan tafiyar da take duk jikin ta sai wanan girgizawa yake musaman ma breast d'in ta. Zahra tana cikin nazari taji mashkhur yace banza mai tafiyar 'yan iska kawai tare da jan wani dogwan tsaki sanan ya shige ya ra6e ta ya wuce abinsa yabar zahra a tsaye tana nazari.

Ci gaba da tafiya zahra tai a cikin zuciyar ta tace tafiyar 'yan iska kuma?, yanzu karo na biyu yaya mashkhur yake cemin mai tafiyar 'yan iska ni kuwa wace irin tafiya nake haka?. Zahra tana gama sauka daga benan ta saki wani sirrin tsaki tare da cewa duk wani nabi na damu kai dan ya gaya min haka wata qilama kawai fad'a yake yi.

Zahra tana gama fad'in haka ta hangi yaya abdul yana shigowa falon. Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa yauwa yaya abdul zo ka yimin parking gashina. Yana qarasawa zahra ta miqa mai ribbons d'in. Kar6a yaya abdul yayi tare da cewa baki da damuwa baby na zo muje mu zauna wana iri kike so. Dariya zahra tai tare da cewa! Mai kyau dai amma karka matse min kai na.

Baki d'auke da sallama mashkhur ya shiga d'akin ammi,. Ammi da ta fito daga toilet tana tsane hanunta da towel, amsawa tai tare da qarasowa ta zauna a gefan mashkhur. Ammi ina wuni mashkhur ya fad'a fuska ba walwala. Lafiya qalau yau naga bakazo da safe ba ko breakfast bakayi ba da fatan dai lfy?. Jinjina kai mashkhur yayi tare da cewa ammi lafiya qalau kawai bacci nake.

Gyara zama ammi tai tare da cewa mashkhur gobe ne jumma'a fa. Kwarai ammi ina sane, gobe ne dady zai raba auran mu da zahra. Cikin jimami ammi tace saki nawa zakayi mata?. Mashkhur bai wani tsaya kwana-kwana ba yace saki uku cif. Cikin mamaki ammi tace saki uku mashkhur wai dan ALLAH kai bazaka iya haquri ka cigaba da zama da ita ba?.

Girgiza kai mashkhur yayi tare da cewa gaskiya ammi bana son ta bazan iya zama da ita ba. Tom shikenan mashkhur ina baka shawara ka tsaya kai dogwan nazari karkazo kuma kayi nadama dan kafin ka samu mace kamar 'ya ta zahra da wuya. Cikin mamaki mashkhur yace wana nazari, nifa ammi bana son ta kuma ko na sake ta ba aure zanyi ba ni bazan ta6a aure a duniya ba.

Ta6e baki ammi tai tare da cewa ai kan ka kayiwa ba wani ba kuma muddun kasan wata alaqa ta shiga tsakanin ka da zahra komin qanqanta ta tofa karma ka sake ka sake ta. Cikin tsarguwa mashkhur yace sabida mai ammi?. Girgiza kai ammi tai tare da cewa ni dai shawara nake baka kawai. Ta6e baki mashkhur yayi tare da cewa! Ni ba abinda ya ta6a shiga tsakanina da ita ko hanunta ma ban ta6a ta6awa ba.

Hmmmmm nikuwa amina bayero nace mashkhur kaji tsoran ALLAH zan tona fa. 😂

Ammi kuwa cewa tai yayi kyau haka ake so ka dai bi a hankula. Mashkhur kuwa miqewa yayi tare da cewa to sai anjima. Sanna ya fuce abinsa, ammi tana ganin mashkhur tasan ba da gaske yake gaya mata hakan ba, kuma ta bashi shawara ne sabida tasan halin mashkhur in dai wata alaqa ta shiga tsakanin da zahra tofa da wuya in zai iya mantawa da ita.

Mashkhur rai ba dad'i ya fita daga d'akin amm. Tin daga saman bene mashkhur ya hango zahra da abdul. Abdul yana kan kujera zahra tana zaune akan carpet ta sunkuyar da kai abdul ya d'uqufa sai tattare mataka kitson yake yana mata parking. Sosai mashkhur ya rinste ido zuciya cike da damuwa.

Nan da nan mamaki ya kama mashkhur akan wai mai yake damun sane duk sanda yaga zahra da abdul sai yaji wani abu mara dad'i a zuciyar shi. Bama abdul ka d'ai ba ko ranar nan da mashkhur yaga ahmad yana mulmulawa zahra goshi a russian sai da yaji wani abu mara dad'i a ransa. Fuskar nan tasa murtike mashkhur ya sauko daga kan benan.

Yana saukowa abdul ya gama yiwa zahra parking d'in gashinta. Ai kuwa parking d'in yayi mata yau sosai nesa ba kusa ba. Wow baby na kinga yadda kikayi kyau kuwa? Murmushi zahra tai tare da cewa oh really yimin picture guda d'aya I want to see now. Mashkhur kuwa wani dogwan tsaki yaja tare da fucewa yabar wajan.

6agaran zahra da abdul bama susan mashkhur yana yi ba. Mashkhur yana fita daga part d'in ammi a cikin zuciyar shi yace to wai ni mene na damun kai na bayan ma nan da gobe zanyi mata saki uku?. Mashkhur yana gama ayyana haka a zuciyar shi yaji zuciyar shi ta d'an yi mai sanyi.

To momy ta dawo gida lafiya qalau, tana shigowa ta wuce part d'in ta. Sanan ta shiga kicin ta fara d'ora farfeson nama wanda yasha maganin mallaka,. Tana gamawa ta juye a plate ta rufe sanan ta had'a zo6o mai masifar sanyi sai wani tashin qamshi yake, lokacin da zata dafa zo6on ta zuba maganin nan na boka da shi ta dafa.

Bayan ta gama had'a zo6an da yasha garin magani qanqara ta samai sanan ta mayar da shi firinji, ta koma bedroom d'in ta. Wanka tayi ta canza kayan sanan ta futo da gyad'ar da boka yace ta bawa zahra, bayan ta futo da ita daga jaka ta ajiye ta a kan merro sanan ta fuce daga d'akin. Tinani momy tai taya zata kira rukee da ruma ta basu farfesun naman nan wanda yasha maganin mallaka.

Haka dai momy ta d'auki zo6an nan sanan ta wuce part d'in su mashkhur. Tana shiga kuwa taci sa'a taga haidar ya futo. Kallan sa momy tayi tare da cewa yauwa haidar kaje ka kiramin ruma da rukee kace na dawo suzo yanzu-yanzu. Cikin ladabi haidar yace tom momy daga haka ya fuce daga part d'in. Momy kuwa ajiyar zuciya tai sanan ta wuce bedroom d'in mashkhur.

Qofar a kulle take amma momy sai ta fara knocking, bata wani dad'e tana knocking ba mashkhur yazo ya bud'e fuska ba walwala. Yana ganin momy ya kwakwalo Murmushi dole tare da matsa mata yana cewa momy shigo. Momy tana shigowa ta samu table ta ajiye zo6an nan da yake tashin qamshi sanan tace yauwa mashkhur dama haka nace bari na kawo ma zo6o.

Dafawa nai sabida ina sha'awa kuma nasan kana son abu mai sanyi. Murmushi jin dad'i mashkhur yayi tare da cewa wow momy na godiya miki wlh, kamar kinsan bana jin dad'i inaso nasha abu mai sanyi, nayi missing d'in ki jiyama nazo sai naga qofar ki a kulle da na tambayi su rukee sai suka cemin wai kin tafi kaduna.

Murmushi mugunta momy ta saki sanan tace kai dai bari mashkhur wlh kawuna ne ya rasu shine na tafi gaisuwa. Allah sarki momy ALLAH ya jiqan shi yasa halinsa na gari ya bishi. Momy a cikin zuciyar ta cewa tai ALLAH dai ya jiqanka yasa halinka na gari ya bika dan kana gab da rasa ranka yaro. A fili kuma cewa tai ameen mashkhur ngd. Mashkhur cewa yayi momy bari na shiga toilet na fito sai nasha zu6an nan dan yawuna har tsinkewa yake.

Murmushi momy tai a zuciya tace bama yanzu zai tsinke ba sai ka yanke jiki ka fad'a zai tsinke, a fili kuma cewa tai tom nima bari na tafi 6angare na sai anjima. Daga haka momy ta fuce shi kuma mashkhur ya shiga toilet zuciya cike da zumud'in ya futo yasha zo6an momy. Momy tana fita cikin farin ciki ta kama hanyar part d'in ta tace hmmm mashkhur kana shan zo6an na, nan da kwana goma zaka mutu, ke kuma zahra yau zakici gyad'ar nan kuma yau zaki mutu gobe a binne ki.................

Hmmm tab wanna shi ake kira da innalillahi'wa'inna'ilaihirraji'un.

Kuna ganin mashkhur zai tsallake tuggun momy kuwa?.

Hmm kuna ganin zahra zata tsallake yau bata mutu ba kuwa?.

Ya zancan auran zahra da mashkhur kuwa?.

Waiiii? 🤔 nima kai na amina bayero ina kokwanta wanan lamarin dan har na miqa kai ga momy.😢😢😢

Ku biyo ni a next page dan jin ya zata kaya.

ALLAH yasa mu dace mufi qarfin zuciyoyin mu, ALLAHUMMA ameen......

Anan na kawo qarshan littafin ADALILINTA na biyu mu had'e ana uku.


ADALILINTA💜❤💜

BY AMINA BAYERO💜❤💜

TYPING.............

*101*

Barja mu da dawowa ADALILINTA na uku wanda shine qarshe littafin daga na uku bazan cigaba da rubutawa ba, fatan anyi wuto mako lafiya.

Momy tana fita cikin farin ciki ta kama hanyar part d'in ta tace hmmm mashkhur kana shan zo6an na, nan da kwana goma zaka mutu, ke kuma zahra yau zakici gyad'ar nan kuma yau zaki mutu gobe a binne ki.................

Haka momy ta koma part d'in ta cike da faran ciki, tana shiga ta wuce kicin domin d'ora abinci sabida yunwar da take ji. Momy tana d'ebo kayan miya ta ajiye sanan ta fuce daga kicin d'in domin hawa sama bedroom d'in ta ta d'auko wayar ta ta bigawa su ruma dan su dawo ta basu maganin mallakar nan.

Momy tana shiga d'akin ta ta hangi rukee ta bada baya akan kujerar mudubi ga dukkan alamu abu take ci. Momy cewa tai uwar kwad'ayi mai suka baki kikeci ina ruma take. Fuska a sake rukee ta jiyo riqe da ledar gyad'ar da momy tazo da ita domin bawa zahra tana cewa momy sannu da zuwa gaban momy ne ya gad'i rasa, rass, rass duk da bata kula da ledar hanun rukee ba amma taji qamshin gyad'ar.

Rukee kuwa cigaba da magana tai da cewav ruma abinci suke ci ga tanan, ni kuma anan naga gyad'ar na d'au!!!!! Ciki tashin hankali momy ta qaraso inda rukee take ta fizge ledarvgyad'ar da take hanun rukee tare da cewa! Ke rukee baki da hankali wanan gyad'ar ta asiri ce zahra zan bawa kuma asirin mutuwa akayi a ciki. Cikin mamaki rukee tace mutuwa kuma momy?.

Cikin tashin hankali momy tace tambaya ta ma kike mutuwar farar d'aya ma. Cikin baqin ciki rukee tace kin gani ko momy ai sai da na baki shawara ki dena cutar 'yayan wasu, gashi yanzu kin cuci wasu ya koma kai na shikenan momy tinda kinyi silar rasa raina, rukee ta qarasa maganar tana tari. Cikin tashin hankali momy ta cewa! In sha ALLAH rukee bazaki mutu ba ai kad'an kika ci gyad'ar koh.

Wani irin tari ruma ta ringa yi tana jan nunfashi da kyar,. Nan da nan momy ta gigice ta rungumo rukee jikin ta.
Mashkhur cikin zumud'i ya futo daga toilet, yana fitowa ya rufo qofar sanan ya juyo ya fara qoqarin tafiya kan table d'in. Mashkhur tsayawa yayi cak saka makwan ganin abudul yana shan zu6on harma ya kusan shanyewa. Da sauri mashkhur ya qasa wajan domin kwacewa amma kafin ya qarasa abdul ya shanye tass.

Cikin rashin jin dad'i mashkhur yace haba abdul kaga yadda nasa rai akan na fito nasha zu6an nan kuwa?. Murmushi abdul yayi tare da cewa! Ayy wlh yaya mashkhur ban san ka qagu kasha ba, nayi tinanin bama ka cikin bedroom d'in zuwa nai muyi hira shine na tarar da zo6an kuma gashi ya ban sha'awa shine nasha ALLAH dai yayi ba raban ka.

Cikin rashin jin dad'i mashkhur yace momy ce ta kawo min shine na shiga toilet fa, kafin na fito harka shanye. Cikin rashin jin dad'i abdul yace oh sorry my bro. Murmushi mashkhur yayi tare da cewa! Ba komai abdul d'ina, bari naje na kar6o wani a wajan momy,. Abdul cewa yayi zona raka ka musha tare dan nima bai ishe niba.

Murmushi mashkhur yayi tare da cewa! Kai dai abdul ka cika kwad'ayi yanzu da guba na zuba da tuna kasha ka mutu nayi asarar ka? . Dariya abdul yayi tare da cewa, nasan ma bazaka ta6a hakan ba tinda kasan kana da kwad'a yayye kamar ni yana shigowa bedroom d'in ka ba izini ba knocking. Girgiza kai mashkhur yayi tare da cewa! Ai kasan bana barin qofar bedroom d'in na a bud'e tsautsayi ne kawai.

Dariya abdul yayi tare da cewa, tsautsayi zan rabaka da zo6o mai sanyi ba. Murmushi mashkhur ya sake yi tare da cewa! Zo mu tafi dai, haka suka kama hanya part d'in momy suna tafe suna hira, abdul ya riqe cup d'in a hanun sa yana tsokanar mashkhur da cewa! Ai muna zuwa ni zan fara sha tinda ga cup d'in a hannu na daga bisa ni in na qoshi kasha ragowa.

Su mashkhur da abdul suna zuwa part d'in momy, mashkhur ya zaune akan kujera tare da cewa! Abdul duba mana kicin ko tana nan, ba musu abdul ya shiga kicin d'in amma ba ga momy ba, sai ya fara duba firnji ko zai ga ragowar so6an amma bai gani ba. Futowa yayi yace yaya mashkhur bata ciki bari na hau sama na duba.

Daga haka abdul ya hau sama ruke da cup d'in zo6an a hanunsa ga bakin sa yayi jajawur duk da bakin nasa jane kuwa amma kana gani zaka shida yasha wani abu mai kala sabida haf harshansa da haqoran sa zo6an ya d'an kama. Abdul yana zuwa qofar bedroom d'in momy yaji kakari da kukan momy hankali tashe ya shiga, yana shiga yaga yaga ruma kwance jini na fita ta hancin ta.

Cikin tashin hankali abdul yace momy lafiya, momy da sauri ta d'ago ta kalli abdul, abdul kuwa sabida tashin hankali yar da cup d'in hanunsa yayi tare da qarasowa wajan da su momy suke a sukwa ne. Abdul yana tsugunawa cikin matsanan cin tashin hankali momy tace abdul mai ya had'aka da cup d'in nan bayan yayan ka mashkhur na kai wa.

Abdul magana ya farayi a firgice bakin nan nasa duk yayi ja alamun yasha zo6an. Momy na shiga d'akin sa yana toilet shine na shanye, abdul ya qarasa maganar yana ta6a rukee cikin tashin hankali yake cewa! Rukee!! rukee!! rukee!! Momy kuwa d'ora hannu tai tare da fasa wani uban iwu ta fad'i qasa sumammiya.

Mashkhur da yake qasa yana jin iwun momy ya miqe, yana miqewa sai ga ruma ta shigo d'auke baki d'auke da sallama. Cikin firgici mashkhur yace ruma maza ki hau sama ki duba lafiya yanzu naji iwu. Cikin ladabi ruma tace to yaya mashkhur amma a zuciyar ta sai tace qilama momy ta aunty rukee take duka tinda ita abin duka baya mata kad'an. jiki a sanyaye ruma ta

Please Login or Register in order to submit comment