Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abdul da yayi ya nufo su. Zahra kuwa mamaki take wanan zagin da mashkhur yayi mata haka na mene, wana laifi tai.

Ahmad yana qarasowa ya bud'e bayan mota tare da cewa! Yaya mashkhur bismillah, mashkhur ji yayi kamar ya wanke abdul da mari amma a fili d'an murmusawa yayi sanan yace ngd. Daga haka mashkhur ya shiga ya zauna zuciya cike fall da baqin ciki, ga wani abu da ya tsaya mai a qrjin sa yama rasa na menene?.

Mashkhur yana shiga abdul ya rufo murfin motar da qarfi sanan ya kalli zahra wanda ta d'an tafi tinanin abin da tai wa mashkhur. Cikin farin ciki yace baby ki shiga gaban mota ki zauna gwara dai inayi ina kallan ki dan naji dad'in driven, ajiyar zuciya zahra ta sauke sanan ta saki murmushi, ba 6ata lokacin zahra ta bud'e murfin motar gaba ta shige abin ta.

Abdul zagayawa yayi ya zauna a mazaunin gaba sanan ya tayar da motar shi ya fuce daga airport d'in a guje. Suna tafiya abdul ya kalli zahra tare da cewa! Baby kinga yadda kika sake girma kika qara kyai kai tinda kika tafi raban da naga mai kyan ki harna manta wlh. Dariya zahra tai tare da cewa! Kai yaya abdul tayaya zakace raban da kaga mai kyau na har ka manta.

Ehh mana da gaske nake wai mai kuke cine haka naga kun sake girma daga ke har yaya mashkhur. Murmushi zahra tai tare da cewa to so kake nai ta zama a haka kenan bana gaba bana baya koh? Girgiza kai abdul yayi tare da cewa! Aaa kawai girman naki ne naga kamar almara.

Hmmm kai ma ai naga ka sake girma sosai, murmushi abdul yayi tare da cewa! Ah banda zagi kina ganina haka-haka kamar ki turo na fad'i. Kai yaya abdul da kenan ai ni banyi ma tinanin zakayi wata qiba kamar haka ba wlh. Dan harara ta abdul yayi tare da cewa! To gama zagina kinji.

Ah ni awa na zagi yayana maganin kukana ta qarasa maganar tana kashe mai ido. Mashkhur kuwa yana daga baya yana jinsu, ya sake cika fammmmmm kamar ya fashe. Haka dai abdul da zahra sukai ta hira har suka qara so gida mashkhur kuwa yayi shiru dan tinda suka shigo mota har suka qaraso bai ce ko uffan ba.

Abdul yana zuwa get ya fara kwad'a horn zahra kuwa nan da nan bakin ta ya sake washewa yama kasa rufowa tama rasa inda zata sa ranta sabida farin ciki. Mai gadi yana bud'e get abdul ya shige, yana shiga ko parking d'in mota bai ba zahra tace ni dai yaya abdul kawai ka tsaya anan na sauka wlh na qagu na shiga ciki.

Murmushi abdul ya saki tare da cewa! Kai baby kikayi haquri ma har kuka dad'e acan sai yau kuka dawo kawai dan parking ne bazaki jira ba, afa gidan zaki kwana yau. Murmushi zahra tai tare da cewa! Yaya abdul kenan wlh bazaka gane ba yadda na qagu bane, nifa da kai parking d'in nan har gwarama ka qara gaba sosai ka sauke ni dan nayi sauri shiga ciki.

Kai baby tom shikenan yadda kikace haka za'ayi, murmushi zahra ta sauke tare da cewa! Kai nifa ban ma san ta ina zan fara ba ko wajan wa zan fara zuwa wayyo dad'i. Dariya abdul yayi tare da cewa! Ki kwanta da hankalinkia kawai ki tafi babban falon gidan nasan zaki samu kowa da kowa acan sabida yau friday suna can suna hira har dady zaki tarar tinda an sauko daga sallar jumma'a.

Murmushi zahra tai tare da cewa tsaya na sauka anan, dariya abdul yayi tare da cewa! Kai zahra wlh kin rud'a kanki da yawa sosai, ki bari mana nai miki iso. Dariya zahra tai tare da cewa tom shikenan, daga haka abdul yayi parking sanan ya futo, yana fitowa itama zahra ta fito sanan shima mashkhur ya futo fuska nan tasa ba yabo babu fallasa.

Ni kuwa amina bayero nace mai mashkhur yake nufi ne!?. 🤔

Suna gama futowa ko takan trolley d'in su basu biba, suka wuce cikin gidan duka su ukun. Haka zahra tai ta zuci-zuci har suka qaraso qofar babban falon gidan, wanda ya karad'e da hayaniyar mutan gidan. suna karasowa abdul ya juyo ya kalli ta tare da cewa! Bismillah amma ni zan fara shiga sai ki biyo bayana ko na samu tabarakin ku a matsayin ku na baqi gidanan yau.

Murmushi zahra tai tare da cewa! To shikenan yaya abdul, daga haka abdul ya tusa ki baki d'auke da sallama. itama zahra bayansa tabi fuska cike fal da farin ciki, zahra tana shiga shima mashkhur ya biyo bayan ta ya tura kansa cikin falon ya wani rufe fuska da p-cap kamar wani mara gaskiya.

Dady zaune yake akan kujera sai hajiya kaka da take gefan sa, ammi itama tana zaune a kujera daga gefe ita da ameer auta,. Faruq da haidar suna zauna a qasan carpet kusa da juna su, ilham kuwa tana zaune ita da rukee sai ruma da take gefan su, suna zaune suna shan hira abin su gwanin ban sha'awa.
Abdul yana sallama gaba d'ayan su suka d'ago tare da amsa mai sallama.

Ai kuwa yaran gidan basu kai da qarasa amsa mai sallama ba suka saki wani uban iwu tare da tasowa kowa yana 'yar rige-rige tawowa a guje saka makwan hango zahra ta biyo bayan yaya abdul, gaba d'aya d'akin ya karad'e da iwu mai sauti. Ilham ce ta fara qarasowa wajan zahra sanan ta rugumeta, daga ita sai faruq da haidar, suma suna zuwa suka rungeme ta gefe da gefe.

Ilham ta runge zahra ta gaba, haidar ya rungume ta ta gefan hanunta na hagu faruq ya rugumeta ta gefan hanun ta na dama, ruma kuma ta rungumeta ta baya. Gaba d'aya su hud'u sukayiwa zahra runfa, ameer da rukee kuwa an barsu a tsaye, shi ameer bai samu in da zai rumgume zahra ba ita kums rukee dama can basa wani good time da zahra ta rasa taya zata fara hug d'in tama.

Ameer kuwa da yaga yayyan sa sun lulu6e zahra da gudu ya nufi wajan yaya mashkhur da gudo yana cewa oyoyo yaya nah. Ameer yana qarasawa wajan mashkhur, mashkhur ya d'auke shi yayi sama da shi fuska cike da farin ciki yace oyoyo my happiness. Dariya ameer yake sosai da sosai dan jin yaji dad'i sabida ya dad'e bai ga yayan nasa ba.

Bayan mashkhur ya sauke ameer itama rukee qarasawa sai ta rungume yayan nata cikin farin ciki tana cewa! Yaya mashkhur sannu da zuwa. Murmushi mashkhur yayi sanan ya sake ta yana d'an ja mata kumatu ta yace lpy qalau rukkayya. 6angaran dady da ammi kuwa baki kamar zai yage sabida farin ciki.

Hajiya kaka kuwa itama da taga bazata iya haquri ba tasowa tai a hanzarce ta fara cewa! Su ilham su sakar mata zahra ta. Su ilham suna sakin zahra nan ma suka fara 'yar rige regin zuwan wajan yaya mashkhur suka fad'a cikin sa dukka ninsu. Da faruq da haidar harma da ilham da ruma duk suka fad'a jikin yaya mashkhur suna cewa! Oyoyo yaya mashkhur.

Hajiya kaka kuwa tuni ta rungume zahra fuska ciki da farin ciki, itama zahra fad'awa tai jikin ta tana cewa oyoyo kaka ta wlh nayi missing d'in ki, hajiya kuwa sai cewa take oyoyo mai sunana dama da raban zan sake ganinki anya ba mafarki nake ba ALLAH yasa ba mafarkin dana saba bane gaske ne. Dariya zahra tai sanan ta sake lafewa a jikin hajiya kaka tana cewa! Kaka ta ba mafarki kike ba da gaske ne wanan nice zahra ki na dawo wajanki.........................

Mu had'e gobe a next page, yau fa ba double page😂 an dawo gidan jiya wlh. 😂😂😂


ADALILINTA 💜❤💜

AMINA BAYERO 💜❤💜

Typing..........

*page 96*

hajiya kuwa sai cewa take oyoyo mai sunana dama da raban zan sake ganinki anya ba mafarki nake ba ALLAH yasa ba mafarkin dana saba bane gaske ne. Dariya zahra tai sanan ta sake lafewa a jikin hajiya kaka tana cewa! Kaka ta ba mafarki kike ba da gaske ne wanan nice zahra ki na dawo wajanki.........................


Alhamdulilahi ALLAH na gadema yau ka cikamin burina ka dawo min da jikoki na lafiya. Sakin hajiya kaka zahra tai sanan tace gashi nan dai yanzu na dawo bazan sake bari na barki ba ina tare da ke kullum fa sai nayi mafarkin ki, zahra ta qarasa maganar tana kwasa da gudu ta nufi wajan ammi tana qarasawa tai tsalle tare da fad'awa jikin ta, tana cewa oyoyo ammi na.

Cikin farin ciki ammi tace wash zahra so kike ki karyani kalar wanan gudu haka har da tsalle zahra har yanzu baki girma ba ko. Dariya zahra tai sanan ta sake rungume ammi tana cewa! Oyoyo ammi na wlh nayi kewarki ta qarasa maganar tana sake rungume ta. Itama ammi dariya tai tare da sake rungume zahra tana cewa zahra kalar wanan girma haka da kika sake ai ko a hanya muka had'u bazan gane ki ba.

Cikin mamaki zahra ta d'ago tace haba ammi da gaske?, da sauri ammi ta girgiza kai tare da cewa! Aa wasa nake miki nasan yanzu sai ki zauna ki ta kuka. Murmushi zahra ta saki tare da cewa! Tabb ammi kenan da kika sani yanzu ko duka na zaki ai bazanyi kuka ba na girma. Kafin ma ammi tai magana hajiya kaka tace to dama ina zaki kuka kema kin kusan dire d'a.

Nan da nan ido ya dawo kan zahra kowa yana mamaki kuma suna so su gano gaskiyar zancan. Musamman ma abdul wanan sai da gaban sa ya d'an fad'i. Mashkhur kuwa mamakin magar hajiya kaka ce ta rufe shi a zuciyar shi yace mai wanan tsowuwar take nufi ne?. Zahra kuwa bata d'au maganar wani serious ba ta sha wasa hajiya kaka take dan haka miqewa tai tsaye tai sanan tace kai hjy kaka baki da dama wlh, yau she mukayi haka da ke kuma?.

Mashkhur kuwa qarasowa wajan hajiya kaka yayi fuska cike da farin ciki ya d'an durqusa tare da cewa! Hjy kaka ina wuni da fatan mun same ku lafiya. Da sauri hajiya kaka ta girgiza kai tare da cewa! Tashi tashi na rungume ka naji d'imin ka a jiki na mai sunan malam, ciki farin ciki mashkhur ya miqe ya rungume hajiya kaka.

Zahra kuwa tana miqewa bata tsaya ko inaba sai wajan dady tana zuwa ta tsiguna har qasa tare da cewa! Dady ina wuni da fatan mu same ku lpy?. Fuska cike da walwala dady yace ah mamana mene haka yau ni kikewa kalar wanan tarbar ko dai yau surukantakar ce ta motsa. Da sauri zahra ta miqe tare da zama a kusa da dad'i tana cewa! Haba dady wai surukantaka nifa so nake na nunama nayi hankali.


Murmushi dady yayi tare da cewa to ai kuwa bazan yadda kimin wayo ba naqi wayon. Dariya zahra tai tare da d'an kwanciya a kafad'ar dady tana cewa yau gani ga dady abu kamar wasa, murmushi dady yayi tare da sa hannu ya rungume zahra ta gefe yana cewa ai kuwa dai yau gani ga mamana.

Mashkhur kuwa yana sakin hajiya kaka ya qarasa wajan ammi. Yana zuwa ya cire p-cup ya wullata kan kujera tare da tsugunawa har qasa yana cewa! Ammi na ina wuni da fatan mun same ku lafiya?. Murmushi ammi tai tare da cewa lafiya qalau mashkhur ya hanya da fatan kun iso lafiya, cikin farin ciki mashkhur yace ammi lafiya qalau muka iso.

Masha ALLAH haka akeso, daga haka mashkhur ya wuce wajan dady ya tsuguna har qasa tare da cewa dady ina wuni da fatan mun same ku lafiya? Murmushi dady yayi tare da cewa lafiya qalau mai sunan baba, da fatan kun iso lafiya ? Lpy qalau dady muka iso.

Jinjina kai dady yayi tare da cewa masha ALLAH ai da baku dawo ba cikin wanan week d'in da zai kama da ka ganni nazo har na fara shirin dawowa,. Hmm haba dai dady ai na d'auka ma da wasa kake, girgiza kai dady yayi tare da cewa! Da gaske nake mana ko dai ka canza ra'ayi ne yanzu kana son zaman russian.

Girgiza kai mashkhur yayi tare da cewa ina fa dady ai zaman haquri kawai nake. Hmmm zaman haqurin ne yasa kaje ka zauna akai-akai ku dawo kuka ki, gaba d'ayan ku bada son ranku kuka tafiya russian nan ba amma daga qarshe da k'yar kuka dawo nifa ban gane ba wai mai yake faruwa ne?, dady ya qarasa maganar yana kallan zahra da take kafad'ar shi a kwance.

Tashi zahra tai daga kwanciyar da tai a kafad'ar dady sanan tace ah dady kasan mai yasa muka zauna a can kuwa? Da sauri dady ya juya ya kalli zahra tare da cewa aa mamana sai kin fad'a. Bama iya dady ba kusan kowa da yake falon sai da ya bawa zahra attention, mussamman abdul da ammi da rukee sunfi kowa baza kunnuwa.

Dady wlh dama wata ze!!!!!! Da sauri zahra tai shiru da bakin ta tare da d'agowa ta zubawa mashkhur ido sabida yadda zaji ya d'an matse mata babban d'an yatsan ta da hanun sa. Zahra tana kallan mashkhur ya kashe mata ido tare da girgiza kai kad'an alamun karta gayawa dady, wani irin kallo zahra ta watsawa mashkhur, kallan da yake nufin akan me.

Mashkhur da yaga gaba d'aya ido ya dawo kan su miqewa yayi tsaye tare da sake qiftawa zahra ido d'aya. Duk da zahra bata qarasa mad'in maganar da zata fad'a ba tabbas mashkhur yasan labarin zee zata bawa dady, kuma yasan indai zahra ta gayawa dady hmmm xai shiga wata sabuwar matsala. Mashkhur yana miqewa ya nufi kujera kusa da ammi yayi zaman sa.

kowa ya d'an sha jinin jikin sa mussamn ma abdul da dady, shi yasa dady ya canza maganar da cewa! wai mamana mai kike ci haka ne naga kinyi qiba, so kikema ki wuce ilham?. Murmushi zahra tai tare da cewa! Hmmm dady kenan wai na sake qiba kowa fa ya qara girma a gidan nan, kawai dan bakwa ganina shi yasa kuke ganin girmana.

Nan da nan abdul yaji duniyar ta tsaya mai cak yana d'an tsoran kar ace dai zahra da mashkhur sun fara son junan su. 6angare guda kuwa kafin kace mene gaba d'aya waje ya karad'e da hirar yaushe gamo duk cikin su bakaji muryar kowa sai ta zahra da ilham tafi qarfi a wajan. Mashkhur kuwa kallan ammi yayi tare da cewa ammi bari naje na huta na gaji.

Hmm kai dai mashkhur har yanzu kana nan da wanan halin naka na rashin son hayaniya da zama a cikin mutane. Girgiza kai mashkhur yayi tare da cewa kai ammi ba haka bane kawai zanje na huta ne na gaji. Ko ita zahra da take mace bata gaji ba sai wani kai, nasan halinka sarai mashkhur kawai hayaniyar nan ce baka so, amma nan gaba zan gani in ka haifi 'yayan ka ya za kai da su.

Wani sirrin murmushi mashkhur yayi tare da cewa! yara kuma ammi tabbb, ai kima dai na maganar wasu yarana, gwarama kice yaran abdul ko zasu zo nan kusa. Cikin mamaki ammi tace kaii mashkhur, ni da nake sa ran nan da watanni ma, shima mashkhur cikin mamaki yace wattani kuma ammi to ina matar?.

Murmushi ammi tai tare da cewa kai mashkhur bana son fa rainin hankali ko dai yauma miskillanci naka ne ya tashi, kaga gayamin gaskiya daga ni fa sai kai duk ba mai jin mu. Da yake su ammin suna da d'an tazara da inda su zahra suke kuma maganar qasa-qasa suke ba da qarfi ba. Hmmmm ammi dan ALLAH kibar wanan zancan, wai ke ko 'yar kunyar nan ma bakyaji kina zan can jika da d'anki d'an naki ma na fari haba ammi, mashkhur ya qarasa maganar yana d'an had'e rai.

Uhmm mashkhur kenan dama haka ka iya zaro magana to tinda ni bana jin kunya gashi kai ka fanshe ni kana ji kaqi ka gayamin gaskiyar zance. To ni dai ammi kinga tafiya ta zanje bedroom d'in abdul na kwanta, in su faruq da haidar sun gama hirar ki gaya musu nace su gyara min bedroom d'in na. Gyad'a kai ammi tai tare da cewa! Bazaka je wajan momy ba ne?.

Murmushi mashkhur ya saki tare da cewa hmmn har kin tinamin wlh tinda mukazo nigeria nake ta zuci-zuci na ganta, amma yanzu bacci nake ji in na tashi zani wajan ta, nasan ma ku banzo ba ita zata so. Murmushi takaici ammi tai tare da cewa eh dama da yake ana zancan momy har ka saki jiki ka fara magana koh?,

kace mu dole akayi ma ma ka zo wajan mu ai da ga shina kana durowa gidan ka wuce wajan ta, ka fara gaishe da ita tinda kasan itama irin kace bazaka same ta anan ba batason shiga cikin mutane. Cikin mamaki mashkhur yace ammi mai ya kawo zan can nan haba ammi ban sanki da saurin fushi ba. Wata siririyar harara ta watasa mai tare da cewa yanzu ce maka nai fushi nai?.

Girgiza kai mashkhur yayi tare da cewa! To ALLAH ya wuce zuciyar ki ya fad'a jiki a sanyeye. Itama kanta ammi bata son fushi nata ya futo fili ba, abin ne ya d'an sosa mata rai wai ita da d'an ta amma bata ta ita yake ba zuci-zuci yaga kishiyarta yake, kishir tata ma ba mai mutunci ba,, ko ganin girman bata yi. Ajiyar zuciya ammi ta yi tare da qaqalo murmushi dole tana cewa hmm wasa nake ma fa kawai dai na d'an yi fushin ne dan naga haryanzu halinka na cewa ka dai na yana nan ko kuwa.

Ajiyar zuciya mashkhur ya sauke tare da cewa! Hmm yanzu dai kinga babu koh? Zuciya ba dad'i ammi tace eh naga ka dai na ai, yanzu dai tashi kaje ka huta, amma dai ka rage qin son mutane da shiga cikin su sabida mutane rahma ne. Jinjina kai mashkhur yayi tare da cewa! In sha ALLAH, ammi zan gyara.

Daga haka ammi bata sake cewa! Komai ba mashkhur ya miqe ya fuce abinsa.
Mashkhur bai fi 30 minutes da fita ba aka fara kiran sallah qarfe 4 dady miqewa yayi tare da cewa, to kowa ya tashi yayi alwala sanan ayi sallah nima na tafi massalaci. Bayan dady ya tifa shida abdul bayan daday yabi zuciya cike da zullumu. ammi kuwa kallan haidar tai tare da cewa! Haidar kai da faruq in kun dawo daga masallaci kuje ku gyarawa yayan ku room da bedroom d'in shi.

Har suna had'a baki wajan cewa! Tom ammi, daga haka suka fuce . Rukee itama miqewa tai tare da cewa! Tom nima bari naje nayi sallah tana fucewa itama ruma tabi bayan ta sabida tasan bala'in momy ba sauqi yanzu in rukee ta tafi ita bataje ba wata masifar ce. D'aki ya rage daga ammi sai hajiya kaka da kuma su zahra da ilham sai kuma ameer auta.

Ilham tashi ki je ji d'auko mana dadduma da hijabai muyi sallah, dan ni gaskiya bana son hawa saman nan yanzu sai anjima. Ah ammi kawai kice sabida 'yar ki ta dawo ne shi yasa bakyaso ki tafi ki barta karki dawo kika ta bata nan ta gudu russian. Daga ammi har zahra da hajiya kaka dariya suka kwashe da ita.

Ilham baki da dama amma bari ahmad ya zo gidan nan tinda zahra ta dawo zan aika nace dan ALLAH ya taimaka in an turo magatan nan asa sati d'aya sabida yanzu kin addabe a gidan nan ba dama nai magana sai kin fassara wai kin girma koh, ammi ta fad'a tana d'an watsawa Ilham harara. Zahra kuwa cafe zancan tai da wlh kuwa ammi kina aike na sai naje dama muna good time da yaya ahmad wlh tuni zai yadda.

Ilham kuwa cewa tai ehh to ki je ki fad'a mana wlh ai ni ammi da zahra tai makona kukayi dan wlh nama gaji da zaman gidan nan so nake ayi-ayi a miqani d'akin miji na ta qarasa maganar tana wucewa sama gudu-gudu sauri-sauri, tana dariya. Cikin mamaki ammi tace kai hajiya wlh yanzu ilham batajin kunya ta kamar fa bani na haife taba har k'wara dadyn su tafi jin kunyar sa, yanzu kinaji abinda ta gaya min fa.

Murmushi hajiya kaka tare da cewa ee mana ai gwara ta nuna muku tana so, da tuni bazaku aurar da ita ba inma badda zamanin yanzu ai kamar su ilham ada suna da yaya uku zuwa hud'u. Zahra kuwa bata san sanda dariyar da take toshewa ta futo ba, tai sauri ta sunkuyar da kai qasa tana toshe baki. Hmmm hajiya kinga ni ko itama kanta zahra da take da aure kunya take ji bare ita da ko sa rana ma ba'a yi ba.

Wlh ammi abin ne ya bani dariya wayaga ilham da yara har uku tab wayaga mama ilham kenan, zahra ta qarasa maganar tana sakin dariya. Yo kema dai zahra gane min hanya rikicin tsofa ne kawai irin na hajiya kaka ammi ta fad'a tana gyara zama. Ba wani rikicin tsufa ke yanzu mai sunana ba gashi na taimake kiba nasa anyi miki auran wuri gashi yanzu har kin samu qaruwa, kin kusan dire me miki addu'a.

Ah wayyo dad'i shikenan na kusa nayi d'a ALLAH na godema ilham da ta qaraso maganar tana ajiye hijaba da daddumar da ta d'ebo akan kujera. Zahra kuwa cikin mamaki tace wai hajiya kaka waye yace miki ina da wani ciki, ammi kina ji dai ko?. Murmushi ammi tai tare da cewa hmm ni dai kinga tashi bari naje nayi alwala bayan munyi sallah na raba muku fad'an......................

ADALILINTA 💜❤💜

AMINA BAYERO 💜❤💜

Double page............

Itama zahra miqewa tai tare da cewa! Nima bari nayi sallah ko ta azahar ma banyi ba, ilham taso muje muyi alwala. Girgiza kai ilham tai tare da cewa! Sai dai na rakaki kiyi ni yau bana sallah, mai kuka dafa yau zahra ta qarasa maganar tana cire hijab d'in ta. Miqewa ilham tai tare da cewa! Pride rice muka dafa,.

Kai gaskiya bazan iya ci ba, wani kallan tuwuma ilham, ta watasawa zahra tare da cewa to duk sanki da pride rice d'in. Hajiya kaka kuwa miqewa tai tare da cewa! Ai kad'an daga cikin sharrin juna biyi kenan, kai yau na shiga uku a cikin gidan nan haba hajiya kaka nifa bani da wani ciki wlh. Oh kyaji da shi ni dai bari naje nai alwala.

Please Login or Register in order to submit comment