Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce miki take care ko?  To badaban halinki ba take care, gwalo ilham tai mai  tare da cewa!  Yee kadai yi sai na dawo. Daga haka suka fuce daga gidan.

Suna fita shima ahmad ya futo a tsai-tsaye suka gaisa da yake sun kusan makara,  sanan suka shige cikin mota ahmad yaja suka fuce daga gidan,  tunda suka fito har suka isa school d'in su zahra ba wanda yace koma!  Suna isa zahra tace ku gaida gida yaya ahmad sai anjima,  qaqalo murmushin dole ahmad yayi tare da cewa!  Ok qanwata ayi karatu da kyau sai anjima,  in sha ALLAH yaya ahmad daga haka  zahra tai fucewar ta school. Tana fita yau ahmad bai takurawa ilham akan sai ta  dawo gaba ba haka yaja motar shi suka fara tafiya.

Abin mamaki shiru-shiru ahmad bai cewa ilham komai ba ita ilham bata ce masa ba.  Ahmad yana so ya tambayi ilham akan mai ta yanke game da soyayyar da yake mata,  amma yana tsoran karta gaya mai abinda bazai iya qarasa kai su gida ba,  shiyasa ma bai tambaye ta ba abinda ta yanke ba,  kawai ahmad yana daurewa yake tuqine amma hankalinsa ba ajikinsa yake ba.  Sabida gudun da ahmad yake har sun qaraso gida,  suna karasowa gida yayi parking d'in motar shi,  shiru yayi yana tinani taya zai fara tambayar ilham.

Yana juyawa yaga ilham ta mugun had'e rai dama tun sanda ya suka futo daga gida yaga ilham tana had'e mai rai, shiyasa ma hankalinsa ya tashi,  tun kafin ilham ta gayawa ahmad amsar shi,  ahmad yasan mai zata gaya mai abinda yanayin fuskar ta.  Sosai ahmad ya jiyo ya zubawa ilham ido,  sanan yace mata!  Ilham ni muslmi ne kuma zan kasance mai d'aukar qaddara mai kyau ko mara kyau kamar yadda addinin muslinci yace muyi,  pls ilham ki gayamin abinda kika yanke game da soyayyar da nake miki,  kin amince ko kuwa ya qarasa maganar yana runtse idanuwa. Jim ilham tai batace komai ba,  tanaso ta miqa mai takaddar amma tana jin muguwar kunya,  muryar ahmad ilham taji yana cewa ilham pls ki gayamin abinda yake zuciyar ki?.  Da kyar Ilham ta iya d'aga hanunta,  ta miqawa ahmad takaddar hannu na rawa tace!  Gashi nan yaya ahmad amsar ka tana ciki,  rai  ta had'e sosai sanan tace sai anjima ta bud'e murfin motar tai ficewar ta,.  Wata nanauyar ajiyar zuciya ahmad ya sauke ko bai bud'e ba fuskar ilham ta gama nuna mai amsar shi, har zuciyar ahmad ya bayar ilham bata amince ba,  haka nan yaji ya kasa bud'e takardar jiki ba kwari ya bud'e murfin motar ko zare key d'in bai tsaya yiba ba ya wuce part d'in shi.

Yana shiga bedroom ya wuce,  direct toilet ya nufa ya d'oro alwala bayan ya futo,  daga toilet d'ib dadduma ya shinfid'a ya fara gabatar da sallah.  Raka'a biyu yayi a sujjadar qarshe sai daddu'a yake ALLAH yasa yaga alkhairi a cikin takaddar duk da kuwa ahmad baya tsammanin sai ga alkhairin,  daran jiya ma kwana yayi yana sallah yana rokwan ALLAH akan,  Allah yasa ilham ta amince da soyayyar sa,.  Bayan ahmad ya idar da sallar addu'o'i ya qarayi sanan yayi wa annabi salati goma,  bayan ya idar hannu na rawa ya d'auko takaddar a aljiwunsa ya fara bud'ewa,  yana gama bud'ewa ya rintse ido da qarfi gam ya rufe idonsa sabida yana tsoran mai zai tarar a takaddar.

Ahmad yafi minti koma a haka can kuma ya sawa zuciyar shi jarumta yayi ta maza ya bud'e takaddar,  cikin tashin hankali Ahmad ya fara karanta takaddar kamar haka!  Yaya Ahmad tabbas ka cika namiji mai kirki ga ilimi da saninya kamata,  kuma duk duniya in mutum yace yana son ka ya gama yi ma komai,  dan haka nima yaya ahmad ina mai farin cikin sanar da kai na AMINCE da SOYAYYAR ka kuma ina SON KA ina QAUNAR KA nima.  Ahmad yana kai nan ya saki wata qarar farin ciki tare da sakin takaddar qasa yana furta ALHAMDULILAH ALLAH  nagode ma ALLAH nagode ma ALLAH nagode ma.................

Mu had'e a next page.


ADALILINTA💜❤💜  

BY AMINA BAYERO💜❤💜

                                    Typing............

                                 *page 73*

Ahmad yafi minti koma a haka can kuma ya sawa zuciyar shi jarumta yayi ta maza ya bud'e takaddar,  cikin tashin hankali Ahmad ya fara karanta takaddar kamar haka!  Yaya Ahmad tabbas ka cika namiji mai kirki ga ilimi da sanin ya kamata,  kuma duk duniya in mutum yace yana son ka ya gama yi ma komai,  dan haka nima yaya ahmad ina mai farin cikin sanar da kai  na AMINCE da SOYAYYAR  ka kuma ina  SON KA ina QAUNAR KA nima.  Ahmad yana kai nan ya saki wata qarar farin ciki tare da sakin  takaddar qasa  yana furta ALHAMDULILAH ALLAH  nagode ma ALLAH nagode ma ALLAH nagode ma................. 

Nan da nan ahmad yaji jikinsa yayi mai kwari ada yau gani yake kamar bazai iya zuwa school ba,  amma da ya karanta takaddar ilham sai yaji jikinsa yayi mai mugun kwari,  da sauri ya miqe ya fara neman key d'in motar shi,  sai da ahmad yayi wajan minti ashirin,  yana nema key d'in motar shi sanan ya tina ashe bai d'auko key d'in ba.  Murmushi kawai ahmad ya saki sanan ya wuce yabar part d'in nashi gaba d'aya,  yana fita ya shige mota zuciya cike da farin ciki. 
6angar ilham kuwa farin ciki ba kama hanun yaro,  ranar ma ko abinci kirki bataci ba.

Washe gari.......

Bayan ahmad da ilham sun sauke zahra a school zama sukayi a cikin mota suka sha soyayya,  tsayawama gayawa masu karatun ADALILINTA irin soyayyar da ahmad da zahra suka sha 6ata lokaci ne dan har sai na gama page uku ban gaya muku ba,  sun d'au wajan awannin suna hirar soyayya,  dan har aka futo da su zahra break suna nan suna hira,  da dady ne ya bigowa ahmad da sauri ahmad ya kalli  ilham yace innalilahi kinga dady ne yake kirana mai zan cema?  Jim ilham tai tana nazari har wayar ta tsinke can kuma tace mai kawai kace ka barni makarantar su zahra sai an tashi zaka d'auko mu tare. 

ai kuwa haka akayi dady yana sake bigowa ahmad ya sanar da shi abinda ilham tace,  dady kuwa cewa! Yayi tom shikenan ba damuwa.  Daga haka ahmad da zahra suka cigaba da shan soyayyar su,  ahmad kuwa sam ya manta ma da wasa lectures shida tinda yazo rasha bai ta6a fashima sai yau.  A taqai ce dai ranar sai da aka taso su zahra sanan suka tafi gida,  lokacin da zahra ta ahigo motar tayi tinanin ma dawowa sukayi d'aukar ta,  dan haka bata kawo komai a ranta ba tace to yaya ahmad ya kazo da wuri tun yaushe kazo.  Maimakwan ahmad ya bawa zahra amsa sai ya kalli ilham da take gaba mota suka sa dariya.

Zahra kuwa sakin baki tai tana kallon ikwan ALLAH,  daga haka ahmad yaja motar shi suka fara tafiya,  suna tafiya suna hirar soyayya su,  dan gaba d'aya sun manta da wata zahra a bayan mota,  zahra kuwa mamaki ne ya kusan kashe ta a zuciyar ta cewa!  Tab dama yaya ahmad  ya iya soyayya lalai,  dan batayi mamakin ilham bama tasan zata iya abinda yafi haka. Kai ranar zahra taga ikwan ALLAH,  sabida dad'in soyayya ahmad har sai da ya wuce get d'in gida,  cikin mamaki zahra tace yaya ahmad naga ka wuce get d'in gidan ina zamu kuma.

Da sauri  ahmad yaja birki tare da cewa!  Au ai ni namanta ma qanwata kina nan,  wlh ban kula ba.  Ya qarasa maganar yana sakarwa ilham murmushin qauna,  itama Ilham d'in mayar masa tai tare da cewa! Hmm nima ai ban kula munzo ba dana tina mai.  Nan take mamaki ya kashe zahra a zaune,  har wani cizar le6e take sabid taga abin yana qoqarin fin qarfin kanta. Rubos ahmad yayi sanan suka shiga get d'in,  zahra tana qoqarin sauka taji ilham tace dan ALLAH zahra ki jirani a waje ina zuwa.

ALLAH sarki zahra baiwar ALLAH murya a sanyaye tace to sai kin futo,  daga haka zahra ta sa6i jakarta ta fuce,  ta tsaya a bakin mota tana jiran ilham.  Kallan ahmad ilham tai tare da cewa! My hubby yanzu ya zamuyi kasan fa gobe zamu koma Nigeria jirgin safiya zamubi.  Zabura ahmad yayi tare da zaro ida yana dafe qirjin haba ilham gobe zaki koma amma baki gaya min ba.  Dan hararar qauna ilham tai mai tare da cewa! Au ka manta shekaran jiya ne ko jiya bana gaya ma mun kusan komawa ba?.  Rai ba dad'i ahmad yace ehh hakane na tina,  yanzu shikenan ko waya bazamu d'inga yi ba.

Cikin farin ciki Ilham tace sosai ma zamuyi,  da sauri ahmad ya kalle ta tare da cewa! Tayaya?  Murmushi ilham tai tare da zira annunta a lanjiwo ta zaro sabuwar wayar da dady ya siya mata tare da cewa! Ta wanan mana,  da sauri ahmad yasa hannu ya kar6i wayar tare da cewa! Taki ce,  gyad'a kai ilham tai tare da cewa! Ehh tawace,  jiya dady ya siya mana nida zahra da sauran 'yan uwana amma baka san suba.  Ehh ba lalai ne na sansu ba amma dai kamar nasan wasu baza biyu,  kamar 'yan biyu, suna kama da abdul sosai ko su kike nufi?.

Girgiza kai ilham tai tare da cewa! Basuwa wanan ya faruq da ya haidar ne kuma su suna da wayar su,  sufa wanda nake nufi mata ne, aunty rukayya da ruma.  Murmushi ahmad yayi tare da cewa au ita ruma rai nata kikayi kenan da bazaki ce mata aunty ba?  Wata siririyar dariya tai tare da cewa! Ai qanwata ce na bata wajan wata hud'u zuwa biyar taya ma zance mata wata aunty,  ahmad yana jin hakan yasan ba uwarsu d'aya da ruman ba mamaki ne ya kamashi dama dady matansa biyu.  A fili kuma cewa!  Yayi au kenan ba mamanku d'aya ba koh?.

Gyad'a kai tayi tare da cewa! Ehh dukkansu ba maman mu d'aya da suba,  mamansu d'aya da yaya abdul, jinjina kai yayi tare da cewa! Amma dai ke daga ganinki qanwar mashkhur ce,  sabida kamar da kukeyi ya qarasa maganar yana murmushi,  da sauri ilham ta d'an zari ido tare da cewa! Ah ni dai gaskiya bana kama da shi,  shifa namiji ne ni kuma mace,  sosai ilham ta bawa ahmad dariya,  cikin dariya yace kai ai mace tana iya kama da namiji sosai ma,  murmushi ilham tai har cikin ranta taji dad'in da yace mata tana kama da yaya mashkhur,  komin banza tasan yaya mashkhur kyakyawa ne.

Kallan ahmad ilham tai tare da cewa! Yanzu sai ka samun number taka,  in muka koma Nigeria zance ayimin layi sai na kiraka,  jinjina kai ahmad sanan ya fara rubutawa Ilham number,  yana gamawa yayi mata save da my husband to be in sha ALLAH.  Sanan ya miqa mata yace duba kigani sunan yayi,  da sauri ilham ta kar6a,  da sauri ilham ta zaro ido tare da dafe qirji tace what?  Wani kallo ahmad ya watsa mata tare da cewa! To ba gaskiya na fad'a ba?  Ajiyar zuciyar ilham tare da cewa! Hakane amma ka tabbata in ammi ta gani tofa na kade gaba d'aya.

Murmushi ahmad yayi tare da cewa! In sha ALLAH ma bazata gani ba,  murya a sanyaye Ilham tace tom ALLAH yasa,  bari na tafi koh?  Kamar ahmad zai yi kuka yace bazaki qara ko minti 5 ba?  Girgiza kai ilham tai tare da cewa! Aa kar dady ko yaya mashkhur ya ganni,  murya asanyaye ahmad yace to,  nasan dai daga haka bazamu qara magana ba sai kin koma Nigeria,  pls ilham kina komawa Nigeria ana yi miki sim d'in dan ALLAH ki kirani,  karkiqi kirana ilham.  Jiki a sanyaye Ilham tace in sha ALLAH hubby zan kiraka,  ana fara yimin sim d'in kai zan fara kira.

Shima ahmad murya a sanyaye yace!  Bama lalai sai kin kirani ba kinsa kira zai ci miki kati sosai ko ta WhatsApp ne kiyimim magana ni sai na ringa kiran ki ko?.  Gyad'a kai tayi tare da cewa! By my hubby take care,  murmushi dole ahmad ya kwakwalo tare da cewa! Take care too my wife to be in sha ALLAH,  murmushi ilham tai tare da sa hannu biyi ta rufe fuskar alamun kunya.  Shima ahmad d'in kwaikwaiyar yadda tai yayi yasa hannu ya rufe fuskar shi,  tana sauke hannu shima ya sauke,  baki suka had'a suka sanya dariya mai ciki da nunawa junan su tsantsar QAUNA.

Daga haka Ilham hannu tasa ta bud'e murfin motar ta fuce da sauri,  tana fita ta rufo qofar tare da kallan zahra da take shanye ajikin mota tana jiran su,  wata uwar harara zahra ta sakarwa ilham, nan ta wuce abinda,  da sauri ilham tabi bayan ta tare da cewa!  Ya haquri,  cikin fushi zahra tace bazan haquran ba,  da yake bakisan ya kamata kin wani shayyani,  gashi na gaji daga makarantar fa na dawo.  Murmushi ilham tai tare da cewa! Hmm zahra kenan zan miki uziri sabida bakya soyayya,  wani siririn tsaki zahra taja sanan ta fara hawa kan step d'in benan.

Da sauri ilham ta ruqota tare da cewa!  Au zahra na manta ban sanar da ke ba,  kinsan mene?  Tsayawa zahra tai tana kallan Ilham d'in,  tace mene?  Am in dama yaya ahmad muncewa dady muna tare da ke ya baroni a makarantar wajan ki,  tom karki sakin layi fah.  Zaro ido zahra tai tare da cewa! Kai amma ilham baki da hankali ina kukaje haka bai dawo da ke gida ba?,  dan sosa kai ilham tai tare da cewa! Bafa inda mukaje zama mukayi a makarantar ku mukayi hira da shi,  shiru zahra tai dan mamaki ne ya kusan daskarar da ita,  dan yanzu al'amarin ilham da yaya ahmad ya fara bawa zahra tsoro.

Jiki a mace zahra taja qafafuwon tacigaba da  tafiya tana cewa!  To ALLAH ya kyauta,  murmushi ilham tai tare da cewa! amen my zahra,  Allah ya barmin ke,  qara had'e rai zahra tai,  da sauri ilham ta riqe hanun zahra tare da cewa! Wlh zahra muna haifar 'yar mu ta fari nida yaya ahmad in dai maca ce sunanki zan sa mata.  Zahra batasan sanda wata dariya ta kwace mata ba,  had'e rai ilham tai tare da cewa! Ke me kikewa dariya ko gani kike auran bazai yiwu ba,  zaro ido zahra tai tare da cewa! Wa ni na isa nace aure bazau yiwuba?  Kawai dai naga kin cika zumud'i ne,  shi yace miki zakuyi aure? .

Da sauri  ilham ta jawo zahra da take qoqarin bud'e qofar ta shiga,  juyowa zahra tai tare da cewa! Ke mene haka?  Murmushi ilham tai ta bud'e wayarta tare da miqawa zahra tace duba kiga da kansa yayi save d'in sunan.  Da sauri  zahra ta kar6a ta zubawa wayar ido,  a fili ta fara karanta save d'in number,  cikin zazzaqar murya zahra tace my husband to be in sha ALLAH,  zahra tana kai nan ta saki wani qasai taccan murmushi tace kai,  Masha ALLAH  da hanunsa ya rubuta wanan d'in,  gyad'a kai ilham tai alamun ee,  jinjina kai zahra tai tare da cewa! Ai ni sai nafi kowa farin ciki da had'in nan wlh sabida yaya ahmad mutumin kirkine,  ALLAH ya tabbatar da alkhairi.

wata irin mugun hugg Ilham ta kai wa zahra wanda hakan sai da yakusan sawa wayar ilham,  d'in da take hannun zahra ta kusan fad'uwa,  da sauri zahra ta riqe wayar hanun ta da kyau,  ilham kuwa tana rungume zahra tace kai gaskiya zahra ina qaunar sosai,  ALLAH ya barmu tare,   murmushi zahra tai tare da cewa! Amen ilham sake ni mu shiga ciki,  ba musu Ilham ta saki zahra suka shige cikin. suna shiga ciki ba su wuce ko ina ba sai kicin saka makwan qamshi da sukeji yana tashi.

Abdul suka gani tsaye da cokali juya miya a hannu,  murmushi zahra tai tare da cewa!  Wow gaskiya yaya abdul  ka cika gidan nan da qamshi, daga ji girkin nan zai yi dad'in sosai,  murmushi shima abdul d'in yayi tare da cewa! Hmm tinda ilham yau ta gudo sabida kar tai mana girki muce shiyasa nima yau nace bari na nuna mata na fita iyawa,  aa yaya abdul nifa ba guduwa nayi ba,  hararar wasa ya watsa mata tare da cewa! Ai gwarama da baki dawo ba da tini kinyi mana kwa6a,  murmushi ilham tai tare da cewa!  Shiya jiya naga kaci ka lashe kwano,  dariya abdul yayi tare da cewa! Wa ni ai tab gaskiya idanki baya gani yaya mashkhur ne fa yaci ya lashe kwanan.

Dariya zahra tai tare da cewa! Ilham zo muje muyi wanka,  nasan ka fin mu futo yaya abdul ya gama dafawa,  sai naci na raba muku musunnan naku,  amma dai tun kafin naci nasan na yaya abdul sai yafi dad'i,  ta qarasa maganar tare da fucewa daga kicin d'in.  Ilham kuwa binta tai tana cewa!  Ai dama dole kice na yaya abdul zai fi dad'i sabida kowa yasan ke ta gidan shi ce ni kuma da yake kin rai nani koh?.  Suna shiga bedroom zahra ta wuce toilet domin yin wanka itama ilham d'in toilet d'in,  ta wuce dan itama tai wanka,  dan bazata iya jira zahra ta futoba.

Bayan sun futo shiryawa sukayi,  sanan suka fita fallo sukaci abinci,  bayan sun gama cin abinci kumawa d'aki sukayi.  Suna komawa zahra tace ilham zokimin kitso tinda gobe zaku tafi!  Zama ilham tai akan bed tare da cewa!  Tom d'auko kibiya da kum,  ba musu zahra ta wuce wajan dorowa ta bud'e ta dakko kum da kibiya sanan ta koma wajan da ilham take ta miqa mata sanan ta zauna a qasa, cire d'aukwalilin kanta tai,  sanan tace ciremin ribbon d'in na ya kamanin kai sosai,  hannu Ilham tasa ta fara cire ribbon d'in tare da cewa!  Ke zahra me yasa kika d'aure kanki haka.

Bafa ni na d'aure ba yaya abdul ne,  da kyar Ilham ta iya cire ribbon d'in tana cirewa gashin zahra ya bazo har gadan baya dan harma fuskarta ya fara hauro mata.  Yauwa ilham 'yan qananu zakiyi min sabida kar ya tsufa da wuri,  tabb zahra gashi nan naki ga yawa ga santsi ga tsayi ai sai mukai magariba ba'a gama ba, kai ilham bansan sharri duk gashin nawa kikewa sharri haka, ai kema naki yana da stayi kuma yana da yawa koh?  Kwarai amma ai bai kai naki stantsi ba,  kefa ana kamawa yana qoqarin warwarewa in da gama ba sai na sa kyauro na dad'aure jelar gashin sabida kar ya ware da wuri.

Murgud'a baki zahra tai kamar Ilham,  tana ganinta tace!  Tubarakalla masha ALLAH,  murmushi ilham tare da cewa!  Hmm nifa yanzu na dena wanan fad'a fad'an bari na baki labarin soyayyar da mukasha da yaya abdul, murmushi itama zahra tai tare da cewa!  Tom inaji gayamin mana.  Nan da nan ilham ta fara bawa zahra labarin abinda ya faru,  wasuma ta manta sai daga baya take tunowa a taqaice dai sai da ilham ta bawa zahra labarin abinda ya faru tsakaninta da yaya ahmad,  tun zahra tana ganewa har ta fara dena ganewa sai da ta bita da um da ehh,  wajan awa biyu suka dauka kafin su gama kitson har ilham ta gama kitso bata gama bawa zahra labarin ba.

Tofah su dady da yaya abdul harma da ilham,  sun gama shirya-shiyan tafiya,, zuwa gobe da safe jirginsu zai d'aga,  dady ya siyarwa zahra komai da komai 6an garan kayan abinci,  abubuwan amfanin gida,  kayan sawa sabulan wanka dana wanki maya-maya kai komai dai da ya kamata an siyarwa zahra.
      Daran ranar kuwa Ilham kusan kwana tayi tana kuka wai zata rabu da yaya ahmad,  sosai zahra ta d'in ga rarrashin Ilham,  amma fir ilham taqi haqura daga qarshema zahra rabuwa tai da ilham tai kwanciyar ta,  ita kuma Ilham sai da tasha kukanta ta qoshi sanan ta kwanta da mugun ciwan kai.

Washe gari..............

Tofah tunda asubayi su dady suka fara shirya-shiyan tafiya gida Nigeria,  zahra kuwa sam bata cikin walwala da kyaf take iya yin komai,  duk jikinta yabi yayi sanyi sam batasan tafiyar su dady amma ba yadda zatayi.  Su zahra suna gama abinci suka zauna suna ci,  amma zahra da Ilham da abdul kowa ya kasa cin abinci,  ita zahra tana jimamin rabuwa da su dady,  ilham tana jimamin rabuwa da yaya ahmad shi kuma abdul yana jimamin rabuwa da zahra. Haka dai suka ci abinci a daddafe sanan suka fara shirin tafiya airport.

Komai ya kammala,  duk sun zuba kayan su a motar mashkhur,  lokacin da ilham taji yaya ahmad zai musu rakiya tayi farin cikin hakan sosai dan haka suna fita,  taja hannun ameer da zahra suka wuce motar yaya ahmad.  Ilham taso ta shiga gaba amma tana tsoran kar yaya mashkhur ko dady su gano wani abun shi yasa ta shiga baya,  itama zahra baya ta shiga hannunta riqe dana ameer.  Motar mashkhur kuwa dady ne ya zauna a baya shi kuma yaya abdul ya zauna a gaba,  sanan suka ta da motar suka fuce daga gidanan.


Sosai ilham ta fara lala6a amir dan yayi bacci,  sabida suyi magana da ahmad,  tasan amir da shegen suruto yanzu in yaji sunyi mana sai ya gayawa ammi ko dady,  ahmad kuwa magana yayiwa ilham,  amma sam taqi amsawa sai da suka had'a ido ta mudubi sai tayi mai alamu da yayi shiru ta nuna mai amir,  ahmad kuwa ya gane abinda ilham take nufi dan haka shiru yayi da bakin sa. Dama amir bashi da wuyar bacci,.  Yana yin bacci ilham ta saki ajiyar zuciya tare da cewa!  Yauwa hubby yayi bacci fah, murmushi ahmad yayi tare da cewa! Alhamdulilah.

Nan da nan ilham da yaya ahmad suka 6arke da hirar su ta masoya,  abinda gwanin sha'awa har sha'awa suke bawa zahra da take gefe abinta.  Haka sukayi ta hira har sai da suka qaraso airport,  haka zahra da ahmad sukai sallama kamar zasuyi kuka,  6angaran zahra da ilham kuwa,  rungume junansu sukayi suka fara kuka,  ba wanda yayi mamaki hakan sabida kowa yasan sai sun aikata hakan in ka cire ahmad,  da kyar dady da yaya abdul suka rarashin su,  sanan suka saki juna,  zahra tanaji tana gani su ilham da dady harma da yaya abdul da amir suka shige jirgi,  ba jimawa,  jirgin nasu ya tashi.

Jiki ba kwari zahra ta wuce motar ahmad ta shige,  ta saki wani saban kukan,  shima haka ahmad ya shiga jiki ba kwari,  sabida kewar ilham da zai yi,  yana so ya bawa zahra haquri amma ya kasa,  sabida shima kansa a halin da yake ciki neman rarrashin  yake. Mashkhur kuwa girkin su dady yana tashi ya sharari motar shi yabar airport d'in ko takan zahra da ahmad bai biba.  Ahmad kuwa da kyar ya iya jan mota ya fara tafiya,  a lokacin da ya futo daga airport d'in ko hayaqin motar mashkhur bai gani ba.........

*shinya kuna ganin zahra zata iya  bin shawarar da ilham,  ta bata akan mashkhur da zee?.

*shin ya kuke tinanin zama mashkhur da zahra zai kasance?

* Kuna tinanin zahra zata fita daga qonci da take ciki ta fara zaman yan ci ko zata cigaba da zama cikin baqin ciki?

Ku biyoni a next page dan jin yazata kaya,  jumma'atul kareem da fatan za  kuyi hutun  weekend cikin qoshin lfy.


ADALILINTA💜❤💜

BY AMINA BAYERO💜❤💜

Typing........

*page 74*

Mashkhur kuwa jirgin su dady yana tashi ya sharari motar shi yabar airport d'in ko takan zahra da Ahmad bai biba ahmad kuwa da kyar ya iya jan motar ya fara tafiya, a lokacin da ya fito daga airport d'in ko hayaqin motar mashkhur bai gani ba.........

Haka Ahmad yaja motar shi jiki ba kwari har suka qarasa gida. Suna shiga cikin get d'in gidan sukaga motar mashkhur alamun ya dawo gidan, jiki ba kwari zahra ta bud'e murfin motar tai fucewarta ko sallama bata tsaya yi da yaya ahmad d'in ba. Shima Ahmad

Please Login or Register in order to submit comment