Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta. Ammi ce ta fara rarrashin su cikin tausayawa dan itama zuciyarta ta karye bama ita kad'ai ba har zahra da ilham da suke zaune a wajan. Bayan ruma ta saki momy, ammi ce ta kalli su ilham cikin had'e fuska tace ke ilham da zahra baku iya gaisuwa bane kun zauna kamar an sassaqa ku.

Ilham ce tace momy ina wuni sannu da zuwa, itama zahra baki na rawa tace momy ina kwana sabida tsabar rud'ewa ma bata son tace ina kwana ba maimakwan tace ina wuni. Momy fuska a sake tace lafiya qalau zahra da ilham fatan na same ku lafiya. Daga haka momy ta samu waje ta zauna a gefe. ammi kuwa tasa ruma ta d'aukow momy yarinyar domin ta ganta.

Lokacin da za'ai bikin abdul har kaduna na aika a kai miki invitation amma wai akace ba kowa a gida. Au anyi bikin abdul kenan masha Allah, wlh da yake munyi aure ni da saratu to amma ni yanzu aure na ya mutu, kuma mahaifiyar mu ta rasu saka makwan hatsarin mota shi kuma mahaifin mu bayan sadakar uku zuciyar shi ta buga ya rasu shima.

Sabida baqin ciki ga talauci ga kuma gashi jna zama ba aure, bugu da qari ga halin da saratu take ciki a gidan mijin ta. Bayan anyi arb'i d'in iyayan namu shine gidan haya suka zo suka kore ni, to da kyar na samu yanzu nake zama a gidan kawuna shima de zaman ba dad'i kullum cikin 6acin rai da haquri nake. Jiya bayan saratu ta had'u da qawarta.

Maqociyarta ta gidan tsowan mijinta, shine take gaya mata maman zahra ta gaya mata ruma da ilham sun haiwuwa. Bayan saratu ta gayamin hakan ne yasa na samu kud'in mota dance da kyar na tawo duk da nasan ba lallai a barni na shigo ba. Momy ta qarasa maganar hawaye suna zubo mata. Ah haba halima za'a barki ki shigo mana ki dena kuka komai yayi zafi maganin sa Allah.

Share hawayanta momy tai sanan tace gaskiya ne maryam, ashe abdul shima yayi aure, auran ruma ba ban san anyi ba sai haiwuwa naji. burina kullum abdul ya yafe mu ya cigaba da duba ta a matsayin uwa amma nasan hakan ba zai samu ba dan ko a hanya ya ganni ba lallai ya kalle ni ba. Aa in sha ALLAH komai zai zo qarshe ki kwantar da hankalin ki ai auran abdul ko sati biyu be yiba..

'Yar saratun ya aura nana, qanwar zahra, itama kuma ruma doctor habib ta aura bayan rukayya ta rasu sai dadyn su ya mayar da baikwan kanta. Momy taji dad'i hakan dan tasan doctor habib mutumin kirkine, kuma yana da rufin asiri sosai, 'yar ta ruma baza ta sha wahala ba.

Ammi cewa tai amma kar ki damu kafin ki tafi sai a kai ki gidan abdul ki gani. Cikin tsoro momy tace aa maryam ni de nan d'in ma ya isa na godewa Allah daya sa na shigo banyi tinanin ma za'a barni na shogo ba. Ah kar ki damu halima in sha ALLAH ba abinda zai faru cewa ammi.

Tom allah yasa momy ta fad'a zuciya ba dad'i. Bayan momy ta d'auki jikan ta d'an ilham ta d'auka shima tai mai addu'a kamar yarda tai wa jikarta ta. Daga haka abdul da yake kan cinyar zahra ya farka daga bacci ya fara kuka, sai a lokacin momy ta lura da yaron dake hanun zahra sabida ita gaba d'aya a tsorace ta shigo. Ah zahra kice kema kin haiwu kenan.

Qaqalo murmushi dole zahra tai, ammi ce ta iya cewa ee ai ta riga su haiwuwa dan yanzu harma anyi wata hud'u zahra kawo mata shi ta gani. Gaban zahra ya fad'i rass da jin maganar ammi amma dole ta miqe da kyar ta qarasa wajan momy ta miqa mata abdul sanan ta dawo in da ta tashi ta zauna jikin ta a sanyaye sabida ita gani take kamar momy zata iya cutar musu da yaro.

Ya sunan shi? momy ta fad'a tana kallon yaron, suna abdul ne da shi ammi ta fad'a a taqaice. Ah masha allah, ga shi kuwa suna kama da baban sa ALLAH uaban giji ya raya. Amen ammi ta fad'a fuska a sake.
Zahra adede lokacin taji alamun shigowar message wayarta. Da sauri ta bud'e dan tana tunani mashkhur ne. Kamar yarda zahra tai tunani mashkhur ne ya turo mata message da! Na qaraso ki fara shiryawa.

Gaban zahra sake fad'uwa yayi rass, amma sai ta turawa mashkhur reply da tom. Har wajan 10 minutes momy bata bawa zahra abdul ba yana hanunta, zahra tana son qar6ar yaron amma tana jin kunya da nauyin haka dan haka dole sai shiru ta zauna. Ba a wani d'auki lokacin ba mashkhur ya murd'a handel d'in qofar baki d'auke da sallama ya shigo.

Bayan ya shigo ya gai da ammi, shi sam bai ma kula da momy ba ya qarasa bakin bed ya zauna. Mashkhur baka ga baquwa bane cewar ammi. Mashkhur ko kallan matar bai ba cikin musukilanci yace ina wuni a taqaice. Lafiya qalau mashkhur ashe an samu qaruwa to Allah ya raya.

Gaban mashkhur ne ya fad'i rass jin murya mai maganar, mashkhur ko zai manta kamar momy ba zai iya manta muryar ba da sauri mashkhur ya d'agowa ganin da gaske itace ko gizau murya take mai.

Ai a hanzarce mashkhur ya miqe tsaye kamar an tsikare shi, ganin tabbas momy ce kuma abin mamaki ga abdul a hanun ta sai lumshe ido yake. Da saurin gaske mashkhur ya qarasa in da momy take zaune, ba 6ata lokaci yasa hannu ya warce abdul da yake hanun momy da qarfin gaske tare da zuba mata wani mugun kallo. Nan da nan jikin momy yayi sanyi ammi tana son yin magana amma ta kasa. Dawowa kan zahra mashkhur yayi ciki fad'a yace.

Zahra dama ashe ban san baki da tunani ba ba sai yau wanan matar kika bari ta d'auki abdul ko kin manta wacece ita? So kike ta salmantar mana da shi tinda ita mguwa ce. Zahra tama rasa mai zata ce shiru kawai tai tare da sunkuyar da kai, dallah tashi mu tafi mashkhur ya fad'a yana nufo inda su zahra suke a zuciye. Dole zahra ta fara qoqarin miqewa ta sa hannu ta d'auki mayafin kusa da ita dan bama nata bane.

mashkhur yana qarasowa yaja hanun zahra da qarfi gaske suka bar bedroom d'in. Zahra ko jakarta bata samu damar d'auka ba sabida masifar mashkhur, itama wayarta da badan tana hanunta ba sai dai ta barta a nan.

Haka mashkhur ya riga jan zahra da sauki ko takalmin babu a qafarta har tuntu6e take, zahra sai cewa take yaya mashkhur yaya mashkhur dan Allah ka cika ni kar na fad'i, amma ina sam mashkhur ya kasa sauraran zahra. Sabida mashkhur ran shi ya 6ace sosai.
Mashkhur ba shi ya tasaya ba har sai da suka fita hara bar gidan suka qarasa parking space d'in gidan, inda yayi parking d'in motar sa.

Yana zuwa ya bud'e motar, sanan ya bud'e murfin gaba cikin tsawa yacewa zahra ta shiga. Dole zahra ta shiga tana shiga mashkhur ya d'ora mata abdul a cinya ta sanan ya rufo motar da qarfi gaske. Bayan ya rufo dawowa yayi mazaunin drive ya shiga ya zauna shima, sanan ya rufo murfin motar a zuciye.

Bazaki riqe shi da kyau ba sai ya fad'i ai dama naga alama ba darajar sa kika sani ba, mashkhur ya fad'a a tsawace. Zahra da tuni ta fara kuka hannu biyu tasa, ta riqe abdul. Wai ita da bataji ta gani ba amma mashkhur ya rufe ta da fad'a. Haka mashkhur ya ja motar a guje suka bar gidan, zuciyar a harziqe kawai dan yaga zahra tana kuka ne amma da ba abinda ze hana ya cigaba da yi mata fad'a.

Cikin 'yan minutes kad'an zahra da mashkhur suka koma gida sabida gudun da yayi. Mashkhur yana parking zahra ta bud'e murfin motar ta fuce hannu riqe da abdul. Shima haka mashkhur bayan zahra yabi rai a 6ace. Bayan sun shiga direct sama zahra ta hau tana hawa ta wuce bedroom ta kwantar da abdul sanan ta sulale a qasa ta saki kuka mi cin rai sabida ita ba abinda yake sata kuka sama da fad'an mashkhur.

AMMI.

Ammi sosai ta ringa bawa momy haquri momy kuwa bataji haushin mashkhur ba bare abinda yayi ya dame ta, sabida tasan komai ya faru ita ta jawa kan ta. Momy miqewa tai da niyar tafiya dakatar da ita ammi tai tace bari tasa haidar ko faruq ya kai ta gida yaya abdul. Hjy kaka fafar taqi yarda haidar ko faruq ya kai momy gidan abdul tace wlh baza a cutar mata da jikoki ba dan haka dole sai driver ne ya d'au ki momy domin ya kai ta gidan yaya abdul.

Ko da suka qarasa gidan a dede lokacin abdul ya futo sallah magriba. Ko da yaga momy bai nuna jin dad'i zuwan taba dan ko gidan ma bai bari an shigar da ita ba cewa driver yayi ya mayar da ita inda ya d'auko ta. Bayan abdul ya wuce masallaci a zuciya, driver bigawa ammi yayi ya sanar da ita yarda su kai.

Ammi ta nuna rashin jin dad'in hakan dan haka ne yasa ta bigawa abdul. Tayi mai fad'a sosai dan tun da ammi take da abdul bata ta6a yi mai fad'a kamar haka ba, kuma ta ba shi umar ni akan ya gaggata bari momy ta shiga gidan, ba yarda abdul yayi haka ya bigawa mai gadi aka bud'ewa momy qofa suka shiga.

Ko da abdul ya dawo a farfajiyar gidan yaga momy sai zaro ido take dan haka dole ya gai da ita fuska babu yabo sanan yayi mata iso zuwa cikin gida. Suna shiga zaune suka tarar da nana tana kallo daga ita dai riga iya guiwa mai siririn hannu. Duk da nana bata san wace abdul ya shigo da ita ba.

Hakan bai hanata sakin fuska ba da gaisar da ita cikin mutumci. Abdul kuwa sama ya haye zuciya ba dad'i. Ruwa nana ta kawowa momy da lemo sanan tace mata tana zuwa. Bayan abdul nana tabi dan sanin wace wanan matar. Zaune ta tarar da shi akan bed fuskar shi babu annuri, zama nana tai a kusa da shi tare da cewa yaya abdul wacece ita?.

Gauran nunfashi abdul yaja dan har kunyar cewa nana maman sace abdul yake sabida tsabar irin cutar momy. Sake dafa shi nana tai tare da cewa honey magana fa nake ma. Qaqalo murmushi dole abdul yayi sanan yace zan gaya miki babyna amma ba yanzu ba. Nana tana qoqarin magana taji wayarta tana ringing. Miqewa tai daga kusa da abdul ta qarasa inda ta ajiye wayar.

Ammi ce take kiran ta, da sauri nana ta d'auka tare da cewa hello ammi ina wuni, bayan sun gama gaisawa. Jim nana tai tana sauraran abinda ammi take gaya mata, bayan ammi ta gama gayawa nana, nana cewa tai tom shikenan ammi in sha ALLAH za'ai yarda kika ce. Daga haka su kai sallama nana ta ajiye wayar. Fuska cike da fara'a nana tace yaya abdul dama momy ce tazo amma kaqi gayamin to ammi de tace ta kwana biyu kafin ta tafi.

Shiru abdul yayi bai ce komai ba. Nana fuska a sake ta miqe tare da cewa bari naje kar na barta shiru. Kafin abdul ya kai da magana nana ta fita da tsangalaliyar rigarta kan nan ko d'an kwali babu kamar ba wajan suruka zata ba. Nana tana sauka qasa ta qarasa wajan momy fuska cike da fara'a tace momy kiyi haquri kinji ni shiru ashe kice.

Momy murmushi kawai tai ba tare da tace komai ba,. Kafin kace me tini nana ta cikawa momy gaba da abinci kala-kala, fura, tuwo, snacks, lemuka dade saurayin abubuwa. Haka nana tai ta jan momy da hira tana cewa taci abinci. tun momy bata sakin jiki harta fara sakin jikinta. Ba jimawa momy ta saki jikin ta sosai ta fara cin abinci da nana ta kawo mata.

Dama ita nana kun san bata da wuyar sabo tana son mutane. Ko da momy taci to qoshi ta gama cewa tai zata tafi nana hana tai, tace mata ai ammi tace karta tafi ta kwana biyu. Kuma nana tacewa momy in yaya abdul ya fita batajin dad'i shiru take zama. Momy bata yarda ba daga farko amma haka nana ta zauna ta ringa yi mata magiya har ta amince da haka.

Nana taji dad'in hakan sosai, sai wajan qarfe 10 dare suka gama hirar. Nana tacewa momy tazo su hau sama amma momy tace aa ita qasa ma ya ishe ta. Hakan ne yasa nana ta kai momy bedroom d'in qasa. Momy tana ji dad'in yarda nana take mata sosai da sosai dan bata ta6a tunanin a cikin a halin zahra za suyi mata ko kallon arziki ba.

Bayan nana sunyi sallama da momy sama ta wuce wajan mijinta abdul. Tana shiga ta murd'a handel qofar sanan ta shige. A baje taga yaya abdul akan bed ta tafi duniyar tinani. Nana da sauri ta qarasa ta fad'a jikin abdul duk da tana da 'yar qiba amma haka take fad'awa abdul jiki, kuma gashi shi, bashi da qiba kamarta.

Adede lokacin abdul ya dawo daga tunanin daya tafi. Wai yaya abdul naga yau ka canza kamar baka farin ciki da zuwan momy. Murmushi dole abdul yayi tare da cewa aa kawai dai yau ne gaba d'aya naji bana jin dad'i. Tom shikenan yaya abdul nana ta qarasa magana tana sakar mai murmushi. Daga haka dai nana da abdul suka tafi duniyar ma'aurata.

Mashkhur and zahra.

Zahra ta jima a durqu she a wajan nan tana kukan baqin ciki. Mashkhur kuwa toilet ya shiga yayi wanka da ruwan sanyi kamar yarda ya saba in yana 6acin rai. Bayan ya futo zama yayi akan bed sai da zuciyar shi tai sanyi sosai sanan ya miqe ya nufi bedroom d'in zahra. A durqushe ya tarar da ita ta ci kuka ta godewa Allah sai ajiyar zuciya take.

Mashkhur bai ji dad'in hakan ba sam sabida shi harga Allah baya son ganin zahra tana kuka. A hankula yake takawa har ya qarasa inda take sanan ya russina qasa dede inda take. Zuba mata ido yayi kamar mai nazari, can ya kira sunan ta cikin sanyayiyar murya. Zahra kuwa ko kallan mashkhur ba tai ba bare ma yasa ran zata d'ago.

Dafata mashkhur yayi sanan ya fara magana a hankula! Kiyi haquri ki dena kuka kin san bana son ki ringa zubar da hawayan ki,. Bada son rai na nayi miki fad'a ba duk da nasan bakya son hakan, amma nayi mamaki yarda kika bari waccan matar ta d'auki abdul, kuma bayan kin san muguwa ce bata son ki bata so na, to bakya tunanin zata iya cutar mana da shi.

D'agowa zahra tai fuska cike da hawaye tace! Nima bada son raina na bata shi ba, amma tinda tana son d'aukar shi ai bazan hanata ba ko dan darajar yaya abdul, ni yanzu kenan sai ka ringa yi min fad'a akan abinda banyi ba sai kace wata yarinya. Hannu mashkhur yasa ya gogewa zahra hawayan fuskar ta sanan yace tom shikenan.

Naji na dena yi miki fad'a tinda bakya so amma pls netx time ki kiyaye irin hakan. Gyad'a kai zahra tai alamun to,. Yauwa teddyna kiyi min murmushi mana mashkhur ya qarasa maganar yana jan kumatun zahra. Noqe qafad'a zahra tai alamun aa, hannu biyu mashkhur yasa yana wasa da kumatun zahra yana cewa kamota nan kamota nan kamar wata baby.

Zahra bata san sanda wani kyakyawa murmushi ya kwace mata ba. Yauwa teddyna maman abdul koke fa, d'agowa zahra tai ta hararie mashkhur cikin sigar wasa. Baki mashkhur ya kai yayi mata rad'a, bayan ta gama ji murmushi tai sanan itama ta rad'a mai amsa a kunne. Bayan ta gama ta cize kunan kad'an kamar yarda ta saba.

Rungume junan su suka yi zuciyoyin su cike da qaunar juna. Zahra ganin mashkhur yana son wuce gona da iri hakan ne yasa ta ture shi tare da cewa aa. Kallon ta mashkhur yayi sanan yace sabida me dear ki barni mana?. Cikin muryar kuka zahra tace sabida bana sallah magana. Sauke nunfashi mashkhur yayi sanan yace zamu had'u next time.

Daga haka mashkhur ya shirya tasf domin ya tafi masallaci bayan ya tafi masallaci kuma daga nan ya wuce gidan ammi dan zuciyar shi ta kasa samun nutsuwa akan abinda ya aika ta yasan ammi tabbas bataji dad'in hakan ba kuma mashkhur sam baya son ya 6atawa ammi rai. Mashkhur yana fita zahra ta d'auki abdul tana mai wasa sabida ya fara kuka.

Bayan yayi shiru ta bashi nono, wanka ta shiga tayi sanan ta dawo ta kwanta zuciya cike fall da jimamin abinda mijinta mashkhur yayiwa momy, duk da kuwa tasan ya dace ayiwa me irin halin momy abinda yafi haka ma. Amma sam zahra bataji dad'in hakan ba daga haka dai bacci yayi awan gaba da zahra da abdul.

Mashkhur

Sai da yayi isha'i sanan ya nufi gidan ammi misalin qarfe 8:30 motarta ta shiga gidan su. Baya yayi parking a hanzarce ya shiga cikin gidan. Mashkhur yana shiga ya wuce 6angaran ammi, bayan ya shiga direct d'akin ta ya wuce. Sai da yayi knocking ammi ta bashi izinin shigowa sanan ya murd'a handel d'in bedroom bakinsa d'auke da sallama ya shige.

Kallo guda ammi tayiwa mashkhur ta d'auke kai ta cigaba da ninke kayan baby's, sallamarma a ciki-ciki ta amsa. Dama mashkhur yasan hakan zata kasance qarasawa yayi ya zauna kusa da ita tare da cewa ammi barka da dare. Fuska ba walwala ammi tace barka. Jim mashkhur yayi na wasu lokutan sanan yace ammi kiyi haquri ya qarasa maganar yana sunkuyar da kai tare da sosa qeya.

Haquri kuma ai bani zaka bawa haquri ba mashkhur kaban mamaki,. Haba mashkhur ai ko ba komai bai kamata kayiwa halima haka ba duk da abinda tai bai dace ba, sai ka raga mata taci darajar abdul. Wanda ya d'auke ni kamar uwa ko nace fiye da uwa ma, yana bani respect sosai kaf cikin 'yarana abdul ne kawai nake iya gaya mai magana sau d'aya yaji.

Abdul yana mutuntani yana bani daraja biye da kowa a duniyar nan yana so na, ta ai ko dan haka ma ka d'agawa mahaifiyarsa qafa. Ko abdul baya son halima ai dai uwace a wajan sa kuma uwa tafi qarfin wasa. Dan haka gaskiya banji dad'in abinda kayi mata ba, ni bance dole sai kun yafe mata citar da tai muku ba amma ai ya kamata ku ringa girmama ta.

Gaskiya banji dad'in abinda kayi ba mashkhur kwata-kwata kuma ina fata da gargad'in ka akan karka sake aikata abu makamanci haka. Haka mashkhur yayi shiru ammi ta gama yi mai fad'a kamar yarda ta saba in yayi mata lefi. Bayan ta gama tayi shiru mashkhur cikin ladabi yace to ammi in sha ALLAH hakan bazataa sake faruwa ba dan Allah kiyi haquri bana so kina fushi dani.

Hmmm mashkhur kenan ni ba fushi nake da kai ba kuma na yafe ma duniya da lahira Allah yayi maka albarka komai ya wuce, amma dan allah a kiyaye gaba. Tom nagode ammi allah ya saka miki da gidan aljanna. Haka mashkhur yayi ta jan ammi da hira har sai da yaga ta sauko sosai sanan ya tashi yayi mata sallama. Ya biya wajan dady ya gai da shi sanan ya wuce gida..........

Momy.

Momy tana jin dad'i yarda nana take kula da ita, nana ta takurawa yaya abdul akan ya dena zaman doya da manja da momy. Dole abdul ya haqura yake sakarwa momy fuska ko dan sabida nana da ammi. Daga qarshe abdul yaga abunda yake bai kyauta ba tinda ya lura momy tayi nadama. Ya farajin tausayin ta sosai, dan haka duk abinda ya dace yana siya mata.

To momy sai da akai sunan su ruma sanan ta fara shirya-shiryan komawa. Shima bada son ran nana ba, abdul ya siyawa momy waya sanan ya bata kud'i masu dama. Sanan har kaduna ya kai ta ya siyar mata kayan abinci ya kama mata hayar gida. Yade futar da momy daga halin talauci da qunci da take ciki.

Koma haka nana take sawa akai-akai yake zuwa gai da momy har wataran itama tana yi mata girki sanan su tafi tare ta gai da ita. Abdul yana jin dad'in haka da nana take duk da ba wani son mahaifiyar tashi yake ba. Hakan ne yasa abdul ya qara son nana sosai. Ga kulawar da yake bata sabida a lokacin tana da qaramin ciku...........

Mu had'e a last page.

ADALILINTA 💜❤💜

BY AMINA BAYERO 💜❤💜

Last page

Typing.............

Hakan ne yasa abdul ya qara son nana sosai. Ga kulawar da yake bata sabida a lokacin tana da qaramin ciku...........

6angaran zahra da mashkhur kuwa soyayyah suke sosai, suna qaunar junan su suna kulawa da junan su sanan suna kula da yaran su abdul wanda ya sake kyau da wayo, yanzu ya girma sosai. Gashi yaro bashi da rigima hakan ba qaramin yiwa zahra da mashkhur dad'i yake ba.

After 5 months.

Bayan wata abdul yayi wata 7 zahra ta fahimce tana da cikin wata biyu. Hmmm zo kuka tashin hankali wajan zahra kamar cikin da bashi da uba. Tayi kuka sosai dan har cewa tai sai ta zubar da cikin nata. Sabida zahra ta tsorata da haiwuwa kuma gashi ko yaye abdul daga nono ba tai ba. Mashkhur yayi lallashi sosai akan zahra tabar cikin amma taqi yadda.

Sai da mashkhur ya nunawa zahra fushin sa sanan ya shawo kanta da kyar ta haqura zata haiwu. Mashkhur yacewa zahra tasan ma ko baby girl zata haifa musu hakan ne yasa tabar cikin nata dan zahra tana son ta haifi 'yar mace. Haka zahra da mashkhur suka cigaba da rainon ciki da abdul, bayan abdul ya cika 10 month dole zahra tai mai yaye dole.

Dan alokacin yana shan madara da kamu dade sauran abubawa. Kuma yana da girman jiki dan inka gan shi sai kai tinanin yayi shekara 1. Bayan yaye abdul da wata guda nana ta haifo kyakyawar babyn ta masha Allah mai kama da ita. Nana ta so a sawa babyn sunan momy sabida suna d'asawa sosai.

Amma abdul yaqi yace shi sunan zahra zai sa mata. Ai kuwa haka akai ranar suna yarinya taci sunan ta fatima zahra. Zahra tayi farin cikin hakan sosai da sosai,. Zahra sai da tayiwa takwarar ta akwatin kaya saiti bakwai, farin ciki zahra tai sosai kuma har zuciyar ta taji tana qaunar 'yar ta kuma takwarar ta.

After 5 month.

Zahra ta sauka lafiya ta samu baby boy again, shima de same abdul dan da mashkhur yake kama sosai. Zahra duk da mace taso haifa hakan bai hanata farin ciki ba, shima mashkhur yayi farin ciki da hakan sosai kuma sai da yayiwa zahra kyautar saitin gold. Ranar sona yaro yaci sunan shi abubakar sadeeq wato sunan dady kamar yarda zahra ta buqata, ana yi mishi kara da sadeeq.

Bayan zahra tai wata uku da haiwuwa itama ilham ta haifi kyakyawar babyn ta mace, wanda taci sunan maman su zahra wata aisha. Tun daga haka zahra da ilham su kai planing sabida kar su sake d'aukar wani ciki.
Kullum zahra da mashkhur sake son junan su suke sam basa gajiya da junan su.
Abun de gwanin burgewa haka suka ciga da rayuwar su suna kula da yaran su.

Momy.....

Allah de ya temaki momy ta samu miji ta aura shima de d'an kano ne. Matan sa biyu amma uwar gidan ta shi ta rasu tabar yara 4 biyu maza biyu mata, kuma ita kishiyar tace bazata riqe ba hakan ne yasa ya auri momy domin ta kulamai da yara. Mutumin yana da rufin asirin sa ba lefe, tinda momy bata rasa ci bare sha.

Momy tsakani da Allah take kula da yaran nan kamar uwar su sam bata cutar da su m komai tana yi musu dede gwargwado. Suma

Please Login or Register in order to submit comment