Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wanan maganar ko?

Au harma da tambayata ma mai zakai da ita koh?, to ai kafi kowa sanin mai za kai da ita tinda kana bin matan banza a waje. Da sauri mashkhur ya d'ago tare da cewa haba dady nifa ba wasu matan banza da nake bi d'an ni ban ta6a ZINA ba aruyuwata . Kallan banza dady ya watsa mai tare da cewa, sai kaje ka gayawa wanda bai sani ba, kuma wlh dole ka zauna da mamana a matsayin matar ka.

A zuciye mashkhur yace haba dady nifa wlh basan yarinyar nan nake ba da zaku aura min ita. Jinjina kai dady yayi yana mamaki yanda mashkhur yake mayar mai da magana gatsau amma bai yi mamkin hakan ba sabida yasan shaye-shaye yake. To da kake cewa baka santa ai ita ai ba sanka take ba, inma banda qaddara mai mamana zatai da kai dubi duk ka lalata rayuwar ka.

Kuma bari kaji sati mai kamawa in zaka koma rasha da ita zaka tafi. Haba dady wlh ni ba inda zani da ita nifa wlh saki uku ma zanyi mata. Wasu kyawawan tagwayan maruka dady ya qara sakarwa mashkhur jikake tass-tass, tare da cewa wlh mai sunan baba hardai ka sake ka saki zahra ba Ni ba Kai sai dai ka nemi wani UBAN ba dai niba. daga haka dady ya fuce daga part d’in a fusace yabar mashkhur a tsaye.

Mashkhur kuwa jinjina kai yayi tare da furta wlh kuwa sai da kuzo ku d'auki GAWAR 'yar ku daga haka ya wuce sama a zuciye. Yana zuwa ya shige bedroom d'in sa tare da, samai key. Kayansa ya fara cirewa yana gama cirewa ya shige tolet ya watsa ruwa ya futo, d'aura da towel, a ugu. Kayan baccin ya zura sanan ya fara shan kayan maye, yana gama sha ya baje a kan bed ya kwanta.

Zuciyarsa wani irin quna take mai, wai shi aka aurawa, zahra jin abin yake kamar al mara. Haka ya shiga tinani kala-kala zuciyarsa kuwa sai tiririn baqin cike take. Wai ADALILIN ZAHRA dady yake cewa zai iya rabuwa da shi. Jinjina kai yayi zuciya cika da baqin ciki, daga haka bacci mai nauyi ya kwashe mashkhur saka makwan kayan mayan da yasha..........

Zuwa anjima da daddare zan sake yi muku posting d'in ragowar wanan page d'in. Wannan page d'in yana da tsayi sosai ba kamar sauran pages d'in baya ba ajjima da daddare in na gama typing.. Zan yi muku posting.

New book on 2023.

ADALILINTA💜❤💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

My number 09162226240.

Jinjina kai yayi zuciya cike da baqin ciki, daga haka bacci mai nauyi ya kwashe mashkhur saka makwan ganin kayan mayan da yasha..........

Washegari.........
Knock d'in qofar ne ya tashi shi daga baccin da yake. Da kyar ya iya bud'e indanunsa cikin kasalaliyar murya yace waye?. Muryar ammi yaji tana cewa nice, da kyar ya iya tashi jiki ba kwari ya nufi qofar. Yana bud'e qofar ya juya, ya koma kan bed ya sake kwantawa. Baki d'auke da sallama ammi ta shigo, murya qasa-qasa mashkhur ya amsa mata sallamar.

Ammi tana qara sowa ta zauna akan bed d’in tare da zubawa mashkhur ido, wanda ya lumshe idon sa kamar mai bacci. Mashkhur sunan sa ammi ta abbata, a hankula ya bud’e' idanuwanta shima ya zuba mata ido yana kallansa kamar yadda take kallansa. Can ammi tace mashkhur tashi inaso, muyi magana, shiru mashkhur yayi can kuma ya tashi ya zauna kamar yanda ta umarce shi.

Gyara zama ammi tai tare da cewa mashkhur yanzu abinda kake ka kyauta?. Langwa6e murya mashkhur yayi tare da cewa ammi lokaci guda kin tsaneni kin dai na sona sabida qaddara ta same ni koh?. Shuru ammi tayi tana tinanin maganar mashkhur, da ammi fushi take da mashkhur kwata-kwata ta dena kula shi, amma yanzu da hjy kaka ta gayawa ammi asiri akayiwa mashkhur, yake shaye-shaye, tausayin mashkhur ne ya kama ammin.

Ajiyar zuciya ammi tai tare da cewa wlh mashkhur ban tsane kaba, ka ta6a jin inda uwa ta tsani d'anta? Girgiza kai mashkhur yayi alamin aa. Cigaba da magana ammi tai da cewa mashkhur bana so naga kana shaye shaye da bin ma!!! Da sauri mashkhur ya toshewa ammi baki da hanunsa tare da furta haba ammi karki gayamin maganar da dady ya gayamin wlh zuciyata bazata jure ba.

Haba mashkhur nifa uwarka ce, kuma dole na gayama gaskiya lokaci yayi da zaka rabu da matan bazan nan, tinda gashi mun d'aurama aure da matarka ta sunna. Wani siririn tsaki mashkhur yayi, da yaji ancewa zahra matarsa. Murya a sanyaye kamar mashkhur zai yi kuka ya riqe hanun ammi tare da cewa, ammi nasan ke kika haifeni, kuma kinsan halina koh?.

To wlh tinda naka ba ta6a kusantar wata 'yar mace ba nayi zina , haba ammi ku fahimceni dan ALLAH ku dena yimin kallan ma zinaci ko mai bin mata pls ammi, mashkhur ya qarasa maganar kamar zai yi kuka. Zuba mai ido ammi tai, d'an jikin ammi yayi sanyi tunda taga mashkhur yayi mata hakan tasan tabbas da gaske yake baya bin mata, dan in dae mashkhur yana aikata abu, in dai yayi mata qarya zata gane, kuma yanzu ta tabbatar da gaske yake.

Ajiyar zuciya ammi ta sauke tare sa cewa to in baka aikata hakan mai yarinyar nan take zuwa wajan tayi?. Koh ammi bata gayawa mashkhur wace yarinya take nufi ba yasan, zee take nufi, kuma yana jin hakan ya tabbatar Ahmad ne yazo yayi musu zancan zee, tinda shi kad'ai ne ya santa a Nigeria. Ammi wannan fa qawata, ba wani abu da yake tsakanin mu in ba abota ba.

Shiru ammi tai tana mamaki wai yau ne mashkhur yake kula wata harda ce mata qawarsa, shida ko zancan mace bayaso ada. Maganar mashkhur ce ta dawo da ammi da tinanin da ta tafi, ammina wai dan ALLAH sabida mai kuka d'auramin aure da yarinyar nan, wlh ammi na tsane ta bana son ta a rayuwata. Nan da nan ammi ta d'aure fuska tare da cewa haba mashkhur wai mai zahra tayi ma haka ne a duniya?. Shiru mashkhur yayi ba amsa.

Kuma naji abinda kayiwa dadyn ka jiya yanzu mashkhur ka kyauta?, amma ammi kinsan dady bai kyauta ba, da ya had'a auranan kuma yace dole sai na tafi rasha da ita. Jinjina kai ammi tayi tare da cewa shikenan, yanzu dai ya kamata kaje ka bawa dadyn ka haquri, akan abinda kayi mai, kuma ka roqe shi akan basai ka tafi da zahra ba, sabida nima sam banaso ka tafi da zahra, tinda ba jituwa kuke ba, kar kaje ka ringa zalintar ta, kamar yadda ka saba a baya.

Girgiza kai mashkhur yayi tare da cewa wlh ammi dady yana da kafiya, tinda ya yanke hukunci, ba zai canza ba. Shiru ammi tai can kuma tace, eh ko bazai yanda ba kaje ka bashi haquri, akan abinda kayi mai jiya da daddare. Tom ammi zani. Yauwa mashkhur sai kuma magana ta qarshe, ammi ta fad'a murya a sanyaye. Tom ammina ina jinki?, dan ALLAH mashkhur ka dai na shaye-shaye nan wlh bana so.

Sunkuyar da kai mashkhur yayi tare da cewa wlh ammi nima inaso na dai na amma na kasa, pls ki tayani da addu’a kawai?. In sha ALLAH mashkhur zan ringayi amma kai ma ya kamata ka dage da addu’a da kuma sallar dare, sanan kullum ka ringa azkar safe da yamma?. Tom ammina zan ringa yi in sha ALLAH. Qoqarin miqewa ammi ta fara, da sauri mashkhur ya ruqo hanunta tare da cewa ammi kin manta da abu d'aya fa.

Kallansa tayi tare da cewa mene?, bud'e mata hannu mashkur yayi tare da cewa hug, hararar wasa ammi ta watsa mai, tare da nuqe kafad'a tana cewa aa, bazanyi hug d'in ba, zaro ido mashkhur yayi cikin mamaki yace because of what?, sabida ka girma yanzu kuma gashi har aure, kayi, had'e rai sosai mashkhur yayi musamman ma da ya tina da zahra aka d'aura mai aure.


Ammi da taga haka murmushiyayi tai tare da dacewa matsawa gab da shi, ta bud’e mai hannu alamun hug, ba musu mashkhur ya fad'a jikin ta, suka rungume junan su. Lumshe ido mashkhur yayi da yaji shi a jikin ammin tasa, wani irin feeling yake ji, sabida raban da ammi tai mai hakan har ya manta, wani irin san mahaifiyar tasa ne ya lulu6e shi. Itama ammin lumshe idon ta tayi tana jin qaunar d'an nata tana ratsa sassar jikinta.

Sunfi minti goma a haka, dan mashkhur ma har ya fara bacci a jikin ammin, muryar ammi ce ta ratsa kunan mashkhur!! Mashkhur sakeni na tafi, ina da abinda zanyi. Haba ammi ki barni mana nayi bacci a jikin wlh nayi missing d’in kulawarki sosai ammi. Ammi da taga bazata iya biye wa mashkhur ba ture shi tai da qarfi, daga jikinta, tare da kama hanyar fita.

Murmushi mashkhur yayi tare da cewa wlh ammi na, ina son ki, girgiza kai ammi tai tare da yin murmushi ta fuce daga bedroom d’in. Mashkhur kuwa tashi yayi yai wanka sanan ya shirya ya nufi hanyar babban falon break fast.

Zahra.........

Yau fah zahra ko bacci ba tai ba kwana tayi tana kuka, sai da asuba ta samu ta rintsa. Misalin qarfe goma na safe dady ya aiko ilham ta kira zahra, zahra tana bacci ilham ta tashe ta, tace mata wai dady yana kiranta. Toilet zaha ta shiga ta wanke baki da fuskarta da ta kunbura suntum tai jajjawur. Tana kammalawa ta futo daga toilet d'in, sanan ta d'auki mayafin ta tasa, ta wuce kiran dady.

Zahra tana zuwa falo ta tarar da faruq da haidar harma da ammer suna break fast akan draining table, shi kuma abdul yana gefe da magaguna a gabansa fuska ba annuri, dady yana kan kujera a zaune, ilham kuma tana qasan a kefan kujerar da dady yake zaune. A dai-dai lokacin ammi ta dawo da d'akin mashkhur, itama ammi kama waje tai ta zauna tana yiwa abdul sannu. Zahra kuwa qarasawa kusa da ilham tai sanan ta zauna tare da cewa dady gani. Cikin kulawa da qauna dady yace mamana taso ki zauna a kusa dani?, girgiza kai zahra tayi alamun aa.

Murmushi dady yayi tare da cewa ok wato har kin fara jin kunyar surikinki kenan?. Zaro ido zahra tayi tare da saurin miqewa ta zauna a kusa da dady ido cike da kwalla. Abdul kuwa ji yayi kamar dady ya zuba mai garwashi, a zuciyar sa, ammin kuwa murmushi tai da jin maganar dady su faruq da ilham kuwa dariya suka farayi qasa-qasa. Kallan zahra dady yayi tare da cewa! Mamana, cikin murya kuka zahra tace na'am.

Nan da sati d’aya ke da mijinki zaku zafi, rasha tare. Abdul da masifar baqin ciki ta ishe shi, da sauri ya tashi yabar wajan ya nufi part d’in su. Abdul zai futa kenan shi kuma mashkhur ya shigowa, mashkhur kuwa tsayawa yayi da tafiyar saka makwan jin muryar zahra cikin kuka tana cewa aa gaskiya ni dady bazani ba, wlh in dai nabi yaya mashkhur kasheni zai bazan dawo da rai ba.

Mashkhur kuwa yana jin hakan wani shu'umin murmushi ya saki a zuciyarsa yake kwaraii, kuwa kashe ki zanyi.
Cikin muryar rarashi dady yace, haba mamana ba wanda ya isa ya kashe ki sai kwanan ki ya qare, kinji?. Mashkhur ne ya shigo baki d'auke da sallam bai jira amsar kowa ba ya nufi kan dinining, ya zauna domin break fast. Dady kuwa cigaba da magana yayi da cewa kin yarda zaki je ko mamana?. Girgiza kai zahra tayi alamun aa.

Haba mamana nasan ke mai biyayya ce, kiwa dadyn ki biyayya mana, shiru zahra tayi bace komai ba. Dady sake magana yayi tare da cewa dan ALLAH mamana ki yarda kutafi kinji?, ba yanda zahra ta iya bazata ta6a yiwa dady musu ba tinda harda ALLAH ya had'a ta, a ala dole zahra ta d'aga kai alamun ta yanda. Yauwa mamana ALLAH ya yi miki al barka. Wani haushine ya kama mashkhur da yake zaune akan draining din cin abinci, cikin zuciyarsa yace wato, ita harda roqanta ake akan ta amince, shikuma da mari da barazana ake so ya amince. 😂

Haushin zahra, mashkhur yake ji sosai, musamamn yanda yaga ta kifa kanta akan cinyar dady yana rarrashin ta. Lalai wanan ya rinyar ta shanyewa dady zuciya, sabida baqin ciki mashkhur ko abincin ma bai ciba ya fuce a fusace daga d'akin. Part d’in su ya koma ya d'auko key d'in motarsa da wayarsa ya fuce daga gida ya tafi wajan ahma domin sanan da shi mai ke faruwa..........

Misalin qarfe tara na dare mashkhur ya dawo, bedroom d’in sa ya shiga sanan yayi wanka ya canza kaya. Kamar ance ya fita ventilation d'in bedroom d’in yana shiga ya hango dady a can qasa a lambu yana shan iska, dama sometimes dady yana yawan zama, anan ya sha iska da daddare. Dan haka a hanzarce mashkhur ya zura takalminsa ya fuce somin zuwa wajan dady.

Mashkhur yana isa lambu ya nufi inda dady ke zaune yana shan iska. Mashkhur Yana qarasawa yayi sallama cikin ladabi. Dady kuwa ko d'agowa bai yi ba ya amsa. Mashkhur samu waje yayi ya ra6a a gefan dady ya zauna. Dady barka da hutawa?, fuska a d'aure dady yace yauwa. Dama dady inaso na baka haquri akan abinda ya faru jiya da daddare in sha ALLAH bazan qara ba. ALLAH yasa dady ya fad’a a taqi ce.

Shiru mashkhur yayi na wasu lokutan kafin yace dan ALLAH dady kayi haquri, ka janye batin tafiya ta rasha da zahra, wlh dady, banaso naje mu ringa samun sa6ani da ita tinda kaka ba jizuwa muke da ita ba. Kada ALLAH yasa ku jitun, tafiya ce sai kunyi ba fashi, cewar dady. Dan ALLAH dady wana lefi nayi ma haka had'a ni aure da ita. Ko d'aya ra'ayi ne kawai, cewar dady.

Dady in sha ALLAH daga yau zan dena duk abinda bakaso dan ALLAH ka raba auran nan. WLH mai sunan baba abu uku zakai min na raba auran nan kai da zahra. Da sauri mashkhur ya d'ago tare da cewa dady inaji menene. Gyara zama dady yayi tare da cewa abu na farko shine ya zama dole ka tafi da zahra rasha. Na biyu kuma sai ka dai na munanan halayyarka ta shaye-shaye miyagun kwayoyi. Na uku kuma sai ka futo da ruselt mai kyau a jarabawarka ta karshe.

Ni kuma nayi maka al qawarin hardai kaje rasha ka aikata wanan abubuwa, wlh in dai baka fara son zahra ba da kai na zan sa ka sake, saki UKU ma. A zuciyar mashkhur cewa tabb wanan banzar yarinyar zan so?, Ajiyar zuciya mashkhur yayi tare da cewa shikenan dady wannan sune abubuwan da kake so kwai. Gyad'a kai dady yayi tare da cewa eh su nake so. Murmushi mashkhur yayi tare da cewa dady na AMINCE.

da biyu mashkhur ya amince da hakan na farko dai yasan ko ba komai nan da shekara d'aya da rabi yana dawowa daga rasha zai rabu da zahra, na biyu kuma ya d'au alwashin sai ya ganawa zahra azaba mai radad'i ya horar da ita da azaba. . murmushi samun nasara dady yayi tare da cewa Yauwa mai sunan baba ALLAH ya bada sa'a. Amen dady, daga haka suka cigaba da hira abin sha'awa, kamar ba su bane sukai baran-baran jiya da daddare..........

To fah shirya-shiryan tafiya mashkhur da zahra rasha ya kankama, shima abdul a ala dole ya danne son zahra da kishin sabida mashkhur ya bashi labarin yanda sukayi da dady. Ba abinda ammi ba tanadarwa zahar na tafiya rasha ba. Kaya kala-kala man shafawa, kayan baccin audiga pants bireziya komai dai ta shiryawa zahra. 6angaran zahra kuwa kullum kuka take tun ammi da abdul suna rarrashi har sun gaji...

Tom yaufa ta kama ranar tafiyar su zahra rasha, harda dady da ilham da kuma abdul zasu raka zahra rasha. dan haka tunda asuba, suka fara shiri. Zahra kuwa kuka kawai take, ammi kuwa sai da ta yiwa mashkhur magiya akan karya zalinci zahra, ko hannunsa kar yasa ajikinta da niyar duka, barema yay mata kallan banza?, mashkhur dai yace to amma ba har zuciyarsa ya fad'a ba.

Momy kuwa kirawo mashkhur tai tare da ziga shi akan ya ringa dukan zahra yana azaftar da ita?, mashkhur kuwa yaji dad'in hakan koma ya amince, da abinda momy tace mai. Wajan qarfe shida na safe su zahra suka gama shiryawa tsaf, domin tafiya rasha. Hjy kaka kuma ta bawa zahra ta kadda da addu’a yanda zata ringa amfani da su. Kowa kuka yake hatta su haidar da ruma sai da su kai kukan rabuwa da zahra, kai harma ammi da hjy kaka. Momy da rukee kuwa ko kwalla basuyi ba, dama ALLAH ya tai maka ammer yana bacci shi yasama abin yayi sauqi.

Haka su zahra suka shige motar drive yayi gaba da su. Lokacin da sukaje airport sun had'u da ahmad. Ba 6ata lokaci suka shige jirgi, domin tafiya, zahra da take zaune a kusa da ilham kwanciya tai a jikinta tana ta matsar kwallah. Mutane sana gama shiga jirgi ya tashi zuwa rasha.........

RASHA...
Su zahra sun sauka garin rasha lafiya, kuma ba 6ata lokaci suka wuce masaukin su mashkhur. Zahra kuwa harta fawwalawa ALLAH ta dai na kukan. Suna zuwa zahra da ilham suka shiga bedroom sukai wanka sanan suka canza kaya sanan suka baje a kan bed bacci mai nauyi ya kwashe su. Dady da abdul ma bedroom d'in mashkhur suka wuce domin hutawa, shikuwa mashkhur sauka qasa yayi ya wuce wajan ahamd.....

Tom yau wajan kwanan su zahra hud'u a rasha, dady yasa zahra a makarantar boka, ta qasar rasha, ya sai mata uniforms da books, school back, takalmi, da sauran su. Harma waya da layi dady ya siyarwa zahra dan sun ringa gai sawa. Sanan dady ya sake siyar wata sabuwar motar ya bawa ahmad key, tare da bashi amnar zahra, kullum ya ringa kai ta makaranta, in zata fara zuwa, sabida dady yasan alin mashkhur ba kai zahra makarantar zai ringa yiba.

Ahmad ba musu ya amince, kuma ya yiwa dady al qawarin in sha ALLAH zai kula da zahra amana kamar qauwar sa, duk abinda take so zai mata, dady kuwa yaji dad’i hakan sosai. Tunda sukazo rasha ilham ta lura da yanda ahamd yake ta kallanta amma bata kawo komai a ranta ba.

Tofa rana baza qarya sai dai uwar d'aya taji kunya, yau sati su dady d'aya a rasha, kuma yau zasu koma Nigeria. Yasalam hankalin zahra ba qaramin tashi yayi, ba kuka take sosai, itama ilham d’in kuka take sosai sun riqe junan su ita da zahra. Abdul kuwa ji yake zuciyar sa kamar ta buga wai yau shi zai rabud da zahra na tswan shekara da watanni. Sosai dady da abdul suke rarrashin zahra.

Gefe guda kuwa oga mashkhur ne yake sakin wani shu'umin murmushi, wanda fassarar sa take nufi zaki gane kuskuran ki dani kike, zancan sai kinyi nadamar sanina a rayuwa. Da sauri zahra ta saki ilham ta rungume yaya abdul d'inta, sabida tasan zatai rashin d'an uwanta masoyinta. Abdul ji yayi kamar ya janye zahra sabida yasan yanzu ita ba maharramar sa bace, matar yayan sane.

Mashkhur kuwa a zuciyarsa cewa yayi ji wani iskanci har da rungume shi, wai a haka ita matar aure, ni mai ma zanyi da wanan wlh sai kin gane kuskuranki, yanda ya kamata. Zahra sakin abdul tai ta koma ta rungume dady, tana kuka kamar wata zautacciya, shima dady rungume ta yayi yana rarrashin ta. Mashkhur kuwa a zuciyarsa qara cewa yayi tabb lalai iskancin yarinyar nan yayi qarfi, kace ba qanin mijina harma da surikin take hugging?.

Lalai 'yar nan zan sai ta miki zama wai, ita bata yanda mai suriki koh?. Mashkhur duk a zuciyarsa yake fad'in hakan. Dady kuwa da yaga lokacin yana tafiya 6ab6are zahra yayi dag cikinsa yaja hannun ilham suka fuce. Shima abdul d'in fuska cika da kwalla ya bi bayana su. Mashkhur kuwa wani mugun kallo ya watsawa zahra tare da bin bayan abdul, sabida shi zai kai su dady airport a motar sa.

Aham kuwa tausayin zahra ne ya kamasa ganin ta d'urqoshi qasa, kuma ta kifa kanta a kan guwairta tana ta kuka mai cin rai. Da sauri aham ya tashi ya fuce ya nufi part d’in sa a qasa sabida bazi iya jurar ganin bai war ALLAH nan tana kuka ba, kuma gashi ba maharramarsa bace matar abokinsa ce, bare ya rarrasheta,.

Su dady sun qarasa airport cikin qoshin lafiya tun a mota dady yake yiwa mashkhur nasiha da fad'a akan karya sake ya daki zahra. Mashkhur kuwa tana shiga ta kunansa na dama tana futa a na hagu kawai to yake cewa dady. Mashkhur yana kai su dady airport suka shige jirgi ilham sai fama kuka take, shi dai abdul zuciyarsa tab da baqin ciki.

Dady ma ba'a san ransa yabar zahra ba sabida harga ALLAH yana qaunar zahra kuma yana tausayinta. Su dady basufi minti goma ba jirginsu ya tashi zuwa Nigeria........
Mashkhur kuwa yana ganin haka ya shige motar ya nufi hanyar gida, zuciyarsa fass, dan ko ba komai zai takurawa rayuwar zahra............

shin ya kuke tinanin zaman zahra da mashkhur zai kasan ce?

Shin kuna ganin mashkhur zai ragawa zahra kuwa?.

Shin waca azaba mashkhur zai ringa ganawa zahra?.

Shin kuna ganin mashkhur zai shiryu ya dai na shaye-shaye ya futo da result mai kyau?.

Shin kuna ganina mashkhur zai cika buransa na sakin zahra?.

Shin mashkhur zai so zahra kuwa?.

Shin zahra zata so mashkhur?.

Kubiyoni a littafin ADALILINTA na biyu domin samun amsoshin tambayoyin nan.

Nex book free ne shima bana kud'i ba.
Littafin ADALILINTA gaba d’aya, bana kud'i bane, free book ne.

ALHAMDULILLAHI........

ANAN NA KAWO QARSHAN LATTAFIN ADALILINTA NA D'AYA. ABINDA MUKAYI KUSKURE ALLAH KA YAFE MANA ABINDA MUKAI DAI-DAI ALLAH KA BAMU LADA.

Ina miqa dubun gaisuwa da godiya ga wanda suke bibiyar littafin ADALILINTA, ALLAH ya bar qauna.

Zan tafi hutun sati biyu ko uku koma wata kafin na cigaba da rubuta littafin ADALILINTA book 2. Ga wanda suke buqatar littafin na biyu in na fara rubutawa su ringa ka rantawa qofa a bud'e take, zaku iya yimin magana ta wannan number 09162226240, KU yimin magana ta WhtsApp. Free book ne bana kud'i.

Game buqatar littafin ADALILINTA full shima ya yimin mgana ta wannan number 09162226240. Free book ne bana kud'i ba.


ADALILINTA💜❤💜

BY AMINA BAYERO💜❤💜

BOOK 2.

Typing.............

*Page 51*


Barkanmu da dawowa littafin ADALILINTA da fatan kowa yayi hutu lafiya? ALLAH yasa hakan ameen.........

In masu karatu zasu tina mun tsaya in da dady ya d'aura auran zahra da mashkhur kuma ya tirsasasu akan

Please Login or Register in order to submit comment