Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daga haka ahmad ya katse wayar, dirtiest ya wuce gida sabida yau basu da lectures su mashkhur ne suke da lectures kawai da yake shi mashkhur d'an science ne shi kuna Ahmad d'an art.

Zahra tana shiga harabar makarantar tajiyo sautin ihu tana dagowa taga classmate dinta sun tawo da gudu sun rugume ta, daya daga cikin su ce welcome my friends we seens looking for your coming 😊, zahra ta jiyo wajen ta cikin fara'a tace ohhh sorry dear sukai hugging din juna baturiyar ta sakar mata kiss πŸ’‹, tace let's go our class room suka rankaya zuwa class, kafin su qarasa ajin zarah taga ikon Allah dan kowa kallon ta yake yara da manya, abun har dariya yake bata abun dai se wanda ya gani, niko amina bayero nace wa yaga ba sabon baπŸ˜†.

Nan ta qara sakin wani murmushi a zuciya tace yara ai kune abin kallo dan samun kalar ku a Nigeria se an tona ......
ga mamakin zahra suna shiga class d'in su se taga classmate dinta na jiya da su kai ta sha mata qamshi yau sune har da tasowa da sauri suna yiwa zahra welcome , wani lallausan murmushi ta sakar musu itama tare da cewa welcome too my friends how was your night, hk dai suka gaisa ta tafi sit dinta ta zauna.

Yaufa zahra ba laifi ta gane karatu sosai da yake an bata littafin da kuma laptop. Kuma ba laifi yau class meant d'in ta sun sakar mata fuska sosai ba kamar jiya ba, yanzu kowa a ajin yana kulata, kuma duk abinda zahra bata ganeba suna qara yi mata bayani.
Yau tun kafin a tashi yaya ahmad yazo domin d'aukar zahra, dan haka ana tashi ba 6ata lokaci ya d'auke ta suka kama hanyar gida.

Har lokacin Ahmad bai dai na ganin kamar zahra da mamansa ba, amma kawai dai ya danne ne. Ahmad yana sauke zahra ta hau sama ta fara kwankwasa qofar, tayi rabin a wa a zaune amma ina qofar a rufe, zama tayi a wajan tana tinanin taya zatayi sallah? Kuma sam bataso ta shiga part d'in ahmad, ko bata da aure bazata iya shiga ta zauna ba barema tana matar aure. Tana cikin saqa da warwara ta hangi motar mashkhur ta shigo gidan a guje sai a lokacin ta tina ashe ya tafi school.

Yaufa anci sa'a ba madam zee akazo gidan, shi ka d'ai ne abinsa, fuska a murtike mashkhur ya hawo kan step d'in benan, yana hawa ya watsawa zahra wata uwar harara, zahra tana ganin haka gabanta ya fad'i sabida taga harrar yau tafi ta ko da yaushe. A zuciye ya bud'e qofar falon ya shige, zahra kuwa a tsorace itama tabi bayan sa. Mashkhur kuwa zahra tana shigowa, ya rufo qafar gamm, zahra kuwa ra6ewa tai a bango jiki sai rawa yake. A zuciye mashkhur ya juyo yana bin zahra da wani razanan nan kallo.

Nan ma hankalin zahra qara tashi yayi gumi ya fara geto mata a zuciye zahra taga mashkhur ya nufota gadan-gadan. Ja da baya zahra ta farayi har sai da tazo qarshan bango jikita sai fama rawa yake. Shima mashkhur d'in qure zahra yayi a bango tare da kaiwa fuskarta damqa, sosai mashkhur ya matse fuskar zahra yana wani fitar da wani irin wuci mai zafi, zahra kuwa sam kukanma ta kasa, hankalinta yayi mugun tashi, murya a dake taji mashkhur yace kee wai 'yar iska mara kamin kai koh?.

Shiru zahra tai ta fara zazzaro idan dama ya riqe mata fuska ya matse mata baki bama zata iya magana ba, hanunsa guda biyu yasa yayi mata runfa yarda baza ta6a iya guduwa ba. Cikin 6acin rai mashkhur yace, mene had'in ki da abokina Ahmad? Shiru zahra tai dan batama da amsar da zata bawa mashkhur dan tasan ko ta gaya mai gaskiya ba yarda zai ba. nace miki mene had'in ki da Ahmad da yake ta6a miki fuska?. Jiki na rawa zahra tace ba!! Ba!! Bako maimai! Kawai dai bigewa nai a goshina, shi yasa ya milmila min amma wlh ba wani abu a tsakanin......

Tun kafun ta qarasa maganar mashkhur yasa hannu yaja le6anta da qarfin gaske tare da cewa so kike yarda rayuwa ta lalace ADALILINKI shima tashi ta lallace koh? Zahra kuwa sakin kuka tai sabida tsabar azabar da takeji. Murya a dake mashkhur yace ni nasan halin abokina bazai ta6a abinda bai dace ba, amma nasan ke shu'umace zaki iya aikata komai? To bari kiji wlh ki kama kan dan bazakije ki jajamin masifa ba, wani abun ya shiga tsakanin ku dady yace bazan sake kiba.

Wani baqin ciki ne ya sake tur nike zuciyar zahra, yanda taji mashkhur yana jifanta da miyagun magagganu. Sake matse leban zahra mashkhur yayi tare da cewa nina san ba ammi ce ta koya miki hakan ba, dan kinga ba a gaba idanta bane kike wanan iskanci ko? To wallahi zan miki kashedi na qarshe!! Daga yau ko kallan wani kika sakeyi sai jikinki ya gaya miki, ki bari duk sanda na sake ki saki UKU sai kiyi duk abinda kikeso, dan bazan ta6a iya cigaba da zama da ke a matsayin mata ba, sabida NATSANEKI, ke daga yau ma karki sake tunanin cewa wai ni MIJINKI ne..................


ADALILINTA πŸ’œβ€πŸ’œ

BY AMINA BAYERO πŸ’œβ€πŸ’œ

MY NUMBER 09162226240.


Typing............

*page 61*

To wallahi zan miki kashedi na qarshe!! Daga yau ko kallan wani kika sakeyi sai jikinki ya gaya miki, ki bari duk sanda na sake ki saki UKU sai kiyi duk abinda kikeso, dan bazan ta6a iya cigaba da zama da ke a matsayin mata ba, sabida NATSANEKI, ke daga yau ma karki sake tunanin cewa wai ni MIJINKI ne..................

Wata irin azaba zahra takeji har kwakwalwarta, dan sosai mashkhur ya riqe mata le6an na qasa, mashkhur kuwa goshin zahra ya zubawa ido dan ya tabbatar da Gaskiyar zancan nata. Ba laifi yaga goshin nata ya dan kubira kadan harma yayi ja, qara jan bakin nata mashkhur yayi tare cewa ai duk wani taku naki ina sane da ke sai ki ringa fita da sassafe waje tunma kafin ya fito kai ki makarantar salan ace ina takura miki ko? To wlh daga yau kika sake kika qara fita waje in dai bashi yazo yace ki futoba sai na karya mike qafa BANZA wawiya kawai mara hankali da tinanin, wlh bana QAUNARKI a rayuwata.

Ya qarasa maganar tare da sakin bakin zahra ya wuce bedroom room d'ina sa a fusace, Allah sarki zahra nan ta durqushe ta fashe da wani gigitaccan kuka, ga munanan magagganun da yaya mashkhur ya jefeta da su, ga kuma le6anta da yake mata mugun zafi. Zahra tafi minti goma anan tana kukan nan mai ta6a zuciyar mai saurare, can kuma ta miqe da kyar ta sunkuci jakarta ta wuce d'akin. Tana shiga ta fada kan bed ta qara sakin wani saban kukan.

Sai da zahra tai wajan 20 minit Tana kukan nan mai cike da baqin ciki, sanan ta tashi ta shiga toilet, alwala ta d'auro sanan ta zira dogwan hijab d'in ta ta fara gabatar da sallar azahar, in dai zahra ta kifa kanta sai ta kai wa Allah qarar yaya mashkhur akan ya bi mata haqqin ta. Tana idar da sallah bayan ta gama lazimi hijab din ta cire sanan ta nufi kujerar merro ta zauna, tare da tsurawa fuskarta ido. Le6an nan nata na qasa yayi jajir ya kunbura, ga wani irin azabar zugi da yake mata, tagumin zahra ta rafka tana tunanin yaya makomarta zata kasance?.

Can kuma ta miqe saka makwan wani zazzafi da ciwan kai daya rufeta. Da kyar ta iya canza kayan makarantar zuwa doguwar riga, daga haka tabi lafiyar gado tai kwanciyar ta. Sam zahra batajin yunwa dan ko sha'awar abincima bataji, kawai magaganun yaya mashkhur ne suke dawo mata kai, haka dai tai ta juye-juye akan bed, nan da nan zahra taji wata sabuwar muguwar tsanar yaya mashkhur ta lulu6a ta, sam yanzu ko fuskarsa batasan gani yarda ya tsaneta itama haka ta tsane shi, amma gaskiya dai tsanar mashkhur tafi ta zahra yawa, sabida shi mashkhur koh tausayi zahra bata ta6a bashi ba, sai sau biyu, ranar da hjy kaka tazo da ita tana jaririya, da kuma ranar daya qulleta a windo. A haka dai bacci mai nauyi yayi awan gaba da zahra.

MASHKHUR.............

Rai a 6ace mashkhur ya shige bedroom d'in shi, yana shiga ya qure A. C bedroom d'in sosai, tare da cire rigar jikinsa, I ko da ya cire rigar jikin nasa bai ji dai-dai ba sai da ya had'a da wanda duk ya cire ya koma daga shi sai three kwata, duk sanyi da ake a garin amma mashkhur zafi kawai yake ji, wani irin baqin cike ne yake damunsa, musamman in ya tuno yarda yaga zahra da ahmad, a halin daya gansu d'azu. Bakomai ne yake jefa mashkhur cikin baqin cikin nan ba, face ace wai matar sace da wani namijin can a waje.

Afii mashkhur yace!! Gaskiya dady kuncuceni yanzu a haka kuke cewa wanan ce matata yarinyar da ko ciwan kanta bata gama sani ba, wai a hakan kuka auramin ita? Sam wlh an cuceni. Can qasan zuciyar sa mashkhur yana baqin cikin cewa wai matar sace zahra, aganin mashkhur yau da matar da yake mutuwar sone ya ganta da wani can daban to wlh da sai ya kusan kashe kawai dai dan baya qaunar zahra kwata-kwata. Bawai dan mashkhur yana kishin zahra ba yayi hakan aa shide a tinaninsa ba kishi bane kawai, sabida komin banza da auran sa akanta shine kawai.

Jiki ba kwari mashkhur ya shiga toilet domin yin wanka, ko da ya shiga sam ji yayi baya buqatar ruwan zafi, dan haka da ruwan sanyi yafara wanka, duk da kuwa mugun sanyi da akayi a garin. Yana gama wanka ya d'oro towel ya fito, sai a lokacin mashkhur yaji sanyi ya fara ratsa sasan jikinsa, nan da nan wata mura mai zafi ta kama shi, wardrobe ya bud'e ya kwaso kayansa, sanan ya zira, yana gama zirawa ya nufi falon, yana zuwa falo kai tsaye ya nufi firij.

Maganin mura ya d'akko guda d'aya tare coca cola, bayan ya dakko rufe firij d'in yayi, sanan ya nufi kicin, yana shiga ya d'auki cup sanan ya wuce bedroom d'in shi. Yana shiga ya haye kan bed sanan ya bud'e jarkar coca cola, bayan ya bud'e zubawa yayi a cup, sanan ya fara sha, sha uku yayiwa coca cola ya gama da shi da yake ba da yawa ya zuba a cup d'in ba. Bayan ya gama sha, bud'e totalin d'in yayi, ya juye shi a robar coca cola d'in, sanan ya jijiga, bayan ya ga jijigawa a hankula ya bud'e dan karya zube, yana bud'ewa ya kafa jarkar a bakinsa, bashi ya sauke taba sai da ya shanye kaf.

Yana shanyewa ya miqe ya nufi qaramar drowar gefan gado ya bud'e. wasu fararan kwayoyo ya d'ago a cikin wata ma dai-dai ciyar roba, yana cirowa ya bud'e robar ya d'ibi guda biyu, ya watsa a bakinsa, sanan ya kora da ruwa. Yana gama sha ya mayar da robar kwayoyin qaramar drowar, sanan ya dawo kan bed ya kwanta tare da lulu6e jikinsa da bargwansa mai laushi da qamshi. Nan da nan jikin mashkhur ya mutu sam yama dai na ganin komai dishi-dishi kawai yake gani, ga wani nanauyan bacci da yake ji, ko 3 minutes mashkhur bai qara ba a wanan halin bacci mai nauyi yayi awan gana da shi. Hmm nikuwa amina bayero nace ALLAH ya shiryeka mashkhur, yasa asiri da sammun da yake jikinya ya fita, allahumma amen.

ZAHRA..............

Zahra tinda ta kwanta ba ita ta tashiba sai hud'u na yamma lokacin ana kiran sallah la'sar. Jiki ba kwari ta miqe, ga wani zugi da le6anta yake mat. Tana miqe ta hango yarda le6anta ya kunbura suntum, ta mudubi gashi yayi wani, kawar da kanta tai daga kallom merron ta wuce toilet ta d'auro alwala, sanan ta futo tai sallah. Bayan ta idar da sallah wata yunwa ta faraji , sai yanzu ta tina da abincin, dan rabanta da abinci tunna safe da taci.

Hijab d'in ta cire sanan ta nufi hanyar fita falon dan ita yanzu ta dai na wani tsoran muguntar mashkhur, dan harma ta fara saba da zalincinsa, amma dai duk da hakan tana bala'in tsoran yaya mashkhur. Tana fita fallo kicin ta nufa, tana shiga ta fara qoqarin dafa jalof d'in taliya da kifi, dududu batafi 30 mints ta gama abincin ba, tana gamawa ta zuba a plate, sanan ta koma fallo, ta bud'e firij tana bud'ewa kamar kullum taci karo da kwalaban magungunan shaye-shayen mashkhur, kawar da kai tayi daka kan kwalaban tare da d'aukar lemon da ruwa.

Tana d'auka ta rufe firij d'in sanan ta nufi kan draining ta d'auki plate d'in abincinta ta wuce bedroom d'in ta. Tana shiga ba 6ata lokaci ta fara cin abincin ta, abinci yayiwa zahra dad'i sosai, amma sai dai da qyar take iyaci saka makwan, le6an ta da ya kunbura yake mata ciwo sosai. Haka dai zahra ta daure ta cigaba da cin abincin ta harta cinye tass, sanan ta kora da lemanta mai sanyi, bayan ta sha leman ta qara da ruwa. Daga haka ta fitar da plate d'in ta mayar kicin, zahra bata futo daga kicin d'in ba sai da tai wanke-wanke sanan ta gyara kicin d'in fass.

Tana futowa ta hau gyaran falo, sai da zahra ta gyara fallon tass ta goge komai sanan ta faisa mai air freshener, wajan sai qamshi yake kwanin dad'i. Zahra tana san kunna tv tayi kallo amma tana tsoran kar yaya mashkhur ya futo ya sameta ta jawowa kanta wata sabuwar muguntar da bata shirya ba dan haka ba 6ata lokaci ta koma bedroom d'in ta shima ta fara gyara shi, bayan ta gama toilet ta shiga ta had'a ruwan zafi mai d'imi, sanan ta gasa bakinta bayan ta gasa bakinta tai wanka sanan ta d'auro towel ta futo.

Wani irin mugun sanyi zahra takeji duk da kuwa A. C ba akunne take ba kuma glass d'in ventilation d'in ta a kulle yake. Wardrobe ta b'ude ta dakko kayan ta tasa sanan ta dora rigar sanyi akai, bayan ta gama shiryawa qur'ani ta dakko tafara maraji'a. Sai da zahra ta karanta izu biyu dan har sai da aka fara kiran sallar magriba sanan ta idar da karatun, ta d'auro alwala tai sallah, bayan ta idar da sallah ta cigaba da karatun qur'ani.

Haka zahra tai ta karatu har isha'i tayi, lokacin sallah isha'i yanayi zahra tayi sallar ta sanan tasha maganin rage zugi da kunburi, tana sha tabi lafiyar gado ta kwanta tare da rufe jikinta da bargo mai kauri da laushi, tai kwanciyar lamo ta fara tinane-tinane kamar kullum har bacci yayi awan gana da ita.........

MASHKHUR..........

tinda mashkhur ya kwanta ba shi ya tashi ba sai misalin qarfe takwas lokacin ana kiran sallah isha'i. Lokacin da mashkhur ya tashi shi duk a tinanin sa kiran sallar la'asar ake da yake duk window da ventilation d'in bedroom d'in a rufe suke kuma ga labile ga light blue d'in glob in ka shiga bedroom bazaka ta6a tinanin qarfe nawa ba, dare ne ko kuwa safiya ce?. Jiki ba kwari ya jawo wayarsa kiran zee ne ya fara gani akan screen d'in wayar, wani siriri tsaki mashkhur yaja tare da zuba idonsa akan time d'in wayar.

Ai gaban mashkhur ne ya fad'i rass ganin qarfe takwas na dare shi duk a tinanin shi, kiran sallar la'asar akeyi ashe na isha'i akeyi. Hankalin mashkhur ya tashi sosai da sosai, ba komai ne ya tayar mai da hankali ba face salolin da suka wuce shi. Astagfirullah!! Kawai mashkhur yake firtawa, a hanzarce ya yaye bargon daya lulu6a da shi sanan ya sauka daga kan gado. Mashkhur bai tsaya ko ina ba sai toilet da sauri ya d'ora alwala sanan ya futo ya fara gabatar da salolin da ake binsa, bayan ya idar da salolin da ake binsa sanan ya fara gabatar da ta isha'i.

Bayan mashkhur ya idar yayi lazimin, istigfari ya farayi, akan rashin sallar da baiyi da wuri ba, sam mashkhur bayajin dad'in zuciyar sa, sabida sam bayaso sallah ta wuce shi, duk abinda mashkhur yake sam baya wasa da sallah, kuma baya qaunar sallah ta wuce shi, sabida yasan ALLAH gaba da komai yake. Dama haka 'yayan ammi suke sam basa wasa da sallah kwata-kwata, in kuwa basuyita akan lokaci ba kuwa! hankalinsu zai yi mugun tashi musamman yaya mashkhur da zahra da kuma ilham. Hmm dama haka akeso ba'asan musulmi ya ringa wasa da sallah anaso ya ringa yinta akan lokaci dan Allah 'yan uwana musulmai mu kula mu kiyaye. πŸ™

Rai ba dad'i mashkhur ya miqe ya fice daga bedroom d'in, shi ya koma falo. Yana zuwa ya zauna akan sofa tare da rabka uban tagumi, tinani mashkhur ya tafiyi! mashkhur dai harga ALLAH yanason dena shaye-shayen nan amma ya kasa gaba d'aya. Wani baqin cikine ya sake turniqe shi, sam mashkhur ya rasa sabida mai ya kasa dai na shaye-shayen nan! Sometime mashkhur yanaso ya dai na amma ya kasa, wata ranama har dai nawa yake bayan kwana biyu kuma sai yaji in bai shaba kamar zai mutu.

Mashkhur ya tsani shaye-shayen nan duk abinda zai shiga tsakanin shi da uban gijinsa, sam baya son shi ko mene zai iya dainawa, amma sai dai gashi kash ya kasa hakan. ya salam! Abinda mashkhur ya furta a fili kenan, sam ya kasa gane lamarin nan shi da in dai ya tsani abu komin kyansa da dad'in sa ya barshi, amma sai gashi yau ya kasa barin shaye-shaye nan? Shi abin ma har tsoro yake bashi wataran, yana cikin duniyar tinanini yaji ana knocking d'in qofar fallon.

Shiru mashkhur yayi yana sauraran knocking d'in kamar bazai miqe ba. Can kuma ya d'aure ya nufi hanyar bud'e qofar, jiki ba kwari mashkhur ya bud'e qofar, Ahmad ya gani tsaye a bakin qofar. Kallo d'aya mashkhur yayi Ahmad sanan ya d'auke kansa ya wuce ya bar Ahmad tsaye a bakin qofar. Ahmad kuwa shigowa yayi tare da rufo qafar, dreck Ahmad wajan mashkhur ya nufa, ya zauna akan sofa kusa da mashkhur d'in.

Daga mashkhur d'in har Ahmad d'in ba wanda yace qala sun d'auki minti goma a hakan. Can Ahmad daya gaji da shirun yace mashkhur lafiya kuwa? Shiru mashkhur yayi can kuma yace mai ka gani? Naga kamar wani abu yana damun ka ne shiyasa na tambaye ka. Girgiza kai mashkhur yayi tare da cewa I'm ok, shiru Ahmad yayi bai sake cewa komai ba. Can kuma yace mashkhur dama zuwa nayi wajanka sabida na roqi gafa a wajan ka.
Cikin rashin fahimtar maganar Ahmad mashkhur yace gafara kuma tame?.

Gyara zama Ahmad yayi tare da cewa ahhh dama!! uhhh!! amm!! D'agowa mashkhur yayi ya stare Ahmad da manya idonunsa, tare da cewa lpy naga kana kakarewa? Da sauri Ahmad ya girgiza kai tare da cewa!! Aaa ba kakarewa nake ba, dama akan abinda ya faru d'azu tsakanina da matar ka zahra ne akan!! No Ahmad pls bana buqatar wanan maganar, mashkhur ya katse Ahmad.

Shima ahmad d'in katse mashkhur yayi da no mashkhur zahra matar kace, dole in yima bayani sabida zuciya bata da qashi ko nine naga wani da matata a wanan yanayin to dole zan zargi wani abun. Shiru mashkhur yayi tare da kawar da kansa gefe, sam bayasan yana cikin wata damuwar a qara jefa shi cikin wata shi yasa yayi qoqari katse Ahmad amma Ahmad yakasa gane hakan.

Cigaba da magana Ahmad yayi da cewa!! Dazu garin sakkowa daga bene ne, ta bige a goshinta, hakane yasa nace sai na milmila mata. Dan ni a matsayin qanwata na d'auke ta, Ina cikin mulmula mata ne ka sauko, sai daga qarshe kuma nayi tinanin abin da nayi bai dacewa dan Allah ina roqan gafara akan hakan, sam zahra bata da lefe ko kad'an, nine mai laifin. Shiru mashkhur yayi bai ce komai ba, Ahmad kuwa qara cewa yayi pls mashkhur wlh hakan bazata sake faruwa ba. Da qyar mashkhur yace it's okay Ahmad na yarda da kai sosai kuma nasan bazaka ta6a ai kata abinda bai dace ba............

Daga yau na dena yi muku posting da safe sai da daddare zan d'inga yai muku kamar dai yarda nake muku da can baya. Inayi muku fatan alkhairi, ALLAH yabar qauna, Amen.


ADALILINTA πŸ’œβ€πŸ’œ

BY AMINA BAYEROπŸ’œβ€πŸ’œ

MY NUMBER 09162226240.


Typing............

*page 62*

Shiru mashkhur yayi bai ce komai ba, Ahmad kuwa qara cewa yayi pls mashkhur wlh hakan bazata sake faruwa ba. Da qyar mashkhur yace it's okay Ahmad na yarda da kai sosai kuma nasan bazaka ta6a ai kata abinda bai dace ba............

Murmushi Ahmad yayi tare da cewa tom abokina nagode sosai da shedar arziki, sai kuma abu na gaba. Cikin qosawa mashkhur ya d'ago tare da cewa menene kuma? Ah mai da wuqar kawai dai so nake na qara tinatar da kai kamar kullum, shiru mashkhur yayi domin jin mai Ahmad zai ce. Kallan mashkhur Ahmad yayi tare da cewa ni dai mashkhur bazan gaji da gayama ka rabu da yarin yarnan zee ba, wai mashkhur sabida da mai ka kasa fahimtar a matsayinka na mai basiri, wlh yarinyar nan kawai lalatama rayuwa takeso tayi, wannan ba qawar arziki bace.

Lumshe ido mashkhur yayi tare da cewa kwarai Ahmad na sani, amma sam bata da laifi nine nake da laifi dana kasa dai na wasu halayya irin nata. Girgiza kai Ahmad yayi tare cewa! Wai mashkhur sabida mai bazaka iya rabuwa da garinyar nan ba? Ya kamata fa

Please Login or Register in order to submit comment