Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaskiya ALLAH yana sona,  ya qarasa magana yana kashe mata ido d'aya.  Zaro ido waje ilham tai sanan tace!  Lalai ma to ni bani da watsu almatsutsai kaje can ka nemo 'yar uwarka mai almatsutsai ka aura ba dai niba ta qarasa maganar tana zaro mai ido kamar zata kai mai duka.

Lumshe ido sa ahmad yayi sabida hakan da ilham tai ba qaramin kyau ta mai ba,  cikin murya mai dad'i yace hmm pretty na kenan wlh shiyasa nake qara qaunarki,  yanzu dan ALLAH mubar wanan fad'an muyi hira masoya mai dad'i kinji ya qarasa maganar yana zuba mata kyawawan idanuwan sa biyu.  Ajiyar zuciya ilham ta sauke har cikin ranta take qara jin qaunar ahmad d'in a fili kuma cewa tai,  naqi d'in sai da ka gama cimin mutunci wai mai almatsutsai sanan zakace muyi hirar soyayay to bazan yi ba ta qarasa maganar tana sakar mai harara.

Nan da nan ahmad ya ta da hankalinsa murya na rawa yace haba my pretty dan ALLAH kiyi haquri, wlh wasa nake miki,  kece d'in kina da abin mamaki,  wai sai mun gama fahimtar junan mu kwatsam sai ki had'e rai kamar ba kece ba,  wlh hakan yana d'agamin hankali pretty.  Dan Allah dan annabi kiyi haquri, daga yau na dena yi miki abinda bakyaso ni dai burina ki dena had'e min rai kinji.  Ahmad ya qarasa maganar fuskarsa babu annuri abin tausayi,  ilham kuwa ji take kamar ta fad'a jikin ahmad ta rarashe shi amma ina ba hali dan ko yana kusa da ita bazata iya haramcin nan ba barema basa kusa.

Murya a sanyaye ilham tace,  haba my future husband kai ma kasan ina qaunar ka sosai bazan so abinda zai cutar min da kai ba,  tinda baka so na dena kayi haquri ta qarasa maganar fuska cike da tausayin masoyin nata.  Ajiyar zuciya ahmad yayi tare da cewa! Tom shikenan ni yanzu burina kawai naga kinyi murmushi shine kawai abinda nake buqata a halin yanzu.  Ahmad yana kai aya ilham ta saki wani qayataccan murmushi mai kashe zuciyar masoyi.

nan da nan ilham ta sake kashewa ahmad zuciya da qasai taccan murmushi nan nata,  shima ba 6ata lokacu ya sakar mata nasa murmushi yana cewa!  Wow my pretty kinga yadda murmushi nan yayi miki kyau kuwa?  Kai ALLAH ya mallakamin ke my pretty,  dan Allah zaki aure ni?  Murmushi Ilham ta sake saki sanan tace hmm nima ban sani ba tukunna ka tambayi dady ko abokinka yaya mashkhur in sun baka ni ai sai a d'aura ta qarasa maganar tana rufe fuskarta alamun kunya.................



Tofah ranar ilham da ahmad sun sha soyayya yadda masu karatun littafin ADALILINTA basu ta6a zatofa,  dan sai da sukayi wajan awa uku suna shan soyayya,  sai da suka qara sace zuciyoyin junan su sosai, sanan sukayi sallama,  sallamar ma badan sun ran su ba. Ahmad kuwa nan da nan yaji jikinsa ya qara kwari sosai da sosai,  ji yayi ba abindda yake damunsa a zuciyar shi ba kamar da ba,.  6angar ilham ma ranar cikin farin ciki ta kwana ta wuni,  komai in zatai da qarfinta take........

Tofa yau kimanin wata d'aya da barin su dady rasha,  kuma abubuwa da dama sun fara canzawa,  musamman ma ta 6angar zahra yanzu ta dena fuskanta aikin da zee take sata ko kallan banza zee bafayiwa zahra,.  6angar mashkhur kuwa shima sam ya dena zalintar zahra dan yanzu ko kallo zahra bata ishe shi ba duk kuwa abinda zatai a cikin gidan.  Itama zahra taji dad'i sosai sabida ta fara samun sakewa har kallo yanzu tana yi a gidan, ga shi kullum sai sunyi chat da 'yan uwanta,  wataran ma har video call sunayi.

Babban burin mashkhur shine yaga ya dena munanan d'abi unsa,  ko ya samu ya rabu da abar tsanar shi zahra kullum yana qoqarin dena shaye-shayen ya mayar da hankalinsa akan karatu amma ina abu ya faskara,  abu Kamar almara sai ma qaruwa yake.  Watarana mashkhur in yana jin yunwa da daddare in ya tashi yaga ragowar abincin zahra yana ci ba laifi.  Zahra kuwa data lura da hakan sai ta fara tofa mai addu'o'i acikin abinci,  wataran na ma musamman sabida shi take dafa abinci da ruwan addu'o'i ta zuba a bilas sabida yaci.

Kai tun mashkhur yana bin dare sabida ya ci abinci zahra harma ya dena bi,  wata ranama tana gama abinci kafin taci shi zai fara zubawa yaci.  Amma abin mamaki shine har yau tsanar zahra a zuciyar mashkhur bata fita ba kwata-kwata.  Zahra kuwa abinda yake damunta shine kullum a cikin yiwa yaya mashkhur addu'a take amma yaqi ya shiryu.  Kusan duk qarshan sati sai hajiya kaka tasa ilham ta turowa zahra addu'o'i da zahra zata ringa yiwa mashkhur.

Sam zahra bata wasa da addu'o'in da ake bata kullum in ta dungura goshenta yimai take bawai dan tana san shiba,  aa kwai sabida tayiwa hjy kaka abinda take so,  sanan tasan ko ba komai zata sa iyayanta farin ciki in ya shiryu,  wato ammi da dady.   Kullum burin mashkhur da zahra iri d'ayane wato su rabu da junansu,  sabida sam basa qaunar junan su,  dan zahra har addu'a take akan ALLAH ya raba auranta da yaya mashkhur,  ya aura mata yaya abdul, dan yanzu ita yaya abdul take son ta aura. ............

6angar ilham da ahmad kuwa abin ba'a cewa komai, dan soyayyar su ta sake qarfi sosai har ta kai ta kawo in basuyi video call ba sam basa samun sukuni,  da ilham, taga ammi tafara qoqari gano wani abu game da soyayyar da yaya ahmad,  ba shiri ilham ta koma part d'in hjy kaka da zama,  sam ba wanda yasan komai game da soyayyar ilham da ahmad, sai zahra da hjy kaka,  itama hajiya kaka sai da ilham tai roqeta akan karta gayawa dady ko ammi,.  Dama Hjy kaka haka takeso taji dad'in soyayar Ilham da ahmad dan ita dama ta fiso a aurar da su ilham batasan karatun nan mai tsayi,  shi yasa take farin ciki da hakan,  kuma take rufawa ilham asiri, tare da goya mata baya..............

Ina godiya ga masoyana,  masu nuna kulawarsu gareni da masu yimin ya jiki,  ina godiya.  Kuma ina farin cikin sanar da ku na samu lpy in sha ALLAH,  zanyi iya qoqarina wajan yi muku typing,  dan ina tinanin a cikin wanan wata mai shigowa zan kammala rubuta littafin ADALILINTA.

Ku biyoni a next page......


ADALILINTA💜❤💜

BY AMMINA BAYERO💜❤💜

                                  *page 76*

                                   Typing..........

Dama Hjy kaka haka takeso  taji dad'in soyayar Ilham damana,  ad dan ita dama ta fiso a aurar da su ilham batasan karatun nan mai tsayi,  shi yasa take farin ciki da hakan,  kuma take rufawa ilham asiri,  tare da goya mata baya..............

Tom haka rayuwa tai ta juwaya,  komai yana shud'ewa.  6angar yaya abdul kuwa kullum burinsa guda yaya mashkhur da zahra su dawo a raba auran shi kuma ya auri zahra sabida har ga ALLAH yaya abdul yana son zahra fiye da tinanin mai tinani.   6angan ahmad da ilham kuwa sun fahimci junan su soyayya suke mai stafta,  sam basa fad'awa junan su kalaman da basu dace ba,  sanan suna ganin mutunci junansu suna girmama junan su.  6angar mashkhur da zahra kuwa wani zama suke na ko in kula  ko kallo basu ishi junan suba musamman ma mashkhur da ya dad'e bai dora idansa akan zahra ba..........

7 monthly litter.

Bayan wata bakwai.

Tofa a cikin wanan watannin abubuwa da dama sun faru masu dad'i da marasa dad'i,  amma 6angar mashkhur da zahra ba abinda ya canza game da rayuwar su tana nan yadda kuke tinani.
Haka nan mashkhur yau yaji jikinsa yana mutuwa,  sam ya rasa mai yake damunsa haka nan yaji baya jin dad'i zaman garin yau.  Yana kwance akan gado yana juyi nan da nan ya fara tinani wai yaushe zasu komai Nigeria a raba auran nan nasa da zahra?.

Gaban mashkhur ne ya fad'i rass-rass sakamakwan  tinawa da yayi yanzu sunyi shekara d'aya har da wata uku a rasha,  nan da nan ya fara tinanin to saura wata nawa su koma?  Da sauri mashkhur ya fara tinanin saura watanni nawa su koma kenan?  Ai mashkhur yana gama lissafin nan ya zabura ya miqe tare da furta innalilahiwa'inalilahirraji'un.  Ba komai ne ya tayarwa da mashkhur hankali ba face yanzu saura wata hud'u su komai,  rasha bai gyara halin saba.

Kenan baza'a raba aurena da zahra ba?  Mashkhur ya watsawa kansa tabbayar?,  da sauri mashkhur ya girgiza kansa tare da furtaa no impossible wlh,  bazan ta 6a yadda na cigaba da zama da wanan kucakar yarinyar a matsayin matata ba. Wata nanauyar ajiyar zuciya mashkhur ya sauke,  can qasan zuciyar shi yaji tana cewa ai kuwa in baka gyara halinka ba tofah ya zama dole zahra ta cigaba da zama matar ka ta muddin rai.  Da sauri mashkhur ya girgiza kai a fili ya fara cewa wlh zan gyara wlh zan gyara,  kamar wani zautacce.

Haba mashkhur ka nutsu mana ka nemawa kanka mafita,  sai kace ba namiji ba,  namijin ma mashkhur,  cool down mana,  duk zuciyar mashkhur ce take gaya mai hakan.  A firgice mashkhur ya miqe ya fice daga falo,  sabida tsabar tashin hankali ko riga babu ajikinsa ya fuce.  Lokacin daya fita zahra tana zaune akan sofa tana kallon tv hankalinta kwance,  yadda taji mashkhur ya rufe firinji da qarfine yasa ta juyo ta kalle shi,  zahra tana kallansa gabanta ya yanke yayi mugun fad'uwa rass-rass-rass har sau uku.

Da sauri ta kawar da kanta daga kallonsa ta mayar da idanuwanta kan tv,  nunfashinta har wani d'aukewa yake saka makwan yanayin da taga mashkhur a ciki,  ba riga wanddan ma 3 kwata ne bai qarasa sauka ba,  jinjina kai zahra tai tana mamakin dama haka jikin yaya mashkhur d'in yake?,  nan da nan tsoro ya kama zahra, ganin jiki yaya mashkhur kamar na wasu 'yan dambe ga faffad'an qirji,  Kai jikin nasa dai kamar na jarumai komai yaji.

6angar mashkhur kuwa sam bai masan da wata halitta zahra a wajan ba,  yana d'aukar ruwansa ya shige bedroom.  Nan da nan jikin zahra yayi sanyi sai rawa-rawa yake,  dan tinda zahra take bata ta6a ganin wani namijin babba ba  a haka ba sai yau,  lalai a she riga tana rufawa mutun asirin jikinsa zahra ta watsawa kanta tambayar?,  amma ina ba amsa,  kawar da zancan zahra tai tamai da idanta kan tv domin cigaba da kallo,.  Aa abu kamar wasa zahra ta kasa kallan,  ba abinda take gani a tv sai  yaya mashkhur ba riga,  kamar dai yadda ta ganshi yanzu.

Ba shiri zahra ta kashe tv ta komai bedroom d'in ta,  dama da yake wajan goman dare ne lokacin.  Tana shiga ta haye kan bed ta shige bargo ta runtse idanta gam.  Amma ina har yanzu bata dena ganin yaya mashkhur a wanan yanayin ba,  nan da nan zahra ta rud'e baki na rawa ta fara karanta addu'o'i kala-kala kamar wanda tai tozali da wanda ba maharraminta ba.  Zahra kuwa ji take kamar  ta aikata mummunan haramci duk tabi ta rud'e,  tun zahra  tana sanin wata addu'a take harma ta dena sanin mai take fad'a addu'o'i ta ringayi barka tai har bacci mai nauyi ya kwashe ta.

6angar mashkhur kuwa yana shiga bedroom d'in ya zauna akan bed ya fara qoqarin bud'e robar ruwa,  ruwan yana da sanyi sosai har tiriri yakeyi,  dan harma ya kusan fara qanqara.  Mashkhur yana bud'e jarkar ruwan bai wani tsaya zubawa a cup ba ya kafa a bakin sa.  Tinda mashkhur ya kafa jarkar a baki bai sauke ba sai da ya shanye ruwan tass duk da kuwa mugun sanyi ruwan.  Yana ajiye jarkar ya saki nanauyar ajiyar zuciya, tare da dafe kansa da hanuwansa biyu.

Lumshe ido mashkhur yayi tare da tambayar kansa taya zai magance matsalolin nan kuma mai dady yake so yayi?.  Na dena shaye-shaye na rabu da zee kuma na futo sa result mai kyau a school, mashkhur ya bawa kansa amsa.  Tinani mashkhur ya farayi saura kwana nawa suyi final exam d'in su?  Jim mashkhur yayi can kuma yace remain 3 month,  jinjina kai mashkhur yayi yana nazarin taya zai fara shawo matsalar nan,  sai da mashkhur, ya d'au awa d'aya yana tinani,  kuma daga qarshe ya gama yanke shawarar yadda zai shawo kan lamarin............

Tofah a 'yan kwanakin nan mashkhur ya dena fashin zuwa makaranta kullum sai yaje,  ga mugun karatun dayasa a gabansa.  Yanzu duk kayan shaye-shayen nan mashkhur ya rage ta ammali dasu,  a sati bai fi yasha sau d'aya ba in yayi yawa sau biyu,  shima yaso ya dena gaba d'aya amma in ya dad'e bai shaba sai yaji kamar zai mutu,  duk duniyar tai mai zafi.  Zee ma yanzu mashkhur ya hanata zuwa gidan sosai, a sati bai fi tazo sau biyu ba.  Ba laifi mashkhur ya nutsu ba kamar da ba,  yanzu ko makara bayayi bare ma fashi.

Duk karatu da ya wuce mashkhur,  mashkhur sai da yabi ya karanta,  yanzu yamai da hankalinsa sosai ta fanin karatu ya zama good student,  kamar dai da,  amma har yanzu mashkhur bai dena kula zee ba,  kuma bai dena shaye-shayen ba,  amma dai shaye-shayen da sauqi ba kamar da ba.
   6angar zahra kuwa itama tana karatun ta ba laifi gashi sai wani kyau take qarayi da qiba,  tayi wani fresh abinta,  yanzu hankalinta a kwance yake sabida kusan kullum sai tayi video call da yaya abdul d'in ta sun sha hira..........

Tofah abu kamar wasa yau su zahra saura wata uku su koma rasha,  kuma a lokacin ne zahra ta fara qoqarin zana jara bawar qarshe wanda zata fita daga senior.  Sosai zahra ta mayar da hankalin ta tana karatu domin cin jara bawarta.  Yanzu zahra sam ta dena yawan danna waya ko isha-shan kallo batayi,  daga karatun exam sai na Quran. 
       Tofah su zahra sun fara zana jarabawa,  dan haka yanzu hankalinta ya tafi kan exam ko isha-shan abinci bataci,  burun zahra kawai ta zana jarabawarta ta koma Nigeria dan ko jiran mashkhur bazata staya ba. Acewar zahra ba cewar amina bayero ba.












Tofah sai da zahra sukayi 2 week's suna yin jarabawa sanan suka kammala.  Ranar da zahra suka kammala jarabawa ko bacci bata iyaba sabida farib ciki,.  Zahra tanajin ''yan ajinsu suna cewa zasuyi gaggarimin candy amma kawai binsu take da to d'an ita gani take kafin wata biyun nan su cika tama koma Nigeria harta dad'e,  dan ko ruselt d'in ta bazata tsaya kar6a ba sai dai yaya ahmad ya kar6o mata.
      Washe gari zahra ta bugawa dady ta sanar da shi sun kammala exam,  dan haka tanaso ta dawo Nigeria.

Dady kuwa tambayar zahra yayi akan ta kar6o result d'in ta?  Aa dady wai sai nan da too month in an koma school kuma ni bazan iya jiraba yaya ahmad ya kar6o min.  Murmushi dady yayi tare da cewa! Kinga kuwa fad'uwa tazo dai-dai da zama shima yayanki nan da wata biyu zasuyi jarabawa kinga sai ki jirashi in yayi sai ku tawo tare.  Haba dady yanzu sai na jira yaya mashkhur ya gama jarawa kenan zan dawo wlh ni na gaji da zaman rashan nan na tsargu na dawo Nigeria.

Gyan murya dady yayi tare da cewa! Haba mamana,  kikayi shekara da watanni ma,  amma nan da wata biyu ki kasa zama,  haba mamana pls kiyi haquri, kamar yau ne fa.  Murya a sanyaye zahra tace tom shikenan dady ALLAH ya kaimu lokacin,  amen mamana ko kefa,  daga haka dady da zahra suka sha hira haka dai zahra ta haqura da tafiya Nigeria badan taso ba,  sabida kawai dai ba yadda zatai.........

To haka kwanaki sukai taja yanzu dai ya rage saura sati uku su mashkhur su fara jarabawa. 6angar mashkhur kuwa abun ba'a cewa komai, kullum yana maqale da littafi yana karatu watarana ma ko bacci bayayi,  sosai mashkhur yake karatu duk ya tattara kayan shaye-shayen nan ya ajiyesu a gefe.  Kai yanzu zahra ta kula da yadda mashkhur yake karatu dan something ma,  suna yawan had'u a kicin,  ko' a falo kuma duk sandda suka had'u zahra da littafi take ganin mashkhur a hanunsa,  duk yabi ya rame.

6angar ahmad kuwa sosai yake farin ciki da gabatowar lokacin jarabawar nan dan ko ba komai,  yasan ya kusan komawa Nigeria ya had'u da sahibar shi ilham........
     Tofah satin jarabawar su mashkhur ya shigo fa,  zo kaga tashin hankali a wajan mashkhur,  dan yanzu sabida karatu har ya kusan zaucewa,  shi dai burin shi guda ya futo da ruselt mai kyau sabida ya cika burinsa na rabuwa da zahra,.

Yanzu ya rage saura kwana biyu su mashkhur su fara jarabawa. Kai mashkhur kuwa yanzu ya dakatar da karatun dare,  in dare yayi kawai sallah yake,  yana roqan ALLAH akan ALLAH yasa ya samu result mai kyau,  duk da mashkhur baya sa ran zai sake d'aukar ta d'aya kamar yanda ya ta6a d'auka a baya......
Tofah akace rana bata qarya sai dai uwar d'iya taji kunya,  yau ta kasance ranar Wednesday kuma ranar su mashkhur zasu fara exam.  

Asubar fari mashkhur ya shiga toilet yayi wanka sanan ya d'auro alwala ya fito yayi sallah,  bayan yayi sallah direct kicin ya nufa ya d'ora ruwan t dan yau bazai iya jiran zahra har ta tashi ta dora abinci ba,  sabida jarabawa da zai yi.  Coffee ya d'ora,  bayan ya dawo a gaggauce yasha ya fita,  daga gida.  Yana fita ya had'u da ahmad dan haka mashkhur motar ahmad ya shiga bai tsaya d'aukar tashi ba sabida,  yana so ya qara karatu kafin su qarasa makarantar a fara jarabawa.

A nitse ahmad yake driving,  shi kuma mashkhur hankalinsa duk ya karkata kan book d'in shi yana karatu.  Ahmad kuwa kallan mashkhur yayi tare da cewa!  Mitumina wai mene sirrin ne naga kwana biyu ka koma ga Allah duk ka mai da hankalinka kan karatu ka nutsu sosai.  A nitse mashkhur ya d'ago tare da watsawa ahmad wani kallan up and down dama mashkhur ya kware wajan irin kallan nan,  cikin fine voice d'in shi mashkhur yace au da ni ba na ALLAH bana kenan,  ya qarasa maganar yana juya manya idanunsa.

Dariya ahmad yayi tare da cewa!  Aa ni ba haka nake nufi ba,  ina nufin naga ka nutsu ka dena wasu munanan halayyan ka.  Jim mashkhur yayi can kuma yace!  Okay ashe ina da mugayan halaye wana kala kenan sai ka lissafomin naji.  Sosai ahmad ya mai da hankalinsa kan driving d'in da yake kafin yace sosai ma ai sai na lissafoma tunda so kake kaji,  kaga na d'aya shaye-shayen da kake na biyu wannan stupid girl d'in da kake kulawa wato zee,  na uku kuma humm ade bar kaza cikin gashinta.

Aa ai dama ka qarasa fad'ar ragowar kar ya kasheka,  mashkhur ya fad'awa ahmad haka cikin yanayin ko in kula.  Da sauri ahmad yace ah in sha ALLAH ma bazata kasheni ba,  nida nake shirin muna komawa Nigeria zan auri farin cikin rayuwata,  to taya zakamin fatan mutuwa ban aure taba,  ahmad ya qarasa maganar yana sakin murmushi sabida tinawa da yayi da ilham d'in shi.  Ta6e baki mashkhur yayi tare da cewa!  To ita kuma wanan wace mara raboce take soyayya da abokin mai mugun hali?.

Murmushi ahmad yayi tare da cewa!  Hmm karka damu nan gaba zaka santa duk da kuwa nasan ka ta6a ganinta,  jinjina kai mashkhur yayi bai ce komai ba ya cigaba da karatunsa.  Muryar ahmad yaji ta katse shi yana cewa!  Wai mashkhur sabida mai naga kabada attention sosai akan karatu,  a taqaice mashkhur yace sabida za'a yi exam mana.  D'an harara ahmad ya watsowa mashkhur tare da cewa!  Lalai tunda da ake jara bawar baka mai da hankaliba sai yauzu.

D'an ajiyar zuciya mashkhur ya sauke tare da cewa!  Ehh sabida wannan itace finely exam shiyasa.  Jim ahmad yayi kafin yace duk da hakan dai mashkhur nasan tabbas da akwai dalilin da yasa ka nutsu haka.  Runtse ido mashkhur yayi tare da cewa!  Pls ahmad ka rabu dani kasan bana san surutu,  surutunka ya fara hawar min kai,  kuma inaso na qarasa karatuna,  yanzu in kana magana taya zanyi karatun?.   Da sauri ahmad ya girgiza kai yace no sai ka gayamim in ba haka ba bazan barka kayi karatun ba,  har mu qarasa school ina magana ko na kunna TV nayi kallo yanzu a motar.

Wani siririn tsaki mashkhur yaja tare da cewa!  To mai kake so ka sani?,  murmushi ahmad yayi tare da cewa!  Dalilin da yasa naga kwana biyu ka nutsu ka mayar da hankali kana karatu,  ahmad yana rufe baki mashkhur ya bashi amsa da cewa!  ADALILINTA mana,  da sauri ahmad ya kalli mashkhur yace itawa?  Jam mashkhur yayi kafin yace waccan yarinyar da muka baro a gida mana.  Shiru ahmad yayi kafin yace au wai zahra kake nufi?  Cikin qosawa mashkhur ya gyad'a kai  alamun ee.

Yanzu mashkhur zahran ce tasa ka ringa karatu,  haba mashkhur ka gayamin maganar da kai na zai d'auka nida a yadda na sani ko kallo bata ishe kaba.  Wani dogwan tsaki mashkhur yaja tare da cewa!  Haka na gayama ita tama isa tai min dole nayi abinda bana so,  ina nufin sabida na rabuda ita mana in mun koma Nigeria,  month d'in baya da suka wuce bana cema dady yace in muka dawo daga Nigeria na futo da result mai kyau zai raba auran muba.  Pls ahmad na baka duk amsar da kake buqata karka sake tambaya ta,  maganar ta isa haka.

Jinjina kai ahmad yayi tare da cewa oh sorry mutumina na tina ka ta6a gayamin mantawa nai wlh,  shiru mashkhur yayi bai ce komai ba. Can kuma ahmad ya cigaba da magana da wlh mashkhur inaga ranar regret (ladama)  d'in ka tana daf da qarasowa.  Da sauri mashkhur ya d'ago ya kalli ahmad tare da cewa regret kuma ahmad?  Akan mai zanyi regret nifa inaga tinda nake ban ta6a dana sani ko nadama a rayuwata ba.



Jinjina kai ahmad yayi tare da cewa!  Ai kuwa mashkhur har dai ka rabu da zahra dole kayi na dama.  Wani wawan tsaki mashkhur yaja tare da cewa!  Sabida 'yar gwalce ba.   Kwarai mashkhur dan zahra tamafi 'yar kwal,  mace iya mace,  ga kyau,  ga hankali,  ga ilimin addin,  ga sanin ya kama,  bugu da qari ga haquri,  kai duk inda ake neman mace mai nagarta a addinin musulinci zahra ta kai,  wlh zahra al'mar'atussaliha ce,  duk wani abu da ake nema wajan mace a zahiri da bad'ili zahra ta tara.

Da qarfin gaske mashkhur ya donqule hanunsa ya daki rubar motar ta gabansa har sai da ta tsage,  a tsawace yace pls ahmad shut up! banasan maganar banza mana ina ruwana da abinda ta tara ko itace autar mata ta duniya bazan cigaba da zama da itaba sabida na tsane ta,  kai ka bari in na saketa sai ka aure ta.  Sosai hankalin ahmad ya d'an tashi da yake shi mutum ne mai sanyi sam bayasan hayaniya,  cikin sanyayiyar murya yace,  sorry mashkhur cool down cool down.

Banza mashkhur yayiwa ahmad bai sake cewa komai ba,  shima ahmad d'in shiru yayi bai sake cewa Komai ba har suka qarasa makarantar.   Suna qarasawa school d'in tun kafin ahmad ya gama parking d'in motar mashkhur ya bud'e ya fuce a fusace.  Jinjina kai ahmad yayi tare da cewa!  Hmm mashkhur kenan ni nasan ranar qin dillanci tana nan zuwa,  ALLAH dai ya kyauta.  Daga haka ahmad ya fuce daga motar ya shige cikin makaranta..........

*shin ya kuke ganin zata kaya kuwa?

*kuna tinanin wani abu zai faru tsakanin mashkhur da zahra kafin su koma rasha?.

Hmmm ku biyuni a next page, dan ku samu amsar tambayoyin ku.........


ADALILINTA💜❤💜

BY AMINA BAYERO

typing...........

*Page 77*

Suna qarasawa school d'in tun kafin ahmad ya gama parking d'in motar mashkhur ya bud'e ya fuce a fusace.  Jinjina kai ahmad yayi tare da cewa!  Hmm mashkhur kenan

Please Login or Register in order to submit comment