Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ni nasan ranar qin dillanci tana nan zuwa,  ALLAH dai ya kyauta.  Daga haka ahmad ya fuce daga motar ya shige cikin makaranta..........

To masha ALLAH yau su mashkhur sun zana jarabawarsu lafiya, kuma mashkhur yaji dad'i jarabawar da yake duk ya gane Question d'in kuma ya amsa gaba d'aya.
To haka dai mashkhur ya cigaba da zana jarabawarsa, cikin qoshin lpy, kullum yana had'awa da add'u a da sallar dare akan ALLAH ya bashi sa'a ya ci jarabawar nan.

To su mashkhur sati d'aya suka d'auka da kwana d'aya suna jarabawa yau ta kasance ranar da su mashkhur zasuyi jarabawar qarshe, kuma ranar ce ta kasnce zahra zataje school itama suyi candy sanan ta kar6o result d'in ta. Dan haka itama tunda safe ta fara shirye-shiryan zuwa school, da yake 'yan ajin nasu, sun gama had'a yadda candy d'in nasu zai kasance ta group d'in WhatsApp.

Dama zahra yaya ahmad ya gama siya mata komai na candy har kayan graduation duk ya siya mata. Mashkhur kuwa tunda safe ya fice sabida jarabawa, zahra kuwa sai wajan qarfe goma yaya ahmad ya kai ta school da yake su ahmad sun riga su mashkhur gama jarabawa shi ahmad ya gama jarabawar shi da yake shi d'an art ne.

Tofa su zahra sun sha graduation sosai sunyi hotuna sunci abinci kala-kala, kuma sun kar6i ruselt d'in su, kuma alhamdulilah zahra taci jarabawarta, kuma tayi farin ciki da hakan sosai da sosai. Misalin qarfe uku su zahra suka gama graduation, kuma suna gamawa aka fara d'aukar student da yake tun kafin su gama wasu sukazo d'aukar yayan su.

Haka dai akai ta zuwa ana d'aukar student, yanzu dai ya rage saura mutum biyu, wato zahra da wata qawarta maryam, dama itama musulmace, 'yar saudiya ce zaman aiki ne ya kawo su nan shine itama akasata a school d'in su zahra, da yake makarantar ta musulmai ce. Zahra tanata jiran yaya ahmad amma shiru, har wayarsa ta buga amma taqi shiga da yake yau zahra da wayarta ta zo makarantar, ba iya ita kadai ba har sauran d'ali bai.

Misalin qarfe hud'u na yamma akazo d'aukar maryam abokiyar zaman zahra, maryam ce ta kalli zahra cikin harshan turanci tace, zahra ko zaki biyoni mu sauke ki ne a gida?. Da sauki zahra ta girgiza kai tare da cewa aa maryam kawai ki wuce gida nima nasan yayana, yanzu zai zo ya d'auke ni, haba zahra an kusan rufe makarantar fa! Yanzu saura mu kad'ai a farfajiyar makarantar nan in na tafi bazaki ji dad'in zama ke kad'ai ba.

Jim zahra tai tana tinani, da qarfi maryam taja hannunta tace zo muje mana ko bazaki gane hanyar ba, aa maryam ki tafi kawai cewar zahra. Noqe kafad'a maryam tai tare da cewa!  hmm ni dai bazan yadda ba sai kin zo mun tafi tare, ba yanda zahra ta iya dole haka tabi bayan maryam suka tafi, suna qarasawa suka shiga bayan motar sanan drive yaja motar suka fara tafiya.

Sam zahra bama tasan sunan ungur da suke ba bare tai kwance, dan haka hanya kawai take nunawa da yake ta gane hanyar tass, dama shekara ba wasa ba ai dole zahra ta gane hanyar gida. Suna tafiya zahra tana hira da maryam sanan tana nunawa drive hanyar da zai bi. To a haka-haka har driven maryam ya kawo ta har qofar gida.

Murmushi zahra tai ta kalli maryam tare da cewa!  Hmm yanzu maryam sai yau she kenan nasan bazamu sake had'uwa ba dan na kusan nabar rasha, itama Mary am d'in murmushi tai tare da cewa!  hmm ke dai bari zahra nima next week zamu koma saudiya, dama ni ake jira na kammala karatuna, dan dady na ya gama aikin da ya kawo shi nan.

Ajiyar zuciya zahra ta sauke tare da cewa!  In sha ALLAH ma zamu qara had'uwa dan inasa ran kafin na mutu zanzo saudiya aikin haji ko na umara, farin ciki ne ya kama maryam, ta rungume zahra tare da cewa!  To ALLAH ya kaimu lokacin, daga haka zahra da maryam sukayi sallama, zahra ta sauka daga motar su maryam suka wuce, suna d'agawa junan su hannu.

Su maryam suna wucewa zahra ta juya ta shige get d'in gidan, zahra tana shiga taji gabanta yana fad'uwa rass-rass-rass, nan da nan zahra, ta fara addu'o'i sabida tasan duk lokacin da wani abu zai sameta gabanta yana irin fad'uwar nan. Tofa wanan ranar harda ita zahra bazata ta6a mantawa da ita a tarihin rayuwar taba, shin mai zai faru da zahra kenan? .

A hankula zahra ta fara taka step d'in benan kamar bata so, guntun hijab d'inta da farar rigar graduation d'inta duk sun sha rubutun maka kala-kala, sabida singing d'in da 'yan ajinsu sukayi mata. Zahra tana qarasawa bakin qofar taji gabanta ya sake fad'uwa rass, dan haka tsayawa tai a gaba qofar kamar bazata shiga ba. Zahra tafi minti goma a tsaye a bakin qofa bata shigaba.

Can kuma tasa hannu ta murd'a Handel d'in qofar,ai kuwa zahra taci sa'a qofar a bud'e take ba sai ta buga ba. Ajiyar zuciya, zahra ta sauke sanan ta ta bud'e ta shiga cikin,, zuciyarta na buguntara-tara,. ga mamakin zahra tana shiga sai taga wani qaramin table daga gefe an d'ora wani qayataccan cake, blue and golden Colors yasha rubutu da bakin Zane.

A hankula zahra ta qarasa shiga ciki, zahra tana zuwa wajan table d'in ta nutsu domin karanta tsararan rubutun. Rubutune a tsare, a cikin rubutun an rubuta! Happy finally exams my honey,. Zahra kuwa mamaki ne ya kamata da yake batasan yau su mashkhur suke jarabawar qarshe ba, kamar ance zahra ta kalli kwalaban biyu da suke gefe cake d'in.

Gaban zahra ne ya fad'i rass sakamakwan abinda taga an rubuta a kwalabar, da manyan baqi taga an rubuta ALCOHOL jim zahra tai tana nazarin ko idon tane bai ga rubutun dai-dai ba Ko kuma itace bata karanta dai-dai ba, sai da zahra ta karanta sau biyar, amma dai bataji kalmar ta canzaba alcohol d'in ce dai. Cikin zuciya zahra tace to mai ya kawo giya gidan nan kuma? .

Wata zuciyar tace mashkhur mana, da sauri zahra ta girgiza kai dan haka nan jakinta ya bata ba mashkhur bane kuma bazai iya wanan aikin ba. Zeee kamar almara zahra taji zuciyata, ta ambaci zee, jinjina kai zahra tai sai yanzu ta fara gane lissafin, dama dai tasan cake d'in yiwa mashkhur akai to waye yayi mai in ba zee d'in ba, kuma tasan zee ce kawai take cewa mashkhur honey.

Bugu da qari zahra tasan zee ce kwai taza iya aikata wanan mugun abu a cikin gidan. Nan da nan zuciyar zahra ta farayi mata zafi sosai, dan duk wani abu da ALLAH ya hana sam zahra k'yamarsa take sosai, duk da dai ba zahra ce zata sha giyar nan ba amma ai tasan mashkhur ta kawowa, kuma tasan shi'uman ci zee ko mashkhur, bai yi niya sha ba, zata iya yimai wani makircin da zai sha, duk da kuwa bai ta6a sha ba.

Duk da zahra ta tsani mashkhur bazata so ya sha giyaba kai koma ta6awa bazata so yayi ba, dan ko ba komai jinin ammi da dady ne. Kamar ance zahra ta d'ago, tana dagowa ta hango zee, sanye da qananun kaya ta futo daga d'akin mashkhur,. Tana wani tafiya cikin gadara, tana qarasowa zahra tace mata kee mai yasa kika shigo mana da wanan banzayan kayan gida, ko shi yasa ki kawo mai ne?.

Wato zahra tana nufin mashkhur, murmushi zee tai tare da girgiza kai tana cewa ko d'aya, honey ma bai san nazo gidan nan ba a motar shi na dakko key d'in gidan, kawai dan inyi surprises d'in shi nayi mai wanan, sabida yau final exam d'in shi ce, shiyasama na kawo mai giyar dan ya fara sha yaji yanda take. Wani dogwan tsaki zahra taja tare da cewa!  To wanan na tambaye ki?

Ni ina ruwana da wanan? maza-maza ki tattara ki fita da giyar nan kafin ya dawo. Dan mu a addinin mu ba kyau shan wanan ku da kukaga zaku iya kije can kuyi tasha mudai bazamu iya qazantar nan ba, zahra ta qarasa maganar tana watsawa zee harara. Zee kuwa wani dogwan tsaki taja tare da cewa!  To ni ina ruwana, giyace dai yau dole honey na yasha bazan fitar da itaba tinda ba gidan ki bane 'yar aiki da ke kin takurawa future wife d'in mai gida.

Wani murmushi takai ci zahra tai tare da cewa!  hmm lallai ai ke matar shi ce wanda kuke sa ran zakuyi aure nan gaba koh? Da sauri zee ta saki murmushi tare da cewa! Kwarai kuwa hakane. Itama zahra wani shu'umin murmushi ta saki kafin tace ni kuma matar shi ce, yau wajan shekara d'aya da watanni da auran harma ina d'auke da babyn sa a cikin, zahra ta qarasa maganar tana shafa cikinta kamar gaske.

Wani mugun zaro ido zee tai tare da cewa! Karya kike house girl d'in shi ce ba matar shiba ke daya tsane ki ma. Murmushin tura takai ci zahra tai tare da cewa!  hmm da kika sani kenan, yanzu kinga yana nunamin tsana ne tun yaushe iyayan mu sukazo suka sasanta mu, ai shi yasa watannin baya da suka wuce ya hanaki zuwa gidan nan yace miki dadyn sane yazo.

Nan da nan zee ta fara zaro ido tana cewa! Da gaske kike? zahra kuwa saura qiris ta kwashe da dariya amma ta dake tace kwarai kuwa, ke kin ta6a ganin a addinin musulinci mace ta bi namijk wata qasar ba tare da anyi musu aure ba? da ne baya sona amma daga baga dayaga na cika mace shi yasa ya fara sona ko bakiga na qara girma bane zahra ta fad'i maganar tana d'an juyawa zee jikinta.

Zaro ido zee tai tana kallan zahra nan da nan zee ta sake rikicewa ganin zahra ta qara qiba ba kamar kwanakin baya ba da akazo da ita qarama ba, kuma tabbas zee ta farajin qamshin gaskiya a maganar zahra, yanzu taga mashkhur baya takura mata kamar da sam kuma ya dena horata, cikin tashin hankali zee tace are you really? Jinjina kai zahra tai tare da cewa!  Yes I'm really, jekima Ki bigamai waya ya dawo in ya dawo ki tambaye shi nima zan mai mai ta abinda nace miki a gaban sa.

Zee bata tsaya wata-wata ba ta koma bedroom d'in mashkhur da mugun sauri dan ta d'auko wayarta ta bigawa mashkhur, kamar yanda zahra ta umarce ta. Zahra kuwa ajiyar zuciya, tai dama so take zee tabar wajan, dan ta ai watar da abinda take ganin shine dai-dai, zee tana tafiya zahra ta ajiye wayarta akan kujera ta d'ibi gwalaban giyar na duka biyun ta fuce da su da sauri.

A dai-dai lokacin zee ta futo daga bedroom d'in mashkhur riqe da waya a hanunta tana futowa taga zahra ta fuce a guje amma bata gama ganin dame ta fita ba, zee tana qarasowa table taga sam ba alcohol din nan, da gudun gaske tabi bayan zahra itama tare da cewa! Kee kee ki tsaya mai zaki ai kata ne haka. Zahra kuwa tana qarasa fita daga fallon tai sauri ta zira kwalaban ta sama benan ta sake su suka sauka qasa, suna sauka qasa ji kake tass tass tass.

Zahra tana gama sakin kwalaban qasa Zee ta futo, a mugun tsawace zee tacewa zahra kee ina kika kai giyar? A gadarance zahra ta juyo tare da nunawa zee can qasan benan, zee tana kallan qasa taka kwalaban giyar wanwar a gasa duk sun fashe, zahra tana qoqarin komawa ciki zee ta janyo ta a fusace, da sauri zahra ta riqe qarfan benan dan saura qiris ta fad'i.

Zaro mata ido zee tai tare da dango hijab d'in zahra da qarfin gaske tana cewa!  Akan mai zaki zubar min? Yau zaki gane baki da wayo sai na zaneki a cikin gidan nan. Da sauri zahra ta fincike wuyan hijab d'inta daga hanun zee ta fara qoqarin shigewa, ai kuwa zee ta ruqo zahra tai tare da sharara mata wani kayakyawan mari mai shiga jiki.

Da sauri zahra ta riqe kuncinta sabida harga ALLAH taji zafin marin da zee tai mata sosai, a fusace zee ta sake d'aga hannu zata qara kaiwa zahra mari, da saurin gaske zahra ta riqe hanun zee ta yarfar qasa, sanan ta sakar mata kyawawan maruka guda hud'u da hannu bibiyu ji kake tass tass tass tass, sai da zahra ta jerawa zee kyawawan maruka guda hud'u a jere.

Wani tangal tangal zee ta fara kamar zata fad'i sabida tinda aka haifeta a duniya ba wanda ya ta6a sa hannu ya mare ta sai yau. Wani irin mugun huci zee ta farayi dama gashi tanajin haushi zahra matar mashkhur ce harma tana da cikinsa. Da mugun qarfi zee tai kukan kura ta danqi zahra, tai mugun wirgida ita. Zahra tasa hannu kenan dan ta ruqo qarfan benan taji qarfan ya daki kanta da mugun qarfi.

ai zahra kanta yana dukan qarfan nan ta fara gangarawa qasan benan da mugun qarfi, wata irin gigitacciyar qara zahra ta saki, ai kuwa adai-dai lokaci Ahmad da Mashkhur suka shigo gidan a motar mashkhur. ahmad ne yake tuqawa mashkhur yana drive, zahra tana sakin iwun nan gaban mashkhur ya fad'i sabida ji yayi kamar a kunansa ta saki iwun duk da kuwa suna da tazara kuma glass d'in motar a bud'e yake.

Da sauri ahmad yaja wani wawan birki a dai-dai lokacin zahra ta qarasa fad'owa daga matata kalar benan, da mugun qarfi ta fad'o, ahmad da Mashkhur kuwa har suna 'yar rige-rige fita daga motar, dan ahmad ma ko motar bai tsaya kashewa ba barema su rufe murfin dan sunma manta ana kashe wata motar ko rufewa a duniya..............

*hmmm kuna ganin zahra taza rayuwa kuwa? 🤔😭😭

* kai kuna tinanin zahra in ta rayuwa zee bata yi mata illah ba kuwa?.

*kuna gana mashkhur zai hukunta zee ko kuwa?.

*kuna tinanin hankalin mashkhur zai tashi ko kuwa?.

Ku biyoni a next page.

Ni dai amina bayero nace ALLAH ya tsine miki zee... 😭😭😭😭😭

ADALILINTA💜❤💜

BY AMINA BAYERO

Typing.......

*page 78*

Da sauri ahmad yaja wani wawan birki a dai-dai lokacin zahra ta qarasa fad'owa daga matata kalar benan, da mugun qarfi ta fad'o, ahmad da Mashkhur kuwa har suna 'yar rige-rige fita daga motar, dan ahmad ma ko motar bai tsaya kashewa ba barema su rufe murfin dan sunma manta ana kashe wata motar ko rufewa a duniya..............


A sukwane ahmad da mashkhur suka qaraso inda zahra take sheme akwance. Da sauri mashkhur ya tsugune a kan zahra ya zuba mata ido hankali a tashe, sam ma ya kasa ta6a jikinta, sabida tashin. Mashkhur yasa hannu kenan zai d'ago zahra yaji muryar zee tana cewa! Honey da gaske motar kace, kuma tana d'auke da juna biyun ka a cikin ta. Sakin baki ahmad da mashkhur sukayi suna kallan zee da take saman bene wanda ko ajikinta abinda ya faru.

Zee kuwa cigaba da magana tai da cewa! Amma gaskiya honey in dai hakane baka yimin adalciba, kuma wlh sai naga bayanta ita da abinda yake cikinta barima kaga yanzu zan qarasa kasheta, zee ta qarasa magana tana qoqarin saukowa. Ai wani kukan kura mashkhur yayi tare da wani mugun tsalle ya tsallake zahra a wajan ya hau kan step d'in benan ya nufi zee a zuciye.

Da sauri zee ta fara ja da baya tana cewa! haba honey nice fa, cool down mai kake qoqarin aikatawa? Honey nifff ai kafin zee ta qarasa maganar mashkhur ya kaiwa wuyanta danqa. Da qarfin gaske mashkhur ya danqi wuyan zee tare da gwara qeyarta a bango,. Wata siririyar qara zee ta saki sabida har cikin kwakwalwarta taji gwaruwar da mashkhur yayi mata.

Hannu mashkhur yasa ya ringa naushin baki da fuskar zee. Zee tana so tayi ihun neman tai mako amma ba hali da yake mashkhur ya shaqeta sosai bazata iya wani kwakwaran matsiba bare ma tai wani ihu. Sosai mashkhur yake naushin baki da fuskar zee, lokaci guda fuskar zee ta kunbura kamar alala, bakinta kuwa yayi suntum kamar an zubamai fauda.

Ahmad kuwa nan da nan ya zaro waya ya bigawa motar asibiti da 'yan sanda. Ahmad bayan ya gama wayar yana daga qasan bene sai magiya yakewa mashkhur akan ya rabu da zee kar yayi mata illah, yan sanda zasuzo. Amma ina mashkhur bai ma san abinda ahmad yake fad'a ba kawai lugudar zee yake kamar ya samu jaka. Mashkhur!! mashkhur!! Zo kaga kamar fa zahra bata nunfashi, ahmad ya fad'i hakan a razane.

Ai lokacin da mashkhur yaji hakan da sauri ya saki zee tare da juyowa ya fara saukowa a sukwane, mashkhur yana qarasowa inda zahra take sheme akwance ya tsuguna tare da d'agota ya janyota jikinsa. Tashin hankali nan sa nan hankalin mashkhur da ahmad ya qara tashi saka makwan ganin jini ya wanke fuskar zahra, jini har ta hanci zahra zubowa yake.

Cikin mugun tashin hankali Da qarfin gaske mashkhur ya fara jijiga zahra yana cewa! Zahra! Zahra! Kina jina ki tashi mana?. Amma ina zahra ko nunfashi batayi bare kwakwaran motsi, cikin tashin hankali ahmad yace inalilahi wa'inna'ilahirraji'un mashkhur anya zee bata kashe zahra ba kowa? Nan da nan mashkhur ya fara zazzaro ido kamar an kwashewa karya 'ya'ya.

Cikin tashin hankali mashkhur yace inalilahi ahmad na shiga uku wlh zee nima ta kashe ni, inalilahi zee ta jefani a ciki matsala. Nan da nan mashkhur ya cigaba da jijiga zahra yana ambatar sunan ta amma ina shiru. Daga qarshema jinine ya fara futowa ta hancin zahra, cikin tashin hankali mashkhur yace ahmad ya kamatafa mu tafi asibiti.

Da sauri ahmad yace! Aa mashkhur ko munje asibiti bazasu kar6i zahra ba sabida ba 'yan sanda, amma na kira 'yan sanda da motar asibi tinda bamu da nisa da su nasan yanzu za kaga sun zo. Ahmad yana qarasa rufe baki, jiniyar motar 'yan sanda ta qarad'e wajan. Zo kaga tashin hankali a fuskar zee da taji jini yar 'yan sanda ba shiri ta miqe daga zaman da tai ta fara neman hanyar guduwa.

Da gudun gaske zee ta sauko daga step d'in benan sanan ta fara qoqarin fucewa daga gidan. Da sauri gaske ahmad ya miqe tare da ruqo zee da qarfin gaske. Ahmad yana ruqe zee 'yan sanda suka fara bayyana a cikin gidan. Kafin kace fit 'yan sanda sun zagaye zee da ahmad, can gefema kuma sun qara zagaye, mashkhur da yake qaqqame da zahra a jikin sa.

Nan da nan police suka fara watsawa mashkhur tambaya amma ina mashkhur ba amsa yayi tsuru-tsuru kamar shi ya aikata laifin. Sai ahmad ne dai aka samu yayi musu bayanin iya abinda suka sani idanusu yazo ya gane musu, ana cikin haka motar asibiti ta qaraso,. Dan haka ba 6ata lokaci likitoci suka futo da gadan d'aukar festions suka 6anbl6are zahra daga jikin mashkhur suka d'orata sanan suka shigar da ita motar asibiti.

Sai da 'yan sanda suka sa hannu a takadda sanan aka tafida da zahra hosbitol,. 6angare guda kuwa tuni 'yan sanda suka tusa qeyar zee a mota sukayi gaba da ita. Gida dai ya rage daga ahmad sai Mashkhu,, mashkhur yayi rashe-rashe a qasa ya qifa kansa a guiwa rigarsa duk tabi ta jiki da jinin zahra sai qarnin jini yake. Ahmad ne ya qaraso inda mashkhur yake tare da cewa! Mashkhur tashi kaje ka canza kaya muma mu wuce asibiti, dan musun a wana hali zahra take.

Da kyar mashkhur ya iya miqewa cikin tashin hankali yace! Ahmad kawai muje a haka bazan iya canza rigar nan ba, bana ciki nutsuwa duk hankali na yana kan zahra. Girgiza kai ahmad yayi tare da cewa! Kagafa yadda jikinka ya jiqe da jini, haba mashkhur kaje ka canza riga mana. Jiki a sanyaye mashkhur ya miqe ya wuce matattakalar benan zuciya cike da zullumi.

Mashkhur yana shiga ciki ba 6ata lokaci ya wuce toilet ya watsa ruwa a hanzarce, sanan ya futo, yana futowa daga toilet ya wuce wardrobe ya kwaso kayansa yasa a hanzarce sanan ya fesa turare ya fuce. Ni kuwa amina bayero nace anya mashkhur hankalin ka ya tashi🤔 tunda gashi baka manta inda hanyar turare yake ba.

Mashkhur yana futa ahmad ya watsa mai wani kallon takai ci, a zuciyar ahmad yace hmm lallai mashkhur harda ma wani wanka ya tsaya yi?. Daga haka ahmad ya wuce mota ya shige, jiki ba kwari mashkhur yabi bayan ahmad,. Yana qaraswa ba 6ata lokaci ya shige motar shima, dama ahmad bai kashe motar ba dan haka ba 6ata lokaci suka wuce asibiti.......

Lokacin da su mashkhur suka je asibitin ba su sha wahala ba suka gane an wuce da zahra enmagency room. Haka ahmad da mashkhur suka samu waje a inda aka tanadarwa 'yan uwan majinyata suka zauna. Wani uban tagumi mashkhur ya raf ka, ji yake abun kamar a marki, ba abinda yake furtawa sai zee kin cuceni zee kin jefani a cikin matsala wlh.

Wani siririn tsaki ahmad yaja tare da cewa! Ka dai cuci kanka koh? Tun yaushe nake cewa ka rabuda zee amma kaqi rabuwa da ita sam kai watsi da magana ta gashi yanzu ta janyoma masifa, dan kasan iyayan zahra sukaji wanan abun wlh zaka shiga cikin gaggarumar matsala koh?. Ai lokacin da ahmad ya ambaci iyayan zahra ba wanda suka fad'owa mashkhur a rai sai dady da ammi harma da hjy kaka.

Nan da nan hankalin mashkhur ya sake mugun tashi cikin rawar murya yace! Ahmad ka taya ni da addu'a ALLAH yasa zee batayiwa zahra wani lahalin da su dady zasu gane ba. Wani mugun dogwan tsaki ahmad yajawa mashkhur tare da cewa! Lalai ma mashkhur wato kai kana tinanin zahra zata rayu koh? Ai lahanima da sauqi mashkhur, dan wlh da kyar in zahra taza rayuwa, ahmad ya qarasa maganar kamar zai zubar da hawaye.

Wata muguwar razana mashkhur yayi hankali a tashe ya kalli ahmad yace! Inalilahi mutuwafa kace ahmad? Yanzu shikenan zahra zata mutu da aure na ban sake taba? Ahmad yanzu in ta mutu shikenan ranar lahira a matata zata tashi? Yanzu ahmad ba'a sakin mace in ta mutu koh? Ko dsi zan iya sakinta in ta mutu ne?. Sakin

Please Login or Register in order to submit comment