Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma tana ta faman jijiga babyn, kai zahra dan ALLAH ki dena jijiga yaran nan haka ki barshi ya wuta, inaga ma yunwa yake ji amma kin kama shi kina jijjaga shi, kawai ki bashi nono ya sha shine magana. Zahra dena jijiga shi tai kamar yarda ilham tace sannan tace tom.

Amma yanzu bacci nake ji ni bari sai na tashi, zahra kenan zakiga kunya kita wahalar da bawan ALLAH dallah ki bashi yasha meye haka ke ko tausaya mai ba k'ya yi?.Zahra ji tai yaran nata ya bata tausayi sosai sai kuka yake fuskar shi duk tayi ja abun tausayi. Murya a sanyaye zahra tace to zo ki d'an zugemin zif d'in rigata.

Okay ilham ta fad'a sanan ta ajiye plate d'in hanun ta, bayan ta ajiye tasowa tai ta zugewa zahra zif d'in rigarta. Bayan ilham ta zugewa zahra zif zahra cewa tai yauwa ilham jeki ki rufo qofarnan kar a shigo je kisa key. Miqewa ilham tai sanan tace hmm manya ana shayarwa. Bayan ta rufe ta dawo ta d'auki plate d'in ta sanan ta cigaba da cin farfesun ta.

ilham dai tana kallan zahra tana noqe-noqe amma sai tai mata shiru kamar bata gani ba, dan tasan halin zahra yanzu tana yi mata magana iskanci zai qaru. Zahra bayan ta gama noqe-noqe ta haka ta ciro brest d'in sanan ta fara qoqarin bawa babyn. Zahra ki gyara mai wuyan sa kar kan sa ya qage mana cewar ilham.

Ban gane ba ya zan yi masa da wuyan nasa? Dawowa kusa da zahra ilham tai sannan ta gyara kan babyn, bayan ta gyara tace in zaki bashi nono haka zaki ringa yi masa da kan sa, zahra cewa tai to sanan ta fara qoqarin bawa babyn nono. Haka dai babyn yayi ta qoqarin kamawa, bayan ya kama ya fara sha a hankula.

Tom zahra dai babyn bai dad'e da fara shaba ta fara yiwa ilham complain akan ita bazata iya ba zafi take ji sai ta wuta. Haka dai ilham tai ta bawa zahra baki da yake ta san kan mutuniyarta. Sosai ilham ta ringa bawa zahra baki har sai da babyn yasha ya qoshi sosai, dan har yama fara bacci sanan ilham ta rabi da zahra.

Zahra tana zare brest d'in ta ta mayar da shi sannan ta zuge zif d'in rigar ta. Ta samu waje ta kwantar da babyn bayan ta kwantar da shi, itama kwanciya tai a kusa da shi. Haka suka fara hira sama-sama da ilham ba jimawa bacci mai dad'i yayi awan gaba da zahra. Dama baccin ba isarta yayi ba kawai de bata son bacci a hospital d'in ne.

Yamma.
Da yamma misalin qarfe 4 bayan an gama abinci kowa yaci, nana wanka ta shiga tayi sanan ta fito ta shafa hoda da kwalli harma da man le6e daga nan ta d'auko doguwar rigarta tasa. Rigar ta d'an kama jikin ta kad'an rigar tayi mata kyau sosai, sannan ta samu mayafin ta qarami ba wani mai tsayi ba ta yafa. Ta d'auki wayarta da jakar ta.

Nana ina zaki? Cewar mama, mama ba wani nisa zan ba bazan dad'e ba zan dawo gidan su qawar nan tawa yar kano da nake baki labari zani. Kai nana da yamman nan haka? Ah mama ba jimawa zanyiba fa, to yanzu sai dai ki hau keke napep kije kenan. Ee mama amma in zan dawo zan kira yaya abdul ya d'auko ni.

To shikenan nana amma kalli mayafin jikin ki fa nan kano ba irin kaduna bane ba, ba da ko wace shiga zaki iya fita ba, yanzu ana ganin ki kallon mara tarbiya za'a yi miki. Kai mama dan ALLAH ki barni naje haka ba komai in sha ALLAH ba wani jimawa zanyi ba. To bazaki tafi da dan rakiya ba ko khaulat ce ta raka ki? Aa mama ni ka d'ai sai nafi sauri. Ok tom sai kin dawo ALLAH ya tsare hanya, murmushi nana tai tare da cewa ameen.

Nana haka ta fita da sauri, sai wani zambad'a sauri take kamar zata tashi sama. Tana futowa farfajiyar gidan taji wayarta ta fara ringing. Zaro ta tai kamar yarda tai tinani yaya abdul ne yake kiranta. A hanzarce ta d'auka tare da cewa ganinan zan futo yanzu amma ya kacemin sunan wajan da za'a sauke nima?. Jim nana tai tana sauraran abdul.

Bayan ya bata amsa okay tace sann ta kashe wayar ta mayar jaka ta cigaba da tafiya da sauri har sai da ta fita daga gida. Tana fita taci sa'a ta samu adedeta sawu ta hau sanan ta gayamai wajan da yaya abdul yace mata. Bayan sun fara tafiya basu wani jima ba mai adedeta yace anzo. Nana cewa tai tom bari ina zuwa.

Sanan ta zaro wayarta ta kira yaya abdul ta sanar da shi cewa tazo inda yace mata. Leqawa nana tai bayan ta hango motar yaya abdul d'in kashe wayar tai sanan ta mayar da wayar jaka ta zaro d'ari biyar ta bawa mai adedeta ko canji bata tsaya qar6a ba tace ya barshi sanan ta fuce a hanzarce.

Tafiya kad'an ta qarasa motar yaya abdul d'in sanan ta bud'e ta shiga gidan gaba tana mai da nunfashi kamar wanda tai tafiya mai tsayi. Kallon ta abdul yayi tare da cewa sannu koh? Murmushi nana tai sanan tace yauwa baby yanzu muje koh?. Abdul kawar da kai yayi sanan ya fara tuqa motar yana cewa! Kinsa wani abu kuwa?.

Girgiza kai nana tai tare da cewa aa baby sai ka fad'a fuska sake abdul yace sam mayafin nan bai miki kyau ba. Nana cewa tai to ko zan koma gida na canzo wanda kake so ne?. Ko kin koma ba lallai kisa wanda nake so ba. Zan sa mana yaya abdul wanne kake so?. Hmmm nana bana son ganinki da irin mayafin nan sabida yayi qanqanta sosai.

Shiru nana tai ba tare da tace komai ba, duk wanda ya ganki da mayafin nan kuma yaga rigarki ta matseki zai yi miki wata fassarar ta daban ne. Haba yaya abdul mai kake nufi dani ne nifa irin wanan shigar na saba a kaduna in ka fita haka ba laifi. Tom naji nana ya haquri baki fahimce ni bane, kin san dole kai kishin abinda kake so.

Bazan so wani ko wata su ganki haka ba amma in kinji haushi kiyi haquri. Tom shikenan yaya abdul tinda baka so na dena. Yauwa nanata ba iya garin nan nace ba har kaduna ma in kin koma bana so ki cigaba da irin wanan shigar kinji nanata. Tom yaya abdul na dena yauwa nana yanzu bari naje na siya miki wani mayafin ki canza ko dan baza mu iya zuwa a haka ba.

Tom baby yarda kace muje, haka abdul da nana su kai ta hirar su gwanin ban sha'awa har suka qarasa wajan siyar da kayan. Bayan abdul yayi parking d'in motar fita yayi domi siyarwa nana mayafi. Bai wani jima sosai ba dan befi 10 minutes ba ya dawo hannu riqe da laida. Yana shigowa ya miqawa nana tare da cewa gashi zaki iya canzawa.

Nana kuwa ko bud'e ledar ba tai ba ta cire na jikinta, ga jikin nata masha ALLAH dama dai kunsan nana tana da 'yar qiba ba laifi komai yaji. da sauri abdul ya kawar da kai gefe ba wai dan baya son kallon nana ba aa kawai dai yana gujewa haram ne dan yasan har yanzu nana bata zama maharramar saba. Abdul bashi ya jiyo ba har sai da nana tace yaya abdul kaga yayi kyau.

Juyowa abdul yayi sanan yace masha ALLAH ko kefa, kefa hajiya ce ba qaramar mace bace. Murmushi nana tai tare da cewa nagode. Daga haka abdul suka wuce wajan shaqatawa suka sha ice cream, sanan sukai pictures d'in su, kums suka sha soyayyar su. Bayan nan suka wuce wajan sai da kayan baby su ka hau siyowa babyn zahra da mashkhur kaya kala-kala.........

[13/05, 12:54 pm] AMNA: ADALILINTA💜❤💜

BY AMINA BAYERO💜❤💜

DOUBLE PAGE

Tofa nana da yaya abdul basu suka koma gida ba sai da aka fara kiran sallah isha'i sanan suka shiga gida. Time d'ina har baby da me jego an gama yi musu wanka sun kwanta zasuyi bacci. Ammi ba laifi tana shan hidima sosai da zahra da babyn ta. Kuma maman zahra tana jin dad'in hakan sosai a zuciyar ta tana ta farin ciki zahra tayi sa'ar iyaye kuma surukai.

Shiyasa sam bata qin ta bawa nana abdul ko dan daddy, dukvda kuwa har ranar mama bata dena ganin baqin halima ba wato maman abdul. Dama tunda can maman zahra tana qaunar abdul tun data gan shi yana yaro, kuma taji dad'in labarin da taji yarda yake nunawa zahra kulawa da soyayyah tun tana yarinya har kawo lokacin.

Washe gari.

Washe gari misalin qarfe goma ruma tazo ita da mijinta sunyiwa zahra barka.
6angaran maman zahra kuwa sun fara shirin komawa kaduna, amma banda nana wanda tace ita sai bayan suna zata dawo tana tare da zahra da kuma babyn ta. Misalin qarfe 4 maman zahra da qannan nana suka kama hanyar tafiya kaduna.

To zahra tana ganin mutane iri-iri suna zuwar mata barka da wanda ta sani da wanda bata sani ba harma dangin mamanta tun daga kaduna zuwa suke,. Babyn zahra da mashkhur kuwa yana shan d'auka sosai, duk mutan gidan kowa burunsa in yana gidan yaga yazo d'auka babyn zahra. Ga yaran masha ALLAH yana sa6ewa kyan shi yana sake bayyana.

5 days litter.

Misalin qarfe biyar na yamma mashkhur ya qaraso gida. Yana shigowa yayi parking d'in motar sa sanan ya shige ciki. Tun kafin ya shiga fallon ammi yake jin hayaniyar mutan gida. Baki d'auke da sallama ya shiga, faruq, haidar, nana ameer sai babyn su zahra da yake hanun nana haka suke ta kasa shi kamar wasu yara in wanan ya d'auka wanan ya d'auka.

Nan da nan suka amsa sallamar yaya mashkhur sannan suka fara gai dashi cikin ladabi, yaya mashkhur barka da zuwa yaya mashkhur ina wuni. Kamar yarda ya saba wataran in baya son magana, cikin shan qamshi ya kau da kai sanan ya fara amsa musu mrya sama-sama kamar mai jin bacci. Gade babyn shi mashkhur yana gani a hannun su duk san shi da d'aukar shi dole yayi haquri ya bar musu.

Mashkhur direct ya wuce sama, yana zuwa sama ya shige bedroom d'in ammi wajan matar sa zahra, murd'a handle d'in bedroom d'in mashkhur yayi baki d'auke da sallama ya shiga. Kwance ya tarar da zahra akan bed tana danna waya. Zahra tana jin sallam mashkhur ta miqe zaune tare da ajiye wayar tana amsa sallama.

A gajiye mashkhur ya qaraso kamar wani saban maraya ya hau bed d'in ya zauna kusa da zahra. Kallon shi zahra tai tare da cewa dear lafiya nagan ka wani iri. My wife nifa kewar ki nake kinji, ajiyar zuciya zahra tai sanan tace oh shine duk kabi ka canza nayi tinanin ma wani abun ne. Kallon ta mashkhur yayi tare da cewa! To shi wanan d'in ba abu bane.

Tom naji abu ne amma yanzu ba gashi ka ganni ba, murmushi yaqe mashkhur yayi tare da cewa ni ce miki akai irin wanan gani nake so nai miki. Wani kallo zahra ta watsawa mashkhur tare da cewa mai kake nufi, to gwara ka cirewa ranka wanan dan sai nayi 40 days cif, haba yaufa 5 days da haiwuwata.

Hmmm na sani mana amma 40 days kikacev zahra anya kina tausaya min, oh kai kana tinanin ko nayi kwana arba'in d'in da haiwuwa zan yarda ne lallai yaya mashkhur. Tom shikenan zahra in kika kashe ni ai kin wuta. Ba wani kisa da can da bakayi mai ya same ka, to ai kinga da kika ce kuma ban saba ba sai da kika d'and'a namin zuma a baki.

Ajiyar zuciya zahra ta sauke sanan tace gaskiya yaya mashkhur ni bazan iya wanan abun ba amma na amince maka kaje ka auro wata kawai ni ka barni na wuta kaji. Wani kallo mashkhur yayiwa zahra sanan ya kafe ta da idanuwa yana cewa haba zahra da bakin ki kike cemin haka sabida kinga na damu dake koh?.

To bari kiji ni sam duk duniya mace bata birge ni ban damu da wata mace ba in ba keba, kuma ni bazan iya ta6a jikin mace ba barema har nayi ma'amalar da kike nufi da ita ba in ba ke da kika zama dole na ba, ni ko wace mace kyankyamin ta nake ji ta sigar ma'amala zahra ke kad'ai nake so kuma ke kad'ai zan iya kusan ta ki dena yimin maganar wata.

Ko da ace mutuwa kika to wlh haka zan ta zama sai dai na mutu ba aure ni ba macen da take ban sha'awa in ba ke ba kuma! Da sauri zahra tasa hannu ta toshewa mashkhur baki tare da cewa haba yaya mashkhur wasa fa kawai nake yima amma naga duk ka birkice ka canza cool down yaya mashkhur.

Zahra ta qarasa maganar cikin tausayawa, a hankula ta saki bakin mashkhur ta miqe tana tafiya a hankula ta nufi fridge. Tana zuwa ta bud'e ta d'auko ruwa mai sanyi sanan ta rufe fridge d'in,. Ta dawo kan drowar gefan gado ta d'auki glass cup sanan ta nufo mashkhur, ta dawo gefan mashkhur ta zauna sanan ta fara qoqarin bud'e bottle d'in ruwan.

Bayan ta bud'e ta fara zuba ruwan mai matuqar sanyi dan har hayaqi sanyi yake. Dama haka mashkhur yake duk sanda ransa ya 6ace ko ya shiga damuwa sai yasha ruwa mai sanyi ko yayi wanka da ruwan sanyi yake dawowa dai-dai. Bayan zahra ta cika cup d'in miqawa mashkhur tai a hankula, mashkhur kuwa harda hanun zahra ya had'a ya kai cup d'in bakin sa ya fara sha.

Zahra zubawa mashkhur ido tai tana mamakin yarda lokaci guda son ta ya kame mashkhur staff ya hana shi sukuni ko kad'an hmm Allah mai iko zahra ta fad'a a zuciyar ta. Bayan mashkhur ya gama shan ruwan jim yayi bai ce komai ba itama zahra bata ce komai ba, har sai da zuciyar shi tai mai sanyi. Sanan ya dago fuska ba a sake ba kuma ba a had'e ba.

Cikin low voice mashkhur yace dama zuwa nai na tambaye ki wana suna kike so mu sawa babayn namu? Dazu dady ya tambaye ni, shine nace sai nazo na tambaye ki, wana suna za'a sa masa?. Murmushi zahra tai sanan ta kamo hanun yaya mashkhur tace haba my hero ai a zato na kama san sunan da za'a sawa babyn nan ko ban fad'a ba.

Tunani mashkhur ya tafiyi dan shi yasan duk zaman sa da zahra tunda ta samu ciki bata ta6a gaya mai sunan da take so a sawa baby mace ko namiji ba in suka haifa. Hannu zahra tasa ta shafa fuska mashkhur da ya tafi gajeran tuani sanan tace in gaya maka?. A hankula mashkhur ya gyad'a kai, murmushi zahra tai sanan tace to kawo kunan ka kaji.

A hankula mashkhur ya matso da kunnan sa sai tin bakin zahra. Zahra matsowa ta sake yi sanan ta kai baki kan kunan mashkhur ta ciza kad'an sanan ta fad'a mai sunan cikin rad'a tare da kai mai rankwashi a hankula cikin lallausar sumar shi tana cewa ladan mantuwa. Mashkhur cije le6an shi yayi kad'an yana qarewa zahra kallo cikin wani yanayi, shi ba mai nuna haushi ba kuma ba mai nuna jin dad'i ba.

Amma kallon yafi kama dana mamaki, ah ya mashkhur lafiya ko baka gamsu da hakan ba?. Da sauri mashkhur ya girgiza kai sanan yace na gamsu mana sweet ina alfahari da mai sunan dan haka za'a sawa babyn mu sunan da kike so yarda kikace haka za'ai. Nan da nan zahra ta saki wani murmushi jin dad'i tare da cewa ALLAH yasa yayi halin mai sunan sa.

Janyota jikinsa mashkhur yayi tare da cewa nayi missing d'in ki my babe. Itama rugumo shi tai tare da cewa miss you too my husband, amma karka damu kamar yau ne zan dawo d'akin ka mu cigaba da rayuwar mu cikin farin ciki tare da babyn mu. Sake rungumo ta mashkhur yayi tare da cewa wlh zahra ina fatan ranar da zaki dawo gare ni ke da babyn mu.

Mashkhur yana kai nan sukaji qarar murd'a handle da sauri suka fara qoqarin sakin junan su. Suna qarasa sakin junan su ammi tana shigowa baki d'auke da sallama hannu riqe da botikin ruwan zafin wanka zahra. Kallo one ammi tai musu ta kawar da kai gefe ta wuce toilet a zuciyar ta tace oh mashkhur bazaka bar zahra ta wuta ba sai kace wani tsowan maye.

Amma a fili yi tai kamar bata ankare da abinda suke ba bayan sun gama gaisawa mashkhur ya fuce domin zuwa wajan dady. bayan mashkhur ya fita zahra miqewa tai suka shige toilet aka farayi mata wanka yamma. Bayan an gama yi mata ammi ta sauka ta kar6o babyn shima tai mai wanka ta shirya shi, sanan ta bawa zahra ta fara shayar da yaron ta.

To washe gari tunda safe ake shirya-shiryan sunan babyn su zahra da yake sunan saura one day. Su maman zahra ma tun qarfe 10 suka dira a gidan,. Shirya-shirya sosai ya kanka ma itama ilham qarfe 3 tazo gida, mutane ma sun d'an fara zuwa gidan kad'an kad'an, duk da zahra bata son mutane sosai amma dole haka ta daure.

Washe gari.

Ranar suna da sassafe aka yiwa yaro haqiqa akai mai hud'uba da suna ABDUL MAJID. Wato babyn zahra yaci sunan yaya abdul, hmmm gaskiya kam zahra ta nunawa abdul kara da kawai ci. Mutan gidan basu mamakin haka ba sabida sun san tsakanin zahra da abdul sai Allah, zahra da abdul suna qaunar junan su.

Zahra ko sunan karan nan taqi yarda a sawa babyn ta sai abdul kawai ta yarda ace mai. Hmmm zo kuga murna wajan abdul, sabida farin ciki har hawaye yayi. Abdul yayi farin cikin da karamcin da zahra ta nuna mai tsayawa ma gaya muku farin cikin da abdul yayi 6ata time ne. Dady da ammi ma sunyi farin ciki da hakan.

Tom ranar an sha suna sosai da sosai anyi bidiri ba qarya anci an sha, har da masu guziri. Zahra tayi kyau sosai duk da taqi yarda ma ai mata makeup, amma duk da hakan tayi kyau ba qarya. Mutane da dama ranar zahra ta gansu har wanda ma tinda uwarta ta haife ta bata ta6a ganin su ba sai ranar.

Mutane sun cika sosai har daga kaduna anzazo ba laifi. Sai wajan qarfe tara su zahra suka samu kan su sabida jama'a. A lokacin ne kowa ya tafi mutane kad'an kad'an ne suka zauna suma washe gari zasu tafi. Sai wajan goma zahra ta samu aka yi mata wanka ita da babyn ta sanan taci abinci, bayan taci ta shayar da babyn ta, daga nan ba jimawa bacci yayi awan gaba da su......

Mu had'e a next page.
[14/05, 9:56 pm] AMNA: ADALILINTA 💜❤💜

BY AMINA BAYERO 💜❤💜

Typing........

*146*

Sai wajan goma zahra ta samu aka yi mata wanka ita da babyn ta sanan taci abinci, bayan taci ta shayar da babyn ta, daga nan ba jimawa bacci yayi awan gaba da su......

To fa zahra tayi bacci sosai ba ita ta farka ba sai wajan qarfe 11 na safe. Shima ba tashi kanta bane kukan abdul ne da kiran da mashkhur yake mata a waya ne ya tayar da ita. Tana tashi ta shiga toilet tai fistari sanan tai brush, bayan ta gama ta futo a hanzarce ta d'auki abdul da yafe ta faman kuka ta fara rarrashin sa, bayan ta rarrashe shi yayi shiru rigar ta ta bud'e sanan ta fara feeding d'in shi.

Bayan ta gama feeding d'in abdul wayarta ta d'auka ta kirawo mashkhur, sun d'an jima suna hira sanan tai sallama da shi. Bayan zahra tai sallama da mashkhur miqewa tai ta fuce domin sauka qasa taci abinci. Ilham nana ammi mama su hud'u ta samu a qasa suna breakfast. Itama zahra samun waje tai ta zauna a gefan ilham ta d'auki spoon ta fara cin abinci.

Bayan sun gama cin abinci ammi ce tace to zahra ya kamata de a farayi miki wanka jegoba nan tinda kin fara samun sauqi koh?. Girgiza kai zahra tai tare da cewa aa ammi ba yanzu ba de, mama cewa tai hmmm ni kam bazan iya ganin wanan abun ba bari mu tashi mu fara shirin tafiya. Ah haba dai ai tafiya ba yanzu ba abinda ko naman suna ba'a soya ba.

Kuma gashi naga har yanzu zahra bata wuce gajiyar suna ba, bazata iya tafiya kaduna yau fa. Cikin mamaki zahra tace kaduna kuma ammi akan me zanje kaduna mai zanyi acan. Wani kallo ammi ta watsawa zahra tare da cewa gidan ku zakije kiyi acan ba gidan ku bane, to bari kiji ni bazan iya da wannan rashin mutunci nake ke da mashkhur ba.

Wai nan sunan kin tawo wanka jego amma kusa kullum yana maqale da ke, tun kafin ku dawo da aiki baya gwara kin tattara kin koma kaduna can, tinda ni kun dena jin kunya ta ai sai kuji kunya mama. Kai ammi ni gaskiya bana son tafiyar nan, bari naje wajan dady na gaya mai dole yace a barni. Maza kije ki fad'a ni kuma ba sai na gaya mai abinda yasa nace sai kinje can kaduna.

Mama kuwa taji dad'in hakan sosai sabida itama tun farko taso zahra tazo wanka jego wajan ta sabida ta gyarata sosai, amma tana kunyar su ammi shi yasa ma bata ce zahra ta dawo ba, sai gashi yanzu allah ya dubi zuciyar ta ammi da bakin ta tace ta bisu kaduna. Kai ni gaskiya ammi bazan iya tafiya daga nan har kaduna ba.

Haba aunty zahra wai sabida me bakya son zuwa kaduna gida ne sai kace mutuwa ake acan, nana ta fad'a tana tsare zahra da ido. Hararar nana zahra tai sann tace ban sani ba, kai zahra ni dai ban sanki da musu ba amma yanzu duk kin 6aci, ammi ta fad'a cikin mamaki. Haba zahra ke da gidan ku kike gudun zuwa ai ba a mota zamu koma ba tinda bakya son tafiya mota.

Sai mu tafi ta airplane zahra fuska ta duk ta canza alamun de bata gamsu ba. Ana haka hjy kaka ta shigo, nan da nan zahra ta koma kusa da ita cikin shagwa take kai mata qarar ammi. Hjy kaka da farko bata goyi bayan hakan ta amma daga qarshe dataji dalilin tafiyar kuma taga maman zahra tana son tafiya dole ta amince ta hau rarrashin zahra.

Haka hjy kaka da ilham suka hau rarrashin zahra har sai da ta amince zata bisu kaduna. Mama da nana harma da ragowar qanan zahra sunyi farin ciki sosai jin zahra zata bisu kaduna.
To haka dai mama da ammi suka hau aiki soya naman sunan abdul, har sai wajan magriba suka kammala,...

Washe gari.

Washe gari fa zahra ta murtuke ido tace ita wlh karma a sai ticket kan ta ciwo yake mata bazata tafi yau ba sai gobe. Zahra tana sane tai wanan iskanci ba wani ciwan kai take duk sabida jiya mashkhur bai zo ba kuma yau take sa ran zuwan sa, bata gan shi ba kuma za'a tafi da ita. Daga qarshe dai sai nana da qannan tane akace su fara tafiya driver ya kai su ta mota.

Zuwa gobe in zahra ta samu sauqi sai ita da mama su tafi. Haka su nana suka had'e kayan su da dai abubuwan da ya kamata da naman sunan da za'a rabawa jama'a sukai gaba. Zahra kuwa lokacin da mashkhur yazo zama sukai suka sha hirar su sosai sun jima, tana so ta gaya mai abinda yake faruwa amma ta kasan dan haka bata fad'a mai ba haka sukai sallama ya tafi gida cikin farin ciki.

Washe gari.

Zahra ma ta fara iskanci iri-iri akan ba zataje ba har ammi tayi fushi

Please Login or Register in order to submit comment