Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

YA KAWO SOYAYYA MAE ZAIFI TSAKANIN ABDUL MAJID DA ZAHRA?. WACECE ZAHRA?.

Ku biyoni domin ku sami amsoshin tanbayoyin nan.

SHAKARUN BAYA DA SUKA SHUD’E........
Wanene Malam Muhammad? wato mahaifin alhaji abubakar.
Malam Muhammad cikakkyan d’an garin kano ne. Yayi karatin arabi da bako. Amma karatin arabi yafi yawa’ a kan na boko.

Iya scondry suchool ya tsaya a boko, b’an garan karatin muhammadiya wato islamiya, yayi karatu mai zurfi, yayi saukar al Qur’an da wasu littatafan addini. Malam abubakar cikakkyan d’an kasuwa ne. Yana da babba shago a kwari. Kuma yana da azziki dai-dai gwar-gwado.

Mahifinsa da mahaifiyarsa su biyu suka haifa shida qan warsa sadiya.
Malam ya had’u da hajiya fatima wato hajiya kaka, ranar wata asabar sunzo siyayya shagwan su. Kuma cikin qanqanin lokaci suka saba da juna, har aka fara maganar aure.

Hajiya fatima (hjy kaka) Iyayan ta haifafun‘yan KADUNA ne. Amma ma zauna kano ne. Wato a kano suke zaune. Mahaifin hajiya fatima yana da rufin asiri dai-dai gwargwado. Sanar sa shine ya fitar da shinkafa zuwa wasu garuruwan. Kuba su biyu ya haifa ita da qanwarta SUMAYYA.

Wannna kenan.

Maganar auran Hajiya fatima da malam abubakar ta kankama. Kuma ankai kud’i da lefe, biki ya rage sauran sati d’aya.
Ranar asabar aka d’auran auran hajiya fatima (hjy kaka) da malam abubakar. An kai amarya d’akin ta lafiya.

Tom haka hajiya fatima da mijinta malam abubakar zuka zauna cikin zaman lafiya da farin ciki. Shekararsu d’aya da aure ALLAH ya azirta su da d’a namiji wato Alhaji Abubakar (DADY). Zoka ga farin ciki a wajan malam abubakar.

Ranar suna dady yaci sunansa abubakar. Haka hajiya fatima tai-ta rainan sa cikin kulawa da qauna. Hajiya fatima bata sake haihuwa ba sai bayan shekaru biyar. Bayan shekara biyar ta sake haifan d’an ta umar faruq. Alokacin dady ma ya faru zuwa makaranta.

A boko yana prym 1. Shima yayi farin ciki sosai da haihuwar hajiya fatima, sabida yana san qani. Haka hjy fatima tai-ta rainon yaranta tana basu tarbiya mai kyau. Kuma malam Abubakar yana nuna musu soyayya komai ya samu nasune. Duk abidda suke so yana siya musu.

Sai da haiya fatima tai wata shekara biyar d’in kafin ta qara samun haihuwa, Ta qara haifar d’anta namiji. Kuma ranar suna yaci sunansa musa. Bayan hajiya fatima ta haifi musa da sati biyu, qan warta ta sumayya ta haifi kyakyawar ‘yar ta mace, wato AMMI.

Ansha suna sosaii kuma ranar suna ammi taci sunanta maryam. Haka hajiya fatima da qanwarta sumayya sukai ta rainon ‘ya’yansu cikin kulawa. Bayan shekara d’aya da wasu watanin hajiya fatima ta yaye musa. Alokacin dady yana da shekar goma sha d’aya (11),

Qaninsa umar yana da shekara biyar, shi kuma musa yana da shekara d’aya da wata biyu. Bayan ta yaye musa qanwarta sumayya wato mahifiyar ammi, itama ta yaye ammi kuma ta kawowa hajiya fatima Wato hjy kaka yaye.

Haka hjy fatima ta kulawa da musa da ammi. Bayan an kawowa hjy fatima yayen ammi da sati d’aya ALLAH yayiwa sumayya wato mahifiyar ammi RASUWA. Zokaga tashin haankali da firgici a wajan dangi, musamman ma hajiya kaka tafi kowa jin mutuwar nan.

Bayan an share makoki hajiya kaka ta qeqashe qasa tace ita zata riqe ammi, tundda sumayya ita ta bawa hajiyar ta tun kafin ta rasu. Ba yandda aka iya haka aka bata duk da mahifin ammi bai so hakan ba, sabida ammi ce kawaii ALLAH ya azirtashi da ita, ita ka d’ai sumayya ta haifa mai.

Haka hajiya kaka ta d’auki ammi da had’a da musa tai ta rainonsu tana basu kulawa. Tun ammi tana kuka akan rashin ganin mahaifiyar ta sumayya harta haqura ta dae na. Haka ta d’inga ganin kamar hajiya kakace mahifiyarta sabida tsananin kamar da sukeyi da sumayya...........

Wannan page d’in na sadaukar da shi ga ~ummu Abdullah🌹🌹🌹😘 sabida itama kullum in nayi posting sai tayimin comment........
ga wadda yasan yana yimin comment kullum yaga ba sa d’aukar mai da page ba tom yayi qauri zan yimae.

ADALILINTA 💜❤️💜

BY AMINA BAYERO❤️💜❤️

*Ina godiya ga masoyana masu bibiyar littafin nan mai suna ADALILINTA. ina yimuku fatan alkhairi. Kuma da fatan zauku cigaba da bibiya ta harna sauke littafin ADALILINTA.

*Dan ALLAH in kun karanta ku d’inga comment........pls, sabida hakan shi zai bani qarfin guwai cigaba da rubutawa.💜❤️💜

*Ga masu buqatar littafin ADALILINTA, sai su biyoni ta wannnan number 08142246343 WhtsApp kawai bandda kira. Kuma free book ne bana kud’ib, new book.

New book on 2023.
[11/06, 22:24] Maman Xuhra: “ADALILINTA”
ADALILINTA 💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

Typing...........

* Page 14*
Haka ta d’inga ganin kama hajiya kakace mahaifiyarta sabida tsananin kamar da sukeyi da sumayya.............

“Tom haka rayuwa fa tai’ ta juyawa ammi da musu suka qara girma, dan harsun fara zuwa makaranta.
In kaga ammi sai ka rantse yan biyu ne “iita da musa, sabida kamar da suke.

Dama musa kamarshi d’aya da hajiya kaka.
Ammi ta shaqu da ‘yan uwanta sosai musumman ma, musa dan koh abinci tare su keci . Suma su dady da umar haka suke son ammi sosai koh abu suka samu ita suke kawowa.

Dan har kud’insu suke cirewa su siya mata abu. Musamman ma dady da yake a lokacin ya girma zai’ yi shakara sha biyar. Ban garan malam Muhammad mahifin su dady, kuwa duk ya fifita ammi ga duk ‘yayansa dan kamar shi ya haifeta.

Hakan ba qaramin dad’i yayiwa hajiya kaka da danginta ba. “Toh haka rayuwa tai, ta juyawa, cikin farin ciki da sab’a nin haka.
A halin yanzu duk yaran Hajiya kaka sun girma.

Dady zai’yi kimanin shekara 24, qaninsa umar zai yi shekara ashirin, shikuma musa da ammi zasuyi shekara 15. A lokacin dady ya zama cikakkyan d’an kasu Kuma gashinan yana daf da kammala karaintin sa, sabida yayi karatu mae zurfi.

Ana cikin haka bikin ‘yar aminin malam Muhammad wato malam balarabe ya tashi. Aminin mlm Muhammad ne sasai koh kasuwacin su tare sukeyi. Alokacin bakin ‘yar aminnin dady ya gabato, ya rage saura ‘yan kwanaki kuma ya kasance ba a garinnan za’ai bikin ba.

Acan Adamawa za’ai,, dama aminnin malam balarabe d’an garin adamawa ne. Alokacin hajiya kaka bata da lafiya, dan haka aka yanke shawarar za’a bar hajiya kaka da ammi a gida, za’a tafi da qanwar malam Muhammad wato sadiya.

Alokacin dady yana da jarabawa A jami’a dan haka shima baza’a da shiba, sai dae a tafi da su umar da musa, da kuma qanwar malam Muhammad, sadiya.
Ranar jumm’a bayan sallar jumma’a suka kama hanya zuwa adamawa.

Basu suka isa adamawa ba sai da daddare. Washe gari asabar aka sha d’aurin aure. Ranar asabar malam Muhammad da sadiya qanwarsa da kuma umar da musa suka shirya domin dawowa kano.

Sun sha tsaraba kala-kala ga karamci da aka yimusu. Haka suka kama hanyar dawowa kano. Suna tafiya a mota sun kusan shugowa garin kano, Ai kuwa motar su tayi karo da tifa. INNALILLAHI’ WA’INNA’ILLAHIRRAJI’UN.

Ai duk cikin mutanan matar nan ba wadda yayi rai duk sun mutu. daga cikin su kuwa harda malam Muhammad da sadiya qanwarsa gasu umar da musa.
Kaii zo kaga tashin hankalin da ba’a samasa rana. Mutur nan ta girgiza hajiya kaka dasu ammi.

hjy kaka kuwa da ammi har zuwa dady ba wandda bae yanke jiki ya fad’a ba, da yaga gawar su musa. 6an garan mahaifiyar mlm Muhammad da sadiya kuwa tundda taga gwarai ‘ya’yanta da jikokonki zuciyarta,ta buga ta fad’i qasa matacciya.

Innalillahi’wainna’illahirraji’un. Ai ranar dangi da ‘yan uwa da abokan arziqi sun girgiza sosai. Dama mahaifin malam Muhammad ya jima da rasuwa. Haka aka share makoki ciki tsananin rashi da tashin hankali.

Ban garan hajiya kaka bata cewa umm bare aa. Tun lokacin da ta far’fad’o batayin magana sae dae tabi kowa da ido. Ko addu’a ma a zuciyarta takeyi. In ta zauna a waje bata mosti inndai ba lokacin salla ne yayi ba ko kwanciya za tai dan ko ta kwanta ma bata iya bacci.

Ban garan dady kuwa shima mutuwar ta girgiza shi yayi kuka har sae da hawayan sa suka dae zuba. A bisa dole ya fara danne mutuwar dan ya rarrashi mahifiyarsa da qanwarsa ammi. Itama b’an garan ammi abin ba’a cewa komai dan taqi ci taqi sha kullum zan canta musa, umar, babansu.

Daga ammi har hajiya kaka sai dady yayi musu dole suke samu susa abincci abakin su, haka yay ta rarrashinsu da basu haquri da nuna musu ALLAH ne ya basu su musa, kuma ALLAH ne ya karb’a abinsa, dan yafimu son su.

A hankula ahankula su hjy kaka da ammi suka fara warewa. Malam balarabene aminin dady ya d’auki duk wata d’awai niya gidan malam Muhammad. Kama daga abinci kud’in makarntar ammi, da kuma kula da karatin dady.

Duk da kuwa malam Muhammad ya barwa su hajiya kaka kud’in da dama. Haka rayuwa tai-ta, juyawa, hajiya kaka tana ta kulawa da ragowar yaranta dady da ammi. Musamman ma ammi, tundda a lokacin dady ya girma sosai.

Bayan mutuwar su musa da shekara guda, dady ya gama karatun sa. Amma dae yafi mae da kankalinsa wajan kasuwanci. Dan a halin yanzu ya zama babban d’an kasuwa, dan yabud’e manya-manya shaguna a kasuwa daban-daban.

Kuma a lokacin ne ALLAH ya jarafci Dady da san ammi. Shima kansa dady yana mamakin yadda ya kamu da san ammi lokaci guda, duk da yana yimata kallan qanwarsa uwa d’aya uba d’aya. Alokacin ammi ta girma ta zama ‘yan mata, za tai kimanin shekara sha shida (16 years) shi kuma dady zae yi ashirin da biyar (45 years).

Ammi kyakyawa ce sosai, black beauty ce. Tana da tsananin kyau sosai yadda duk wandda ya ganta sai ya kyasa. Shi kuma dady farine tas dan kamarsa d’aya da malam Muhammad bata indda ya baroshi. Ita kuma tana kama da mahifiyarta sumayya, shiyasa kamarsu zato d’aya da hjy kaka.

In dae kaga hjy kaka saeka rantse ita ta haifi ammi.
Tun dady yana iya boye soyayyar ammi a ransa harya dae na b’oyewa, yanzu afili yake nuna mata soyayya. Hajiya kaka dae tana ganin su amma ta zuba musu ido. Dady kuwa sae da yayi nasarar sace zuciyar ammi. Ita yanzu duk duniya ba wadda take so kamar dady.

Ta dae na kula kowa bata jin kowa a zuciyarta sai dady. Dady da kansa ya samu hjy kaka ya sanar da ita yana san ammi kuma ta aura mae ita. Hajiya kaka kuwa tace sae ammi ta yadda zata bashi ita. Kuma sai taji ta bakin ammi.

Ai kuwa haka akayi hjy kaka ta samu ammi da maganar. Duk da kunyar ammi sae da ta futo ta fad’awa hjy kaka itama tana san yaya abubakar. Hajiya kaka ba qaramin farin ciki tayi da jin haka ba. Dan haka takanas ta kano, taje ta sanar da mahifin ammi da sauran ‘yan uwa.

Mahifin ammi kuwa yayi na’am da murna sosai kuma yace ya bawa hajiya kaka wuqa da nama tindda kamar ita ta haifi ammi ita za tai iko da ita.
Bayan mutuwar mahaifiyar ammi baban ammi ya qara aure, kuma harya samu ‘yaya shidda. Uku maza uku mata.............

Wannan page d’in na sadaukar da shi ga twins wato hassana da hussaina becos i like yours, 🥰kuma suna yimin comment........

Typing.......

ADALILINTA 💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

Free book💜❤️💜

*ina godiya ga masoyana masu bibiyar wannan littafin na ADALILINTA, ina yi muku fatan alkhairi. Kuma da fatan zaku cigba da bibiyata harna sauke littafin ADALILINTA.💜❤️💜

*Dan Allah in kun karanta ku d’inga yin comment....... pls. Sabida hakan ne zai bani qarfin guwar cigaba da rubutawa.💜❤️💜

ADALILINTA 💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

Typing..........

*Page 15*
Bayan mutuwar mahaifiyar ammi baban ammi ya sake aure, Kuma harya samu ‘yaya shida uku maza uku mata..........

‘Yan uwama da abokan arziki sunji dad’i maganar, auran dady da ammi, kuma sun amince.
Kamar wasa-wasa sai gashi an fara qoqarin bikin ammi da dady.
Biki ya qarato kai har, an kai kud’in auran ammi gidansu mahaifinta. Dady kuma ya had’a wa ammi lefe na bajinta, na azo a gani.

Biki ya rage saura sati d’aya. Hajiya kaka ta siyarwa ammi kayan d’akin na bajinta. B’an garan mahifintama haka. Shima dady ya siyar mata, abun dai ba’a cewa komai har sae da kaya d’aki da na kicin, sukayiwa ammi yawa.

Ranar asabar aka d’aura auran Abubakar da Maryam, wato dady da ammi. Ai kuwa anyi biki nagani da fad’a anci ansha, kuma an gama lafiya. Ankai amarya d’akain mijinta.
Dady da ammi sunyiwa hajiya kaka magi ta biyosu su zauna tare, amma hjy kaka ta qeqashe qasa tace bazataba ita a gidanta zata zauna.

Dady kuma dayaga haka ya d’auko mata ‘yar aiki tana tayata zama.
6an garan dady da ammi ku suna zamansu lafiya kuma suna shan soyayyar su. Bugu da qari dady yana kula da ammi yadda bakwan zato.

Duk abidda takeso shi yake mata wadda bataso kwa ya barshi. Ko da baki ammi ta nuna abu indai tana so sai dady ya siya mata. Itama ammi tana kula da mijinta tana nuna mae qauna sosai, koh kad’an bata bari ransa ya b’ace. A ta qaice dai suna kula da junnan su suna bawa junansu kuwala sosai.

Haka rayuwa tai, ta juyawa,kuma ammi da dady suna cikin farin ciki. Har kulluma basa gajiya da yiwa hajiya kaka magiyar ta dawo, ita kuma bata gajiya da ce musu su rabu da ita, a gidanta bazata dawo ba.

SHEKARA D’AYA.
Sai da ammi da dady sukayi shekara guda suna shan soyayyar su sannan ammi ta samu ciki.
Hmmm zo kaga murna da faran ciki a wajan dady. Dady ya kasa tsaye ya kasa zaune sabida farin ciki. 6an garan hajiya kaka itama tayi murnada faran ciki sosai .

Haka dady da ammi sukai ta rainon cikin nan cikin kulawa da qaunar juna. Dady dae ko tsinke baya bari momy ta tab’a. Kulawa yake nunamata fiye da farkwan auransu. Wataran ma qiri-qiri zai qi fita wae zama zaiyi ya kula da ita.

Haka su kai ta rainon cikin har watan haihuwarta ya shigo. Lokacin da cikinta ya shiga watan haihuwa hajiya kaka ta tattaro kayanta, ta dawo domin kula da ammi kafin ta haihuwa. Ammi dae yanzu cikin ya girma haihuwa ko yau ko gobe.

Ranar wata alhamis da daddare ammi ta fara naquda. Haka dady da hajiya kaka suka d’auke ta, izuwa azibiti ankali a tashe. alokacin wajan qarfe biyun dare ne. Ana kaita asibiti aka shiga d’akin haihuwa da ammi.

Dady kuwa da hajiya kaka suna daga waje suna tayiwa ammi addu’a ALLAH ya sauketa lafiya. Suna cikin wannan hali a lokacin ba afi minti Ashirin ba sukaga likita ta futo fuska d’auke da fara’a tana cigiyar wanda suka kawo ammi.

Har dady da hjy kaka suna had’a baki wajn cewa ga munan lafiya dae koh? Ta saukane. Mumushi likitan tayi tare da cewa Congratulations. Allah ya sauketa lafiya ta samu d’a namiji. Ai tana rufe bakinta dady ya kalli gabas yayi sujjada yana godewa ALLAH.

Itama kaka hamdala ta shiga yiwa Uban giji.
Ai kuwa likin tasha tukuici a wajan dady. Daga haka ta karb’i kayan baby ta shiga ciki. Batafi minti goma ba ta futo hannunta d’auke da baby. Tana karasowa ta miqawa dady.

Yasalam abidda dady ya iya furta kenan lokacin da yayi tozali da kyakyawar fuskar baby. Farine tass har wani ja yake. gashi kyakyawa na ajin farko. Ko su kansu likitocin da suka karb’i haihuwar ammi sai da suka, jinjina kyau da hallita irin ta baby. Ga shinan koshashe kuma lafiyayye abiddai ba’a cewa komai.

Sabida inna tsaya gaya muku irin kyan baby nan zamu iya kwana😁. Washe gari da safe da aka duba ammi da babyn ta akaga lafiyarsu lau aka sallame su. Nan da nan ‘yan uwa da abokan arziki aka cika gidan, daga wanna ya fita sae wannan ya shigo.

Duk wadda yayi tozali da babyn ammi sai ya tofa al barkacin bakinsa sabida tsananin kyawunsa. 6an garan hajiya kaka kuwa baki yaqi rufuwa sae murna take tayi jika. Dady kuwa jikinsa sae rawa yake shine siyo wannan siyo wannan.

Haka hajiya kaka tai, ta kula da ammi da babyn ta har ranar suna tazo.
Ranar suna kuwa baby yaci sunan kakansa wato mahifin dady, mijin hajiya kaka kenan. Yaci suna shi MUHAMMAD ake mai kara da MASHKHUR. Anci ansha harda masu guzirin abincci.

Gaskiya koni amina bayero na shaida kud’in dady sunyi kuka a sunan Muhammad mashkhur. Sabida dady raguna hud’u ya yanka wa mashkhur na suna. An gama suna lami lafiya kowa ya koma gidansa. Hajiya kaka kuma ita, ta zauna takewa mashkhur da ammi wanka.

Wata irin kulawa dady da kaka kae harma da ammi suke bawa mashkhur dan ko quda basa so ya zo indda yake. Barema suji kukansa ai nan hankulansu zai tashi. Kwata-kwata Basa bari ko quda ya ta6a mashkhur. A haka dae sukayi arba’in suka yada wanka jego.

Bayan an gama wanka jego da sati d’aya hajiya kaka ta tattara kayan ta zata koma gidan ta. Ba irin magiyar da dady da ammi basuyiwa hajiya kaka akan ta zunaba. amam ta fafire tace sae ta koma gidan ta.

Haka hajiya kaka ta koma ba’a san ransuba. Itama hajiya kaka kanta bataji dad’in tafiyar taba sabida yadda take son mashkhur.
Haka ammi da dady sukai ta rainon mashkhur cikin kulawa.

Amma hajiya kaka duk satin duniya sai tazo duba jikanta mashkhur. Haka ammi da dady zasuyi ta yiwa hajiya kaka dariya da sha qiyanci, wae taqi ta dawo ta zauna dazu amma duk sati tana kan hanya zuwa.

Yanzu mashkhurwatan sa biyarda haihuwa. yayi qiba yayi mulmul, zallar madarar kyaun sa ya sake futuwa. Yara har rububin d’aukar sa suke. Ammi kuwa bata bari a d’auki mashkhur sabida bakin mutane yayi mae yawa kowa ya ganza sai ya yaba kyan sa. kullum sai ammi ta tofeshi da addu’a tsari sabida baki da mayu.

Hajiya kaka kuwa da taga baza iya ba tattaro kayanta tai ta dawo gidan su ammi. Sabida irin sandda takewa mashkhur kullum zancansa da tinaninsa take. Haka ta dawo ta cigaba da ba shi kulawa. Gaskiya mashkhur yana shan gata sosai duk da kuwa bae girma ba.

Hajiya kaka dae ta dawo gidan su ammi da zama. Kuma haka suka cigaba da zamansu cikin faran ciki da qaunar juna Shikuwa mashkhur kullum kyansa qara bayyana yake, yana girma yana qara kyau. Ga wayan tsiya. Mashkhur wayo ne da shi sosai...........

Wannan page d’in na sadaukar da shi ga meenah Muhammad. Kullum in nai posting tana yimin comment............

Typing.........

ADALILINTA 💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

*Ina godiya ga masoyana masu bibiyar littafin nan mai suna ADALILINTA. ina yi muku fatan alkhairi. Kuma da fatan zaku cigaba da bibiya ta harna sauke littafin ADALILINTA.💜❤️💜

*Dan ALLAH in kun karanta ku d’inga comment...... pls. Sabida hakan shi zai bani qarfin guwar jigaba da rubutawa.💜❤️💜

Gamasu buqatar littafin ADALILINTA da nayi posting su gani kuma su karanta.sae suyimin magana ta wannan Number 08142246343 WhtsApp kawai badda kira. Kuma littafin free book ne bana kid’i ba. New book.

On book on 2023.
[11/06, 22:24] Maman Xuhra: “ADALILINTA”
ADALILINTA 💜❤️❤️

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

Typing...........

*page 16*
Yana girma yana qara kyau. Ga wayan tsiya, Mashkhur yana da wayo sosai......

Tun yana yaro haka yake da wayo, baya yadda kwata-kwata wasu su d’auke shi in dae ba ammi da dady ba sae kuma hajiya kaka, daga su baya bari wani ya d’auke shi. Kuma bashi da kuka sosai, gashi baya tsoran shan magani komai d’acin sa. Ba abidda yake bawa mashkhur tsoro.

In dae kaga mashkhur yana kuka tofa ba qaramin abu a kae mae ba. Ko kuma wasu ne suka d’auke shi. A ta qaice dae tun yana yaro yake jarimi.
Toh haka rayuwa taita juyawa mashkhur yana qara kyau da wayo, kuma kullum girma yake qarayi.

A halin yanzu dae mashkhur yayi shekara d’aya (1 years). Harya fara qoqarin tafiya, kuma yanzu baya yadda yasha nono sai dae a bashi madara ko costom, ko dafafan kwai ko kifi da dankalin turawa. ko kuma inyaga su ammi suna cin abinci yay ta zura hannu shima yana d’an ci.

Jikinsa yayi wani irin luwai-luwai. Sai dae kawai d’an ya rage haske fata ba kamar yadda haka haifeshi ba. Farine amma ba kamar da ba. Fata shi har wani kyalli take sabida tsabar jin dad’i da hutu. Yanzu dae mashkhur ya yaye kansa ya dae ba shan nono.

In ammi ta bashi bama yasha a dole ta haqura itama ta yaye shi ga bad’aya.
Ban garan kasuwanci dady kuwa sae bud’ewa yake dan yanzu dady ya zama babban d’an kasuwa. Yawanci duk wasu states-states d’in Najeria ya bud’e shago, dady dae yayi suna sosai.

Alokacin ne tafiya ta kama dady “zuwa kaduna domin yin wani mitten da wasu baqin turawa a kaduna da yake yana da manyan shaguna a can. In ya tafi sati d’aya (1 Week) zai yi acan.
Ranar asbar da safe dady yabi jirgi kaduna. Bayan sunyi sallama da hajiya kaka da ammi, ya tafi ciki da kewar mashkhur d’ansa d’aya tilo.

Bayan dady ya sauka garin kaduna ya kama musu hotel shida baqin sa turawa. Dady kwanan sa d’aya a kaduna bakin sa suma suka qaraso. Kuma washe gari suka fara mitten. Bayan sun kammala mitten d’in ranar ko wanan su ya tafi d’a kinsa, da zummar gobe zasu cigaba da mitten d’in.

Dady kuma yana shiga d’akinsa yayi wanka ya haye kan bad. Yana kwan tawa kawai yaji duk duni ba abidda yake san ci irin kyad’a da rogo, duk da kuwa ba cinsu yake sosai ba. Ba shiri ya tashi ya fita domin nemo gyad’a da rago.
Daya fita sai da yayi nisa da hotel d’insu kafin ya had’u da mai roga da kyad’a.

A hanzarce ya qarasa domin ya siya. Yana zuwa yabawa mae rago da kyad’a umarni ta zuba mae. Wata budurwa da take tsaye a wajan itama tazo siyan rogo da gyad’a ta zubawa dady ido kamar mayya.
“Shikuwa dady bema san tana yiba, kawai danna wayarsa yake a nitse.

Dady jiyayi yana jin qishirwa, dan haka yacewa mae rogo bari ya shiga kantti kusa da ita ya suyo ruwan. Bae fi minti biyar ba ya fito daga kanttin bayan ya siya ruwan ya sha. Yana qaraso wa wajan mae siyar da rogan ya zaro kud’in tare da karb’ar laidar rogan.

Daya miqawa mae sai da rogan kud’in rogan ce mae tai wai an biya mae kud’in. Cikin mamaki dady yace anbiya mun kud’in toh waye ya biya min?. Nuna mae can bayan sa tayi tare da cewa wacca budurwar ce gata can a bayan ka ita ta biya ma.

Cikin mamaki dady ya juya domin ganin wacece. Ba kowa bace face wanna budurwar da take ta kallan dady d’azu da yazo siyar rogo. Kallanta yayi sae jifan dady da murmushi take. Abin ya d’aurewa dady kae sosai sae kallanta yake ko zae gane wace amma ina, dan dady yasan bae tab’a ganinta ba.

Tana da d’an haske amma ba sosai ba kuma ka ganinta zaka san tana qarawa da mae . Ita ba mae tsayiba ita ba gajeriya ba. Haka zalika ita ba mae qiba ba ita ba siririya ba. Bata da wani hanci sae dai idanuwa, bakinta yana da d’an girma, tana da kuma fad’in fuska.

A han zarce dady ya qarasa indda take tsaye dan ya tanbaye ta mae

Please Login or Register in order to submit comment