Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauri yace momy ina wuni?. Ai ba iya momy ba har ammi abin ya bata mamaki shida mashkhur koh kallan momy bayayi, tindda suke da momy koh kallo bai ishe taba. Washe baki momy tayi tare da cewa lafiya qalau yayan abdul ina zuwa haka?

Ata qai ce mashkhur yace masallaci zani, tom shikenan a dawo lafiya, daga haka mashkhur ya wuce masallaci. Ita dae ammi abin ya d’aure mata kai sosai, tinanita shiga yi kala-kala. A ganinta Addu’ar da takewa mashkhur ne ALLAH ya karb’a ku kuma ya dai na taurin kai, haka dae ammi tai, ta tinani kala-kala amma bata kawo komai game da hakan ba, kawai dai tafi tinanin mashkhur halinsa ya canza.

Tom tindda ga ranar da momy ta bawa mashkhur maganin boka, bai tab’a bashin zuwa gai sheta ba koh wace safiya sae yaje ya gai she da momy. Kai yanzu ta kai ta kawo mashkhur har part d’in ammi yake zuwa suyi hira koh ta taya shi home- work. Daga dady har ammi abin yana basu mamaki sosai.

Amma kwata-kwata basu kawo wani mumunan tinanin ba. Tom ana cikin haka ammi ta samu ciki, kowa yayi farin ciki sosai sabida ammi ta dad’e bata haihu ba tun lokacin haihuwa mashkhur bata sake haihuwa ba.
Yanzu mashkhur ya mayar da momy kamar abokiyar sa, duk abidda zai yi sae ya tanbaye ta.

Bugu da qari ma, duk abidda momy tacewa mashkhur baya musu koh taurin kai, ate a wajan yake cika umarnin ta. Amma dae duk da haka wani abun mashkhur yana mata taurin kai, da yake shi taurin kan ajininsa yake. 6an garan makaranta kuwa mashkhur ya mae da hankalin sa sosai yana karu.

Kuma yanzu ansa abdul a makaran ta tare ake kai su. Shima abdul yana da qoqarin karatu sosai abin dae gwanin ban sha’awa. 6an garan hajiya kaka ma ta lura da yadda mashkhur yake rawar qafa wajan momy itama bata kawo komai ba, kawai dae tayi tinanin ammi ce ta tirsasa shi akan ya ringa yiwa momy haka.

Tom haka wattani suka shud’e abubuwa kala-kala suna ta faruwa. Wataranar laraba da rana ammi ta fara naquda. A hanzarce hajiya kaka da momy suka tafi kai ta asibiti da yake dady baya nan. Bayan sun kai ta aka shigar da ita d’akin haihuwa. Ba jimawa likita ta futo ta karbi kayan baby. Bayan wasu ‘yan mintina likinta ta qara futo hannu riqe da baby.

Tana qarasowa ta miqawa hajiya kaka baby tare da cewa an samu baby boy wato namiji. Masha ALLAH kyakyawa ne sosai baby kamar su d’aya da abdul da yake abdul da dady suke kama. Sae da yamma aka sallami su ammi a lokacin ma dady ya dad’e da zuwa asibintin.

Mashkhur da abdul sunyi murna samun qani sosai, musamman ma abdul dan yafi mashkhur murnar samin qani wae shima zai zama yaya.
Tom ranar suna yaro yaci sunan qanin dady da ya rasu wato UMAR FARUQ. Anyi suna lafiya kuma an gama lafiya, kowa ya koma gidan sa lafiya. Haka ammi ta cigaba da rainon umar faruq cikin kulawa da kwanciyar hankali.

Kuma har lokacin Abdul bae koma wajan momy ba yana wajan ammi. Kae in mashkhur ya cewa abdul momy ce ta haife shi kuku yake sakawa harda birgima wae shi Wallahi ammi ce ta haife shi ba momy. Hakan kuwa ba qaramin b’atawa momy rai yake ba, gashi har yanzu bata sake haihuwa ba,

Gani take yanzu ammi ta had’a yara uku ita kuma bata da ko d’aya, dan ma yanzu dad’in ta d’aya ta mallakem mashkhur, kuma yana zuwa ya tayata hira ai da kad’ai ci ya isheta.
Alokacin ne aka tashi bikin qan warta saratu amma dady qiri-qiri ya hana momy zuwa bikin.

Momy kuwa tace Wallahi sae taje dan bai isa ya raba ta da‘yar uwar taba, shi kuwa dady yace Wallahi in dae ta tafi karta dawo mai gida ya sake ta. Dady ba qaramar tsana yayiwa saratu ba tun sandda tazo ta kawowa momy maganin boka, dady gani yake kamar saratu ce take koyawa momy zuwa wajan boka..............

ADALILINTA 💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

*Page 25*
Dady gani yake kamar saratu ce take koyawa momy zuwa wajan boka........

Momy tana ji tana gani dady ya hana ta zuwa bikin saratu ba yadda ta iya haka ta haqura. Ranar wuni tayi a d’aki dan baqin ciki koh waje bata leqo ba. Sae da yamma shima mashkhur ne yazo wajan ta dan suyi hira, haka sukai ta hira har zuciyar momy ta d’an yi sanyi.

BAYAN SHEKARA D’AYA.
Ammi ta sake haihuwar d’anta namiji shima kyakyawane sosai, a lokacin da ta haife shi faruq bai fi shekara d’aya ba. Ranar suna yaro yaci sunan ta ALIYU HAIDAR. Amma har yanzu duk yaran ammi ba’a samu mai kyan mashkhur ba, duk da suma suna da kyan amma duk cikin su ba mae kama da mashkhur.

Duk sunfi kama da abdul sabida da dady suke kama, shikuma mashkhur da ammi yake kama. Amma duk qannan mashkhur sunfi shi hasken fata dan su fatar su ma har wani ja take, shi kuma haske ne da shi kawai shima hasken ba qalba.
.Masha ALLAH yanzu ammi yaran ta uku, in kuma aka had’a da abdul dan wajan momy hud’u kenan.

Alokacin momy baqin ciki kamar ya kashe ta dan har lokacin ALLAH bai sake bata haihuwa ba tundda ga kan abdul majid gashi yanzu abdul d’in ma an kwace mata shi. Sam baya yadda da ita ko part d’inta ma, ba sosai yake shugowa ba ko ya shago ma baya jimawa, in dae ba ganin mashkhur yayi a can ba.

6an garan mashkhur kuwa ya qara girma kulluma qoqari yake qarayi, dan yanzu a ajinsu ma duk ya fisu qoqari. Amma fa har yanzu yana nan da taurin kansa in dae yace yana son abu yana so in kuma baya so tofa ko zai mutu bazai ba. Niku Amina bayeo nace tabb 🤔abin babbane .☹️

Tindda dady yaga mashkhur yana girma yana qara taurin kai kuma dole sae abidda yake so yake, dady ya fara qoqarin tankwara shi ta qarfi da yaji. Dan yanzu dady ya dae na bashi ko biyar kuma ya hana ammi da kaka suma su bashi koh biyar. Amma mashkhur yana zuwa wajan momy take bashi kud’i duk da kuwa itama dady ya hanata.

Yanzu dady ya miqe tsaye sosai hakan mashkhur, shiyasa mashkhur ya raye yiwa dady taurin kae, sosai dady yake hura mashkhur amma bada duka ba kuma bada zagi ba. Shiya yanzu mashkhur yake jin maganar dady duk da ba sosai ba,Amma dae yafi da.

Yanzu ba dama a gidan nan mashkhur yayi laifi sae momy tace baza ai mae fad’a ba, sun sha fad’a dady akan hakan da take. Sam momy bata ganin laifin mashkhur duk abidda yayi ita take d’aure mai giddi. Dady kuwa da yaga zata lallata mashkhur yayi qoqarin ya hana mashkhur zuwa 6an garan momy.

Amma abin ya faskara a ala dule dady ya haqura. Tom yanzu watan haidar uku a lokan ALLAH ya bawa ammi ciki, hmmm zoka ga murna a wajan momy gani take uwa cikin fari dan ji take kamar bata tab’a haihuwa ba. Tsirfe kala-kala a wajan momy wata ranama da tsakar dare zata tashi dady daga bacci tace ya suyo mata abu.

Dady abisa dole yake zuwa ya siyo mata dan har ALLAH-ALLAH yake in yaje part d’in momy kwananta ya qare ya dawo na ammi, sabida momy ba qaramin uzzira mae take ba.
Tom haka momy tai, ta rainon cikinta har ya cika watan haihuwa. Momy ta jibgo kayan baby sosai kamar haihuwar fari sae rawar qafa take.

Ranar wata asabar da safe momy ta fara naquda, kafin kaka da ammi su kai ga kai ta asibiti harta fara yunqurin haihuwa. Dan haka dole hjy kaka da ammi suka kar6i haihuwar momy a gida. Masha ALLAH, ALLAH ya sauki momy lafiya ta samu ‘yar ta mace fara tas mae kama da ita. Yan gidan sunyi farin ciki sosai da samin baby girl.

6an garan momy kuwa baki har kunne sabida ita ta fara haifawa dady ‘ya mace. Dady shima yayi farin ciki sosai da ya samu baby girl, amma sai addu’a yake ALLAH yasa kar’ta kwaso halin uwar ta. Ranar suna yarinya taci sunanta RUKAYYA. Ake mata kara da rukee. Anyi suna lafiya kuma an gama lafiya.

Tofa tundda momy ta haifi Ruqayya bata bari kwata-kwata yaran gidan su tab’a ta mussaman ma ammi, dan gani take kamar zata kwace mata rukee yadda ta kwace mata abdul. Mashkhur ne kawai take yadda ya d’auki rukee shima ba sosai yake d’aukar ta sabida mashkhur bae damu da d’aukar yaro ba mussaman ma da yaga maca ce.

Yanzu duk ‘yan gidan sun gane momy bata so su d’auki rukee dan haka kowa ya dae na zuwa d’auakar ta. Kai hatta hajiya kaka ma bata d’aukar ta. Tindda ak haifi rukee sau uku hajiya kaka ta d’auke ta, itma ammi bata d’aukar ta tindda taga alamar momy bata son a d’auke ta.

Yanzu rukee ta fara wayo amma har yanzu momy tasa taka tasam-stam akan ta. Koh abdul in yazo d’aukar ta zai fita da ita kwace ta take, wae sai tace zai je ya kaiwa uwar goyan sa ammi. Tindda abdul yaji tace haka ya dae na zuwa d’aukar rukee sabida baya son momy ta ringa, kushe ammi duk da abdul yaro ne alokacin.

Dan bazai wuce shekara shidda ba. Tom haka rayuwa tai, ta juyawa. abubuwa suna ta shud’ewa. Yanzu ruqee shikarar ta d’aya da watanni kuma a lokacin ne ammi ta samu ciki. Haka tai ta rainon cikin ta cikin kwanciyar hankali da kulawa.

6an garan mashkhur da abdul suna qoqari a makaranta sosai, musamman ma mashkhur. Dan wanna qarshan shekarar mashkhur zai yi saukar QUR’ANI duk da ba wani babba bane, kuma a qarshan shekarar zai fita daga primary. Hakan ba qaramin dad’i yakewa dady da ammi har da ma hajiya kaka. Dan yanzu mashkhur ya zama abin al faharin su, duk da har yanzu bae dai na taurin kai ba.

Kuma har yanzu mashkhur bai dai na kula momy ba dan yanzu ya mafi jin manya maganar momy akan ta ammi. Kaka kuwa ta lura da hakan dan har wajan malam Ibrahim taje ta kar6o mae rubutu. Amma koh ta bashi in yaje ya nunawa momy sae ta kwace ta zubar kuma ta hana shi sha, hadda cewa kar yayi addu’a da hjy kaka tace yayi.

Da yake momy ta mallake mashkhur duk abdda tace haka yake.
Yanzu cikin ammi ya tsufa sosai dan har ya shiga watan haihuwa, kuma a lokacin ne kawun hajiya kaka a kaduna ya rasu, dan haka hajiya kaka ta shirya dumin zuwa gai suwa. Alokacin da hajiya kaka ta shirya dady zai kae ta abdul majid yace zai bita.

Ammi da dady suka ce bazi je ba sabida makaranta. Kuka abdul ya saka harda birgima akan sae yabi hajiya kaka, hjy kaka tace su barshi ta tafi tare da ita tindda yana so kuma yau jumm’a ranar lahadi zata dawo kafin a koma boko sae ya haqura da zuwa ta asabar da lahadi.

Ba musu ammi da dady suka amince, haka su dady suka kama hanyar zuwa kaduna. Su dady sun isa garin kaduna lafiya qalau. Bayan dady yayi musu gai suwa ya huta yacewa hajiya kaka zai wuce gida ranar lahadi da safe zai zo ya d’auke su ita da abdul.

Daga haka sukayi sallam da dady ya wuce kano yabar hajiya kaka da abdul a garin kaduna. Ranar asabar akayi sadakar uku ga gida ya cika da mutane sosai koh wajan kwanciya da kyar hajiya kaka da abdul suka samu ma, ga Abdul sae kuka yakewa hajiya kaka wai shi wajan ammi zai koma.

Hajiya kaka tacewa abdul sae dai yayi haqu dan baza ta tawo da yamman nan ba. Gaskiya hajiya kaka ta na gaji da zama a gidan nan duk mutane sunyi yawa, jiya fa da kyar muka samu wajan kwanciya dan ALLAH hajiya kaka ki tawo mu koma gida, ki bigawa dady yazo ya d’auke mu. Haka abdul yay ta damun hajiya kaka da mita.

Dan haka hajiya kaka ta yanke shawarar kawai ta tawo kano. Bayan sallar la’asar hajiaya kaka ta fara shirin tawowa kano a motar haya, abdul kuwa sae cewa hajiya kaka yake ta kira dady ya d’ake su, amma hajiya kaka tace aa ita dae da kanta zata dawo, bazata wahalar da dady ba.

Sai wajan qarfe biyar da rabi hajiya kaka ta futo daga gidan mutuwa. Tana zuwa wajan hawa mota taci sa’a ta samu motar kano. Haka suka kama hanya suka fara tafiya, koh daga garin kaduna basu fita ba aka fara kiran sallar magari ba. Dan haka drive ya fita yayi sallah, abdul dae yasao yabi drive nan suyi salla amma hjy kaka ta hana shi zuwa.............

ADALILINTA 💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

*ga masu buqatar karantta littafin ADALILINTA da nayi posting sae yayi min magan ta wanna Number 08142246343 WhtsApp kawai badda kira, Free book ne bana kud’in ba kuma new book.
[11/06, 22:24] Maman Xuhra: “ADALILINTA”
ADALILINTA💜❤️💜

BY AMINA BAYERO💜❤️💜

Typing..........

*page 26*
Abdul dae yaso yabi drive nan suyi sallah amma hajiya kaka ta hana shi zuwa.............

Sae da sukayi wajan minti ashirin (20 minit) kafin drive nan ya dawo. Bayan ya dawo ya tayar da motar amma abin mamakin motar taqi tashi. Drive nan yayi iyakacin qoqarin sa amma ina motar nan taqi tashi, dan haka ba 6ata lokaci drive nan yayi gaba domin nemo mae gyara.

Su hajiya kaka da sauran ‘yan motar sukayi ta jiran drive amma bae dawo da wuriba. Tun suna jira har wasu suka fara tafiya domin samun wata motar su hau.Yanzu ta kae ta kawo, kowa ya tafi ya rage daga hajiya kaka sae abdul, har wajan qarfe tara na dare. Abdul kuka ya farayi yana cewa hajiya kaka shifa ya gaji.

Itama hajiya kakan ta gaji dan haka ta yanke shawarar su samu wata motar su hau. Suna fita suka fara tafiya hannun hajiya kaka riqe da abdul. Wajan kamar daji-daji yake kamar qauye-qauye shukoke, ne kawai a wajan kuma ba wani haske sosai hasken watane kawai sae na futulin bakin titi ne yake haska wajan.

Abdul kuwa ya qanqame hajiya kaka alamin tsoron wajan yake ji. Itama kanta hajiya kaka tsoro takeji sabida wajan abun tsoro ne. Sauti suka fara ji a hankula- a hankula alamin taku mutum. Tsayawa hajiya kaka tae cak tare da qanqame abdul da hannuwan ta biyu. Dan hajiya kaka ta kasa motsi ma, sabida tsoro.

Da k’yar hajiya kaka ta iya juyawa 6an garan da take jin sautin takun mutum, shi kuwa abdul ya qanqame hajiya kaka ya rintse idon sa sosaii. A hankula hajiya kaka ta qarasa juyawa 6an garan ciki da fargabar mae zata gani. Mamaki ne ya kama hajiya kaka sabida abidda idon ta ya gane mata.

Wata matace fara tas kamar ba bahaushiya ba, sabida kyan ta da haskenta. Hijab ne ajikinta har qasa, madai dai ciya ce matar ita ba siririya ba haka zalika ita ba mae qiba ba. hannun wannan matar ringume da towel fari. Ajiyar zuciya hajiya kaka tayi, sabida kawai jikin ta ya bata ba cutar da su zatai ba. Mayar da kallan ta hajiya kaka tai kan abdul tare da cewa,

Abdul d’ina bud’e idonka kaji, aaa hajiya kaka ni dae tsoro nake ji . Bakomai kaji abdul ka dena jin tsoro insha ALLAH ba abindda zai same mu!!! Tana kai qarshan maganar taji sallamar matar nan cikin sanyyar muryar ta!!! Salama’alaikum. Qara binta da kallo hajiya kaka tayi tare da cewa wa’alaikissalam baiwar ALLAH, lafiya dae koh?.

Abdul majid bud’e idon sa yayi dan yaga wake magana, kafe matar yayi da ido tare da cewa ina inawuni?. Murmushi matar tayi tare da cewa lafiya qalau yaro da fatan kana lafi koh?. Girgiza kae abdul yayi tare da cewa aa ni dae tsoro nake ji so nake mu tafi gida. Rungume towel d’in tai da hannu d’aya a qinjinta,

tare da dafe kan abdul da d’a yan hannun nata,
Sannan tace ka dena jin tsoro ba abidda zai same ka kaji, Namiji ae baya jin tsoro koh, d’aga kai yayi alamin to, ya sunan ka?. Abdul majid ya bata amsa a taqai ce. Ta bud’e baki zata sake magana kenan muryar hajiya kaka ta daki kunnnata!!!

Bawair ALLAH ina tanbayar ki daga ina kuma mae ya kawo ki mufa sauri muke mu samu abin hawa dare yana sake yi. Ajiyar zuciya matar ta saki tare da sake rungume towel d’in hannunta, cikin dashashiyar murya matar tace dan ALLAH hajiya TAI MAKO nake son kiyimin. Jinjina kae hajiya kaka tayi tare da cewa ALLAH yasa na iya yimiki kuma in tai makwan bai fi qarfina ba.

Wasu hawayene suka zubuwa matar, da mamakin hajiya kaka kawae sae taga matar ta miqo mata towel d’in hannun ta, hajiya kaka sauke idon ta tae akan towel d’in, dan ganin mae ke ci?. sakin baki hajiya kaka tayi saka makwan ganin abidda ke cikin towel d’in. Bakomaii bane acikin towel d’in bace JARIRI kuma daga gani sabuwar haihuwa ne.

baki sake hajiya kaka tace keeee lafiya kika bani jariri mae zanyi da shi? Kuma wana kalar tae mako zan miki?. Dan ALLAH hajiya fara riqemin baby nan tukunna nayi miki baya ni. Girgiza kae hajiya kaka tayi tare da cewa Wallahi bazan karb’i jaririn nan ba inje ina da da jaririn?. Wasu hawaye ne suka sake wanke fuskar matar tare da cewa aaa hajiya ae ba tafiya zakiyi da ITABA.

Ki tae maka ki riqe min ITA, zan karb’e TA yanzun nan. Jikin hajiya kaka yayi sanyi kuma ta yadda da matar dan haka hannu na rawa tamiqa hannu domin karb’ar jaririyar. Sae da matar ta cire wata takadda sanna ta miqawa hajiya kaka jaririyar. Bayan ta bawa hajiya kaka baby ta juya ta miqawa abdul takaddar hannun tata.

Bayan ta bawa abdul takaddar ta juyo ta mae da kallan ta wajan hajiya kaka. A hanzar ce hajiya kaka tace bawar ALLAH Kefa nake jira, dare yana sake yi, kiyi sauri kiyi abindda zakiyi ki karb’i jaririyar ki. Hawaye ne ya cigaba da zuba daga cikin idon matar tare da cewa hajiya yau da safe na haifi yarinyar nan, ni mahifiyar tace.

Kuma ‘yata ba shegiya bace, tana da uba ta hanyar aure muka samu yarinyar nan. Mahaifin ta yana raye kuma yana da dukiyar da zai yi mata gata, sabida haifinta sananne ne a garin kaduna. Amma sai dae kashhh yarinyar nan tana cikin HATASARI ba lallai ne ta cigba da rayuwa ba in dae tana tare da ni da mahaifin ta.

Hajiya ina son yarinyar nan sosai , shima mahifin ta nasan zai sota sosai amma hajiya bani da mafitar da ta wace RABUWA DA ‘YAR NAN. Hajiya kaka binta da ido take yi tana saurarranta dan tama kasa ce mata komai kawai so take taji qarshan zancan. Shima abdul ya zubawa matar idon ya riqe takaddar da ta bashi sosai.

Kukane ya kwacewa matar amma duk da haka bata dena maganar ba, hajiya ga ‘yar ta nan na baki ita AMANA na d’an wasu lokutan, hajiya nasan zaki riqe min AMANAR ‘yata kuma na yadda da ke sosai, jikina ya bani ke ba muguwa bace. duk wani qarin bayani yana cikin takaddar da take hannun abdul.

Tana gama fad’in hakan kuka yaci qarfin ta. Jin muryar hajiya kaka tae tana cewa Wallahi baiwar ALLAH Bazan tafi da ‘yarki ba, kuma duk wani tsanani ai yana tare da ALLAH koh ki kar6i ‘yar ki ku tafi ALLAH zae nema miki mafita. Dan ALLAH hajiya ki tae maki rayuwar yarinyar nan ki tafi da ita. Zaro idanuwa hajiya kaka tayi tare da cewa!!!

Ke nifa bazan karb’i yariyar nan ba gwarama ki karb’i ‘yarki, sabida rashin tinani irin naki kin tab’a jin anyi sadakar ‘yar ne?. Cikin muryar kuka tace hajiya AMANA fa nabaki fa na wasu lokutan ba sadaka ba, mae da kallan ta tae kan abdul tare da cewa abdul majid ga qanwarka nan kana san ta koh? D’aga kae abdul yayi alamin eee.

Zaka kulamin da qanwar ka ko abdul?. Ehhh zan kula miki da ita, cewar abdul, yauwa Abdul nagode sosai. Kee malam ki karb’i ‘yar ki koh na ajiye miki ‘yar ki anan Wallahi. A fusace hajiya kaka ta fad’i hakan. Ai kafin hajiya kaka ta rufe bakinta har matar nan ta fara tafiya cikin sauri.

A hanzar ce hajiya kakq ta riqe hannun abdul tare da rungume jaririyar nan a qujinta da hannu guda, tabi matar nan cikin tauri. Matar kuwa tana juyowa taga hajiya kaka tana binta a baya, ai kuwa da gudun gaske matar nan ta taka. Hajiya kaka da taga matar nan zata iya b’ace mata, sakin hannun Abdul tayi itama ta bita a guje rungume da jaririyar.

Ahan zarce matar nan ta shige wajan bushiyoyin nan, a guje. Ita hajiya kaka da gudu ta bita, hajiya kaka tana zuwa wajan bishiyoyin ta nemu matar nan sama koh qasa bata ganta ba, kashh, kuma gashi wajan yayi daji da bishiyoyi da yawa, hanyar ta rabu kashi uku hajiya kaka bazata iya ganewa ba.

Hajiya kaka kuwa ta yanke shawarar ta fara bi ta dudduba hanyar duk da kuwa akwai duhu a wajan. Har ta fara tafiya sae ta tina da abdul da ta barshi a baya, kuma gashi dare yana sake yi. Da sauri ta juya domin taje ta d’auki abdul, hannayan ta riqe da jaririyar nan. Cikin sauri ta koma indda ta bar abdul.

Samun shi tae tsaye a wajan, hannu riqe da takaddar da matar ta bashi. Da sauri ta qarasa inda yake, tsaye tare da ruqo hannun sa, tana cewa abdul kayi haquri nasan tsoro kake ji ko?. Aaa kaka nifa na dae na jin tsoro ba maman baby nan tace na dae najin tsoro ba ni namiji bane . Ya fad’a yana nuni da jaririyar da take hannun hajiya kaka.

Hajiyar zuciya hajiya kaka tayi tare da cewa gaskiya matar nan batai mana adalci ba, yanzu ya zamiyi da jaririyar nan da ta bar mana ta gudu. Hajiya kaka tana qarasa maganar taga wani asken futular cucilan yana tun karosu, zuba ido tayi domin ganin wanene kuma ya sake zuwa. Daga ita har abdul zubawa mutumin da yake tunkaro su ido sukayi, dan ganin waye..................

Wannna shafin na sadaukar da shi ga N@uwal, sabida kullum tana yimin comment.... in nayi posting...

Kuma abidda yasa kukaga kwana biyu bana yi muku posting bani da lafiya.... kuma gashi wasu daga cikin ku koh nayi posting sun karan ba comment... sukeyi ba,🙅‍♀️ ina sane da wandda basa comment.... Ahhh to💁🏻‍♀️

*ina godiya ga masoya na masu bibiyar wanna littafin mai suna ADALILINTA, ina yi muku fatan alkhairi, kuma da fatan zaku cigaba da bibiya ta harna sauke littafin ADALILINTA...💜❤️💜

ADALILINTAA 💜❤️💜

BY AMINA BAYARO💜❤️💜

Typing...........

*page 27*
Daga ita har abdul zubawa mutumin da yake tunkaro su ido sukayi, dan ganin waye..............

Bakowa bane bace driven su hajiya kaka wandda motar sa ta lallace, suka futo samu wata motar, Da sauri driven ya qaraso inda suke tsaye. Yana zuwa yace hajiya lafiya kuka futo nan ku da na barku a mota. Nunfashi hajiya kaka ta sauke tare da cewa, Wallahi drive futowa mukayi dan mu samu wata motar.

Duk passenger sun tafi sun samu mota sun hau, muma muka gaji da jira shiyasa muka futo dan mu samu wata motar, sae gashi qaddara ta sameni. INNALILLAHI lafiya dae ko wannan wace qadda ra ce haka haka? Wallahi malam wata mata na had’u da ita, ta bani ‘yar ta kagan ta nan jaririya ce, kuma sabuwar haihuwa,

Wae na riqe mata ita na wasu lokutan, nace mata aa, kaga dae daga qarshe guduwa

Please Login or Register in order to submit comment