Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a gefan ciwan take shafawa. Dogwan tsaki mashkhur yaja tare da sa hannu ya lakuce maganin daga hannun zahra ya fara shafa mata a hanzar ce.

Da sauri zahra ta saki wata siririyar qara tare da ruqe hanun mashkhur tana cewa! Da zafi fa, kayimin a hankula. Baza'a yi miki a hankula ba, uban waye yace kice sai an sallamo ki?. Shiru zahra tai tare da gallawa mashkhur harara tana cewa eh sabida bazan iya zaman bane, shi yasa ai da zan iya zama a can da mai zai dawo da ni gidan nan na cigaba da shan wahala.

Kallo mai ciki da takaici mashkhur ya yawa zahra tare da cewa!! Ai kuwa sai kin kwanmace zaman asibi da jinya ta yarinya. Zahra kuwa a zuciyar ta cewa tai yanzu ma ka fara jinyi wlh, sai na wahalar ma da rayuwar ka.
Haka dai zahra ta daure mashkhur ya gama shafa mata maganin, bayan ya gama shafa mata na kan, qara tatso wani yayi shima ya fara shafa mata a 'yan yatsunta.


A hankula mashkhur ya fara shafawa zahra maganin a 'yan yatsunta, zahra kuwa lumshe idon ta tai sabida wani zafi-zafi da qaiqayi-qaiqayi da take ji. 6angar mashkhur kuwa ji yayi hanun zahran yayi masa wani laushi sosai, haka ya cigaba da shafawa a hankula, bayan ya gama shafa mata a hanun dama hanun ta na hagu ya kamo shima ya fara shafa mata.

Haka nan mashkhur yaji ya kasa sakin hanun zahra sai shafa shi yake sabida yana shafa hanun yanajin zuciyar shi tana mai sanyi. 6angaran zahra kuwu itama sosai take jin dad'i yadda mashkhur yake shafa mata maganin sabida ji take kamar yana sosa mata hanun nata. Mashkhur kuwa bashi ya saki hanun zahra ba sai da yaji zuciyar shi ta wuce tayi sanyi.

6angaran zahra kuwa sabida tsabar dad'in da takeji kamar yana sosa mata ciwan, har bacci yayi wan gaba da ita. Mashkhur yana d'agowa yaga zahra tana sauke nunfashi a hankula alamun bacci take, ajiyar zuciya yayi yana mamaki yadda lokaci guda zuciyar shi tai mai sanyi kawai dan ya d'an shashafa hanun zahra.

Fulo mashkhur ya janyo ya gaya mai zama yadda in ya kwantar da zahra kanta zai hau ka fulon. Bayan ya ajiye fulun a hankula ya d'an d'aga zahra ya mayar da ita tsakiyar bed d'in, ya d'ora kanta a dai-dai fulan. Zahra tana jin mashkhur ya d'agata ya gyara mata kwanciya amma sai tai shiru abinta ta sake lumshe ido kamar mai bacci gaske.

Bayan mashkhur ya gama kwantar da ita a tsakiyar bed d'in, wani filo ya sake d'auka ya ajiye a wajan qafar ta, sanan ya d'aga qafarta mai ciwan ya d'ora bayan ya d'ora mai ciwan ya d'auki d'ayar mara ciwan ya d'ora sanan ya d'auko maganin da ake shafa mata ya tatsa a hanunsa. Bayan ya gama tatsawa zama yayi a gefan santaleliyar farar qafar zahra ya fara shafa mota.

A hankuya yake shafawa zahra sabida karta ta tashi, 6angaran zahra kuwa tana jin shi tai lamo kamar mai bacci. Few minutes mashkhur ya d'auka ya gama shafa mata magananin sanan yasa hannu ya gyara mata rigar ya janyota ya sake rufe mata qafar, daga haka ya wuce toilet ya wanke hanunsa sanan ya fito.

Yana fitowa ya nufi wardrobe ya d'auko blanket guda biyu, daya ya jefa shi akan sofa d'aya kuma ya nufi kan bed d'in zahra da shi, ahankula mashkhur ya fara rufawa zahra blanket d'in. Ya rufe mata ko ina jikinta amma banda fuskar, bayan mashkhur ya gama rufa mata blanket d'in hannu yasa ya kunna blue glob d'in gefan gadan.

Nan da nan hasken bedroom d'in ya canza daga fari zuwa blue, d'akin ya d'anyi duwo ka d'an baka ganin komai sai haske blue d'in glob. Juyawa mashkhur yayi ya nufi sofa, yana zuwa ya d'auke blanket d'in sanan ya kwanta, yana kwanciya ya d'au robot d'in A. C yana d'an qara qarfin A. C d'in.

Dama shiya ya lulu6awa zahra blanket sabida A. C da zai kunna. Daga haka shima ya shige cikin bargo, duk da kuwa bai ji dad'in kwanciyar da yayi akan kujeraba haka ya haquri, dama shi bai ta6a kwana a sofa fa ba sai yau dai zai fara.......................

HAPPY FRIDAY.......

Ayi hutun weekend lpy fiya ina mufatan alkhairi.

Mu had'e a next page.


ADALILINTA💜❤💜

BY AMINA BAYERO💜❤💜

Typing.............

*page 87*



Daga haka shima ya shige cikin bargo, duk da kuwa bai ji dad'in kwancyawa ya farka da sauri tare da miqewa zaune. Kasa kunne yayi dan ya tabbatar wai da gaske zahra ce take kukan nan ko kuwa?.

Tofah baccin zahra da mashkhur yayi nisa sosai. 6angaran mashkhur kuwa kamar a mafarki yake jin kuka sama-sama,, mashkhur sam ya kasa tashi bare yayi kwakwaran moti sabida baccin da yake kansa. can dai mashkhur yaji kukan yayi yawa, dan haka ba shiri ya tashi a d'an firgice, sabida shi bai saba da hayani ya ba in yana bacci.

Ai kuwa muryar zahra yaji tana raira kuka shi bada qarfi ba shi ba'a hankula ba. Wani dogwan tsaki mashkhur yaja tare da cewa kee dallah mene kika cikamin kunne da kuka?, zahra kuwa maimakwan tayi shiru cigaba da kukan tai. Da kyar mashkhur ya iya miqewa saka makwan bacci da yake kansa yana miqewa ya qarasa baki bed ya canza haske bedroom d'in daga blue zuwa white.

Yana kunnawa ya mai da kallansa kan zahra wanda take kwanci kamar dai yadda ya barta jiki lili6e da blanket, fuska ce kawai a waje, kuka take amma ko d'ugwan hawaye babu a fuskar tata. Wani siririn tsaki mashkhur yaja tare cewa! Kee wlh in baki rufemin baki ba sai nayi miki rashin mutunci, inma banda iskanci irin naki ina bacci sai ki ringa tashi na, ke bakisan ba'a tashina ina bacci ba ko? Mashkhur ya qarasa maganar fuska a had'e.

Shiru zahra tai tare da cewa! Ni yunwa nake ji kuma inaso na shiga toilet naga kuma kayi bacci shi yasa na farayin kukan ko zaka tashi. Zahra ta qarasa maganar tana saki wani kukan, mashkhur da yake tsaye saki baki yayi yana kallan zahra sabida tayi matuqar 6ata mai rai qololuwa. A zuciye mashkhur ya kai hannu jikin zahra, yana gab da kai mata duka ya janye hannun ko mai ya tina oho.

Au kuwa tana ganin haka ta qara sakin kuka wanan karan kukan ma ba hawaye, fuskarta a fushe cikin kuka tace? Gaskiya ni na gaji da zaman nan kullum sai ai ta zalintata wlh dady yana sake buguwa sai na gaya mai komai in yaso sai yazo ya d'auke ni na huta kafin ku kashe ni kai da mugunwar budurwar taka.

Har zuciyar shi mashkhur yake jin maganar da take gayama dan haka ba shiri ya fuce daga bedroom d'in, sabida yasan in dai ya cigaba da zama ba abinda zai hana ya nad'awa zahra na jaki. Mashkhur yana fita ya fad'a kan kujera zuciya sa tana sake mai quna, dan shi sam baya san yawan tashin dare in yana bacci ko kuma hayani, kai koma baya bacci bayasan hayaniya barema yana baccin.

Nan da nan mashkhur ya hau tsinewa zee da zaginta a zuciyar shi sabida yasan duk ita ta jefa shi a cikin jarabar na. Mashkhur yafi minti goma a zaune anan sam ya rasa mafita. Can kuma yaji kukan zahra yana sake tashi da qarfi take kukan harda shasheqa, dan tindda ga bedroom har falo yana jin kukan.

Dole haka mashkhur ya miqe jiki ba qwari ya nufi hanyar komawa bedroom d'in shi, yana shiga yaji kukan zahra ya sake dakar mai kunne da qarfi, nan da nan mashkhur jikinsa yayi sanyi sosai sabida ji yayi tausayin zahra ya d'an kama shi. A hankula ya qarasa kan bed d'in da zahra take kwanci ya d'an zauna a gefe yana nazarin taya zai sa zahra ta dena kukan nan?.

Masha yafi minti biyar a zaune yana tinanin mafi, zahra kuwa sai kukanta take duk tafi ta cika bedroom d'in da sautin kukunta. Can mashkhur yayi qarfin halin sa hannu ya kwashe blanket d'in gaba d'aya daga jikin zahra. Maimakwan zahra tai shiru sai ta qara sautin kukan naglta,, shiru mashkhur yayi tare da zuba mata manya idanun nan nasa, dan shi gani yake bazai ta6a iya rarrashin zahra ba.

Yadda mashkhur yake kallan zahra ya d'an bata tsoro kad'an, kamar tinani yake kamar kuma kallansa yake. Zahra ta tsargu da kallan sosai, dan haka ba shiri ta kama bakin ta ta kulle ta fara sakin hajiyar zuciya. 6angaran mashkhur da yake kallan zahra kuwa wata ajiyar zuciya ya saki tare da furta alhamdulilahi a zuciyar shi.

Shima kansa bai san me yake kallo a jikin zahra ba kawai dai ya zuba mata idanuwa ne, sabida tsabar haushin ta da tausayin ta da yake ji kuma gashi ya rasa mafita. Muryar mashkhur zahra taji yace? Sannu kin gama kenan ya fad'a hakan fuska ba walwala ba fara'a,, sauke ajiyar zuciya zahra tai tare da d'aga kai alamun ehh.

Jinjina kai mashkhur yayi yana mamakin iya shege na zahra. Miqewa yayi tare da cewa tashi na kai ki toilet d'in. Ya mutsa fuska zahra tai tare da cewa! Bazan iya ba. Rai a 6ace mashkhur yace au ni kike so na tasar da ke zauna ko?. Eh komawa dai wane ya tayar da ni ba dole sai kai ba,, ni d'in ce kawai bazan iya tashi ba. Kada Allah yasa ki tashi, ai kan ki kikayiwa, mashkhur ya qarasa maganar yana juyawa zai bar wajan.

Murmushin mugunta zahra ta saki tare da cewa! Ah mene amfanin bed d'in ai sai nayi abuna a kwance,, dan ni bazan iya barin fitsari a cikina ba. Da sauri mashkhur ya juyo tare da cewa! Kai ashe baki da hankali koh? Gyad'a kai zahra tai tare da cewa! Ina naga wani hankali ai tin sanda wanan muguwar matar ta cilloni daga sama hankali na ya ragu,.

Rai a 6ace mashkhur yace to wlh in baki wasa ba sai na dawo miki da hankalinki jikinki, yanzu kuwa. Wani kallo zahra ta watsa mai tare da cewa! Da kuwa ka tai make ni wlh. Murya a shaqe mashkhur yacre wlh tallahi kika sake kikayi fitsari a kan bed d'in nan yau sai kin gane baki da wayo. Tom shikenan, bani waje ka gani, ai nafiso ma ka bani mamaki.

A zuciye mashkhur ya nufo zahra gadan gadan, zahra kuwa data ga hakan hannu biyu tasa ta toshe kunuwanta tare da sakin wata gigitacciyar qara a tsorace. Mashkhur kuwa da sauri ya qarasa inda zahra take mai makwan ya yi mata hukunci kamar yadda yayi niya sai ya sa tafin hanunsa guda d'aya ya toshe bakin zahra da qarfin gaske.

Wani uban iwu zahra ta sake saki, amma ina sam iwun ya kasa fitowa saka makwan sosai mashkhur ya toshe mata baki sam iwun ya kasa futowa. Sosai mashkhur ya matso da fuskarsa sai tun fuskar zahra tare da cewa! Ai na gaya miki wlh duk iskancin ki a tafin hannuna yake in kin isa ko kwakwaran motsi kiyi kiga yadda zanyi da ke.

Hannu zahra tasa ta fara kici-kici cire hanun mashkhur a bakinta. Mashkhur kuwa da sauri ya sa d'ayan hannun nasa ya had'e hanun zahra duka biyun ya riqe gam. Zahra kuwa nan da nan ido ya raina fata fuska abin tausayi, nunfashinta kawai ne yake iya motsi a jikinta. Mashkhur kuwa cewa! Yayi maea kunyar banza kawai, ai tinda kin iya rashin kunya zaki iya kwace wa.

Ya qarasa maganar yana sauke idanuwan sa ana zahra wanda sukayi narai-narai da kwalla. Wani qasai tacan murmushin mashkhur ya saki tare da cewa! Yaro-yaro ne kad'an ma kika gani ai ni baki isa kin tayarmin da hankali ba sai dai ki tayarwa kanki. Zahra kuwa rintse ido tai cike da baqin ciki da kuma mamakin yadda taga mashkhur ya saki qasai tancan murmushin da ya qara mai kyau, dan ita zata iya cewa! Bata ta6a ganin murmushin mashkhur ba kusa da kusa irin yau.

6angaran mashkhur kuwa a hankula ya saki hanun zahra amma bai bud'e mata bakin nata ba. Murya a kausashe yace! Wlh na sakar miki baki kikayimin iwu sai na shaqe miki wuya. Mashkhur ya fad'a ne kawai sabida da ya tsorata zahra amma yasan bazai iya shaqewa zahra wuya ba, koma dan dai sabida karya sake fad'awa cikin jarabar daya fad'a yanzu.

A hankula mashkhur ya janye hanunsa daga bakin zahra. Wata nanau yar ajiyar zuciya zahra ta sauke, nan da nan wasu zafafan hawaye suka fara kwaranyo mata. A zuciyar ta kuwa sai fama qarewa mashkhur zagi take. A hankula mashkhur yasa hannu wansa a qarqashin bayan zahra ya d'agota kamar wata mara lafiya. Zahra kuwa da wani mugun kallo ta bishi kamar tasa hannu ta kwashe fuskar shi da Mari.

D'a gowa mashkhur yayi, ya ga zahra tana mai irin wanan kallon. Au ni kikewa wanan kallon koh? Ya tambaya fuska a murtike, murya a shaqe zahra tace ai ni bazaka barge ni ba sai ka kashe ni gaba d'aya nabar duniyar. D'an zaro ido mashkhur yayi tare da cewa! Ni awa na qarasa gawar da ba tawa ba, ai ke yanzu baki da maraba da gawa, banza gawa taqi rami kawai.

Nan da nan zahra take fashe da wani saban kukan mai cin rai da baqin ciki. Wani siririn murmushin mashkhur ya saka a zuciyar shi yana mamakin saurin kuka irin na zahra, shi kukan nata ma nishad'i ya bashi dan haka yana daga gefanta yana kallonta zuciya cike da mamaki da nishad'i. 6angaran zahra kuwa kuka take haiqan, in ta tina mashkhur yace mata gawa taqi rami har wata shasheqa take.

Muryar mashkhur zahra taji yana cewa! Aikin kawai, raguwa ai na gaya miki ko ban dake ki ba da bakina zan ta saki kuka, dan ni kukan ki shine farin cikina, ya qarasa maganar cikin nishad'i. Da sauri zahra ta d'ago da rinanin idanuwan ta tare da cewa! Wlh kayi ka d'an ka sani kuka na gaya ma, baka ksi matsayin da zanzauna ina maka kuka ba. Ta6e baki mashkhur yayi tare da cewa! Daga baya kenan dallah can ni matsa gefe.

Nan ma zahra taji haushi amma sai ta dake sabida ta d'au alwashin mashkhur bazai qara sata kuka ba, dan taga in tana kuka kamar sake raina ta yake ke. Hannu na rawa zahra ta fara qoqe fuskar ta da tai jajir sabida kukan da ta sha, hmmmm abinka da fararan fata. 😩
Zahra tana gama share hawayanta tai shiru tana sauke ajiyar zuciya, daga ita har mashkhur d'in ba wanda yace komai.

Can mashkhur ya miqe tare da miqa mata hannu yana cewa! Taso na koya miki tafi dan daga yau bazan sake d'aukar wata na kai ta toilet ba sabida ni ba d'an iska bane. Murya a shaqe zahra tace bazan taso ba d'in nima ce maka akayi 'yar iskar ce inma banda qaddara mai zai sa na yadda ka d'auke ni harka kai ni toilet ta qarasa maganar tana turo baki.

Iskanci ma na nawa, ke da kika tafi namiji yana ta6a miki kai wai ke baki yadda ba kin bige mai ya kai wanan iskanci. Ina ruwanka ai d'an uwana ne koh?, wata uwar harara mashkhur ya watso mata tare da cewa! Dalah can kallan dangi taya ahmad ya zata d'an uwanki,, in ma d'an uwanki ne ai bai kamata ba sabida komin banza dai an kina da aure. Wani siririn murmushin takaici zahra ta saki tare da cewa!

Tabb ina ruwana da auran ka, ai dashi da babu duk d'aya, da sauri mashkhur ya cafe zancan da cewa! Yauwa 'yar gari ashe kin gane, dan muna komawa nigeria zan miki saki uku rasss ajare. To ka sakeni mana ai ni ina da wanda zan aurama qarewa. Wana mara hankalin ne zai aure ki da mumunar fuskar ki, mashkhur ya qarasa maganar yana sakin murmushin mugunta.

Zahra kuwa har cikin ranta taji maganar yaya mashkhur d'in, kamar tai kuka tace! YAYA ABDUL mana, kyakyawan namiji mai kyan hali da farar zuciya. tana ambatar sunan Abdul mashkkhur yaji wani yarrrr, nan da nan annurin fuskar sa ya dauke,. Fuska ba walwala yace sai dai shi, shi d'in ma tai makwanki zai yi, inma ba shiba au ba wanda zai iya da baqin halinki.

Nan gani nan bari kanaji kana gani za'a d'auramin aure da yaya abdul. Wani siririn tsaki mashkhur yaja tare da cewa! Ai kuwa sai da shi d'in, ni dallah in baza ki tashi ba wlh zan tafi na kwanta. Zahra kuwa cewa tai nifah bazan iya tashi ba ah to gwarama kaje ka kiramin yaya ahmad,.

Harara mashkhur ya watasa mata tare da cewa! 'Yar iska ai anan kinfi kauri to baza'a kira shi ba. Daga haka mashkhur ya sa hannuya ya d'auki zahra kamar yadda ya Sabah. Zahra kuwa iya qarfinta ta saki sosai duk sabida ta wahalar da shi.
To kamar dai dazu bayan mashkhur ya kai zahra toilet futowa yayi sai da ta gama ya d'auko ta ya dawo da ita kan bed.

Yana ajiye ta zahra tace! Saura abinci kuma bana son indomiee bana san tea kuma karka kawo min fruit abinci nake son ci kawai. Mashkhur kuwa fuska a d'aure ya miqe ya fuce daga d'akin dan gani yake tsayawa ma tankawa zahra 6ata lokaci ne. Zahra tayi hakan ne dan tasa mashkhur ya d'an sha wahala kafin yayi girgi, sabida tasan in zai dafa indomie ko tea, zai gama da wuri.

To mashkhur ya d'auki 40 minutes kafin ya dawo d'akin hanunsa d'auke da plate. Jalaf d'in taliya ce a cikin plate d'in dan zahra tana gani sai da yawon ta ya fara tsinke wa. Ajiye plate d'in mashkhur yayi tare da cewa! Gashi d'auki kici. Ya mutsa fuska zahra tai tare da cewa! Bazan iya ba. Rai ba dad'i mashkhur yasa hannu ya d'auki plate d'in taliyar ya d'ebo a fork ya fara bata.

To haka dai mashkhur yayi ta fama da zahra sai iskanci kala-kala take yi amma haka ya d'aure ya kau da kai ya cigaba da bata. Bayan ya gama bata ruwa zahra tace ya kawo mata, haka mashkhur ya d'auko mata ruwan zuciya ba dad'i ya kawo. Bayan ya gama bata ruwan, komawa tai ta kwanta ya sake lili6a mata blanket d'in, sanan ya canza glob d'in daga white zuwa blue.

Baya ya gama shima ya koma kan sofa ya kwanta zuciya cike da damuwa. A ganinsa tun kafin kwana d'aya zahra ta fara bashi wahala haka, nan da nan mashkhur ya fara addu'a a zuciyar shi akan ALLAH ya bawa zahra lpy, su koma nigeria ya ranga d'a mata saki uku ya huta da masi fah,, to da wanan tinanin bacci ya kwashe shi.
6angaran zahra kuwa haka tai ta tinanin yadda zata wahalarwa da mashkhur rayuwa kafin ta qare jinyar nan har bacci ya kwashe ta.

Washe gari............

Mashkhur da asubar fari ya tashi, yana tashi ya tashi zahra ya kai ta toilet, bayan ta gama kama ruwa
Mashkhur ya koma ya tai maka mata tayi alwala bayan ta gama ya shifid'a mata dadduma sanan ya koma bedroom d'in ta ya d'akko mata hijab domin taya sallah. Daga haka shima ya koma toilet ya d'aura alwala sanan ya wuce masallaci.

Mashkhur yana dawowa daga masallaci ya shiga kicin ya had'awa zahra breakfast, dan shi sam hankalinsa baya kan breakfast kawai hankinsa yana kan mai zai je ya tarar a result d'in shi. Bayan ya gama had'a mata breakfast d'in, dakko ta yayi ya dawo da ita falo, sanan ya zauna ya fara bata abincin,, sam mashkhur bai biyewa zahra ba duk yadda ta kai da rashin mutuncin ta haka yake binta dan shi yanzu sam ba itace a gaban saba.

Mashkhur yana gama bawa zahra abinci da magani ya koma bedroom ya shige toilet domin yi wanka. Bai d'au wasu lokuta ba ya gama bayan ya gama wanka ya fito, shiryawa yayi a hanzarce ya d'auki wayarsa da key d'in motar sa ya fuce daga bedroom d'in. Yana fitowa falo ya tarar da zahra a zaune yadda ya barta. Ko kallanta bai yi ba ya kama hanyar fita.

Muryar zahra mashkhur ya jiyo a kunnuwansa tana cewa! Ina zuwa. Da sauri mashkhur ya juyo cikin mamaki yace inda kika aike ni. Ya mutsa fuska zahra tai tare da cewa! To ka barshi kawai ba sai kaje ba. Hararar ta mashkhur yayi tare da cewa! Uban mai zan miki a gidan in na zauna. Komai ma zakayi min dan inaso ka dafamin abinci da dai sauran su.

To uwata bazan dafa ba kuma in na fita daga gidan nan bazaki qara ganin qatafa ba sai dare yayi in yaso naga ta iskanci. To sai mai qarqarinta dai in ina buqatar abu nai ta kwallara iwu, in da akwai na annabi su fito su tai makamin. To sai mai kanki kika yiwa ai ko ma zaki kwana kina kuka ba wanda zai zo ya taimake ki anan. Da yake cema akayi irin kukan jiya da daddare zanyi ba ko, ai wanan iwun mai sauti zanyi.

Kuma ana shigowa zan ce a tai makamin da waya na bigawa dady na gaya mai komai. Da sauri mashkhur yace kai haba sai ki gaya mai kuma,, murmushin mugunta zahra tai tare da cewa! Hmm to ka fita ka gani mana, zaka tabbata da wasa nake ko kuwa. A hankula mashkhur ya dawo tare da koma bedroom d'in shi. Bai fi 3 minutes ba ya dawo hannun sa riqe da wayar zahra.

Qarasowa yayi tare da d'an zama a kefan zahra, zahra kuwa ajiyar zuciya ta sauke tare da lumshe ido sabida qamshin turaran mashkhur da taji ya daki hancin ta. Qasa-qasa mashkhur yayi da murya tare da cewa! Yanzu zan dawo fah ba dad'ewa zan yi ba, kawai school zani na kar6o result d'ina, ga wayar ki nan ki danna ko hira ne kuyi da ilham kafin na dawo.

Noqe kafad'a zahra tai tare da cewa! Naqi d'in, wlh kana bita dadyn zan kira a wayar na gaya mai koma. Da sauri mashkhur ya

Please Login or Register in order to submit comment