Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suna jin dad'i zama da momy. Momy tana zaman haquri ne kawai in banda ci da sha da sutura da haqqin aure bata samun koma daga wajan mijin nata. Ba kamar gidan dady ba momy tasan har abada ba zata sake samu miji mai hali da mutunci irin dady ba, dan haka dole ta kwantar da kai ta cigaba da kula da yaran, tinda yaran suna son ta kamar ita ta haife su ita tana son su.

SARATU.

Bayan taji wuya sosai da sosai a wajan kishiyoyinta Allah ya azirta ta da ciki ta haifi 'yan biyu mace da namiji. Saratu tayi farin ciki da hakan dan ita tini tama cire rai da samun haiwuwa a duniya. Tun daga nan saratu ta dage da rokwan uban giji akan ya kawo mata sauqi da mugunta da makircin kishiyoyinta. Dan yanzu saratu ta da momy sun tuba sun koma ga Allah basa bin wasu boka ye.

Bayan yaran saratu sun tasa sunyi wayo, mahaifin su yaga yarda ake zalintar su a gidan haka ne yasa ya raba saratu da kishiyoyinta ya canza mata gidan ta ita ka d'ai. Saratu taji dad'in hakan sosai kuma ta godewa Allah ta cigaba da rayuwar rufin asiri dede gwargwado da yaranta kullum cikin tuba da istigfari take.

Zahra and mashkhur.

Yaran su sunyi wayo sasai kusan kai d'aya suka tashi kamar dai twins. Abdul yana da shekara 3 shi kuma sadeeq yana da shekara biyu. A lokacin ne aka sa su a school sabida suna maga sosai. Zahra ta sake fresh tai kyau kamar ba ita ta haifi yaran taba. Shima mashkhur haka hankalinsa ya kwanta sosai ya sake kyau kullum cikin qaunar junan su suke.

Zahra ta yanke shawarar cire planing d'in ta sabida har lokacin tana son ta haifi baby girl Allah ya jarrabe ta da son 'yar mace. Bayan zahra ta cire planing d'in ta, mashkhur visa umara yayi musu. Daga nan su wuce London, paris germany. Domin su je su wuta daga ita sai mashkhur zasu tafi a gida zasu bar su abdul. Zahra gidan ilham ta kai abdul da sadeeq da yake school d'aya suke da yaranta.

Zahra da mashkhur sun sauka saudiya lafiya sunyi umara bayan sun kammala suka fara shiga qasa shan da zasu je. Hmmm fad'a muku soyayah da mashkhur da zahra suka sha acan 6ata time ne. Sai da suka yi 3 month sanan suka fara shirya-shiryan dawowa. Dan a lokacin ma zahra tana da cikin wata biyu.

Bayan sun dawo zahra ta d'auko yarantan ta suka cigaba da rayuwar farin ciki.
Da cikin zahra ya shiga watan haiwuwa sam zahra bata bacci kullum cikin sallah dare take Allah ya azurta ta da d'iya mace. To da lokacin haiwuwar zahra yayi ta haifi sankata sankatan yaranta twins kuma abun farin cike shine matane gaba d'aya. Masu kama da zahra sak kamar an tsaga kara.

Hmmm zo kaga farin ciki wajan zahra kamar an mata bu da aljannah. Shima mashkhur yayi farin ciki da hakan sosai sabida Allah ya amsa musu add'a su. Kai bama zahra da mashkhur ba har su ammi da ragowar dangi sunyi farin cikin haka. Mashkhur sai da ya sake siyawa zahra sabuwar galleliyar mota mai kyau. Ranar sona aka sawa yara maryam da aisha.

Wato sunan ammi da mama,. Maryam ana mata kara da meera aisha kuma esha. Zahra ta gyara kan ta sosai lokacin arba'in dan tace daga haka bazata sake haiwuwa ba. Bayan zahra tai arba'in ta dawo daga kaduna. Suka d'ora daga inda suka tsaya ita da mashkhur. Suna bawa yaran su kulawa sosai, zahra tana fama da sadeeq sosai sabida tsokanar abdul da yake.

Allah ya tekama abdul silent ne koya tsoka ne shima ba biye mai yake ba hakan ne yasa zahra take jin dad'i 'yan matan zahra sai tasawa suke kyan su yana sake futowa. Kamar su d'aya sosai dan in ba zahra ba ba wanda yake gane su shima mashkhur d'in se yayi da gaske sanan yake iya tantace yaran sabida suna kama ba sosai.

After 5 years.

Babban gida ne mai hawa biyu, rantsatse ne dole in ka kalle shi sai ka qara gidan ya had'u sosai dan bama da kayan nigeria aka gina gidan ba. Hmmmm ku biyo ni mu shiga gidan. Ina shiga babban falon gidan qasa wani babban frame na gani na hoton zahra da mashkhur sai dariya suke sunyi kyau sosai. D'ayan 6angaran kuma frame d'in hotan zahra da mashkhur ne da kuma yaransu su shida.

Uku maza uku mata abdul yana gefen mashkhur shi kuma sadeeq yana gefan zahra. Sai twins d'in su a tsakiya su. hanun mashkhur riqe da kyakyawa yaro mai ruwa biyu wato yana kama da zahra kuma yana kama da mashkhur. Zahra kuwa wata kyakyawar baby ce a hanun ta wanda bata wuce 5 months ba, ita gaba d'aya ma bata kama da su sosai.

Hmmm kayan da akayiwa room d'in decoration lissafo muku ma bata baki ne. Dole haka naja jiki na haye hawa na biyu. Hmmm shima hawa na biyun yayi mugun had'uwa sosai. Bayan na gama kallace-kallace na so na hau hwa na uku amma ban samu dama ba sabida na hangi mutan gidan suna zaune akan draining table suna cin abinci dare.

Zahra tana face d'in mashkhur, abdul da sadeeq a gefan ta, twin kuma a gefan mashkhur sai annor a zaune akan cinyar mashkhur yana tasa da spoon a abincin mashkhur. Qafa mashkhur yasa ya take 'yan yatsun zahra, da sauri ta d'ago, suna had'a ido suka sakarwa juna murmushi. Nan da nan suka fara maganar su ta ido yarda yaran su ba zata su fahimce me suke nufi ba.

Ummie nah kinga yaya sadeeq yana sha min juice ko? meera ta fad'a. Kafin zahra tayi magana itama esha tace ummie nah kiyiwa ya sadeeq magana ya dena ta6a mana abinci. Juyowa zahra tai tare da cewa haba dadyna meye hakan kaci abinci ka ka dena tsokanar su kaji. Murmushi sadeeq yayi tare da cewa to ummie amma ai kad'an na sha.

Kai dady ka dena tsokana baka ga yarda yayan ka abdul yake ba mashkhur ya qarasa maganar yana zubawa sadeeq ido. Ee abbie na gani, that is good kai ma haka nake so ka zama kaji. Ok abbie zan zama kamar yaya babba. Daga haka zahra da mashkhur suka cigaba da maganar su ta ido cikin kulawa sai wasa suke da qafafuwan su.

Bayan sun gama cin abinci zahra wanka tayiwa twins d'in ta sanan ta shirya su tasa muku kayan bacci. Sanan ta kwantar da su a kyawawan bed d'in su. Da gadon kowa a cikin su daban yake, amma ko an kwantar da su sai sun dawo sun had'e, dan haka dole aka had'e musu bed suke kwanciya tare. Bayan zahra tasa sunyi addu'a kashe musu globs tai ta kunna musu na bacci.

Tabi ko wanan su tayi muku kiss suma sukai mata, sanan tace good night, had'a baki mera da esha su kai wajan cewa good night too ummie. Daga haka zahra ta fuce, tana fita ta shiga bedroom d'in su abdul da sadeeq

Zahra tana shiga d'akin, bed d'in sadeeq ta wuce tare da cewa dadyna kayi addu'a ko?. Ee ummie nayi, yauwa dama kai nake ji sam bana jin yaya abdul d'i na sabida nasan zai yi. Nima ummie na kusan zama mai hankali kamar yaya babba. Murmushi zahra tai dan tasa da wuya sabida sadeeq ya fiya tsokana da rashin ji.

Girman su d'aya da abdul amma sai kai tinanin sadeeq ne babba sabida ya fiya wayo, gaba d'aya yaran zahra silent ne amma sadeeq banda shi kullum cike tsokana yake. Qarasawa zahra tai sanan taiwa sadeeq kiss tare da cewa to Allah yasa, ammen ummie ina so ki. daga haka ta wuce tayiwa abdul, shima d'agowa yayi ya yi mata sabida yana son maman sa sosai.

Kullum zahra sai tabi yaranta tai musu kiss shine sallamar su. Bayan zahra ta kashe muku globes, kama hanyar fita tai tare da cewa good night suma de har suna had'a baki wajan cewa good night too ummie. Bayan zahra ta rufo qofar bata tsaya ko ina ba sai d'akin su ita da mashkhur.

Bayan ka bud'e qofar shima wani rantsatsan falo ne sanan 2 bedroom masu faces d'in juna, duk acan saman qarshe d'a kunan su zahra da yaran au na bacci yake.

Bayan zahra ta shiga ciki bedroom ta wuce, mashkhur ta gani kwance da annoor akan girjin sa sai zuba mai shagwa6a yake mashkhur yana rarrashi. Zahra kuwa babynta ta d'auko ta shayar da ita sanan tai mata wanka tasa mata kayan bacci. Sai da mashkhur da zahra suka tabbatar bacci ya d'auke annoor da noor sanan suka fuce hannu riqe dana juna suka shige d'ayan bedroom d'in.

Zahra tinda daga haiwuwar twins ba cire ran sake haiwuwa, amma bayan twins d'in sun girma sunyi wayo. Kuka suke mata kullum akan sai an siya musu baby irin na gidan su afnan wato 'yar ilham. Hakan ne yasa dole zahra ta cire planing d'in ta domin ta sake haiwar ko d'aya ne. Bayan zahra ta haifi annoor ta sha'afa sosai bata mai da planning d'in taba. Hakan ne yasa ta sake d'aukar cikin noor.

Annor sunan baban zahra aka sa mai, ita kuma noor sunan hajiya kaka aka sa mata. Har yau hajiya kaka tana nan digirgir, kamat ba tsowuwa ba tana yawan ta. Kuma tana matuqar qaunar yaran zahra da mashkhur, musamman ma da akayi mata takwara noor.

ADALILINTA πŸ’œβ€πŸ’œ

BY AMINA BAYEROπŸ’œβ€πŸ’œ

typing.........

Zahra da mashkhur suna shiga suka fara bawa junan su haqqi cikin shauqi da jin dad'i. Har rana mai kama da yau mashkhur bai dena jin dad'i zahra ba in suna saduwa. Kuma har yau bai dena jin shauqi da dad'in ta ba kullum burinsa su kasance da zahra dan ma yanzu sun tara yara amma duk da hakan basa hana su jin dad'i junn su.

Washe gari.

Ranar ta kasan ce ranar friday tun bayan sallah asuba zahra ta tashi ta shiga kicin domin had'a musu breakfast, da kuma abinci school. Sai misalin qarfe shidda zahra ta gama komai. Tana gamawa bedroom d'in su abdul ta shiga ta tashe su domin suyi wanka, da yake su yanzu sun iya wanka. Daga haka zahra ta wuce wajan twins d'in ta, ta tashe su.

Su de kam basu iya wanka ba sai shagwa6a da sauri kuka kamar dai zahra. A tare zahra ta shiga yi musu wanka. Hmmm zo kuka wanka twins na gai she ki zahra. Su basu yarda ayi musu wanka daban daban ba sai dai in an wanke wa d'aya hannu guda itama d'ayan a wanke mata nata. Haka de zahra tai cigaba dayi musu dan ita har ta saba da ta6arar su.

Bayan ta gama tazo ta busar musu da gashi kan su,. Bayan ta busar musu da gashin, parking d'in gashin da ribbon tai musu. Sanan ta shafa musu mai bayan ta shafa musu mai, uniform ta fara sa musu.

Shima dai kamar yarda akai wanka haka ake sa uniform d'in, in ansawa esha riga sai a sawa meera haka dai har zahra ta gama shirya 'yan matan ta. Hmmm masha allah yara kamar larabawa sunyi mugun kyau. Hannu riqe da junan su suka fita domin breakfast zahra tana biye da su a baya.

A lokacin abdul da sadeeq suma sun fito har sun zauna akan draining. Ba 6ata lokaci zahra tai saving d'in su. Bayan sun fara ci kallo sadeeq zahra tai tare da cewa dadyna banda tsokana bari naje sama ta taso abbie kafin ku gama breakfast d'in. Tom ummie sadeeq ya fad'a yana tsare zahra da idan sa kamar na uban sa.

Wucewa zahra tai ta haye hawa na uku cikin sauri,. Zahra bedroom d'in adede time d'in mashkhur ya futo daga wanka, ugu d'aure da towel sai kuma wani towel d'in yana goge jikin sa. Hmmm abbie yau she zaka barni na wuta kai ma ka wuta. Kallon ta mashkhur yayi cikin kulawa yace hmmm mai kuma ya faru 'yar rigima.

Komai ma ya faru, kai yanzu kace baza ka ta6a yarda drive ya kai su abdul school ba sai kai, ni kuma kullum ni zan d'auko su. Hmmm sorry dear ki bari su qara wayo mana sai drive ya ciga da kai su amma fa yanzu yara ne. Ajiyar zuciya zahra tai tare da cewa it's okay, Allah ya kai mu lokacin, kallon ta mashkhur yayi cikin so da qauna yace ameen wife.

Daga haka mashkhur ya shirya tsaff sanan suka fuce hannu riqe dana junan su. Haka zahra da mashkhur su kai ta takawa har suka qara wajan draining glass d'in. Bayan mashkhur da zahra sun qarasa hannu riqe da juna, tun kafin su kai da zama a draining d'in yaran suka fara good morning abbie.

Fuska cike da murmushi mashkhur ya amsa cikin kulawa yace morning too my lovely children. Bayan mashkhur da zahra sun zauna domin breakfast. Cikin shagwa6a meera tace abbie pls yau ka dawo da wuri, mashkhur sauke cup d'in hanun sa yayi tare da cewa to ammimi, in na dawo mai zakiyi?.

Esha ce ta cafe zance da cewa gidan ammi mana zaka kai mu yau da wuri zamuje bada yamma ma ba, esha ta qarasa maganar tana juya ido kamar wata babba. Tom shikenan esha abbie yarda kuka ce haka za'ai. Meera da esha har suna had'a baki wajan cewa good abbie I love you.

Murmushi zahra da mashkhur suka saki, basa mamaki esha da meera sabida halin su d'aya shi yasa maganar su take yawan zuwa iri d'aya kuma a tare. Some time in za suyi magana d'aya ce take farawa d'aya kuma ta qarasa. Bayan sun qarasa breakfast d'in zahra cewa tai kuwa ya d'auko school back d'in sa. Daga haka ita kuma ta shiga kicin ta futo musu da plask d'in food d'in su.

Sanan kuma ta d'ebo musu biscuit da chocolate da milk da juices. zubawa kowa a hand bag d'in sa zahra tai, bayan sun futo kowa ya d'auki jakar shi da hand bag d'in tsugunawa zahra tai sukayi azkhar da addu'a fita daga gida. Bayan sun gama one by one suka fara rungume zahra tare da kiss, itama zahra tana yi musu. Bayan sun gama suka ce bye ummie take care.

Murmushi zahra tai tare da d'aga musu hannu itama alamun byee tana cewa take care too my fine children. Bayan gaba d'aya sun fuce mashkhur kallon zahra yayi tare da miqa mata hannu cikin voice qasa-qasa yace taso nima kimin teddyna ko kin dena so na ne?. Miqewa zahra tai ta saki murmushi sanan ta nufo inda mashkhur yake tana cewa haba ni na isa na dena son ka hero, zahra ta qasa maganar tana hugging d'in shi.

Shima rungume ta mashkhur yayi sanan yace ah kin manta ada in nayi fushi dake sai ki fara kuka kice na dena son ki. Dariya zahra tai tare da cewa hmmm dah da bani da wayo kenan amma yanzu nasan kana sona, nayi kane-kane a zuciyarka ba wani saura space. Kiss mashkhur yayi mata sanan yace haka ne wife, yau zan dawo da wuri kamar yarda twins suke so.

Ki bari ni zan d'auko su daga school ba sai kinje ba, tom shikenan abbie ka kula da kan ka kaji ni? Zahra ta fad'a tana shafa qirjin mashkhur. Lumshe ido mashkhur yayi tare da cewa tom dear naje, kema ki kula min da kan ki da annoor da noor, tom shikenan abbie sai ka dawo. Daga haka zahra ta raka mashkhur har qofara fita farfajiyar gidan sanan ta koma ciki.

Tana komawa ta shiga bedroom d'in su abdul da sadeeq ta gyara tsaff sanan ta gyara bedroom d'in su esha da meera. Bayan ta kammala ta shige kicin ta gyara shi shima. Haka dai zahra ta fara gyara gidan duk da kuya yana da girma amma ba ko ina take gyarawa ba, hawa na uku take gyarawa kullum da yake anan bedroom d'in su na bacci yake.

Tsakiya kuma anan kicin da draining area yake, yawan ci de anan yaran ta suke wasa. Can qasa kuma basa wani yawan sauka, shi yasa ma zahra bata wahala wajan gyarawa. Kullum mashkhur sai yayi da zahra a samo mata 'yar aiki amma zahra taqi. Sabida sam bata son wata ta shigo mata gida ta fison su ringa rayuwar su daga ita sai yaran ta, waran kuma mashkhur in yana gida yana taya zahra aiki sosai.

Bayan zahra ta gama aiki wajan annoor da noor ta wuce, tayi musu wanka sanan ta bawa annoor abinci a baki yana ci yana mata gwaranci. Bayan zahra ta gama bashi noor ta d'auka ta bata nono sannan ta sa musu kaya. Haka annoor ya ringa bin zahra duk inda tai kamar yarda yake mata kullum. Kicin zahra ta shiga tai musu girkin rana sanan ta koma sama ta d'an kwanta.

Bayan ta d'an wuta toilet ta wuce tai wanka bata wani jima da shiryawa ba mashkhur ya dawo tare da yaran su. Mashkhur yana dawowa ya shiga toilet domin yayi wanka sabida tafiya sallah jumma'a. Zahra wajan abdul da sadeeq ta nufa domin d'auko musu kayan da zasu sa sabida mashkhur tare da su yake zuwa sallah jumma'a.

Bayan zahra ta d'auko musu farar shadda da wula, taya su shiryawa tai. Yaran sun shirya tsaff sunyi kyau, dama gasu kyawawa daga haka mashkhur ya wuce da su masallaci. Zahra kuma wani wanka tayiwa twins tasa musu kayan su masu kyau,. Bayan su mashkhur sun dawo daga masallaci. Zaman cin abinci su zahra su kai suna gamawa mashkhur yace su tashi su tafi gidan ammi.

Dama ko wace ranar friday mashkhur yana kai su gidan ammi suyi wutun weekend a can. Acan aka sa su a makaranta suke zuwa tafiz, d'in asabar da lahadi, uniform d'in su duk yana can . Mashkhur in ya kai su jumma'a sai ranar lahadi da yamam in sun dawo daga tafiz ko da daddare yake d'auko su. Zahra da mashkhur kuwa suna jin dad'i hakan sabida suna shan sha'anin su ba takura.

annoor ma kuka yasa wai shima sai ya bi su, dan haka dole mashkhur ya tafi da shi. Ko da ya kai su gidan ammi acan mashkhur ya baro annoor ya dawo wajan matar sa zahra,. Gida ya rage daga mashkhur sai zahra da autar su noor.

Wanka zahra da mashkhur suka shiga a tare tun daga toilet d'in mashkhur ya fara shafe zahra. Bayan sun futo suka fara kissing d'in juna cike da shauqi. Nan da nan dai suka tayarwa da junan su muguwar sha'awar. Daga haka suka fara sex. Sosai zahra ta saki baki tana yiwa mashkhur kukan dad'i, shima mashkhur sai sambatu yake.

Bayan sun gama suka rungume junan su cike da soyayyah. Bacci su kai sosai mai dad'i, bayan sun farka a tare suka zubawa juna ido. Cikin murya qasa-qasa mashkhur yace zahra wlh ina matuqar qaunarki qauna ta har abada kullum sake shiga rai na kike yi zahra ta,. Cikin shagwa6a zahra tace nima wlh ina qaunar ka yaya mashkhur.

Yauwa zahra ta mu qarayi koh? Cikin jin dad'i zahra ta gyad'a kai alamun ee, dama abinda take son tace kenan. Yauwa Allah uban giji yayi miki albarka matata ya saki a aljannah al mar'atu saliha,. Daga haka zahra da mashkhur suka sake lulawa duniyar dad'i. Sabida su dama basa gajiya da junan su musamman ranar weekend in yaran su basa nan, sosai suke shan soyayyah........

Hmmm ni kuwa amina bayero nace allah yabar qauna, zahra da mashkhur.

A yanzu mashkhur yana da company 4 na kansa, sanan kuma yana da company 4 da yake had'a da hanun jari a cikin su, dan yanzu har qasar waje yana fita sabida a can suke tattaunawa,. Shi kuma abdul ya gaji dady dan ya zama cikakkyan babban d'an kasuwa. Shima ahmad mijin ilham yayi kud'i a yanzu sosai, duk kan su de sun zama manya mutane.

Yanzu yaran zahra da mashkhur shida, yaran ilham da ahmad suma su shida maza biyu mata hud'u, yaran nana da abdul kuma su had'u ne biyu mata biyu maza. yaran ruma kuma biyar ne uku mata biyu maza. Zahra da ilham sun yanke shawarar daga haka sun gama haiwuwa kuma sai raino. Dan har sunje kwararriyar doctor tayi musu d'inki na musamman sabida sun gama haiwuwa.

kullum kan zahra da ilham sake had'uwa yake komai tare suke. Sai su kashe su rufe ba wanda ya sani. Zahra bata da abokiyar shawara sama da ilham, ilham ma bata da abokiyar shawara sama da zahra. Hatta yaran su kusan komai iri d'aya ake musu, yaran ma suna son junan au sosai.

Shiguna uku ne a jere, zahra tana da shigowa saloon da gyaran jiki. Ita kuma Ilham tana da shigowa makeup, nana kuma tana da shigowa d'inki. Duk da kuma ba kullum suke zuwa ba sai sati-sati suke zuwa yara ne kawai suke musu aiki a shagunan.

A yanzu shekara abdul d'in zahra 8 sadeeq kuma sherar shi 7 twins meera da esha sherar su biyar, annor shekara d'aya da rabi noor auta watanta shida a duniya.
Hmmm zahra da mashkhur fa suna son junan su suna kula da junan ko yawan samu sa6ani basayi yanzu, kai ku sun samu sa6a ni a take a wajan suke shiryawa, suna rayuwar su mai dad'i kuma suna kula da yaran su sosai.

Tom allah ya qara d'ankwan qauna.

ALHAMDULILLAH.
ALHAMDULILLAH.
ALHAMDULILLAH.

Ni amina bayero anan na kawo qarshan littafin ADALILINTA.

Astagfirullahi
Astagfirullahi
Astagfirullahi.

Ya Allah abinda nai ba dede ba ka yafe, dama shi d'an adam ajizine dule za'a samu kuskure.

Wanda na 6ata musu rai a rubutun littafin ADALILINTA ina neman yafiyar ku.

Hmmm nasan baza kuji dad'i gama littafin nan ba kamar nima yarda banji dadi ba. Dama ance komai yayi farko zai yi qarshe kuma laifin dad'i qarewa.

Nima nasan zanyi kewa sosai wlh sabida na kusa yin shekara biyu ina rubuta littafin ADALILINTA da dad'i da ba dad'i na tafi wuto nayi yaji na dawo, na cigaba da rubutawa, yau nai posting gobe ban ba, wataran ma a sati saud'aya nake.πŸ˜‚

Har wasu suna ganin kamar ma bazai qare ba, nima kai na rubutan har fita yayi daga rai na.

To gashi dai yanzu komai yazo qarshe ALLAH NAGODE ma da ka bani DAMA da LOKACI na qarasa rubuta littafin ADALILINTA. Kuma na dad'e ina jiran wanan ranar.

Wanan littafin ADALILINTA na sad'aukar da shi ga duk wanda suka karanta sukaji dad'i sa.

To yau kuma sai dai nace mi had'e a next book ba a next page ba.😒😒😒

Ina sa ran bayan babbar sallah zan rubuta next novel d'ina, kar ku bari a baku labri, dan labari ne mai zafi yafi littafin ADALILINTA ma.

Byee..































Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment