Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mazaunin gaba sanan mashkhur yaja motar suka bar gidan a guje.

Sosai mashkhur yake sharara gudu a tsakiyar kyakyawan titin qasar, gudu yake sosai kamar zai tashi sama. Sai a lokacin ahmad ya yayiwa mashkhur magana da cewa! Haba mashkhur kabi a hankula mana sai kace wanda zamu tashi sama?, sai da mashkhur ya d'an jawa ahmad aji kamar bazai amsa ba can kuma yace, laifi ne dan nayi saurin?.

Girgiza kai ahmad yayi tare da cewa! Ba laifi bane dan kayi saurin, amma dai an fisan komai a bi a sannu, sannu sannu daga ALLAH ne. Shiru mashkhur yayi bai sake cewa komai ba, mai makwan ya rage gudu da yake sai ma ya qara sharar motar a guje. Shiru ahmad yayi tare da saki murmushi ya sunkuyar da kai abinsa a zuciyar shi yace hmm ALLAH ya shirye ka mashkhur.

To mashkhur bai tsaya da gudun nan ba har sai da suka zo qofar qerarran get d'in asibitin da aka kwantar da zahra sanan ya dakata da gudun, ana zuge musu get, mashkhur ya shige zuciya cike da zullumin abinda zai je ya tarar. Suna fita daga motar wayar ahmad ta fara ringing, yana d'agawa bai d'au wani tsawan lokaci yana wayar ba, kawai cewa yayi okay, zamu zo nan bada jimawa ba daga haka ya kashe wayar.

Ahmad yana kashe wayar ya d'aga kai, amma sai yaga ba mashkhur, yana juyawa yaga mashkhur har ya kusan shigewa cikin asibitin. Sosai mamaki ya kama ahmad, ba komai ne yasa shi mamaki ba face yadda yaga mashkhur yana rawar jiki yau, ba kamar jiyaba da ya nuna ko in kula akan zahra. Jinjina kai ahmad yayi a zuciyar shi yace! Hmm lallai mashkhur lamarinka abin tsoro ne, lamarin ka sai kai.

Daga haka ahmad yabi bayan mashkhur d'in a hanzar ce. Lokacin da su mashkhur suka shiga ciki basu tsaya ko ina ba sai a reception, ba 6ata lokaci suna bada sunan zahra, a wajan manager d'in hospital d'in. Basu d'au waso lokuta ba ta duba musu a inda zahra take. Taca musu yau da asuba an futo da ita daga emergency room, an bata d'aki kuma har ta gaya musu number room d'in.

Ba 6ata lokaci ahmad da mashkhur suka kama hanyar tafiya d'akin da aka kwantar da zahra. Lokacin da su mashkhur suka qarasa room d'in a kulle yake, kuma doctors sunce baza'a bud'e ba sai zuwa nan da one hour, kuma an shedawa su mashkhur tun jiya da suka kawo ta bata farfad'oba, amma in sun damu da san ganinta zasu iya leqawa ta glass d'in room d'in dan suga a halin da take ciki.

Ahmad da mashkhur kuwa basuyi qasa a guiwa ba suka qarasa room d'in zahra domin leqawa ta glass, kamar yadda doctor ya shawarce su. Sosai ahamd da mashkhur suka zubawa zahra ido, da take kwance hanci d'auke da oxygen, kanta kuwa an nad'e shi da farin bandeji, qafarta ta hagu itama an nad'e ta da farin bandeji, ga wani qarfe da aka qaqaba mata a qafar.

D'an yatsan ta na hagu kuwa shima yasha d'auri, na dama ma shima d'aya daga ciki ya sha d'auri. Nan da nan zuciyar mashkhur ta tsinke sosai wani irin mugun tausayin zahra ne ya kama mashkhur ko ta ina ji yake kamar ya zubar mata da hawaye, sosai ya zuba mata ido yana qarewa halin da take ciki kallo, mashkhur ji yayi qafafuwan sa suna barazanar kasa d'aukan sa dan haka juyawa yayi ya koma kan sit ya zauna.

6angaran ahmad kuwa har sai da ya zubarwa davzahra kwalla sabida tsabar tausayinta da yaji. Shima jiki ba kwari ya koma kusa da mashkhur ya zauna dan zuciyar shi bazata ta6a iya jure ganin zahra a wannan halin ba. Shiru mashkhur da ahmad sukayi, ba wanda ya iya cewa d'an uwansa qala kowa yana cike da jimami a zuciyar sa.

Can kuma ahmad yace mashkhur taso mu tafi police station, d'azu da muka shigo hospital d'in nan sun kirani sunce suna neman mu game da maganar Zee. Wani wawan tsaki mashkhur yaja tare da cewa! Ina ruwana da wannan muguwar yarinyar, ko mune iyayanta da zamuje, kawai kaje ni bazani ba ina nan sai ka dawo. Girgiza kai ahmad yayi tare da cewa! No mashkhur akan fa maganar biwa zahra haqqin tane, ko zaka bari zee taci biliss ne ta illata banza ne kenan?, ahmad ya qara maganar yana zubawa mashkhur ido.

Shiru mashkhur yayi ba amsa, ahmad kuwa cigaba da magana yayi da cewa! Kaga dai nan qasar ba irin Nigeria bace in aka cuci mutum suna bimai haqqin sa ko d'an gidan wane kuwa, duk da nasan zee 'yar manyan mutane ce a qasar nan amma nasan hakan bazai hana aqi kwatarwa zahra 'yanci taba, dan haka kawai ka tashi mu tafi. Shafa fuskar sa mashkhur yayi tare da cewa! To ita zahran fa.

Aa ai ba jimawa zamuyi ba kafin ta tashi ma mun dawo kawai dai zamu cike wasu takaddu ne, haka dai mashkhur ya tashi badan ransa yaso ba. Ko da suka fitama ahamd ya bawa mukullin motar dan shi mashkhur gani yake bazai iya driven ba sabida yana cikin tashin hankali, suna tafiya ahmd yana d'an jan mashkhur da hira wai dan mashkhur ya saki ransa amma ina mashkhur sam baya cikin hayyacin sa.

Suna isa ba 6ata lokaci suka shige ciki,, lokacin da su mashkhur suka shiga ciki, sun tarar da iyayan zee sun zo. Mashkhur kuwa ji yake kamar ya kashe iyayan nata ya huta, sabida gani yake sun kawo mai annoba duniya. Jiki na rawa maman zee tazo wajan su mashkhur ta fara yi musu magiya akan su gafarci zee, su yafe mata.

Wata uwar harara mashkhur ya watso mata kamar zai sharara mata mari, da badan ammi ta koyawa mashkhur girmama manya ba da a ranar sai ya kikifawa momyn zee mari. 6angare guda kuwa zee tana can gefe a cikin sel, duk da kuwa sel d'in mai 'yan cine, ba irin na Nigeria ba wajan tass-tass gwanin sha'awa. Wani irin kallo zee ta fara yiwa mashkhur daga nesa, kallan yana nufin ya yafe mata ita masoyiyar shi ce.

Tsayawa gayawa mai karatun littafin ADALILINTA, hararar da mashkhur ya watsawa zee 6ata lokaci ne ma, dan wata harara ya watasa mata wanda ko zahra daya tsana bai ta6a yiwa irin hararar nan ba, ko shi kansa ma bai san ya iya taba sai yau. Ba 6ata lokaci 'yan sanda suka miqawa mashkhur da ahmad takadda akan su ciki jibi a turasu koto.

Jiki na rawa mashkhur ya fara qoqarin ciki takaddar, da sauri baban zee da mamanta suka qaraso suna yiwa mashkhur magiya akan kar ya ciki, D'an sanda ne ya daka musu tsawa tare da cewa! Kar su sake magana, haka dai iyayan zee suna ji suna gani mashkhur ya cike takaddar tafiya koto sanan ya bawa yan sandda sanan ya fuce. Bayan haka kuma 'yan sandda suka ce duk kud'in da ya kamata ayiwa zahra jinya har a sallamo ra sai sun biya, 'yan sandda ba 6ata lokaci sukayi musu list.

A take a wajan sukayiwa ahmad transfer, dan shi mashkhur ko ta kansu bai biba yana gama cike takaddun ya wuce motar. Shima ahmad an gama yimai transfer d'in ya futo a hanzarce. Yana shiga motar,, mashkhur ya kallib ahmad tare da cewa! Mai ka tsaya yi ne ka dad'e haka?, tayar da motar ahmd yayi sanan yace! Na tsaya ne kar6ar kud'in kwanciyar zahra a asibiti har ta samu sauqi, kasan likitoci sunyiwa police list d'in kud'in da za'a buqata.

Wani dogwan tsaki mashkhur yaja tare da cewa! Aikin banza mai za'a yi da kud'in wanan azzaluman mutanan koce musu akayi bani da shi bazan iya biya bane?. Da sauri ahmad ya qirqiza kai tare da cewa! Aa bacewa kayi bazamu iya biya ba, kasan dokar qasar nan kenan in mutum ya jima wani ciwo shi zai biya kud'in maganin shi ne kawai...............

ADALILINTAπŸ’œβ€πŸ’œ

BY BAYEROπŸ’œβ€πŸ’œ

Typing...........

*page 81*

Da sauri ahmad ya qirqiza kai tare da cewa! Aa bacewa kayi bazamu iya biya ba, ka san dokar qasar nan kenan in mutum ya jima wani ciwo shi zai biya kud'in maganin shi ne kawai...............

Wani siririn tsaki mashkhur yaja tare da kawar da kai gefe, gyara zama ahmad yayi tare da kunna motar suka kama hanyar komawa hospital d'in da aka kwantar da zahra. Basu d'au lokaci mai nisaba suka isa asibitin da yake police station d'in bashi da nisa da hospital d'in. Suna isa asibitin bayan sunyi parking d'in motar su, ba bata loaci suka shige asibitin.

Suna shiga asibitin suka kama hanyar room d'in, da aka kwantar da zahra" da yake sun gane d'akin. Lokacin da suka qarasa doctor yace musu an bud'e room d'in zahra zasu iya shiga su ganta amma, kar suyi hayaniya su tashe ta, su bari ta farfad'o da kanta, da yake har time d'in zahra bata farfad'oba,. Mashkhur da ahmad sunji dad'i hakan da haka basuyi qasa a guiwa ba suka kama hanyar shiga room d'in.

Suna qarasawa room d'in a hankula mashkhur yasa hannu ya tura qofar, yana turawa ya shige ahmad ya biyo shi a baya. Mashkhur yana qarasa shiga room d'in bai tsaya ko ina ba sai bakin bed d'in zahra. A lokacin an cire mata oxygen d'in, sai sauke nunfashi take a hankula, ga drip an jona mata, ga kan nan nata yasha d'auri, da farin bandeji" qafarta ta haguma itama tasha d'auri da farin bandeji, sosai.

Ga 'yan yatsun tama guda biyu dana dama dana hagu sun sha d'auri. Ajiyar zuciya mashkhur ya sauke, nan da nan yaji tausayin zahra ya sake rufe shi a karon da bai san adadinsa ba zuwa jiya da yau, da kyar mashkhur ya d'ago ya kalli ahmad cikin siririyar murya yace ahmad anya kuwa qafarta ba karyewa tai ba? " a hankula mashkhur yayi maganar yanda bazai iya tashin zahra ba.

Da sauri ahmad ya girgiza kai tare da cewa! No mashkhur qafarta bata karye ba, haka fa doctor yace mana, qashin qafarta ne ya goce" d'an yatsan ta ne na haqu ya karye, na dama kuma d'aya yayi targad'e d'aya kuma shima qashinsa ya goce" ahamd ya qarasa maganar yana zubawa mashkhur ido. Gyad'a kai mashkhur yayi tare da cewa! To ALLAH ya bata lafiya.

Amen mashkhur, daga haka ahmad da mashkhur suka zauna akan sit domin jiran farkawar zahra. Ahmad da mashkhur suna zama doctor ya shigo, doctor yana shigowa zahra ta fara bud'e idonta alamun farkawa. Amma sam su mashkhur basu kula ba duk hankalinsu ya karkata ga doctor d'in dan suji da mai yazo. Doctor ya bud'e baki kenan zai fara yiwa su mashkhur bayani, zahra ta saki wata gigitacciyar qara.

Ai nan da nan hankalunsu ya dawo kanta, da sauri mashkhur ya miqe tare da nufar zahra da gudu, shima ahmd bai yi qasa a guiwa ba yabi bayan mashkhur,. Sosai zahra take kururuwa kamar alokacin take fad'owa daga step d'in benan. Mashkhur kuwa yana qarasawa zahra tai dif,β€Œ, su mashkhur sun d'auka shiru zahra tai, sai da mashkhur ya ambaci sunan zahra, amma sai yaga ina kamar bata motsi.

A dai-dai lokacin doctor shima ya qaraso, ahmad baki na rawa yace! Mashkhur kamarfa bata nunfashi ko? A firgice mashkhur ya kai hannu hanci zahra domin tabbatar da gaskiyar maganar ahmad. Ai mashkhur kasa janye hanunsa yayi daga hancin zahra sakamakwan jin nunfashi ta ya tsaya cak. Nan da nan ahmad ya fara sakin salati tare da cewa! Doctor duba kaga kamar ta mutu.

Nan da nan mashkhur ya sake gigicewa kafin kace kwabo guminsa har ya fara d'iga a fuskar zahra, duk da kuwa A. C da take wajan. Da sauri doctor ya kai hannu wuyan zahra yana duba jijiyar wuyan ta,, ajiyar zuciya doctor ya sauke tare da cewa! Ba mutuwa tai ba suma tai, sai a lokacin mashkhur ya iya janye hanunsa daga hanci zahra tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya, yana furta alhamdulilah!!.

Shima ahmad d'in hamdala!! Yayi kamar yadda mashkhur d'in yayi, nan da nan doctor ya mayarwa da zahra oxygen d'in da aka cire mata, sanan ya d'auko ruwa mai sanyi ya zuba mata sai gashi zahra ta fara nunfashi. Kallan su mashkhur doctor yayi tare da cewa musu su fita su jira a waje yanzu zau kirawo babban likita ya sake dubata.

Mashkhur kuwa shiru yayi kamar ba su akewa magana ba" sai da ahmad yaja hanunsa sanan ya iya taka qafarsa, sabida tsabar firgici da razani. Su mashkhur suna fita likitoci suka shigo suka qara duqufa akan zahra. Hmmm ni kuwa amina bayero nace zahra kinga takanki, ALLAH ya baki lpy. πŸ˜­πŸ™

To su mashkhur suna fita suka samu sit suka zauna, mashkhur kuwa wani uban tagumi ya raf ka zuciya cike da damuwa da zullumin. Ahmad ne ya kalli mashkhur tare da sa hannu ya janyewa mashkhur tagumin da yayi! Haba mashkhur yanzu fa addu'a ya kamata kayiwa zahra ba tagumi ba" ahmad ya fad'i hakan fuska cike da damuwa.

Lumshe ido mashkhur yayi ya bud'e sanan yace hmm ahmad kenan, wlh na shiga matsanancin tashin hankalisosai" yanzu in zahra ta mutu ko wani abun ya sameta na cewa dady da ammi me?. Jinjina kai ahmad yayi tare da cewa! Hakane mashkhur bama iya dady da ammi ba har iyayan zahra mai zaka ce musu. Mashkhur bai san sanda yace ai bata da iyaye" ammi da dady ne kwai iyayan ta.

D'an zaro ido ahmad yayi tare da cewa! Kamar ya bata da iyaye tsinto ta akayi ko kuwa wanan waca kalar magana ce haka mashkhur?. Ai sai a lokacin mashkhur ya san ma maganar ta fito, dan shi yayi tinanin maganar iya zuci ta staya. Mashkhur? na tambaye ka kayimin shiru, ahmad ya qarasa maganar yana bin mashkhur da idanuwa.

Ajiyar zuciya mashkhur ya sauke tare da cewa! Aaa ba haka nake nufi ba, abinda nake so nace ma shine iyayanta sun rasu, tun tana jaririya, shiyasa ma a ka kawo ta gidan mu. Karo na farko kenan da mashkhur ya ta6a qarya akan ya rufawa zahra asiri, a idon mutane. Ahmad kuwa nan da nan fuskarsa ta canza kamar ze yi kuka yace! Kai ALLAH sarki zahra na tausaya mata sosai, ya qarasa maganar kamar zai zubar da hawaye.

Shiru mashkhur yayi bai ce komai ba,, ahmad yana qoqarin magana sai ga doctor ya fito, da sauri mashkhur da ahmad suka miqe, domin jin da mai doctor yazo. Ahmad ne yayi qarfin alin cewa! Doctor ya ake cike ne da fatan komai lafiya?, gyad'a kai doctor yayi tare da cewa! Ku kwantar da hankalinku, komai zai tafi dai-dai" yanzu dai abinda ya kamata ayi shine za'a qara mata jini sabida jininta yayi qasa sosai.

Tom doctor sabida mai tayi qarar nan da ta farfad'o, karfa tai loosing d'in memory d'n ta fa, mashkhur ya watsawa doctor tambayar hankali a tashe. Da sauri doctor ya girgiza kai tare da cewa! No abinda yasa tai qarar nan ta firgita sosai lokacin da ta fad'o daga sama, tom shine data farka take ganin kamar a lokacin take fad'owa, kuma rashin jini ne yasa ta suma da ta farka.

Nan da nan mashkhur ya sake nanauyar ajiyar zuciya sai a lokacin hankalinsa ya fara kwanciya. Ahmad kuwa cewa yayi doctor yanzu ya za'ayi a qara mata jinin ko za'a gwada namu ne?. Gyad'a kai doctor yayi tare da cewa! Ehh za'a iya gwada naku in yayi sai a sa mata, yanzu kuzo muje lab room sai a gwada jinin a gani.

Ba 6ata lokaci su mashkhur suka bi bayan doctor domin zuwa a duba jinin nasu, mashkhur har addu'a yake ALLAH yasa jinin ahmad ko nasa yayi dai-dai a sa mata. Suna isa lab room d'in ba 6ata lokaci doctor ya fara gwajin jinin su. Ba a d'au lokaci sosai ba doctor ya gama gwajin jinin mashkhur da ahmad.

Saka mako ya futo mashkhur jininsa O ne zai iya bawa zahra a sa mata. Dan haka ba 6ata lokaci aka bawa mashkhur gado ya kwanta aka fara d'iban jininsa. Ana fara d'iban jinin da gudu ya ringa fitowa alamun da jini sosai a jikinsa. Ledar tana kusan cika doctor yacewa ahmad yaje ya siyowa mashkhur kayan marmari da kayan dai da zai mai qarfin jiki.

Lokacin da ahmad ya dawo har an gama d'iban jinin mashkhur d'in, dan haka zama yayi ya fara bawa mashkhur kayan marmari da multina da ya siyo mai yanaci suna hira abinsu. Bayan mashkhur ya gama ci abincin, bai san sanda bacci ya kwashe shi ba, da yake jiya da daddare bai yi bacci ba" dama haka bacci yake ba'a cin bashin sa......

To fah mashkhur ya d'au tsawan 3 hour's yana bacci, ahmad kuwa yana daga gefan shi yana chatting da gimbiya ilham. Ilham sai faman tambayar shi take wai ina zahra taga jiya da yau bata hau online ba,, kuma zahra tace zata turowa ilham hotan candy da sukayi, yaje ya duba mata ko lafiya. Ahmad kuwa ce mata yayi tanan zazza6i take shi yasa bata hawa online d'in.

Haka dai suka cigaba da chatting cike da soyayya. Suna cikin chatting mashkhur ya farka,, yana farkawa ya kalli ahmad tare da cewa! Ahmad ya jikin nata kuwa?, da sauri ahmad ya kashe data tare da cewa! Tana lpy in sha ALLAH, tinda ka tafi bacci ina nan ban shiga room d'in ta ba, sabida jini ake qara mata. Jinjina kai mashkhur yayi tare da cewa! Tinda ga toilet mu shiga muyi alwala, koh? In mun idar da sallah, sai muje mu dubata?.

Gyad'a kai ahmad yayi tare da cewa! Taso mu tafi ko sai na d'aga kane bazaka iya tashi ba ahmad ya qarasa maganar cikin zaulaya. Murmushi mashkhur yayi tare da cewa! Haba ahmad sai kace wata mace? Kawai dan an d'ibi guntun jini na sai na kasa tashi? Mashkhur ya qarasa maganar yana miqewa daga kwanciyar da yayi.

Hararar wasa ahmad ya watsawa mashkhur tare da cewa! Hmmm nasan ai jurewa kawai kake dan kar nai ma dariya rago kawai. Dunqule hannu mashkhur yayi tare da cewa! To bari na gwada naushin ka ko sau d'aya ne in yaso sai ka sheda inada da qarfi na har yanzu. Da sauri ahmad ya girgiza kai tare da cewa! Aa ni karka illatawa pretty na fuskar nan tawa ina gab da komawa Nigeria tace ta fasa.

Sauke hanun mashkhur yayi tare da cewa! Hmm wanan pretty ta sacewa abokina zuciya zanso na gantaa. Murmushi ahmad yayi tare da cewa! Hmm ai kama ta6a ganinta, jinjina kai mashkhur ya tare da cewa! Wacece? Girgiza kai ahmad yayi tare da cewa! Zan gaya ma amma ba yanzuba sabida tace bataso kasan muna soyayya.

Murmushi mashkhur yayi tare da cewa! Kai ahmad harda sharri haka kawai sabida kar ka gayamin wacece? Ai in tai tsami naji, daga haka mashkhur yayi wucewar shi toilet. Shima ahmad d'in bayansa yabi yana cewa to zakaji kuwa kafin ma tai tsami. Basu d'au wani lokaci ba suka d'aura alwala sanan suka fito suka fara gabatar da sallah.

Bayan sun idar da sallah ba 6ata time suka wuce room d'in zahra. Suna isa suka tarar an cire mata oxygen d'in,, kuma an sa mata jinin mashkhur d'in da aka d'iba harma ya kusan qarewa" sai faman sauke nunfashi take a hankula. Su mashkhur suna shiga ko minti goma basuyi ba doctor mace ta shigo,. Ta basu magungunan zahra sanan ta sanar da su nan da 20 minti zahra zata iya tashi sanan in ta tashi su bata abinci taci, kafin su bata maganin.

Dan haka ahmad fita yayi domin ya siyowa zahra kayan t da cup d'in da za'a had'a mata t da dai saura su. Mashkhur kuwa ahmad yana fita ya d'auki sit d'in shi ya koma kusa da bed d'in zahra, sanan ya ajiye kujerar ya zauna, yana zama ya zuba mata ido. Sosai mashkhur yake qarewa fuskar zahra kallo,.

Tunda yake bai ta6a yiwa zahra kallan qurillah ba sai yau. Mashkhur yana cikin kallo zahra yaga kyakyawan jan bakin ta yana motsawa kamar zatai magana, sosai mashkhur ya sake tsurawa fuskar zahran ido dan son gano mai ke faruwa da ita. On expected zahra ta bud'e kyawawan idanuwan ta tangararai, ai kuwa sukayi 4 eye πŸ‘€ πŸ‘€ πŸ‘€ πŸ‘€ da mashkhur wanda yake mata kallan qurillah..............

Yanzu kunga sai dare yayi sosai nake muku posting koh, wlh abubuwa ne sukayi min yawa shi yasa, sai dare yayi nake samu nayi muku typing d'in. Ina miqa dubun godiya ga masoyana masu bibiyar littafin ADALILINTA ALLAH yabar qauna.

Mu had'e a next page.

ADALILINTAπŸ’œβ€πŸ’œ

BY BAYEROπŸ’œβ€πŸ’œ

Typing...........

*page 82*

sosai mashkhur ya sake tsurawa fuskar zahran ido dan son gano mai ke faruwa da ita, On expected zahra ta bud'e kyawawan
idanuwan ta tangararai, ai kuwa sukayi 4 eye πŸ‘€ πŸ‘€ πŸ‘€ πŸ‘€ da mashkhur wanda yake mata kallan qurillah..............

Kallan kallo zahra da mashkhur, suka shiga yiwa junansu kowa da abinda yake saqawa a ransa. Kawar da idanunsa mashkhur yayi daga kallan zahra tare da cewa! Sannu ya jikin naki?,, mai makwan zahra ta amsawa mashkhur kawar da kanta tayi daga kallansa tai shiru abinta. Mashkhur da yaga zahra bata amsaba cewa yayi! Ko wani abin ne yake damunki ya qarasa maganar yana shafa hanunta daya sha bande ji.

Nan ma zahra bata ce komai ba daga qarshe ma juya kanta tai wani 6angaran domin ta dena kallan mashkhur d'in. Mashkhur kuwa jim yayi yana tinanin mai kuwa yake damun zahra ta share shi haka?. Yana cikin wanan tunanin ahmad ya shigo riqe da ledoji a hanunsa. Mashkhur mai kuma kake anan sai ka tashe ta? Ahmad ya watsawa mashkhur tambayar.

Mashkhur kuwa ajiyar zuciya yayi cikin sanyayiyar murya yace, ai tama tashi daga baccin sannu da zuwa har ka dawo?. Haba ta tashi alhamdulilah, ahmad ya fad'i hakan fuska cike da farin ciki. Ajiye ledojin ahmad yayi sanan ya qaraso kusa da bed d'in zahran.

Please Login or Register in order to submit comment