Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta d'an cikurkud'e ka d'an ka d'an. Ba laifi da ya d'an tara sumar kad'an a kan sa ta d'an taru amma ba can sosai ba.

Sumar kan mashkhur ta birge zahra sosai, sabida tsabar yadda samar mashkhur ta tafi da zahra batasan sanda ta kai hannun ta kan sa ba. Ai kuwa zahra tana kai hannu kan sumar mashkhur, mashkhur ya bud'e idanuwan sa duka biyu, zahra kuwa bama tasan mashkhur yafarka ba sabida yadda ta ji laushen gashin sumar dan hanunta har nitsewa yake sabida tsabar laushi da taushi.

Mashkhur kuwa jikinsa duk ya mace yana so ya d'aga hannu ko dan ya bige hanun zahra daga kansa amma ya kasa dan a halin yanzu ko magana ma bazai iya ba, bare kwakwaran motsi. Zahra kuwa mai makwan ta cire hanunta daga kan mashkhur sai ta fara shafa sumar kansa kamar ta samu gashin jaririn d'an ta. Mashkhur kuwa kuwa lumshe ido yayi sabida har cikin zuciyar shi yake jin yadda zahra take shafa mai sumar kai.

Zahra kuwa sam ta manta da sumar kan mashkhur take shafa dan tama tafi wata duniyar tunani, ta daban. 6angaran mashkhur kuwa sabida yadda yake jin dad'in shafar sumar kansa da zahra take har bacci yayi awan gaba da shi.
6angaran zahra kuwa tana dawowa daga cikin hayyacinta tai sauri ta saki kan mashkhur tana mamakin taya akai take shafa kan mashkhur haka amma bata ankare ba.

A hankula ta leqa fuskar mashkhur ganin yayi bacci, yasa tai saurin sauka daga kan bed d'in a hankula sanan ta canza globe d'in d'akin daga white zuwa blue, tana gama canzawa ta wuce kan sofa ta kwanta. Duk da zahra bataji dad'in kwanciya akan sofa ba haka ta haqura ta kwanta, tana tinanin yanzu haka yaya mashkhur yake quqarin kwana akan sofa nan kullum. A haka dai bacci yayi awan gaba da ita............

ASUBAYI......

kiran asubar farko a kunan mashkhur, amma sam ya kasa tashi saka makwan yadda jikinsa ya mutu sosai. Haka akayi ta kiraye-kirayan sallar asubayi mashkhur yana ji ya kasa miqewa. Har sai da yaji an fara sallar asubar sanan ya d'aure ya fara qoqarin miqewa. Mashkhur yana miqewa ya zubawa blanket's d'in da zahra ta lulu6a mai ido, yana mamaki waye haka ya zuba mai iyayan bargunan.

Can kuma ya hangi zahra da take kwance akan sofa, cikin zuciyar shi yace ai ko ba'a gayamin ba nasan aikin tane wanan.
Nan dan abunda ya faru a daran jiya ya d'an fara dawowa mashkhur. Ajiyar zuciya yayi sanan ya miqe da kyar ya sauka daga bed d'in. yana saukowa daga bed d'in ya wuce toilet jiki a mace yana shiga ya d'aura alwal sanan ya futo. Yana fitowa ya koma ya canza globe d'in d'akin daga blue zuwa white.

Sanan ya nufi wardrobe ya bud'e ya d'auko dadduma, bayan ya d'auko ya shifid'a ta a gabas sanan ya fara gabatar da sallar asubayi dan yau ji yayi kwata-kwata bazai iya fita massalaci ba. Bayan ya idar da sallar ya gama lazimi miqewa yayi ya koma kan bed ya d'auki blanket guda d'aya ya nufi kan sofa da zahra take kwance sakamakwan yadda yaga ta takure jikin ta waje d'aya alamun tana jin sanyi asuba.

Yana zuwa ya fara lulu6a mata blanket d'in a hankula, mashkhur yana cikin lulu6a mata ya saki wani guntun murmushi, a zuciyar shi yace hmm zahra rigima ALLAH na godema jinya tazo qarshe amma dai ko ba komai kin cazamin kai ya qarasa maganar azuciyar shi tare da d'an lakuce mata hancin ta kad'an.

Mashkhur yana gama lulu6a mata blanket d'in ya kowa ya canza globe d'in d'akin daga white zuwa blue, yana canza globe d'in ya koma kan bed ya kwanta, bayan ya kwanta ya shige cikin blanket sanan ya karanta addu'ar bacci ba jimawa mashkhur ya koma bacci...

Qarfe bakwai na safe dai-dai zahra ta farka, tana farkawa ta miqe zauna tana shafa lalausan blanket d'in wanda yake qamshin turaran mashkhur. Ajiyar zuciya zahra tai tare da miqewa dan ko ba'a gaya mata ba tasan yaya mashkhur ne ya lulu6e ta. Zahra wani siririn murmushi ta saki, sakamakwan tunawa da yadda ta ringa cazawa yaya mashkhur kai, kai ni zahra banso jinyar nan ta tsaya haka ba amma komin banza kaji a jikin ka, zahra ta fad'i hakan a zuciyar ta.

Zahra kama hanyar fita daga bedroom d'in tai, a hankula tasa hannu ta murd'a Handel d'in qofar, bayan ta bud'e qofar ta fuce sanan ta rufo qofar a hankula yadda yaya mashkhur bazai tashi ba. Tana fucewa ta nufi bedroom ta, tana shiga ta shige cikin toilet, tana shiga ta hau wanke toilet d'in bayan ta wanke toilet d'in, fita tai ta d'auko towel a wardrobe.

Tana d'aukowa ta koma toilet tai wanka, sanan ta futo, riga mara nauyi. Nan da nan zahra taji iska tana shigar ta kota ina. Ajiyar zuciya ta sauke sanan ta dawo kan bed ta fara ninke kayanta, bayan ta gama ninkewa trolley ta d'aukko ta fara jerasu, sabida zahta tasan sun kusan barin russian su koma nigeria shi yasa bata shan wahalar mayar fa kayanta wardrobe ba, iya na baccin ta kawai ta bari a cikin wardrobe d'in.

Bayan zahra ta gama shirya kayanta bedroom d'in ta fara gyarawa, staf zshra ta share shi sanan ta goge shi ta fesa mai air freshener, d'aki ya d'auki qamshi yayi tsaf-tsaf abinsa. Daga haka zahra ta fara sa kayanta data ware, atanfa ce riga da skert ce mai kyau wadda zahra bama ta ta6a sa kayan ba. Lokacin da zahra zata sa kayan ta d'anji jiki sosai da yake kayan sun d'an matse ta.

Zahra tayi mamakin hakan sosai, sabida time d'in da ilham ta kawo mata kayan zuruf suka shige ta, amma sai gashi yanzu da kyar ta sa. Kayan sun d'an kama jikin ta sosai. Zahra tana gama sa kayan ta fuce ta wuce kicin, tana shiga ta fara feraye dankali bayan ta gama ferayewa soyawa tai, tana gama soya dankali ta dafa tea, sanan ta zuba ta goma falo ta zauna akan draining taci abinta hankali kwance.

Bayan zahra ta gama ci tinani tai ya kama ta kai wa yaya mashkhur ko iya tea ne daga nan sai ta duba jikin na shi. Haka kuwa zahra tai, ta zuba tea d'in a cup d'in sanan ta nufi hanyar bedroom d'in mashkhur d'in. Zahra tana zuwa ta murd'a Handel d'in qofar a hankula, ta shiga baki d'auke da sallam. Zahra ji tai shiru ba'a amsa sallamar ba.

Rufe qofar zahra tai a hankula, sanan ta kama hanyar zuwa bed d'in. Zahra tana qarasawa, ta kalli mashkhur da yake qudindine a blanket dan har kan sama yana ciki blanket d'in. Kawar da kai zahra tai, sanan ta fara tinanin ta tashe shi ko kuwa. Hmm zahra kenan jikin kine zai gaya miki wlh, yadda kika samu lafiyar nan ai jibgar ki zai yi karma ki soma Wlh.

Duk zuciyar zahra ce take gaya mata haka. Zahra kuwa a hankula ta juya gefe sanan ta fara qoqarin ajiye cup d'in akan dorowar gefan bed. A dai-dai lokacin mashkhur ya farka tare da yaye blanket d'in, daga fuskar shi. Kamar almara mashkhur yaga mutum a gefan sa. Da sauri mashkhur ya zubawa, zahra ido, da take qoqarin ajiye cup d'in tea a gefan dorowar bed d'in.

Mashkhur gani yayi zahra ta sake haske sanan kuma tayi wani girma. Zahra tana juyowa tai 4 eyes da mashkhur ya zuba mata kwala-kwalan idanuwan sa. Zahra kuwa sai da ya d'an zabura, ita da ta gan shi a cikin blanket yana bacci kafin ta ajiye tea ta jiyo har ya farka ikwan ALLAH, zahra ta fad'i hakan a zuciyar.

Muryar mashkhur zahra taji ta daki kunta yaba cewa! Ke mai ya kawo ki bedroom d'in nan mashkhur ya fad'a fuska a had'e. Zahra kuwa d'an shafa wuyan ta tai tare da cewa! Dama cewa nai bari na kawo ma ruwan tea kasha, ya jikin naka. Wani kallo mashkhur ya watsa mata tare da cewa! Ban sani ba muguwa dama can da lafiyar ki kike wahalar dani koh?.

Dan turo baki zahra tai tare da cewa! Ina fah dama kasan ance kwanciyar wani tashin wani, to inaga dai hakan ne ya kasan ce damu, kana kwanciya cuta ni kuma ina tashi zahra ta qarasa maganar tana qarkata d'an kwalin atanfarta. Hakan da zahra tai sai mashkhur yaji sa birge shi sosai kuma ta bashi nishad'i, dama rashin kunyar zahra tini ta dena bawa mashkhur haushi kawai dariya take bashi.

Mashkhur lumshe ido yayi ya bud'e sanan ya fara yun kurin tashi zaune zahra kuwa tana ganin hakan ta kama hanyar fita gudu-gudu sauri-sauri, mashkhur kuwa binta yayi da ido yana cewa tsoran banza da ki tsaya mana. Juyowa zahra tai tare da murgud'awa mashkhur baki tana cewa! Baza'a tsaya ba d'in. Daga haka ta fuce da saurin ta.

Daga yadda zahra take tafiyar ta har abinda tai mashkhur ji yayi hakan ya sake bashi ni shad'i. Wani qasai taccan murmushi ya saki sanan ya miqe ya shige toilet yayi brush bayan ya gama yayi wanka sanan ya futo yana fitowa ya goge jikinsa da towel, bayan ya gama ya sa kaya, direct ya wuce ya d'auki cup d'in tea d'in da zahra ta kawo mai ya fara shan tea d'in...................


ADALILINTA πŸ’œβ€πŸ’œ

AMINA BAYERO πŸ’œβ€πŸ’œ

Typing..........

Double page

Nigeria................

Ilham tana fita dady yayiwa ahmad gyaran murya wanda ya shagala da kallan ilham wadda ta d'an jima da fucewa daga sitroom d'in. Jiyowa ahmad yayi da sauri ya sunkuyar da kansa cikin jin kunya. Dady kuwa kawar da zancan yayi tare da cewa! Malam ahmad inajin ka. Ahmad kuwa ba 6ata lokacin ya fara korawa dady jawabin abinda ya kawo shi.

Am dama dady abinya ya kawo ni shine inaso na sanar da kai, ina son ilham shine nace bara nazo na gayama a bani dama mu fahimci junan mu daga haka sai manya su shiga zance in ba damuwa dady. Jinjina kai dady yayi a zuciyar shi yace dama buri yayi kama da mutum a fili kuma yace okay shine ya kawo ka?. Da sauri ahmad ya gyad'a kai tare da cewa! ee dady.

Jinjina kai dady yayi tare da cewa! Masha ALLAH gaskiya kayi tinani mai kyau da ka sameni da zancan amma ka bari tukunna zanje na samu maman ta in mun shawarta ta kuma ita ilham d'in ta amince, sai a baka damu kazo wajan ta ko zaku samu ku dai-dai ta. ahmad kuwa a zuciyar shi cewa yayi dady ai muda ilham mun dai-dai ta kawai amincewar ki muke nema, afili kuma cewa yai tom shikenan dady ALLAH yasa muji alkhairi.

Jinjina kai dady yayi tare da cewa! Ameen ahmad To ya 6angaran abokin naka naga ka dawo kuma su basu dawo ba lpy dai koh?. Gyad'a kai ahmad yayi tare da cewa! dady suma suna kan hanya zuwa ni d'in ne nai saurin dawowa ka wai, amma lpy su qalau suma very soon zasu dawo ai mun gama jarabawar gaba d'aya. Gyad'a kai dady yayi tare da cewa tom shikenan ALLAH ya dawo da su lpy.

Daga haka dady da ahamda suka d'an yi hira sosai, bayan sun gama ahmad yayiwa dady sallama, dady yace mai in sha ALLAH, zuwa gobe sai ya dawo duk shawarar da suka yanke sai yaji. Ahmad yana tafiya dady ya wuce bedroom d'in, shi yana shiga ya d'auki wayar shi ya kira ammi.

Bayan ilham ta kai wa Ahmad ruwa tana futowa ta koma bedroom d'in ammi. Suna shiga ammi ta fara zaulayar ta da hmm har kin dawo kenan, kinje kinga farin ciki rai nake koh? Murmushi ilham tai tare da cewa! Ammi kenan kinga yadda naga ya sake kyau kuwa, kai dama haka yake da kyau ni ban sani ba ma, Ilham ta qarasa fad'in haka tana cire hijab d'in jikin ta.

Sakin baki ammi tai tana mamaki yadda ilham take gaya mata magana ko kunya. Ilham kuwa zama tai ta cigaba da korawa ammi bayani tun ammi tana mamakin ilham har ta saki jikin ta, ta biyewa ilham suka cigaba da hirar ahmad. Bayan kamar 50 minutes da shigowar ilham, sai ga wayar ammi tana ringing. Da sauri ammi ta d'auki wayar ta tare da duba sunan.

Sunan dady ta gani da sauri ammi ta d'auka tare da qarawa a kunan ta tana sallama. Daga haka ammi tai shiru ba jimawa kuma tace tom ganinan zuwa. Ammi tana ajiye wayar ta kalli ilham tare da cewa! Dady ne yake kira na kuma nasan akan maganar ki da ahmad ne. Da sauri ilham ta d'an zabira tare da cewa! Haba ammi taya kika gane?.

Murmushi ammi tai tare da cewa! Ni ai na sani kuma nasan shawara ce zamuyi akan zancan ki da ahmad ba dai kina so ayi miki aure nan kusa ba?. Da sauri ilham cikin zumud'i tace ee wlh ammi inaso, girgiza kai ammi tai tare da cewa! Ilham kenan yaro yaro ne bai san wuta ba sai ya taka itafa soyayayar nan da kike gani ana aure zaman haquri akeyi zaki iya ko?.

gyad'a kai ilham tai tai da cewa! Wlh ammi zan iya insha SLLAH baza ku jiba ba zaku gani ba. Sosai maganar ta bawa ammi dariya cikin dariya ammi tace oho inma munji ko mun gani haquri ne namu tinda dai kina so in sha ALLAH zan yi qoqari wajan dady ya amince da zancan daga haka ammi ta kama hanyar fita daga d'akin zuciya fass da nishad'i sabida yadda taga lokaci guda Ilham ta canza ko kunyar tama ta dena ji.

Ilham ammi tana fita da miqe ta daka uban tsallan faran ciki sanan ta d'auki wayar ta ta fara darling number ahmad. Kira biyu ahmad ya d'auka, bayan sun gama gaisawa ahmad ya fara sanar da ita yadda sukayi da dady. Murmushi ammi tai tare da cewa kai dai hubby ka kwanta da hankalinka kasan yadda mukayi da ammi kuwa?.

Ahmad da yake driving d'in mota girgiza kai yayi tare da cewa! Aaa my pretty sai kin gaya min. Lumshe ido ilham tai sanan fara sanar da ahmad yadda sukayi da ammi. Ahmad yayi farin ciki sosai tare da cewa! In sha ALLAH, ilham bazaki nadamar za6ata amatsayin miji ba yadda kika nunamin hallacci wajan ammi har ta amince nima zanso ki ko minyi auran bazan bari ki zubar da hawaye ba..............

Ammi tana murd'a Handel d'in qofar baki d'auke da sallama ta shiga. Tsaye ammi taga dady a bakin merro yana taje sumar kansa da kum, yasha farar shadda kai yayi kyau kamar wani sauri kai bakace ya ajiye mashkhur da abdul ba kai harma haidar da faruq. Amsa sallamar, dady yayi tare da cigaba da taje kan nasa. Ammi kuwa qarasowa wajan mudubin tai tare da cewa! Ina zuwa haka ko dai ko dai?.

Kallan ammi dady yayi ta merro tare da cewa! Ko dai ko dai mai? Ki qarasa mana in ba tsoro ba. Wata siririyar dariya ammi ta saki tare da cewa! Ina nufin ko dai wajan ta ukun za'a ne? Murmushi dady yayi tare da cewa! Aa wacece ta ukun ni banma santa ba, oho ai kai zan tambaya ni ina gida ina zan san ta kuwa?.

Ke dai kawai kice yau kishin kine ya motsa amma kinsan ai ke kin ishe ni ba sai na qaro wata ba. Dan harara ammi ta watsawa dady tare da cewa! Ina ai ni duk dad'i bakin nan naku na maza na san shi, tinda kasan na ishe ka kaje ka qaro ta biyu lokacin ma ina qarama sosai, mashkhur fa kawai na haifa shima ko wani ishashan wayo bai yi ba.

Ah ki dena fad'in hakan kema kinsa kina rai na fa wanan d'in ma qaddara ce ALLAH ne ya rubuta hakan amma nifa ke ka d'ai ce a rai na. Ta6e baki ammi tai tare da cewa! Daga baya kenan ni fa nasan dad'in bakin ku na maza, gani nan dai nazo wace magana zamuyi? Ammi ta qarasa maganar tana wucewa kan bed tare da zama a gefan gado.

Shima dady dawowa kusa da ammi yayi ya zaunavtare da cewa! Yauwa wata magana ce mai mahimmanci nace bari dai nazo muyi shawara karna yanke hukunci ni ka d'ai, gyad'a kai ammi tai tare da cewa! Gaskiya ne ina ji to. Nan da nan dady ya fara korawa ammi jawa bi kamar haka! Nasan kinsan ahmad abikin mashkhur wanda suke karatu a russian tare kin gane shi?.

Gyad'a kai ammi tai tare da cewa! Na gane shi wanan yaran mai kirki koh? Ehh shifa to dama shine yace wai yana son 'yar wajan mu ilham, a bashi dama su fahimci junan su daga nan in sun fahimci junan su sai ya turo magabatan sa, to shine nace ya kike ganin za'ayi ni dai nasan ahmad mutumin kirkine sosai ta fanin hankali da nutsuwa da tarbiya, ya kai amma kina ganin hakan zai yuwu kuwa, dady ya qarasa maganar yana tsare ammi da ido.

Ammi kuwa cewa tai! Qwarai ahmad mutumin kirkine yaya, kawai ina ganin a bashi dama koh?, jim dady yayi can kuma yace! amma maryam kina ganin kamar in mukayi hakan bai dace ba, ilham fa yarinya ce, kar muyi mata auran wuri fa. Cikin mamki ammi tace auran wuri kuma haba yaya, tana wajan shekara 18 year's zakace mata yarinya, duk wani abu da ya kamata 'ya mace ta mallama ilham ta kai ta cika.

Kai auran wuri ma ya wuce na zahra wanda akayi mata tin kafin tai candy, tana fa s. s 2 mukayi mata aure fa, kuma kasan dai abinda mukayiwa zahra zamu iya yiwa Ilham duk d'aya suke a wajan mu, itama fa ilham d'in tana san auran to ai sai ai mata. Jinjina kai dady yayi tare da cewa! Gaskiya kika fad'a maryam amma wani hanzari ba gudu ba ita ilham ce tace miki tana son aure.

Murmushi ammi tai tare da cewa! Ka kira ta kaji da bakinta sun jima suna soyayya da shi bamu sani ba, kuma ita da bakin ta tace min tana son aure dama ni sam banason karatun nan mai tsayi in tayi aure tayi a d'akin ta yanzu duk malaman yanzu 'yan iskane lalata d'alibai fa suke kawai yaya tinda ta nuna son auran nan muyi mata.

Jinjina kai dady yayi tare da cewa! Tom shikenan jeki ki kirawo ta naji daga bakin ta, kinga in ta amince sai na aurar da su itama rukkayya, kinsa doctor habib yace tinda an aurar da mamana a bashi ilham ko dai daya daga cikin yaran gidan nan, kinga kawai sai na bashi rukkayya. Jinjina kai ammi tai tare da cewa! Haka ne bari naje na kira to.

Dady cewa koh karki wahalar da kanki kirata ta waya. Daga haka ammi ta d'auki wayar dady ta kira ilham, ilham tana d'agawa ammi tace tazo dady yana neman ta. Daga haka ammi ta kashe wayar, ta ajiye gefe, sanan ta zubawa dady ido tana kallansa, shima dady da yaga haka zuba mata ido yayi suka fara kallan junan su kamar wasu sababan masoya.

Knocking d'in ilham ne ya dawo da su daga hayyacin su, sabida yadda suka zira junan su ido duk sai suka shagalta. Murya a sanyaye ammi tace ilham shigo. Ilham murd'a Handel d'in qofar tai sanan ta shiga baki d'auke da sallama,. Har ammi da dady suna had'a baki wajan amsawa ilham sallamar,.

Ilham tana shigowa ta zo gaban su dady ta zaun abinta tare da cewa! Dady gani nan, kallan ta dady yayi tare da cewa! Dama akan maganar ahmad ne mai son ki, shine nake so na tabbaye ki, kin amince da shi?. Shiru ilham tai tare da sunkuyar da kai qasa cikin jin kunyar dady dan ita yanzu tama dai na jin kunyar ammi kamar dady.

Ammi ce tace muna jinki fa? Sake sunkuyar da kai ilham tai tare da cewa! Ammi duk abinda kuka yanke dai-dai ne, gyaran murya ammi tai tare da cewa! Ni dai ba ruwana in dadyn ki ya yanke hukunci karki kuka dani ki kuka da kanki tinda bazaki iya fad'ar gaskiya abinda kike so ba. Miqewa tsaye Ilham tai sanan ta kama hanyar fita, Sai da tazo baki qofa sanan tace ehh na amince.

Sanan ta fuce da sauri, nan da nan dady ammi suka kwashe da dariya sabida ilham Ta basu dariya sosai. Bayan sin tsagai ta da dariyar ammi ta kalli dady tare da cewa! Hmm gaji da kunan ka koh? Kwarai naji ai ilham tana da wayo sosai, ai ko ba komai mun kusan tara jikoki a gidan nan. Murmushi ammi tai tare da cewa ai kuwa abun kamar wasa, Daga haka ammi tai komawar ta tsakiyar gadon daday tai kwanciyar ta tare da cewa! A dawo lpy ni dai ina nan bacci zan yi.

Miqewa dady yayi ya koma qofa ya rufo tare da dawo wa, ammi da take a kwance kallan dady yayi tare da cewa! Naga haka kuma kai da zata fita ka rufo qofa ka dawo?. Cire rigar shadda dady yayi tare da ajiye ta gefe yana cewa! Na fasa fita nima bacci zanyi. Hmm ka dai ji da shi ni bazan kulaka ba ammi ta qarasa maganar tana juya baya. Murmushi yayi tare da cewa! To bari dai nazo na gwada miki irin qaunar da nake miki tinda kinqi yards, ya qarasa maganar yana fad'awa kan bed..............


ADALILINTAπŸ’œβ€πŸ’œ

BY AMINA BAYERO πŸ’œβ€πŸ’œ

GARA6ASA page. πŸ˜‚

Russian.........

Yau kimanin kwana uku kenan da barin zahra d'akin mashkhur. A cikin kwana ukun nan sun koma rayuwar su kamar da, ba mai cewa a d'an uwansa uffan, zahra ko kallo bata ishi mashkhur ba shima mashkhur ko kallo zahra bata ishe shiba. Shaye-shaye mashkhur kuwa ya dena ko sha'awa baya bashi. Kuma yaune ta kasance zahra zatai tsarki jininta ya d'auke.

Misalin qarfe 4:30am zahra ta shafa shampoo bayan zahra ta gama shafa shampoo d'in zama tai sabida ya d'an kama kanta, misalin qarfe biyar na yamma zahra ta shiga toilet ta wanke kan nata sosai da yake yayi datti kwana biyu bata wanke shi ba sabida larura. Bayan zahra ta wanke kan ta debo maya mayan wanke gashi tai da sabilan shampoo ta sake wanke kan nata tasss.

Kai mashkhur ALLAH kan zahra ya wanku yayi baqi wulik mashkhur

Please Login or Register in order to submit comment