Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jin tsoron sa kamar da ta dena saki jiki da shi kuma.

Cikin damuwa mashkhur ya miqe ya nufi kan bed d'in jiki a sanyaye. Wani irin mugun tausayi zahra ta sake bawa mashkhur ganin yarda jikin ta yake rawa a blanket. A hankula mashkhur ya janye blanket d'in, yana janyewa zahra ta rufe idon ta gam tare da duqunqune jikin ta alamun tsoro. Cikin sanyayiyar murya mashkhur yace my teady?.

Baki na rawa zahra tace dan Allah kayi haquri karka dake ni, ni kawai ka kai ni gida tinda ka dena sona zahra ta qarasa maganar zafafan hawaye suna zobowa daga idanuwan ta. Da sauri mashkhur ya qara matsawa kusa da zahra cikin tausayawa ya kifa fuskar sa a fuskar zahra tare da cewa i'm so sorry teady na, wallahi ban dena sonki ba ina qaunar ki teady na.

Zahra bana so kiyi nisa dani ko kad'an na saba rayuwa da ke zahra ta, shi yasa kikaga bana son ki tafi ki barni. Pls ki yafemin wlh bada son rai na nayi miki shouting ba, kin san dai bana son hayaniya kuma bana son naga kina zubar da hawaye yana ta6amin zuciya ta, kuma gashi na rarrashe ki kinqi haqura shi yasa nai miki shouting, nima kai na ban san nai miki hakan ba.

Cikin muryar tsoro zahra oh yanzu yaya mashkhur baka ganina a matsayin mata kana nufin zaka iya cigaba da duka na, in na 6atama rai?. No my teady waya gaya miki haka, ni ai ba jahili bane, sam bazan daki matata ba ko a russian ban ta6a dukan ki ba har muka qare zaman mu bare ma yanzu da kika zama jinin jikina. Da sauri zahra ta bud'e ido cikin mamki tace anya kuwa baka ta6a duka na a russian ba.

Kwarai my wife ni ban ta6a dukan ki ba ki tina sai dai na baki punishment koh?. Jim zahra tai tana tinanin tabbas haka zanca mashkhur yake ko a russian bai ta6a dukan ta ba sai dai ya bata punishment mai wahala sosai sai kuma time d'in daya shaqeta dan yaga ahmad yana mulmula mata kai. Mashkhur sumar sa ya goga a kumatun zahra sanan yace, shikenan my wife tinda kin za6i kibar mijinki a mawuya cin hali ki tafi baki har one week hakan shine farin cikin ki na amince miki kije.

Mashkhur ya qarasa maganar cikin murya mai ban tausayi jiki ba kwari ya d'auke fuskar sa daga ta zahra sanan ya miqe yasa hularsa yana cewa tashi ki wanke fuskar ki na kai ki. Itama zahra tashi tai zaune mashkhur duk ya gama kashe mata jiki da kalamai nan da nan ya mashkhur ya sawa zahra kokwantan ta tafi ko kuma ta tsaya wajan mijin ta.

Zahra zubawa mashkhur ido tai cikin tausayawa tabbs tasan mashkhur in bai damu da kasuwa ba ko sauti baya bayarwa, tabbas zahra tasan mashkhur yana son ta sosai in ta tafi ta barshi zai shiga damuwa. Nan da nan zahra tausayin mashkhur ya kamata dama dai kunsan zuciyar mata tana da sauri karyewa musamman ma irin ta zahra mai tausayi.

Jiki a sali6e zahra ta fad'a kan qirjin mashkhur fuska cike da hawaye da majina cikin kuka tace dan Allah yaya mashkhur kayi haquri na haqura da zuwa zan zauna tare da kai zahra ta qarasa maganar tana qanqame shi. Shima mashkhur rungume ta yayi cikin farin ciki yace yauwa my wife ALLAH yayi miki albarka, shi yasa nake qara qaunar ki sabida kina da tausayi ga haquri.

Dai dai kunan ta mashkhur ya fara yi mata magana kamar mai rad'a. Hmmmm tofa nima amina bayero naso naji mai mashkhur yakecewa zahra dan har kasa kunne nayi amma banji ba, wayyo da naji dana gaya muku. Mashkhur yana gama yiwa zahra rad'a zahra ta saki mashkhur daga hugg d'in da tai mai ta d'ago fuska cike da farin ciki tana sakin dariyar jin dad'i.

Bayan zahra ta gama dariyar cewa tai hmmm ina qaunar ka mijina soyayya mai qarfi har muddin rai na. Murmushi mashkhur yayi tare da cewa hmm nima ina qaunar ki matata uwar 'yaya na mai d'aki na yi sauri kije ki wanke fuskar taki kizo mu tafi. Ba musu zahra ta shiga toilet ta wanko fuskar ta sanan ta d'auki babban mayafi ta yafa ta rufe jikinta ta ko ina.

Miqewa mashkhur yayi tare da cewa yauwa matata wanda tasan ya kamata. Dariya zahra tai tare da rufe fuskarta da tafikan hanun ta. Hanun ta mashkhur ya jawo tare da cewa tawo muje kar yamma tayi. Murmushi zahra tai sannan ta kalli qirjin rigar mashkhur tare da cewa kallifa rigar ka ta 6ace da majina ta da hawaye na mazakaje ka canza ba?.

Murmushi mashkhur yayi tare da shafa qirjin sa yace na gani mana, amma dai ki barni a haka tinda dai nasan zanyi missing d'in ki kafin nazo na d'auke ki kinga ai sai na ringa ganin jirwayan hawayan naki ko ya d'ebe min kewa. Murmushi jin dad'i zahra tai tare da cewa gaskiya ne my hero daga haka ta juya ta d'auko wayar ta wanda ilham ta cika ta da miss call yafi goma.

Bayan zahra ta d'auko wayar ta mashkhur kama hanun ta yayi suka sauka kan bene suna hirar su ta masoya. Daga haka suka nufi wajan parking space, sai da zahra ta za6i motar da take so su fita aciki, sanan mashkhur ya koma cikin gida ya d'auko key d'in motar, bayan ya fito ya bud'ewa zahra mufin mota ta shige,. Bayan ta shiga ya rufe murfin shima ya shige sanna ya tayar da motar mai gadi ya bud'e musu get suka fuce zuciyoyin su cike da qaunar juna.

Oh mata da miji kenan ba mai shiga tsakanin su sai Allah wato har sun jone sun barmu baki sake.πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

To fa mu had'e a next page my fan's.

ADALILINTAπŸ’œβ€πŸ’œ

BY AMINA BAYERO

TYPING.........

*page 134*

Bayan ta shiga ya rufe murfin shima ya shige sanna ya tayar da motar mai gadi ya bud'e musu get suka fuce zuciyoyin su cike da qaunar juna.

Bayan sun qarasa gidan su suna shiga gidan mashkhur yayi parking zahra ta fara qoqarin bud'e murfin motar amma gam. Wata doguwar ajiyar zuciya zahra ta sauke tare da cewa meye haka yaya mashkhur ka bud'e min qofar mana. Cikin muryar mai sace zuciya mashkhur yace to sai ki tafi ki barni ba sai ki jira mu tafi tare ba. Oh dole sai mun jera kowa yasan tare mukazo gidan kenan?.

Zahra ta qarasa maganar tana gyara mayafin ta wanda ya zamar mata kaya. Uhmmm kowa sai ya sani mashkhur ya qarasa maganar yana ruqo hanun zahra. Zahra bata sake cewa komai ba tai shiru, mashkhur kuwa hanun zahra ya cigaba da shafawa cike da soyayah dan sun d'au wajan 5 minutes a haka ba wanda yacewa d'an uwan sa qala.

Can zahra ta fizge hanun ta tare da cewa wai kai baka son zuru ba, dan ALLAH ka bud'e min na shiga ciki tin dazu sai jamin rai kake. Murmushi masoya mashkhur ya zubawa zahra tare da cewa ki bari mana nifa ban qoshi da ke ba mashkhur ya qarasa maganar cikin kasalaliyar murya. Cikin 6acin rai zahra tace to tinda baka gaji dani ba sai ka cinye ni ka wuta.

Oh haka kikace mashkhur ya qarasa maganar yana lashe kyayawan lips d'in shi. Hararsa zahra tai tare da cewa ee haka nace, to ta ina zan fara cinye kin? Mashkhur yayiwa zahra tambayar cike da shauqi da tsokana. Rai a had'e zahra tace ta inda zai fi maka sauqi, juyowa mashkhur yayi sosai yana kallan zahra.

Sanan ya d'orawa dugwan kyakyawan dan yatasan sa a kan le6an zahra na qasa tare da cewa tanan zan fara nasan kema zaki so hakan koh?. Ya qarasa maganar yana mata wasa da dogwan yatsan sa a le6an ta, kamar dai tafiyar tsutsa. Zahra da ta gama qulewa sai da ta bari mashkhur ya shagala da wasa da le6an nata ta bud'e bakin ta tare da gantsara mai cizo.

On expand mashkhur yaji cizon zahra wani siririn iwu dad'i ya saki, dan shi cizon ma dad'i yayi mai da yake ba can sosai ta cije shi ba. Zahra kuwa bata saki yatsan mashkhur ba haka tai tabi tana ciza a hankula a hankula. Mashkhur kuwa lumshe ido yayi lokaci qanqani ya tafi wata duniyar shauqi. Ya lumshe ido kamar mai bacci.

Zahra da ta shagala tana cizon yatsan mashkhur kamar ance ta d'ago tana d'agowa taga mashkhur ya lumshe ido kamar mai bacci. Da sauri ta saki hanunsa ta dena cizo, sanan ta daki qirjinsa a hankula da hanunta tana cewa wai bazaka bud'e min qofar na fita bane?. A hankula mashkhur ya bud'e kyawawan idanuwan sa ya zuba su akan zahra.

Lokaci guda idanuwan mashkhur suka canza suka komai kamar na mai jin bacci. Hanunsa zahra ta riqe cikin muryar rarrashi tace dan Allah hero na ka bud'e kaji kasan ina qaunar ka fa sosai. Murmushi mashkhur yayi tare da cewa tom shikenan teadyna tinda kina so zan bud'e amma da sharad'i fa. Kamar zahra zatai kuka tace namenene kuma?.

Kawo kunan ki kiji, a hankula zahra ta matsarwa da mashkhur kunan ta. Shima a nitse ya sai ta bakinsa saitin kunanta ya fara yi mata rad'a. Sautin voice d'in rad'an mashkhur ma kad'ai ya isa ya shagalar da mutum sabida dad'i murya,. Naso naji abinda mashkhur yake cewa amma sabida sautin dad'in murya sa danaji bacci ne kawai yayi awan gaba dani amina bayero a wajan. 😒

Bayan mashkhur ya gama yiwa zahra rad'a dagowa zahra tai sanan tasa tafin hannuta ta rufe fuskar ta alamun kunya. Wani kallo mai cike da fassarori kala-kala mashkhur ya watsawa zahra tare da cewa kin yarda koh?. Cikin kunya zahra ta d'aga kai sanan tace hmmm na yarda, cikin farin ciki mashkhur yace yauwa my wife i love you to the extent of my life

Mashkhur ya raqasa maganar yana bud'e qofar motar. Yana bud'ewa zahra ta fuce a hanzarce, shima mashkhur zahra tana fita ya futo ya rufe murfin motar yana kiran ta amma ina ko jiyowa batayi. Wani siririn murmushi mashkhur ya saki yabi bayan zahra a zuciyar shi yace hmmm zamu had'u ne dama nasan ladabin muzuru kikeyi min.

Zahra tana shiga babban falon gidan ta saki doguwar ajiyar zuciya alamun tasha, zahra idon ta yana sauka akan yaya abdul da yake zaune akan kujera yana danna waya ta saki wani qasaitaccan murmushi, tare da cewa oyoyo my yaya abdul zahra ta qarasa maganar tana qarasawa inda.

Da sauri abdul ya dago yana ganin zahra ya saki wani tattausan murmushi tare da cewa your welcome my sister yana qarasa maganar yana kashewa zahra ido d'aya alamun yaji dad'in ganin ta. Zahra taso dai tai hugg d'in abdul kamar yarda ta saba amma taga bai bata fuskar hakan ba kuma ita taji ta kasa hakan bugu da qarima tasan mashkhur yana nan tafe a bayan ta.

Dan haka qoqarin zama ta farayi a kusa da shi, a dede lokacin mashkhur ya shigo baki d'auke da sallama. Mashkhur yana shigowa ya fara jifan zahra da wani kallo wanda ita ka d'ai tasan mai yake nufi. Da sauri zahra ta matsa can qarshan kujerar da abdul yake a zaune ta zauna. Mashkhur yana qarasowa ya saki fuskar shi tare da miqawa abdul hannu suka gaisa.

Bayan sun gama gaisawa zama mashkhur yayi a tsakiyar zahra da abdul. Zahra kuwa lokaci guda ta canza fuska dan sam batajin dad'in abinda mashkhur yake mata yanzu yana nufin zai rabata da yaya abdul d'in ne ko kuwa?. Haka mashkhur yayiwa zahra fin qarfi tana son magana da yaya abdul amma ya hana ta sai wani jansa da hira yake kuma in tayi qoqarin magana sai ya take mata qafa ta gefe.

Zahra kuwa sai zafgawa mashkhur harara take amma mashkhur sam bai masan tanayi ba. Can mashkhur ya juyo ya kalli zahra tare da cewa taso muje mu gai da ammi, zahra rai ba dad'i ta miqe ba tare da tacewa mashkhur komai ba tai hanyar sama abinta. Shima mashkhur miqewa yayi yabi bayan zahra.

Zahra tana hawa sama bata tsaya ko ina ba sai bedroom d'in ammi baki d'auke da sallama ta shiga rai ba dad'i. Fuska a sake ammi ta amsa gaisuwar tare da cewa uhmm ni ai harna cire rai da zuwan ki zahra. Rai ba dad'i zahra ta qarasa ta tsuguna tare da cewa ina wuni ammi?. Lafiya qalau zahra tashi ki zauna naga kina wani had'e rai sai kace wanda akayiwa dole ko bakya son zuwa ne dole yayi miki.

Miqewa zahra tai ta zauna a gefan ammi tare da cire mayafin ta tana cewa nifa ammi sam bana jin dad'i abinda yaya mashkhur yake min. Zaro ido ammi tai cikin mamaki tace to mai kuma yake miki ya ALLAH?. Kumar zahra zatai kuka tace yanzu ammi sam yaya mashkhur baya so na ra6i yaya abdul so yake ya rabani da shi ba kuma!!.

Zahra rufe bakin ta tai gam saka makwan jin sallamar mashkkhur alamun zai shigo. Mashkhur yana shigowa ya qaraso inda ammi da zahra suke zaune ya tsuguna har qasa sanan yace ammi ina wuni da fatan mun same ku lafiya?, murmushi ammi tai sanan tace! Lafiya qalau mashkhur kuma da fatan kun iso lafiya kuma kuna zauna qalau.

Murmushi mashkhur yayi tare da d'an satar kallon zahra da ta had'e rai gam yace muna lpy ammi ba komai a tsakanin mu sai zaman lafiya. Tom masha ALLAH haka muke fata ammi ta fad'a cikin jin dad'i hakan. Miqewa mashkhur yayi sanan yace bari naje na gaida hajiya kaka, tom shikenan cewar ammi.

Mashkhur yana fita ammi ta mai da kallan ta kan zahra tare da cewa ki tashi ki bishi ku tafi tare mana. Da sauri zahra ta girgiza kai tare da cewa aa ni daban zani ko so kike yarda ya hanani magana da yaya abdul itama hajiya kakan ya hanani magana da ita. Murmushi ammi tai tare da girgiza kai tace haba wane shi ya hanaki magana da hajiya ai bazai yi hakan ba.

Amma ammi ya hanani zama a kusa da yaya abdul kuma ya hanani magana da shi, zahra ta qarasa maganar kamar za tai kuka. Oh ya haqura mana zahra akan wanan zaki d'aga hankalin ki, taya mashkhur zai rabaki da abdul kowa yasan ki ai ya sanki da abdul kuma nasan kin shaqu da abdul fiyema da mashkhur ki kwantar da hankali ki in sha ALLAH ba abinda zai rabaki da abdul sai mutuwa.

Amma ammi sabida mai yaya mashkhur baya son ma'amalata da yaya abdul. Hmmm ni nasan halin mashkhur kawai yana kishi da abdul ne akan ki, kuma da kin san dai baya yi miki haka sai yanzu da ya fara son ki duk kishi ne yake sashi hakan ki bishi a hankula komai zai zo da sauqi, duk da kuwa nasan ba lallai ki shawo kan shi da wuri ba.

Murmushi zahra tai a zuciyar ta tace hmmm ammi kenan ai yanzu yaya mashkhur yarda kika son yaro haka na mai da shi duk abinda nake so shi yake dole yayi min shi. Allah ko zahra lallai kam so ba wasa ba, da sauri zahra ta jiyo tana mamaki taya akai tai su6utar baki a gaban ammi. Hmm nima haka nake so zahra a ciki qanqanin lokaci ki canza min shi ya zama mai sauqin kai.

Girgiza kai zahra tai tare da cewa har yanzu fa ammi yaya mashkhur yana nan akan bakarsa na taurin kan nan, wlh ba komai yake iya yimin ba, amma dai yawan ci yana qoqarin ganin yayi abinda nake so. Yanzu ma ya hanani zuwa na kwana bayan biki na koma, nayi-nayi da shi yaqi.

Ki kwatar da hankali ita fa mace tana iya canzawa namiji ra'a yi da kisisina. Ki ringa bin komai a hankula duk yarda ya kai da kafiya to zaki juya shi yarda kike so in dai kina qoqarin faranta mai da yimai biyayya. To ammi taya kema ai mace ce kuma kin kasa canza shi sai ni?. Hmmm zahra kenan har yanzu yarinta bazata bar kan ki ba, akace miki uwa da mata d'aya ne.

Ni mahaifiyar shi ce, ke kuma matar shi a halin yanzu dai kin fini kusanci da shi nesa ba kusa ba, kinga yanzu tare kuke rayuwa ni kuwa wataran in miskilanci sa ya tashi ko kallo na bayayi ko zai gai dani kan sa a sunkuye, nasan duk rashin son maganar shi dole ya ringa yi miki magana ai koh?. Gyad'a kai zahra tai tare da cewa sosai ma nima ina mamaki yarda yake yawan yin magana in muna tare.

Yauwa kinga ni to haka dai in kuna tare in sha ALLAH zaki canza shi yarda kike so kiyi haquri kinji zahra ta. Tom shikenan ammi ba komai na haqura, yauwa zahrata da fatan dai kuna zaune lafiya ba abinda yake faruwa. Murmushi zahra tai mai cike da ma'ana kala-kala,. Itama ammi murmushi tai tare da cewa hmm masha ALLAH iya yanayin fuskarki ma ya nuna min kuna zaune lafiya.

Sunkuyar da kai zahra tai alamum jin kunya, girgiza kai ammi tai fuska d'auke da murmushi tace Allah yayi muku albarka ya baku zaman lafiya, yasa ku cigaba da zama aure har abada mutuwa ce kawai zata raba ku. Allah yasa muku albarka a cikin zaman auran ku da fahimtar juna yasa nan da wata 9 ki haifamin kyakyawan jika mai kama da ke...............


[23/04, 7:39 am] Oum Farhan❀️🩷: ADALILINTA πŸ’œβ€πŸ’œ

BY AMINA BAYERO πŸ’œβ€πŸ’œ

Typing..........

*page 135*

Allah yasa muku albarka a cikin zaman auran ku da fahimtar juna yasa nan da wata 9 ki haifamin kyakyawan jika mai kama da ke...............

Sake sunkuyar da kai zahra tai sanan tace aa ni ban shirya haiwuwa yanzu ba ammi. Hmmm ba wani nan mu munshirya kar6ar jiki yanzu in bakyaso in kika haiwu sai ki kawo mana jikin mu. Murmushi zahra tai tare da miqewa tace to ammi bari naje wajan ilham zahra ta qarasa maganar tana d'aukar mayafin ta, sannan ta fuce zuciya cike da qaunar ammi.

Murd'a handel d'in qofar zahra tai baki d'auke da sallama ta shiga cikin bedroom d'in, ilham da taji sallamar zahra da sauri ta qaraso su kai hug d'in juna cikin farin ciki. Bayan sun saki juna ilham tace kai zahra ai harna gaji da jiraki na fitar da rai tun dazu har yamma ta fara kawo kai.

Hmmm ke dai bari ilham ba laifi na bane kin san in dai ta zumud'i nane da tina na shekara da zuwa gidan nan. Hmmm laifin yaya mashkhur ne kenan zo ki ban lbr nasha ilham ta qarasa maganar tana jan zahra suka zauna a kan bed. Ke ilham dad'i na dake son jin gulma, ba kyau jin sirrin ma'aurata fa. Murmushi ilham tai tare da cewa dan ALLAH ke kuwa ya akai kika dad'e ke a taqaice ma zaki kwana ko kuwa?.

Girgiza kai zahra tai tare da cewa ki riqe sadakin ki yarinya wlh bai barni ba wai bazan ta6a zuwa na kwana ba har a gama bikin nan. Kai ai ni na sani yaya mashkhur hmmmm, ke dai bari kafin mu tawo ma sai da ya gama 6atamin lokaci bayan na shirya nan ma ya 6atamin time, ke mun dad'e da shigowa cikin gidan nan amma bai bari na shigo ba yaqi bud'e min murfin motar sai da ya 6atamin lokaci.............

Bayan zahra da ilham sun gama shirya-shiryan su misalin qarfe 8:30pm mashkhur ya dawo ya d'auki zahra domin komawa gida. Zahra dai bata so hakan ba amma dai ba yarda ta iya a bisa dole ta koma gida. Bayan sun koma sunyi wanka, suka hau shan soyayyah kamar zasu cinye juna haka dai sukai tayi kamar yarda suka saba.

Washe gari akai henna day, bayan henna day, washe gari suka fara bakin su kamar haka! Ladys party, bayan ilham da ruma sunyi ladys party, washe gari akai kamu washe gari akai cocktail washe gari dinner, washe gari sukai party, washe garin party aka rufe da d'aurin aure.

Masha ALLAH biki yayi kyau ba qarya 'yan uwa da abokan arzi harma da mutan kaduna wato su nana da mama sun halacci taro. Bayan an gama biki da yamma an kai amare gidajan mazajan su an dawo gida. Zahra dai ji tai sam yau bazata koma gida ba kamar yarda take kullum da yake ta gaji sosai, dan haka suna dawowa daga kai amarya ta kashe wayarta sanan ta haye sama tai kwanciyarta.

Ba jimawa bacci mai nauyi ya kwashe zahra, mashkhur dai haka ya qaraci kiran shi wayar zahra a kashe, daga qarshe kuma yazo gida akace mai zahra har tai bacci haka dai ya koma gida badan yaso ba, sabida a halin yanzu zahra ta zamewa mashkhur jinin jiki. Ranar dai da kyar mashkhur ya iya bacci sabida tsabar baqin cikin rashin zahra, bashi yayi bacci ba sai bayan sallah asuba bacci yayi awan gaba da shi.

Washe gari.

Bayan zahra tai sallah asuba ta koma bacci ba ita ta farka daga bacci ba sai wajan 11am sabida tsabar gajiya. Tana farkawa mashkhur ne ya fara fad'o mata rai. Wani murmushin ta saki mai cike da fassarori da dama, sanan ta miqe ta shiga toilet tai brush, sanan ta sauka qasa domin yin breakfast. Bayan zahra ta qarasa draining ba wanda ta tarar sai nana da abdul suna shan hirar su ta masoyah.

Murmushi zahra tai tare da jan kujera ta zauna tana gyaran murya dan ta lura basu san da zuwan taba ma. Murmushi abdul yayi tare da cewa barka da sakkowa aunty zahra, wani kallo zahra ta watsa mai tare da cewa kai yaya abdul yaushe kuma na zama aunty taka?. Murmushi abdul yayi sanan yace hmmm ke da zaki bani qanwar ki ai kinga kin zama auntyta kuma bugu da qari kina auran yayana.

Wani siririn murmushi zahra ta saki tare da cewa uhmm amma kaga ita da yake bata da kunya ko gai dani ba tai ba,. D'an hararar zahra nana tai tare da cewa aunty zahra ina wuni, hmm bana son gaisuwar taki sai dana roqa ai yaya abdul mun baka ita halak malak ba sai ka kawo kud'in zance ba bare lefe kai sadikin ma bada ban dole bane sai nace abarshi.

Allah ya kiyaye dai sai kace wata 'yar tsana wlh sai anyimin komai wanda akewa 'ya mace in za'ayi mata aure. Dallah can matsa ni in banda rashin kunya na ta6a ganin mace tana hira da saurayin ta a gidan su wai harma wani abinci kike bud'e baki kici a gaban sa kai yah ALLAH abun ya munana zahra ta qarasa maganar cikin sigar tsokana.

To haka dai zahra da abdul harma da nana sukai ta hirar su gwanin ban sha'awa har suka qarasa breakfast d'in su. Bayan sun qarasa zahra miqewa tai ta koma sama ta d'auki wayarta ta kirawo number mashkhur. Sai da zahra tai kira uku sanan mashkhur ya samu damar d'agawa ko da mashkhur ya d'aga shiru yayi ba tare da yace komai ba.

Murmushi zahra tai cikin jin dad'i tace good morning my husband?. Jim mashkhur yayi kamar bazai amsaba can kuma cikin muryar bacci yace morning, hmm lafiya hero naji kamar muryarka kamar na tashe ka daga bacci. Rai ba dad'i mashkhur yace ban sani ba, murmushi zahra tai sanan ta sauke ajiyar zuciya tace ALLAH ya wuce zuciyar mijina wai mai ya faru naga kana wani shamin qamshi?.

Oh ni zaki rainawa hankali ko ai kinfi kowa sanin mai kikayi. Cikin murya mai kashe zuciyar masoya zahra tace uhmm nifa ba abinda nasan nayi ni kewarka nake ma. Shuru mashkhur yayi yana jinjina rashin mutunci irin na zahra, har wani kashe mai murya take dan ta sake jefa shi a wani hali kenan. Naji kayi shiru ni bama wanan ba yaushe zakazo

Please Login or Register in order to submit comment