Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dole zahra ta kwakwulo tare da cewa!  Tab dady haka kake tunani?  Gyad'a kai dady yayi alamun eh.

Da sauri zahra ta Girgiza kai tare da cewa to gaskiya dady ka dena d'aga hankalinka,  ku kwantar da hankalin ku,  nifa tinda nazo gidan nan ko kallan banza yaya mashkhur bai ta6a yimin ba,  zahra ta qarasa maganar cikin kokwanto sabida qaryar da tayi,  a zuciyar tama sai da tai istigfari.  Shiru dady yayi yana nazirin magana zahra ita kuma ilham da take gefe jinjina kai tai tana tinanin yadda akayi zahra ta iya sharo qaryar nan ko sarqewa batayi,  ba kamar da ba da in zatai qaryar sai tayi qinqina,  a zuciyar ilham tace lalai zahra tasha horan ya mashkhur.

Mamana kin tabbata abinda kike cemin da gaske kike?  Gyad'a kai zahra tai tareda cewa eh dady da gaske nake.  Gyara zama dady yayi tare da cewa! To ya zancan wanan qawar tasa zeza take da suna kowa?  Gaban zahra ne ya fad'i rass amma sai ta dake tare da cewa!  Dady zeza kuma,  wace kuma wata zeza?  Shima kansa mashkhur da yake la6e a bakin qofa yana sauraran maganganun da dady yake da zahra sai da gabansa ya fad'i,  yana addu'a a zuciyar shi ALLAH yasa zahra karta tona mai asiri,  dama tin da mashkhur yaga dady yayo hanyar bedroom d'in zahra hankalinsa ya tashi dan yasan dole ya komai,  gashi ya manta bai jawa zahra kunne akan karta gayawa dady komai ba.

Shiru dady yayi yana nazari can kuma yace zee nake nufi ai nasa kinsan ta,  da sauri zahra ta Girgiza kai tare da cewa!  Aa dady ni ban ta6a jin sunan tabama sai yau,  kallon ta dady yayi cikin mamaki dady yace!  Yanzu kina nufin bakisan ta ba,  gyad'akai zahra tai alamun ehh.  Anya mamana in yarda da abinda kike gayamin kuwa?  Sunguwayar da kai zahra tai tana wasa da yatsun hanunta,  tare da cewa! Wlh dady da gaske nake mah kasan dai bana yima qarya,  jinjina kai dady yayi tare da cewa it's okay,  zan yarda da abinda kike gayamin amma sai naje na tambayi ahmad nasan bazai min qarya ba,  kuma in dai na tambayi ahmad naji sa6a nin hakan zan 6ata da ke,  kuma harda ke zan d'auki mataki,  zaki mamaki sosai mamana.

Gaban zahra ne ya fad'i rass har sai da gumi ya d'an futo mata duk da kusa sanyi da ake,  amma batama san sanda tace ehh dady ka tambaye shi na amince,  kayimin hukunci da ya dace in dai ka gano zancena ba haka bane,  jinjina kai dady yayi tare da cewa! Mamana karfa ki d'auka da wasa nake dan fa bada gaske kike ba hmmm abin dai ba'a cewa komai sai kin gani dad'i ya qarasa maganar yana sakin murmushi,  itama zahra murmushi ta saki tare da qarasa sunkuyar da kai.  Ji wani yarda kike sunkuyar da kai kamar wata mage ilham ta fad'a cikin tsokana murmushi dady yayi tare da cewa!  Hmm ke kuwa ba dole ba tana magana da surikin ta.

Zaro ido zahra tai tare da d'agowa ta kalli dady ta langwa6e murya tana cewa!  Haba dady suri ki kuma ko uba?  Ta qarasa maganar tana d'an 6ata rai da turo baki,  murmushi  dady ya sake yi tare da cewa!  To naga ai kina jin kunya kamar kina magana da surikin naki ne,  qare had'e rai zahra tai tare da juyawa dady baya!  Alamun sai an rarashe ta,  dariya dady yayi tare da janyo zahra yana cewa haba mamana kin ta6a ganin uwa ta gari tayi fushi da 'danta haba ke mamata ce,  juyowa zahra tai tare da cewa,  kai ma dady ka ta6a jin inda d'a ya tsokani mamansa.

Daga dady har ilham dariya sukayi sabida hakan da zahra tai ba qaramin birge su yayi ba. Itama zahra murmushi tai tare da fad'awa jikin dady kamar dai yadda ta saba acan baya,  bibiga bayanta dady yayi,  yana rarashin ta kamar wata 'yar yaye.  6angar mashkhur kuwa tinda yaji dady ya ambaci zai je wajan Ahmad hankalinsa ya tashi sosai,  dan haka bai wani 6ata time ba ya fuce,  daga part d'in.  Yana sauka daga step d'in benan,  ya wuce part d'in ahmad yana zuwa a hanzar ce,  ba 6ata lokaci ya fara bugawa ahmad gofa da qarfi-qarfi.

Bai fi minti uku ba ahmad ya futo, dagq shi sai kayan bacci kana ganin sama zaka sheda daga bacci ya taso,  yana bud'e qofar ya zubawa mashkhur ido yana mamakin mai ya kawo mashkhur haka da sassafe,  dan yasan shi bai saba shigowa da safiya haka ba.  Kallon mashkhur  ahmad yayi  tare da cewa!  Mashkhur shigo mana,  ba musu mashkhur ya shigo tare da rufo qofar,  ko zama bai yi ba ya fara korawa ahmad bayani kamar haka!  ahmad kansan menene?  Girgiza kai ahmad yayi tare da cewa aa amma ya kamata mu zauna ai,  kafin ka gayamin.

Girgiza kai mashkhur yayi tare da cewa! Nan ma ya isa, kallon sa Ahmad yayi tare da cewa! To shikenan ina jinka mai ke tafe da kai?  Sumar kansa mashkhur ya shafa tare da cewa Ahmad pls ko dady ya tambaye ka akan maganar zee, to kace mai na rabu da ita,  sanan in ya tambaye ka akan maganar waccan yarinyar karkace ina takura mata pls?.  Kallon up and down ahmad ya watsawa mashkhur tare da cewa au,  ahine kake min magana a gadaran ce kamar mai bani umar,  kawai kace temako kazo ka nema ko?,  rai mashkhur ya had'e tare da cewa!  Kaga ahmad karka rai namin hankali mana.




                        Lalai ma mashkhur to bari kaji in dady ya tambaye ni sai na gaya mai komai tin daga yadda kake quntatawa zahra har yadda alaqarka ta qara qarfi da zee da kuma shaye-shaye da kake,  ahmad ya qarasa maganar yana qoqarin komawa ciki,  da sauri mashkhur ya ruqo shi tare da cewa!  Dan Allah ahmad kayi haquri pls karkamin haka,  mamaki ne ya kama Ahmad sabida tinda yake da  mashkhur bai ta6a bashi haquri ba sai yau.  Juyowa ahmad yayi tare da kallon mashkhur d'in,  sai da sukayi wajan minti biyu suna kallon-kallo da mashkhur d'in.

Can kuma yace to yanzu in ban gayawa dady ba taya kake tunanin zan qwatarwa zahra 'yancin ta nasan dai in na gayawa dady dole ya raba auran ka da zahra kuma gashi kai ba santa kake ba ai kaga na tai make ka kuwa.  Yanzu mashkhur mene ribarka nayiwa zahra hakan tana qaramar yarinya kana qoqarin ka lalata maka rayuwa,  ka dora mata ciwan hawan jini da zuciya to ni tin kafin ka cuceta zan nema mata mafita a wajan dady gwara ka sake ta ta hutu tinda basan junan ku kuke ba.

Zaro ido mashkhur yayi tare da cewa! Ai ahmad da wanan ne zai ta dady ya raba aure na da zahra tofah da tini mun rabu da zahra,  dan da kai na ma zan cewa zahra ta bigawa dady ta gaya masa ina azaftar da ita,  amma daga ranar da dady yasan ina azaftar da zahra tofah aure na da zahra ya qara kulluwa tamau ba rabuwa,  sabida kafin muzo rasha dady yayimin alqawarin in bana dukanta bana takura mata kuma na dena shaye-shaye da kula zee tai kuma na futo da ruselt mai kyau a school to yace zai raba auran in muka koma Nigeria har dai in bama son junan mu,  to yanzu in yaji haka kana tinanin ma zai raba auran nan kuwa,  koma dai ni kasan ba santa nake ba.

Lalai mashkhur to inaga har ka mutu da auran zahra akanka zaka mutu dan ko dady bai tambaye ni ba,  sai naje na gayam mai gaskiya.  Zaro ido mashkhur yayi tare da cewa! Yanzu ahmad haka zaka yimin?  Karfa ka manta mu abokai ne wlh sam bana qaunar yarinyar nan dan in kace na zauna da ita na muddin rai tofah wlh sai na gudu na tafi wata qasar ta daman,  ko kuma na kashe ta sanan na dawo na kashe kai na kowa ya wuta.  Zaro ido ahmad yayi tare da cewa! Mashkhur  kana da hankali kuwa?  Kasan me kake cewa?.

Kwari ahmad nasan mai nake cewa,  wlh bakasan yadda na tsane taba ne shiyasa ,  jinjina kai Ahmad yayi tare da cewa! Tom shikenan mashkhur naji zan rufama a siriva wajan dady amma da saharad'i na guda  uku  baki na rawa mashkhur yace eh ahmad wlh ko mene zan iya in dai bai fi qarfina ba,  jinjina kai ahmad  yayi tare da cewa! Na farko dai sai ka amince zaka dai na zalintar zahra ko kallan banza karka sakeyi mata,  na biyu kuma zaka rabu da zee,  na uku kuma zaka dena shaye-shaye nan to in dai ka yarda da wanan zan rufama a siri a wajan dady.

Eh ahmad na yadda duk abinda kace zanyi hakan,  mashkhur ya fad'a ne kawai amma ba har cikin zuciyar sa ya amince da hakan ba.  Kallansa ahmad yayi tare da cewa!, yau zaka school ko?  Girgiza kai mashkhur tare da cewa! No bazani kallansa ahmad yayi cikin mamaki yace sabida mai kawai bana buqatar zuwa ne shi yasa,  shiru ahmad yayi yana nazari akan wanan rashin tinani irin na mashkhur,  can kuma yace to in dady ya tambaye ka mai zaka cemai?  Cemai zanyi jiya da yau bamu da lectures daga haka mashkhur ya fice yabar ahmad cike da jimami.

Lokacin da mashkhur ya koma gida har dady sun gama hira da zahra dan harma ilham da zahra sun fara had'a breakfast,  shima zama yayi a falo shida abdul suka fara hira.  Yau da su zahra suka gama dafa abinci suka jera mashkhur bai jira bismillar kowa ba ya fara cin abinci.  Suna cikin cin abinci dady ya kalli mashkhur yace!  mai sunan baba yau bazaka makarantar bane ba?,  murmushi mashkhur ya saki tare da cewa!  Ai yau bamu da lectures shiyasa,  jinjina kai dady yayi tare da cewa!  Ai nayi tinanin bazaka bane ashe baku da lectures ne.

Haba dady sai kuma in qi zuwa school ai ni inaga tinda mukazo rasha wanan karo ban ta6a fashin zuwa school ba.  Zahra kuwa da taji qaryar mashkhur har sai da ta d'an kware,  dady kuwa mayar da kansa cikin abincin yayi tare da cewa!  Haka ake so,  mashkhur kuwa suna had'a ido da zahra ya sakar mata muguwar harara yana yi mata kallan munafi ka,  kawar da kai zahra tai ta cigaba da cin abinci ta sabida ita inda sabo tama riga da ta saba.  Bayan sun gama cikin abinci dady da abdul komawa sukayi suka kwanta,  dama amir bai tashi daga bacci ba.

Mashkhur fita yayi ya tsaya a korudan matattakala benan yana shan iska,  zahra da Ilham suna bedrom d'in zahra,  zahra tana mofe bedroom d'in ilham ta bud'e korudo d'in ventilation tana leqe da shan iska duk da kuwa garin da d'an sanyi.  Can ilham ta fara kwallawa zahra kira kamar haka!  Zahra!!  Zahra!! Murya zahra ta d'aga tare da cewa  Na am, yi sauri kizo maza-maza zo ki gani,  ba shiri zahra ta ajiye mofar da take goge wajan ta nufi ventilation d'in,  tana zuwa ta shige dama da yake ilham a bud'e tabar glass din bata zuge ba.

Zahra tana qarasawa tace ilham wanan wana irin kira kikemin haka?  Da sauri ilham ta nunawa zahra qasa tare da cewa! Kinga, da sauri zahra ta mai da kallonta kan abinda ilham take nuna mata,  zee da mashkhur ne a tsaye,  taci matsatsun kaya riga iya ugu wanda ma ya matseta sosai sai dogwan takalimi,  kana gani zaka sheda fad'a yake mata amma su kansu basusan fad'an mai yake mata ba,  amma zahra tasan bazai wuce na zuwa da tayi gidan bane,  yanzu zahra wanan ce zee d'in Ilham ta tabbayi zahra cikin mamaki.  D'aga kai zahra tai tare da cewa!  Itace mana ilham.

Gani sukayi zee ta nufi motar ta data faka a packing space ta fuce. Da sauri zahra ta ta jawo ilham sukayi baya dataga mashkhur yana qoqarin d'ago idan sa sama.  Cikin rawar murya tace ilham mu koma ciki karya ganmu,  ba musu suka shige suka zuge glass d'in.  Suna shigowa ilham ta zauna akan bed ita kuma zahra ta cigaba da mofin d'in da take,  tana gamawa ta fita da mofar sanan ta dawo ta zauna a kusa da ilham.  Ilham ce ta fara magana kamar haka!  Yanzu zahra wanan kwarmashashiyar yarinyar ce zee wanda ta kwace miki miji kuma take saki aiki a cikin gidan mijinki.

Shiru zahra tai bata bawa ilham amsaba sabida ita sam bataso a kira ya mashkhur da mijinta,  au kina jina kika yimin shiru cewar ilham,  to  ilham mai zance miki kuwa?  ilham ta bud'e baki zatai magana kenan amir da yake kwance a bayansu ya farka tare da cewa!  Ke ilham zo kimin wanka!  Ya fad'a yana dukanta ta baya,  murmushi zahra tai tare da cewa!  Lalai ma amir yanzu ko aunty baya ce miki,  itama ilham murmushi tai tare da cewa!  Tab wataran in yayi niya yana cemin aunty,  yanzufa duk yabi ya rai nani sabida yaga nice abokiyar wasansa a gida.

Daga  haka Ilham taja hanun amir suka shige toilet,  suna shiga tai mai wanka sanan suka futo,  zahra ce ta fara samai kaya ita kuma ilham ta fita zubo mai breakfast,  da zahra ta gama sawa amir kaya ficewa amir yayi daya gaji da jiran ilham yana fita ya hangi mashkhur akan sofa yana danna phone d'in sa,  da sauri amir ya qarasa ya fad'a jikin mashkhur d'in, rungume amir mashkhur yayi,  amir kuwa cewa yayi yaya mashkhur good morning, wata siririyar dariya  mashkhur yayi tare da cewa!  morning too how are you?  Shima amir dariya yayi tare da cewa!  Fine,  inye ashe ka iya gai suwa da turanci,  dariya amir yayi tare da d'aga kai alamun eh.

Muryar ilham sukaji akan su tana cewa!  Amir ga abincin zo muje na baka,  manne kafad'a amir yayi tare da cewa! Aa ni yaya mashkhur ne zai bani,  harara ilham ta watsawa amir tare da cewa! To da waye yake baka?  Yaya mashkhur d'in ne zai baka abinci ko?  To ka dad'e baka ciba! Harara ilham mashkhur yayi tare  da cewa  mara mutunci kawai wlh wata rana baki wasa ba sai na fasa miki baki,  mara kunya kawai,  Bani plate d'in  kafin na wanke ki da mari ya fad'a yana qara fata rai ba musu ilham ta miqawa mashkhur plate d'in da cup din,  tare da cewa!  Ya haquri.












Rufemin baki bana son haqurin naki,  shiru ilham tai tana tinanin taya akayi yaya mashkhur ya koyi sauri fad'a haka?  Lalai zahra tana qoqarin zama da shi,  amma dai ilham tasan mashkhur bazai duke taba kawai dai ya fad'a ne,  sabida tunda baya yawan dukanta ko agida in sunyi laifi ita da haidar ko faruq baya dukan ta sai dai ya dake so,  sabida yana qaunar ta sosai,  da yake ita ka d'ai ce qanwar sa mace,  uwa d'aya uba d'aya,  yana mutuwar san ta yadda ya kamata,  sam baya san ganin 6acin ranta ba kamar zahra ba da yake nuna mata tsantsan qiyaya.

Dallah can tafi kibar nan wajan,  tsugunawa Ilham tai kamar zatai kuka tace yaya mashkhur nice fah,  dan ALLAH kayi haquri na dena wlh.  Nan da nan mashkhur ya saki ranshi tare da cewa!  Tom shikenan jeki,  murmushi ilham tai tare da cewa!  Yauwa yaya mashkhur shiyasa nake qaunar fiye da yaya abdul,  ta qarasa maganar tana sakin murmushi,  dariya mashkhur yayi saka makwan ganin abdul da yayi riqe da ugu yana sauraran abinda ilham tace,  dama Ilham ta fad'a ne kawai sabida yaya mashkhur ya wuce,  amma ba har zuciya ta fad'a ba sabida shima tana son yaya abdul d'in.

Sannu muna fuka ai dole kifi san shi,  tinda baya had'a miki jiki ko?  Baya dukan ki,  da sauri ilham ta juyo tana mamakin taya akai yaya abdul ya futo bata sani ba.  Da ilham ta rasa mai zata ce,  da gudu ta wuce tabar wajan sana saki Dariya,  shima abdul dariyar ya saki yana girgiza kai sabida yasan halin Ilham sarai,  sometimes shima tana yawan cemai tana qaunar shi fiye da yaya mashkhur in tana so yayi mata wani abun,  qarasawa abdul yayi kusa da mashkhur,  tare da cewa! Kai ilham da akwai shafta yaya mashkhur,  kasan wataran in tana so nayi mata abu cewa!  Take tana qaunata fiye da kai ya qarasa maganar yana sakin siririyar dariya.

Murmushi mashkhur yayi tare da cewa!  Kai ai ilham bata da dama abdul,  tana da abin dariya sosai,  daga haka abdul da mashkhur suka hau hira,  mashkhur yana bawa amir abinci a baki kamar wani d'an yaye.
6angar ilham kuwa tana shiga d'akin zahra ta saki dariya tare da fad'awa gado tana sakin ajiyar zuciya,  ke ilham lafiya?   cewar zahra,  nan da nan ilham ta fara basa zahra labarun abinda ya faru,  itama zahra dariya tayi sosai tare da cewa!  Ke Ilham shiyasa ba'a so ka ringa haka,  yanzu daba dan yayan ki bane ai kunya zaki ji wlh............

Kwana biyu kunga bana yi muku posting koh?  Wlh biki mukeyi shi yasa,  ina yi muku fatan alkhairi,  happy weekend...


ADALILINTA💜❤💜  

BY AMINA BAYERO💜❤💜

                                    Typing............

                                    *page 70*

6angar ilham kuwa tana shiga d'akin zahra ta saki dariya tare da fad'awa gado tana sakin ajiyar zuciya,  ke ilham lafiya?   cewar zahra,  nan da nan ilham ta fara basa zahra labarun abinda ya faru,  itama zahra dariya tayi sosai tare da cewa!  Ke Ilham shiyasa ba'a so ka ringa haka,  yanzu daba dan yayan ki bane ai kunya zaki ji wlh............ 

Dariya Ilham tai tare da cewa!  Ai kuwa dai danaji babbar kunya,  gyarazama zahra tai tana cewa!  To ALLAH ya shiryemu baki d'aya,  ammen zahra.  Zama itama ilham ta gyara tare da cewa! To zahra mu koma kan maganar mu ta d'azu,  ajiyar zuciya zahra tai tare da cewa inaji kin ilham,  jim ilham tai na wani lokacin kafin tace yanzu zahra wanan tsigigiyar yarinyar ita kike tsoro koh?  Gyad'a kai zahra tai alamun ehh,  hmm to zahra in banda abinki mene abin tsoro a jikin waccan yarinyar,  duk da ta girmeki amma ai bata fiki komai ba,  ya rinyar da ko shap d'in arziki bata da shi ko a haka kin fita komai bare ma baki gama girman kiba, jitafa wata siririya kamar ki hure ta fad'i  Ilham ta qarasa maganar tana bin zahra da ido.

Hakane ilham amma yanzu ya kike so nayi da ita yaya mashkhur ne yake son zuwanta gidan nan bani ba kuma kinsan ko ta ina yaya mashkhur yafi qarfina ban isa na hanata zuwa gidan nan ba ko?.  Kwarai zahra baki isa kin hanata zuwa gidan nan ba amma kin isa kisa wanda take zuwa gurinsa yasa ta dena na?  Cikin mamaki zahra tace ilham tayaya zanyi hakan?  Hmm zahra ki kwanta da hankalin ki zan gaya miki,  duk da nasan ba lallai ne ki iya ba. Shiru zahra tai tana sauraran ilham,  abu na farko da zan gaya miki shine duk abinda zee ta saki a cikin gidan nan karki sakeyi tinda ke ba bai warta bace.

Zaro ido zahra tai tare da cewa!  Amma ai yaya mashkhur zai sani punishment ko ma ya dake ni,  tsaki Ilham taja tare da cewa ai ke matsalar ki kenan,  ke wai bazaki iya dai na jin tsoran yaya mashkhur d'in nan bane tinda ai bashi ya haife kiba koma bai hallicci kiba.  Aa ilham abinda nake tsoro karya illatani fah,  gyara zama ilham tai tare da cewa!  Duk sanda ya sake qoqarin dukan ki ko to karki tsaya ki gudu,  ai ilham ko na gudu ban tsiraba sabida ina futowa in zanci abinci kuma ina futowa in zani makaranta ai kinga dole ya kamani ko?. 

Shiru ilham tai tana tinanin mafita,  can tace ga shawara in zaki iya,  kallon ta zahra tai tare da cewa ina jinki kuma ALLAH yasa na iya, duk sanda yaya mashkhur yazo dukan ki ko?  ki fad'a jikin shi ki qanqame shi da iya qarfin ki karki sake ki sake shi komai zai ce miki,  Zaro ido zahra tai tare da cewa!  Tab gaskiya bazan iyaba ki canza wata shawarar,  ni bazan iya wanan ba taya ma zan iya hakan ke in kece zaki iya?  Da sauri  ilham tace kwarai kuwa harma abinda yafi haka zanyi,  in dai zan kwatarwa  kai na 'yanci,  ke nifa da nice na tsinci kai na a halin da kike cike zahra da tini na nemawa kai na mafita.

Ke ilham gaskiya ki canza wata shawarar gaskiya banda wannan,  shiru ilham tai ta zubawa zahra ido,  tana ganin ikwan ALLAH,  haba ilham mene haka kike zubamin ido kiyi magana mana zahra ta fad'a tana ta6a fuskar Ilham,  hajiya zuciyar ilham ta saki tare da cewa!  Ai kece naga sam bakya d'aukar sha'wara,  murya asanyaye zahra tace!  Tom naji dan ALLAH kiyi haquri ki canza wata banda wanan.  Shiru ilham tai tana tinanin wata mafitar,  can tace yauwa na tuno wata mafita mai kyau kin san meye?  Da sauri zahra tace aaa mene?.

Kawai kicewa dady ya siyar miki waya,  zaro ido zahra tai tare da cewa!  Waya kuma ilham ?  Kwarai zahra wlh in baki hakan ba bani da wata mafitar,  to in ya siyar min wayar mai zanyi da ita?   Murmushi ilham tai tare da cewa!  Zahra kenan,  yanzu kuwa zakisan me zakiyi da ita kinsan me zakiyi da ita?  Girgiza kai zahra tai tare da cewa!  Sai kin fad'a,  yauwa daga rana da muka bar qasarnan ko to kada zee ta sake saki wani aiki kiyi,  ko kallon arziki karkiyi mata inta saki aiki kiyi mata banza  kibarta a wajan,  shi kuma yaya mashkhur in yazo zai dake ki kice wlh har dai ya sake ya dakeki to fah sai kin bigawa dady kin gaya masa.

Gyara zama zahra tai tare da cewa!  To in ya kwace wayar fa?  To kema in banda abinki ba 6oye wayar zakiyi ba,  duk abinda zai miki karki sake ki futo da wayar,  sanan kuma in yayi miki abu ki dena nuna mai kin damu,  ko kuma kiyi sauri kukan,  rai naki fa yake in yaga kina wanan kukan,  kema ki zama jaruma ki wani dena jin tsoran shi,  ke in ta kama ma ko gaishe shi ki denayi ki bawa banza ajiyar shi kiyi harkar gabanki,  kuma duk abinda ya hanaki najin dad'i a gidannan ki cigaba in kina san kallan tv to ki kije ki kunna ki kallah,  kar wani kiji tsoro in yazo zai dake ki kice sai kin gayawa dady punishment kuwa in ya qara saki karma kiyi ki wuce bedroom d'inki ki kulle ki barshi a wajan.

Ajiyar zuciyar zahra ta saki tare da cewa!  Anya kuwa zan iya Ilham?  Kwarai kuwa zaki iya sai dai baki sa kanki ba zahra,  jim zahra tai can kuma tace tom shikenan ilham zan gwada,  harara ilham ta watsa mata tare da cewa!  Bawani zaki gwada ba za dai kiyi zakice,  tom shikenan ilham  zanyi.  Gyara zama ilham tai tare da cewa!  Sai abu na gaba  kuma yadda zaki sace zuciyar shi,  wai zahra sai kace ba mace ba?  Ke duk rangwad'a da rausaya baki iyaba ne?  Tab yaya mashkhur d'in zanwa rangwad'a gaskiya ilham bazan iyaba,  lalai ma to kina cikin wahala kuwa,  yanzu yan qananun kayan nan bazaki iya sawa ki rikirkita shi tinda shi ba qarfe bane ki sace zuciyar shi ba?.

Gaskiya ni bazan iya wanan iskanci ba,  tabe baki ilham tai tare da cewa!  Shikenan ki yadda kike so bazan takura miki akan sai kin so yaya mashkhur ba,  amma ki sani in yaya mashkhur bai fara sanki ba tafah ba ta yadda zaki rama cin kashin da yayi miiki ba ahto.  Ke ilham ni dai ban damu da sai na rama ba,  kawai burina ya sakeni,  na auri wanda nake so dan bazan ta6a iya rayuwa da yaya mashkhur ba,  ajiyar zuciya ilham tai tare da cewa!  To ALLAH ya za6a miki abinda yafi alkhairi,  murya a sanyaye zahra tace amen.

Washe gari.....

Da sasafe zahra ta fara shirin tafiya school, 

Please Login or Register in order to submit comment