Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM GODIYA YA TABBATA GA ALLAH DA YA BANI IKON FARA WANAN NOVEL DIN A CIKIN KOSHIN LAFIYA YADDA MUKA FARA SHI LAFIYA UBANGIJI YA BAMU IKON GAMAWA LAFIYA.

DA FATAN SAKON DAKE CIKINSA ZAI ISA GA INDA YA KE BUKATAN ZUWA GURIN MATA YAN UWANA ALLAH UBANGIJI YASA MU ANFANA DASHI

WANAN PAGE DIN FREE PAGE NE DAGA SHIMFIDAR LABARIN MAI SO ZATA IYA TUNTUBANA DON YIN REGISTER SHIGA GROUP DIN

NAGODE TAKU HAR KULLUN ZAINABUN KU


Hasken farin watan daya haski taurarin da suka zagaye shi masu fitar da kyalli daga ganin su,
Wanda hakan yasa sun kayata gari matuka hadi da sanya zukatan bayin Allah a nishadi
Wanda mafi yawan zukata mutane musan man na kauye inda babu wutan lantarki a garesu cikin jin dadi da walwala.
Ga iska mai dadi da yake dan kadawa lokaci lokaci gami da kamshin kasa dake tashi gwanin dadin shaka.
Ga yara dake jin dadin yanayi duk da dare yayi amma suna waje suna wasan su don babu duhu da zai sa ashige gida a lokacin
Tafe take da sauri iskana dan kada ta hannuta rike da farar roba mai marfi da ta dauko nikan awara da zasu soya da safe kafin ta tafi makarantan boko.
Tafe take cike da nishadi a zuciyar ta wanda yanayin yake saka ta jin dadi har tana lumshe idunuwan ta.
Tana tafe cikin sauri bata da wani guri daya wuce taga ta isa gida ta tatace markaden wanken da ta dauko daga gurin nika.
Wasu mutane ne zaune wanda magidanta ne dabian su shine duk dare a shimfida katon tabar kofan wani gida su dinga yan ciye ciye kafin su shiga gida gurin iyalinsu da aka bari da tuwo da miyar kuka bakifi ko nama a cikin sa haka mace zata rufe idon ta taci har sun saba.
Basu da wani aiki idan idan sun zauna sai tsirko da sa ido idan mace tafito zuwa unguwan dare zasu fara cewa wance ce matar wani ko diyar gidan wani ne waccan.
Idan akwai abin da naki jini a rayuwana shine na wuce wanan bakin daban na yan gulman shiyan mu.
Don duk mutuncin da kai masu baka taba tsira a gurin su sai sunyi gulmanka idan kaba da baya.
Ina kawo gurin kamar na wuce na share su amma hakan baiyuyuwa don hasken farin watan dake akwai a lokacin.
Ina kawowa gurin su na dan duka ina fadin ina aunin ku suka amsa kusan a tare da lafiya kalau.
Nasa kai na wuce su nasan cewa ba tsira zanyi ba nima daga kaidin su lokacin.
Sauri nakeyi ba abinda ke raina kamar naga nashiga gida na idar da abinda ke gabana lokacin.
Ina shiga gida da sallama na samu su Inna zaune tare da yan uwayena suna cin abincin dare mahaifina shima ya dawo gida a lokacin.
Gaishe su nayi inna ke cewa dani kin karbo nikan ne nace da ita eh inna.
Ban tsaya bana na tube zanin jikina kada ya baci na daura wani kodaden zani nawa duk dashima wanda na cire din kodadde ne sosai amma wanda na daura yafi kodewa sosai.
Nafara tatsan kullun wanke dake cike fam ga roba ina jin suna hiran su na manya har nagama abinda nakeyi sai a lokacin na samu saidan kaina.
Kwanon tuwo na najawo na tasa a gabana don naci amma ina kallon tuwon naji banajin cin sa sai kallon tuwon masaran kawai nake yadda yai sanyi kalau a kwano har ya fara bushewa daga sama.
Muryan mahaifiya na naji tana fadi wai Rahama bazaki ci abincin nan ki tashi ba ?
Kin saka tuwo a gaba haka kina kallo yanzu zaki iyacewa yai sanyi bazaki ci ba ki kwana da yunwa.
Jin maganan ta yasa na dan kai hannu ga kwanon na fara tsakura a hankali nasan cewa idan naci sai ya tayar min da zuciya na don haka nake tuwo mai sanyi baya bani lafiya.
Gashi kuma Allah ya hallice ni a gidan tallakawa tallakan ma na kwarai don ko a kauyen mu mahaifana basu dashi ko kadan.
Hakane yasa muke cikin wahalan rayuwa sai nayi dan talla zamu samu abinda mukai lalurar rayuwan mu dashi.
Duk da hankan da muke zance Alhamdullahi don munajin dadin rayuwan da muka tsinci kan mu a hakan.
Idan na dawo boko zan dauki tallan abubuwa iri daban daban nayau daban na gobe daban.
Tun daga kan awara da safe idan na sayar na wuce boko idan kuma na dawo na dauki shimkafa da wake dafafa zuwa yamma wani lokaci na dan je islamiya wani sain kuma na kara fita da tallan gujiya ko rogo ko marau, marau wani lokaci har kwai dafafe nake dauka ina yawata dashi.
Duk wani abinda za, a dora min sai Allah yaban sa, a na sayar na dawo a cikin lokaci.
Da haka muke samun dan abin rufin asirin mu bamu zama da yunwa a gidan mu.
Akan ce talla yana bata yarinya ni dai zance sai dama an tarar da halin baci ga yarinyar don bana tsayawa wasa da maza balle har akai ga min maganan banza.
Ko hannu namiji ya rike min zan tsaya nai mai cin mutunci da gobe bazai kara ba ma.
Ganin yadda Allah yake ban sa, a ga sana, ata har wasu iyayyen sukan min kazafi wai kila loko ake tsayawa dani aimin juye abani kudi ko suce akwai wanda na lakanta da ke bani kudi na cas.
Abin basu san daga Allah bane sa, a yake na saka a raina nema wa mahaifiyata zaman lafiya a dakin ta.
Kishiyar Inna ta takan ta faman sake magana da diyan ta don su basu da irin hazakana ta ko ina.
Duk da ba wani issashen karatu nake samun yi ba amma kuma Allah yabani kokari ga karatuna na boko da na mahammadiya din.
Don ba, a taba mayar dani baya ba ga karatuna shiyasa ko yaya ne nake dagewa naga naje kowani don na dan samu.
Duk da mahaifin mu baison tallan mu dole ne yasa yake bari don idan yai magana yasan amsan da zai samu gun uwayen mu akan tallah.
Wata rana an kawo mai kara hafsat diyar kishiryar innata yashigo gida rai a bace yana fada sai cewa Mama tayi.
Yo idan basuyi tallaba kan mu zamuci mayye amfanin diya mace a gare mu idan ba tallaba damay zamu tara masu kauan aure ga lalurorin da baka iya tsare muna.
Ka kwaso mu ka cika a gida kamar zaka kai kurmi sai diya muke zubawa ba wani tallafi a gurin ka.
Baba yace amma saboda Allah ko ban iya tsare maku komai ai baikamata ace har an kawo karan yaran nan ba gareni kan talla.
Mama tace idan baka son suyi talla sai mu gani a kasa kaga sun huta muma mun huta.
Su yan gulman da sukazo fada maka ga aibun su ina duk karkaran nan ba gidan da yaran su basu talla.
Murmushi yayi kawai yace lauratu wata rana zaki gane magana ta gaskiya ne, idan yaro yayi ba daidai ba har kasamu mai fada maka gaskiya kamata yayi ka tsaya ka duba baka hau fada ba.
Tace ai dole na hau fada tunda anzugaka kashigo zakai mun tujara a tsakar gida haka.
Ba lawisa ce kawai ke tallaba a gidan nan amma don ana hassada da ita andauki tsana an sakawa yarinya ita kadai.
Fita yayi daga gidan don baida tacewa don mama ba wani power yake dashi ba agurin ta.
Mahaifiyana ma haka take zaman hakkuri da ita tana binta don azauna lafiya kawai.

****** ********* ******
Na dawo daga makaranta ke nan ina kokarin cire uniform dina naji murya sanusi dan gidan mama Altine makwabciyar mu yana sallama.
Tsarabane ya kawo gidan mu yana fadin gashi inji maman shi tace yakawo muna wai anty Sa,ade tazo daga birni.
Sabulun wanki ne clean da biscuits a cikin wani roba aka sako mai kunsan halin yan kauye da kara ko yaya abu yake sai makwabci ya san ma makwabcin shi idan yana da dan yawa.
Da sauri na daga labulen dakin jin sunan wace akace tazo daga birni yar gayu ce ta karshe don ko maganan ta abin sha, awane gata da son mutane bata kyaman yan kauyen mu ko kadan.
A yadda naji wai diya take ga mama altine yar kaunata ce ta birni da ta rasu su biyu ne a gurin iyayyen su shine da mahaifiyan ta ta rasu ta mayar da mama Altine kamar uwar cikin ta.
Da sauri na daga labule ina cewa anty Fara tazo sanusi ?
Yace tazo har ta haihu da yar ta maikyau da sauri na juya na jawo tsohon hijjab dina na saka na suri yan tsufin takalmana da duk sun sude gurin yawon talla ba asai min wasu ba nafice daga gidan mu.
Ina jin Inna ta kwada min kira da ke ke don bata kiran sunana saboda ina yar fari gurin ta.
Ban tsaya ba don nasan kiran akan dafafan gyadan da aka dafa min ne nazo na fita dashi.
Ina shiga gidan na samu ta dauko buta zatai alwala sai naja na tsaya don kunya.
Saboda ina matukar jin kunyan ta haka kawai tun ina karama idan tazo ina like da ita kafinta tashi zaka gane don ina shan kwalliya da kitso irin na yan birni kalakala akaina.
Don Allah ya yalwantani da yawan gashi mai santsi da tsawo gashi baki amma bai samun gyara don ba lokacin yin hakan gare ni saboda busy akan talla tun ina yar ficiciya ta.
Idon ta yakai gareni tace cikin murmushi a, a wa nake gani haka kamar yar Rama rama na ?
Nabi bango ina karasowa inda take duke zata fara alwala a lokacin mama altine tafito daga dakin ta na bunu take cewa itace mana.
Ba ta girma ba yanzun kuma kunyar ki take ji tagama maki fitsari a kwance nace kai haba mama ai dane wannan.
Ida mama take tsaye rike da yarta na karasa nace mama diyar anty ne wanan ?
Ina mika hannuna ina kokarin karban yarinyar dake dauke a hannuta nace mama yar anti ne wanan mai kyau haka ?
Yarinyar sai kamshi takeyi kamar kamfanin turare a jikin ta nace kukan kunji dadin ku komai naku na birni ji yar nan mama kamar baturiya.
Dariya magana ta yaba anty dake alwala batai magana ba sai da ta gama alwala tana mikewa take cewa ni dai Rama baki gaishe niba fushi nake dake ai.
Nace don Allah anty kiyi hakkuri idan kinyi fushi dani ai na bani.
Dariya ta karayi har hakoran ta na makka ya dan baiyya na a fili tace kai Rama har yanzun dai kina nan da shirmay ki ashe .
Yanzu Rama na kece kiga girma haks idan wani guri na ganki ai bazan ce kece ba haka.
Kunyan maganan ta naji mama ce tace ga ta saura aure ta girma abinta fa bakiga har ta wuce kidan dangiba komai acan acan da ita.
Don ma Asiya tana azama mata talla ba hutu gareta ko kadan ta samu yarinyar ta mayar kamar injin.
Mama bata rufe baki ba sai ga kani na Nura yashigo yana cewa Rahama Inna tace kizo wai gyadan da kika bari wa zai fita mata dashi ?
Mama tace bakaji ba maganan da nake fada maki ni nasan ba, a rasa abin fitarwa ai yanzun haka.
Nace kace gani tafe zan ga antyna ne tukun kafin nazo yaron ya juya yana fadin wallahi zanje nace kince bazaki zo ba.
Ban damu da zancen shi ba nabi bayan anty zuwa cikin dakin mama dauke da yarta a hannu na.
Na zauna nan na shantake gurin kallon yarinyar ina mamaki irin kyaun da Allah yai mata haka.
Har ta idar da sallah ina zaune mama tana waje tana dan aiyukan ta na tsakar gida.
Tana idarwa ta juyo gareni bayan ta shafa tana cewa Rama ke nan kinga yadda kika girma kuwa ?
Na kara jin kunya ina sune kaina ajikin yarta wace nake jin dadin kamshin ta sosai har cikin raina.
Tace ina fatan dai kina karatun ki ko har yanzu baki daina ba ?
Nace lah anty banayi maki alkawarin zanyi karatu ba kince fa idan nai karatu watarana zan kai ki nima.
Tace kwarai kuwa Rama kilama har kifini haka muke fata insha Allahu nace cikin dago kaina ina mamakin abinda tace.
Anty wane ni, ni dake kauye kullun talla bani da hutu idan ba dare yayi ba na kwanta.
Tace to kin san abin Allah ne ?
Nace kamar wata babba cikin girgiza kaina da a, a amma gaskiya da wuya hakan ya kasan ce.
Tausayin yadda yanayina ya kasance da nake maganan taji har a cikin ranta ga yarinya har yarinya amma babu wadata ga kauyanci zai illanta ni.
Gafara dai masu gida muryan mama Laure ne kishiyar inna ta tayafo tabiyo ni da cin mutunci har gidan mama altine.
Sun gaisa sama sama da mama Altine take cewa halan mutumiyar taki tana ciki ko ?
Da hannu tai mata nuni da dakin take cewa tana ciki kuma kun san tunda Sa,ade ta sauka garin nan kuda samun hankalin Rahama kuma sai baba yagani sai saade tabar garin nan.
To in ba shedana irin na Rahama ba ace uwarta ta dafa mata sana,a amma tanajin ance saade tazo ko minti daya bata kara ba ta suri takalman ta tayo nan.
Daga cikin daki ina jin ta na balai akaina akan an aiko nazo naki zuwa na lake a nan, na dan turo bakina nace ni ba inda zan tafi ina nan yau da Anty ina zan tafi nabar wanan yar mama altine dama ko goyo bata iya ba tabarta a kasa.
Kai Rama yanzu mama din ne bata iya goyo ba ni waya goyani har nakai haka yanzu ?
Lokacin mama altine da mama suka shigo dakin mama tace wai mai take fadi ne ?
Dariya ya kama anty sai kyalkyala takeyi nan dai suka gausa da mama laure ta hauni kuma da fada.
Muryan anty ne ya katse fadan ta tana cewa wai gyadan har na nawa ne mama ?
Tace kai yana da yawa fa kin san sherin Rahama yawa gare shi idan ta tashi amma ta yaya uwarki tayi sana, a zaki zo nan kiyi zaman ki.
Maimakon na tashi ga mamakin mama ko har tai min zan bar duk abinda nakeyi na kama wanda ta sani amma yau sai gani zaune ko gezau ban yi ba.
Rahama wai ba dake nake magana bane mama ta kara nanatawa cikin hasala.
Anty Saade tace gyadan na nawane mama ?
Tace zaikai na jakka biyu fa idan taso sayarwa ko da dan kai sama.
Mikewa tayi zuwa inda hand bag dinta yake ta dauko kudi a ciki dubu daya mikakan ta tana cewa ina gashi da na yau da gobe don Allah abar min Rama na ta huta mama.
Harara mama laure ta watso min daga gurin da nake tana cewa dama haka kike so ai.
Ji fa mama ita da ko yaushe take cikin kyashewa tallana shine wai take fadin haka don taga kudi.
Ta juya tafice daga gidan tana zuba magana tana fita nace lah Anty aida baki bata ba baki san halin mama laure ba ko ?
Yanzu bai wuce tabawa mamana jakka daya tace ai shi kika bada, daga inda mama altine take tace karamin aikin Laure ne hakan.
Tace to bari idan zaki wuce nabiki a boye sai kikai wa inna ta rike a hannun ta bashi ke nan ba.
Aiko kamar na sani hakan tayi don tana shiga gida dakin ta ta fada ta dauko jakka daya da rabi tabawa Inna na wai inji anty Sa,ade tace arabawa yara gyadan ta saye sana,ata na kwana biyu.
Inna tace kai ita bata gajiya da dawainiya ne da yarinyar nan idan tazo gari ko yaushe cikin dawainiya take.
Allah ubangiji ya bar zumunci baki mama ta tabe tace kwadayi dai madudin wahala ne karamar yarinya tasan ta lakewa masu hannu da shuni tun tana kara ma idan ta gan su gashi har girma abin yabita Allah dai ya kyauta kawai.
Ban shigo gida ba sai da magariba koshi don nasan baba idan ya dawo ban gida zai min fada ne shiyasa.
Don mu kadai yake da ikon yaima fada a zauna lafiya a gidan batare da anyi tada jijiyan wuya ba.
Nashigo ina dan rabe rabe na samu suna sallah don haka nima suri buta na wuce zuwa alwala.
Na idar da sallah Inna tana zaune tana addua nace Inna nawa mama ta kawo maki dazun.
Tace ina ruwan ki ai a gaban ki aka bata takawo min ko don naji nai saurin cewa eh jakka biyar ba sabuwar ta fil a mike.
Humm din da naji Inna tace yasa nagane anyi cuta ke nan kai mama dai ba, a girma wallahi na fadi a raina.
Kudin da anty taba sabbi fil ban ko tsaya kidayawa na fitar daga haban zani na dana kulle nace ma inna ta Inna gashi inji anty tace na kawo maki.
Don na fada mata mama bazata baki su duka ba dazun shine tabani wanan nakawo maki.
Bakina Inna takaiwa duka tana cewa kika aibanta uwarki agaban bakuwa aiko yaya take dai uwarki ce ita din.
Bakin nawa da Inna ta daka na dafe cikin jin zafi amma hakan bai hanani kokarin mika mata kudin ba da nakeyi.
Takarba da mamaki tare da kirgawa ta dago da sauri tana cewa ke yar nan har jakka hamsi ne fa tabaki ?
Nace ban kirga ba ta daice na kawo maki kiyi amfani dasu kafin ta wuce na fara talla.
Take cewa ikon Allah ita din aikin may takeyi haka har ta samu wanan kudin masu yawa take kyauta dasu ?
Nace Inna ba, a birni take ba ance kudi abirni banza ne duk wanda yaje fa sai yai kudi a can.
Tace ke rufa min baki da maganan wautar ki can a ina kika samu wanan labarin karyan haka ?
Idan da banza ne may zaisa wasu suje su dawo tsula yadda suka tafi ?
Mahaifinku sau nawa yake zuwa birni bai samo ba da zaki fadi hakan.
Nace to inna kin sani ko baiso ne shi yafi son zaman mu haka ?
Kallon takaici tai min tace ke kan ban san ranan da zakiyi wayau ba wallahi.
Nace killa sai na girma ko Inna ?
Wani irin takaici na kara bata tace to ai sai ki tsaya har ki girma din sai kiyi wayon.
Sai dan shiru da ya biyo baya a dakin can tace ki saurare ni da kyau kiji abinda zan fada maki.
Na gyara zama ina fuskantar Inna na tace banda kwadai banda roko don yafi komai zubar da mutuncin mutum da sauri.
Ki kawar da idon ki ga abin duniya sai ki zauna da kowa lafiya a duniyan nan.
Allah ne ya hada ki da ita jinin ku ya hadu haka don haka ni bazan hanaki hurda da ita ba don ban taba jin wani abin assha daga gare ta ba banda alherin ta da nake ji a gurin uwarta ko yaushe.
Don haka ki kama mutuncin kan ki don Allah ki rufa min asiri ni da mahaifin ki.
Inda sabo na saba jin nasiha irin haka ko yaushe a bakin Inna ta don haka wanan ba bakona bane sai ma cewan da nayi.
Ai ina dazun da mama altine ta dafa mata kaza tace nazo naci nace da ita na koshi.
Tace kin daiji na fada maki don ke har yanzu naga ba wayo ne dake ba.
Haka ya kasance tsakanina da Inna ta har mahaigin mu ya dawo daga kasuwan kauye da yake zuwa tallan buhun shi na saka kayan masarufi aciki.
Lokacin Inna ta fita don itace da girki ranan idan tana girki dakin mama laure nake kwana haka ma idan mama laure ce da girki dasu Lawisa muke kwana a dakin Inna ta.
Ba zancen awara da safe don haka na fito daga dakin Inna ina gaida baba da dawowa.
Yace a, a Rahama yau ba atafi kai nikan bane nace baba ai bazan yi tallah ba har kwana biyu.
Yace ikon Allah damay ya faru kuma sarkin tallah ?
Nace baba Anty Sa,ade ta zo na gidan mama altine itace ma tace na zauna gida har sai ta koma.
Yace a, a kice min uwar dakinnki ko uwar goyon ki har yanzu ashe ana tare ke nan ?
Mama na zama take cewa kai kwadai bayi ba wallahi yanzu kaida kan ka kake koya mata harkan kwadayi ?
Ashe bari nabar ganin laifin uwarta ita kadai abin ruwan dare ne ashe Allah ya kyauta.
Muna nan maji magani wai an bizzine tsohuwa da ranta.
Yanzu may ye abin kwadai a furin nan ina dai jinin sune ya hadu da yarinyar nan tun tana karama suke tare ?
So kike nace ta daina kulata ko may kike son nayi Allah ne fa ya hada jinin su.
Yara nawa ke garin nan wakikaga ta mama idan ba ita ba da Allah ya hada jinin su.
Yanzu dai ni may nace kuma wanan ai koyawa yaro kwadaiyin abin duniya ne ba akidar alheri bane .
Baba bai kara mata magana ba yajawo turen abincin shi kawai ya soma ci ranshi a bace

Da dare na shiga kwanciya har na kwanta a saman dan keson tabar da nake zuwa kwana dashi naji mama laure tana tashina tace ke Rahama tashi muyi magana.
Wallahi idan naji kin fadawa sokuwar uwarki ko nawa aka bani gidan Altine sai rayuwan ki ya baci a gidan nan kin dai san halina wallahi ko.
Nace ni mama ai ban san ma ko nawa tabaki ba balle na fadi tace munafuka kece baki san kudi ba ?
Kin dai ji abinda na fada maki saina lahira yafiki jin dadi wallahi ko.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
MARICCIN KAN DUTSE, , ,

WANAN LITTAFIN NA KUDI NE CIGABAN SHI SAI DAI ZAKI FARA KARANTA FREE PAGE DINA A KYAUTA YAR UWA IDAN KINA DA RAAYIN HAKAN.


Yau da sauri na shirya zuwa makaranta tunda ba tallan safe gareni ban tafi ba sai da na leka gidan mama Altine tukun.
Ita kadai ce a tsakar gida tana yan aikace aikacen ta muka gaisa nace ina baki tace wai ke ma kin san ai basu tashi da wuri haka.
Tace yau da wuri haka za, a bokon ?
Nace mama kin manta anty ta saye tallen nawa sai hutu yanzu tace humm hakane fa na shafa sam.
Duk da ance suna barci bai hanani lekawa ba dakin nasu suna kwance saman gadon mama da yasha shimfidan sabon zanin gado.
Barci suke hankalinsu a kwance na dan dade tsaye a kan su ina kallon su cikin sha, awa komai nasu gwanin ban sha, awa dashi.
Najuya nafito mukaci karo da mama

Please Login or Register in order to submit comment