Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ki da har zaki dauka zaki iya taimaka min dashi a matsayinki ko don kawai kinga kina auren dan uwana kina juya shi yadda kike so to ni ba shi bane ko maji ki sani.
Murmushi nayi kawai nasan ban taba fari a gurin ta amma ni don Allah kawai nai niyar taimaka mata.
Nace a fili ba matsala anty ni don Allah nazo gurin ki don mu san mafita kawai idan kina da lokaci ki tashi muyi magana dake mu san abinyi tun ba, a kai maki kayan ki ba a wancan gidan yawan.
Wani kallo ta watso min kafin tace ina sauraren ki nace nagode naci gaba da fadin nasan bawai baki son Ibrahim bane a yadda nasan kun dade tare dashi kuna soyayya.
Kawai dai wanan matsalace ta gurin zama yasaki bacin rai irin haka sai nake gani idan yace zai canza maki gurin zama duk wanan matsalan zai iya wuce a tsakanin ku tunda soyayya ce ta hada ku ba kiyayya ba.
May kike fadi mutumin da ya kafe akan shi baida kudin da zai karasa ginan shi kuma baida wanda zai iya kama min hayan irin gidan da nake so a yanzu.
Nace insha Allahu anty idan don gurin zamane na rokeki Allah ki kwantar da hankalinki ayi wanan bukin cikin farinciki.
Yadda kowa yazo lafiya don farin ciki ya koma gida da farinciki a ranshi anty baku gaji yin kunya ba a rayuwan ku balle kuji kunya don Allah ni dai yanzu abinda nake so shine ki kwantar da hankalinki ki koma kamar babu abinda ya faru a baya don marasa da suyi kunya don yanzu kinga ido aka sakawa mama aga yaya zata kaya ana farin ciki zaki shiga gida mai kuntatawa.
Wani kallone takara watso min tare da cewa wanan shine dama maganan da zaki fada min din.
Nace eh anty don Allah tunda kuna son juna da Ibrahim kiyi hakkuri ki daure ayi wanan abin cikin rufin asiri insha Allahu bazaki zauna a wanan gidan ba.
Tsuki taja tare da marya da kanta a saman filo tace na zaci wani shawaran arziki kikazo min dashi har na bata lokacina a kanki haka.
Na dade a zaune ba tare da tajuyo gare ni ba ga wayan ta dake ta verviration taki dagawa.
Wanda nasan ba kowane ke kiranta ba a lokacin sai angwan ta wanda yake a cikin tashin hankalin kan cewan da tayi bazatayi auren ba ta fasa.
Nagaji da zama ina batun tashi anty maryam ta shigo dakin kallon mamaki tai min ganina da tayi a zaune ga maidakin ma kamar bata san ina zaune a gurin ba.
Tace ke kuma may kikeyi anan ina can ina neman ki mama tace wai wanan kayan kitchen din da aka fitar a mayar dasu a kwali tunda babu inda za, a saka su a gidan.
Tajuyo cikin zafin rai daga inda take a kwance idanuwan ta sunyi ja jajir dasu don kukan da tasha sosai.
Tace sai naga iban da akewa shirin auren da har ake maganan rage wasu kayan daki can akai badai ni ba.
Nikan da kyat na mike tsaye muka fita maryam tana mata dariyar mumuke muka fice.
A gajiye na bar gidan don dare yayi a lokacin yaya Sagir ne ya kaimu gida da kan shi don ban driving saboda matsalan cikin dake jikina.
Sai da nai wanka nafito falo na samu Iyya tana gyaran abin da zamu karya dashi tana kwaba abin da zatai muna sanasir dashi.
Ina zama ana kirana ga waya yaya sadauki ne wanda bai ma kasan yai tafiya a lokacin.
Mun gaisa yake tambayana ko mun dawo gida ko muna can gidan su mama har lokacin .
Nace mun dawo tun dazun har munyi wanka gani a falo ma zaune zan sha magani na kwanta.
Yace maji ta kirani tana fada min iskancin da wanan mara hankalin kewa mutane tun jiya wai ta fasa auren ko ?
Nace yaya bafa fasawa tayi ba kune dai baku fahince ta ba bawai bata son Ibrahim bane a, a gidan da za, a kaita ne bai bata ba don a cikin family house din su ne inda uwargidan shi take zaune.
Kaga kasan halin anty Amira da tsandan mutane bata son yawan hayani ita tafi son ta zauna koda yaushe silent bata son yawan hayaniya.
Ya karba kafin naci gaba da fadin don taita mugun hali ko?
Nace haba yaya ya kamata a taimakawa anty please bai kamata abar rayuwan ta a haka ba don Allah.
Yace ok yanzi so kike nima na biyewa haukan ta nace a fasa auren taita zaman gida ko?
Nace ba nufina ke nan ba yaya abinda nike nufi shine ka taimaka da baiwan da Allah yai ma na falala ka sama mata inda zata zauna don wanan auren nata yai karko kamar na kowa please ?
Ban fahince ki ba Fatima kima nifin nine zan bada gurin da Amira zata zauna da mijin ta ko may ?
Nace ai ba mijin ka zakaiwa ba yar uwar haihuwan ka zaka taimaka kamar yadda Allah ya taimake ka kaima ka sama mata gurin zama yadda take so.
Don yin haka kawai shine shedan dan uwata ya samu kuma mai taimako ne ga jinin shi don kaga ba Amira ba kawai wallahi har mama hankalinta a tashe yake akan wanan magana daurewa kawai mama keyi don ta bata karfin gwiwa amma ran mama baiyi dadi ba ace a wanan gidan za, a kai Amira gaskiya.
Yanzun dai na fahince ki yace nine zan aurar da ita kuma na bata gurin da zata zauna kamar na matsu da ita a gida ko ?
Nace wallahi yaya ba haka nake nufi ba ni nufi na shine kawai ka taimakawa rayuwan su tunda Allah ya hore ma abinda zaka iya yin haka din.
Idan kai haka ba karamin lada zaka samu ba har a gurin Allah don shine shedar zumunci yanzun fa kaine uwar mu kaine uban mu gaba dayan mu har kai.
Amira ba ko Nafisa ce da irin wanan matsala din zaka iya taimaka mata idan kaso saboda Allah.
Ji nayi ya katse layin tare da jan guntun tsoki haka yasa banji dadi ba a raina nasan bai yarda da shawaran da nake gani shine a matsayin mafita ba ni.
Bayan mun gama waya nasha magani na mun dan taba hira da Iyya akan zencen tana fadin ahi yasa ba, a son mutum ya faye bakin hali wallahi don karshen shi baya kyau.
Yanzu ga irin ta nan ai tace ita tafi kowa bata ganin kowa da daraja kamar ba mamace ta haife ta ba tafita daban a cikin yan uwa.
Nace Iyya kin san kowa da kalar halin shi ita nata rayuwan ke nan haka Allah yayi ta daban.
Ai ba za, a biye mata ba idan ana son auren yai karko sai a taimaka mata anyiwa banza ma balle ita.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , , , ,


IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH , , , ,



Washegari da kyat na shirya muka kwasa saigidan su mama gurin shagalin bukin da akeyi na samu yan uwan mama saura sun iso nan na shiga gaisawa dasu cikin mutunci da girmamawa.
Na samu guri na kai zaune don indan huta saboda tafiyan da nayi sai ga mama ta fito daga cikin dakin ta tana ganin mu tace , a, a kun karaso ashe.
Nace eh mama nai mata ina kwana tare da tambayan ta ya gajiyan jama, a ta amsa da fara, a da alhamdullahi.
Maryam ta rigani isowa sai gata tafito da alama a tare da mama suke a dakin.
Nan muka shiga gaisawa da ita tana min ba, a wai bata tsanmani ta gannin ba yau yadda na gaji da jigila jiya.
Muryan mamane mukaji tana cewa Fatima ke da maryam kuzo ba bata lokaci muka bi bayan mama din data shiga dakin ta.
Zama tayi saman kujera yayin da ta umurce mu da zama a bakin gadon ta sai dai kafin mu kai ga zama tace maryam kira min wanan yar butsar maryam tace wa anty Amira?
Mama tace ita mana a takaice maryam din ta fita ta barmu ni da mama a dakin sai dai babu wanda yai magana a cikin mu dagani har mama din har suka shigo dakin.
Kowan su guri ya samu ya zauna muna sauraren abin da mama din zata fada muna.
Fatima dafarko dake zan fara abinda ta fada yasani saurin dago kaina da sauri na dan kalle ta sai kuma nai saurin mayar da kaina a kasa.
Tace ban san irin godiyan da zan wa Allah ba da yahadani dake a matsayin diya kuma sarakuwa ta gari a cikin zuria ta.
Fatima ke alheri ce a gare mu abin alfaharin kasancewa a cikin zurian gidan nan a baki daya.
Jin yadda mama take yabona bamu san dalili ba dukan mu yasa Amira saurin daga kai tana kallon mama da mamaki may yakawo wanan yabon haka ne wai.
Mama taci gaba da fadin fatima kin yi abinda ko wace sarakuwa take gurin gani ga ko samu ga matar da danta ya aura a cikin zurian ta.
Nasan baku san abinda yasa nake mata wanan yabon haka ba sai na fada maku.
Yau da asuba yayan ku ya kirani yake fada min cewa Fatima ta kirashi a cikin tashin hankali tana mashi magiya kan lalai sai ya sayawa Amira gida nata na kan ta inda zata zauna.
Yamzun dai in takaice maku tsohon gidan shi daya gina ya tashi a ciki ke maryam na kusa daku ya mallakawa Amira shi halal malak.
Ke kuma yace idan ya dawo za, a duba gida kwatankwancin wanan din ko ya gina maki naki a matsayin naki kema maryam.
Gaba daya sukayo kaina da murna suka rike ni nayi mamaki yadda yau Amira ta sauko haka lokaci daya kan abin duniya.
Tace cikin muryan kuka Bintu ban san godiyan da zan maki ba duk da dai bake ya kamata naiwa godiya ba amma kuma ke ce silar hakan.
Nace anty babu godiya a tsakanin mu don ku yan uwa nane na jini dole mu taimakawa junan mu idan ya dace amatsayin mu na uwa daya uba daya duk dai ni din bare ce acikin ku amma banda uwa da uban da suka fi min baba da mama a duniya har lahira don sun min komai a rayuwana nakarasa a cikin kuka nace don may nima bazan dinga kokarin gani saka dan uwan mu a hanya ba tunda Allah ya hore mai abinda zai kula damu.
Fatima mungode da wanan karamcin don ba kowane akewa alheri ya samu ya tuna baya ba haka.
Yayan ku ya fada min baki taba rokon shi da ya taimakawa kowa naki ba a duniyan nan ba sai idan shi yaga ya dace yai masu wani abin.
Amma mu sai gashi kina ta iya kokarin ki gurin ganin ya kyautata muna nasan ko alherin da yaiwa iyayyen shi kwanaki shawaran kine wanan.
Nan dai mama ta kara ja muna kunne na mu hada kan mu da zurian mu koda bayan ta don haka shine tabbacin dauruwan zumunci mai karko.
Nan dai muka dan taba hira akan yadda za, a bullowa al, amarin bukin da saura kwana daya a saka lalle.
Nice nace mama yanzu shi Ibrahim din ya kamata mu kira muji tashi shawaran ko zai yarda da hakan ko ?
Da sauri anty Nafisa take cewa kamar yaya zai yarda idan bai yarda basai a fasa ba don ni wallahi Allah ban zama a wanan gidan nasu na yawa.
Kinji halinki ko inji mama ta fada a cikin fada da sauri na tare nace anty don Allah kibi al, amarin nan a sanu shi fa sauri baya haihuwan alheri ke da Ibrahim dai kuna son junan ku baida shine ne anty yanzun kuma tunda Allah ya hore mai ai ba zaiki ba ko.
Abar maganan a hannun yaya shi yasan yadda zai bullo mashi da maganan don kin ga wanan magana ce ta maza.
Haka yasa kowa yai shiru dakin don sun san magana ta gaskiya ne mama tace mu tashi mu tafi shi ke nan .
Maryam da ta riga mu mikewa take cewa sai muje gidan muga abinda ya dace ayi ciki ko don kayan dake ciki yaya za, ayi dasu kuma ?
Nace wanda za, a cire aba su mama Abu mana bashi ke nan ba sai dai kwasan su daga nan zuwa can ne aiki ai inji maryam nace ba wani aiki da anyiwa yaya bashar magana suna da manyan motoci sai a kwasa akai masu har gida.
Mama kan dadi ya hanata magana don bats san may zata fada kuma irin wanan alherin haka samun dan uwa shine samun kowa ai namike ina fadi nabar dakin.
Kamar yadda muka tsara din ina fita na kira yaya akan yaiwa ibrahim din maganan tare da kuma yi mashi godiya sosai.
Yace haba queen nine fa ya kamata na gode maki bake ba kin kuwa san irin albarkan dana sha kan wanan zancen gurin mahaifa na.
Idan baki halkantar dani ba hakan yaushe tunane na zai barni na kai ga tuna hakan da akayi kinga ai yanzu an wuce gurin ko?
Ya kira ibrahim din yai mai magana tare da bukatan idan ya dawo ya kawo takardun shi zasu samu ida suka sakashi a maikatar su.
Ya tun kari mahaifiyar shi da maganan taso ta musa mashi amma a hankali ya fadakar da ita alherin dake cikin yin hakan dole ta yarda data ji cewa harda aiki za, a sama mai.
Karshe cewa tayi ya daiyi adalci a tsakanin iyalin shi yace insha Allahu mama.
Shi da kanshi yazo har gida da yamma yai muna bayanin amincewar mahaifiyar shi a kan zancen wanda dama muke hasashen matsalan komai daga gare ta ne don bata son yabarsu.
Ba bata lokaci aka tafi gidan tare da masu gyaran guri decoration din gida mun masu bayani komai yadda zasu gyara mata shi wanda a shagona aka sayo duk kayan da aka saka mata a gidan na miliyoyin naira.
Sosai akai ta shagalin bukin da har su Umma ance mai hali baya barin halin shi har sun fara gulma akan zancen.
Amma da sukaji gidan sadauki tsoho za, a aje Amira kuma ba gidan iyayyen mijin ta ba sai kuma sukai gum.
Anyi angama lafiya shima sadauki ya dawo ran daren daurin aure sune suka shugabanci bukin.
Amarya ta tare gidan ta lafiya kowa sai murna da farin ciki yakeyi yadda dan uwanta ya kashe mata kudi haka na.


****** ********* ******

Bayan buki da kwana biyune na tashi ban jin dadin jikina nasan dan jigilan bukin da mukasha ne dole naji ba dadi haka dama don yawancin event din ma a gidana akayi shi.
Gashi washe gari yaya zai koma Abuja gurin aikin su don yanzu sam baida lokaci ko kadan yanzun ma don shagalin bukine ya dan dauki hutun kwana hudu kawai.
Har yafita motsa jikin shi wanda yanzu bai faye fita waje ba yi akwai kayan motsa jiki kala kala da ya sayo yakeyi saboda tsaro.
Kwance ya samay ni yarda ya fita ya barni da farko yana cire rigan jikin shi hankalin shi yana akaina.
Lafiya kike kuwa har yanzu baki tashi ba karfe kusan tara fa yanzu na safe.
Na dan bude idanuwana da sukai min nauyi nace a hankali wallahi ban dai jin dadin jikina ne sosai yace zan shiga wanka hada min abincina kafin nafito ina son zuwa gurin baba ne nagan shi.
Da kyat na samu na mike zaune yana shiga bathroom din lokacin na sako kafana kasa da zuman na mike tsaye.
Yadda naji an tokare ni ban san lokacin dana sake yar kara ba na koma na dunkule guri daya.
Jin karan da nayi ne yasa shi saurin fitowa daga bathroom hankali a tashe yana tambaya cikin kidimaywa may nene may ya faru ne wai ?
Cikin daure wa nace ba komai bane mara nane kawai ya yanka min da dan ciwo.
Yace oya mike mugani aiko mikewa ya gagareni na sake jin an kara yankoni kasan marana da karfi na sake wani dan kara again.
Yace cikin rudewa O god kingani ko ina ta fasa maki cewa kiyi a hankali kin san condition din ki amma duk baki jiba yanzu gashi zaki jawowa kanki matsala kuma.
Yace barin watsa ruwa sai muje asibiti a gani ko may nene matsala ya juya yana min sannu ya shige bathroom da kyat na samu na mike zuwa dakina.
Dakyat nake iya daga kafana zuwa daki ina shiga kamar an kara min ciwon maran ne a lokacin.
Tsaye nayi na dafa mirrona ganin abin ba na wasa bane yasa na dan duka a gurin wasa wasa nakai durkushe cikin tsananin ciwon mara dake damuna.
Shigowan shi yana fadin kin shirya mu tafine yai arba dani cikin wani hali sai zufa ke karyo min tako ina da sauri ya karaso inda nake duke yana fadin subbahanallahi.
Abinka ga geant din mutum ya yunkura zai dauke ni da sauri cikin wani murya nace mai ya dakata don Allah.
Ido ya kura min daga gurin da yake tsaye yana kallona danaji abu tafe min ban san lokacin dana rike shi gam ba iya karfina na nisa da karfi sai ga yaro ya fado kasa rikon da nai mai duk da karfin shi sai da yaji shi sosai a jikin shi.
Ganin yaro ya fado ne yasa na dan sasauta rikon ina mayar da numfashina a hankali take yarude hankalinshi ya tashi sosai.
Ga yaron yana ta faman tsala ihu a kasa saman ties na nuna mai zanina dake gefe ya miko min na saka yaron a ciki.
Shi kuma yafita daga dakin da sauri hankali a tashe yana kwallawa iyya kira cikin tashin hankali.
Iyya tafito dakin da sauri hankali tashe ganin yadda ya rude bakin shi na rawa yake fadin don Allah Iyya shigo da sauri ki taimakawa Farima ta haihu yanzu a dakin ta.
Haihuwa Alhaji haihuwa fa takara fadin hakana cikin sauri ta nufi dakin hankalinta a tashe sosai takaraso inda nake tsugune.
Reza take fadi nace tabude drower akwai reza a ciki da sauri ta dauko ta yanke cibin yaron dake ta faman kuka cikin zani.
Ta juyo inda nake tana fadin sannu uwar dakina ke kuma haka haihuwanki yake wata bakwai.
Tsab tagyara ni ga gyara yaron shi yana falo ya kasa zama kuma tsoro ya hana shi ya shigo daga ciki.
Yana ganin iya tafito diban bakin sabulun da ta hada a dakin ta ya tare da sauri yana fadin.
Iyyya yaya dai tana lafiya ko kuma yaron zai rayu kuwa yana ma dai rai kuwa ?
Tace insha Allahu zai rayu ba haka ta haifi magidana ba yau bagashi kamar zakaran turawa ba.
Haka nata haihuwan yake wata bakwai take haihuwa ita ke nan.
Ya sauke ajiyan zuciya nan ya jawo waya yashiga fadawa su mama can gida.
Yan uwan mama dake shirin tafiya suka tanbaye ta da sukaji tana fadin ikon Allah ta haihu fa kace yace wallahi ko mama yaro namiji ta haifa.
Nan kuma gida ya rude kowa yana mamaki suna tausaya min sai cewa suke yi boyar Allah bata zauna ba duk jigilar bukin nan da ita akayi shi ashe tana jin abinda take ji a ran ta .
Nan aka kwaso zuwa gidan mu ba bata lokaci kafin duk su iso maryam ta riga kowa zuwa ta samay ni na fito wanka ina saka kaya a jikina.
Tace madam haka kuma abin ya kasance dake ashe ta nufi inda yaron yake dan karami dashi ta dan bude zanin da iya ta nade shi a ciki tana kallon shi.
Tace wanan ai duk Amir ne aje wallahi duk uban su suke kwasowa yaran basu biyo ki.
Nai murmushi ina kaiwa zaune nace yafini karfin jini ne shiyasa hakan tace yadai fiki kwazo ragguwa kawai nace nadai ji.
Shigowa yan gida yasa gida ya kara rudewa lokaci guda sai sannu suke min.
Yace wa mummy sai mu tafi asibiti aji idan na shirya don a duba yaronkuma aga lafiyan shi.
Dole haka na fito muka kwasa sai asibiti ni dashi da mummy da maryam.
Anyi duk aune aunen da za,ai muna antabbatar dagani har yaron muna da lafiyan mu.
Haka yasa hankalin shi ya kwanta sun so wai a aje yaron amma mummy bata ba da surport ba kan hakan muka dawo gida.
Nan kuma na fara jego ba shiri don haihu a bazata sosai ake kulla da yaron yadda aka kafa muna doka akan shi.
Wanka sau daya ake mai a wuni koshi ba kamar yadda akewa sauran yara ba towel ne za, a dan dinga jikawa cikin ruwa dumi ana goge shi dashi a hankali wanda mummy ce keyiwa yaron .
Babu mai daukan shi don wasu saboda kwakwafi sai suce abasu yaron su gani.
Mummy ta hana ko mama Asiya dake zama da dare a gurin mu nan take kwana a tare da mu.
Naga yan uwa da abokan arziki masu zuwa barka don wasu ma ba sanin su nayi ba .
Shiko sadauki duk hankalin shi bai kwanta ba yana ganin yaron zai mutu ne ba zai rayu ba.
Ranan suna yaro yaci sunan mahaifin Umma watau Abdullrahaman nima sunan nawa mahaifin ke nan amma shi Abdullahi yake.
Sai da komai ya koma normal ne ya samu komawa gurin aikin shi tare da jaddada muna akan mu kula da yaron wanda a hankali yake ta hiling.
Nan dai komai ya koma normal a gare mu anyi auren su anty Nafisa wanda mijin dake son ta ya bukaci anyi da wuri sadauki ne ma yadan ja lokaci don ta samu tayi istibira,i kafin auren.
Nan ta dawo gidan mu ta zauna kafanta kafana ko tafiya zanyi tare muke zuwa da ita.
Har Allah ya taimaka tagama aka saka ta lalai muka sha buki muka kaita kano gidan Iyayyen mijin ta muka barta can.
Mutane ne masu matukar addini da sanin darajan bako don ko sun daraja mu sosai ga abin arzikin da mukaje mata dashi sai dai ita a Abuja zata zauna a can mukai mata jeren kayan takayan gara ne kawai muka kai kano gidan mijin ta.
Ko a kanon ma an gyara mata dakin ta na can kano din sosai komai acan acan dashi.
Bayan kamar wata hudu akai bukin Raiha aka kaita maiduguri gidan mijin ta shima dai a Abujja yake aikin shi na soja.
Itama dai zama tare yasa sadauki ya taimaka mata sosai don yai mata goma na arziki sai da tai kuka don murna.
Iskancin su bai bari sun aje komai ba na kasan su sai iskanci da bushasha kawai suka saka agaba

Please Login or Register in order to submit comment