Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da murya yace maji kiyi hakkuri don Allah don kin ga akanki suke sauke haushin su ko yaushe don haka zan masu yadda yake so a zauna lafiya.
A hankali mamatace Allah yai maka albarka ya baka ikon kyautata masu ko yaushe.
Yace amin maji tace ina fatima yace ta koma barci yau weekend bata fita tace yana dakyau ta dan huta don nasan anjima kadan yau gidan maryam zasu dire.
Yace kaman ko kin sani mama aini dai yanzun nasan ni da samun kanta,sai sun gama bukin nan kan.
Tace kaima ka sani tsakanin maryam da Fatima ai sai Allah yace da yake muna fukai ne ba sun hade wa sister na kai su biyu.
Ba wani hadin kai halinta dai ne sai ita Amira tafita daban a cikin ku sai kace diyar umma.
Dariya tabashi cewan da tayi sai kace diyar umma take yace itama dai zatai auren ai ta huta da fadan kowa hakana.
Dadai yafi mata alheri taje kowa ma ya huta da bakin halin ta hakanan.
Suna gama wayan da mama sukai sallama kowa yana cikin farin ciki duk kan su.

****** ********* ******
Sai da nai barci na mai ista na tashi batare da ya tayar dani ba nata shi wanka na fada nafito ne ina zaune ina shafa mai ya shigo dakin.
Shima yai wanka don a shirye yake a lokacin idanuwan shi a kaina yace ashe barcin ba mai nisa bane inace ko sai biyu zaki tashi.
Nace cikin murmushi da yau anty maryam ta yankani ai tun fa safe take kirana a waya.
Sai da na shirya duk yana zaune a bakin gadona yana dakilar wayan shi tsab na gama nace mashi nashirya yaya.
Yadago kai yana kallona yace au yaune zakuyi bukin ke nan da sauri na,ware idanuwana nace yau kuma yaya ?
Yace to wanan uban kwalliyan haka dana ga kinyi aina dauka zumudi zai sa kuyi shagalin bukin ne yau ?
Yamike yana cewa ni dai yanzun nasan ba a da time dina sai dai yadda Allah yayi dani kawai.
Nace haba dai yaya yanzun ne ma fa zan bar gida to eleven fa yanzu ake nema kamata yayi ace ina gidan tun bakwai ai.
Eh tunda gaki ungwazoma ba sai kije bakwai kiwa jariri da uwar shi wanka ko.
Dariya nayi kawai nace tau ni fa ai yanzun komai zanji amma bazanyi fushi ba tunda ina son abar ni na tafi.
Shi yajamu zuwa gidan ya sauke mu a kofan gidan ni da iya don maryam tana dakin ta bata koma gida ba.
Uwar mijin ta daine tadawo gidan nasu da zama inda yake zaine na dan kalla tare da gyara tsayin mayafina don gyale na saka yau nace sai mun dawo ke nan yace four zan dawo na dauke ku fa.
Kaina na langabe nace haba yaya four fa inace ko sai magariba yace idan kika bata min rai wallahi yanzun zaki shiga ki fito mu wuce nace da sauri iam sorry sir don nasan karamin aikin shine hakan.
Ko don ya batawa maryam din rai na bude mota zanfita naji yace ban son fitina fa da kowa kuyi lafiya a watse lafiya nace insha Allahu yaya.
Nafita ina cewa mun gode sai ka dawo yaja mota yanajin dadi komai kankantan abu sai nayi godiya akan shi.
Ya furta a fili simple life .
Muna shiga gidan tun a kofa muke jin hayaniyan mutane yan uwan yaya bashar sun cika gida sai surutu sukeyi.
Nai sallama iya tana bayana nagaidasu ina fadin to abani ruwan zafin ajuyo nai mata wanka duk aka kwashe da dariya.
Inna dake gefe tana gasa jariri tace hai Fatima kwana nawa ance ma maye ga nama.
Daga daki maryam ke fadin ki koma ban so tunda bakiyi farin ciki da zuwan baby naki ba sai yanzun ne zaki zowa mutane.
Na daga labulen daki tana zaune da cup din kunun kanwa a gaban ta sai zufa takeyi tako ina nace bura uban nan wani abu ko sai haihuwa wallahi anty kece haka kace kace cikin zafi.
Na zauna saman gado ina cewa wayyo Allah na wallahi duk na gaji sai kace nice na haihu wallahi.
Ta kurba kunun tare da lumshe idon ta tace da waye ya haihun bake ba ni sunan nai cikine kawai ai dan nakine.
Nace kada ki sa na gudu dashi fa yau gidan mu tace aida yayan ki ya tare maku a gida kinko ga jiya da kyat inna ta samu yatafi ya kwanta ya barmu wai shi anan zai kwana nace Allah yabaku maryam.
Ke da yaya wallahi kuna sha,anin ku harara ta kara watso min tace kunan daban ne Bintu ?
Tace wai da sauri na manta ina gadon asibiti ma nace Bintu ance za,a balbalani balle yanzu ina dakina zaune.
Wanan dan rikici halin shi sai shi wallahi yanzun ma cewa yayi wallahi idan nai tsiya dani dake yanzun zamu shiga mu fito tace dako na hada shi da maji wallahi.
Nace kina hada shi da ita nabi mijina don ban son fadan nan dakike sa ana mashi ko yaushe.
La la la Bintu ni kike fadawa haka yau kan yaya eh lalai kan mage yaji gishiri kuwa.
Waya na jawo na fara dan dana nomba sai ko naji ya dauko yana fadin hello na,shake muryana nace yaya love kaji anty maryam tana ce min Bintun daka hana ko.
Ya ko hau fada maryam wallahi zan zo na balbalaki tace iyye watau karana kika kai ma ke nan lalai Bintu wai Fatima wuyan ki yai kauri ashe.
Nace sorry yaya ta gyara yanzu tace Fatima din kayi mata hakkuri tsuki yaja yace mashiririta kawai kuka sani nace asauka lafiya na kashe wayan.
Tace yar iska ke dai kin kirashi da,wayyo kiji muryan shi kawai ba,wani kai karana da kikayi.
Indai yayane wallahi naga take taken shi yarinyar har tausayi kike bani don nasan baki da hutu.
Nace abu cikin duhu sirine ne tace kwarai kuwa nayarda sirine don nagani yanzu a zahiri.
Sai lokacin Iyyan Rabi ta leko dakin tana gaida maryam din na tuna nace Allah sarki iyya na manta fa kina waje kiyi hakkuri kinji.
Muna nan dakin sai hira mukeyi shigowan matan yaya Imirana dakin shine yasa muka kwasa muka yo waje can sai ga wasu yan school din mu da suka kare da ita sun shigo.
Wasa wasa gida ya fara cika iya ta mike zuwa inda ake aiki takama masu aiki.
Shigowan matar yaya Ahmad tanbele ya tashi sai hira take muna ana kwasan dariya wanda hiran nata duk kusan batsa take yi wai ita hira ke nan.
Sai ga Umma da mama sun shigo barka da wata kawar mama makwabciyar mu nan muka shiga gaidasu sai dai yadda Jamila matar yaya Ahmed tayi masu banji dadi ba.
Don ta nuna rashin da,a sosai a gare su kamar bata san sune ba abin duk ya bamu mamaki ganin su baisa ta fasa abinda takeyi ba sai ma ci gaba datayi da abinda takeyi.
Basu dade ba sukai sallama suka tafi har kofa muka rako su ni da matar yaya Imirana Hadiza wace ke da dan matashin ciki yanzu.
Gani bai sa umma ta fasa fadin abinda tai niya ba don cewa tayiwa Hadiza ki yi haraman komawa gidan ki don banga abinda kukai wani taruwa nan kunayi ba kamar haihuwan gidan sarki.
Tace ai shine zai zo ya dauke ni yace tace to kindai ji na fada maki ki maza ki koma gidan ki ban son irin shige shigen nan.
Sai da muka dawo cikine take cewa sai mutum nason ya shigo yan uwan shi amma aita hanashi .
Jamila tace walleh ke an nan nikan anso akawo min wanan control din amma tuni na wuce gurin don ban yarda uwar miji ta hanani shakat.
Hadiza tace nikan sai lokacin da yazo zan tafi mutum yana cikin yan uwa yana dan walawan shi amma sai duk a takura maka.
Jamila takara cewa yanzun dadafa ke akaji inda tsofin gana walleh har yanzu su kishi sukai harda diyan su kosu kegane su kaman kan su a hade walleh cin kan su suke tsakanin su.
Kowa gulman dan uwane yakai idan daya baya kusa ni jiranakai watarana su shiga gonana nai masu tas wallahi.
Nidai da maryam bamuyi magana ba muna jin su don da mun tanka namu ne zai fita nasu ya boye.
Nan dai muka wuni anata faman shiririta irin na matasan mata idan sun hadu zallansu.
Sai naji ranan naji dadin haduwan mu haka saboda bamu taba haduwa haka ba tsakanin mu sai bayan sallah la,asar muka fara watsewa daya bayan daya nikan yaya yai min halarci sai yamma lis yazi daukan mu muka koma gida.
Yace ma Iyya kada ta damu kanta da zancen girki zai sawo abinda za,aci da dare.
A gajiye nake don kai da komon da mukayi a gidan maryam wanka nayi nai sallah muka fito falo yana dawowa shima wanka yayi yafita gidan.
Nan muka zauna da iyya muna hira tsakanin mu tana bani labari akan matar yaya Ahmed bata da mutunci ko kadan bama wanda ya zaci har zasu kai wanan lokacin dashi ai.
Iyya ta dan tausa muryan ta kamar wani na jin mu tace ke irin su Nafisan Umma ta fa duk harkan su guda.
Nace Allah mai iko watau kowa dai Allah ya bashi a dakin shi ke nan ba mai fadawa wani kuma.

****** ********* ******
Sannu sannu suna yana matsowa sai shirye shiryen bukin suna akeyi inda yaya sadauki yaiwa maryam duk wani nauyi da iyayye suke dauka na yar su.
Nice mama tasa a gaba akan na auwatar da komai daya dace da shirin sunan.
Haka yasa ban zaunu ba don ma na samu iyya tana da kokari itace na samu take yawancin zirga zirgan na komai a gidan.
Komai mun hada Alhamdullahi ranan suna yaro yaci sunan mahaifin uban shi wanda dama tun kafin suna Inna ke kiran shi da Alhaji karami.
Cikin yan uwan Inna da sukazo ne nazo zan wuce naji wata na fadin wai ba Fatima bane nan najuyo na kalli matar naga kamar na san ta.
Sai dai nace mata nice batare dana gane ko wacece ba sai cewa tayi halan baki ganeni ba dai ko nace gaskiya ban gane ki ba.
Tace Asmau matar marigayi Kabir da kika tashi aure nace Allah sarki ankoyi haka wallahi.
Nan na tsaya muka gaisa da ita na tambaye ta yaran ta tace sunan lafiya sun girma yanzu suna makaranta.
Tace min ai tayi sabon aure ta auri wani miji amma dan sanda ne tana nan cikin gari yanzu.
Nace ina anty tace itama tayi aure anan gari tana auren wani malamin yan izala masu da,awa tana zaune a arkilla ne.
Nan nakawo mata abubuwan abinci dana buki na karamata sosai takuma ji dadin haka tace nai mata kwatancen gida na zata zo.
Nawuce ina tunanen duniya matar da da take jin kan ta wani abu yau itace takoma haka kai duniya abin tsoro ne wallahi Allah dai yasa mu gama da duniya lafiya kawai.
Anci ansha maijego tafito yadda ya dace duk
wanan abin da mukeyi zakace Amira ba yar uwar maryam bace tana tsabare abinta ita dai haka Allah yayi ta kawai nake gani.
Munyi photuna sai da mutane da sukazo sunan inda aka hada walima wata malama tai wa,azi akan hakin iyayye ga yayan su dakuma hakkin diya ga iyayyen su.
An raba gift na robobi da yan wasu kayan sha taro ya,watse lafiya akabar mu mu zalla yan gida da dare bayan na idar da sallah maryam tana zaune tana shayar da yaron ta na kura mata ido ina tunane.
Tana tambaya ko an aikawa makwabtanta da abinci gidajen su banji may take fadi ba sai da take ce min wai may kike tunane ne haka Fatima ?
Na lumshe idanuwana nai murmushi tare da sauke ajiyan zuciya nace wallahi ba komai anty tace ba komai kike zurfin tunane haka.
Nace maryam yaya ya fara min zancen haihuwa fa tace to may ye abin damuwan kai ciki.
Ya baki mana yagani in baki dauka ba wayasani ko lefin shine banaki ba kadama ki damu kan ki da wanan har yaushe akai auren da za,a fara wanan magana haka.
Ba kowa ya zuga shi ba nasan Nafisa ce tun ranan naji tana ce mai wai ita yanzun baby din shi kawai take jira suzo don ita sune yaran ta.
Kuma nasan tana fada mai hakane kawai don ya maryar da hankalin shi ga zancen.
Idan ma yai maki magana kice mashi yabaki aiba kece zakiba kanki bako ?
Maganan ta yai min dadi sai da na shirya mata komai sanan na kirashi yazo ya dauke ni tace na dauki duk abinda nake so daga cikin abinda ta samu.
Dariya nayi nace haba dai anty aiko da ban gode ma Allah ba yanzun haka fa ina da turamay sunkai ashirin da ban dinka ba aje.
Tace kaji masuyi don jallah inda nice ai ban iya ganin turumi ban din ka ba tace da tuni nagama dasu.
Na dan bata rai nace kin san halin yaya shifa yafi son ko yaushe ya sayo min dogayen riguna irin na kasashe da yake zuwa kuma yafin yaga na sasu.
Tace kuma wallahi suna maki matukar kyau ko dazun naji wasu na gulman ki ai wai duk shigan da kikayi kamar kece kika halicci kanki.
Nace kai kaji mutane da gulma kuma ina ruwan su dani tace wallahi Fatima kin dace da Allah yasa yaya yazama mijin ki da bakece matar shi ba da sai dai muyi taganin abu a gidan wasu.
Allah yana da hikima da basira kila dalilin hakane ya jefo rayuwan ki a cikin mu fa?
Nai murmushi nace sanin gaibu sai lillahi anty amma gaskiya yaya baida matsalan komai inba wanan shan ba kuma yanzu sai nake gani kamar yama daina yi.
Mun ware turame wasu umma da Inna harda iyyya Rabi saida maryam tace aba turmi daga ciki da kannen mijinta su sahura su biyu.
Sai goma yazo ya dauke ni muka bar gida zuwa namu gidan kowan mu har iya duk mun gaji a lokacin.
Wanka mukayi don kowa a koshe yake sai kwanciya ba school yasa na kwanta washe gari bamu fito ba sai after eleven muka fito daga daki kowa agajiye yake.
Nan muke falo ranan bai fita zuwa ko ina ba sai dai wayan da yake ta faman bugawa kawai.

****** ********* ******
Ranan bayan suna da kamar sati biyu wanda bai zaunu ba don ginan sabon site din su da akeyi ya mayar da hankali sosai ga aiki.
Ya dawo da la,asar don ya huta yace yabajin kan shi na mashi balain sarawa a lokacin.
Sai wayan shi yai kara Baba sani naji yace yadauka suka gaisa dashi baba din ke fadin yana son ganin shi da dare anjima ya amsa da to Baba ina nan zuwa insha Allahu.
Magani na kawo mashi cikin wani dan karamin plate da ruwa a cup ya hadiye maganin.
Can naji yaja tsuki yana fadin ko kuma yau mai baba Sani ya samu yake nemana a gidan shi.
Mutumin da abaya ya tsane ni kamar may ko gidan shi cewa yayi bai son yana gani na,shida baba Shaibu ni tun lokacin suka fita raina wallahi.
Zancen auren Raiya ne ma da baba ya matsa lokacin sai anyi yasa nake dan zuwa kada ran shi yabaci idan yaji banzuwa.
Amma haka idan naje kiranta zasu yi tamin wullakanci yara da samarin gidan suna cewa ga dan wiwi din nan yazo.
Na dan yi murmushi don nasan cikin bacin rai yake magana nace ba babanka bane yaya duk abinda sukayi ai don kan su wallahi.
Kadai je kaji may yake neman ka dashi yafi kada yace kuma yakiraka kaki zuwa kiran nashi.
Yace ai zan tafi naji may yake nemana dashi kuma ne wai kwanaki fa da haihuwan na na maryam sai da maji tasani gaba na basu yan kudade duk kan su har gwagwanin mu.
Nace Allah ya saka da,alheri ai duk yiwa kaine hakan ma.
Sai da yai sallah ishai ya shirya cikin wani shadda mai ruwan maku dinkin garen hannu haka ma rigar iya cinya akayi mai shi, ya nufi gidan baba sani ban kawo komai ba tun da kanin mahaifin shi ne.
Yana isa ya buga waya yace gashi kofan gida ya iso baba yace ya iso mana yashigo yana falo zaune.
Yasamay shi zaune tare da matar shi ya gama cin abinci suka gaisa duk cikin kyankyamin yadda falon ya koma yake.
Ya tambaye shi harko ki shi da matar shi yace duk Alhamdullahi.
Can baba yace dama ba wani abu bane yasa na kira sai akan zancen ka da yar uwar ka Raiya ne naga gara kawai ace anyi abin nan tunda dai ita ba wai auren tayi ta kuma gama karatun ta bana.
Dama dai can kuna son junan ku dan matsalane aka samu na munafunci ya shiga tsakani.
Ba karamin mamaki Sadauki yaji ba yadda baba yau ya murje idon shi ya iya mai wanan magana.
Ya manta yadda yaci wa mahaufin shi fuska yana kirarin wai zai bawa yar shi mashayi dan wiwi dan giya.
Ya kuma tuna Irin halin da maji tashiga a lokacin irin cin fuskan da akayi mashi kan wanan auren hadin da akaso yi bayan tun Raiya tana karama duk sallah sai ankai mata kayan toshi.
Itama kanta Raiya din sai da taci mai fuska daya buga mata waya lokacin da yaji labarin sai ce mashi tayi.
In aure ka in kaika ina kama big girl ace na tsaya auren wani mashayi wanda baida aikin yi sai shaye shayen tsiya kada ka kara kirana daga yau na fada maka .
Yana tuno haka ya dago kai yai murmushi yacd Baba naji abinda kace amma na farko kasan nayi aure ko.
Nabiyu kuma ita Raiya fa ta bude bakinta tace min bata sona bata kaunana idan na haihu cikin maji kada na kara kiranta.
Don haka Baba don Allah abar zancen da yawuce yawuce kawai Allah ya bata mafi alheri a gareta ni yayan ta har gobe najini zanyi duk wani abinda duk wani yaya yakewa kaunar shi.
Mama suwaiba tace haba Umar ai kasan halin yarinta har nawa Raiya take hakkuri zakayi tunda kuna son juna.
Yamike yana cewa gaskiya Baba abar wanan zancen ba zai yuyu ba tun da tun farko an fara shi da tsegumi masuyi kuma ba fasawa sukayi ba.
Baba yace dakai da Raiya duk daya kuke a gare ni don haka ina da ikon yin komai akan ku murmushi kawai yai masu yace shi zai koma ayi hakkuri.
Raiya da yan uwan ta suna labe sunajin yadda akayi sukace kingani kin wa kanki tace aiko yaki ko yaso sai na shiga gidan nan wallahi koda tsiya ne.
Jifa irin kafirar motar da ranan mukaga matar shi naja dayan tace kice dai ta koma kamar diyar wani presedent da ita.
Dan iska kudi yake samu har na tsiya wallahi ba ance albashin su ma,wai yafi na wasu gwaunoni ba kudi.




ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,

IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH YABI MUNA HAKKIN MU AKAN KI

Tukin mota yake yana tunanen wanan hali na Baba sani wanda ya rasa gane kan shi.
Son kaine ko kuwa rashin tunanen may yadace ne don yai matukar jin wanan magana daga bakin Baba Sani din.
Ko da ya iso gida ya samu har nayi barci ko shima sai da ya gama duk abinda zaiyi ya hawo gadon ya kwanta.
Inda nake kwance ina barci ne ya kalla kamar ya tayar dani sai kuma ya fasa ya dan kura min ido yana kallon yadda nake barcina a tsanake.
Tausayi yaji na bashi yasan dani da iyayyena sun mai komai yadda suka dauke ni suka bashi .
Bayan nashi jinin sun kyamace shi sun ki shi saboda halaiyan shi da sukace baida kyau.
Amma kuma shine yau kuma da ake ganin kamar ya zama wani abin kwarai zasu dawo suce wai dashi zasuyi.
Kai wai mutanen duniya ne suka lalace koko duniyan ce ta lalace haka da kan ta.
Yanzu shi Baba Sani har ya manta da cin fuskan da sukaiwa mahaifin shi shi da matar shi ne da zasu dawo suce shi ne kuma suke son ya auri yar su ko may ?
Da kyat dai ya samu har barci ya dauke shi yana cikin tunanen irin halin Baba sani da wasu mutanen da basu san kunya ba.
Da safe koda muka tashi ganin shi nayi kamar wanda baijin dadi don yau ko fita judging bai samu yi ba na safe.
Har nai wanka na shirya nafito naji shi shiru a daki na nufi dakin nashi na leka shi.
Yana kwance a saman gadon shi ya kifa cikin shi alaman motsin da naga yanayine yasa na gane ba barci yakeyi ba a lokacin.
Na nufi bakin gadon nashi ina fadin ina kwana yaya love?
Sai lokacin ya dan dago kai ya juyo gare ni har na kawo bakin gadon na dan zauna daga gefe tare da tokaro hannu na daya ta baya saman katifa na sa shi a tsakiya.
Yace yaya dare naga jiya kin samu barci sosai baki ma san dawowa na ba.
Murmushi nayi tare da dan dukar da kaina daidai saitin fuskan shi nace nima wallahi ban san yadda akayi har nai barci ba haka da wuri daga fa wai na dan jiraka kadawo shine barci mai nauyi ya dauke ni hakana.
Nace tashi kai wanka ka karya yaya yace ki tayar dani to duk banjin dadin jikin nan nawa yau.
Da sauri nace subbahanallahi yaya may ya samay ka kuma maimakon yabani amsa sai ya jawoni zuwa jikin shi yana sauke numfashi a hankali.
Can naji yace Fatima na amsa na,am yaya yace tunda kun samu hutu sai ki shirya nakai ki kiga su mama duk da ba haka naso mu tafi masu ba don akwai dan planing din da nake son yi a kan su.
Wani irin sanyi naji ya sauka min a raina ina fatan zaki je ki dawo batare da wani matsala ba dai.
Nai maza nace mashi matsalan may kuma yaya bayan gida na tafi gurin su mama.
Yace to fada min inji da kanki kwana nawa zakiyi a can idan kin tafi don inji ko kina da adalci .
Shiru nayi ina nazari nace nace ko nace sati uku don na samu na zagaye dangi da yan uwa da abokan arziki.
Sai kuma nai tunane ko a gidan baza su amince min nan da Rabah nai wanan kwanakin ba haka.
Amma a fili cewa nayi ko kwana nawa kace nayi ai zanyi ne na dawo , yadan shafo fuskana da hannun shi yace.


Please Login or Register in order to submit comment