Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

man shanu daga cikin ledan tana jerawa a kasa.
Ya dan juyo gare ta yana tsuki abinda ya dakatar da su daga fitinan da suka dauko yi da sabuwa ke nan.
Yace ai gora hudu ne ko kibawa kowa nata ke Amarya ya duban gurin da nake ina gyara wutan huran da muka nasa yana zabarbaka daga tukunya.
Jeki ki karbi gorunan ki bawa kowa nata kason ta dauka da sauri na nufi gurin mama hauwa din na fara kaiwa mama hausatu ta zaba na mikawa mama hauwa na ta,na dauki daya zuwa gurin yaya sabuwa da nata goran .
Tun kafin na karaso na ji tace may kike nufi wai ke yar wayo ko kin zabi mai kauri kn kawo min mai ruwa ko ?
Da sauri na juya inda dayan goran yake na dauka na kai mata ta zaba sai da ta karba ta jijiga ta kara juyawa sama da kasa sai ta miko min wanda na aje da farkon na juya don duk a tsorace na ke a gaban ta kada ta make ni.
Kaiyya inji mijin su daga gurin da yake zaune saman wani dutse dake tsakar gidan.
Yana na kallon yadda muke kwasa da ita kan man shanun da ya sayo muna daga kauyen da suka tafi.
Tace ana dai rabon son kai a gidan nan ace da may iyali da mara iyali duk kaso daidai za,ayi shi wai haba wanan ai dul cikin zalumci ne wallahi Allah ko.
Zaki soma ko ?
Wai ke Sabuwa baki ba kanki lafiya ne ki rufawa kanki asiri ne haka wai ?.
Kin manta da yadda aka kwasa a baya ko da kyat fa na samu malam shehu yai bugun gaba yaje ya dawo dake .
Au to kina son fada min cewa kece kika tura biko na ko may ?
Daga inda yake zaune yace ke dama kina daukan cewa zata canza halinta ne ai mai hali baya barin halin sa.
Yace ke hausatu dauko min tsimayn nan nawa na dan sha don banjin alaman dadin jikin nan.
Nan dai kowa ya watse ya kama gaban shi muma muka gama hura kusan nice nai aikin huran don na iya dama tun a gida.

****** ********* ******
Kamar yadda mata idan sun taru sai zancen mazan su hakane ke kasancewa yanzu a gurin maza.
Taron da akeyi na fadanci a kofan gidan na Alhaji garbati wanan karon ma sun hadu ana fadanci don dan abin da suke samu daga gare
shi.
Baba salla ne ya fara cewa aikai Alhaji sanyin babana lafiya lau kake ga amarya ga sanyi .
Ko ba a fada ma jikin ka ya nuna ka samu lafiya ga hakan nima dai kukewa zanyi naga na samu koda bazawara ce mai dan dama na kawo gida ko zan samu dan gurin hutawa bana.
Jin zancen su kawai yake amma zancen yana tsuma shi sosai haka yasa ya yanke cewa zai gwada ya gani dai ko ya samu lafiya shima ya fara murzan amarci da yar amaryan shi.
Ranan da akai wanan zancen a dakin sabuwa yake dama ta ishe shi da mitan ita a bukace take fa.
Bayan ya shigo gurin ta ya kokarta yaga ya samu gamsuwa amma ya kasa hakan gashi ta isheshi da minta wai ai da amarya ce inda yake kare karfin shi gurin yar karamar yarinya dan yai bajinta ta gani.
Shiko ya na samun kanshi daga gareta ya fara wani irin nishi yana jin kamar ranshi zai fice mai a lokacin.
Da kyat yaga safiya sabuwa ce ta tayar da mutanen gidan don neman taimako a kan shi.
Ba,a bata lokaci ba da safen nan aka nufi asibiti dashi hankali a tashe duk kowa gidan ya koma jigun, jigun abin babban gida take a kashiga tsegumi ga Sabuwa.
Wasu suce kila wani mugun abin tai mashi har taso halaka shi, wasu kuma suce dama ba lafiya gare shi ba kila bakar jarabanta da ta sabane ta matsa mashi har ta so halaka shi.
Nidai da yake akwai kurciya a tare dani ba fahintar zancen su nakeyi sosai ba amma na shiga halin damuwa don ance sabo turken wawa ne.
Dan zama na gidan ko ba komai yana bani kulawa yana tattalina yadda ya dace ayi.
Sai zuwa karfe biyu suka dawo tare dashi yaji sauki sosai kamar ba shine aka fita dashi gidan da taratara ba..
Sun tara mu duk kan mu matan shi a dakin mama hausatu sun muna bayani cewa likita yaba da doka kan cewa mahaifin su har yanzu bawai yaji saukin lalurar shi bane don haka akula don Allah kada a dinga matsa mai kancewa lalai sai yayi wani abu da watan mu a bishi a hankali.
Ni dai na fahinci suna magana suna yawan kallon inda nake zaune ni da sabuwa ne amma ba wai na gane manufan su bane.
Sai da yai mata kwana biyun ta ya dawo dakina kamar kullun idan nice zanyi girki na kammala komai da nakeyi wanda ba sai na fita tsakar gida nayi shi ba.
Don ni ai fadan sabuwa zance gaba ya kaini don Allah ya rabani da tuwon taro komai a dan karamin shiya na da aka kebe min nake abina wanda hakan yakaiwa Sabuwa ko ina.
Tayi mita akan itama sai ya kebe mata nata shiyan daban kamar yadda ya ke be min nawa ni kadai nake kwamacala na ba wanda ke ganina sai wanda ya shigo inda nake.
Girki dai Alhamdullahi don tun a gida nakeyin abina tun mama nacewa wai Innata tana sa ina masu jagwalgwale har ta gaji ta sa ido ranan girkin inna ta idan na dawo tallah da wuri kafin naje diban ruwa zan tsaya na taya ta aikin girki da gyaran gida.
Haka yasa yanzu ban sha wani wahala ba a gidan auren nawa da na tsinci kaina a ciki da rana tsaka.
Yau da yake ba fita hira yakeyi ba sai gashi ya dawo gurina tunda magariba, anan yai sallolin shi kofan daki inda yasa nai mashi shimfida.
Nakawo mai abinci na koma daki na zauna ina ciki naji ya kirani yana cewa fito mana Amarya ki barni kuma ni kadai a waje ina maki gadin kofa.
Haka yasa na fito daga ciki na samu gefen tabarman da yake zaune na zauna can dan nisa kadan dashi.
Ya soma cin abinci koda na fito yace wai ke waya koya maki girki haka ne yar karama dake amma kin iya girki haka.
Nace Lah inna ta ce ai nice ke mata girki idan ina gida, yace kai amma gaskiya ta kyauta min sosai.
Yaushe rabon da na dinga cin girki haka acan acan mai dadi a gidan nan ?
Cikin shirmay yara nace kai haba Alhaji ga mama hausatu ga mama hauwa ga kuma yar barayan ka duk kace baka cin girki mai dadi ?.
Yace ai sunayi amma nakin yafi dadi ne Amarya da ina da lafiya ai wanan girkin da kika iya da na more ma hannun ki .
Don ance yadda mace ke aikin ta ko mai nata haka ake samun shi nace to kila magi ne basu sakawa kamar yadda nake sakawa a nawa ?
Murmushi kawai naga yayi min yace to ke naga bakici komai ba mana ko har kinci naki ne ?
Sai da na dan tabe baki can nake cewa nifa ko a gida tuwo bawai ya damay ni bane nafi son naci shimkafa komai rashin dadin shi ko abu mai dan ruwa.
Shiyasa ma mama takan ta fada da inna ta wai itace take koya min rashin cin tuwo gani diyar tallakawa dani sai karya.
Nace kuma fa Alhaji babu laifin Inna a ciki nice dai bana so idan an matsa min naci sai na amaye shi kaf.
Yace ikon Allah abin naki halita ne ke nan nace haka naji Inna ta tana fadi shiyasa koda zanyi auren nan maganan inna ta ko yaushe shine kada nai sakaci da kunnu don shine abincina.
Yace to ashe sai na dinga sawo maki shimkafa kawai kina sarafawa kina ci ko ?. Nace a, a kada ka wahal da kanka ai na saba da hakan don ni abinci bai damay ni ba.
Yace ashe shiyasa man shanun da na sayo maku ke naki kamar ba, a amfani dashi tunda baki cin tuwo ?
Muna cikin haka dashi sai ga mama tashigo gaidashi tace a, a ango da amarya ake hira ashe Sabuwa na bayan ta tafe.
Sai ji mukayi tace ai abinda yakeyi ke nan yana biye mata kullun jiya wa yau abu yaki ci yaki cinyewa an kwaso muna mai farar kafa tana batun mayar damu marayun dole.
Haba Sabuwa may yakawo wanan magana haka kuma a gurin nan wanan yar cikin taki ne zaki tsaya yiwa wanan magana haka ?
Tace Allah ya raba yata da wanan bakin jaraba na wanan yarinya dubaki gani don tsaban rashin kunya wai zaune take shimfida daya da Alhaji adole ita wai ga mace ?
To yin haka laifine kuma mace da mijinta ana raba su zama ga shimfida daya tunda anriga da anzama daya ko ?
Dama yaya kune masu daurewa karya gidi ai take gani kamar ta kai mace ?
Kai yauko ga wata magana ga sabuwa uku gareki uke ke gareta to mayye banbanci a nan.
Ya dakatar da ita da cewa yanzun dai may ya kawo ki nan din don ina fama da kaina ban son fita ?
Tace dama zuwa nayi naima yaya jiki sai na samu kana ma a cikin raha ne ashe kai ?
Yace eh kin san ina gurin da ake kwantar min da hankali kamar yadda nake bukata ko yaushe.
Ai naga alama sai ayi a sannu don kaji dokan likita idan da son samune ma kabar gurin yarinyar nan har ka samu lafiya don nasan kana ganin ta ba kyaleta zakayi hakana ba ?
Yace shi likitan ne yaba da dokan na kauracewa iyalina din ?
Kada na basu kulawan da ya dace dasu sai na nisance su ko ?
Kadai yi a hankali don ko banza ita a ganiyar kurciyar ta take yanzu tunda jarababban yarinya ce ta na iya saka yin abinda bashi ba ?
Yace kamar yadda kika sani yin dole shekaran jiya ko kika tashi kashe ni ke nan ?
Idan ban kashe ka ba ai wanan mai ido tsakiyar kai zata kashe ka ita.
Ta juya ta wuce abinta yace sakariyan banza kawai mara hankali da tunane.
Nan mama dake sauraren su tun zuwan su ta nisa tace kai halin sabuwa sai ita kullun ba a girma.
Yace ina girma ga sabuwa anan bakin kishin yarinyar da bata ma san tanayi ba yana batun kashe ta don ita kanta kawai ta sani a duniya.
Sai lokacin nace mama ina batun zuwa gaida ke da wuni sai gaki kuma kin shigo yanzu tace to na hutar dake ai nazo duba jikin maigidan ne dama.
Yace jiki Alhamdullahi da sauki sosai yanzun ma nake batun shan magani na da likita ya ba ni ai.
Tace to amma malam a tsaya ga na likita kawai ba a dan gwadawa dana gargajiya agani kuma ko a dace.
Yadda aka fita dakai a gidan nan fa shekaran jiya ya tayar wa kowa da hankali sosai.
Yace ai ina kan gwadawa ke ma kin sani al,amarin ciwo ne yanzu idan ya kama sai a hankali fitan shi.
Ta nisa tare da cewa haka ne kuma Allah dai ya kawo sauki kawai za, a ce .
Ta juyo inda nake na dukar da kaina ina wasa da kafana dana ke kadawa a hankali, take cewa to mu kwan lafiya Amarya.
Nace mama Allah ya bamu alheri tace amin ta juya tafice tare da rufo min kofan shigowa sashen nawa.
Yace bari na koma daga ciki sai ki samu ki shige da kayan nan ciki ko ?
Nan ya mike da kyat zuwa cikin daki ni kuma naci gaba da kawar da kayan da yai amfani dasu a gurin.
Haka a dadafe yai kwanakin da zaiyi a daki na ya koma gurin sauran matan shi can.
Ranan naji shakat a raina don nan yake zaune duk wanda yazo gaishe shi ciki zai shigo su gaisa dashi.
Haka yasa na kasa sake jikina a gurin nawa don yawan manyan mutanen kauyen mu da ke shigowa gaida shi.
Shi ko na lura yana jin dadin azo a samay shi a gurin nawa da yake acan acan ko yaushe a cikin gyara da kamshi.
Don ina manejin dan kayan kamshi da anty ta turo min dashi daga birni saboda mama altine ta kashe lokaci gurin yi min bayani a kan kamshin dakin mace.
A ranan da ya koma dakin mama washe gari sai ga Iyyaye na sun samu labarin rashin lafiyan nashi sunzo gaida shi.
Ina dakina ban san shigowan su ba ashe har sun dan jima da shigo sai mama Altine ne ne kewa ni banga diyata ba fa ?
Lokacin mama ta tura a kirani ana fada min na taso da murna na nazo dakin inda suke da zuwa ina ganin su maimakon nai murna sai kawai na fashe da kuka kawai.
A, a ashe da mun san haka zakiyi muna da bamu zo ba sai dai mu tsaya daga kofa mu gaidashi mu koma.
Da kyat suka samu nai shiru mama altine tace ashe har yanzun yar tawa bata daina wanan tabaran nata ba ?
In banda haukanki ai sai a dauka ko wani mugun hali ake maki gaki kinyi kyaunki bulbul dake daki ya karbe ki.
Na kara shigewa jikin mama altine ina cewa wallahi mama nayi fushi ace idan ita Inna ta taki zuwa ta dubani har dake mama bazaki zo ki gan ni ba sai kace nai maku wani laifi ?
Yanzun baga mutanen gidan ku masu kirki da karamci suna kula dake ba duk halin da kike ciki fa muna da labari.
Mama altine da dayan makwabciyar mune kawai suka bini zuwa dakina ita Inna ta taki zuwa nan ta zauna dakin mama hausatu har su fito daga guri na su tafi.
Narasa irin taron da zan masu don murna nace mama ni nama rasa may zan baku wallahi tace, ba mu ruwa ya wadatar damu tunda munsha a dakin yar uwarki amma zamu sha naki.
Ruwan randan kasa na da yai matukar sanyi har naso bayan randan ke bayarwa don sanyi.
Na debo masu suka kinkima sosai nan muka kara gaisawa dasu suna ta yaba kyaun dakin danayi.
Nace mama yaya wajen anty na kuna da labarin ta ko ?
Tace Anty ki Alhamdullahi don ta samu lafiya sosai har naji tana cewa tana son zuwa ta duba mu ma nan.
Nai murna kwarai dajin wai antyna zata zo garin duba mu mun jima da su mama muna dan hira sukace zasu koma sai ga yarona habibb da leda wai Alhaji yace abawa bakin da sukazo suyi hakkuri.
Ban tsaya duba ko may ke cikin ledan ba na mikawa makwabciyar mu ledan sukace ashe mu dawainiya muka kawo maku kuma mu da mukazo duba lafiyan maigidan.
Kafin su barni su kara jamin kunne nayi hankali da Sabuwa da diyan ta a gidan don gujewa makircin su.
Ban sani ba ashe bayan tafiyan su fitina ya tashi tsakanin Alhaji da Sabuwa wai don may zai ba su mamana leda da abuba ciki ?
Wa nafi da zai fifita uwaye na akan su ai itama matan gidan su suna zuwa gaidashi amma bai taba basu komai ba sai ni za , abawa iyayyena.
Da kyat aka samu wutan ya mutu bayan kakausan kashedin da yai mata yana hurta sai ya sake ta wanan karon.
Jin kalman saki yasa ta ja bakin ta tai shiru tasan tunda ya furta hakan zai aikata ne don bai taba hurta mata kalma na saki ba a duk rikicin da sukeyi tsakanin su.
Sai gashi yau akaina yana furta mata cewa ta ishe shi da fitina a gida ai itama wasu ta samu a gidan kuma ba abinda bai mata ba lokacin da take ganiyar amarcinta har zuwa yanzu.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , ,

IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WA WANDA BAI BIYA BA ALLAH NA GANIN KI DON AMANA NE, , ,


Izuwa yanzu komai na gidan ba matsala saboda kakausar kashedin da manyan diyan Alhaji suka taru a tsakar gida sukayi.
Kan abar masu mahaifin su ya samu lafiyan shi don yawan futinan da aje saka shi zai iya jawo mai wani sabon matsala kuma.
Sunyi barazanan daukan mataki akan duk wace take kawo masu yawan tashin hankali a gida.
Wanan dalilin yasa gidan ya samu kwanciyan hankali na kwana biyu.
Gashi dai zan iya cewa Alhaji yana cikin mazan dake kokarin ganin yaba iyalin shi kulawa don bai make aljihun shi ga iyalin shi.
Kwanciyan hankalin da na samu ba fitina ba tsangwama yasa na sake murjewa nai kyau nai haske sosai.
Nan kan kula da yanayin Alhaji idan yana dakina sai naga ya tsura min ido kawai can naji ya sauke ajiyan zuciya a sanyaye.
Ban daukan wanan a komai sai dai naga kamar wani abune ya shige mai a duhu yake saka shi a tunane.
Ban sani ba ashe tausayina ne yake ji yana ganin kamar ya shiga hakkina da yawa.
Yakawo ni gida ya girke ba biyan bukatan komai a kaina bai san ni haka wani gata ne Allah yai min ba da hakan.
Allah bai barin bawan shi mai hakkuri ya tabe banza a duk inda yake watarana sai kaci riban hakkurin ka insha Allahu mudfin kayi shi da zuciya daya.
Ranan na tashi da safe na shiga nai wanka bayan na gama yan aiyuka na sai ganin nayi jini yana zubo min a gabana.
Tun ina bini bini kewayawa na wanke har tsoro ya fara kamani gashi naki sakin jikina ko cikin gida naki shiga na taya su aikin komai a ranan.
Sai bayan sallah azahar da naji kowa ya shige dakin shi na idar da sallah na nufi gurin mama hausatu.
Na samu ta idar da sallah tana zaune tana lazumi ita kadai a daki tana ganina tai dan murmushi a fuskan ta tana cewa Amarya .
Yanzun fa nake zancen ki a zuciyana yinin yau banga kin fito ba tun safe da muka gaisa nake cewa ko dai lafiya kuwa ?
Nakai zaune tare da cewa wallahi mama yau banda lafiya akwai matsala shine nazo na fada maki.
Cikin sauri tace subbahanallahi may ya samay ki kuma yar nan ?
Shiru nayi ban san may zance da ita ba a lokacin sai dai kaina dana sada a kasa kawai.
Tace may yafaru amarya gaya min mana nifa ban dauke ki a kishiya ba matsayi diya ta ta cikina nake daukan ki.
Na kara dukar da kaina a kasa nace mama dama sai nai shiru can kuna na dago na kara cewa a sanyaye dama yaune naga jini kawai yana ta zuwa min a karkashina tun safe da na tashi ga marata sai ciwo yake min.
Nace barin fada maki ko zanga likitane tun cutar bai min yawa ba ?
Tace cikin mamaki ikon Allah Rahama dama baki fadi bane sai yan zu ?
Na dago kai da sauri na dan kalle ta tace wanan ne karo na farko da kikaga haka ko may ?
Nace mata a sanyaye eh mama.
Tace to ki saurare ni kiji da kyau wanan abin da yazo maki zan iya cewa ba cutane ba kuma cuta bane alama ce ta girma yazo maki da hankali da samun natsuwa.
Duk ko wace mace da kike gani tana yin wanan abin a rayuwan ta wace bata yi kuma to tana da matsala kuwa babba.
Wani irin ajiyan zuciya na sauke taci gaba da fadin kada ki tsorata da hakan nan tafara yi min bayanin yadda zan kama kaina a lokacin da nake cikin wanan laluran na fashin sallah.
Kamar yadda uwa zatai wa yarta bayani haka ta zauna tai min bayani sai daga karshe tace da zaran kin gama zakiyi wanka kamar yadda kike yin wankan janaba.
Nace wankan janaba mama tace eh idan kin kwana da mijin ki ba kikan yi wankan tsarki ba ?
Nace eh kawai ba tare dana fahinci may take nufi ba tace to shima hakan zakiyi sai dai gurin niyya ya banbanta ne wacan janaba zaki ce wanan kuma haila.
Nan dai ta kara koyar dani komai nace nagane mama a makarantan boko dana islamiya duk an koya muna shi na kuma rike.
Nace mama dama wanan jinin shine jinin hailan da ake nufi tace shine amarya sai jinin haihuwa shima tai min bayani da kwanakin da ake son mace tayi ta fara yin tsarkin shi.
Na gamsu sosai da bayanin mama akarshe take ce min sirina ne daga ni sai mijina kawai daya zama dole ya sani ake son ya sani idan ma ina fashin sallah naga kowa ya tafi sallah na shige daki nima kada na zauna a waje kowa ya fahinci ban salla don siri ne babba ga mace.
Nai mata godiya tare da mikewa na wuce zuwa dakina na kimtsa jikina kamar yadda tai min bayani nayi.
Ina fita na bata tausayi sosai sai dai bata ga laifina ba sai na iyayyena dake da alhakin haka akaina.
Gashi yar karama dani a wanan zamanin an min auren cushe ga miji, mijin kuma babban mu kamar alhaji gashi ashe ko hankalina ban gama mallaka ba.
Kamar yadda mama ta fadakar dani hakan ne nayi na gyara jikina tsab mai makon na ma dinga shiga mutane sai kawai na dinga nisanta kaina da jama, a baki daya gani one two one ta na kewaya na gyara jikina.
Da maigidan ya shigo gida ne mama ke fada mashi cewa ashe amarya sai yanzu ta fadi yau ta samay ni cikin damuwa take fada min don bata san kaiba.
Shima yai mamaki kwarai jin sai a lokacin na fadi ashe kuma ban san komai ba akan faduwa hakan na nufin ke nan har yanzu ina a matsayina na cikakkan budurwa as a virgin .
Tausayi na ne ya kara kamashi a lokacin ne yai daya sani shiga rayuwa na da yayi da wuri haka nan.
Ke nan zancen da kishiyar mahaifiyana ta fada mai nacewa gara ma da yazo nema don ni watsatsace ban da kamun kai na san maza ko zan iya zama dashi ai ban ganin tsufan shi tunda maza nake so a rayuwana.
Wanan magana babu inda ya hango kamshin gaskiya a cikin sa don dai halin rayuwa na ya nuna mai ta ko ina ni yarinya ce mai mutunci da kima nasan darajan kaina da iyayyena.
Don haka dole ne yai min adalci akan zaman da nake dasu don ya fahinci yarinya ce ni sharaf ban san komai ba na duniya.
Wanan dalilin ne yasa ya kara jawo ni jikin shi sai naga yana haba haba dani fiye ma da farko da yake min.
Mutanen gidan ganin kwana biyu bana yawan fitowayasa suke shigowa daya bayan daya suna tambayana may ke faruwa dani ne wai ?
Sai cewa masu nake banda lafiya ne bana jin dadin jikina na ne shiyasa.
Su daukan su na samu cikine, wai, sai naji suna cewa Allah ya ingata ya kawo muna mai albarka.


Please Login or Register in order to submit comment