Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mu.
Tafe nake ina tunane a zuciyata sam bana cikin natsuwa ko kadan a lokacin zuciya bata kwanta ba da wanan hadin da ake son yi min.
Sam garbati bai min ba gashi dai dattijo a gurina na ni yar sha biyar tsoho kutuf nake ganin shi,
Koma da ace lokacin kuruciyar shi yake nidai bai mun ba don bakine wulluk kakaura dashi sai dai ba can kwarai ba.
Ga fuskan shi duk ya bar gemu a ciki baje baje wai shi sunnan kauye babu dai wani abin armashi a cikin sa ko kadan.
Sai dai ban da wani zabi ga gakan tunda ba zan iya bijirewa hukuncin mahaifina ba akaina.
Duk da har lokacin ba wai ma na fahinci may ye zaman aure ba tunda a gidan mu ba wani zaman auren dadi naga anayi ba ma balle na koya.
Nasan irin rayuwan da inna ta tayi na zaman bakin cikin rayuwa ni ma dai din shi zan je naitayi gidan nawa auren ke nan.
Ban da wani zabi a hakan don ban isa na bijirewa zabin mahaifina ba haka zan ta kokarin tursawa zuciya na kaunan shi koda kuwa zuciyan nawa na barazanan kamuwa sa ciwo ne.
Ganin yanayin da na dawo gidan yasa bayan na dan shiga da yan mintoci Inna ta mike daga inda take zaune ta biyo ni dakin mu.
Nan ta samay ni nayi zaune nayi tagumi ga ledan da nashigo dashi na tasa a gabana.
Tocilan hannun ta ta haska ledan da shi sabulai ne sai clean manya biyu sai turare fesawa na passition da turmi zani guda biyu sai kudi wai kudin dinki dubu uku.
Baki Inna ta ta rike tana cewa kai anya Alhaji garbati bai dauko hanyan riya ba ga alamarin nan kuwa ?
Yanzu ace duk yawan iyalinshi zai iya binsu da makamancin kayan nan haka ne ?
Gaskiya ni ban son abinda tun ba, aje ko ina ba zai shafa maki bakin jini akai .
Duk wani abinda zaiyi a gidan nan tamfar a kunnen iyalin shi ne don dai yaya tana hurda da sabuwa da can baya.
Daukan ledan tayi wai zata kai wa babana da mama dake waje da sauri na tura hannu ciki na kwashe kudin don nasan idan ankaisu mamace zata kwashe su da wani dadin bakin ta.
Inna dai bata ce min komai ba ta juya ta fice daga dakin ina jin su baba yana cewa kai kaya haka kamar za, a kai lefe ?
Mama sai faman binciken ledan take da sauri nasan kudi ne take nema a ciki gashi ta wani tsuke fuskan ta tamau da ganin kayan.
Can taja tsuki tare da tura kayan a gaban babana tana fadin kaiyya sai dai tsiyan abin duk wanan gatan tsoho ne.
Da yaro ne shine za ai farin ciki da nuna rawan kai amma tsoho ga karamin yaro may za, a gane ciki haka.
A, a lauratu inji babana kon san da haka kikace nai maki alfarma na bada ita gare shi tunda da dan uwanki akazo neman ta ?
Idan kin san haka ne may yasa kika sakani gaba saida na furta na bada ita yanzu zaki zo min da wanan sabon zance kuma ?
A, a ni yanzu may nace kuma ai gaskiya na fada yanzu ba ga abin arziki ya fara sauka maka ba har kuna murna.
Cikin mamaki yace murna kuma kamar yaya lauratu akan wanan kayan ne zanyi murna da rayuwan da yata zata shiga ?
Nifa don ki na yarda naba Rahama ga wanan mutumin may naci nasa da zanji nauyi shi a baya ?
Ashe ke nan ke da wata manufa kika sa na bada Rahama gare shi ke nan ?
Manufar may kuma malam banda abin arzikin da na hada ni idan bashi din ba akwai wanda ka taba jin yazo ya sallama akanta ne a gidan nan bayan duk ta gama zubar da mutuncinta ga samarin gari.
Daga inda nake ina sauraren su na hade wasu yawun bakinciki a raina tare da hawayen da yazubo min.
Koma may zan tarar a gidan gara na tafi na huta da kullin sherin mama da yaranta hakana nida inna ta akaina.
Jin hayaniyar tasu zai yi karfi ne yasa na fito waje inda suke don mama ba komai bane hassada ta nuna min karara .
Tayi min hakane don ta jefa rayuwana dana mahaifiyata a kunci ne kawai.
Basuyi aune ba sai ganina sukayi a waje durkushe a gaban su ina cewa baba don Allah kabar wanan magana haka.
Indon nice na yarda da kaddaran da Allah ya kawo min na auren garbati bazan bari kayi kunya ba a kaina insha Allahu.
Tausayi na bashi yai shiru tare da yi min wani irin kallo na ban tausayi yagane manufata bazan bari yai magana biyu ba yace eh yadawo yace kuma a, a daga baya.
Yace shike nan Rahama Ubangiji ya tsare mun ke a duk halin da zaki riski kan ki a gidan shi nace amin baba na share kwallan da suka zubo min na mike na koma dakin mu.
Ina jin mama bayan sun gama hayaniya ta juya dakin ta bata dade ba ta rufo kofan ta hakan ya nuna ranan bazata yarda na kwana a dakin ta ba ke nan.
Inajin Innata bata shigo daki ba da taga haka dakin da suke aje shirgin su har bunun dakin ya zabbace ta gefe daya don wahala ta dan gyara min gefe daya tace na kwana a can ko naje gidan mai kuli na kwana.
Nace dare yayi Inna bari kawai na koma can na kwanta yanzu mama ta rufe gidan ta nasani.
Baba tana ganin haka ya nufi dakin mama ya na bugawa tace daga ciki wai lafiya kake dukan min kofa haka kuma may kuma zan maka ?
Yace ki bude Rahama ta shigo ta kwanta tace ai kaba uwar ta daki ka bani don haka ku kwanta tare da ita mana tunda ta zama yar gwal matar Alhaji yanzu.
Dole ya juya ya barta zuciyar shi na tir da Allah waddai da halin mace ba haguwa irin ta.
Sai ta kaika ta baro kuma ta tsira ma sabon fitina dama wanda ya kaucewa Allah dole ya fuskanci kalubali irin haka a rayuwan shi.
Hakana na kwana dakin ga sauro ga beraye suna ta hawa min jikina ba dadi ko kadan dakin don yawan shirgin kayan aikin su dake cikin dakin.
Kwana biyun girkin Inna haka tayi shi a cikin kunci a gidan rai a bace mata duk nabi na damu ga bacin ran da mahaifiya ta take ciki ga zancen auren da ake son yi min na dole.
Haka nake zaune a takure ga mama ta saka mu gaba da gori ita da diyan ta duk mun kasa sukuni a tare da mu.
Na dai yanke shawara zuwa yamma na shiga gurin mama altine ko zan dan sarara a tare da ni.
Nan samu mama tana dan aikace aikacen marance na shigo da sallama na na karbi tsintsiyan da take shara a hannun ta na karasa mata sharan.
Na dawo gurin da take zaune tana gyara geron da zatayi birbisco dashi na abincin dare na karba ina gyara mata.
Kallon yanayi na tayi abinka da babban mace ta fahinci babu dadin rai a tare da ni lokacin.
Take cewa lafiya kuwa yar gidan anty na gan ki yau wata iri dake haka ?
Maimakon nayi magana sai hawaye ne suka biyo baya tace subbahanallahi may ke faruwa ne Rahama ?
Sai da nayi kuka mai isata nake cewa mama baki ji kaddaran daya fada akaina bane halan innata bata samu shigowa ta fada maki komai ba ?
Tace Asiya ta kwana biyu bata shigo gidan nan ba gaskiya may ya faru.
Ina kuka nw nake labarta mata komai da ya faru a gidan mu akaina cikin kuka tace waye shi wanda aka baki din ne ?
Nace Garbati cikin rike kirjin ta tace wani garbatin ba dai Alhaji garbatin dan bida ba dana sani ?
Nace a sanyaye shi mama.
Tace subbahanallahi yanzu shi mahaifinki da ranshi da lafiyan shi zau dauki ya kamar ki ya mika wanan gidan na sa, an nin kakan nin ki ko may ?
Nan ta haufada tana cewa idan Salihu bai yi hankali ba sai Lauratu ta kona shi tun a cikin duniyan nan wallahi ko.
Fada sosai mama tayi tare da kara kwantar min da hankali take cewa zan tafi gurin anty ki ance min ita ma bata jin dadi ga abokan zaman ta ba kirki ne dasu ba.
Kin san kishin yan birni ba irin namu ne ba na kauye kishi suke suna hadawa da yahudanci aciki.
Rayuwan ne na kowa tasa ta fishe shi akeyi wai suna ganin su wayewa ne a gare su.
Inbashi ba dan uwan ka baida lafiya ina zaka kawar da kai gareshi haka kana tsabagan gaban ka.
Nace mama Anty na bata da lafiya ne ?.
Tace ina fa taga lafiya tunda tazo din nan take fada min wai bata da lafiya ajikin ta har zasu tafi kasan waje da maigidan a dubata.
Allah yaba anty na lafiya nace tace amin Rahama ita nake gani ta tuna min da mahaifiyar ta don dan uwan ta shi namijine baidamu damu ba kamar yadda ita take kula mu.
Na sake cewa mama dama anty tana da abokan zama ne tace tana dasu mana har biyu ma.
Ai anyi aurenta ba a kokai shekara ba uwar mijin tasa ya auro yar uwarta shima mahaifin shi wai akwai yar abokin shi da yake son hada shi dashi tun farko shima yasa ya auri yarinyar.
Zoki ga irin yadda suka saka min yarinya a gaba da fitina suna ganin itace bare a cikin su sai abinda suka ga dama suke mata a gidan .
Allah dai yasa shi mijin yana son abin shi haka yasa basu samu yadda suke so ba akanta.
Yanzu ga ciwo yazo ya sakata agaba haka wama yasani ko ije ne aikai mata ya hanata jin dafin rayuwan ta.
Nace mama ije kuma may nene ije ?
Tace baka ji maganan ba keda zaki shiga kishi cikin tsofon mata Rahama baki san ije ba kuma sai may.
Nan tashiga yi min irin kissan ije da dalilin da ke sa aiwa mutum asiri idan anga hankalin miji nagareshi da yaran shi.
Nan nai mutuwan zaune nace na shiga uku mama koma don ai min ne yasa mama ta tura baba ya kaini wanan gidan akashe ni kowa ya huta dani kamar yadda take fadi.
Har na dawo gida duk yadda mama taso ta fahintar dani hakan bai samu ba daga gare don na kasa fahintar dongon sharfin da take min akan ije wai shirin kishiya .
Ko da na dawo gida na samu ranan har baba ya dawo daga kasuwa ko suna zaune da mama yake tambayana daga ina nace na shiga gurin mama altine ne na taya ta aiki .
Bai yi magana ba sai bina da yayi da harara har na shige dakin mu ban dade da shiga ba Inna ta kamala abinda takeyi sai ji kawai nayi ta rufo kofan dakin ta garam.
Nace ashe yau akwai tsiya a gidan nan ke nan don Inna zata rama abinda akai min ne kwana biyu na barina na kwana dakin shirgi ni kadai sai bera ye.
Lawisa ce tashigo gidan daga gurin hira ta fara zuwa dakin mu don ta kwanta taji shi a kargamay.
Ina jin ta lokacin data juya zuwa inda iyayyenta suke tana fadin wai Asiya ta rufe kofan ta don haka suke kiran Inna da sunan ta gazatsau ba sayawa.
Mama tace kamar yaya ta rufe kofan ta a ina take son ku kwana yau din ?
Nace a raina jifa mama da son kai ta manta abinda tai min ni .
Ban dai ji baba ya tanka masu ba har lokacin tasowa mama tayi ta shiga dukan kofan mu da karfi amma ko motsi Inna batayi ba ga wani katon dutse da tasa ta kare kofan dashi.
Ranan inna tasha zagi gurin mama shima baba yazo ya buga amma taki budewa ban san ya suka karasa ba da yarasu yan so a gidan mudai basu kwana ba a dakin mu.
Haka na kwana da wanan damuwan a rana washe gari tun da farar safiya na fito daga dakin da nake mu dana kwana.
Ina alwala naji mama na tayar dasu Lawisa wai su fito kada beraye su kashe su a dakin wai sun kwana suna ihun bera.
Dariya ya kumay ni daga inda nake nace farau da dadi ramuwa da ciwo ke nan tai min taji dadi yanzu an mata wai taji zafi.
Baba da ya dawo daga sallah dakin mu ya fado yanawa Inna fada wai bata kyauta ba da ta rufe dakin ta inda yake shiga ba nan yake fita ba.
Har ya gaji ya juya ya fita daga dakin don kan sa ba wanda ya kula shi.
Na fito ina shara naga fitowan Inna daga dakin saye cikin zumbudeden hijjab din ta na sallah idanuwan ta yana fitar da hawaye.
Kai tsaye na fahinci manufarta da sauri na yada tsintsiyar dake hannuna na nufe ta tare da shan gaban ta na riko mata hijjab din ta.
Allah ya taimake ni duk suna daki a lokacin nace inna ina zaki ?
Inna ta juyo idon ta yana zubar da hawaye cikin raunaniyar murya take ce min.
Yarinya bari na tafi gidan mu na gaji da wanan tauye incin da ake min a gidan nan haka.
Take nawa idanuwan suka kawo ruwa a lokaci daya ganin yadda Inna ke zubar da hawaye ga nata idon.
Nace Inna may zai sa ki tafi a lokacin da nafi bukatan ki a kusa dani ?
Hannun ta na kama sai naga bata mussa min ba na jata muka koma dakin mu ni da ita.
Sai bayan mun shiga naji motsi a tsakar gida ashe mama ce tafito don ta hura wutan kunu.
Nace haba Inna may zai sa ki bari shedan ya rude ki a daidai lokacin da mukafi bukatan zaman ki a gidan nan a tare da mu.
Don Allah inna kiyi hakkuri hakan mama ta dade tana son gani daga gareki.
Inna sai kuma da komai ya kusa kai karshe zakice zaki fice kibar mata gida taji dadin gallazawa rayuwan mu yadda take so.
Kiyi hakkuri Inna wata rana sai labari insha Allahu.
Kallona Inna take yadda karama dani nake jero mata wanan maganan haka.
Zama naga tayi bakin gadon ta sai da ta share hawayen dake fuskan ta hakan ya nuna min tayi taushi ga magana na.
Tace haba yarinya da za, a daina da zuwa yanzu yaci su daina sai abu yai dan sauki sai kuma abu ya sake dawowa sabo.
Ni wallahi nagaji nagaji wallahi duk haihuwan da nayi a gidan nan nayi shi ne bisa rantsatsen rabo kawai amma ba da son raina ba.
Nace cikin sanyin murya inna ki dai yi hakkuri ko dan darajan mu don Allah.
Cikin fushi tace dani yarinya ina son na kwaci inci mune a gidan nan daga ni har ku an mayar damu kamar wasu bayi can a gidan nan bamu da incin kan mu ko kadan.
Nace ki dai dan kara hakkuri inna don Allah komai da sanin ubangji akeyin sa baki san tana din da Allah yai ma hakkurin mu ba.
Shiru tayi tana nazari niko ina tsaye na kura mata ido cikin tausayi nasan Inna tana matukar hakkuri agidan mu sosai.
Na share hawaye nace inna ki saki ranki kamar komai bai damay ki ba zakiga mama abin ya kuma koma mata ciki.
Ai ance mace ko a dakin ta tana yaji ko ?
Gashi naga kin fara daukan wa kanki fansa a gare su ai basu taba tsan manin zaki iya masu haka ba da kikeyi yanzu.
Nan dai nai ta bata hakkuri har na samu ta sauko naga ta dan sake jikin ta muryan mama ce ke cewa ina mai sharan nan take ne kin bar shara iska zai kwashe.
Sai ji nayi Inna na fadi aiki take min a daki a sa wasu su share ba ita kadai bace ai a gidan.
Nace a raina taufa ance mai hakkuri dama bai iya fushi ba mama zata kai inna ga bango ke nan.
Muna nan zaune wani dabara ya fado min a raina na saurin daukan hijjab dina nace wa Inna ta ina zuwa na fice daga gidan.
Kofan gida na koma na tsaya ban dade ba naga baba ya fito gaidashi nayi yana kallona yace Rahama may kike a wanan gurin da sanyin safiyan nan haka ?
Nace baba kai nake dako kafito akwai maganan da nake son muyi dakai ne.
Kallon mamaki ne yai min nakai durkushe a gaban shi nace don Allah baba alfarma nake nemawa inna ta akan zaman su da mama a gidan nan.
Duk zaman da suke na kishi a tsakanin su baba ba wai lalai bane sai ka saka bakin ka a ciki tunda kai ba mazauni gida bane baka san waina da ake toyawa ba a bayan fitan ka.
Kallona yake cikin mamaki yace Rahama har ankai lokacin da za ki tari gabana akan maganan uwayen ki.
Nai saurin cewa baba ba hakana bane yaune naga inna har ta shirya wai zata bar gidan bata iyawa ta gaji da abinda ake mata shine nace bari nai magana.
Yanzun haka wallahi inna batasan zan yi wanan maganan da kai ba ma hakkuri dai nake baka baba ko dan darajan mu a tsakanin ku ka rangwanta ma rayuwan ta hakana.
Shiru yayi kamar mai nazarina can yace naji amma ita Asiya ne yau har tai niyar yaji ?
Nace kwarai kuwa baba Allah ya gyara ni kadaine a waje na tare ta data fice daga gidan.
Yace to jeki naji Allah yai maki albarka idan nadawo zanga ita innar taki zamuyi magana da ita na fahinta nace baba nagode Allah ya kara rufa asiri.
Ya wuce na juya na shiga gida zuciyana fes na san ko ba komai killa Allah ya kusa kawo muna saukin al, amarin mu ne a gidan.

****** ********* ******
Tun daga wanan lokacin da mukai magana da babana ta fahinta naga al, amura sunyi wa inna sauki sosai ba inna kawai ba har ma diyan ta da akewa kahonzuka a gidan mun dan samu saida sosai.
Ya zuwa yanzu ba karamin alheri Garbati yake kawowa ba gidan mu wani naci wani kuma dangin tufafi ne duk ba, a tabawa sai gurin mama altine ake boyewa.
Cikin hakane na roke shi yai hakkuri har na zana jerabawa na na karshe kafin ayi bukina dashi.
Da kyat na samu ya amince min wanda zuwa lokacin har labarin zancen aure na dashi yabi gari wanda mama ce da diyan ta suke yada zancen a gari.
Don mama har iyalin shi sai da ta fada masu irin alherin da yake kawo muna gidan mu .
Wai yanzu duk neman shi a kaina yake karewa komai kawo muna yake dani da uwata idan anga yadda muka koma wasu bulbul damu don mun samu ya rike muna kan maciji muna wasa da bindin shi.
Haka yasa matan shi suka tayar da hankalin su su basu yarda ba ya dauko masu yar jikan su a matsayin kishiyar su mafarin nazo ina masu rashin kunya a cikin gida.
Yace shi ra, ayin shi ke nan mai zama ta zauna wacce bata iyawa hanya a bude yake mata.
GNin da gaske yakeyi yasa suka kama kan su bayan ya saka masu waigi ga zancen da cewa.
Kada yaji wani ko wata yaiwa yarinyar nan ko iyayyen ta wani sheri zai dauki mumunan mataki akan ko waye a gidan.
Dole suka saka mai ido ba yadda zasuyi namiji idan yaso abu kunya fice mai yake a idon shi.

Mama altine ta tafi birni ganin anty da tadawo daga waje ganin likita akan matsalan ciwon ta.
Sai washe gari bayan ta huta anty ke tambayan ta wai mama ina Rama na take tana nan tana karatun ko ?
Mama tace wani karatu Sa, ade Raman ki kan aure zatayi bada dadewan nan ba.
Haba mama wani aure yarinya kamar Rama kuma ?
To ai sai kiyi Rahama kan har an kawo sadakin ta itace ma ta hudu a gidan mijin ta.
Anty dake kwance tace what ?
Mama wai da gake kike ko wasa tace ina wasa dake ne balle na fada maki wasa.
Uban ta yaba da ita ga wani tsohon maikudi na garin mu aure yanzu haka karatun data kwallafawa raine ya hana ayi bukin kin san ta samu sa, a don kokarin ta an kaita gaba yanzu bana zata fita daga makarantan ma.
Ran anty yai matukar baci dajin wanan labarin da tayi na zancen aure na nan dai mama ta koro mata komai akan zancen.
Na bata matukar tausayi tace mama in ba abin kauye ba ko mu da mukai aure da girman mu yaya muka kwashe da kaidin kishiya balle yarinya karama akaita cikin guzamay mata haka ?
Mama tace mu a kauye ai hakan ba komai bane gare mu amma duk da haka Rahama tayi kankanta kwarai agidan nan.
Da mama zata dawo sakon zannuwan gado da sauran kayan aiki dasu kudi anty ta bayar akawo na shagalin buki na wanda baifi wata biyu ba ayi yanzu.
Harda yan din kuna kala biyar da sauran abubuwa duk ta hado min tace aba Inna hakkuri saboda jikin ta bata samun zuwa bukin .
Amma idan ta samu lafiya zata zo taga dakina daga baya insha Allahu.
Mama tace kice wanan tafiyan na Rahama ne nayi ai taso ta biyoni sosai amma nasan mahaifinta ba zai yarda ba shiyasa na bata hakkuri.
Da mama ta dawo daga birni sai washe gari muka shiga taron ta don da dare ta iso garin.
Ai nan ta baje muna sakon anty na muna kallo wani abin ma ni ban san yadda za, ai amfani dashi ba agidan.
Ban san lokacin da na dunkule na fara kuka ba da kyat mama ta lalashe ni na wanke fuska na.
Sai da naje gida nake labartawa Inna ta abinda ya faru ta rike baki cikin mamaki tana cewa kai wanan boyar Allah ni ban san abinda zan saka mata dashi ba a duniyan nan ?
Mama ko sai gori take sake muna da habaici wai rana bata karya sai dai uwar diya tai kunya.
Daga uwar har uban sai kudi ake ci amma ko roba ba asai wa yarinya ba na aure .
Su dai gasu gani wai an bizzine tsohuwa da ranta suga yadda za afita kunya duk tallan da nayi Inna ta kasa saye min wani abin kwarai.
Dama tayi haka ne don ta kure inna don tasan ba, a aje min komai na aure ba a yanzu tunda mun sakakance cewa ni
boko zanyi ba aure ba yanzu.
To yanzu ga aure ya taso suga ta tsiya tasan dai gidan su Inna ba wata tsiya zasu barkata min ba don suma nema sukeyi.
Magana duk yabi gari inna bata aje min komai ba ga aure ya taso ba abin kaiwa gidan miji.
Lokaci ko kamar jira yake sai kara matsowa yake niko sai karatun jerabawa na dake gabana nakeyi kawai.
Ba abinda yai min tsinanen zafi akan maganan mama da diyan ta a gidan mu.
Garbati yasa aka gina min daki mai

Please Login or Register in order to submit comment