Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ashe.
Itakan Nuriya bata da ranan aure a rayuwan ta cewan ta ai aure tauye rayuwane kawai ba incin kai.
Wanan dalilin yasa na daina hurda da ita don naga bata da alaman kintsuwa tare da ita.
Ko tazo bani ma bari ta gan ni har tagaji ta daina zuwa dama don Nafisa muke mutunci yanzu kuma Allah ya rufa mata asiri takama kan ta.
Nan dai al, amarin sadauki ya bunkasa ya zama daya daga cikin miloniyan matasa na kasa masi fada aji yanzu.
Yarana sunyi wayo sai masu kyau dasu kamar diyan turawa gashi bamu faye zama kasan ba ko yaushe muna kasan waje tare dai da iyya muke tafiye tafiyen da mukeyi don kula da yaran mu.
Na kara samun wani ciki shima da namiji na kara haihuwa wanda naso ace diya mace na samu don ina son diya mace a rayuwana sosai.
Sunan shi ya sakawa yaron sai dai duk yafisu zatin girma sosai.
Gaba dayan su yaran kamar su daya idan ka gansu gwanin ban sha, awa dasu ga kula suna samu sosai dani dasu a gurin mahaifin su.
Naso ace na huta hakanan wanan karon amma sai dai ina sai kuma ga wani cikin ya kara samuwa again.
Na tayar da hankalina sosai kan hakan amma babu yadda zanyi dole na hakkura dashi.
Don ya bata ranshi kancewan da nayi zan zubar da cikin har karana yakai gurin mama inda tai min fada sosai dole na hakkura takuma ce na bashi hakkuri.
Na bashi hakkuri amma sai da yai min fada yana cewa wai kila shine banso yasa nake gudun haihuwa dashi yanzu.
Nace haba yaya idan ban son ka wa zanso kawai dai naga abin ne ba hutu ko yaushe daga goyo sai ciki nasone kawai na dan huta har gaba.
Yace basai ki jira gaban ba amma ciki ya zama rai don baki da imani zakice wai a zubar dashi akan may zan biye maki muyi kissan kai a tare.
Nace ni dai ayi hakkuri abar zancen hakana tunda ankai karata gurin mamana har tai min fada.
Ikon Allah wanan haihuwa ban haihu wata bakwai ba kamar sauran sai da cikin ya cika wata tara da dan kwanaki na haifo yar diyata mai kama dani sak.
Yana shigowa dakin ya kalli yarinyar yaji wani sonta ya matukar shiga ran shi sosai a lokaci daya.
Yadauke ta ya rugumay ta ajikin shi yana mai jin dadi a ran shi take ya kira yarinyar da uwata nan nagane sunan mama ke nan yarinyar taci.
Ranan suna aka rada mata hauwa, u suna kiranta Ummi kowa na gidan.
A ran daren suna ne jikin baba ya motsa mai akatafi asibiti dashi amma kafin safe yace ga garin ku.
Allah yasa sadauki yana gari a lokacin don haka yayi sa, a a hannun shi kamar yadda baba ke da gurin ya cika dan shi na gari.
Allah ya karba mai ya rasu a gaban shi cikin yadda ake son ko wani musulmi ya cika da kyau da imani.
Sai bayan sun yi sallah asuba ne suka fara sanar da yan uwa da abokan arziki rasuwan baba din.
Ya bugo waya ya sanar da mu ni da kaina najamu zuwa gida hankalin mu a tashe don rashin da akai muna.
Take gida ya cika fam da yan uwa nesa dana kusa an kawar da baba akai zaman kwana uku kowa ya watse.
Baba ya tafi ya bar iyalin shi a cikin rashin jittuwa a tsakanin su yadda yaso.
Sai bayan sati biyu ne aiko yaya Ahmed ya tayar da kayan baya akan a raba gado abashi nasa.
Haka ya kara tayar wa kowa da hankali sosai lokacin sadauki baya gari amma an buga mai waya yace abari yazo.
Amma yaya Ahmed da matar shi ta zugo shi yace bai san wanan ba dole araba ai sadauki ba girmuwar shi yayi ba.
Haka ne ya tunzura ran sadauki yace ana iya rabawa amma banda gida da gona don baba ya sayar mai dagona tun yana da rai yace sagir ya kai takardun kowa ya gani.
Ai kuma sai zance ya koma wani sabon tashin hankali don dama gidan yakewa da gonan a raba a bashi ya sayar sai ga zance ya koma kasa kuma.
Ya buga kasa yace sam shi bai san zancen baba ya sayar da gona ga wani sadauki can ba.
Mummy tafito tace anyi haka kuwa don ita tasan da zancen don ita sheda ce a hakan.
Ya sayar ya gina masalllatai da kudin shi yayi gyaran wasu kuma duk da kudin.
Babane hanata ya ce kada ta fadawa kowa sai bayan ranshi za, a sani don haka kowa yaje ya nemi takansa.
Sai na kashe sadauki wallahi yaya za, ace yafi mu kudi yafi mu komai kamar shi kadai ne kawai dan da aka haifa a gidan nan.
Ya zare kamar wani sabon mahaukaci yana cewa idona idon wanan mugun guy din sai na halakashi wallahi.
Hankalin maji ya tashi sosai yadda taga Ahmed din ya zare masu a lokaci daya ya koma kamar wani mara hankali dashi.
Wayana ta kira take ce min naiwa masu gadin gidan mu magana su kula ga abinda Ahmed yace zaiyi kada yazo bai samu sadauki ba yaiwa jikokin ta illa.
Nima hankalina ya tashi danaji nace a kidimay mama kefa dake gidan kada fa yazo yai maku wani illa a gidan.
Mama tace Fatima niku nakejiwa dai don naku yafi damuwa na sosai wallahi hankalina a tashe yake Fatima da kalamin yaron nan gashi na kira mijin ki ban samu layin shi ba.
Nace mama bazaki samay shi ba don suna meeting ne da tun safe da suka shiga yace sai uku zasu fito.
Bayan munyi sallama nima sai hankalina ya tashi don nasan yaya Ahmed mugu ne zai iya yi komai daya fada.
Nakira sadauki na samay shi a waya nake fada mai abinda yaya Ahmed yace akan shi din
Dariya yayi yace kai Ahmed din may can insha Allahu bazai iya komai ba da yardan Allah.
Duk da haka ya kafa matakan tsaro sosai a kan mu ganin hankalina dana mama yai matukar tashi sosai a gidan.
Ranan da sadauki ya shigo gari ya tafi gida gurin mama take kara fada mai yadda akayi da Ahmed din yace mama
Kwantar da hankalin ki Ahmed ba abinda zai min naso ya bari mu rabu lafiya dashi kamar yadda nake fatan mu rabu lafiya da kowa.
Haka dai ya kwantar mata da hankalin ta sosai har ta aminta da zuciyar ta sosai.
Bayan tafiyan shi da kwana biyu yara zasu tafi makaranta mai daukan su yazo har sun fara hanyar fita na ji zuciyata tana halbamin.
Namike tare da cewa Nura direba ya bari nazo mu tafi tare mu sauke su a school din.
Tun bayan fitowan mu a layin mu ne na hankalta da wata mota dake bin mu a baya na fadawa Nura driver abindana gani waya muka bugawa security din mu suka biyo mu a baya aiko mu motar kebi da gakiya don muna shiga titin da zai kai makarantan motar tasha gaban mu suka take mu da bindiga wai mu fito.
Muna kokarin fitowa ne Allah ya takaita muna wahalan mu security din suka iso gurin aka fara musayan wuta dasu na tara yarana a jiki na kwanta masu sai rokon Allah nake yakawo muna agaji.
Allah ya rufa muna asiri yansanda suka kawo muna agaji nan Allah yabada sa, a aka kama wasu daga cikin mutanen.
Mu kuma aka tafi damu gida cikin tsaro ai kafin wani lokaci labari ya karade gari.
Sadauki yana samun labari hankalin shi yai matukar tashi sosai duk da yaya bashar ya kwantar mai da hankalin shi amma bai hanashi dawowa gida ba hankali a tashe.
Nan ya sa na shirya yara yana fadin garin zai bari damu baki daya duk yadda naso ya barmu bai yarda ba tare muka bar garin dashi muka kwasa har da Iyya sai Abuja.
Sai bayan tafiyan mu ne muka samu labarin ashe yaya Ahmed ne ya turo mutanen nan suyi kidnapping din mu
Ran yaya sadauki yai marukar baci bai san kiyayyan ya kai haka ba har ga iyalinshi sai da wannan abin ya faru akan iyalin shi.
Kuma wai dan uwanshi najini uba daya yasa ai mashi wanan irin aika aikan haka.
Da Ahmed zaice ya bashi duk abinda yake dashi da zaifi mashi sauki akan dauke mai iyalan shi daya saka ayi ko kuma shi yai mai wani abin can ba yaran shi da matar shi ba.
Anso a daure Ahmed amma yaya sadauki ya hana karshe ma ya bashi kudi masu yawa a matsayin jari a gare shi don yasan talauci ne ya jawo mai wanan batar haka.
Daga wanan lokacin zaman mu ya koma rabi Abuja da anyiwa yara hutu kuma mubar kasan zuwa waje.
Haka rayuwan ya dinga ci gaba iyayena da yan uwan mijina kowa yana moriya daga gare shi har ni da yarana.
Kowa yana alfahari da samun shi an manta da baya abubuwan da suka faru adduan iyayye yayi amfani Allah ya shirya kayan shi ta yadda ba, a zata ba.
Don haka Addua mahaifa take da amfani ga yaran su komai dadewa insha Allahu zamu samu riban adduan iyayyen mu.
Dafatan Allah ya bamu ikon yawaitawa yayan mu addua ta alheri don ganin cigaban rayuwan su a kullun.

Nagode da lokacin da muka bawa junan mu gurin tsayawa karanta wanan guntun labarin dafatan duk wani dan fadakarwan dake ciki zai amfane a gidajen mu da al, umman mu
Ka taimaki wanda ke bukatan taimako koda addua ko da karfin ka don kaima Allah ya taimake ka ta hanyar da baka zata ba watarana.
Sai mun hadu a sabon novel din mu maizuwa insha Allahu da fatan kuji dadin labarin a zukatan ku wanda duk banyiwa daidai ba ta yafe min don Allah.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment