Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba,abi ba ni dole na kafawa mutum ko baiwa Allah dole ko abi.
Ke a dole wai ga yar gwal ba, a tabaki uwar ki ta shigan maki ba kunya ba tsoron Allah.
Inda ma mutum nada wani asalin kwarai ne har zai muna yanga da kyau yo ina kyaun ma yake don dai haske fatan da ake kuri dashi kawai bayan shi din sai may kuma ?
Inna dai bata tanka taba sai ci gaba take da masifan ta tana cewa ni za, a gwadawa rashin mutunci ni da mutunci ya ganni ya gudu.
Idan kace zaka shiga tsabgata wallahi sai inda karfi na ya kare a kan mutum duk da haka kana doso ni da rashi mutunci in kama mutum in mashi dukan tsiya a gidan nan inga uban da zai ramawa mutum.
Mu dai muna daki abin mu muna jin ta tana faman haushi tana neman mai tanka mata ta sauke mai.
Da babu wanda ya tanka mata sai ga lawisa ta dawo da kayan sana, an da mama ta dora mata batai ciniki ba.
Nan mama ta juye fadan kan yar ta tace shiyasa ake ganin daman ku ana maku yadda rai yaso harda sheri.
Ko da yake kubaku iya shiga lungu ai maku juye ai abinda akeso da ku ba a baku kudi.
Mama tana nugin nice mai shiga lungu da maza da sana, ata ana min juye idan anyi lalata dani.
Ban san lokacin da na ce Allah ka isar min ban yafe ba sai Allah ya , , ,
Marin da Inna takaiwa bakinane yasa naja nai shiru ban karasa fadin maganan da nake fadi ba.
Tana cewa kul na sake jin kina jawa babba Allah ya isa sai na fasa bakin nan naki.
Duk wajawo min wanan bake da ban isa na tsayar dake inda naso ba da kin dauki sana,an ki kin tafi wa zai ganki a gida yai maki maganan banza haka.
Kamar nace Inna aiko bani gida mama zata fadi hakan ne a kaina don bayau ta fara fadin hakan ba.
Da dai tagaji da fadan naji tana cewa ai tunda abin haka ne wallahi mu zuba da mutum a gani.
Inna tafito yin alwalan la, asar ne mama take cewa kada ta dibi ruwan randan ta don dashi take son yin wanka don randan ta ba ruwa a cikin sa.
Inna bata saurare ta ba ta duka tana diban ruwa ne ta ji saukan duka a bayan ta daga gurin mama din.
Yaya abin yakai harda duka tace na doke ki ko zaki rama ne mara mutunci kawai.
Ta sake daga hannu zata kai wa Inna duka ina tai cikin ta Allah ya bata sa, a ta kwashe kafan mama tai kasa tim, ta bita ta haye taita dukan ta.
Ga mama babu ko dan buje a jikin ta sai tsiraicin ta da ya baiyana a fili lokacin.
Jin haya niyar sau yasa mukayo waje gaba dayan mu muka shiga ihu don bamu taba gani ba.
Ganin haka su Lawisa suma suka far wa Inna da duka ina ganin haka nai kan lawisa sauran suka biyo ni suna duka Allah yaban sa, a na jefa ta a randan ruwan su saida ya fashe.
Ta samu targade ta yanka wani irin ihu kamar ranta zai fita a lokacin ganin haka Isa ya dauko tabarya yai kan Inna dashi bai kai ga buga mata ba ni rike shi yai baya yafadi kasa shima sai da yaga wani wuta ya gifta mai.
Wani ihu suke kurma wa na neman taimako mama tace shigiya mai karfin doki wace ta san ma diyan ta mugun abu.
Su mama altine da wasu makwabtane suka shigo don jin kururuwan da yai yawa a gidan.
Da kyat aka banbare Inna ajikin mama sai zagi da ashar mama ke faman sakewa aka bata zanin ta, ta daura.
Inna tace sakariya kawai wawiya wacd bata riki darajan ta ba balle na uwargidancin da bai amfana mata komai sai zalunci an fada maki shirushiru tsoro ne dama.
Mutane sai fadi suke asha Lauratu mai yakai wanan taasan haka bayan karfi ba daya ba ?
Gaskiya wanan abin dai kan baiyi dadi ba wallahi yarinyar nan tana maki biyayya yadda ya kamata karami yai wa babba amma sai da yau kika kaita bango.
Makwabta kowa na fadin albarkancin bakin shi abindai kan baiyi dadi ba wallahi don babu wanda bai san halin da gidan mu ke ciki acikin su.
Har da anty Sa,ade sai da tashigo gidan dauke da yarta a hannun ta tajani gefe tana min nasiha yadda ya dace.
Jinya sosai mama tayi a ranan har dare suna daki ita da yaran ta da sukai tangarde tana jiran dawowan baba.
Tun a hanya yan unguwa suka tare baba suka fada mai tare da bashi shawaran ya saka ido ga halin da iyalin shi suke ciki don babh inda akejin wai kishiya don samun guri ta daki kishiyar ta koma wacece bazata kyale ba .
Haka yasa koda baba ya dawo gida bai dauki wani matakin da mama taso ya dauka ba.
Ganin baba bai dauki matakin da taso ba na farwa inna ta da duka ya rama mata ba ita da diyan ta.
Wanan zance yasa har saida Iyayen mama suka ziyarci gidan mu nan suka zauna kowa ya mayar mai da bayanin kan maganan.
Nan dai suka taru suka bawa mama rashin gaskiya yadda ya dace akai masu nasiha da suci gaba da zaman lafiya.
Tun daga wanan ranan mama ta kwashe kayan ta na aiki dake a tsakar gida ta boye kuma wasu ma da kudin sana, ata aka saye su.
Nice nake labartawa anty da mama take anty tabani kudi tace kada na koma gida naje na sayo wa mama duk abinda bata dashi komai da yakamata na aikin mu saida na hado shi kamar wata babba can dani.
Aiko mama tana ganin haka hankalin ts kuma ya tashi ta fara sabon habaici tana fadi sai dai haka dama an samu kayan banza ana amfani dasu.
Take cewa wai na dauki kaina na saka a cikin kishin su ai tasan magani na indai itace.
Wanan kalamin na mama da takance wai tasan magani na kullun na rasa wani maganin me zatai min wai ?
Mu dai bamu biye mata ba haka zaman ya koma na doya da manja a gidan na mu.
Naji dadin zuwan anty Sa, ade a wanan lokacin don ko ba komai ta fitar min da uwata a kunya.

****** ********* ******
Ban san da zancen tafiyan anty ba sai dana dawo daga school nashiga don nagan su.
Sai mama ce kawai na samu a gidan cikin karaji nace mama ina antyna ?
Idona yana gurin da kayan ta suke a dakin mama, murmushi mama tai min tace yar gidan anty ai yau anty ki tai muna na baki.
Dazun mijinta yazo ya dauke ta suka tafi sun koma birni inda suka fi wayo in ma ba don Saade yarinyar kirki bace ina zata iya zaman garin nan har tsawo sati daya haka?
Inda kinga irin daulan gidan iyayyen ta da na mijin ta ai bakyace zata iya ko zama ba anan din.
Duk wanan maganan da mama take bana jin ta don nayi nisa ga tunane ina fadin yanzu shike nan anty ta tafi tabarni zan koma ga turke na mai cabo ke nan na talla.
Gashi dan kwana biyun da nayi bana talla har na dan yi kyau na koma wata wayayiya dani.
Ashe anty tasan zata fi a yau shiyasa jiya tasa na sance kaina tai min wani sabon kitso a kaina duk da wancan na farkon da tai min bai tsufa ba?
Muryan mama ne ya katse ni tana cewa ga sakon nan ta bayar abaki tace kiyi hakkuri idan ta samu hannu na gari zakiga sakon ta.
Dakin ta shiga ta dauki min wasu kaya tufafi ne na anty da na santa dasu na jikin ta, ta bani.
Sai sauran tarkace irin su sarka takalma da gyale da sauran su ta bani nai amfani dasu.
Haka na karbi kayan jikina duk a sabule na juya jiki ba lakka zuwa gidan mu inajin kamar na kurma ihu a lokacin.
Mama tabi bayana da kallon tausayi tana mamakin wanan irin shakuwa dake tsakanina da yarta tun ina karama.
Don itama antyn ta tafi dani a baki tana fadin Allah sarki wallahi mama da mahaifin Rama zai yarda dana wuce da ita kano taje can tayi karatun ta .
Mama tace raba kan ki da zancen yarinyar nan Sa,ade iyayyen ta basu da mutunci don basu san haka ba.
Wanan dalilin yasa taja bakin ta tai shiru ba don ranta yaso ba ta kyale zancen.
Nan na dawo kan sana, ata ban ko tsaya Inna tai min umurni ba na dauki wake na wanke nakai nika da sauran abinda ya dace inyi.
Ganin ina wanke wake yasa mama take cewa yau kuma karya ta kare wa buddari ne za, a koma inda akafi wayo.
Ban dai kulata ba naci gaba da abinda nakeyi don na nasa a raina washe gari bazan shiga makaranta zan zage naiwa Innata sana, a ne don nagane shine kawai rufin asirin mu a gidan.

Na dade a zaune ina kwalliya irin ta mu na yan kauye idan zamu fita nacewa inna na dauki kayan da anty tabani ne na saka.
Tace ba naki bane idan zaki saka sai kin tambaye ni na jawo ledan kayan da tunda nashigo dasu ban bude ba tun jiya sai a lokacin nan.
Na fara budewa naga emvlove a ciki a mike a hankali na bude kudine yan duba a cikin har dubu ashirin sai yar guntuwar takardan da ke ciki.
Da mamaki na dauki kudin na kiraga duba ashirne cif din su sai na dago kai na kalli Innata data kura min ido.
Takardan na bude na fara karantawa ga abinda tace a cikin takardan kamar haka.
Rama na nasan lokacin da zaki samu takardan nan nakai kano kiyi hakkuri ban fada maki yau zan tafi ba don kada ki fasa zuwa makaranta da fatan zakiyi hakkuri ki kula min da kanki.
Ga kudi nan daga ciki nakine kibawa Inna bana son kina wanan tallan a rayuwa na idan sun kare insha Allahu zakiga sakona.
Kada kiyi wasa da karatun ki kidage sosai don watarana ki samu ki taimakawa Innan ki don tana bukatan taimakon ki sosai saboda halin da kuke ciki a gidan ku.
Dafatan zaki fahinci abinda nake nufi naki antyn ki Saade sa, adu rano.
Kifewa nayi ina kuka a gurin wanda ban san dalilin yin kukan nawa ba a lokacin ko na may nenw?
Sai da nayi mai isata na fita na wanke fuskana na dawo na shirya na fice daga gidan dauke da roban tallan wara na.
Ina fitowa mutane suka fara tambayana ko nayi tafiya ne kwana biyu sun daina ganina a garin.
Ba wani cikakken amsa da nake basu sai kawai ina nan boko nake zuwa shiyasa.
Saura kadan ya rage min a roba don haka nai haraman komawa gida don nasan yanzu diban ruwa yana can yana jirana ko karfe nawa zan kai a wajen tallan.
Ina tafe bugujan buganjan dani a cikin sauri naji muryan dattawan nan dake zama a gindin cidiyar uguwar mu suna fadin ke mai wara kawo wara mu dan taba.
Ban ja ba na juya zuwa gurin su inda suke a zaune tare da durkusawa na fara gaida su tare da aje roban a wara a gaban su.
Nawa nawa ne dayan ya tambaya nace mai biyar ashirin yake yace to kiba kowa na ashirin anan.
Na shiga saka masu na ashirin a leda ina mika masu daya bayan daya suke karba.
Don ina gurin bai sa su fasa hiran da sukeyi ba na matan su sai faman dariya suke a tsakanin su.
Muryan dayan naji yana cewa ka samu daidai wanan ka saka a gida ai damana da sanyin bana lafiya ga mutum.
Sai suka fashe da wani irin dariya fuska na a daure daidai lokacin da na gama mika masu a sanyaye nake cewa na gama zan tafi.
Dari biyu ya miko min ina kokarin banye kudi na bashi canji naji yana cewa a, a ki bar canji kawai ki tafi dashi ai gobe ma ma hadu ko ?
Cikin sanyin murya nake cewa Inna ta ta hanani rike kudin maza a guri na don haka ga canjin ka na aje mai a gaban shi ashirin uku na mike tare da daukan roban tallah na bar gurin cike da jin takaicin su.
Ina ba da baya naji daya na fadin ga yar gutsun uwa arziki na binki kina ki dan shashanci kawai.
Daya ce bata san arziki bane in bashi ba aiko yaro mara hakori yasan sa, a a yanzu balle ita da tafito cikin rana nema.
Mai kudin yace ku kyale ta in kunga haka tarbiyan da uwarta tai matane take bi dagani danya ce shatab.
Sai duk suka sa dariya a lokaci daya dayan yace yaya dai mutumina sai naga kamar fa ka kyasa Allah ?
Yace ko na kyasa may wanan yar shilar zatayi dani da hurhura na har a mugun guri.
Cab di ai sai dai idan ka tsuke aljihunka ne za, ace ba, ayi dakai zamanin nan amma ina wani hurhura can kawai watarana sai ka nema ka rasa kana kwasan kurciya gurin yar yarinya ka huta da wa yan nan tsufin kwaman kwana biyu.
Ayi haka ga yara ina zan kai wanan yar shilan cikin wanan dabin iyalin nawa ai sai su farwa yar mutane tun dai ban ce ma kaciya ba ?
Aff ina ruwan ka da wanan mace ce ma fa ita kada kaji mamakin ka shigo gida wataran kasamu ta zage tana masifa a kan ka.
Dariya sosai suka kwashe dashii har nai nisa ina jin sautin dariyan su na shige gidan mu abina tafe nake a cikiin sa, a na akoda yaushe haka Allah yai min baiwa ni.
Abinci na dan tsakura na kwabe kaya na tafi diban ruwa marance da nakeyi.
Sabbin robobin da na sayowa inna ta saida na cika su taf da ruwa na kawo marafan su na rufe su akofan mu.
Shine yaba mama haushi sosai tace wai karama dani na iya bakin makirci kamar wata tsohuwar mace.
Da baba ya dawo ina ta tare shi da zance wai bata san inda muke samun kudi ba da inna na yanzu ya duba yaga irin kayan da muka saye ?
Idan ba dai maza na fara bi ba ina kawowa Inna ta kudi muna shagalin mu a daki ba wanda yasani.?
Ita ba don komai tai magana ba don zama tare ne kada wani abu yazo ya samay ni ace tana gidan ta sa ido.
Baba ya hasala da zancen sai gashi ya daga labulen dakin yana cewa ke Asiya kki fada min gaskiya gidan uban wa kuke samun kudin da kuuke wanan bushashan haka agidan nan keda yar ki ?
Shiru inna tayi har saida ya kara maimaita tambayan shi gareta ba dake nake magana ba ne wai ko bakiji may nace bane ?
Iinna tace bada amsa baida amfani don ko na fada ba yarda zakayi ba tun da an fada ma sheri.
Ni dai nasan kulba dade kulba jima Allah yana tare da mai gaskiya komai dadewa kuwa.
Yace to yayi kyau ya juya ya fita da daren nan Inna ta shiga gidan mama altine da kudin da anty tabani na karatuna.
Bayan sun gaisa tai mata godiya take cewa mai kuli nazo gurin ki ne don ki bani shawara akan kudin nan.
Kinga kudi bazasu aju ba don haka nazo neman shawaran ki da na aje kudin nan a guri na sai naga kamar na baki su ki sayowa yarinyar nan kayan tari ki barsu anan gurin ki kamar zaifi.
Don ko na barsu ban san ranan da zan sake samun irin su ba haka sai ma mu dinga zara da guda da guda har mu kashe su ga banza.
Idan kuma yaya ta gane karshe ma rance su zatayi tace zata juya muna don ni ko malam ban son yasan da zancen kudin nan yanzu.
Mama Altine tace kin kawo shawara mai kyau Asiya nima sai da nai tunanen haka tun farko.
Amma sai na bari naga hankalinki da fun tunii kike wanan dabara da tallan yar nan da yanzu ansan abinda aka aje mata ai.
Amma kin bari ana maki wayo kullun ana karbewa baku aje komai ba sai bakin wahala ke a wahalce ita yarinyar a wahalce.
Inna tace to ita yarinyar takice indan anyi maganan haka sai tace ita karatun boko zatayi mai zurfi irin na anty ta.
To ke kyabi tana ta ballantana a kauyen nan yaushe karatun bokon ya mace ke zurfi suma ainaga sun jima suna karatun don tana son abin.
Yanzu da miji yazo zakiga afitar da ita karatun ya tsaya ke nan cak ba ci gaba sai wahalan aure ya biyo baya.
Ai mai kulli mukan kauye ana kwarar mu wallahi kai wahalaa dan ka a wahala shine rayuwan mu kawai.
Tun wanan lokacin Inna take daukan dan riban da muka samu ga tallah bayan ta cire na amfanin mu take kaiwa mama altine ba tare da sanin kowa ba.
Zancen da mama tayi na zuga baba ina samo kudi ba asan inda nake fitowa dashi bane yasa aka kafa min doka akan talla sau daya a wuni.
Haka yasa har na mayar da hankali ga karatuna daga baya ma sai na kirkiro sana, ata a kofan gidan mu anan nake suyan warana shima din nan a take na sayar da abina na shigo gida.
Hakan kuma sai ya jawo sabon fitina gurin mama again take cewa wai maza nake tarawa a kofan gidan mu ana abinda bai dace ba.
Shima baba yai fadan shi har yagaji baida yadda zaiyi ya hanani talla ne da yahana ni yadda ya sha zugi gurin mama din.
Ina aji hudu akai min jumping a school din mu don kokarina don munyi debet na sa school din mu tayi nasara na samu wanan daukakan haka.
Nan ma mama tace ai inba ina tare da malaiman ba babu yadda za, ai min hakan ni kadai don banfi kowa a school din ba.
Nan ma baba ya hau ya zauna akan zance haka ya jawo mama tasawa karatun nawa kahon zuka sai da a ka dakatar dani daga karatun boko na ga baki daya hankalinta ya kwanta.
Tsayawa fadin irin bakin cikin da naji alokacin bata bakine gurin fada.
A makarantan mu sun samu labarin babana ya fitar dani daga makaranta haka yasa suka tausaya min sukazo har gida suka samay shi kan zancen.
Amma yace suyi hakkuri abar zancen da suka matsa mai yace a bari sai yayi shawara tukun.
Badakowa zaiyi shawara ba nasan da mamacd idon itace kuma babu yi ke nan na sani.
Daya tunkare ta da zancen cewa malam mu ne sukazo akan zancen dakatar dani daga kararu sai cewa mama tayi dama may na fada maka ?
Tare take dasu yanzu sunga basu samun ganin ta su kwakwaleta shine suka biyo sawun ta har gida.
Nan baba ya kara turjewa bazan koma karatu ba idan mana samu miji aure zai min kowa ya huta.
Jifa ga Lawisa ga Rukaiyya da Naja wai amma nice baba ke maganan aure na.
Ganin za, a cuta min a gida yasa shugaban makarantar kai karan babana a gidan maigari.
Kan zasu cutawa rayuwana kasancewa ta yarinya mai kwazo ga karatu ya kamata ace ko dai secondry din ne na gama ai.
Da kyat baba ya yarda koshi sai da maigari yai mai jan ido ya yarda don yasan idan yadawo gida akwai matsala tsakanin shi da mama idan taji zan karasa karatuna a shekaran nan.
Haka kuwa akayi don ranan ba karamin tashin hankali akayi ba tsakanin baba da mama.
Take cewa ai dama har dashi cikin cin kudin da mazan dake lalata dani suke bani.
Idan bashi ba don may zaice sai na karasa karatuna may ye amfanin karatun diya mace na boko da za, a kare shi a gidan miji.
Tana kurin tana karatun boko watafi kyau da za, a nace kan sai nayi boko nakai wasu can daban
Ni dai tunda naji baba yace na shirya gobe na koma makaranta nake cikin farin ciki da zumudi don ina gani kila ina da rabo ne a duniya.
Washe gari tun da safe na bar gidan duk da na saba idan zan tafi sai na sallami kowa na gidan kafin na fita.
Yau ma dana shirya munyi sallama da inna na nufi kofan mama tun ban karaso ba tana hangoni take cewa za, a yawon tazubar din ko akuyan daure ta samu saki.
Duniya ce dai ayi ta a sannu don maza ba abin goyo bane da sun gama yayin ka su ka hango wata kai kuma ka tashi aiki ke nan.
Ni dai ban biye taba nace mama ni na tafi kafin ma naji amsan da zata bani har na fice daga gidan ko.
A kofa na hadu da babana da zai shigo gida na dan rabe gefe nai mashi ina kwana yabini da harara yana cewa har zaki tafi ke nan ?
Nace eh baba yace Rahama ki kula da rayuwan ki kada ki ja min abin kunya a garin nan.
Duk dai har yau babu wanda ya taba kawo min karan ki na assha amma dai kuma maganan maman ku abin dubawa ne.
Don diya mace ba, a saka mata ido tayi yadda take so dole sai da tsawatawa akai.
Nace nagode baba insha Allahu zan fake na tafi ina tunanen halin baba idan mama bata kusa zakaji ya dan sanyaya ma al, amarin mu .
Amma da zaran yaga idon mama damu da makiyan shi duk daya muke gare shi kamar zai yanka mu da ran mu.
Bani ba har yan kanne na biyu hakan ya shafa don dai kawai su maza ne basu zama gida su.
Ina isa makaran ta ban tsaya ba sai office din malam Mudi don nasan shine kadai zai iya min wanan kokarin.
Na samay shi yana shirin fita na duka nagaida shi cikin ladabi nake cewa kuma malam nazo ne nai ma godiya don nasan kaine da wanan kokarin.
Yace hakane Rahama don haka kema ki kula da rayuwan ki don ban san dalilin yin hakan ba ga mahaifinki.
Ko da yake mun samu labarin cewa takurawan kishiyar mahaifiyan ki ne akan ku ya shafe ki.
Ki kula ki mayar da hankalin ki wata rana sai labari idan kin dage Allah zai kawo maki mafita da yardan ubangiji.
Nai mashi godiya tare da sallama na koma class sai sheri yan uwana dalibai suke min wai ta fudu ta dawo.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, ,


IDAN KIN BIYA KI KA BAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH YAR UWA, , , ,


A haka na juya zuwa cikin gida jiki a sabule min ina dauke da ledan da suka bani a hannu na.
Har lokacin Inna suna gurin zaune da babana nazo na wuce su zuwa cikin dakin

Please Login or Register in order to submit comment