Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

girma da fadi yadda zai isheni aka kewaye shiyan daban cikin na iyalin shi can gefe daya an shafa farar kasa yaji sai kyali yakeyi.
Haka ya kara bankantawa iyalin shi rai sosai har suka so tayar da hankalin su.
Amma da ya basu dan wani abu suma suyi gyara sai baki ya mutu murus kowa ta shiga sha, anin gaban ta da diyan ta amma kishin yana nan daram a ran su.
Duk inda yabi sai ba, a ake mai na ya fado gari ya zarta maza zai bare yarinyar dalleliya a ledan ta sai ya washe baki cikin jin dadi yana dariya.
Mama ko sai auki fadawa mutane karya da gaskiya takeyi akan zancen bukin tana zunden inna ta.
Inna ta duk tabi ta ramay sai dan wuya daga ita sai uwar dakin ta mama altine suke shirin bukin sai yan uwan su tsiraru da sukaji suka gani.
Ko su ba wai sun san shirin da Inna da mama altine sukayi min bane haka ake tafiyan a dunkule.
Gaba daya daga inna har baba babu wani mai kwanciyan hankali dama ma inna dake nuna halin ko in kula da bukin.
Idan ka cire mama da yaran ta wanda su ko a kwalar rigan su bai shafe su ba.
Ta dai zuga shi ya zugu yanzu kuma ta saka mai ido yaji kunya dan kudin sadakina da aka kawo dashi ne yake kokarin sayen komai.
Na dan gadon katakon da za, a sai min ma ya gagara daga karshe ganin haka tasa inna dabaran cewa yaba mama altine kudin ta shiga birni ko na hannu ne ta sayo min.
Tayi hakane don idan kudin ya shiga hannun su sai su san dabara mama altine ne ce ta koya mata wannan dabaran.
Baiki shawaran Inna ba tamika masu dan abinda ya saura takaiwa mama altine ta shirya sai birni da kudin daga karshe anty ce ta cika aka sayi min saitin gado da dan wardrove da katifa har da karin tarkace.
Wanan matar ba abinda zamuce mata sai dai Allah ya bata lafiya ya shirya mata zurian ta da albarkan sa kawai.
Ganin babu komai a dakin inna ta yasa mama ta samu baba da zancen da yamma bayan ya dawo gida take cewa.
Yanzu malam kana ganin haka zaku kai yarinyar na aure babban gida irin haka babu komai da uwarta ta tana da mata na fita kunya kaima sai nake ganin a furin ka hakan ne ?
Baba da yanzu ya fahinci mama so take taga wallen shi kuma tasan sirin abin sai ya boye mata ba su mama kudin sadakin da yayi yace anyi auren ne ko kikaga uwarta ta kaita hakana ?
Haka yasa taji haushi taja bakin ta ta tsuke ta bar zancen sai ido tana cewa ni dama taimakon ku naso nayi ko mu tafi gida tumba dillaliya adan samu abinda aka tsintar mata gurin ta in yaso bayan bukin abinda aka samu sai abata kudin ta.
Baba yace ko tabarma Allah ya hore mata daga gare ni sai na kaita dashi .
Yafice abin shi gidan ya barta nan tana mashi dariyar mumuke ta baya tana an daiji kunya wallahi anyi shigewa ai ciki amma ba, a iya fitar da yarinya kunya.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE , ,

IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA KINCI AMANAN ALKAWARI DON ALLAH ZAI TAMBAYE KI HAKKINA NAYI HAKA A KAN KI DON SAI DA NA ROKE KI KADA KI FITAR MIN DA NOVEL DINA DON ONLINE NOVEL NE BA NA SHAGO BANE WANNAN DA FATAN ZAMU JI TSORON GAMUWAR MU DA UBANGIJIN MU ALLAH RANAN GOBE KIYAMA AMANA YAR UWA IDAN BAKI IYA RIKE AMANA KIYI MAGANA NA BAKI KUDIN KI DON BA ZAN YAFEWA HAKAN BA
MUJI TSORON ALLAH KADA MU BARI SHEDAN YA RUDI ZUKATAN MU PLEASE, , , ,


Haka rayuwan zaman sabon gurina ya kasance min agidan mijina kuma babana uwayen gidana da sukai jika dani.
Manyan diyan shi maza ko matan su sun kusa haihuwa na don haka mazan nake kiran su da yaya matan su da anty.
Haka ya jawo min saukin zama gidan don sun kula ban zo masu da fitsara ba ko kadan.
Bani kuma kyashin taya mutum aiki koda na sana, an shi tare dani za, ayi shi har a gama kuma da zuciya daya.
Wanan dalilin nee yajawo min sasauci sosai a gaare su gashi zan sha aiki idan an bani naci bana ci don ban saba da irin ciye ciye haka ba barkatai.
Wankin kayan Alhaji daya cire kafin ya tashi na kwasa na wanke sai dai ya sake wasu wanka
kuma ya zama kullun sabanin da da sau daya ko sau biyu zaiyi wanka a sati.
Ga maclean da brushe da yakeyi akai akai yanzu yake wanke baki dashi wanda na kula shi kan shi alhajin zuwa yanzu yana jin dadin sauyin rayuwan da ya samu.
Don ko wa yagan shi cikin sati dayan da nayi a gidan yasan ya samu sauyi sosai a rayuwan shi.
Don nakan ji matan shi suna mashi ba, a wai auren yarinya yasa shi ya sauya ga abinda basu san shi dashi ba a baya.
Sai ya basu amsa da nata sallon ke nan ke ai baki min ba a lokacin ki dana sauya din tun can.
Ranan da na cika sati daya ne agidan har lokacin ba wani abinda ya taba shiga tsakani da shi ban maga alaman hakan ba daga gare shi.
Ina kasa ya na saman gado kwance da ya kwanta kuma sai barci mai nauyi ya dauke shi sai safe.
Amma a gurin mutane suna ganin akwai abinda ke shiga tsakani na dashi a cikin dare don nakan ji sabuwa na cewa dashi ya daiyi a hankali kada ya takura karfin shi kan karaman yarinya yaje yajawa kan shi matsala kuma ?
Dariya yakan yi mata yace ai yafi son haka don lokacin ta ne abar ta tayi nata zamanin.
Sauran matan ba ruwan su da sha, ani na sai girmamawa amma sabuwa kan kullun sai tayi kokarin sake min magana a tsakar gida wanda zai bata min rai.
A banza don wani zancen ma ban san wai dani takeyi ba har ta kare haukan ta.
Idan ina zaune wani sain nakan ce ashe haka shine aure ba takura ba matsi ba tsangwama irin na mama a gidan mu ?
Gashi duk Alhaji zai shigo sai ya dan sayo min dan abin tabawa watarana ma har kayan shayi da biscuit da su sweet zai bayar akawo min .
Haka yasa na sake jikina sosai dasu wani sain har yar hira mukan yi dashi kafin yai barci sai dai hiran tamu nakan ga yana dariya sosai idan ina shirmay na.
Ranan ya dawo daga kasuwa ya tara mu a dakin mama Hausi uwar gidan shi kusan nice ta karshen shigowa dakin inda suke zaune.
Ina shigowa na samu guri na durkusa tare da gaida su gaba dayan su suka amsa min ina nan dai durkushe sai cewa mama tayi.
A, a Amarya samu guri mana ki zauna ai ina ganin magana Alhaji zaiyi da mu.
Nace mama har dani ?
Tace kai amarya ke ba matar shi bane yanzu har da ke mana.
Shi dai murmushi yayi kawai yana sauraren mu can bayan mama Hausi na koma na takure kamar uwata.
Can dai yai gyaran murya alaman zai fara magana ke nan a lokacin don haka naga kowan su ta natsu.
Yace to Alhamdullahi yau dai amarya ta gama satin ta daya kamar yadda sharia ya tana da.
Don haka yau ne zan koma dakin wace keda girki a cikin ku don haka ina rokon alfarma gurin ku.
Wanan yarinyar da Allah ya kaddari zaman ta a cikin mu da kuji tsoron Allah ku rike ta amana kamar yar cikin ku.
Yar cikin mu kuma Alhaji kishiya ce zan rike kamar yar cikina ta kwana da kai in kwana da kai kuma in rike ta kamar ya ta ?
Wanan maganan baiyi ba gaskiya ka dai sake wani maganan inji sabuwa dake magana a hasale a lokacin.
Murmushi yayi yace sabuwa ke nan ba laifi yadda kika dauke ta a tafi a haka sai dai saukin abin Allah yasa bake kadai nake aure ba.
Kuma bake ce uwar gidan gidan nan ba kinga ashe ba wani matsala ga hakan.
Ita Rahama har wani kishi ta sani a yanzu bayan daukan ku uwayen ta da takeyi tana maku bauta may kuma kike so a gare ta.
Eh yanzu kan hakane a/a idan ta goge ai babu shegu nan gaba kamar mu, balle yadda naga kana rawan kafa haka a kan ta wai kai ka samu yar jikan ka ka saka a daki kana abinda bai dace ba da ita.
Haba sabuwa wai may yasa baki da hakkuri ne ke inji mama Kulu matar shi ta biyu.
Yai murmushi tare da cewa ai ba rashin hakkuri bane gani takeyi abinda tazo gidan a lokacin tana maku rashin kunya shine itama yar mutane tazo dashi zatai maku.
Sai dai ki sani alama ya nuna tarbiya ba daya ba wallahi don ke ko kwana ba, ayi ba kika fara sakani ga fitina.
Amma yanzu ki duba karamar yarinya tasan daraja na tasan naku hakama na iyalina baki daya.
Au to kana nufin ta fini ke nan yanzu maji magana ai gara da ka fito fili ka fada min kowa yaji.
To bari kaji Alhaji wallahi duk ranan da yarinyar nan tai gigin shiga harka na sai dai uwarta ta haifi wata don ko ban halaka ta ba zaka dawo ka samu ankaita jiya gidan su.
Yace ke ko da kin kwana a gadirom rana wallahi da karshen zaman ki gidan nan yazo sabuwa da kinyi nadama mara adadi a rayuwan ki.
Yace naga abin naki ba wasa bane yanzu wallahi duk ranan da kikai gigin taba lafiyan yar mutane sai na lahira yafiki jin dadi a garin nan.
Lalai ma ba, ayi ba yanzu aka soma ke nan don kayi dandane haukace ka zauce kamar wanda bai taba jin dadin bujen mata ba ko ?
Yai murmushi yace kaiyya a fili tare da girgiza kan shi yace ashe kin gane wani bujen yafi wani buje ke nan.
Ranta yai matukar baci bata karasa ba taji yace dama abinda yasa na tara ku nan shiine ke hausi ke ce babba ke zan roka alfarma don Allah.
Ina son yarinyar nan ku dauke mata nauyin girki a gidan nan don kunga karfin ta bai gama kaiwa ba don Allah a dan sahirta mata wanan aikin har ta dan kara tasawa nan gaba idan Allah ya ce.
Cabdijam ba ta iya aiki amma tana iya shigewa da kai daki tai shiru har safe ko ?
Kai sabuwa inji mama kulu tace waban bai dace ba gaskiya shi fa ke da gidan shi balle ma wanan yaushe zata iya tuka tuwon gidan nan haka ?
Ai dama nasan duk da hadin kan ku don ai min bakin ciki kuka hada baki akawo ta gidan nan idan hakane bazatayi girki ba sai dai nima na dinga yi ni da yarana kawai wallahi.
Isan kinyi hakan ma daidai ne inji Alhajin amma ki sani cikin ki tayi don su nan duk suna da sarakai da zasi girka masu ba sai sunyi ba kece mai yara kanana da yawa kuma.
Tace koma maye na dai ji muddin wanan yar mussan da ka kwaso baitai girki ba nima bazan yi ba wallahi yace har da shan wallahii tace eh na sha.
Mama hausi ta bude baki zatai magana ya dakatar da ita yace Hausatu kada kice komai hakan ma yafi min komai dadi daga yau kowa ta girka nata da diyan ta ita kuma Rahama ta girka wanda zataci can shiyan ta.
Dama ba yau ba kike min korafin sai nasa sarakaina suna girkin gidan nan naki biye maki amma yanzu tunda haka kike so hakan yai min dadi wallahi.
Sai dai kada ki manta ba leken tallen kowa ba kuma wani zancen na wance yafi nawa na kashe wanan korafin a gidan nan.
Yarinyar na kuma ba ruwan ki da ita ko irin habaicin da nake ji kinawa yar mutane kada na kara jin shi a gidan nan.
Idan ba haka ba wallahii rai zai baci don haka ke Kulu da hausi ga amanan wanan yarinyar gare ku da diyan ku na danka maku don Allah ku tayani bata tarbiya yadda ya dace.
Sukace insha Allahu Alhaji mu yarinyar nan bata tsare muna komai ba wallahi har yaran mu tunda tasan darajan mu.
Ko yaran nan suka dawo kasuwa har kofan su takee binsu tai masu sannu da kasuwa yaran su kuma tana haba haba dasu .
To yaron da yasan haka may zakace akan shi kuma sai fatan alheri yadda muma muka haifa itama Allah ya bata nata tasaka a cikin mu ba shi ke nan ba.
Yace nako gode dama nasan bazaku ki duk wani abinda na koso ba gidan nan indai har alheri ne da jin dadi na don haka Allah yai maku albarka suka ce amin a lokaci daya.
Yace ke kuma Rahama tarbiyan nan da iyayyen ki sukai maki ina son kici gaba dashi don shine tubalin zaman ki gidan nan.
Can sabuwa tace muma da ba a saka muna ba Allah yai muna shi sannan yaya zancen namu kayan dakin daka saya mata.
Cikin mamaki yace kayan daki kuma nine ma na saya mata kayan dakin nata ke nan.
Tace idan ba kai ka saya mata ba uban waya basu kudin sayen wanan kayan haka giredi masu kyau ?
Yace toni wallahi ko ku yarda ko kada ku yarda ban san komai ba akan wanan zancen.
Ita bata da mahaifa ne da zasuyi mata ban san lokacin da nace nikan anty na ta birni ce tai min komai ba wani ba.
Yace to kinji tai wani irin murguda baki tace haka dai akace kawai amma wata anty gare ta na birni da zatai mata wanan.
Yace to yanzu dai kowa yaji kowa ya tsaya a matsayin shi babba ya rike girman shi karami ma ya rike nashi.
Yace ku tashi ku tafi na gama magana na ni ban son wani abu kuma ya biyo baya.
Bayan fitan su sai ni ban fice daga dakin ba mama tace Rahama tashi zuwa dakin ki kinji.
Nace mama ni anan zan kwana tsoro nake ji ni daya a dakin nan kada sabuwa ta kashe ni.
Subbahanallahi inji su suna hada baki ita da mijin ta yace kin gani ko ta riga da ta tsorata a gidan nan da sabuwa.
Mama hausi tace kinga tashi na sa zuwaira ta tayaki kwana a dakin naki ba shi ke nan ba.
Daga ranan muka fara kwana ni da zuwaira a dakina kafin mu kwanta mukan yi hira na ta karanta muna labarai a littatafai.
Idan nace ina da wani matsala kuma nai karya girkin abinda zanci ma sai na so don idan su mama sunyi nasu suna saka min wani lokaci naci wani sain kuma nace na koshi.
Gashi ban gajiya gurin kama masu aiyukan su tun suna hanawa har sun gaji sun kyale ni ina yi da zuciya daya don yadda uwa da yar ta suke haka nake dasu su biyun.
Idan girki ya zo kaina a dadafe cikin takura nakeyin shi don Alhaji kan min nauyi a dakina har yanzu na kasa sake jikina dashi.
Sai ma kwana da zuwaira yafi min ace shine zai kwana a dakin duk da ba komai yake min ba sai lalashi da ban hakkuri wanda ni ban fahinci na maye ba.
Nayi kyau dani haskena yafito har dan kiba na kara gani shar fes dani idan kin gan ni.
Har kirjina dake a shafe sun fara tasowa yanzu sai dai duk wanan dadin da nake ci hankalina yana gurin Innata ko yaushe don yanzu ban san wake dibar mata ruwa ba wake mata talla wake mata aiki don kanni na duk yan maza ne.
Kaunata mace yar karama ce sosai ita aka yaye ba a haifi wani ba bayan ta ko may yasa inna bata kara haihuwa ba oho ?
Sallaman wani yaro ne a kofana rike da dakwalen kaji guda biyu a hannun shi sai kayan miya a wani leda mai yawa yace Alhaji ne yace ya kawo min.
Na karba yaron zai tafi nake cewa ya tsaya nazo na shiga daki na dauko mai biscuit na bashi har ya fara tafiya yace.
Amarya Alhaji ko na tsaya na taya ki gyaran kajin ?
Nace to shi ke nan dauki kaje a yanka bari na sa ruwan zafi kafin ka dawo ya juya dasu yafita.
Daidai lokacin da sabuwa tafito daga daki yaran ta sun fada mata an kawo kaji a sashe na yanzu sai ko ga yaron tafe dasu za, a yanka.
Tabi kajin da kallo har yaron ya fice daga gidan tanisa tace hum, umm ashe akwaita ke nan ?
Tare da yaron muka gyara ya kama min nayanka na zauka na shuga jajagen kayan miya kafin wani lokaci har guri ya dauki kamshi.
Miya ya kammalu na sauke na dora tuwo duk tare da yaron nan da yace min sunan shi habib ne dan gidan mai faci.
Sai yamma Alhaji ya shigo gidan daga shiyana ina zubawa yaron abinci naji muryan sabuwa tana cewa yau wani sabon cin amana ne da muna funci ya taso a gidan nan kuma ?.
Kamar yaya kuma ya tambaya tace duk munafuncin da kake a gidan nan nabawa yarinyar nan kayan dadi taci don ta yarda dakai ta kwantar da hankalin ta ka murje ra yadda kake so nagane ka.
Mu sai ka tura muna tuwo ita ko daga shinkafa sai taliya kake bata bata taba cin tuwo a gidan nan.
Ga kowa yai cirko cirko yana sauraren ta yace cikin daka tsawa ke sabuwa ban son sheri ni kike kira da munafuki yau.
In ma har munafunci ne ai ake nakeyi don ke ce munafukan kullun a gidan nan ba mai bani bani sai ke, ke, kenan kullun yin karya da ciwon yara ba ranan da zan fita baki karbi kwabona ba a gidan nan karyan yau daban na gobe daban.
Kaji kuma na sayo mata don itace mai girki su nake son ci shiyasa na sayo ke ranan da zan sayo bacewa kikiyi wai nabaki kufin ba ki sayo da kanki dana baki na dawo cewa kikayi n sace kudin ai.
Nawa nake ba wanan yarinyar a gidan nan ko bata nayi yadda nake bata sai dai tace na sayo mata duk abin da ya dace idan na fita.
Sabuwa nan ta hau borin kunya akan wai Allah dai ya kama ka yau kila ma har gashin dare kake kawo mata kai a dole gaka mijin yarinya ko ?
Sabuwa yau dai na gaji da sherin ki a gidan don haka na fada maki akan yarinyar nan zan iya saba maki kifice min daga gida.
Ahayye nanaye abin kunya wai aure da mara kwabo yace balle da kwabona ko kin manta kwabon kika gani a baya kika lake min da aike da komai har na yarda kika shigo gidan don haka yau ko wayai maki tsaye a gidan nan wallahi baki kwana min a gida.
Maimakon ta ci gaba da gudan da takeyi sai kuma jikin ta yai matukar sanyi sosai don tasan takan mashi fiye da haka amma bai taba yanke irin wanan hukuncin ba a kan ta sai yau kuma akan yar karamar yarinya.
Nan dai mama hausi ta saka bakin ta tace asha Alhaji da baka biye mata ba halin sabuwa ne kuma bako a gare ka yau.
Yace bari hausatu nagaji da sherin yarinyar nan yau ta kaini kat ne ita bata ji kunyan yaudara na ba sai nine zanji kunyan ta.
Ina kazan nan a kowan ku da yai girki sai da na saya mai aka girka min naci amma don wanan yarinyar na da girki na sayo zatai min sheri tace ai ba biyu ka saya muna ba kamar nata.
Bai kula ta ba ya shige dakin ta da kan shi ya kwaso kayan shi na kwan ciya ya fito daga dakin nata.
Hankali yai matukar tashi sosai a lokaci don nasan halin kauyen mu yazu labari zai sha banban ace daga shiga na na fara watsa matan gidan da na samu.
Hakana jiki ba kwari na dinga aiken wanan yaron da Allah ya hadani dashi yau yana kai wa kowa miyan duk sai da na kusa rabe naman don yawan gidan.
Mama hausi dake zaune tare da sarakan ta matan diyan ta su uku ta ce kungani ba yanzu ga naman ma karshen ta duk ta rabe shi gare mu.
Har ya fita zuwa sallah ya dawo bata bar gidan ba kamar yadda ya bukata haka yasa shi zuwa har kofanta ya daga labulen dakin yace.
Sabuwa may kike jira ne a gidan nan wai ai tunda gidan nan bana ubanki bane yau na fada maki wallahi baki kwana min a gida ki tafican gidan ku kikarata can.
Idan kuma kin ki fita yanzu na turo masu karfi aja min ke da karfin tsiya har waje.
Ganin haka tasan kuma da gaske yake yi yasa ta fara tattara kayan ta tana kuka wai saboda karamar yarinyar da kokwai bai aje da ita zai koreta gidan shi ita dake da yara bakwai a gidan.
Haka tafice daga gidan bakin ta bai mutu ba ta nufi gidan su a cikin dare kowana na kallon ta a wullakance.
Sai bayan tafiyan tane na fahinci ashe halinta ya ishi kowa agidan sai fadin aibunta kowa keyi.
Nan naji abubuwa da dama akan halinta ashe shiyasa take ganin an auro ni zan karbe mata power da take dashi a gidan da gurin mijin su.

****** ********* ******
Washegari tunda safe na shiga gurin mama bayan na gama aikin da nakeyi na kwashi kayan wankin ta sai aune tayi dani ina wanke tufafin ta.
Ta saka salati tana cewa haba amarya ai sai kina ace muna bautar dake ko iyayyen ki suka samu labari bazasu ji dadi ba gaskiya.
Nace daidai danta babba yana shigowa gidan dauke da dan karamin yaron shi a kafadan shi haba mama don nai maki wanki shine za, ace kina bautar dani kefa uwatace mama ba kishiya ba kamar yadda naji ana fada.
Ko a gida nike wankewa su innata har da mama kayan su idan yai dauda don wanan kayan da baida yawa ma.
Girgiza kan shi yayi yana cewa a ranshi ikon Allah yanzu baba wanan karamar yarinyar daya kwaso kurciya zalla haka may zai gane a gurin ta ne wai.
Nan dai dole uwar ta barni da wankin na wanke su fes na shanya na koma dakina ina jiran su bushe na kwashe mata.
Yaron nata mai suna yaya sani ya shigo dakin mahaifiyar tashi ya samu guri ya zauna daga gefen ta yace.
Mama dazun sai nake jin ki da amaryan ku a bakin rijiya kuna gaddama kuma akan wanki.
Tace bari kaidai ni kurciyar yarinyar na ya fara daure min kai wallahi bata tasan kyashi ba ko hassada a rayuwan ta komai haka zata zage tayi shi tsakani da Allah.
Yace haka naji nima sai dai mama gaskiya sai kunyi da gaske gurin rike amana tun da dai ba sanin ciwon kan ta tayi ba yarinyar gashi uwarta tai mata tarbiyan da

Please Login or Register in order to submit comment