Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a fili.
Bayan sallah jumma, a aka daura aure duk dai ba wani shagali akayi ba tunda ba auren saurayi da budurwa bane, amma an ci ansha an koshi.
Da yamma aka dauke ni sai gidan Alhaji garbati gida ne babban gida mai cike da iyali fiye da arbain a gidan.
Sai da aka kaini dakina na dan zauna na yan mintina akace na taso akaini dakin uwayen gidan.
Dakin uwargidan mama salla aka fara kaini dattijuwa ce sosai don ta manyanta sosai ba sai an fadi ba itace ta wanke shi ya wanke ta.
Nan iyayyena suke fada mata cewa ga amanan yarsu nan sun kawo masu da fatan zata rike masu ni amana idan nayi ba daidai ba don Allah ta tsawata man.
Tace kada suji komai ai da na kowa ne da fatan nima zan masu biyayya yadda ya dace karami yai wa babba.
Suka ce insha Allahu in wanan ne baza, a samu matsalan komai ba a kaina.
Nan dai suka mike suka bar dakin ina biye a bayan su sai dakin mai bi mata itama dai acan ba matsala sai cewan da tayi na daiyi hakkuri don su yara ne da su sa, a na dama wa yanda suka girmay ni.
Mun bar dakin zuwa dakin wacce nake biwa ita ma din tana zaune da mutane da yaran ta bayan an gaisa aka fada mata zaman lafiya ake nema a gare mu.
Sai cewa tayi haba zaman lafiya a tsakanin kishiya da kishiya ai sai dai zama na ki goga in goga tasan gidan da ta shigo ai har ta yar da ra kutso kai don kwadai ita da iyayyen ta.
Ai babu wani zaman lafiya illa tazo ga tukunya nan lamba ashirin ta tuka mu tuka da ita don yau an zama daya.
Daya daga cikin yan uwan mama tace to shi ke nan Allah ya bata ikin iya tukawa kamar yadda kowa keyi a gidan.
Muka bar dakin muna jin ta tana yadda bakaken magana wai haka kawai an koso yarinya karama don jaraba an kawo masu a g raino a gida ace wai an basu amana.
Dakina aka mayar dani aka zaunar dani a saman gadona da ya sha gyara nan aka shiga jero min nasiha na zaman lafiya har sai da na rasa na kamawa.
Sukai min sallama suka fice gidan suka bar ni ni kadai a daki nai tsuru tsuru dani kamar manya.
Ban san lokacin da wani kukan bakin ciki yazo min ba ga daki har daki amma ba ango a gurin ba gidan zaman lafiya a nan.
Ina nan zaune a takure ni kadai a dakin naji sallama muryan mama naji uwargidan garbati na amsa mata sallaman ta a sanyaye.
Tana dauke da wani zani kamar bargo na rufa da tocila a hannun ta na mike tsaye ina cewa sannu mama.
Tace a, a Rahama ke kadai ce a dakin ashe to ga kayan kwanciyar angon ki na kawo maki idan kin kare girkin ki zakikaiwa wace zata karbi girki kayan ita ma a dakin ta.
Bayani take min amma gabana sai faduwa yake min a lokacin na rasa fahintar komai da take fada min har ta fita tabar dakin ban fahince ta ba.
Na kalli kayan data aje min a bakin gado tare da kura masu ido ina nazarin su.
Na koma daga can kuryan dakin na zauna sama kujera tare da kara bin dakin wanda yake mallakina da kallo.
Sai faman tunanen irin rayuwan da zanyi a gidan nakeyi ga maganan Sabuwa da ya tsorata ni da tace wai ni kishiya nake a gare ta.
Baifi minti sha biyar ba da fitan mama din uwargidan shi sai na ji motsi alaman za, a shigo dakin nawa.
Mamace again tare da maigidan nasu tana mashi jagora kallo daya zakai mai kasan baida cikkaken lafiya a tare da shi don yanayin tafiyan shi ma kawai ya nuna hakan.
Da sallama ta shigo dakin yana biye a bayan ta ban iya amsa sallaman ba don girman su da nake gani.
Tace Rahama ga anginki na kawo maki kin san dai yanayin da yake ciki da fatan zaki lalaba muna shi dai.
Murmushi naji yayi ta juya ta fice daga dakin na mike daga inda nake na durkusa kasa nace a cikin sanyin murya ina wuni baba .
Murmushi yayi yakai zaune a inda na tashi ya dan kalle ni yace yaya hidimar buki amarya ?
Ban iya cewa komai ba sai sada kaina da nayi a kasa kawai babban rigar dake jikin shi naga yana kokarin cirewa tare da aje hular kan shi a gefe daya.
Da alaman dama kayan sun ishe shi a jikin shi yake cewa dani sai kuma ga angon naki da matsala amarya.
Sai lokacin na dan kalleshi naga duk ya ramay ya fada sosai ga yadda na san shi da farko.
Dan tashi mana amarya ki miko min kayan can na saman gado na sauya ko ?
Gurin da kayan suke na kalla tare mikewa zuwa daukowa na kawo mai na durkusa tare da bashi kayan.
Ganin da nayi yana kokarin sauya kayan ne a gabana yasa nai saurin fita daga kofana na tsaya sai dana tabbatar da ya gama na shiga dakin.
Yace yauwa zo ki zauna ko dauko ledan can ki dan samu kici wani abu daga ciki don nasan kina tare da yunwa.
Nace a koshe nake baba sai da Inna ta tabani abinci naci kafin na baro gida dazun.
Yayi shiru yana kallo na tare da nazarina sai kuma fuskan shi da na dan ga yanayin sa ya sauya a lokaci daya.
Yace amma wanan din hakkin ki ne na yau da ya dace na baki ai na kawo maki.
Nace a koshe nake shiyasa.
Yace to ni miko min na danci kafin na kwanta ko ?
Duk a takure nake a lokacin don yanayin yadda ya ke zaune cikin doguwar rigar jallabiya yasa nake kara jin nauyin shi sosai.
To zo mana ki zauna nan amarya gaki tsaye kin kasa sukuni ko ?
Gabana yai mumunan faduwa nace a raina wanan tsohon may yake nufi nazo na zauna zaman sa, a da sa, a dashi ko may ?
Nayi maza na juya can daga gefe nakai zaune a kasa tare da dukar da kaina kasa ina wasa da yan yatsun hannuna cikin dan lankwasa su.
Zuba min ido yayi a inda nake a zaune yana kallo na kafin ya bude baki yace Rahama yau gaki Allah ya kawo ki gidana cikin iyali na amatsayinki na mata tata.
Yace don haka ina son ki kasance yarinya mai ladabi da biyayya ga wa yanda kika sama a gidan.
Idan kinyi min haka kinyiwa kanki da nima adalcin rayuwa.
Don bazan taba jin dadi ba a rayuwa idan har wani rashin mutunci ya fito daga gare ki a zaman ki na gidan nan.
Idan kinyi haka kin min komai a rayuwana wanda hakan zai sakiji dadin zama dani bama ni kadai ba har ma kowa da zaki sama a gidan.
Nace insha Allahu zaka samay ni kamar yadda kake tsanmani a rayuwana yace to Allah yai maki albarka ya tashi kata kata ya mike tare da nufar gadon da yasha shimfida yana cewa ki dai yi hakkuri da yanayi har na dan wani lokaci amarya.
Daga haka naji yana bissimillah yabi lafiyayen gadon ya kwanta tare da mimikewa a sama yana sauke ajiyan zuciya.
Can yake cewa idan kin gama zaki kwanta sai ki rufo muna kofan dakin daga ciki kinji.
Nayi maza nace mashi tau ba, a dauki lokaci ba ina daga inda nake zaune naji ya fara nasari alaman barci ya dauke shi ke nan.
A hankali na mike na nufi kofan na rufo kamae yadda ya umurce ni da nayi idan zan kwanta.
Na koma kasa na kwanta ban dade ba sai barci dama jikina da gajiyan jigilar dana sha na jama, a atare dani.

Bani na falka ba sai asuba ana kiraye kirayen sallah naji motsin shi haka yasa na falka tare da mikewa zaune zubur yace a kasa kika kwanta Amarya ?
Ya dauki buta zuwa bandakin da akai min a kusa da dakina basai na shiga na taron gidan ba sai bayan ya fito ne na shiga nai tsarki na dauro alwala na shiga dakin.
Bayan nayi sallah ban kwanta ba tunda na saba a gida bana kwanci sai aikin gida idan na tashi na gyara gadon daya kwanta tare da sharo dakin har zuwa kofana inda aka kewaye min shi nagyara ko ina tsab.
Na fita zuwa tsakar gidan duk girman shi sai dana share shi kafin gari ya karasa waye,
Na hada kayan wanke wanken da na gani birjit ko ina na gidan na fara wankewa .
Sai lokacin matan gidan da yaran su ke fitowa daga barci duk wace ta ganni sai ta tsaya tana mamaki hakan .
Ina gaishe su daya bayan daya suna shigewa dakunan su da yaran su.
Ina gamawa na juya zuwa dakina na debi ruwa na shiga na watsa na saka wani lace mai laushi dashi cikin kayan da anty ta aiko min dashi.
Duk da ban san kudin shi ba nasan mai tsadane kwarai ga dinkin yai matukar karban jikina kamar an auna ni kafin a dinka min shi.
Can na fara jin hayaniyan matan gidan suna fitowa tsakar gida daya bayan daya haka yasa na gane cewa sun tashi ke nan na yafa gyale a kaina na fito na fara zuwa sashen mama tana kokarin fitowa daga dakin ta tana ganina tai murmushi take cewa a,a amarya baki huta ba gaki da gajiya kika fito kikai wanan aikin haka?
Hutun may zatayi bayan dama an saba da komai tun a waje muryan sabuwa ce dake bayan mu hannun ta rike da wani karamin roba kore.
Na durkusa na gaida mama da ina kwana mama tace lafiya kalau Rahama yaya dare yaya angon naki ?
Sabuwa ta kara cewa dare kan ai kinga inda alaman shi ya nuna ba a wahala ba don ansan komai.
Haba sabuwa wai may yake kawo wanan magana hakan ga wanan karamar yarinyar kuma ?
Wanan ai ba sa, an yin ki bace may ta sani akan zancen ki dakikeyi yanzu sai muryan maigidan mukaji daga bayan mu lokacin ina durkushe a gaban mama yana cewa.
Sabuwa ki kiyaye ni wallahi a gidan nan don zan iya saba maki akan yarinyar nan a gidan nan fiye da tsanmanin ki.
Idan ba hauka ba irin naki yanzu wanan yarinyar zaki titsiye a gaban ki kina fada mata wanan magana haka ?
Ina yatinyar take tashige daki ta kwana da kai ta fito kemaymay da ita har kake kiranta yarinya.
Yarinya kan na bayan uwar ta ai wace bata san shigewa daki da namiji ta kwana ba kuma ta tashi lafiya tarmazazai haka ?.
Ganin dayar matar tana cewa kai haba tunda wanan farar safiyan haka za, a tusa muna wani fitina a gida.
Na mike daga gurin mama na nufe tare da durkusawa har kasa nace ina kwana mama ?
Tace a,a amarya ni ba mamakin bace zaki iya kira na da yaya ko maman Aisha.
Nai murmushi na kara gaishe ta ta amsa fuskan ta ba yabo ba fallasa cikin sa dacewa yaya daren Amarya ya angon naki koda yake gashi nagan shi ya samu lafiya ai a gaban mu.
Inda sabuwan take na nufa itama na gaida ita a cikin ladabi sai cewa tayi ke tashi da kili bibin ki idan ban kwana ba zaki ganni ne nan ?
Yace uhumm kaji ba ke abinda baki taba yiwa yan uwan ki an maki kuma kina jin haushi yanzu .
Ni dai ina ganin sun rikice na juya zuwa dakina ban tsaya sauraren su ba.
Sai zuwa can naji ya shigo dakin shima dai gaida shi nayi tare da mai yaya jikin yace jiki da sauki sosai.
Zuwa can naji anyi sallama ya amsa wata budurwa ce daga cikin diyan shi dauke da kwanon kunu da kosai taje cewa baba ga abin karyawa inji mama akawo maku.
Yace kice ana gaida ita da aiki ko inda nake bata kalla ba tafita daga dakin har takai kofa naji ya kirata yace suwaiba kun gaisa ne da sabuwar umman taki ?
Tace baba ai ban gan ta bane tabashi amsa murmushi tayi tace ina kwana .
Nace mun tashi lafiya yaya gida bata tsaya ba tabar dakin yace taso ki dibi kunun da kosan mai isar ki kisha.
Nace sai zuwa anjima bani karyawa da safe haka ai yace to injin ku yan boko ne ?.
Da naji alaman suna aiki na fito na samu ashe kowa ce ta fito tana aikin sana, anta da takeyi a gidan .
Na kama wa mama dama kokon da takeyi za, a fita mata dashi nan da nan muka gama.
Sai mai bi mata dake dafa shinkafa da wake itama na karbi wanke shinkafan na wanke mata tas na zuba tare da gyara wutan da icce ya jaye na hura wutan sai gashi ya kama.
Ban koma daki ba sai dana kwashe mata shi a kwano na gyara yadda za, a fice dashi na koma daki na.
Na samu maigidan ya shirya zai fita yace ina kika shige ne Amarya nace ina gurin da ake aiki ne.
Yace to ni zan fita sai na dawo zan dan leka waje nagani ko akwai abinda zan iya yi a can na neman kudi.
Kin san angon naki dan bida ne ba mai zaman gida bane ni.
Na durkusa nace Allah yasa a dace Allah yaba da nasara a dawo lafiya baba.
Yace kai ni fa wanan baban ba son jin shi nake a bakinki ba da dai za, a canza min suna ko Alhajina akirani dayafi min alheri.
Nace to Alhaji Allah yaba da sa, a yasa a fita a nasara yace amin yar amarya ta yaushe rabon da naji anmin fatan alheri haka a rayuna.
Nan yasa kai yafice ni gyara dakin na dan zauna sai barci ya kwashe ni afurin mai nauyi ban sani ba.
Muryan yan gidan mu ne da suka shigo ganin kwanana ya tayar dani daga barci.
Na mike zubur ina masu sannu da zuwa idanuwan su fes a kaina suna kallona ban san may suke son fahinta ba daga gare ni.
Na gaidasu daya bayan daya tare da tambayan sauran mutanen gida.
Da yake iya yan uwan inna ne sai kadan daga dangin babana sai cewa sukayi kowa lafiya sai maman ku ne dai da ta saka muna hauka wai sai baban ku ya fada mata inda ya samo kudin da yai maki hidima haka na fita kunya.
Duk rantsuwan da yai mata ba yarda dashi ba wai idan bashi ya yi ba mijinkine yaba da kudin aka boye mata.
Nace cikin murmushi tare da zama kan makarin kujera na kai mama ho yaushe zata bar wanan halin nata ne na hassada da bakin ciki.
Ita da tace da tabar za, a kawo ni yanzu da taga sabanin haka shine kuma ta tayar da hankalinta.
Rabu da mahaukaci wacce bata son azauna lafiya iji kauna babana ta fadi hakan.
To yaya kuka kwashe da matan gidan naku yau da safe da fatan babu wani matsala dai ko daga gurin su.
Nai dan murmushi nace babu komai mama batare da na fada masu abinda ya faruba da safe akaina a gidan.
Sai dayan mama tawa tace ai ina ganin indan dai ta iya binsu zata samu sauki ga biyun mata wanan dai da take biwa ce matsala nake gani sai yaran su kuma don naga yaran a tsaye suke suma.
Nan dai sukaci ga ba da yi min nasihohi na in zauna da zuciya daya dakowa na basu girman su tunda duk sun haifeni baki dayan su.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, ,


IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WASU MUN BARKI GA ALLAH YA BI MUNA HAKIN MU A KANKI YAR UWA DA FATAN ZAMU JI TSORON ALLAH MU RIKE AMANA DON AMANA GIRMA GARE SHI.


Dawowan Sabuwa gidan yasa yanzu na rage fita gidin darbejiyan da matan gidan suke fita hira ko yaushe.
Idan ma na dan fita bani daukan lokaci a gurin don gujewa shiga tarkon ta don ko yaushe ita a cikin fitina take.
Gata irin figagan matan nan ne marasa jiki komai nata dan kyamn, ne a fige sai bakin fitina da mita ga yawan haihuwa a yadda naji matan gidan suna fadi wai bata yayewa take samun ciki.
Ganin na rage fitowa ne yasa ranan mama hausatu take tambayana dalilin kumshewa na daki yanzu murmushi kawai nai mata batare da na bata amsa ba.
Sai cewa tayi Allah ya kyauta halin sabuwa sai ita don mai hali baya barin halinsa komu nan ba barin mu tayi ba ai da girman mu gaban diyan mu da sarakan mu sai taci muna mutunci ba komai bane a gurin ta.
Jin da nayi yarona abokin hirana dan makwabbcin mu habib yana da kwazo ga karatu addini gashi karami amma Allah yai mai baiwa gurin garatu.
Yasa na ke zama dashi muna karatun mu a shiyana muyi karatu idan mun gama muyi ta shiriritan mu kamar yada kauna muke dashi.
Don dan abinda yake samu a gurina gashi na rike shi da zuciya daya shima hakan nake gani a gare shi don bai taba min abu sai ya roke ni .
Wasa wasa sai na fahinci ba karamin karuwa nakeyi ba da karatun da nakeyi a gurin habib din.
Hakane ya bani daman tunanen na roki Alhaji idan zai yarda na rika zuwa makarantan islamiyan dake kusa da gidan mu.
Don akwai daya daga cikin sarakan gidan da kullun ita sai tafita zuwa daukan karatu.
Da naiwa Alhaji magana yace haba amarya kofa wata uku baki kai ba da zakice zaki fara fita ?
Dole na hakkura naci gaba da karatuna tare da habib din amma abin yana a raina.
Dama nayi nisa tun a gida haka yasa na samu saukin karatun a yanzu wani lokaci kuma littafaina na boko na kan dauko nai tabi ina dubawa ni kadai a daki na.
Mama Hauwa tana aikin fura sai dai ba kullun takeyi ba daga shiyana nake jin harshen ta tana fada da yarta mai mata talla wai sunyi rana ga aikin kuma yarinyar ta tsaya tana shiririta ga aikin.
Na mike tare da shiga daki na sauya zanin jikina na jawo kofan dakin da kuma kofan shiga shiyan nawa don akuyoyin gidan masu bakin barna.
Na samu ga gari aje ga aikin gida da yasha mata kai don ita ce da girki ranan.
Ina zuwa nai mata sannu na karbi rariyan dake hannun ta na shiga tankade da gyaran garin.
Na fahinci su kamar mama lauratu na gidan mu suke don basu damu da koyawa yaro aiki ba a gida.
Yar ta Amina tana fitowa ta ganni a zaune ina tankade tace wai har naji dadi amarya dana ganki don yanzu dana fita tunda kin saka hannu ga aikin nan zaki ga na sayar da furar nan a take.
Kai ji wani batu daga can kofan mama hausatu Zuwaira tace mama ai ba karya ta fada ba mun gane idan amarya ta taba kayan sana an mu a take muke saidawa idan mun fita.
Hannun ta yana da albarka sosai wallahi a kaji min yara da sabon surukulle kuma ?
Inji mama hauwa take fadi tana dariya tace muma wallahi zuwaira ta fara lurar damu haka dakuma muka duba muka ga ai hakan gaskiya ne.
Nan dai sauran matan gidan aka taru ana wanan zancen ana dariya ni dai akina nake ban yi magana ba.
Daga can kofan ta sabuwa ce ke cewa daurewa karya gindi ke nan ita waye da zaku ce haka ko watafi sa, a kuke kara zugata tana ganin ta kai wata aba a cikin mutane ji wani sabon tsurkun da kuma kuka camfa mata don taji dadin iya shege.
Ni dai wanan aikin jagwalgwalen badani balle a camfani ni kishiya bata fini ba balle na sa a kaina.
Wanan abar ce zaku tsaya kunawa wanan camfin kamar wata babban mace can da ita.
Nan daya da kacin sarakan mama ta cafe da cewa ai ba camfi bane dama can a garin nan kowa yasan irin sa, an dake ga Rahama ai gurin talla don komai ta dauka sai kudin shi.
Eh hakane dama tunda tana da tsifin dake mata juye subata kudi ta kaiwa uwarta ana cewa sa, a ne yanzu ai gaskiya ya tabbata don mungani koshi Alhajin ba ragowa ne ya kwaso muna ba Allah mudai ya cece mu da daukan ciwon sanyi wallahi.
Shiru gurin yayi don jin inda ta biyo da zancen can mama hauwa tace wanan kuma sabon kake ne don ban taba ji bani kan abin garin nan da ba a boye yake ba.
Tace kece baki sani ba kuma dole ne sai kin sani ba tunda idon ku ya rufe don kawai ai min sheri a hada min kai a gidan nan aga bayana nida Alhaji ko mutu ka raba.
Sai lokacin mama hausatu uwargida tai magana tace kai haba sabuwa in an girma asan an girma mana yanzu wanan yarinyar dako hankalin kanta bata gama mallaka ba zaiyi wanan sheri a matsayin ki na uwa.
Ke ma fa gakin nan dasu a gaban ki indai yaran ne ai ba uwar da zata so aiwa yarta sheri haka ?
Au to yaya abin yakai can baki zakiyi wa yarana kuma?
Ai dama ba yau ba nasan sun kai maku ko ina a gidan nan saboda hassada aiko tashiga bakin ta harshen ta har waje ana jin ta.
Daidai lokacin ne mukaji gyaran muryan maigida yana tafe tare da dan shi babba a baya da mai bi mashi.
Tun a kofa yake fadin wai yaya ne kuma may kuma ya faru haka da rana tsaka.
Ledan dake rike a hannun shi na vaco na je na karbo da sauri yayin da sauran matan ma suka karbi na hannun mazajen su idan ta akan ledan dana karbo take fada.
Na nufi dakin mama hausatu da ledan don itace ranan da girki sai yamma zata fita sabuwa ta karba don girkin namu a jere yake muna.
Ina nufin shigewa dashi dakin ta yace dawo dashi nan mikawa hausatu a raba abakowa nata ta shiga dashi ya juya yana fadin tambaya nakeyi mai ya faru wai ake wanan fada murya har kofan gida.
Shiru kowa yayi babu ma magana a cikin su sai Amina yar shi ce ta shiga koro mai da zancen abinda ya kawo rigiman haka.
Ya kalli inda sabuwa take yace kai amma dai sabuwa ke mutumiyar banza ce wallahi.
Kina zaton yadda kike watsatsa haka kowa ma yake a rayuwan shi tashinki a garin nan aike ce kika so bata tarbiyan yaran garin nan kaf don ke kka zo da wanan halin ko don su nan basu sani ba har kika samu bakin yiwa wata sheri kuma ?
Haba nan ta juye bala,in ta kan shi sai da yai saurin saka mata waigi ta dakata don tasan abin da yake nufi zai iya aikata shi da gasken a kan ta.
Malam wanan kuma Yaya za, a yi dashi tana kokarin fitar da gorunan

Please Login or Register in order to submit comment