Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kanshin da ake min a gidan nan don may har in suna ganin kinyi laifi ne bazasu hukuntaki ba sai sunkirani don raini sun hada dani.
Saboda yana son gyarawa matar raine zai dinga min wullkanci a duk lokacin da ya bushi iskan shi ko may ?
Nagajine wallahi ni may ye yaran yaya basuyi min a gidan nan waya taba jin nayi magana balle nace itace ke daure masu gidin sai ni da aka raina za aiwa cin fuska yadda akaso.
Shiru shiru aiba tsoro bane don sunga ina basu girman su shine zasu dinga takani yadda sukaso.
Inna na kaiwa nan sai ga baba ya daga labulen dakin mu yana fadin ke Rahama daga yau sai yau kada na kara ji ko ganin kin kara hurda da bakuwar birnin nan don ba yar uwarki bace ban san dalilin ki na manne mata ba to na hana wanan hurdan daga yau.
Yana fadi haka a cikin daga murya nasan yana fadi ne don mama taji ya yanke alakata da Anty.
Abinda take muradin gani daji don tasan zamana da ita babban alheri ne ga rayuwan mu idan bata hana ba.
Zama guda ta kashe min kudi haka har jakka sittin ba gaira ba dalili akaina.
Yana gama fadin haka ya juya ya cuce a cikin hasala babu wanda ya tanka mashi yabar dakin dama yayi ne kawai don dadin ran mama takuma ji dadin.
Sai bayan tafiyan shi Inna ke ce wa an daiji kunya wallahi mutum har mutum amma baida ta cewa a cikin iyalin shi sai yadda akace mai.
Hakkuri na kara ba Inna don nasan yau kan ancin ma rashin hakkurin ta a gidan.
Duk da karancin shekaru na ina iya fahintar wasu al, amuran da akeyi a gidan mu wanda ko kadan bai dace ace anyi shiba a tsakanin iyali.
Amma gashi da karancin shekaruna yakai har na fahinci hakan a gidan mu, kai bani kadai ba duk yaron dake gidan mu yasan irin zaman rayuwan da akeyi a gidan.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , ,

IDAN KIN BIYA KIKA BA WA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH YAR UWA, , ,


Tafe nake da robar talla na yau doya ce dafafa gishiri sai kuli, kuli da yaji aciki wana nake barbadawa mutum idan ya saya.
Daya daga cikin tufafin da Anty ta bani na saka wasu material ne masu walkiya walwal idan kana tafiya da su.
Tafe nake nayi irin digirgire din kaya a saman kai din nan hankalina a kwamce nake tafe .
Kai kai kai da sauri dayan mutumin da suke zaune a tare ya juya yana kallon gurin da nafarkon mai magana yake kallo,
Da sauri suka kawar da kan su daga kallo na don na kusa karasowa inda suke a zaune.
Dama yarinyar nan haka take da kyau ashe kamar wata matar gwauna haka da ita ?
Wai may ne ne haka salla ni duk ka cika ni da zancen yarinyar nan yace wallahi ranan da kuke zamcen ta bani kusa sai yanzu nai mata kallon tsab ai.
Garbati idan kana son abinka kawai ka shige kai tsaye nan ai babban iri ne ga wanda ya samu.
Allah na tuba ko kyawawan yaya ake haifa wa mutum a gida ai ya wadatar akan su.
Ni fa ko da kukaji nai magana a ranan ba wai har zuci nake zance na ba amma naga kuna gidada abin haka ku ?
Garbati kada kaiwa kan ka salalalan tsiya walahi in har kana so kasa kai kawai na fada maka kada ka tsaya garin kallon ruwa wani yai maka tsalle.
Kaga dama ina ga ba ai mata wani matsayi ba zuwa yanzu yan uwan tane kawai nake gani suna fitowa hira da dare amma banda ita.
Wanda ake wa fadancin ake kuma zuzuta shi a kaina sai yanzu yai magana yace.
Kai salla, banki ta naku ba fa akan maganan yarinyar nan sai dai gaskiya a yadda shekaru na yakai yanzu sai nake gani ai na wuce tsayawa koda akan yyayyenta ne da kake magana balle ita.
Sannan kaga yarinyar ga ta dai karama ce amma akwaita da kwarji a fuskanta kamar ba karamar yarinya ba.
Gashi kuma bata bada fuska kamar sauran mata ko yaushe fuskan ta a daure yake ba fara, a agare ta.
Sau tari da yawa nakan so na dan mata magana koda na wasa ne amma da na dumfare ta sai naji gabana yana faduwa tana matukar yi min kwarjini sosai a idona.
Salla yace assha Garbati kada ka zama ragon maza mana yanzu kuma manya mata ma mun sha gaban su babu gezau balle wanan yar ficiciyar karamar yarinyar zata kayar maka da gaban ka.
Don haka idan har kana ciki ka bari zan maka iso har gida na gabatar dakai tun wani bai riga ka ba.
Da zaran nema iso a gidan su insha Allahu komai zaizo daidai koda baka zo tadi ba gurin zance sai kawai ayi yadda za,a a daure aure batare da kowa ya farga ita din taka ce ba.
Kai haba salla yaushe rabon da ai irin wanan neman auren yanzu da kai ya waye wa mutane.
Sallah yace kai dai in har kana ciki ce min eh kawai kasha mamaki indai har zaka bude bakin aljihun ka komai zai tafi daidai insha Allahu.
Har na kawo daidai gurin da suke zaune suna zance na ban ko gaida dasu ba don rabin hiran su ya dan zo a kunne na naji.
In ba gulma irin ta mutanen yau ba ina ni ina su Lawisa da koda aka haifesu ba, a auri uwata ba a gidan.
Don an kawo sadakin auren su zasu yi aure aiba abin mamaki bane hakan idan anyi la, akari da irin girmuwan da sukai min.
Ban saka zancen dattijan banzan nan a raina ba don nasan ba abu bane wanda zai yiyu suke magana don jin dadin fatan bakin su ne kawai sukeyi.
Nikan inda naji zance tsofin banzan kamar yadda na sa masu suna a gurin na bar zancen.

****** ********* ******
Sai bayan kamar kwana biyu da zancen ne da dare na dawo daga tallah nayi diban ruwana da wuri na dauko littafaina ina bita don mun kusa zana jerabawan mu na fita tunda na samu an min jummping a school bana zan kare karatun secondary dina.
Ina jin lokacin da baba ya shigo gida bai jima da shigowa ba akai mai sallama yafita.
Ya dan dauki lokaci a waje kafin ya shigo ina jin mama na mitan wai abincin shi yana sanyi bai shigo yaci ba.
Ya dawo cikin gidan yanayin da ya shigo dashi kawai zaka kalla kasan yana cikin damuwa.
Sai da ya zauna yagama cin abincin shine sa, an nan ya umurci lawal yaron mama karami ya kira mai Inna.
Bata jima ba tafito ta samay su zaune da mama a saman tabar ma guda itama ta samu guri ta zauna don tasan magana ce mai muhinmanci zai yi dasu.
Bayan ta zauna ne ya dube su yace ina Asiya tace gani gaban ka ai malam ina sauraren ka.
Yace Asiya wani sha, ani ne ya taso gamay da yar ki Rahama.
Jin haka da yace yasa Inna ta kara natsuwa tana sauraren shi tunda taji yace yar ta Rahama tasan ba abin alheri bane zai fada mata a lokacin.
Don indai lafine a gidan dama bai wuce yaran dakin ta ko yaushe mussan ma ita Rahama din da take kamar ta tsone makowa ido a gidan.
Shiru baba yayi na dan lokaci kamar yana shakkun fadin abinda yake son fada masu a lokacin.
Sai zuwa can ya dan nisa yace dama wani mutum ne yazo yana son auren ita Rahama din .
Nikuma har na bashi saboda naga dacewan hakan don haka na bashi dama akan yazo yaga yarinyar.
Inna tace idan da Alheri a ciki Allah ya tabbatar da alherin sa .
Baba yaji dadin hadin kan da Inna raba shi ba tare da tsayawa jayayya ba akai ko wani kwankwanto.
Tana kokarin mikewa tabar gurin yace idan kin shiga ki turo min ita Rahama din.
Inna tace to kawai ta mike tabar gurin ran ta a bace sai dai su basu gane ba.
Bata kai ga shigewa ba taji mama na fadin ai ma an mata gata koma waye tunda har yau babu ko karen da ya taba sallama mata gidan nan.
Tana shiga daki ta samay ni nabar karatun da nakeyi ina sauraren maganan su.
Tana fada min sakon baba na saka hijjab dina nafito gurin da suke zaune tare da mama din.
Na durkusa tare da gaida baba ta amsa min a kasalance cikin wani yanayi mara dadi.
Sai da ya dan kalle ni Yake cewa Rahama nace uwarki ta kira min ke ne saboda ina son sanar dake Garbati ya gane ki yace yana son ki kuma da aure.
Ni kuma naga dacewan hakan na bashi ke ina son ki zama yarinya mai ladabi da biyayya kibi umurni na don dama nice da alhakin zaba maki mijin da ta dace dake.
Wani irin mugun faduwan gaba naji tare da wani irin jiri a lokaci daya kila badon ina a tsugunne ba dana fadi a lokacin.
A hankali na dago kai nace baba wani garbati ke nan kuma a gatin nan ?
Mama ta tare da cewa ungo nan Garbati nawa kika sani a garin nan Garbati dai mana mai arzikin garin nan dai .
Kasancewa na ya mai tarbiya ga iyayyena da sanin darajan su tare da sanin hakkin aurena ya rataya a garesu don sune ga kaidan musulunci dama ya dace su zaba min miji aure na fari a rayuwana yasa nai shiru.
Amma kuma duk da haka ace kuma Garbati Garbatin da a girmay ya girmay ma baba ba kadan ba.
Gaskiya wanan zance na baba da yanayin sa sun bani mamaki matuka ganin cewa duk yan uwana mata zabin kansu ake basu su aura tun farko.
Bayan haka aiga Lawisa da Rukkaiyya a gidan duk sun girmay min a shekaru don may su ba za, a basu shi ba sai ni da aka rainawa kurar uwata dani.
Ni da ko yaushe nake hango kaina da a mainasara nake ga rayuwana zan tsaya tsayin daka naga nayi karatu mai tsawo a gidan mu, shine zan buge ga auren wani tsoho wanda ma ya girmay ma mahaifina ga shekaru sosai don dai yana da dan abin hannun shine ba, a gane shekarun shi ko may ?
Ko kadan bazan iya yiwa babana mussu ba gama yadda naga mama ta gwagwafe ta tsura min ido tana son taji wani rashin mutunci ya fito daga guri na ko inna a lokacin.
Na sunnkuyar da kaina a kasa murya a tausashe na ce baba na gode Allah ya tabbatar da abinda yafi zama Alheri .
Yace insha Allahu hakan shine alherin ki Rahama tunda kikaga babban mutum haka yazo neman auren ki.
Don haka sai ki shirya don zai fara zuwa zance gurin ki duk da yace shi ba irin na yara zaiyi ba zai dai zo koda saudaya ne kuga juna dashi.
Ki kwantar da hankali ki kada kika kamar shi ba yaro bane kice zaki ta da hankalin ki akai na tabbatar da zakiji dadi a gidan sa don in kiyi la, akari duk kauyen nan babu maihalinsa ga kuma kula da iyalin sa da yakeyi.
Bake ba har mu nan nasan zamu amfana da auren ki dashi insha Allahu.
Take naji gabana ya yanke nace a raina watau auren kudi ne baba zai yi dani ke nan ko tunda har ya soma fadar haka.
A take naji jikina yai min wani irin sanyi a lokaci daya sai faman sake sake nake a raina wanda daga karshe ma banji abinda yake fadi ba sam.
Sai muryan shi naji yana cewa shike nan zaki iya tashi ki wuce Allah yasa mu dace.
Da kyat na iya mikewa tsaye sai kace wace kwai ya fashewa a ciki nabar gurin zuwa dakin mu .
Nan nake jin muryan mama tana cewa dama may na fada maka tunda makwadaitane daga ita har uwar ai yarda zasuyi.
Ina shiga daki inna tace a zaune ta rafka uban tagumi da hannu daya dagani tana cikin tashin hankali ita ma.
Zama nayi a kusa da mahaifiyan tawa cikin muryan kuka nace Inna kinji irin abinda yayi da rayuwana ?
Inna tace cikin jan dogon ajiyan zuciya, naji yarinya yaya zamuyi tunda shi ya haife ki ?
Kuma kin san yadda gidan nan yake da gani ba ra, ayin kasa bane saka shi yin haka akayi don kawai muyi magana ta zama muna abin gori da fade a tsakar gida.
Don haka abinda nake so dake shi kada ki sawa kanki damuwa akan zancen nan ko kadan mu bar wa Allah al, amarin shi don yana sane da komai.
Na dan dago na kalli Inba nace shi ke nan inna nabarwa Allah din komai kamar yadda kikace.
Ina fadin haka na dunkule a saman tabar man da nake kwana zuciya tab da tunane rayuwan da zan fada ciki.
A iya sani na dai gidan Garbati babban gida ne don har da sarakan shi zaune a gidan suke.
Mutum ne mai mai neman kudi yana noma yana kiwo da kuma hadawa da kasuwanci.
Gwargwado akwai kulawa za, ace ga iyalinshi a kauyen mu don baka ganin su a cikin kazanta kamar sauran matan garin.
Amma ina yarinyar yar shekara goma sha biyar za, a aura min tsohon mutum kamar Alhaji garbati.
Haka na kwana ina mutsutsuri saman tabar mana cikin tunane ga matan shi dukka uku bazasu rasa yara sama da takwas ko tara ba ni Rahama yaya zanyi zama cikin wa yan nan kakanin nawa a matsayin kishiyoyi ?
Ashe abinda mu bamu sani ba ta gurin mama suka fara biyowa da zancen itace ma ta hurewa baba kunne akan maganan don yaso yaki maganan.
Amma ra kawo mashi kabbali da ba, adi har yaji yagamsu da maganan ta ya yarda akan zai badani ga garbatin.
A yadda ya nuna ma baison a dauki lokaci ba ai auren ba don kada a hure min kunne.

****** ********* ******
Washegari dagani har inna ta babu wani mai sukuni a gidan mu sai mamace da yaran ta suke gadan su a tsakar gida.
Ina jin Rukaiyya tana wanki tana waka kamar haka yarinya ancuce ki an hada hadaki da tsoho, tsoho wari kakan ki shine kika aure ga hurhura gyamu kamar na kucaki.
Inna tace min kada ki kulata Allah yafiso idan da hannun uwar su fa alamarin nan Allah zai saka maki yarinya.
Dayake ba makaranra a ranan ban yi sana, a ba don bazan iya tallah ba a halin da nake ciki.
Da kyat na iya diban ruwa a randa na tafi na watsowa jikina ko zan danji dama.
Na zauna nai kwalliya na tare da saka tufafi a jikina inna tace na fita na gyara mata gurin girkin su kafin ta fito.
Mama dake zaune saman tabarma tana sauraren redio kaduna ana zabi kanka na yamma.
Ta izo daurin dan kwallinta a gaba kamar wata magajiya da ruwa yakarewa.
Ina fitowa tace kayya kyau da kwalliya ya kare kuma a gidin tsoho atafi akarata can a iske su sabuwa muna nan za, a bamu labari mu dai.
Wasu hawaye ne naji sun zubo min dana duka na fara shara ashe tagani sai cewa tayi ai idan mutum yace kwadayi ne yakai kashe yanzu kam.
An iya shiga lungu da mazan banza sunawa mutum juye ana muna takama wai sa, an talla kega mutum yau ga inda sa, an yakare a gidin tsoho tukuf.
Yo Allah na tuba kodai ni din nan tsuhuwa akace za, a hada da garbati ai sai inda karfina yakare to abinka da wanda ya saba da maza ko gezau babu.
Daga kofa na dago zan ba wa mama amsa naga inna a tsaye kai da kada min alaman kada na soma na tanka mata.
Har muka gama aiki da Inna tana zaune sai maga take sakewa ita da diyan ta a tsakar gida.
Bayan sallah na samu guri a dakin mu na shige ban fito ba har lokacin da naji shigowan baba gida.
Ya zauna don cin abincin dare Inna na gurin shi don itace da girki.
Sai murya wani yaro naji yai sallama ya gaidasu yace wai ana sallama da Rahama .
Gabana yai wani irin mugun faduwa daga inda nake zaune a dakin mu naji baba yana cewa waye ?
Yaron yace ina ganin kamar Alhaji garbati ne da wani a wajen.
Baba yace kace su jira gata nan fitowa daga inda yake zaune, yake cewa ke Rahama kina dai jin ana sallama dake ko ?
Na jawo hijjab dina dake gefe na nasaka tare da yan silifas dina da anty ta saya min nafice daga gidan.
Suna zaune a gidin iccen durumin dake kofan gidan mu inda wani lokaci samari ne ke zama suna hiran dare idan sun dawo daga gurin neman kudinsu.
Su biyu ne bazan iya sheda dayan ba tunda akwai duhu a lokacin sosai.
Sai kamshi turare suke irin na yan kauye mai hawa kai ya saka mutum ciwon kai a lokaci daya.
Na karso inda suke zaune tare da sallama suka wani amsa min kamar wasu kananan yara dasu.
Tare da cewa barka da fitowa hajiya Rahama insha Allahu kila badi dake za, a sauke farali indai kin amince.
Dan gajeren murmushi nayi bayan na fahinci mai magana baba sallah ne dan uwan mama.
Nace baba ina wunin ku ?
Yauwa barka dai Rahama .
Kin wuni lafiya dai ko ?
Na ansa a fili a gajarce da lafiya kalau.
Amma azuciyata cewa nayi ina fa na wuni lafiya bayan bakin cikin da kukajawa rayuwana ?
Baba salla ne ya fara magana yace ba sai mungabatar maki da kan mu ba dai tunda naga alaman babaki da Lauratu sun gudanar da komai yadda ya kama ?
Na dan kai durkushe a gaban su cikin ladabi nace haka ne kan.
Yace yauwa ashe bazamu samu matsala ba ke nan yadda muke tsanmani ?
Malama Rahama ga abokina nan kuma amina na yaganki ya yaba da tarbiyan ki shiyasa yaji yana son kasan cewan ki daya daga cikin iyalin shi.
Don haka yanzu yakike gani ?.
Nace kamar ya fa ?
A yadda nai magana tankar ban fahince su ba nayi.
Sai shi baba sallah din yace kamar na amincewa da shi amin nawa ga bukatan shi a gare ki ?
Nai wani gajeren murmyshi da har ya baiyyana sukajini a fili danayi shi.
Nace lah ni na Isa na ketare maganan mahaifina aida ban fito duya ta gari ba mai tarbiya ga iyayyen ta ba ?
Nace ai babu komai sai dai Allah ya tabbatar da abinda yafi zama alheri ga rayuwan mu.
Sun nuna sunji dadin magana na yadda suke fadin to Alhamdullahi alama ya nuna ke diyace mai tarbiya tun yanzu.
Sai lokacin shi garbatin yai magana da cewa na ji dadi kwarai Rahama da kika amince da bukatana haka da sauri don ban taba zaton hakan ba a gare ki.
Nace to yaya zanyi tunda umurni ne daga mahaifana ai dole nayi biyayya garesu.
Ai ko ban amince don ra, ayina ba dole ne na amice don biyayya ga mahaifa na tunda sune masu iko dani bani ce keda ikon kaina ba.
Cikun wani jin dadi garbatin yake cewa.
Duk da umurni ne iyayyen ki akaina naji matukar dadi da amincewan ki haka ba tare da wani matsala ba.
Insha Allahu kada kiji komai zakiji dadin zama da iyalina don zan kafa masu doka akanki don ke karamace sosai a cikin su.
Sukace zasu tafi sai na kara jinsu dama sunzo ne su tabbatar da idon su halin da ake ciki.
Kuma Alhamdullahi a yadda suka samu taro a gurina sunji dadi kuma sun gode.
Yanzu dai kinga mu ba yara bane don haka bazamu dinga zuwa ko yaushe ba don gujewa idanun jama, a akan mu.
Kindai sai komai a kauyen nan yanzu ana ganin mu labari sai yasha banban kuma.
Bakar Leda ne baba sallah yake miko min yana cewa fa wanan dan tsaraban rano ne da muka shiga dazun mukazo maki dashi.
Na girgiza kaina tare da cewa da kubarshi aiko haka ma nagode kwarai.
Haba haba ayi haka kuma diya ta ki karba kawai wanan ai ba komai bane idan mun samu hadin kanki yadda muke so ?
Nace kada muyu haka daku baba idan ina karban kayan maza Innata fada take min .
Da alama sun gamsu da bayani na yadda naga sunyi sun fahinci dai a karkashin controling din iyayyena nake ba kamar sauran yaran da suka sani ba .
Baba sallah ne yace duk da gaka dai diyata ki daure ki karba zan wa mahaufin ki bayani yadda zai gamsu.
Kinsan kin karban kayan mosoyi wani alama ne na kiyayya kuma.
Haka dai na daure na karba tare da masu godiya na juya nashiga gida raina a bace .



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , ,


IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH YAR UWA, , ,


Shiru mukayi dakin akan hukucin da mahaifi na ya yanke ta alakata da anty birni, yanzu baba akan su mama ya rufe idon shi ya yanke wanan hukunci haka duk da yasan mutunci ne ya hada ni da ita ba wai kwadayin da suke ikirari bane.
Muryan Inna ce take ce min kin dai ji may ya fada don haka sai ki san yadda zakiyi da shiga gidan mai kuli.
Waahegari ban tafi makaranta ba sai da na faki idon mutane na leka gidan mama Altine muka gaisa dasu na wuce.
Haka ma da na dawo ban shiga gida ba sai da na fara shiga gidan gurin su .
Hakana wuni ina fakin idon mutanen gidan namu ina fita zuwa gurin anty sama sama.
Ganin haka yasa suka fahinci akwai matsala na fito zan tafi diban ruwa na shiga gudu gudu gidan.
Nan ne mama take tambaya na ko may ke faru ne yau na kasa tsayawa kamar kullun.
Ban boye ba na fada masu komai da ya faru a gidan mu har baba ya hana ni shigowa gidan su.
Mama ce tace to babu laifi ki natsu ki zauna gidan ku kada kuma ta sa aiwa Innan ki wani abin.
Kin san ance mai hakkuri dama bai iya kai karshe ba sun kai ta karshe ne tunda ta fara basu amsa yanzu.
Allah ya taimake ni aahe mama ta saka ido sosai a kaina kozan tafi gidan mama altine a wunin nan.
Ganin ban fitaba yasa ta fara sakin magana a tsakar gida tana cewa ai na dauka ko ba abin dokar mune inwa uwa da diya dukan tsiya yau a gidan nan.
Idan shi ya kafa doka

Please Login or Register in order to submit comment