Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ance tazo a duba kafan takewa mutane maganan nosenses, wai da kafan ma baka,barta ba sadauki?
Yanzun kuma may ne mata, maji, kawai don za,a duba lafiyan kafan a shafa mata magani shine abin magana kuma.
Maji zatai magana sukaji muryan mata kaman da dan yawa suna kwada sallama a kofan dakin maryam dake tsaye tafito don taga ko waye?
Suna gaisawa daya daga cikin matar tace ance a nuna muna dakin hajiya Atika da hannu Bintu tai masu kwatance su tafi can.
Su na dauke da akwatina sa sauran kayan tarkace irin wanda ake kai kayan lefen mace kayan aure.
Maryam na fadawa Maji ta ce kayan lefe kuwa a gidan nan kaya waye ke nan kuma.
Amirah tace kila Nafisa ce ta samu miji ko Rukaiyya, shine aka kawo kayan su.
Can muka ji suna fadin bamu ba aura wa yar mu mazinaci mai abin kunya abin fadi irin haka.
Nan dai suke ta sake bakaken, magan ganu iri iri suna aibanta Imirah dashi haka yasa duk muka fahinci cewa ashe kayan lefen da akakai na auren Imiran shine gidan matan suka dawo dashi, wai sun fasa saboda labarin da suka samu na abin kunyan da yayai wa yar mutane a gari.
Daga inda nake zaune nace Allahu akbar yanzu a take Allah ke gwadawa mutun laofin shi tun a duniyan nan.
Gashi dai Umma da kafatan suka je gidan su Rahama suka aibanta yaya uwar ta tace am fasa auren yaya da yar su.
Ranan kun, manta babu irin maganan da su mama basu fadi ba, a gidan nan su ke cewa aure sai da muga anayin shi shiyan nan.
Yau ga shi Allah ya mayar masu da martani abinda suka shuka tun ba,a je ko inaba sun fara girban abin su.
Masha yin da suke fadi abin kyama gashi sai a zauna dashi ayi koma hankali a kwance sabanin dan ta katon mazinaci da ko maza yan uwan shi tsoron shi suke ji balle mata.
Muna ta hiran mu hankali kwance ban san cewa yaya Sadauki ya dawo falon ba duk abinda nake fadi a kunnuwan shi.
Ganin Amira tana kallon kofan shigowa falon yasani juyawa naga may take kallo ne wai.
Ganin shi nayi tsaye kinkam ya harde hannayen shi a saman kirjin shi,
Ya zura min ido fuskan shi babu walwala ko kadan a cikin shi ya sha mur sosai dashi.
Ina ganin shi tsoro ya shi ya dan kamani indai har baiji abinda nace gamay da tsohuwar budurwan shi ba.
Sai kawai nai shiru tare da dukar da kaina kasa dariya maryam takeyi tace kai Bintu yanzun fa kike ta masifa kan anwa yayan ki wullakanci yau gashi Allah ya rama mashi.
Maimakon nayi magana sai ma dan kai kaina saman kujera nai shiru tare da lumshe idanuwa na kawai.
Fuska a murtuke ya karasa takowa zuwa tsakiyan falon yana cewa wani gulman takeyi wa mutane ne wai?
Nace ai bani kadai bace magulmaciya kowa ma anan gulman yakeyi akan abinda ya faru.
Yace see your mouth muna fuka ta iya maida magana kamar wata tsohuwa can da ita .
Yarinyar ta iya babban magana da gulma kamar bayerabiya.
Haushin abin da ya fadi naji nace kai nifa wallahi in mutum bai daina kirana da mugun suna ba wallahi zan ramane wata rana.
Ni natsani wanan kalman na munafuka da kake kiramin in hakane ai kaima mugune na karshe.
Cafka guda yai min akaina na yanka ihu da dan karfi ido suka sako muna gaba dayan su da mamakin yadda halaiyan yayan su ya canza yanzu da irin mugunta da yake min.
Bai sake min kai ba nikuma sai fadi nake wallahi zan fadawa mama don Allah yaya ka bari wallahi akwai zafi sosai.
Ba kince ke baki da kunya ba bari na gwada maki mugu nake naja shegen kan nan mai tsawon banza ba gyara.
Ji kan ta kamar ba mace ba kullun a yamutse ko gyara bata iya ba irin na mata, sai shegen gulman tsiya karama dake.
Wai Sadauki may yake damunka ne ban san wanan irin iskancin ba da kake wa yarinyar nan a gidan nan
Tace karya take ba mugun kake ba dubi yadda ka rike mata gashin kai kaman wani mayanki.
Ya dago kai don jin muryan mama a bayan mu ya koma ya dubi gashin da tace ya rike min bai sake ba har lokacin.
Yace wallahi maji Fatima ta raina ni gulmana nasamu tayi da su Amirah shine nake koya mata hankali.
Koyon hankalin ne a haka?
Yace maji wallahi duk kin bari ta raina ni Allah ko.
Tace rufe min baki mara kunya kawai ina maka kashe di akan wanan yarinyar amma bakaji da Baban ku zan hada ka tunda ni ka raina ni.
Jin abinda maji tafadi yasa shi sake min kai tare da kutawa yace sai na balballa ki wata rana.
Ya juya yana gyara hannun rigan shi da yai dan squeezing.
Maji ta girgiza kai tace sai nayi maganin ka wallahi akan Fatima.
Yana fita daga falon ta juyo gare ni tace Fatima ki kiyayi sadauki don ba hankali gare shi ba kada ya halaka ki a banza.
Wallahi mama ban mashi komai ba kawai ya samu muna hirane shine ni ya sauke haushi a kaina.
Tace na dai fada maki ki iya kanki dashi mugun yaro ne bai dariya sai bakin ketan tsiya kawai.
Amirah tace kai maji yayane kuma mugu yau ?
Ba mugun yake ba may yake?
Maji wallahi in kina shiga tsakanin yaya da Bintu watarana fa zakiyi kunyane barsu kawai inda kika gansu a dunkule.
Maganan da Maryam tayi yasa maji kallo na nace ni wallahi mama karya take min ba,wani abin dukule dana sani.
Shiru tayi tare da shigewa daki tabar munan falo maryam na fadi muna ganin wani sabon sallo a gidan nan.
Na ce don Allah anty bari kada ya balballani kinji dai ya fadi ni yanzun ma,in yashigo gudu zan dinga yi yafi min wallahi.
Hummm kamar da gaske nifa nasan komai wallahi.
Tare muka hada baki da Amira muna cewa kin san komai kamar yaya fa?
Tace ni wallahi tun a asibiti ranan na kara gane komai.
Jifa yadda yaya ya rugumay ki yana lalashin ki.
Nace kai anty maryam wallahi kada ki kulla min sheri don Allah rufa min asiri kada kisa yai ball dani a gidan nan.
Shidai kawai ya tsanine yasa yake min haka wallahi in gaskiyane yai maku haka mana.
Sai naga ta sa dariya tace ji min wanan fa yai muna haka mu kannen sa.
O ni ba kanwarsa bane ke nan ko ?
Koma dai may kike ai zamu sani watarana Allah dai ya nuna muna lokacin kawai zakuce na fadi ai.

****** ********* ******
Tafiyan shi yasa na sake jikina sosai don yanzu kusan wata biyu bai garin sai da suna waya da kowa a gidan.
Ko ina gurin idan an miko min bana karba sai dai nace ace ina gaidashi kawai.
Idan sun fada mai sai yace rabu da silly girl kawai inta bata iya bugawa mutum ta gaidashi ne.
Ranan da yai nasara a gurin wasan su duk kasa shen duniya sai labaran nasaran da,team din su ya samu sukeyi .
Ranan Baba da kanshi ya shigo har dakin mu gurin mama yana ta washe baki da fatin ciki yana cewa.
Maijidda kinga iko Allah ashe kowa da inda Allah yai mashi tushen arzikin shi.
Yanzu akan wanan wasan ball din Allah ya daukaka wanan yaron haka?
Yau mutanen da suka bugo min waya suna min murna da farin ciki Allah ne yasan yawan su wallahi.
Yace ba abinda zamuyi sai mu kara godewa Allah da yasa haka ne silar shiryuwan yaron nan dakuma cigaban shi.
Da yanzu yana nan yana zaman kunsa muna bakin ciki da bacin rai zube nakashe a cikin garin nan amma yanzu kinga yadda Allah yai ikon shi akan shi.
Murmushi mama tayi tace nima abin yau har mamaki nakeyi mutanen yanzu sun mayat da harkan ball kamar wani abin addini.
Baba tace Alokaci muke muddin baizai hana shi addinin shi ba ai da sauki al,amarin.
Mamatace na kulla tun fara wasan shi bai wasa da harkan addinin shi yanzu ko kadan.
Allah ke nan inji baba yace shiyasa ko yaushe adduan iyayye keda tasiri sosai akan yaro wallahi.
Ni matsalata guda shine ya aje iyali don gaba dayan su na fada masu su fito da mata suyi aure hakanan.
Yanzu shi wanan shedani gashi yarinyar tace ta fasa batayi kinga ni duk abin ya shige min duhu wallahi.
Mama tace al,amarin sai adduan mafita yana gurin Allah Allah yasan dalilin wanan jerabawan da muke cikin shi.
Da yamma yaya ta bugowa mama waya lokacin duk muna zaune a falon sun gaisa naji tana mashi murnan samun nasaran da sukayi ban san may ya fada mata ba sai dan murmushin da tayi kawai a fili.
Amirah tace abata su gaisa dashi itama sun dade da ita suna hira yace abawa maryam itama dai sun dauki lokaci dashi sai halin ta takeyi na yaya ka,sayo min abu kaza ka sayo min kaza.
Tace yaya ga Fatima ko may yace naji ta kwashe da dariya kawai tana fadin mutumiyar ce fa gata ta taso takawo min wayan.
Na dauka tare da fadin salamu alaikum sai naji yai murushi yace wa,alaikis salam.
Yaya ina wuni?
Silly girl idan ban wuni ba zaki jini, yanzu ke baki ji kunya ba ke baki iya kiran mutum kullu gaki nan kamar wata bakauya can.
Hmm kawai nace mashi yace yar kauye kawai ai zaki gane kuren ki bari na dawo zamu hadu.
Nace ni bakama iske ni don da naji zaka,dawo zan gudu na koma kauye inda nafi wayo.
Ai bako isa ba,wallahi don har kauyen zanje na dauko ki nace wa Baba gudu kikayi wa maman ki.
Murmushi nayi har fararen hakorana suka baiyyana a fili.
Nace munyi murna Allah yasa afi hakan nan gaba.
Yace nagode da,adduan ki.
Na mikawa Amirah dake kusa dani wayan maryam tace wai har an gama fadan ke nan muushi nayi na zauna kawai suna hira da Amirah yana fada mata wai may yasa aka bani waya bakauyan daba tako iya waya ba ma.
Kai, yaya wallahi kaima kasan yanzu Bintu ba bakauya bace kana dai mata sheri ne kawai.
Maryam tace abata ta manta da wani magana bata fada mashi ba.
Amirah zance kusan halin rayuwan su daya da yayanta bata faye magana ba ita kamar maryam.
Ga ta da daukan kai da son girma yar gaye ce ta karshe ga tsabta da iya,kwalliya sosai gare ta.
Maryam din ma ba laifi gaskiya amma ta fiso son jama,a kamar mahaifiyan su hailayanta yake, ita don tana da son mutane gata da saurin sabo.
Nayi sabon saurayi shima dai yana da mata daya da yara biyu yana aikin banki ne shi sunan shi Usman.
Shima Usman gaskiya ba laifi sai dai baida hali irin na Kabir, din shi mutum ne mai son daukan aji da kuma nuna shi wani ne.
Ban faye son shi ba sosai don halin shi ni gaskiya bai min ba yana da son karya sosai.
Ranan da Nafisa ta gan mu tare dashi a kofan gida yazo muna hira yadda naga ta rude mashi ya sani tsinkewa al,amatinta.
Ranan na fahinci, halinta yai nisa bata da kunya bata da ta ido don yadda ta nuna mashi ra,ayin ta afili bata boye ba.
Ina fadawa maryam abinda tai min tace kyale yar iska nan tafi auki aishi ba jahili bane yasan ko ita wacece da ganin ta.
Exam din mu na shiga 300 level yazo don haka ni yanzu ba komai a gabana sai karatu sai ko idan na fito zanyi wani aiki.
Awala nayi zanyi sallah la,asar sai na fito falo don nayi sallah don babu kowa a falon mama tana ciki tana wanka don duk yamma sai sunyi wanka sun yi kwalliya kafin dawowan Baba gida.
Amirah ko tana ciki tana chatting da wayan ta tun bayan azahar takd daki kwance don bata sallah.
Maryam tafita tace zata wankin kai don kanta yana damunta da kaikayi wai.
Bayan na idar da sallah nacire hijjab dina na jawo littafina na fara dubawa don nasan in ban dage ba akwai aiki a gareni don ba wani mugun kokari ke gare ni ba.
Saye nake da dogon rigan atamfa a jikina mai dinkin bubu anty Amira akaiwa bai mata ba tabar min shi ni dinki sai ya karbe ni kamar ni aka dinkawa shi fun farko.
Ban san shigowan shi ba don kaina yana a duke a lokacin, yana tsaye cikin fararen swoth na maza da bakar riga ta ciki mai dogon hannu.
Yana tsaye daga kofa tsayin minti biyar ganin yadda na koma yai matukar firgita zuciyar shi sosai.
Don min kuwa yaga wata biyun da yayi na matukar canza mashi a idon shi, kallona yake ko kyaftawa baiyi .
Wani zazzafan ajiyan zuciya ya sauke wanda yai daidai da jin kanshin turaren shi a hancina abin da yai sani saurin juyo a firgice kenan na kalli hanyan kofan.
A firgice na dago kai ina kallon shi, yana tsaye ya zura hanayen shi a cikin aljihun wandon shi gami da zuba min idanuwan shi.
Gaba daya na rikice da ganin shi na dan dago ina fadin a yaya sannu da zuwa.
Bari na fadawa su mama kila bata san da zaka daao yau bane, cikin lokaci daya nake fadin haka tare da mikewa tsaye.
Yace see you haka ake taron mutum duk kin bi kin wani rude dake bakauyan banza kawai.
Ban tsaya na karasa sauraron shi nidai na shig ina cewa mama, yaya ya dawo.
Ya tako zuwa ga kujera ya zauna tare da harde kafafunan shi, lokacin na kara fitowa na nufi kitchen don na kawo mashi ruwa.
Nafito da ruwan a jug lokacin su mama har sun fito ko na ce fa ruwa yaya.
Yace ba komai ne sai ruwa yar kauye?
Mama tace tau bisimillahi Allah zaka fara ke nan kuma ko kadawo takura ya dawo mata ke nan kuma.
Ya dauki cup din ruwan ya tsiyayya yace mama in ba shirmay taba ruwa kawai zata kawo min.
May kake son takawo maka runda ba wanda yasan da zuwan ka yau din balle muyi maka tanadin wani abu.
Nikan in aje ruwan na koma inda littafina yake nafara tattara su na kwasa zuwa ciki.
Ina kuma zaki ke kuma bayan ga yaya ya dawo zaki fara shegen shigewan dakin ki kenan kamar kinga kura shi yasa yake maki rainin hankali ai.
Na dan yi dariyan yake nace mama dama zan shiga ne na karasa karatuna aciki.
Zauna nace maki ba idan zaki shi dai zai fita ya bamu guri inya gama abinda yakeyi.
Ya dan kalle ni ya girgiza kai , ya bude baki cikin kyarmar murya yace, yanzun kuma da dawowa na Fatima zaki kulla min sheri kuma ?
Na dan kada idanuwa na nace, cikin yanagin yatsina nace, nikan ban maka sheri ba kaine dai kaiwa kan ka.
Yace wallahi maji yar na taki munafukace yanzu dubi da zuwana ta hana ko na samu dan kulawa daga gare ki da nai missing tsawon wata biyu da kwanaki.
Bako so hakan ba da baka dawo muna da mugun halika ba yanzun ina laifinta taga bako takawo maka ruwa kuma ka gwatsale ta haka.
Nidai hada min wanan fruits din da kike hadawa nasha don da kewan shan shi na dawo saboda can wanda muke saye babu dadi.
Murmushi maji tayi tace kai dai baka da kunya wallahi yanzun fa ka gama zaginta kuma kace tai maka aiki.
Nace bamu da fruits sun lalace wanda ya rage dariya Amirah tayi tace wallahi maji maryam dama ta fadi kibar shiga tsakanin su.
Ke kina fada kada ta hada mai itako kinga sai kokarin hadawa ma take watau tabaki kunya.
Nace hai Anty nifa don kawai naga bako ne yau yasa yabano tausayi zan hada mai amma kada ki hada ni da mamana please.
Murmushi yayi yace bari na buga Bashar yazo min dashi yanzu don Allah a hada min kafin na fito don yau a gajiye nake da safen nan fa na shigo kasan nan ban huta ba na kamo hanya don nazo na gan ku.
Ai ka kyauta inji Maji.
Ya ciro wayan shi ya kira Bashar yana sheda mashi ya kawo mashi fruits masu kyau yanzu za ai mai amfani dasu ne.
Bashar yace kai nifa yanzu ina hanyan dauko madam dina daga saloon ne kakoga bukin magaji bai hana na magaiya.
Kai dai kasani nidai na fada maka yanzun nake so kada kaje ka tsaya bakin I love you din ka can.
Dariya Bashar yayi yace kai da baka san shi ba ai sai kaita zama ta zuru kana sa yara aiki.
Watsewa zasuyi soon su barka da maji muga tsiya tunda ka zama tsohon tazuru.
Murmushi yayi, kawai ya kashe wayan, saida ya mike yake cewa wai ina wanan sodan yau ta tafi, maji tace maryam ke nan ko?
Yace ita fa ban ji motsin ta bane tunda na shigo gidan.
Ta tafi gurin gyaran kai dazun yanzu nasan ai tana hanya kila.
Yafice daga dakin a gajiye dashi uwar tabishi da kallon sha,awan yadda taga ya koma mata yazama wani babban mutum yanzu a idon ta kamar ba sadauki ta mai tabara ba.
Maryam ce ta shigo dakin da ledojin fruits da murnan ta tana ina yayan yake tana wani dube dubbe da idon ta ko ina.
Ya tafi wanka inji Amirah ta bata amsa tace yakawo muna tsaraba ne ?
Kai haba anty daga dawowan mutun baiko huta ba kina tambayan tsaraba.
To na hana ko zaki hana kuma ya bamu tsarabane yar gidan mugu.
Murmushi nayi nace ni a suwa?
Rufamin asiri na zauna da Fatima Bintu takafin kisa a canza min suna Binta munafuka.
Dariya tayi tace yanzun ko indai yayane baida wuya ajiku da dawowan shi nace yaushe kuma ai har ya fadi ko.
Murmushi mama tayi tace ni na,rasa wanan munafuncin da,sadauki ke kirawa ya ta.
Nace mama ni nasani barshi kawai inko don wanan ne ko gobe yayi shi sai nai mai munafunci.
Eyye wallahi maji wuyar yar ki yai kauri haka ashe yanzu yaya sadauki kik fada wa hakan ai kin fi kowa sanin halin shi dan kafan ki kawai ya taka amma kika ishi mutane da ihu,
Nace wallahi anty ban ma son na tuna don ba karamin wuya nasha ba a gidan nan.
Muna jin shi ya kara shigowa amma wanan karon ba dakin mu yazo ba cikin gida ya shiga gaida sauran iyayyen shi.
Duk da su diyan su basu zuwa gaida mama sai Sagir ne mai kokarin hakan cikin su don shi gaskiya daban yake a gidan sabodashi uztaszu ustazu ne haka.
Tare da Bashar suke ashe sai da suka shigo falon mu ne muka san da hakan,
Maryam da bata gan shi ba tafito da saurin ta gudu gudu tana fadin yaya sadauki ashe kana hanya bamu sani ba cikin murna da fatin cikin ta.
Ganin tare da Bashar suke yasa ta dan rage rawan kan da takeyi sai naga tawani noke cikin kunya ta dan boye bayan kujera tana fadin.
Yaya har fa wata biyu kayi da tafiya, gaskiya mu ka daina dadewa haka muna missing din ka sosai wallahi.
A hankali yace maryam nasan ai ba komai kikewa wanan tambayan ba sakon ki ne kuma ban sayo ba tunda ko murna baki min ba.
Tace wallahi yaya aiko nafi kowa murna tambayi maji kaji har party nai muna ranan ai nace ke dawa kukai party ?
Lalai ma Bintu sheri zaki kulla min don ki hanani samu wallahi na gane shiyasa yaya ke ce maki yar hana ruwa gudu.
To anty wai yau kuma lafiya naga kin wani boye bayan kujera kamar wata mara gaskiya kifito fili mana kowa ya gan ki .
Murmushi Bashar yayi nace sai cika bakin karya amma kina ganin yaya Bashar kin wani boye can bayan kujera to mun dai san komai mu dai ayi buki musha shagalin mu ko Anty Amirah?
Munafuka kawai wallahi yaya na yarda Bintu munafuka ce da gaske shegen saka idon tsiya gare ta kamar wata yar sandan ciki.
Wait, may naji wanan yarinyar na fadi ne wai kai mugu ashe ka zama dan akuya ne haka ban sani ba.
Dariya Bashar yai mashi yace akan may don ina son kaunata ko may kai wa ya hanaka fitar da naka sai wani kwanaye kwanaye kake wa kan ka abari ya huce dai shike kawo rabon wani.
Na kawo masi salad din sosai suka sha shi sai santi Bashar keyi yace kai mutumina kace min ka huta kawai.
Fuskan shi a daure yake bashi amsa a zazafe yana fadin wallahi zamu bata dakai idan kaja min matsala da raini Allah Bassh.
Wayan shi da aka kira ne ya katse masu challenges din junan su da,sukeyi.
Sai da ya ja dan tsuki yace ya akayi ne cikin daure fuska da mace yake wayan kuma tambayan shi take yau she zai dawo ne wai ?
Yace yau fa nazo gida shine kike tambayana yaushe zan dawo ko ganin mumm ban gama ba ki dai bari zan kiraki idan na fita.
Daga inda muke zaune sai naji wani dan abu kawai a raina ban dai san dalilin jin hakan ba.
Shiko yana kashe wayan yana dago kai inda nake zaune yana fadin ke zo kwashe kayan nan kada wanan mara kunyan ya cinye kwanonin gaba daya.
Fuska na yana a hade take ya fahinci ban cikin good mood a lokaci guda na koma haka to why ?
Sai muryan yaro ya ratso a kofan falon mu yana fadin wai Usman yana wa Fatima sallama a waje.
Maryam tace ga mr love lover din ki can ya iso nasan sun taso ke nan yazo ya damu mutane.
Na yunkura ina fadin babu ruwan ki anty ba dai ke yake damu ba ai, lah yanzu Bintu rashin kunyan naki har yakai haka a gaban su yaya zaki fice I love you ba kunya.
Sai ga mama tafito daga ciki tana fadin ke Fatima kin bar waya a daki sai faman ruri take ita kadai.
Na karbi wayan a hannun mama naga Usman ne nasan yakira ba,a dauka ba shine ya aiko yaron.
Hijjab din Amirah dake kusa na jawo na saka a jikina ina gyara wuyan hijjab din naji yace .
Ke bana ce ki kwashe kayan nan bane ina zaki haka kuma ?
Sai ga yaron ya dawo yace wai yace don Allah tazo yanzu yana sauri ne an kusa yin sallah.
Nace kace mai gani tafe yanzu don Allah.
Mikewa yayi kamar zasu fita shi bai fita daga kofan ba bai shigo ba ma,ana ya tare hanya ke nan ga Bashar daga waje tsaye yana jiran shi.
Na fito daga kitchen na gan shi a gurin tsaye a dan raunane nace zan wuce.
Tankar da dutse nake magana don ko motsi baiyi ba .
Ganin haka na dan jingina jikina

Please Login or Register in order to submit comment