Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuna lafiya yaya mutanen gida tace duk muna lafiya.
Yusuf dama kan zancen da kukayi da yarinyar nan ne nake son maka magana .
Yace mama idan wanan zancen ne ni na gama magana na ba hannuna acikin wanan magana.
Har yaushe ta haihu da zata dauku tashin hankali tasakawa ranta haka ?
Uwar tace na sani Yusuf nasan da haka ai rigimane kawai irin na yarinyar nan don shi ciki ai rabo ne.
Don haka kayi hakkuri abar wanan zancen don bana son ko mahaifin ta ya san da wanan zancen haka.
Don Allah kayi hakkuri kasan halin kowa da irin nashi tunanen hakan yana damun tane yasa take wanan haukan haka.
Inji Saade ke bashi hakkuri bayan sun gama wayan da mahaifiyar hindatu din.
Yace ba komai bane ke jawo min haka sai wullakancin da sukaga daddy da hajiya suna min akan su amma yarinya zata gane kuren ta wallahi.

****** ********* ******
Mama ce daki da baba cikin tausan murya take cewa yanzu malam haka zaka bari wanan daman ya wuce mu a gidan nan.
Allah ya rufa maka asiri sai masu hannu da shunin gari ke zuwa neman yar nan don sa, an ta.
Amma ita da uwarta basu fahinci nasaran haka ba don basu da fahinta akai.
Wancan auren da tayi da suka samu dadin su da wasu kaci ko wanna ma idan yai dadi ai sune zasu ci abinsu muna kallo.
Dadin baki mai ratsa zuciya mama kewa baba kullun akan maganan tun bai yarda ba har takai ya amince da zancen ta ya shiga zuciyar shi ya zauna daram ya kafe zai ba Jatau ni.
Ko ina so ko ban so dole ne na amince da zabin shi tunda shine keda Alhakin zaba min miji ai.
Ranan da baba ya koma dakin Inna sai gashi ya fito mata da zancen wai maganan Rahama da Jatau fa yana nan don haka sai ku fara shiri akan aure nan bada dadewa ba za, ayi.
Take ran Inna ya baci idanuwan ta sun sauya launi cikin bacin rai take cewa .
Malam da ba dakai na haifi yarinyar nan ba sai nace kana hassada da ita ko kiyayya don irin kiyayyan da kake gwadawa yarinya yai matukar yawa a gidan nan.
Yanzu kai ko kunya baka ji garin nan aji zaka kara aurar da yarinyar nan ga wani tsoho don kudi don abin hannun su kukewa kwadai.
Yanzu Asiya ni kike kallin idona kice saboda kwadan abin hannu nake aurar da yarinyar nan.
Inna ta ma rasa may zata ce da shi saboda takaicin daya rufe ta a lokacin.
Cikin bacin rai take cewa ai ba karya na fadi ba don duk wanda ma yaji haka yasan abinda kukewa ke nan.
Yanzu wancan auren abinda ta samu wa ya amfana dashi ba kai ba ina gidan ne kawai kila zata tsira dashi.
Don haka wallahi wanan karon bazan yarda da cin zalun din yarinyar nan da ake muna ba.
Har nawa yarinyar nan take da za, a dinga mata haka ina ga yayyin ta nan zube a gida su ko zancen su ba ayi.
Yace to tunda kin isa da ita duk matakin da zaki dauka kan wanan zance sai ki dauka mu gani tunda kin isa ke .
Wasa wasa magana har takai ga daga murya tsakanin su sai ga mama da ta dade tana sauraren su ta saka baki daga waje tana fadin
Malam kada ka biye mata kasan va hankali ke ga Asiya ba don son abinda yarta ke so ya rufe mata ido bata hangen abinda kaje ya dawo.
Cikin fushi baba yace mata ki kyale ni da ita Lauratu wallahi Asiya kin yi karya dake da yarki ku mai dani mutumin banza a gari.
Duk iskancin da budewan idon ku da kuke ganin kuna dashi yanzu baku kai ni ba don haka ku ci gaba da min rashin da, a ke da yar ki ku gani a gidan nan.
Indan kunce haka kuka dauko sai kun kwammace rashin zaman ku gidan nan dani.
Kallon shi Inna tayi shekeke tace dashi ai kasan kaine keda rayuwan mu a hannun ka .
Indai kan wanan zancen ne sai dai ajimu don nai magana akan hakkin ya ta ai ba haramun bane ko ?
Kuke samun riban auren da takeyi shi yasa kuke son kara tursasa mata sai tayi wanan din taje ta ciwo maku kasuwa gidan.
Duk masifan baba yana ganin ta haukace mai sai jikin shi yai sanyi yasan duk yadda akayi akwai abinda ta digora dashi take hakan don ba halinta bane haka.
Aikin banza inji mama tace may ye bamu sani ba wani dare ne kuma jemage bai gani ba.
Auren da sai anyi kifi kowa zakewa da jin dadi shine har za, a tsaya ana muna tijara akan shi.
Malam ka kwantar da hankalin ka kana nan zakaga yadda take rawan kafa da jiki ita a dole yarta ta samu gurin zama.
Idan ni ban yi rawan kafa ba ai ke sai kiyi tunda ke ma kina da yaya dakin ki sai ki bashi daya daga ciki a wuce gurin.
Tana fadin haka ta koma ta kwanta abinta tare da watsawa baba harara tana fadin don an mayar dakai haka bari a turo ka kai min cin mutunci ko.
Tun ranan da akai fadan nan ina wuta mama da baba su jefa mu ni da Innata.
Duk wani kule kulle da makirci shi mama take kullawa akan zancen sai cin kudin Jatau takeyi tana bushashan ta a cikin gida ita da diyan ta kawai.
Duk wani hanya da baba zai fahinta mama ta toshe shi har yakai ta fara dan fita zuwa gurin malaman ta wai a kulle muna baki duk mu ukun sai abinda tace kawai za, ayi.
Haka Inna take cikin tashin hankali kan zancen don ta fahinci idan bata yi da gaske ba babu makawa sai anyi wanan auren gamin gan bizan dani da Jatau.
Kullun tana hanyan gidan mama Altine kan magana daya duk tafita hayacin ta.
Gashi mama taci kudin shi yakai dubu ashirin da biyar tana karba wai tana bani tana kuma kamun kafa da sauran.
Bata san cewa komai nashi a lissafe yake mai ba don ba mutun ci ne dashi ba akan dukiyan shi ko kusa bai taka kafan Alhaji Garbati ba gurin tara abin hannun shi ba.
Amma mutane don baya ci sai suke gani yafi garbatin ma tara dukiya a garin.
Wata rana ina fitowa zan shiga gidan mama sai ganin shi nayi a kofan gidan mu don kusan a nan yake wuni.
Yana gani na ya fara washe baki ya na dan soshe soshe kamar mara gaskiya.
Ya dan tafo duduke kusa dani yana cewa a, a mutumiyar barka da fitowa ashe yau nazo a sa, a zan gan ki ashe ?
Wani kallo nai mai nace yauwa sannu baba .
Yayi dariya hakoran shi da wanda babu da rinanun sauran dake cikin bakin shi suka baiyyana a fili.
Cikin dariya yake cewa ai ni yanzu ba babane gurin ki zaki dai iya kira na da ango ango mai shirin shan mai ko ?
Nace tau ikon Allah baba aure ne zakayi halan ?
Kallon mamaki yai min yace kamar yaya kike tambayana haka kamar baki san da zancen ba kuma.
Na dan fadada fara, a na nace ban ko sani ba baba a ina kasamu matar ke nan ?
Yace ikon Allah gaki tsaye a gabana kike min wanan tambaya kuma ai ni yanzu nan da kika ganni jira kawai nake a shafa a tsakanin mu don har dukiyan aure na biya ko jiya.
Nace amma bakasan wace ka biya dukiyan akan ta ba ko don bani bace kake zance akai.
Ya sake kallona cikin mamaki yace ai ko ke din ce nan da sati biyu insha Allahu zaki tare a gida .
Dadai kin dan tsaya mun fahinci juna naji dan naki tsare tsaren don kin san shi marigayi garbati ya riga ya shagwabaki so sai.
Ban tsaya sake sauraren shi ba kada ya kara jefani wani sabon damuwa na shige gida abina na barshi nan yana kwala min kira kamar wani tsohon maye.
Na samu inna ta a waje ganin yanayin da na shigo gidan ciki yasa ta barin abinda takeyi tabini daki.
Ta samay ni zaune nayi tagumi sai hawaye nake zubarwa a idona babu sautin kuka.
Hankali a tashe take tambayana ke kuma da kika fita yanzu cikin dadin rai may ya dawo dake gidan haka ne kuma ?
Na dago idanuwa dake zubar da hawaye ina cewa Inna kinji mutanen nan ashe wai har sadakina baba ya karba hannun Jatau.
Cikin mamaki Inna tace yaushe akai hakan bamu da labarin komai akai nan dai ina kuka nake fada mata yadda mukayi da Jatau din dana fita.
Inna ta zuba min ido cike da tausayina domin tasan irin zafin da nake ji a lokacin take cewa.
Yarinya ki kwantar da hankalin ki insha Allahu ba a wanan auren idan kinga anyi shi sai dai bana raye.
Bari yanzu naje naga mamakin mai kuli musan abin yi tun kan mu makara akai.
Koda hakan na nufin rabuwa na da mahaufin ki ne sai dai mu rabu amma ba mai maki dole akai indai ina raye .
Na gaji da wanan mulkin mallakan da ake muna a gidan nan ya Isa hakana wallahi zasu gane basu da wayo wanan zubin.
Gidan mama ta fada muka shiga kusan tare a lokaci daya yadda mama ta gan mu tasan ba lafiya ba.
Nan Inna ta shiga zaiyano mata duk halin da ake ciki itama dai fada ta shiga yi da tsinuwan mama lauratu tana cewa.
Wanan karon saidai abinta ya koma mata amma Allah bai basu ikon yin hakan a kanki.
Mafita daya ne idan zaku iya da dare muje gidan maigari mu samay shi mu fada mai abinda ke faruwa don asaka ma abin waigi tun wuri.
Inna tace may zai hana ni zuwa indai zaki kaimu mai kuli ai mu mafita muke nema tako wani hanya indai hakan zai samu.
Kamar yadda suka shirya dare nayi Inna tace zata shiga gidan su ta gaida wanta da baida lafiya.
Lokacin ni dama ban dawo gida ba ina gidan mama Altine don anan zan kwana
Akai sa, a baba bai hana ba don dama yana son zasuyi magana da mama kan zancen auren gashi kuma kafa ya samu.
Inna na zuwa muka wuce zuwa gidan maigari mun samay shi yana cin abinci muka gaisa dashi da iyalin shi cikin mutum ci.
Sai da ya idar muka isa gurin shi nan mama Altine ta koro mai duk halin da ake ciki dani.
Ya kurkure baki tare da watsar da ruwan gefen shi yana cewa kai amma malam Audi baiyi ba wallahi.
Don ma dai Allah ya hada shi da yar aziki ne ya samu tai mai biyayan akan na farko yanzun kuma shine yake son lakaka mata wani.
Kada ku damu dama mun samu wanan dokan daga birni cewa babu auren dole ga yarinya ko yaro yanzu wanda kuma ya karya doka tara mai tsanani a kan shi.
Don haka kutafi gida gobe da safe insha Allahu zan nemay shi muyi magana dashi.
Mukai sallama dashi muka barshi yana fada yana cewa wasu mutane basu san ciwon kan su ba wallahi ko.
Ina jatau ina yarinyar nan ina zai kaita duk yadda zan fahintar da mahaifin ta illan abinda hakan zai haifar zanyi idan ya kiya kuma nai karan shi.
Hakan matan shi suka ci gaba da bashi labari akan zaman da Inba take a gidan dafin karfin ta da mama take a gidan tana mata mulki kama karya.
Tun da farar Safiya ake kwasa sallama a kofan gidan mu baba ya fita ganin ko waye ?
Sai yaron mai unguwa yagani nan yake fada mai ana neman shi a fada hankalin shi yai matukar tashi sosai don idan akwai abinda dan kauye yaki jini shine kiran maigari.
Yashigo gida hankali a tashe yana fadin zashi gurin mai gari yanzu yaron mai unguwa yazo yace ana neman shi gidan mai gari shida mai unguwa.
Mama hankali tashe take cewa to may kuma ya faru ko anyi wani abin ne kuma.
Bai tsaya bata lokaci ba yafita gurin amsa kiran inda mai uguwan mu yai mashi jagora har gidan.
Bayan an gaisawa ne maigari ya gabatar mai da zancen karan shi da aka kawo kan yana son yiwa yar shi kuma bazawara auren dole da Jatau.
Sai da wani uban zufa ya karyowa baba yana gyara zaman shi cikin kwantar da murya yake cewa.
Rankaidade ba haka na bane ba wai auren dole nake son yi mata ba ita da uwarta ne dai basu fahince ni ba.
Take dattawan fada suka katse shi da cewa shin yarinya ta yarda ko bata amince ba akan auren.
Sai baba ya dukar da kan shi kasa yace a gaskiya ba ra, ayinta bane nawane dana iyayyen ta hakan.
Iyayyen ta uwar da ta haife ta ko wa kokai da yan uwan ka ke da wanan danyen hukuncin akan ta haka ?
Shiru baba yayi don ba amsa sai lokacin maigari ya karba dacewa ko wancen auren na farko dakai mata mun so mu hukunta ku amma sai muka duba shi garbati mutumin kirki ne zai iya rike maka ita amana.
Amma Jatau ko mutumin banza mutumin da bai san darajan kowa ba a garin nan sai kansa.
Babu wanan zancen yarinua dai bazawara ce abarta ta yi zabinta da kan ta dan doka yanuna yanzu ko budurwa ce idan bata son aure kada ai mata dole balle bazawara da tasan ciwon kan ta ko.
Fada sosai akai wa baba ya baro fada sai dai maigari ya boye mai cewa Inna ne da kan ta ta kawo karan shi yadai ce makwabtane suka zo suka fada mai wanan labarin .
Shiko a matsayin shi na maigari yana da ikon karewa yaro da babba hakin su idan za, a cuta masu.
Wanki nake yi kafin na shiga gidan mama Altine ina dan rarage kayan daudan mu ni da kanne na da Inna baba yadawo.
Kana ganin shi kasan babu lafiya tare dashi lokacin Inna ko har ta shirya tana jiran cin mutuncin da baba zai dawo mata dashi daga gidan mai gari.
Yana shigowa mama najin sallaman shi tai but tafito daga daki tana fadin malam lafiya dai ko wanan kira haka tunda sassafe haka ?
Yace lokacin da yake zama saman dutsen dake tsakar ana alwala a saman shi bari ke dai Lauratu munafunci baiyi ba wallahi.
Wai yanzu aka samu munafuki a cikin uguwan nan yakai karana kan auren yarinyar nan da Jatau gurin maigari.
Gaban mama yai mugun faduwa tace kara malam wake da wanan aikin haka yace wayasani yadai ce daga uguwar nan namu ne akai karana gurin shi.
Affan malam wa zaiyi karan ta inba ita da uwarta ba kaiwa kake tsamanin zaiyi haka waya damu da damuwan su anan balle ya kula al, amarin su.
Umm, umm lauratu daga nan ne dai aka fadawa maigari amma ai mace bata ganin mai gari kai tsaye wane ita nan.
Nan suka shiga dura ashar har mama na ikirarin ai ba maigari ne ya haifa mashi ya ba da zai mai iko akan gidan shi.
Baba yace Lauratu na rabaki da wanan zancen kada ki dauko min wani sabon rigima kuma don ni yanzu tsoron mutane nake ji su labe ta baya suna sauran ki.
Mama tace duk mai fadi yaje ya fadi amma aure ba fashi sai anyi shi tunda bashine ya haifa muna diya ba ba kuma cin shi a gidan mu.
Baba ya katse ta da cewa kina da kudin biyan taran da za ai min ke nan ko da kuma dauri kan na shiga hakkin diyata bada son ran ta ba.
Cikin mama ya duri ruwa sai da ta kewaya ban daki tafito ta samu baba a gurin yana fada har lokacin.
Nidai ina wanki na tare da hamdalla a cikin rai na don maigari da mama Altine sun ceci rayuwana ko ba komai sun kwato ni da shiga bani.
Inda nake ina buga zanin da zan shaya mama ta kalla tare da cewa tir dake Rahama kinyi hasara wallahi tunda akan yi yau akai karan mahaifin ki har gurin mai gari sukutum.
In yar arziki kike kin haihu cikun malam yau kije kice wa maigari da miyau bakikin ki za ai wanan auren.
Ban kula ta ba illa idon da suka sako min daga ita har baba din a lokaci daya.
Ganin bazan taka masu ba ne baba yace ai in taki wanan auren nikan ba dai gida na ba wallahi don ba zan zauna da ita ba haka ina ganin bakin ciki a raina.
Fat naji muryan Inna a bayan mu tana fadin a hayye nanaye wanan hukuncin yau yafi nono fari a gare mu don na dade ina jiran anan ranan dama.
Idan baka zauna da ita ba a gida don tana bazawara ai zaka zauna da gandan gadan din yan mata suna maka manne da dare a bayan katanga da samari.
Aure dai ne Allah ya kawo muna saukin shi cikin dadin rai Allah kuma yaiwa wanda yakai kara albarka.
Ikon Allah zamani yanzu Asiya bakiji kunyan wanan maganan ba a duniya ana jinki kina guda akan yar farinki don baki da kunya ga idon ki.
Kunya kunya fa kace malam ai kunya ya kaura ba yau ba ga idon Asiya don ka sani don baku so haka ba.
Gida kuma in kace yarinya bata zama maka gida sai dai dani da ita mubar maka gidan ka a tare don ni ban san zaman da zanyi ba kuma ?
Lalai Asiya kin haihu cikin fulani yau kin sheda min kun bar rugga da dadewa tun da idon ki ya kyakyashe haka kan yar farin ki.
Mu zuba dake a gidan duk inda zaku tafi ku tafi badai gidan Audi ba wallahi ba mai min gori kan abinda na fi karfi yazo yafi karfina a gida na.
Inna tace haka yafi nono fari wallahi yanzu kuwa ba sai anjima ba zamu bar maka gidan ka sai ka zauna da wa yanda kake so kajika kasha.
Magana har takai ga makwabta sun shigo gidan namu suna tambayan ba, asi nan baba ya shiga zagin mu dasu yana cewa wai duk munafukaine mu dasu afice a bar mashi gidan shi.
Hijjab dina na jawo daya bushe na saka nafice daga gidan inajin mama nace indai baki auren Jatau daga wanan fitan kin fice daga cikin mu ke nan.
Nasa kai abina na fice ko waigen ta ban tsaya yi ba sai gidan mama Altine ina shiga take cewa dani Allah mun godema da ya kawo muna saukin al, amarin nan.
Ni yanzu damuwa na shine wanan rantsuwan da mahaifanki ke yi sai kinbar maigidan shi ita kuma Inna ki ta rantse kina barin gidan itama ta bari ke nan.
Nace mama nima shine ke damuna wallahi don bazan so ace saboda ni Inna ta bar dakin auren ta ba akaina.
Zafin raine ke damun su dukan su daga ita har malam Audi din suna cikin bacin rai ne.
Muna nan muna magana sai jin hayaniya mukayi ya kaure a kofan gidan mu da sauri mama ta yafa tafita daga gidan.
Jatau ne yazo ya zauna yana cin mutunci wai kamar shi za, a tozarta a gari ai karan shi don yace yana son .
Indai har ban son shi nafito na bashi kayan shi da naci don shi bai gaji hasara ba akan shi.
But nafito daga gidan mama nace dashi dakata malam ga mutane sun taru wasu har a zanan gida matan aure ke lekowa ta kafan zanan gidan su don gulma.
Nace tsakani na dakai ko uwa ta ka taba ba mu ko kwandalan ka a hannun mu idan dai ka taba ka fada min yanzu na biya ka abinka.
Sai yadan washe baki yace ni da zaki yarda ki amince ai da babu zancen biya a tsakanin mu.
Amma ace ba a bani mata kuma a ci min dukiya na ga banza shine ba zan lamunta ba gaskiya.
Nace to kayi da wanda kaba kudin ka don ni ban san ka raba bani komai ba, muryan mama Lauratu naji daga ta cikin gida tana cewa tau mara kunya idan ke baki ci ba ai mu iyayyen ki munci don nai amfani dashi gida kowa yaci.
Nace kin dai ci ni tundana dawo kin taba girka abincin ki kika bani a gidan nan ko kiba kanne na sai naji tayi shiru nan mutane suka saka salati yan gulma suka hau bakin su.
Aka shiga zuga shi na shige cikun gida abina na barshi nan yana haukan shi shida yan kallin shi.
Nasa kafa zan karasa ciki naji muryan mahaifina cikin kakausar murya yace dakata nan Rahama badai gidana ba wallahi nai maki itaka da gida na daga yau duk inda zaki kije nayafe ki.
Inna dake daki tagama hada kayan ta naga tana fitowa da buhuhuwan data dura kayan ta a ciki.
Nan na duka nafara rusa wani sabin kuka zuciyata tana raya min nace kawai na amince da wanan sabon kaddararen auren akaina kada uwa ra ta shiga wani hali saboda ni.




ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
[16/12, 00:22] Maryam Ummu Firdausi Group Ismail: IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , ,


IDAN KIN BIYA KADA KI TURAWA WANDA BAI BIYA BA KI TUNA DA AMANA NE HAKAN A TSAKANIN MU , , , ,


Ina duke a gurin naji an dafa ni mama altine ce a bayana take fadin taso daina kuka haka zo mu shiga gida wanan tonon asirin haka da may yai kamane wai ?
Ban kiba namike na bita sai ga yara na shigo da kayan inna ta gidan buhu har uku duk na komatsen ta ta hada ciki.
Ba a jima ba tashigo gidan ran ta abace sai dai kana ganin idon ta kasan ranan ba sauki sai na Allah.
Nan mama ta shiga bata hakkuri akan ta zauna amma tace indai ba zai barni gidan shi itama may zata zauna yi a gidan.
Dama don ni da kanne take zama badon wani abuba don haka bazata koma ba sai idan nima ya mayar dani gidan.
Nan dai abu ya yamutse daddatawan unguwa duk sun taru suna ba baba na baki amma ya kyakyshe kasa yace bai san zancen ba tunda mama da tai jagoran ci muke son tozartawa.
Magana zabban kunya yadda baba ke magana kai daji kasan an fi katfin shi.
Shi dai jatau anbashi hakkuri akan cewa ya bari a sulhunta maganan nan da sati daya za, a nemay shi insha Allahu.
Sai dare Inna ta nufi gidan su can taiwa mutanen gidan su bayani suka ce ta zauna suma halin gidan ya ishe su haka na.
Magana har gurin maigari ya koma kan fitinan gidan mu aka kira babana aka bikon Innata amma yace shi ba zai tafi ba kuma zancen Rahama ya yafe ta cikin zurian shi.
Ba, a watse gurin ba sai ga Jatau yazo kan zancen kudin shi yace yai lissafi har sadakin shi dubu sittin yaba

Please Login or Register in order to submit comment